Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yauma haka nashirya natafi kasuwa inazaune cikin tunanin meyasa aisha bata zuwa ina tsaka dawannan tunanin kamardaga sama naji muyaryar antyna tanacewa lpyarki kuwa kanwata aguje natashi ganin anty Aisha nadafeta ina murna zamatai nima nazauna na kankameta kamar wadda za a kwacemin ita sanan nace anty kwana biyu meyasa bake zuwa duk nabi na damu . murmushi tayi sanan tace uhmkanwata kenan to baganiba .anan take bani lbrin mahaifinta ne Allah yamasa rasuwa . shikenan yanzu kema kinzama kamarni .eh hakane nuor amma ni banafuskantar irin azabar da kikesha. Yauwa gakayan danace zan kawo miki .karba nayi inadubawa riga da siketne guda 4 sai dogayan riga guda 3 .najidadi sosai sakamakon tunda natashi nafara girma da kaya kala biyu nake rayuwa kuma sukadai nake dasu .yaukuma gashi nasamu har kala bakwai ba abinda zancewa ubangiji saidai nace Allah na gode maka .juyowa nai nakalli anty nace anty Aisha nagode sosai allah ya barmu tare.amen kanwata nuor ce takara cewa anty ina tsoron ranar da zan rasaki nasan tabbas bazanji dadiba .karki damu nuor ina taredake cewar Ayshat.tom sallama sukai amma nuor kememe taki tafiya guda wai saitaga gidan su aisha kodan wataran haka suka dunguma zuwa gidan su Ayshat Inda suka hadu da kannen Ayshat suka gaisa sanan aysha taraka nuor bakintiti tasata a adaidaita tatafi gida


To nour tana isa gida tai alwala tai sallah sannan taje inna tasammata ruwa buta daya tashiga wanka bayan tashiga bandakinne takasayin wankan sakamakon sanyin dataji ,ahakadai tasamu tayi wankan daker tafito tasaka daya dagacikin kayan da Ayshat tabata

To yaukwana 2 kenan nuor batasaka abinci abakintaba kokadan gashi inna da anty aslamiyya suntafi biki ga batazuwa talla balle Ayshat tabata .nandanan jiri yafara dibanta gabadaya yanayinta ya canza baiwar Allah kenan ,to nuor ahaka tasamu tafito waje kozata samu wani yataimaka matayabata abinci ko loma biyuce , amma yadda tafito haka tajuya don bawanda ya kalli Inda takema ballema tasamu atausaya mata .juyawar da zatai takoma gida taga anbude wani get .wani mutumine yafito da bakalleda ahannunsa yanufi wajan karnuka ya ajiye ,zubawa ledar idotai domin ranta yaba ta abincine ai dagudu ta karasa gurin ta dauke ledar daka gaban karan ta ruga aguge tana gudu karnukan suna binta ,bata tsaya a ko ina ba sai a dakin ummanta ta garkama sakata tazauna tana maida numfashi kamar wadda tai aikin karfi .buce ledar tai shinkafa ne dafadika acikin ai da sauri tashiga aikawa cikinta saida tacinye tass sannan ta mike ta deko ta hundo domin taga karnukan sunanan amma bata gansuba dan har sungaji da jira sun tafi , fitowatai tadauki ruwa tasha sanan ta dawo dakin ummanta ta kwanta hawaye nazuba a idonta hartasamu tai bacci .

Innace da ita da aslamiyya suka dawo bayan sun huta inna ta dora katuwar tukunyar abincin siyarwarta ,bayan tagama takirawo nuor tadoramata tallan, nuor kuwa tana tafiya tana ta sake sake azucinyarta tana cewa anya inna ko tana da imani bafa tatambayeni naci abinci ko banciba ,Allah sarki rayuwata nasan da yanxu ummana ta natare dani dabazan sha wanna bakar wahalarba amma nayi ta wakkali da ubangiji nasan wannan jarrabawace wadda yayimin Allah narokeka kabani ikon cinye wanna jarabawar ahaka ta karasa gurin tallan nasu ,tana karasawa kusa da Ayshat ta zauna tana gaishe da ita ,anty ina wuni ?lagiya kalau, ina kika shigane kwanabiyu duk kinbi kin dagamin hankali ,wllh anty innace batanan , to aina kike cin abinci?bako ina tsawan kwanabiyu banci abinciba sai jiya nasamu naci nan tabawa Ayshat labarin yadda akai ta samu abinci taci,tausayin nuor ne yakamata tace kiciga ba da hakuri nuor tabbas kinaganin jarabawa kala kala amma bakomai Allah yana tare dake , murmushi nuor tayi sanan tace anty kenan aini inda sabo zuwa yanzu yaci ace nasaba da halin Innata ,wllh ni yanzu wahala banajinta domin narigada nasaba .uhm kidai kara hakuri nuor dan ba asabo da wahala ,tom shikkenan anty amma zanso mucigaba da rayuwa tare kodan kaunar da kike nunamin dan ayanzu kece uwata kece ubana banida kowa aduniyarnan daga ubangijin daya haliccemu saike nake da ita, murmushi Ayshat tai sanan tace nagode da wannan matsayan da kika bani. toahaka sukai sallama kowa yatafi gidansu

Yau juma'a kuma itace ranar da nake jiran faruwarta arayuwata kuma itace ranar da tazamarmin farin ciki arayuwata haka zalika kuma itace tazamarmin bakinciki kuma wannan ranar itace ranar da kowane bawa irina mai RAYUWAR KASKANCI yake Fatan damunta ,amma kash narasa abu daya wato antyn Ayshat domin ita din tazamemin wani bangare na jikina ,inaji ina gani haka narasata arayuwata .
Nuor, nuor, nuor? Na am .karasawanai nazauna nace inna gani , ke dan ubanki kinrainani ko harda zankiraki kiki amsawa ko uban me kike acikin dakin ,inna wlh banjiba ne lokacin ina sallah ,tass tabata mari to dan uwarki shine kuma bazaki amsamin kiranaba ,inna idan ana salla ba ayin magana shiyasaban amsaba ,tasss takara mata wani marin dan ubanki nizakigayawa kabali da ba adi to tunkan a haifi uwarki nasan alu anbaki nasan fari da baki shine zaki fadamin magana nuor ni kika zaga dan ubanki, kiyi hakuri inna wlh bazaginki nayiba ,to ubanme kike nufi inba zagina kikaiba to wlh kidau nukannan ki je ki nukomin kidawo sai kin gommace uwarki zainabu bata haifokiba agidannan.inna, cewar aslamiyya ,na am sha lele kin tashine ,inna wai me wanan yarinyar take cemikine naji kamar kina cewa tazageki memakon kikirani naci uwarta agidannan , aa haba sha lele aibasaikin wahalaba barni da ita taje tadawo ina tunanima kashe mutsiyaciya zamuyi kawai mu huta, aslamiyya ce tace ni wlh inna ina mamakin taurin rai irinna wannan yarinyar ji yadda muke mata horon yunwa da azaba amma haryanzu taki tamutu mu huta.innace tacabke zancen dacewa nifa wlh yadda bamu rasa cida shaba amma duk da haka nake doramata talla amma tar iskar yarinyar nan haryanzu rayuwarta take kuma ni sabida wani yasamu yamata ciki naturata tallannan kina ganifa harkara yawan shinkafar danake doramata nai amma yarinyar nan ina tazuba ido danna ganta da ciki shuru kakeji yarinya saikace aljanna ,wlh ni innako Inda nice nakeshan azaftarwar da kikewa nuor datuni bawannan zancen akeba don inaganin guduwa zanyi ,kigudu kije ina ? Inda zan wataya na shana mana , ni inna abin da yake bani mamaki wai yan unguwar nan tamu ko magana basayi akan abinda kikewa nuor .hhhhhh yarinya kenan ai bari kiji sha lele tuni naje gurin boka hankaka yarifemun bakinsu da idonsu akan ganin abinda nakemata shiyasa kikaga bawanda yake taimakonta ita kadai take rayuwarta ,tubarina fadamiki wani abu dabinii saniba sha lele ina wannan yar isakar matar munafuka da goshi kamar girgi ,ee naganeta wai maman hasina kike nufi,eh ita ai itama tuni namika sunan ta gurin boka hankaka ya samata tsanar unguwar nan aranta shiyasa tatattara komatsanta tabar unguwar nan.

Tom suna tsaka dawannan kulla kullan muna furcin nasu saiga nuor tadawo daga nukan ajiyewatai a gaban inna ,sahannu inna tayi tataba sannan tadago takalli nuor tace ke ubanwa yaymiki nukannan bai laushiba saikin koma , inna wlh yace innadawo saiya dokeni ,ya kashekima tashi kifacemun daga gani ,dasauri nuor tafuta tana share hawaye ahaka ta isa gurin nukan ,saida ya daketa iya san ransa sannan ya kara tusamata garin ,bayan yagama ta dakko nukan alokacin karfe 5: 30ta tsallako titi , tana daidai tsakiyar titi saiga wata mota tayanko aguje jikake yufffffffff tayi gaba da ita ,arga allah alokacin nayi tunanin rayuwata tazo karshe,zansamu yanci nabar RAYUWAR bakinciki da kunci ashe abinda nake tunani bazai yuwuba.motarce tatsaya wani mutumine yafito kekkan haske farine tass dogo me saje ,akidime ya daukeni yasani acikin mota baitsaya ako inaba sai asbiti......😳✍️


3
______________________________________________________________________________________________________________________________________________tafi ya yake yana tsuga gudu,sanan yana toshe hancinsa, tsabar warin da jikin NUOR da kanta yakeyi,har ya iso kofar katafaren asbitin AMINU KANO,dake zaune ajahar kano titin zari,a road🚍 yana shiga ,dasauri yafiro,yanufi cikin asbitin,yana kollawa doctor maryam Kira, doctor maryam, doctor maryam,yana shiga dakunan dake cikin asbitin,can kuma yaganota tana duba wata mara lafiya,dasauri ya karasa gurin ya ce, doctor nasamu hatsarine a hanya, ar nakade wata karamar yarinya, gatacan na taho daita tana na mota, ki taimakamin ki dubata, kar inje nayi kisan kai,dasauri doctor maryam,ta ce muje,gudu_gudu sauri sauri,suka shiga yi har suka isa,bakin motarsa, bu'de kofar yay , doctor maryam ta mika hannu zata dakkota, sai taji wani hamami ya doki hancinta, dasauri tadawo da fuskarta waje,tace,HAYAT ina kasamu wannan yarinyar, kazama da ita, haladai,kace wani village dinne ka kadeta,kai oh my god,nidai doctor kitaimaka min dan Allah,kar ta mutu,duk wannen zancen daga Baya mayishi, okay ta zura kai cikin motar da hannu ta dakko NUOR cak ta sabata a kafadarta, tana toshe hanci, tana mita,tana cewa, amma dai wallahi HAYAT ni kabani mamaki ma,kai da bakason kazanta ko kadan amma ka iya sa hannu ka kin kimo, Wanan village girl din haba,daidai lokacin da ta isa cikin dakin ta dorata a gadon asbiti,suka fara bata tai makon gaggawa, shiko HAYAT, fucewa yayi gaba kidaya daga asbitin ya nufi gida, wai wanka zaiyi, sabida waccan kucarkar yarinyar ta taba jikinshi, kayanma da yacire wurgar wa yayi, duk da yacire kayan, har lokacin "ken kemin kansa yakeyi,yama rasa yadda zaiyi ya ji dadi, akalla, yashi ga bathroom yafi sau goma,kawai dan ya cire dattin jikin NUOR da ta sakamasa, bayan yafito yana zaune yana jimamin wai mama meyasa ya kade wanan kazamar yarinyar,wane tunani yake har ya kadeta,jin kiran wayayi, dakamar kar ya daga, kuma daga Baya yaduba me kiran nashi doctor maryam ce, aslmualaikum ya dora wayar a kunnensa,daga can bangare doctor maryam tace HAYAT yarinya nanfa, haryanzu shiru bata tashiba ko motsi batayi, okay ganinan zuwa yacewa doctor maryam.

________________tana zaune agefen gadon NUOR tagama waya,ashe ita NUOR tadade, da farfadowa,kawai lambo tayi ,waidan kar ace tunda tawarke tatashi daga kangadon tatafi gida,Allah yaji yagani NUOR taji dadin kwanciyar gadon da tai,sakamakon tunda take rabonta da hawa gado ,zata iyacewa tun tana jaririya, shiyasa tai lambo dan kar ace tatashi,🤣


Uhmm su NUOR fa anhau gado,allah sarki da ansaba kwana akasa,



****************************************************************************************************************************************************************sallamar HAYAT ne yasa NUOR tadan bu'de idonta ta dan lekoshi,sai ta mayar da idonta ta rufe, azuciyarta tana cewa, nashiga uku 🙆nayi gamo wannan me kama da aljanunfa,hhhh🤣wai HAYAT ne mekama daaljanu,taga big guy, kekkewa wanda ko akauyansu babu me kyenshi sai antona, kai bama iya village ba,har burnin,sai an tona,yauwa hayat ka iso,kagani dai wallahi munyi iya yinmu taki tashi,cewar doctor maryam, okay ina tunanin ta cika, bari kawai na dauki hotonta,na koma, Inda nakadeta, mufara binkicen gidansu,ai NUOR tanajin hakan ta kolla kara ta duro daga kan gadon,ta fashe da kuka tana cewa,dan Allah kurufamin asiri,karda ku mayar dani gidanmu wallahi kasheni zatai,ku tai makeni, ko ayyukan gidane zan dun gamuku,amma nidai rokona karku maidani gidan mu, ni bama sai kun biyani kudin aikinba kawai abinci nake bukatar ku'dinga bani,ta karasa maganar tana fashewa da wani sabon kukan,suko su HAYAT baki dayansu baki suka saka suna kallon ta cikin mamaki, yarinyar da akace ko motsi tadainayi ,likitocin sunyi sunkasa, taki farfadowa, ammashine dagajin,zancen za,a maida ita gida ta farfado,ido suka zuba mata suna kallon ikon Allah,yadda NUOR ta tsaya tana zabga magiya,kamar me rokon aljanna,



****to abangarin inna kuwa ganitai har karfe 10 nadare yayi NUOR batadawoba, hargurin me nukan taje babu NUOR babu labarinta, hakanne ya kara daga hankalin inna matuka, tana tunanin kardai yarinya nan ta gudu,tagaji da azabar da nakemata, indai ko hakane saina ci uban ta "idona idon NUOR sai ta gommace, zainabu bata kawo ta duniyaba, saina shayar da ita ruwan azabata,hmmm wllahi wanan azabar da naimata kadan tagani,shegiyar yarinya ,tun yaushe nakeso naga ta mutu amma taki mutuwa duk azabar da na ke mata,ni wallahi ma ,abin takaicin karta hadu da wani dan shegiyar alhajin ya taimaketa, yabata rayuwa mekyau, wallahi na kijinin inga jinin zainabu yana shakatawa adoran kasarnan nafison nagan su a wulakance,a tagayyare,🙆🤭tana tafe tana faman sumbatu kamar wata sabuwar kamu,

🤣da alamadai inna fa takare mata ,. NUOR kidawo kar kisawa inna hawan ruwa🤣🤣🤣🤣🤣niko nace bari nima nai takaina kar inna ta rufeni da duka🏃🏃🏃🏃🏃🤪😜



________________________________________________________________________________________________________~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~********************************************~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
____________________kurufamin asiri kamar yadda ubangiji ya rufamuku,kudaure kitaimakeni, HAYAT ne ya hade girar sama da ta kasa saifaman cin magani yake yana basarwa😡itako doctor maryam abinka,da ciwon "ya mace na"ya macene, har taji tafara tausayin nuor,dan haka ta dan sassauta fuska,ita ba fushi ba,ita kuma ba murmushi ba,tace,yarinya ki kwantar da hankalinki,insha Allah babu abin da zamuyi miki,abin da nakeso kawai yanxu ki nutsu ki fadamana,ke din wacece, insha Allah zamu taimaka miki,
****karaf hayat yakarbe zancen yace, baza mu taimaka mataba,irin yaran nanne,marasa ji,"yan iskan gari,masu damun mutane,da tashen balaga,tana sane tashiga gaban motata,kawai dan na kadeta,wato kinga kekkewa wan saurayi ko,zakizo kicuceni,toni ba irin karuwan dakuke harka da su bane,yayi tsaki ,ya mike zai fita.


__________allah sarki nuor duk da wadannan baka ken magan ganun da hayat ya ke jifanta dasu bata fasa ruko kafarsa tana rokon ya taimaketa ba,itadin ba, dan Allah ka taimakeki nidin bada sanina nashiga gaban motar ka ba, duk kan abin da kagani ubangiji daman can yariga da yagama tsarawa,dan Allah kuyimin rai,wallahi inna bazata barniba muddum nayadda muka sake haduwa kasheni zatai,tana kuka kamar jata ciro zuciyarta ta yar tsabar zafi,
************************a fusace ya funcike kafarsa yai bal da ita ya wuce,tafadi a gurin,tana zub da kolla me zafi kamar wuta,ganitai kukan bazai karamata komaiba sai ciwankai,dan ita ayanxu babu abinda tafi bukata fiyeda mutuwarta, amma kash tafahimci,da sauran wahala aduniya bata gama kur bar ruwan azabar ba,tukunna dai yanzu ta soma sallama da azaba, muddum ta yarda ta koma gidansu,


. Tashi tai ta koma gaban doctor maryam ta tsuguna tana rokanta ,tana cewa, dan Allah doctor,kitai maka ki roki,danki ya barni na zauna a tare da ku, kicemasa ya daina hararata,wallahi ni tsoroma yakebani, doctor Allah badan wani abu nashiga gaban motar saba, shine nan da kansa ya kadeni nazo tsallaka titi, amma ya tsaya sai cin zarafina yake yana kirana da karuwa,sabida yaga yana da kyau,,,,,,tofa nuor fa ta saki layi,wato duk da halin da take ciki harma, ta hango HAYAT yana da kyau,turkashi😳😁🤭🤔


Ita dai doctor maryam banza tai mata, nuor data ga haka, kawai ta goge hawayen fuskarta, tace doctor ammadai da aljani kukai aure,aka haifi wancen mekama da aljanun ko.🤭🤣

Kai jama,a wayyo cikina, nuor fa taga hayat ya susuta"yar mutane ,tama manta da halin da take ciki🤪

Bude baki doctor maryam tai zatai magana,kawai saitaga nuor tana wani irn abu,atake agurin ta kama cikin ta tashiga kiran sunan ubangiji,tana wayyo cikinta,😭 atsorace doctor maryam ta sakko daga inda take tashiga jijjigata tana cewa,lafiya ke, meke damunki,🤔 doctor dai dataga nuor tana kokarin mutuwa ,sai kawai ta yanke shawarar taje ta sanarwa doctor hayat, yazo yaga meke faruwa,nan ta cika nuor,ta nufi hanyar futa a guje,🏃🏃🏃


Nima bace nayi takaina ,kar doctor maryam suce ni nakashe ta,sabida nikadai aka bari adakin,kafa me naci ban bakiba ,hafsat yi takanki🤣🤣🤣🤪🤪🏃🏃🏃


________________________************~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~************__________________hayat, hayat,hayat, ta shiga da gudu ta shaya agabansa tana maida numfashim,zaro ido hayat yayi cikin tashin hankali dauke akan fuskarsa, yace , doctor maryam lafiya meyafaru? Waccan yarinyar, tafadi, tana yi tana nuna Masa kofar dakin da nuor take, kash doctor ki kwantar da hankalinki,kimin bayani,bangane abin da kike nufiba, know hayat bazaka ganeba, amma kazo muje kaganewa idonka,. Yanzufa yarinyar da kakade tafadi bansaniba ko sumatai ko kuma mutuwa tai ,nidai kawaii naga ta fadi kasa ko mutsi batayi, bata motsifa kikace, doctor,muje,muje dakin yanzu induba,suka fuce gaba dayansu zuwa inda dakin da nuor take,

Suna shiga a kwance sukaganta akasa inda doctor maryar ta tafi ta barta,ko motsi batayi, akidime doctor hayat ya dagata cak,ya maida ta kangadon asbitin,yashiga dubata, amma be ga wani abin da yake damuntaba, dakko abin test din jini yayi ya dibi jininta, kana ya daura mata ruwa ,a hannu,bayan ya gama daura mata ya fuce daga dakin, yatafi gurin gojin jinin,abinda sakamakon yabashi bakaramin girgiza yayi ba ,akidime yace what,wannan yarinyar ,to meya hadata da wadannan cututtukan haka,yasalam ya fuce yabar dakin koma wayayi yasanarwa da doctor maryar nuor tana bukatar karin jini,gashi basusan inda "yan,uwansu sukeba balle adebi nasu,bayadda ya iya jininsa yabada aka duba,aka tabbatar yazo daidai da yadda akeso kuma zai iya bawa nuor jininsa,

________haka aka debi jinin hayat aka karawa nuor,sannan akai mata alllurar bacci don tasamu tai bacci, kafin tafarka yaji ainihin ita wacece,yanzukam ya tabbatar yarinyar tana bukatar taimako,musamman yadda ta kamu da cutar yunwa ,har ci karfinta, ga taifot da take kokarin hudamata hanji sakama kon irin abincin da takeci marasa kyau, da tashin samun kulawa, ayanzu dai halinda nuor take ciki haline na mutuwa ko rayuwa,ba laifi hayat yaji tausayin yarinyar matuka, afarko yazata ,tana sane tashiga gaban motarsa, saikuma yanzu yake danasanin jifanta da kalmar karuwa,😲


,~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~doctor maryam ya samu yafadamata abinda ke damun nuor bakaramin tausayawa yarinyar taiba, hakan yasa ta kuduri niyyar taimakonta,


********************Damisalin karfe 5na asba nuor ta farka, sai zazzare ido take tana ruke ciki sabida azabar yunwar da takeji, doctor maryam ce da hayat suka karaso inda take, suna mata sannu,itako nuor sai binsu take da kallo, musamman ma hayat datake mutukar jin tsoransa, batace musu komaiba, sai dai hannun da tasa ta goge kontacciyar kollar da takeso ta gangaro mata,amma kash sai da hawayen yazubo,murya a sanyaye tafurta,kutaima keni yunwa nakeji, dan Allah,jikina yana murdamin,bazan iya jurewaba, yau kwanana 2 banci abinciba, dan Allah ku daina kallona haka ku bani abinci naci, ko da bazaku taimaka ku baniba, ku bani dan alfarmar annabi muhammad S,A,W, 🙏 nasan,bada ban yana son narayuba, datuni na dade da mutuwa, ubangiji ya rayanine, dan yaga yadda zandauki kaddarata,dakum jarrabawar da yayimun,nikuma bazan gusheba,koda zan rasa rayuwata, bazan daina kiran sunanshiba, kuma bazan daina hada ku da shi akan kutaimake niba,kukantane ya cikarfinta, ta kasa zama hakan yasa ta sakko daga kangadon tashiga murku susu, tana kuka,tun tanayi da karfi har tai shiru sai dai kawaii kaga hawaye yana zuba a,idonta,magana ma ta kasayi ,sai faman girgiza musu kai take alamar su tai maketa, doctor ce tafara zubda hawaye gaba kidaya ta kasa motsi,sakamakon jin kalaman nuor,tabbas zataso taji labarin RAYUWAR nuor,hayat ko dake namijine ya dake,saidai idonsa ya kada yayi jajur,futayayi daga asbitin bakidaya, yashiga dube****dube a hanya, can ya hango me saida doya da kwai cikin sauri ya tsaidashi, yamika Masa dubudaya yace yabashi na dari biyar, medoya ne ya karba ya zuba Masa, hayat ya kama hanya ya nufi asbitin,kwallamasa Kira me doyar ya shiga yi ,amma ina ko takansa bebiba,shiko me doya dayaga haka sai ya kama. Hanya yatafi ,yanacewa kobanza naci riba dari biyar,


Yana shiga dakin ya zube a gaban nuor ya bude doyar, yashiga bata abaki,dan ko hannunta bata iya dagawa,haba wa sai tashiga lauma tana cinyewa tana hawayen, farinciki, azuciyarta tana cewa, Wanan mekama da aljanun,me ye Wanan yake bata me dadi haka,tunda uwarta ta haifeta bata taba cin irin Wanan dadinba🤭🤪🤣



Nima kuma nace nuor koki sammun kina ganidai ina ta hadiyar yawu ,to tuda hakane nikam nayi yajin bada labarinki,sainayi sati,ina hutawa tunda abin hakane, wai kamar ni Hafsat Umar dangoro,dakiyiwa rowa bakomai😡😏😏😏😏😏




__bayan nuor ta gama cin doyarne takallesa tace,Allah ya biyaka dagidan aljanna, Allah yabaka abinda kakeso duniya da lahira, sannan yabaka mata tagari,dakanar bazaj amsaba can kuma ya dan bu'de baki cikin isa da kasaita irin nasu na big guy,


Doctor maryam zo ki kamata ki sata akan gado, okay,tazo takama nuor ta dorata akan gadon,suma guri suka samu suka zauna, akan wani gadon dake face din ta, cikin isa da kasaita hayat yace wacece ke?daga ina kike,?ina iyayanki?

Sunanan nuor,sunan mahaifiyata zainab,sannan sunan "yan uwana,nuoriyya dakuma anty aslamiyya,sai kishiyar mahaifiyata wato innarmu itace mahaifiyar anty aslamiyya,anan fa nuor tashiga zayyana musu labarinta tundaga lokacin da ummanta ta zama mahaukaciyar, har kawo yau da inna ta aiketa hayat ya bigeta,tana kuka hartadasa aya😭


Aguje doctor maryam tafuta daga dakin tai office dinta,tana rusa kuka mara sauti,shiko hayat gaba ki daya mutuwar zaune yayi yajin wani irin daci aransa, tabbas zaiso yayi ido hudu da inna kodan ya ga yadda karshenta zai kasance, sai da alokacin yaji dama yataba haduwa da nuor tun bazanxu ba ,da babu makawa saiya inganta rayuwarta,

Hhhhh🤣kunjifa hayat dawani zance to ai yanxuma bata baciba zaka i"ya taimakon ta,

Futa yayi yabi bayan doctor maryam,azaune yasameta ta kifa kai kan table tana kuka,yasalam, doctor meyafaru haka ,kefadin likitace, amma har akwai abinda zai saki kuka😭, dagowatai ta watsa masa kola__kolan idanuwanta, tana cewa,me kake cewa, kace ni likitace,hmm to dan ni likitace sai akai me nufinka bani da tausayine ko me kake nufi,hayat naga ma jinyata kala__kala, na karbi haihuwar mata dayawa amma ni ban ga abinda yafi tadamin hankali da tausayawa irin wanna ba, natausayawa karamar yarin yarnan, hayat me zamuyi da rudin duniya,ina hankalin mata "yan, uwana yatafi,mesuka dauki duniyar nanne,?, Suna tunanin zasu dawwama acikinta ko me, sun dauki kishin duniya sun dorawa kansu, wallahi summa tallahi hayat kaji rantsuwar dan musulmiko, irin masu halin inna dai_dai kune suke tsallake azabarsu tundaga duniya, kai ,no ,hayat, no,bamasa tsallakewa, Allah yamana tsari dasu, ameeen,sannan zan dauki nuor domin nariketa amatsayin diyata wadda na haifa,

****Know doctor ni zan rike nuor,zan nunamata gata da soyayya tamkar "tar,uwata tajini, what,hayat kanacikin hankalinka kuwa, bazai yuwuba, nuor fa macace ba namijiba,kai kadai kake zaune a babban gidanka dake cikin nasarawa,sai kuma gidan yayanka dake nan kano,kuma kamanta aikine yakawoka kano ,sauran fa wata biyu kacal ka koma gombe,eeh nasan da hakan zan kaita gidan yaya abdul,tazauna da ita da matarsa, kafin nakammala abin da nake,sai natafi da ita gombe,a,a hayat ni ban yardaba saidai kazabi daya acikin biyu indai kana son rukon nuor, okay inajinki fadamin,sharadin shine ko ka aureta, 🥰ko kuma kabar ta agurina na riketa, me ?😳yazaro ido, in aureta fa kika ce, ni din ,kamarni,ni badan na aureta zan riketaba,sai dan kawai na taimaki rayuwarta,hmmm hayat kenan to tunda bazaka iya auren taba ,zaka iya hakura kabarta a hannuna,bazai yuwuba,agurina zata zauna,ya buga table din yajuya, dakatar dashi doctor maryam tai tace,ni dai nafada maka kaje Kayi shawara, zuwa gobe, dan wallahi bazai yuwu kana namiji balagagge ka zauna da ita agidankaba,tunda ba maharra marka bace,kai kawai ya jinjina ya cigaba da tafiya. Saida ya bar asbitin sannan yakira doctor maryam yace tadauki, nuor ta tafi da ita gidanta ta gerata, zai tahomata da kayan sawa,to tace sannan takashe wayarta,


4
***********************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************wai dan uwar yarinyar nan ni zata mayar mahaukaciya, ni makira jikar shegu, ni,ni inna "yar gidan ,tanko,shege,wato nizata gudarwa,haba inna kuyi hakuri,yanzu har iyayan nakima kike shegantawa,matsacan dan ubanki,nashegan tasu din idan nasheganta su ,akwai ubanki,aciki,wallahi zanyi kuli klin kubura dake, shwgiyar yarinya,duk bake kika jamin wannan bala'in ba,tunkan ta girma nace,zan wurgata lahira,saikuma nafasa memakon kibani shawara kikaki,sabida ke "yar abi yarima asha kidane,;)😏kiyi hakuri inna to mekikeso lokacin nace miki,in ban bite mikiba,uwarki,nace,uwarki, aslamiyya,nikike fadawa haka,ai dasaiki taimako da wuka alokacin muyimata yankan rago amma kika ki, gashinan zataje, tasha iskar duniya,oh,ni inna naga takaina,yanzufa mebi tana can tana cin kayan dadi,saiko inna tafashe da kuka,tacigaba da balbalin bala'inta,


________________anty Aysha kiyi hakuri dan Allah kidaina kuka, duk Inda nuor take insha Allah,zamu ganta,aisha ta bare baki tana rusa kuka,wallahi,ba bata taiba,nasan wannan muguwar innar tasuce ta kashemin ita,tun bayauba na tabbatar da matar nan batada imani ,kokadan,batasamu dugonsaba,nasan zata iya komenene,Indai wannan muguwaratarce😭😭


Tofa Allah sarki Ayshat kiyi

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment