Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasa hannu ta rik'e hannun sa tana fad'in "Siddiku lafiyar ka kuwa"Kallan sa tayi taga tsantsar 'bacin rai a fuskarsa murya ta sassauta tare da fad'in"Haba Siddiku bansan ka da wannan d'abiar ba ta dukan mace ba duk laifin da suka maka bai dace ka duke ta ba wai kama manta ne juna biyu gare ta allah ya tsare ya kare idan wani abu ya samu cikin fa " Allah yasa ma ya zube wannan tsinannen cikin d'an shege allah ya isa wallahi" Siddiku ka kosan abinda kake fad'a kana cikin hankalin ka kuwa? " Mama cikin hankalin kai na nake, ya fad'a tare da juyawa ya Kalli samira yace " Kije keda allah na sakeki saki uku allah ya isa tsakani na dake "Innalillahi wa inna'ilaihi'raji'un Siddiku subhanallah" Mama ta fad'a


Samira ta fashe da kuka sosai dan ita wallahi tana bala'in son sa shine ma dalilin da yasa ta aure shi amman gashi nan ya sake ta ina zata sa kanta kuka take wiywiy_wiyyyy


"Wallahi kida uku na baku ku fice min da gida idan ba haka ba hmmmmm wannan ai zaman ku cikin mutane ma najasa ce zaku wuce ko kuwa? D'aya" yana fad'in biyu duk suka ruga aguje sukayi waje ba takalmi ba mayafi


Zama yayi tare da dafe kansa da yake jin yana sara masa












"Ina ne bazaki koma ba eh? " Inna ta fad'a, khadija tayi shuru tare da k'ara sawa cikin gidan ta nemi waje ta zauna

"Khadija ba magana nake miki ba ne"inna me kika ce ne? " Gidan ku nace kinji ga ja'irar yarinya kai wad'an can tulin kayan da kika jibgemin a d'aki na miye khadija badai wani abun kika ma yaron nan ba wanda ya 'bata masa rai har kuka samu sa'bani tsakanin ku yaro mai hak'uri " ni wallahi ba abinda nayi masa kawai dai na gaji ne so nake ya sauwak'emin " Baki inna ta sake tana kallan ta kana tace " Khadija wai kodai wani abu ne ke miki yawo a k'wauk'waulwarki ne idan ba haka ba taya ana miki kallan mai hankali ajiki kina irin wannan maganar ai ba lafiya ba to ko dai shine ya miki wani abun? " Babu abunda yayi min ni kawai nagaji ne "Aah lallai khadija bakyada lafiya duk tsawon shekarun nan da kukayi tare baki ce kingaji ba sai yanzu da rabo ya tsaga a tsakanin ku" khadija tayi saurin d'agowa ta kalli inna tare da tunanin to rabon me ya tsaga a tsakanin su


Inna taci gaba da fad'in" To wallahi k'aryar ki bazaki mayar da ni tsohuwar banza ba dan haka tun wuri ki tashi ki koma d'akin ki yafi miki rufin asiri...............................................












Comment and share fisabillilah

🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK



_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 3️⃣8️⃣➡️3️⃣9️⃣


Tafiya suke ba takalmi dan kwaulin kansu suka cire suka yafa samira ta kalli zulyyy taja tsaki tare da fad'in
"Wallahi zulyyy kin cuceni shikenan kin rabo ni da gidan miji na"Kamar ya na cuceki na cuceki kodai kin cuceni dubi jikina kigani duk 'bardallah bulalace ina zamana qlau wallahi nayi nadamar sanin ki a rayuwa ta"Ke karki gayamin maganar banza wallahi da bakije gidana ba ai da duk hakan bata faru ba wallahi allah ya isa tsakani na dake"Ni ma haka kuma daga yau bani bake wallahi ko a hanya muka had'u kika nuna kinsani sai nasa an kullemin ke "Wanda baisa an kulleni ba gundum bulum bura ubansa" Mu zuba mu gani "Mtssswwwwwwwwww"
Kowa yabi hanyar sa,





Ruwa mama ta kawo masa ya kar'ba ya sha sai da taga yad'an sauko sannan tace "Siddiku" ya d'ago ya kalleta " Ko zaka iya yimin bayanin abunda ke faruwa dan ni ban fahimci komai ba" Mama........................................... Duk abun da ya faru tun daga farkon har k'arshe ya sanar mata, mama hamdallah tayi ga ubangiji da allah yasa ma ba cikin sa bane da abun kunyar sai yayi yawa


Dafa kafad'arsa tayi tare da fad'in "Siddiku allah ya kamata ka godema daya bayyana maka gaskiyar ko wacece ita sannan dan allah Siddiku aure auren nan kayi hak'uri ka daina kar a rik'a nunaka a gari ana fad'in aure sake kake yi duk da nasan dalilin ka nayin auren amman ka tuna aure haihuwa mutuwa duk a hannun allah suke idan allah yayi kanada rabon ganin jinin ka tofa dole saika haihu idan kuma haka allah yake son ganin ka ba tare da yara ba tofa duk matan da zaka aura bazaka ta'ba samun haihuwar ba kayi hak'uri kuyi zaman ku kaida matar ka ka gode allah ma wallahi ya baka mata mai kirki wacce tasan darajar aure tasan darajar yan uwanka wallahi khadija bata da matsala ga ladabi da biyayya dan allah ka rumgumi matar ka ku zauna lafiya nidai shawarar da zan baka kenan "To mama nagode sosai in Sha Allah zan d'auki duk abunda kika fad'a min ai ni yanzu naji duk ka'rin auren ya fitar min a rai allah dai ya k'ara bamu zaman lafiya da matata"



"Amin ya rabbi, wai khadijar bata dawo ba ne "Wallahi bata dawo ba mama dana shiga d'akin kuma banga kayan ta ba"ya fad'a kamar zaiyi kuka


"Kamar ya? " Mama ta tambaya"Nima bansani ba "Aah fa Siddiku kardai kayi mata wani abu ne daya 'bata mata rai dan nasan khadija da hak'uri "Wallahi mama ba abunda nayi mata hasalima cemin tayi waken kitso da k'unshi zataje na bata kud'i" Hmmmmmmm mama ta numfasa da k'arfi kana tace " To yanzu abun da ya dace kaje gidan nasu kaji me ake ciki"To " ya fad'a tare da tashi tsaye

"Allah ya kiyaye "Amin







"Khadija wai bazaki tashi ba ne"Inna ta fad'a tana fitowa daga d'akin, khadija na kwance cikin baranda ta k'ara gyara kwanciyarta "To shikenan ki zauna tunda bakyajin magana ta bara na aika akira min baban ki malam abu ai nasan shi idan ya miki magana dole kiji "Kai inna ni dan allah ki kyaleni wallahi akan yawan maganar nan har na fara jin alamun zazza'bi " khadija kinci gidan ku ni kike fad'ama hakan haka kawai ba laifin zaune bare na tsaye yaro bai miki komai ba kuna zaman ku lafiya kice ke sai ya sake ki to bara kiji walla.....sallamar da akayi ce ta katse mata magana, ta amsa sallamar


Wai ance ana kiran Khadija" Yaron ya fad'a
"Je kace waye? Inna ta fad'a
Yaron ya juya ya tafi sai gashi ya dawo yace " Mijin ta wai"To gata nan tafe "To"

Inna ta juyo ta kalleta tare da fad'in "Sai ki tashi ki shirya ga mijin ki nan yazo ku wuce "

Tashi tayi taja hijab d'in ta ta kama hanya, inna tace"Kayan fa? " Bata ce da ita komai ba ta fito

Tana fita taganshi tsaye, murmushi ya sakar mata, ta gimtse fuska tamau" Gani "Ta fad'a,cikin tattausar muraya yace "Nazo ne mu tafi tare naga har yanzu baki koma bane kinsan gidan bayamin haske idan baki nan sai najini duk wani iri harsai kin dawo" Uhmmmmmmm ai kuwa gwauda ka saba dan bani ba komawa gidan ka " Sadik kusan suman tsaye yayi jin furucinta


Hanya ta kama zata koma ciki, da wani irin sauri yatsa gabanta zuciyar sa na harbawa da k'arfi dak'yar ya iya furta"Khadija kin ko San abinda kike fad'a ? Dan Allah khadija idan wasa kike ki daina kinsan zuciya ta bazata juri irin wannan wasan ba Ni ne fa sadik mijin ki abokin rayuwar ki mai son ki wanda bakyada tamkarsa a duniya shima bayada kamarki "Zancen dah kenan"Ta fad'a

" khadija dan allah ki rufamin asiri kinsan bazan iya rayuwa idan babu ke a tare dani ba ki tausayamin idan ma wani laifin na miki bansani ba ki fad'a min sai na baki hak'uri " Ba laifin da kayi min kawai dai na gaji ne dan haka ka sauwak'emin ka bani takarda ta kowa ya kama gaban sa"Wa'iyazubillah khadija kinsan abinda bakin ki yake fad'a kuwa kinsan hukuncin matar da ta bud'e bakin ta tacema mijin ta ya sake ta "Uhmmm malam idan ka aiko min takarda ta, ta fad'a tare da bangaje sa ta wuce cikin gida, bayan ta ya biyo yana kiran sunan ta tanaji tayi burus


Inna tace"Khadija wai ba mijin ki bane naji yana kiran ki ba "Nifa inna ba inda zanje"ta fad'a ta shige cikin d'aki

"Innalillahi wa inna'ilaihi'raji'un wai me yake damun yarinyar nan ne hmmmm" inna tasa hijab d'in ta tasamu sadik waje ta fad'a masa, dan allah yayi hak'uri yaje ya barta anan ta kwana gobe in Sha Allah zata koma d'akin ta


Badan yaso ba ya kama hanya yana tafiya kamar wanda kwai ya fashema a ciki gaba ki d'aya ya rasa abunda ke masa dad'i














Samira kwance tana jimamin abunda ya sameta, tana susar gabanta dan kamar wani abu takeji yana mata yawo a k'asan ta taji alamun fitsari ta tashi ta d'auki buta tayi band'aki tana duk'awa mai makon tayi fitsarin sai taga tsutsotsi na fitowa a k'asan ta, a mugun razane ta Mik'e tsaye tare da sakin wata uwar k'ara ta fito band'akin hankalin ta a tashe taja mayafin ta ta fito ta samu abun hawa tayi asibity


Tana zuwa asibity aka duba ta likitan, a hankali ya fara yi mata bayani dacewa "Madam a gaskiya kina cikin matsala saboda duk yarda akayi kinyi tarayya da d'an luwadi lokacin da kuke sex sperm d'in dake marar sa ya fara komawa tsutsa shine aka juye miki a mahaifa"

Kuka ta fashe dashi sosai tana fad'in"Wayyoooo allah na na mutu na lalace wayyoooo ahj ka cuceni ka kaini ka baro ka lalatamin rayuwa allah ya isa tsakani na dakai"Sorry madam ki natsu ki jini dakai " Dole sai anmiki aiki Kuma kud'in aikin nada tsada sosai amman kafin ki samu kud'in ayi aiki akwai maganin da zan rubuta miki ki siya wanda idan allah ya taimaka zasu d'an fara fitowa kafin ayi aikin sannan zaki siya pampas zaki rik'a saka shi idan ba haka ba ko zama kikayi zasu rik'a fitowa "Nawa ne kud'in aikin dana magani? " Ta fad'a cikin kuka

"I think bazasu wuce 2million ba" Miliyan biyu fa " ta fad'a tana zaro ido"Yeah "Kuka ta fashe dashi sosai tare da fad'in "Shikenan rayuwa ta tazo k'arshe mutuwa zanyi shikenan allah na tuba ka yafemin..................................................












Comment and share fisabillilah


🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK



_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page4️⃣0️⃣➡️4️⃣1️⃣

Dak'yar ya isa gida, yana zuwa ya wuce wajen mama ya zube k'asa yana kuka, hankalin mama ya tashi sosai ta shiga rarrashin sa tare da tambayar sa abunda ya faru, ya sanar mata inna ta basa hak'uri tare da fad'in"Ni wallahi Siddiku banma yarda dakai ba anya ba wani abu kayi mata ba"Wallahi wallahi inna ba abun da namata "ya fad'a cikin kuka


"To naji yanzu ka tashi kaje ka kwanta allah ya kaimu goben"Amin "Yawwa kayi alwala kayi nafila ka kai kokenka ga ubangiji Allah ya dawo ma da matar ka kaji dai "To inna nagode, ya fad'a tare da Mik'e wa"sai da safe "Allah ya bamu alkhairi"







"Bazaki mutu ba sai lokacin ki yayi ki tabbatar kin samu kud'in dan ayi aikin nan da wuri idan ba haka ba tsutsotsin yawa zasu rik'a k'arawa "In Sha Allah doctor zan k'ok'arta" Kar'bi ga sunan maganin da zaki nema nan wanda zaki fara sha "To likita"Ta kar'bi takardar ta fito, hawaye na ambaliya a fuskarta "Allah kasa kar na mutu allah ka bani lafiya na tuba astagfirullaha! astagfirullaha! astagfirullaha! "




Tana tafiya tana istigfari ( Niko nace su samira sai yau aka tuna da allah Hmmmmmmm d'an adam kenan idan yana aikata laifi ba ruwansa da tunawa da ubangiji allah da zarar allah ya damk'esa koda na yan seconds ne sai kaga ya dawo musulmin kwaurai allah ya kyauta allah ya k'ara muna imani dajin tsoron sa )









Sadik kusan daren nan bai runtsa ba, sai wuraren asuba bacci 'barawo yayi awon gaba dashi, ana fara kiran sallah ya Mik'e ya fito ya nufi masallaci, bayan ya dawo ne zazza'bi ya rufe sa







Inna tun da safe ta aika aka kira mata malam abu, sai gashi yazo inna ta zayyana masa duk abinda ke faruwa, khadija ya kaullah ma kira sai gata ta fito sanye da hijab ta nemi waje ta zauna malam abu ya kalleta tare da fad'in "Amman khadija kin bani kunya yanzu da hankalin ki da wayonki ki aikata irin wannan d'anyen aikin ai abun baima kawo kallo ba haba dan allah muna miki kallan mai hankali tambaya uku zuwa hud'u zan miki idan har ban samu wata amsa gamsashiya ba to wallahi yanzu yanzun nan zaki tashi ki koma d'akin ki naso ma ace harda mijin ki a wajen nan amman bakomai shin khadija kina son mijin ki ko bakya son sa? " Shuru tamasa tayi k'asa da kanta
"Magana nake miki fa"Ina son sa"Ta fad'a " Wani laifi ya miki ko wani abun ya had'a ku har kuka samu sa'bani? "Aah" Baya baki ci da shane ko sutura "Aah "Baya sauke hak'k'insa ne a matsayin sa na mijin ki?" Aah"iKon Allah to wai meya miki duk abunda na fad'a kice aah "Ba abunda ya min" Malam abu ya juyo ya kalli inna ya numfasa tare da fad'in "Ni Wallahi banma san mezan ce ba wannan yarinyar dai dad'i ne yayi mata yawa inbashi ba babu fad'a babu komai ka taso kace wai sai an sake ka to bud'e kunnuwanki dak'yar ki jini yanzun nan zaki tashi ni zan mayar dake gidan ki daman da mota nazo dan haka sai ki kwauso kayan ki muje Wallahi ni khadija kinma sa naji kunya da girman ki da wayon ki................................................... Fad'a yayi mata had'e da nasiha da rarrashi, itama ta basu hak'uri akan abunda tayi tare da fad'in bazata sake ba, malam abu yace"Aikin me yakeyi ne? " Har yanzu bai samu aikin gwamnatiba kasuwan ci yake yi"Okay ai dai takardun sa na nan ko? " Eh suna nan"to idan kinje ki sanar dashi gobe ya kaimin takardun gida na dan akwai wani abokina daya dameni akan na kawo masa takardun d'ana a nemo masa aiki to kinsan duk d'iya mata ne allah ya bani suna d'akin mazajen su kuma dukan su daga bakin secondary suka tsaya " To baba in Sha Allah zan fad'a masa mungode allah ya saka da alkhairi"itama inna tamasa godiya



Ya tasa khadija a gaba sai da ta d'auko kayanta suka wuce,


Yana ajiye ta wuce, yara suka shigo mata da kayan ta, ta basu kud'i suka amsa suna godiya, kayan ta rik'a d'auka tana shiga dasu d'aki ita sam bata lura da mutum dunk'ule a falo ba, sai da ta gama kai kayanta ta cire hijab tazo zama ta gansa jikin sa sai karkarwa yake yi da sauri takai hannun ta ta yaye zanen jikin sa ya d'au zafi sosai har huci yake fitarwa durk'usawa tayi gabansa tare da kiran sunan sa, ahankali ya bud'e ido ganin ta yasa ya fara k'ok'arin tashi zaune amman ya kasa, ta taimaka masa ya zauna cikin raunanniyar murya tace "Baka da lafiya ne meyake damun ka? " Magana yake son yi amman ya kasa jikinta ya fad'a ya rungumota itama ta rungumesa tsam tanajin yarda yake sauke mata ajiyar zuciya, ruwa taji ya d'igo mata masu zafi ta d'ago sa taga hawayen sa ne,




Fuskarsa ta tallafo da hannayenta biyu tana girkiza masa kai itama tana hawayen ta bud'e baki tare da fad'in "Dan Allah kayi hak'uri ka yafe min mijina na tuba bazan sake ba" Murmushi ya sakar mata ya k'ara kwanciya a jikin ta "Kasha magani kuwa?" Kai ya girkiza mata, filo ta janyo ta d'ora masa kansa ta Mik'e zata wuce ya rik'o hannunta a hankali ta furta "Magani zan d'auko"Ya sakar mata hannu ta d'auko magani ta d'ebo ruwa ta ajiye ta d'auko d'an k'ara min towel ta d'ebo ruwa cikin wata roba mai d'an Fad'i


Har zata zauna sai ta tuna da baici komai ba ya kamata ko tea ne yasha sannan yasha magani ta fito, ta fito ta d'auko electric d'inta ta lak'a a wuta dan akwai nefa, ta d'aura tower da take dafa tea a ciki ta zuba ruwa tasaka kayan k'amshi, cikin k'ank'anin lokaci suka tafasa ta kashe ta tace ruwan ta zuba a cup, tayi d'aki, ta d'auko kayan tea ta had'a masa mai kauri ta tayar dashi zaune ta rik'a basa a baki har ya Shanye tass ta 'ballo maganin ta basa, ta kwaushe kayyakin da ta gama amfani dasu ta fitar ta dawo ta matse towel d'in da tasaka a rufa, ya kwanta saman k'afafuwan ta ta rik'a daddana masa kansa da towel d'in nan da nan ko zafin jikin sa ya ragu sosai, bacci ya d'auke sa ganin haka ahankali ta janye ta d'auko filo ta d'aura masa kansa ta d'auki kayan ta fito, ta ajiye tayi 'bangaren mama




Mama da ta ganta akan farin ciki kamar ta Had'iyeta ita kuma sai ta rik'a jin kunyar abun da ta aika ta tace "Mama bara na d'ora girki"To khadija allah ya miki albarka allah ya k'ara had'a hankullanku waje d'aya "Amin mama, ta wuce ta d'aura girki daman tana da nik'ak'k'un kayan miyar ta cikin fridge, bayan ta d'aura ta tattara kayan da tayi amfani dasu ta wanke, ta koma d'aki taga bai tashi ba ta wuce uwar d'aki ta gyara kayan ta ta gyara d'aki...........................................................











Comment and share fisabillilah


🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK



_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page4️⃣2️⃣➡️4️⃣3️⃣
Last page

Har ta share d'akin tayi turare, ta gama girki ta d'aura ruwan zafi tayi wanka duk bai tashi ba, daman gashi jiya bai samu bacci ba ga kuma zazza'bi


Gefen wuyansa ta ta'ba taji zafin jikin sa ya sauka, tayi hamdallah, ta zauna kusa dashi ta kafesa da ido tana kallan yarda yake baccin sa cikin kwanciyar hankali,takai hannu ta shafi gefen fuskarsa, motsawa yayi ahankali ya bud'e idon sa


Tashi yayi zaune idanunsa a kanta, murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa tare da fad'in "ka tashi sannu ya jikin?" Jiki yayi sauk'i yanzu ma banajin komai "Allah ya k'ara maka lafiya mijina"Amin matata tare dake" ya fad'a tare da janyota jikin sa ya rik'o hannuwanta, ya marairaice fuska tare da fad'in "Khadee dan allah kark" khadija tayi saurin d'aura yatsanta saman ta'b'bansa tare da fad'in "Shiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii wannan maganar ta riga da ta wuce dan allah karka dawo da ita baya in Sha Allah hakan bazai sake faruwa ba " Rungumota yayi jikinsa sosai

" Bara nakai ma ruwan wanka yarda zaka k'ara jin k'arfin jikin ka " tashi tayi taje takai masa ruwan wanka, yayi wanka ta kawo masa abinci yaci ya k'arashan magani, suka rik'a fira cikin so da K'auna




Sai da dare yayi ta sanar masa,abun da malam abu ya fad'a mata ta sanar dashi



Washe gari, tunda safe ya shirya yaje ya sanarma mama tayi masa addu'a yaje ya kai masa takardun,koda ya dawo khadija na d'aki kwance ciwon mara ya dame ta, koda ya shiga d'akin ya tar da ita sai murk'ususu takeyi "Subhanallah wai ciwon ne haryanzu kin k'ara shan magani"Kai ta girgiza masa, hannuwan ta dafe da mararta, ya 'ballo magani ya bata, mai makon ciwon ya ragu saima k'aruwar da yayi, wayyoooo khadija ko magana bata iyawa, sadik duk ya gigice ya nufi 'bangaren mama ya sanar da ita ta d'auko mayafin ta sukayi hospital




Suna zuwa aka kar'be su, ganin halin da take ciki, dubata likitar tayi tayi mata allura had'e da ta bacci, nan da nan ciwon ya kwanta bacci ya d'auke ta, likitar ta tsaya nan tana musu bayani " Yanayin kwanciyar da tayi ne ya haifar mata da ciwon mara sannan da ta tashi shan magani sai aka bata wanda bai dace ba maganin da tasha yayima cikin dake jikin ta k'arfi sosai Allah ma ya tak'aita wahalar ba abunda ya samu cikin saboda irin wannan maganin yana iya haifar da abun da zaisa cikin ya zube dan allah sai a kiyaye gaba a rik'a sanin maganin da za'a rik'a bata idan ma ta kama kamata yayi azo asibity a rubuta maganin da ya dace tasha bawai daga taci abu kaza na mata ciwo ba a 'ballo magani kawai a bata dan allah a kiyaye" Tun da likitar ta fara bayani daga sadik har mama suka kafeta da ido suna kallo kamar sun samu tv ko k'iftawa basayi har takai k'arshe




Sadik ya bud'e baki kamar wani mai koyon magana yace "Likita kina nufin ciki gareta? " Eh mana bakusan tana da ciki bane "Likitar na fad'in haka baiko tsaya bata ansa ba ya nufi wajen da khadija ke kwance tana bacci,ya rumgometa yana jin K'aunarta da na abinda ke cikin ta yana k'ara shigarsa, yayi tsaye a kanta hawayen farin ciki na zubo masa yakai hannu yana shafa cikin ta


Inna tace" likita dan allah dagaske ciki gareta" Sosai ma wata d'aya da sati uku " Kai alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah abun godiya ohh allah sarki ashe da rabon naga wannan ranar allah sarki khadija baiwar allah allah ya rabaki dashi lafiya allah abun godiya allah mungode maka da wannan babbar kyautar daka yi muna"Nace ta dad'e bata haihuba ne irin wannan farin ciki da kuke yi "Bari kawai y'ar nan kusan shekararsu hud'u cikin ta biyar da aure ko 'bari bata ta'ba yi ba har mun cire tsammani sai gashi" Allah sarki mama ai bawa baya cire tsammani daga ni'imar allah dole kuyi farin ciki nima ina taya ku murna ubangiji Allah ya inganta ya sauke ta lafiya "Amin Ya allah "




Sadik na zaune gefen ta har ta tashi,ya sanar mata tana d'auke da juna biyu, tayi murna sosai, likitar ta rubuta maganukan da zata rik'a sha ta sallame su tare da k'ara yima khadija congratulation


Nan da nan labarin cikin ta ya kara d'e familyn su, sai kiran khadija ake ana tayata murna tare da addu'ar allah ya inganta ya sauke lafiya


Inna da taji labari itama tayi farin ciki duk da daman tunda khadija tazo take mata kallan mai ciki




Khadija ita dai tunda ta dawo bataga samira ba dan haka ta tambayi mama, ta sanar mata duk abunda ya faru, allah ya kyauta Kawai tace





Sadik aikin da aka nemo masa an samu har yaje anyi masa enter biyu, babban kamfani ne aka d'auke sa, suka basa gida da motar da zai rik'a hawa, gidan gashi babba kuma part biyu ne, suka d'auki part d'aya mama kuma cikin d'ayan

Yan uwa suka had'a musu walima, akaci aka sha akayi wasa da dariya


Khadija kulawa take samu sosai a wajen mijin ta da mama, cikin ta na wata biyar amman idan ka ganta zaka iya cewa lokacin haihuwar ta yayi dan cikin wani irin girma yayi sosai




Sadik kam yanzu bud'i ya k'ara zuwa har wani fresh ya sake yi hasken sa ya fito sosai, wajen aikin sa suna ganin girman sa dan mutum ne mai gaskiya da rik'on amana




Khadija cikin ta tunda ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment