Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK



_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 3️⃣0️⃣➡️3️⃣1️⃣


Lafewa tayi a jikin sa tana sauke ajiyar zuciya, hannun sa ya zuwa bayan ta yana shafawa, zuwa can kamar wacce ta tuna da wani abun ta zabura ta Mik'e daga jikin sa ta sauka saman gadon, ta bud'e wardrobe d'in ta ta d'auko zane ta d'aura,

Tun da ta sauka yake kallan ta, ganin ta kama hanyar fita ne yasa sa saurin cewa " Ina zakije? " Wanka zanyi " ta basa amsa a tak'aice " jira ni nazo muyi tare" Ya fad'a yana k'ok'arin sauko wa

Ko kafin ya sauko harta fice da sauri da d'auki boket ta d'ibi ruwa tayi toilet tana shiga tasa sakata tarufe, koda ya fito d'aure da guntun towel a k'ugunsa ya nufi toilet d'in, yana zuwa ya tura yajisa a gark'ame k'wank'wasa wa yayi a hankali tana jinsa tamasa banza, shi kansa yasan tana jin sa ganin tak'i bud'ewa yasa ya koma d'aki ya jira ta harta fito shi ya shiga



Falo ta tarar dashi zaune bata ko kalli wajen da yakeba ta wuce ciki, Mik'e wa yayi ya fita dan tsarkake jikin sa

Tana shiga ta d'auki guntun towel ta zane ruwan kanta tayi kwanciyarta hannun ta dafe da mararta tanajin ta k'ulle mata ga ciwon da take mata sama_sama, bacci yayi awon gaba da ita,

Koda sadik ya shigo bata ko sani ba ta dai ji yana tadata ta tashi an fara sallah, sannan ya wuce masallaci, ta Mik'e taje tayi alwala tayi sallah takoma gado dan wani irin bacci takeji sosai


Cikin bacci taji ana shafata, bud'e idanuwan ta tayi da suke jajirr cike da bacci ta zube su saman face d'in sadik, suna had'a ido ya sakar mata murmushi, gimtse fuska tayi ta tashi zaune tare da fad'in "Lafiya dai ko? " Qlau ina buk'atar k'ari ne" ya fad'a tare da kashe mata ido d'aya, wani kallo ta watsa masa tare da fad'in " Dan Allah ko kunyar ma fad'ar wannan kallar bakayi ba " Kamarya? " Auu kamanta abun da ka fad'a kenan nida ba haihuwa zanyi ba miye amfanin mu'amalartarta gwaunda kaje inda kasan idan ka zura gugarka zaka janyo ruwan da zasu anfaneka har ka samu k'aruwa ba wajen da bazaka samu komai ba" khadija wai ke magana bazata wuce a wajen ki ba ne " Wace maganar zata wuce a wajena ? " Ta fad'a tare da k'ara kallan sa idanuwan ta cike da hawaye


" Kai a tunanin ka wannan maganar zata wuce a wajena abun da ban ta'ba tsammani zakamin ba sadik da ace wani ne yazo ya fad'a min zaka iya bud'e baki ka fad'i wannan furucin akaina wallahi zan iya rantsuwa da al'Qur'ani nace k'arya ne amman sai gashi ido da ido ka bud'e baki ka fad'a min wai har kace ina maka hassada da bak'in ciki" Ta k'arshe maganar tare da fashewa da kuka, jikin sa yayi sanyi sosai yasa hannu zai ta'ba ta, tayi saurin d'agowa tare da girgiza masa kai kana tace " Wallahi karka kuskura ka ta'ba ni wallahi bana ma san ganin ka kusa dani 😩 katashi ka tafi" Subhanallah khadija kin san kuwa me kike fad'a? " Ni ko nasan me nake fad'a idan baza ka tashi ba ni bara na tashi na baka waje" ta fad'a tana k'ok'arin tashi, ya dakatar da ita ta hanyar cewa " Kiyi zaman ki ni bara na tashi " Ya sauka saman gadon ya nufi falo yayi zaune saman doguwar kujerar falon ya dafe kansa maganganun ta na masa yawo a k'wauk'waulwa




Yana fita taja tsaki tare da gyara kwanciyarta taci gaba da bacci




Washe gari haka suka wuni ba mai cema d'an uwansa uffan gwauda ma sadik yana mata magana ita ke kyalesa abun na damun sa, da dare haka suka kwana tana ciki yana falo


Yau ta kama girkin samira khadija sanin samira ba girkin zata musu ba yasa tasa ayo mata awara d'anya ta kwano d'aya aka kawo mata, tabayar aka siyo mata rabin kiret d'in kwai da kayan ciki, raba awarar tayi biyu tasaka rabi cikin fridge rabi kuma ta yamutse ta fasa kwai guda bakwai ta zuba akai tasa magi da kayan k'amshi da tarugu da albasa ta d'auki kayan cikin da aka siyo mata ta tafasa ta zuba akai ta motse su sosai suka shiga cikin awarar, ta zuba mai kad'an aciki yarda idan ta saka a leda bazata kama ledar ba, ta d'auko ledar ta fara ta k'ulli ta rik'a d'aura awarar a ciki sai da ta d'aure duka, ta bud'e tukunyar ruwan zafin ta dake kan wuta ta juye awarar a ciki ta koma ta samu roba ta k'ara fasa kwai biyar tazuba tarugu da albasa da magi da kayan k'amshi wad'an da zasu kashe garnin kwain ta kad'a, sannan ta ajiye


Zuwa 20 mints ta sauke tukunyar, ta kwaushe awarar, ta had'e sosai kamar alale kwai ya shige jikin ta tayi kyau sosai, kunce ledar ta riga yi bayan ta gama ta fara yayyanka awarar tana manyan yanka, bayan ta gama ta d'auko tallen suyar ta ta d'aura akan wuta ta zuba mai a ciki sai da yayi zafi ta d'auko awarar tana zubawa cikin ruwan kwai tana soyawa, nan da nan gidan ya d'au k'amshin dad'i samira na d'aki k'amshi ya kaima ta ko yaya ta fito tayi zaune tana had'iyar yawu tana lek'en talle, khadija da ta gama sauran kwain da ya rage tayi masar kwai da ita, ta d'auko kula ta zubama mama ta kai mata samira na zaune tana jiran ita ma a zubo mata nata, taga khadija ta tattara kayan ta takai d'aki, kayan da tayi amfani dasu ta had'a ta wanke ta share wajen ta gyara komai, ta d'ibi ruwa tayi toilet dan yin wanka da niyar idan ta fito sai taci




Tana shiga samira na nan fake da ita sai da taji saukar ruwa alamun ta fara wanka Sannan tayi d'akin khadija, duddubawa tayi can ta hango kular ta saki murmushi tare da nufar wajen ta bud'e kular ta fara ci


Khadija na fitowa daga wanka sadik na shigowa, " sannun da zuwa" ta fad'a tare da wuce, bayan ta ya biyo kusan a tare suka shiga d'akin tsaye suka ja ganin iKon Allah samira durk'ushe gaban kulla aka shiga kallan_kallan " Jar uban can" .....................................................


🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK


Ina ma kowa barka da sallah ubangiji Allah ya nuna muna wata shekarar lafiya, Eid Mubarak 🩷 kar a manta da mar'atussaliha 🧕☺️ sannan aci nama ahankali kar a b'arke🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Ahhh to

_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 3️⃣2️⃣➡️3️⃣3️⃣

"Jar uban can" Khadija ta fad'a tare da k'arasa shigowa d'akin ta rik'e k'ugu, samira tayi zumbur ta Mik'e tsaye tana lasar faratan ta " Wallahi tallahi yau ko sama da k'asa zasu had'e sai kin biyani kayana iyyeee lallai ma matar nan ko tsoron allah bakyaji nagama wahalar girki na kizo ki shige d'aki kiyi zaune ki bud'e kula kiyita ci kega mai abu ko wato haryanzu baki sanni ba but kar ki damu zan nuna miki truer color ta wallahi sai kin biya ni kuma nawa nake so nawa wanda na had'a da kaina bana buk'atar na wani"

Sadik ya d'an matso tare da fad'in"Khadijjj" wani irin kallo ta watsa masa wanda yasa sauran maganar tak'ewa kana tace " Kar ka kuskura ka tsoma min bakin ka cikin magana wannan maganar bata shafeka ba kayi gum da bakin ka idan kuma bazaka iya ba ka fita dan allah" haba kema kinsan hakan bazai yuwuba"To shikenan wallahi duk abinda nama kai ka jama kan ka "Wai Khadija miyasa gabaki d'aya bakya jin magana ta ne nace bana son fitina da tashin hankali a gidan nan ki fad'i nawa kika kashe a biya ki"



Cikin jin mamaki da takaici da Khadija ta zuba masa ido tana kallan sa har ya kai k'arshe" iKon Allah ohhhh wato nice ma na tada fitina lallai ma mutumen nan ita da ta d'aukarmin ky baka mata fad'a ba sai ni da aka yima " ta k'arashe maganar zuciyar ta na wani irin zafi,

Cikin zafin nama ta isa wajen samira, da isar ta bata tsaya wata_wata ba kawai ta shak'o wuyan ta, ta wanka mata mari tare da fad'in "Wallahi yau duk uban da yamiki tsaye inba allah ba sai kin biyani kuma sai kin amayo ta " Khadija! Khadija! Khadija! " Sadik na kiran sunan ta ko sauransa bata tsaya yi ba, fita yayi daga d'akin yayi 'bangaren mama dan tazo ta rabasu tunda shi bata jin maganar sa, samira duk da wannan uwar shak'ar da taji ga kuma naushin da take mata hakan baisa taji wani azaba ba saima k'ok'arin kai hannun ta da take ta kwance zanen khadija, ganin hakan yasa khadija ta d'auke ta sama ta zubar k'asa tabita ta haye duka take kaimata ta ko ina, wani duk'a da ta kai mata yasa sai da ta saki wata uwar k'ara hawaye ta zubo mata gefen face ta damk'i wuyan ta da kyau nan da nan ta fara kakarin amai khadija tasa hannu ta danne bakin ta janyota waje giririiiiiiii ta jefar, ai kuwa ta shiga kwaura amai duk abincin da taci sai da ta amayar da shi



"Subhanallah, sadik ya fad'a suna k'arasowa tare da mama, sannu ya fad'a tare da dafa ta ya kawo mata ruwa ta wanke bakin ta ya d'ebo k'asa ya zuba wajen, ya taimaka mata ta Mik'e tsaye




Rik'o ta yayi ya kama hanyar d'akin ta da ita khadija tayi saurin Shan gaban su tare da rik'e k'ugu tace " Bangane ba naga ka jata zaku shige d'aki ba tare da anbiya ni ba "Haba khadija miyasa bakya da tausayi ne ki duba kiga duk abunda taci sai da ta amayar da shi amman hakan bazai sa ki hak'ura ba"Hak'uri kai kasan wannan kalmar ni bansan ta ba hmmmmm kai jimin ma wani ikon allah sadik bazan hak'ura ba sai anbiya ni "


"Khadija, mama ta kira sunanta, ta juyo ta kalleta " Nasan ba'a kyauta miki ba bata yimiki adalci ba itama batama kanta adalci ba amman dan girman allah kiyi hak'uri"Amman mam" Nasani khadija basai kince komai ba kiyi hak'uri ki yafe mata dan allah kinji"Shikenan mama ya wuce " Nagode khadija allah ya miki albarka allah ya nunamin ranar da zaki haifomin yan jikokina" khadija tayi murmushi
Sadik yace "Amin mama da ranar akwai shagal"wani kallo khadija ta watsa masa dashi da matar sa wanda yasa sauran maganar mak'alewa a mak'oshin sa,


Ta wuce tayi d'aki, mama tayi ma samira fad'a sosai sannan ta wuce



Khadija ta sake soya awara amman bata sa kwai ba, sauran wanda samira ta rage ta bama almajiri







Bayan sati d'aya

Khadija ta k'ara kyau fuskarta har wani k'yalli take ta k'ara cika tako ina tayi bullll bullll abun ta gwaunin burgewa, sai dai tana fama da tashin zuciya da yawan ciwon kai ga yawan bacci wanda da bata da irin wannan baccin sosai yanzu har mamakin yawan baccin ta take yi, sadik ya k'ara zaucewa akan ta sai dai har yanzu bata sake bari wani abu ya had'a su ba na tarayya auratayya



Samira har yanzu bata saduba ba akan k'udurin ta na samun khadija





Tun da safe sadik zai fita kasuwa khadija ta fito har ya kama hanya ta kira sa ya dawo " Gani " ka manta ne baka bani kud'in ba? " Kud'in me? " Wanda za'a min lalle"Ohh na manta wallahi yanzu kuma ina ganin kud'in da ke hannu na bazasu yi ba"ya fad'a tare da sa hannu aljihu yana ciro kud'in, dubu da d'ari bakwai ne ya cire dubu da d'ari biyar ya mayar da d'ari biyu yace " Kar'bi wad'an nan basa da yawa kiyi hak'uri dasu nikuma sai na rik'e d'ari biyu tunda yanzu kasuwa zanje" To nagode allah ya k'ara bud'i na alkhairi "Amin ya rabbi kin dai san yau ke keda girki kije ki dawo da wuri kuma yau ba zance d'aga k'afa" Uhmmmmmm" Ni zan wuce" Allah ya tsare "Amin"



Yana fita ta koma d'aki ta fara had'a kayan ta cikin akwautunan ta nasa kuma ta k'ara gyara su cikin wardrobe, ta kwaushe zanen gadon ta ta nad'e, ta fito ta d'aura girki, bayan ta gama ta zuba wanda zata ci ta abincin da tallen tayi 'bangaren mama dashi ta ajiye mama tace "Aah khadija lafiya kuwa naga kin kwauso tallen abinci kin kawo min"Lafiya lau mama fita ne zanyi to kar yara su shigo suyi 'barna "Ai da kin barsa a can ina ga yafi"Aah mama abarshi kawai nan" To shikenan a dawo lafiya"Allah yasa" Amin












Comment and share fisabillilah

🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK



_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 3️⃣4️⃣➡️3️⃣5️⃣

Ta koma 'bangaren su, ta shirya tasa aka kira mata taxi, ta fito da akwautunan ta aka saka su bayan butt, ta dawo ta rufe k'ofar d'akinta ta kaima mama mukullin ta wuce,


koda taje gida inna bata nan ta fita, ta ajiye kayan ta, tayi gidan da za'a yi mata lalle


Kitso da lalle aka yi mata, masu kyau kitson suba manya ba suba k'ananu ba anyi mata style gaba, lallain yayi kyau shima sosai




Inna koda ta dawo ta shiga d'aki ta tarar da akwautuna mamaki ya kama ta sai da ta bud'e taga kayan khadija ne, abun ya bata mamaki ganin kayan ta haka da yawa, yayi zaune tana jiran ta dawo tayi mata bayani




Sadik koda ya koma gida cin abinci bata dawo ba, ransa ya 'baci ya nufi 'bangaren mama can mama ta fad'a masa ga abinci nan ta kawo anan, mama ta d'auko filet ta zuba masa yaci ya tashi


D'akin samira ya shiga tana kwance tana charting da saurayin ta, tana ganin sa tayi saurin kashe wayar gaba ki d'aya, kallo d'aya yayi mata yaga alamun rashin gaskiya a tare da ita sai dai bai ce komai ba kawai yace mata "Khadija bata dawo ba ne? " Eh" okay nizan koma"To yayi " ya fice



Yana fita samira tayi bak'uwa wata k'awarta tazo itama duk sune yanzu ma haka dawowar ta daga wajen wani kenan sun gama shek'e ayar su,


Samira najin muryar ta da sauri ta fito ta rungume ta tana sauke ajiyar zuciya "Wayyoooo my zulyyy kamar kinsan nayi kewar ki wallahi yau zanja ruwa"Hhhhhhh nima nayi kewarki shiyasa kika ganni mushiga daga ciki kar abokiyar zaman ki tajiyo me muke fad'a " Bata nan ta fita bare kuma ko tana nan taji mu ba matsala bane "Auu haba kice itama d'in y'ar hannu ce" Uhmmm aah haryanzu amman sauran k'iris " To allah ya baki sa'a akanta muma muzo mu d'and'ana "Hehehe nidai muje ciki wallahi har na k'asa najini akan ki " Samira ta fad'a tana kaima d'uwawun zulyyy bugu



Suna shiga d'akin kamar wasu mayuwantan zakuna wad'an da suka jima basu samu abincin ci ba suka fara kau'be kayan su suna sakar ma junan su murmushi, harda k'ofar basu rufe ba bare su rufe gidan suka had'e bakin su waje d'aya suna tsotsar bakin juna ( simi simi naja k'afa fuwana na 🚶🚶🚶na fito daga d'akin dan gar na ganema kai na abunda ya girmi kakata na koma bakin k'ofar khadija nayi zaune ina jiran dawowar ta hhhhhh)


Sadik har yaje kasuwa ya sake dawowa sake dubawa yayi yaga d'akin khadija har yanzu a rufe yaje wajen mama ya kar'bo mukulli ya bud'e d'akin cikin d'akin ya wuce, yana shiga turuss yaja ya tsaya yana k'are ma d'akin kallo gabansa yayi mugun fad'uwa ya shiga duba kayan tufafin sa kawai ya gani " Aah to me hakan ke nufi? " Ya tambayi kansa zuciyar sa nasan kawo masa mg amman yana kaucewa, wayar sa ya ciro ya lalubo number khadija bugu d'aya zuwa biyu ta d'aga, shigarta gida kenan wajen inna

" Hello"Naam " wai har yanzu ba'a gama ba ne? " Angama "Ohh zaman ki ne kika yi ko to shikenan kiyi zamanki ma kada allah sa ki dawo" ya fad'a a hasale tare da kashe kiran

'bangaren khadija kuma yana kashe kiran tayi wata shu'umar dariya tare da fad'in "Ai kuwa ka sara a ga'ba dan ba komawa zanyi ba nagaji"




Fitowa yayi daga d'akin kansa na sara masa, har ya wuce d'akin samira, ya dawo dan wani gurnani ya rik'a ji bakin k'ofar ya dawo ya tsaya" Wallahi shiyasa nake k'ara son ki my zulyyy saboda kinsan yarda zaki tafi da imanin mutum a wannan harkan gaki da ruwa kamar kogi " uhmmm kin jiki ai kin fini iya komai wallahi mijin ki ya huta shi kam" Mtswwww kinji ki da wani zance waya ce miki idan ana wannan harkar ana tunawa da namiji ai wallahi gwauda mace ta c *ka sau d'aya namiji koda c goma yayi maka bazai kai kamar mace ba bare har kaji ka gamsu" Allah" Eh mana nida tashi mu k'ara second round kafin lokacin dawowar yayi"



Sadik zuciyarsa rawa ta fara yi masa hannu yakai ya d'aga labunen d'aki, samira ya gani kwance a k'asa zulyyy na saman ta "Innalillahi wa inna'ilaihi'raji'un " ya furta da k'arfi yayi saurin dafe bangon wajen dan wani irin jiri ne ya d'ibesa badan allah yasa ya dafa bangon ba da ya Fad'i...............................................










Littafi fa ya kusa kai k'arshe 😇





Comment and share fisabillilah

🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK



_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 3️⃣6️⃣➡️3️⃣7️⃣


Duk da hakan basu ji saba, zulyyy ta kalli samira tare da fad'in "Wai ina cikin da kika fad'amin kina da ne? " Yana nan" ta fad'a tare da shafa cikin" Har yanzu bai gano ba cikin sa bane" To taya ma zai gane ai allah ne ya bani sa'a akayi dace gashi yana bala'in son haihuwa ina fad'a masa inada ciki sai kinga yarda yake murna yana zumud'i ke akan cikin nan fad'an da suka shayi shida matar sa bansan adadinsa ba"



"Iyyeeeee ke kam allah ya kashe ya baki wanda ya d'irka miki ciki daban mai renon sa daban" Hhhhhhhhhhhhh allah kin ban dariya" Ah to gaskiya na fad'a ai "


Sadik zubewa yayi k'asa zaune, jin abinda suke fad'a ( kenan daman ba cikina ba ne da cikin shege na aure ta Innalillahi wa inna'ilaihi'raji'un samira kin cuce ni kin cuce ni) Sadik ke wannan maganar a zuci, Mik'e wa yayi a fusace ya shiga d'akin



Samira zatayi magana taga an shugo d'akin, a razane su duka suka d'ago kansu suka kalli k'ofar, wanda suka gani tsaye a kansu ne yasa sai da hantar cikin su ta juya zulyyy ta sauka saman samira taja baya samira ta tashi zaune tare da dubin abun da zata rufe jikin ta dashi amman bata ga komai ba dan cikin d'aki suka watsa kayan



Sadik idanuwan sa sun koma kamar barko no akan tsabagen jan da sukayi na tsananin 'bacin rai


"Samira ni zaki ci amana" ya fad'a yana nuna kansa " Ni zaki ci amana"Ya fad'a da k'arfi, samira ta rud'e " Da.. dah dan allah kayi hak'uri ka tsaya zan yima baya ni" Bayani bayanin me zaki yi min duk abunda kuka fad'a naji da kunne na to wane bayani zaki yi min eh" ya k'ara sa maganar yana daka mata tsawa" Wallahi kin cuce ni allah ya isa tsakani na dake samira "

Zulyyy ta bud'e baki dak'yar tare da fad'in"Dan allah Kay" wani kallo ya watsa mata wanda yasa sauran maganar tak'alewa, fita yayi daga d'akin ko wacce su ta nemi wajen da kayanta suke ta saka


Sai gashi ya dawo hannun sa rik'e da bulala ta belt d'in enji irin bulalar nan mai shiga jiki, bai tsaya wata_wata ba kawai ya fara zuba musu ita da wajen da suke so da wajen da basa so zuba musu ita kawai yake, sai ihu suke da neman agaji

Mama jin ihun yayi yawa yasa ta fito daga 'bangaren ta dan dajin wannan ihun bana lafiya bane,



Da sauri ta isa wajen sadik

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment