Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

RAYUWAR KASKANCI~~~~~~~~~~~~~~~~
~~~~ By

Hafsat Umar dangoro BAKIN RAFEE


~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

©️ JARUMAI WRITAR's ASSOCIATION 📚📚⚜️ J. W. A🖋️






BOOK 1 📘







________Godiya

********Bismillahirrahamanirrahim dasunan Allah mai rahama me jinkai tsira da amincin Allah sutabbata da shugaban halitta annabi muhammad saw da yayayensa da sa habbasa bakidaya

****Ina godiya ga ubangijin madaukakin sarki wanda yabani ikon rubuta wannan littafin mai suna RAYUWAR KASKANCI

____________Waddani Hafsat Umar dangoro na rubutashi domin fadakarwa ,da kumailimantarwa, rashin imani ,tausayawa,nishadan tarwa,rashingata, dadai sauransu wada duk acikin wannan littafin zaku hadu da wadannan abubuwa 6





********Wannan littafin nasadaukar da shine ga kanwar mahaifiyata fiddausi wadda take zaune a doguwa dakuma ita kanta maigayya mai aikin wato ummana hindatu sale yusuf yar mutan naibawa yan lemo,



Ina mukufatan alkairi da godiya

agareku mutanan amana

1 masoyiyarka kuma abar kaunarta my blood Rukayya (ameera) ina mika. Sakon gaisuwa agareki ,

2uncle usamma

3musa baffa4baffana


5ummana

6kanwata amina mama


7 nabilata kanwata kuma kawata yayar mujahid da maryam da mina

Pages 1

__________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________A garin kano a cikin kasuwar na ibawa yan lemo wadda a kullum cike take da tarin jama a .masu siye da siyarwa nakusa da na nesa inda kowa kagani agurin harkar gabansa yakeyi musulmai da arna kowa kasuwancinsa yake cikin nishadi da kwanciyar hankali gefe guda kuma wata karamar yarinyace wadda bazata wuce shekara 13 kacal aduniyaba tatusa robar abincin siyarwarta agaba ta zabga ta gumi da alamadai tunanin wani abu takeyi wanda ya shafi rayuwarta don hawayene ke ambaliya daga idonta sai faman gogewa take da wani ya lolan hijabinta duk ya kode ya yayyage kayan jikin tama hakan take domin suma duk sunji faci da gera amma duo da haka wani gurin yayage sabida ita kanta atamfar tagaji da duniya. Da alamadai wanan yarinyar bakaramin talauci take cikiba banace da ita da iyayantaba dan banyi tunanin tanada iyayeba .wata matashiyar budurwace tataso daga inda take sana arta ta dawo kusada wanan yarinyar zamatai kana. Tarike hannunta ta janyo ta jikinta tafara bubbuga bayanta tanacewa .yishuru bAiwai Allah banaso naga yaro yana kuka kokuma naganshi acikin damuwa banason hakan ballantana ma ke dana ganki karamar yarinya mai karancin shekaru .shirutai wanan yarinyar tanajin abinda matashiyar budurwar take cewa wani mutumne yayi tsaye akansu yakirawo matashiyarnan yacemata Ayshat wanan yarinyar da kike gani kullum intazo nan batada aiki sai kuka duk tabi tasawa kanta damuwa ita ba kibaba amma sai nunkufurcin tsiya duk tabi ta tsotse ta kanjame kamar wata me cutar sikila ya isa haka da allah malan bacemun daga gani banisonjin abinda kakecewa meyasa dakaganta cikin wanan yanayin baka taimakamataba cewar Ayshat allah yabaki hakuri Kinga tafiyata nabarku lpy

To yana tafiya Ayshat takalli yarinyar sanna tace yasunanki? (NUOR) masha Allah suna me dadi , nuor ina iyayanki suke? NUOR ce tabude baki zataimagana amma kukanda take yakaracin karfinta tafashe da kuka tanacewa ummana umman hasina babana duk basa tare dani nikadai nake wahala banida kowa sai allah duk tarabani da kowa .to agurin wakike da zama ? Gurin Innata da anty aslamiyya.



Tofa ko itawannan yarinyar wacece to meyasa yarshekara 14 takeyin tallah ina iyayanta suke me ya sa takeyin kuka .kubiyoni donjin sanin ko ita wacece.

Aisha ce tasake jefawa nuor tambaya.to meyasa kuma karamar yarinya kamarki kikeyin talla kuma wacece ta rabaki da ummanki da umman hasina da abbanki? Innatace. Innarki kuma to meyasa ta rabaki dasu kuma wanene yake doramiki talla? Innatace take doramin talla.wacece innar taki ita batasan yaroba kekam ai naga baki isa yin tallaba kuma menene da lilin rabakida iyayanki da tai sanan ita wacece agurinki alokaci daya aisha ta watsowa nuor wanan tambayoyin da ita kanta tambaya daya zata iya amsamata aciki .kinyi shuru nuor baki bani amsaba? Ita din kishiyar ummana ce .to inane gidanku? A unguwa uku nake .what tundaga unguwa uku kike tahowa to amekike zuwa ko adaidaita kike hawa ?a,a akafa nake zuwa nakoma akafa banida kudin adidaita .bangane bakida kudin adaidaitaba to ga kudin tallankinan .a,a idan na kashemata kudi saita yankani . tabdijan amma wataranfa harkarfe 10:00 kina zaune anan gurin kuma ahaka kike tafiya ? Eh saidai wataran inasamun ataimaka aragemin wanya .aysha ce tace nikuwa nuor zanso sanin labarinki zakifadamin ?eh zan baki lbrna .tom nuor kenan baiwar Allah.


Wacece nour?

______________********************************************************************______________Nidin yar asalin garin kano ce haifaffiyar unguwa uku mahaifiyata kam yar asalin garin gombe ce aurene yakawota kano ayadda umman hasina tabani lbarin ummana alokacin da suna yanmata da samari da iya da mahaifina iyayanta sunso hadata aure da kanin mahaifinta wato aziz ansari amma sam mahaifiyata ta tubure ita abdullahi takeso wato babanakenan wannan abindatai yasa **ab************************************banta** yaji haushi yace ya amince zai auramata abdullahi amma da sharadin karda ta kara waiwayarsu amatsayin iyayanta ummana sabida soyayya tarufemata ido bataji bata gani yasa ta amince da sharadin mahaifinta aka daura mata aure da ita da abdullahi sukamata komai dayakamata ayiwa diya kana aka kawota garin kano batare da tasan wani acikin garin kano ba daga babana sai ubangijin da ya haliccemu .satin ummana biyu agidan babana kishiyarta wato innarmu tasa babana yacanzawa ummana layin wayarta yazamana batada number kowa acikin ahalinta .anahaka ummata tasamu wata kawa nankusa da kidanmu itace umman hasina tadauki umanna kamar yar uwarta wadda sukafito ciki daya kwance atashi a gurin Allah ba wuya Inda ummana ta cika shekara 5 agidan mahaifina ko batan wata vatatabayiba gashi inna ta asirce mahaifina gatakura da musgunawa datake samu a gurin kishiyarta da diyar kishiyarta aslamiyya akwana atashi saiga ummana da ciki wannan cikin da ummata samu bakaramin daga hankalin inna yayiba haka tadinga bin bokaye da matsafa amma cikin dai yaki zubewa tunda ubangiji yariga yatsara saina zo duniya to tafitafi cikin umma yacika wata tara da sati daya Inda umma ya bata yara kewawa aibiyu tayi murna sosai da samun yaran inda aminiyarta wato maman hasina ta shiga tafita har aka samu akai suna akasawa yaran nata nour da nuoriyya .masha Allah tafitafi kwana na karewa watanni na dada cinyewa da taimakon ubangiji mukakai shekara 10 danida yar uwata watarana ranar da bazan taba mantawa da ita a rayuwataba ranar datazamemin bakinciki da zama marainiya mara gata muna zaune danida ummana da maman hasina dakuma yar uwata nuoriyya saiga wani hayaki ya taho tacikin hundo yana doso ummana atake yashiga jikinta ta mike tafuta daga ita sai daurin kirji ko dan kwanmli babu nuoriyya ce tafuta tabita aguge tana kiran umma amma umma tariga da tayi nisa mutaneko saibinta da kallo ake kowa yakasa taimakommu harta tsallaka titin aguje nuoriyya tabita aikafintasauka daga kan titin wani me mota yayi awangaba da ita jikake tuss runtse ido nayi sakamakon jinin yar uwa ta da yazubomin afusa atake gurin ya cika da mutane anzagaye gawar yar uwa ta shiko me motar da yayi aika aikar ko tsayawa beyiba yagudu maman hasina nace takarasa gurin aguje ai tana hada ido da gawar nuoriyya ta runtse idanunta dan yadda gangar gikin nuriya tai fatafata wa iyazubillahi .karasawanai gurin nakafe gawar yaddanaga ta dagargaje kamar an malkadata ne yasa nafara ganin jiri atake nasulale akasa wayyo Allah na dasauri maman hasina ta daukeni takaini wani karamin chmis dake cikin unguwa uku tabiya kudin kana tafito zuwa gurin gawar nuoriyya Inda tatarar har an yayyafamata ruwa an hadata sabida baza a iyamata wankaba haka tanaji tana gani akatafi kai nuoriyya gidanta nagaskiya .😭
Ke duniya ina zaki damu Allah yasa mudace Ameen.


Bayan umman hasina takoma chmis din tatarar harna tashi idonako ya kekashe ko hawayanma babu acikinsu sai dai wutar datake ruruwa acikinsu nadaukar fansa . Rikenitai muka huce gidanmu Inda tasamu inna da aslamiyya tunsa kida agaba sai rawa sukeyi wai sun rabu da kaya .hakaneyasa nafahimci dukkan abinda yafaruda ummata da nuoriyya itace sula .umman hasina ce takarasa gurin ta tace haba baiwar Allah memahaifiyar nuor taimiki sanan meyarinya yar shekara 10 kamar nuoriyya taimiki tur da irin halinki muguwa .sanan nuor bazata zauna agurinkiba zanriketa sabida nasan muddum zatazauna a gurinki wataran itama saikin kasheta Wata mahaukaciyar dariya inna tayi sanan tace daman ko kin barta bazata zauna agidannanba wlh inzanga kura tana cin naman jikin wanan yarinyar bazan taimaka mataba.umman hasina ce takama hannuna tana share hawaye muka nufi gidanta yakasance itace cina da shana haka suturata haka kudin makarantata harna kammala js3 zanshiga ss1 wani balain yakara turo kai wazan gani innace atsaye akanmu tarike kugu tanacewa wai tazo tatafi dani umman hasina nace tace bataisaba ba Inda zatatafi dani nan inna tafice tabar gidan a fusace .itako umman hasina zamatai tafashe da kuka dan tasan dolene sai inna ta karbeni nan. Muka zauna danida anty hasina muna rarrashinta hartai shiru .

To itako inna tana komawa gidatatararda babana Allah ya Masa rasuwa nako tafice takirawo mutane akazo aka hadashi akamasa wanka sannan aka tafi kaishi gidansa na gaskiya bayan antafi kaishine inna da ita da aslamiyya suka kaori dukkan mutane da suka zo musu gaisuwa sanan su kashiga murna wai sunci gadon gida.


Waiyazubiyyahi duniya ina zakidamu Allah ya tsaremu da irin wadannan matan uban .

Aslmualaikum inwakowa Fatan alkairi dafatan kowa tanacikin koshin lpy ina Kira da iyaye wadan da suke sake akan rashinyin addua ko kuma sallah akan lokaci hakanne yakesa asiri yake saurin kama mutum sanan ina Jankunne da iyayanmu mata wadanda suka dauki kishi abar gabarsu ko makiyiyarsu dan girman Allah yaruwa agera arage kishisanan ina Kira da kishiyoyinda ba tsoron Allah kotakota acikin zuciyoyinsu wadda suke haukatarda abokiyar zamansu kokuma su haukatata ko sudau yayan kishiya sudinga azaftardashi lake wanan yarinyar nuor bakomaine yaja hankalina akan rubutun wanan littafiba saidan inso na tunasarda yan uwana. Mata da sucanza su gera halinsu dan Allah badanniba inaso kugera


Kuma bama hakaba mostly irinwannan abubuwa nafaruwa sosai aduniyarnan. Dan yazama na yanxu dan kishiya ta wulakanta danda banataba kamar ruwan dare please sisters agera ngdðŸ™

To innace ta debowa maman hasina yansanda inaji tanagani inna ta dauki nuor .haka nakoma gidanmu cikin wahala da tsangoma da kuma kera duk kayana da umman hasina ta siyamun da kayan dakin ummana inna ta kwashe tasiyar ta auno shinkafa tafara doramin tallan shinkafa da wake tabarmin kaya kala biyu da kuma hijabai suma guda biyu da sunake rayuwa duksun yage sun kode ga dakin ummana ko leda babu hakanake shimfida dan hijabidaya na kwanta na lulluba da guda daya gacin naku da beraye duk acikin dakin daker nake iya bacci abinci kuwa saiya kwana uku kafin abani naci batun wankada sabulu tun ina gidan umman hasina .idannaje talla nakai dare tace natsaya karuwanci idankuma nadawo bansiyarba ta dakeni tana kuka takarasawa aysah labrinta sanan ta share hawayan ta . Aisha wadda tuntuni hawaye yawankemata fuska sabida tsananin tausayin nuor sanan tace.kiyi hakuri kinji nuor akwai allah.allah yana taredake kuma duk wanda ya cuci wani sai allah ya sakamai kicigaba da hakuri kinji.

Allah sarki baiwar Allah kenan .
Rayuwar kaskanci by Hafsat Umar dangoro. Yarmutan BAKIN RAFEE ðŸ™__________________________________________________ ******************************** Tom bayan Ayshat ta rarrashi nuor sanan tace mata gashi kuma naga baki siyarda abincin nakiba .eeh baikareba .to jirani nadawo yanzu . Nuor ce tace to .bayan Ayshat tatafi bata********************************************************************************************************************************************************************************************************************************fi minti 10 ba tadawo dakudi masu yawa ahannunta zamatai sanan tace nuor nawane kudin abincin naki .dubu ukune cewarnun to karbi nasiye abincin duka hakan yayi.zaro ido nuor tayi sannan tace anty Aisha ina kika samo kudi haka da yawa . murmushi Ayshat tayi uhm kanwata kenan yanxu inbansharemiki hawayeba wazan sharewa wayata na siyar don nabaki kudin abincin naki sai kidibi yadda zai isheki kici ragowarkuma kibawa almajirai .rumgumeta tai tana kuka sannan tace nagode anty.sanan nuor tadibi abincin taci raguwar ta bawa almajirai .kana sukai sallama da ita da Ayshat kowayanufi gidansu .

To ina karasa wagida natarar da inna a tsaye karasawanai na tsuguna nace inana ga .aikafin nakarasa ta kwasheni da wani wawan marin dasaida na hantsila nai Baya damko wuyana tai tace bani kudina .mikamatanai amma hallokacin bata sakeniba .tacigaba da magana karuwar banza kawai mai irin halin iyayanta daman na san kedai yar shegece dan bakida hali irinna abdullahi saida kika je kikagama karuwanciki sanan zakidawo ni inanan hankalina duk yatashi sabida tsoran kar atareki akwacemin kudi wlh da kudinnn baikaiba yau agidanan ba mai kwatarki sanan kuma ga wankin kayan aslamiyya can tace idan kindawo ki dauka kiyi .fashewa da kuka nai sanan nace dan Allah inna kiyi hakuri wlh babu ruwa agidannan dan Allah kibari gobe sainayi aikafin na rufe baki takaramin wani marin haguda dama jikake tasssss tasss idan nabari saigobe zaki wankemata ubankine zai dauki tallana fuuu ta sakeni tashiga daki tadakkomin bokiti ta cillomin huce kitafi kidaibo tunkafin na karkaryaki agidannan yasalam shigewanai na futa bakowa akofar gidan sabida dare yayi jikake tsit ko ina sai haushin karnika kawai kakeji . Saida nayi tafiya mai nisa sannan naisa Inda rigiyar take bayan nagama dinban ruwanne na juya zandauki ruwana intafi kamar anjawoni tabaya jikake tsundummmm nafada tun ina ihu harnadaina sabida nariga da nafarayin kasa .wani bawan Allah ne ashe tun lokacinda na shigo diban ruwan ya ganni shima ruwan zaidiba akan idonsa nafada rijiyar tsalleyayi yashiga rijiyar dake bawani zurfi garetaba. Yadakkoni yafito dani ba ajiyeni ako inaba sagidanmu sanan yadawo yadauki ruwana ya kaimin gida ganiyay harlokacin ban tashiba hakaneyasa yayi tunanin ko nasha ruwa durkusawayayi yafara danna kirgina zuwa cikina saiga ruwa yana bulbulowa daga bakina bude idonai kana mutunmin yayimin sannu sannan yafice ai yana futa inna tace tashi munafuka wankinne saikinyi taitsaki tashiga daki .

To hakanadauki wankin nafarayi ina kuka bangamaba sai sakiyar dare bakowa saini kadai atsakargida .bayan nagama wankin nashiga dakin ummana na shimfida hijabina akasa na kwanta nafara bacci aikamar da ga sama naji sauro yafara cizona gashi gari balokacin sanyiba balle na lulluba .ahaka dai na daure na dakko dayan hijabina na rufa duk zafinnan harnasamu nai bacci dakerTo haka washegari nuor tatashi da asba taisalla suko su inna sallar bata damesuba dan nidai duk zamana agidan bantaba gani sundau buta sunyi alwala da sunan sallahba .
Garine yawaye Inda inna tadakkomin tulin wankewanken nazauna nawankesu sanan nadau tsintsiya na share ko ina agidan tunda daman nasan aikinane yin wanke wanke da shara .



2

To haka nacigaba da rayuwa agidan kamar baiwa narasa duk wani gata aduniya idanda wuya tana kisa nasan datuni na dade da mutuwa jindadi kuwa da man bansan menene shiba. To yau natashi cikin tsananin rashin lpy kainane yake ciwo ga zazzabi ga ciwon ciki can kuryar dakin ummana na makale sabida sanyin da nakeji wani yalolon hijabina nadakko na lulluba duk ya yage ga uwar dauda ajikinsa ahaka nasamu na rufe jikina .can bayan minti 3 saiga inna tashigo da wata zabgegiyar bulalarta wadda ake mata lakabi da yar sabis tadukan jaki .tana karasowa tafara zubamin bulalar ajikina ihu nashiga yi kamar wadda ake yankar naman jikina . hakuri nashiga bata ina cewa dan Allah inna ki keleni wlh banida lpyne bazaniya zuwa tallaba kirabudani kidaina dukana zanje wlh zanje .tukunna ta keleni tace huce kije kidauka tunkafin na karamiki ai dasauri nafito nadauki dayan hijabina da na wanke ko bushewa be gamayiba daman da ruwa nawankeshi sabinda nasan inna bazata bani omoba aguje na daukayan tallan na fuce daga gidan ina share hawaye.

Innalillahi wainnailaihirraju Allah ya rabamu da irin wadannan matan uban Ameen.

Ina isa gurin tallan natarar da anty Aisha ahartazo takusa sayar da nata nan na karasa muka gaisa .meyafaru dake nuor naga idonki yakumbura kuka kikayine ko yauma innartakice tadakeki shuru namata banmata maganaba sai dai kollar da take idonace takarasa sakkowa . nuor kifadamin gaskiya meyasameki .kukana fashe dashi sanan nace anty banida lafiya kuma tace dole sainazo talla danace banida lafiya shine tadakeni nan na nunamata Inda taga duk jikina yafarfashe sabida duka nibanma kulaba ashe bayana jini yakeyi .daganitai ta kwantar dani ajikinta sanan tasharemin hawayena .kiyi hakuri nuor akwai Allah yana gani kuma shizai fitardake daga hannun wanan azzalumar kishiyar umman taki kicigaba da hakuri allah yana tare dakekinji nuor.anty narasa menaiwa ubangiji daya hadani da wanan jarabawar anty menayiwa inna me na tsaremata aduniya da har ta tsaneni haka .bansan menene dadin uwaba bansan ya ake farinciki arayuwaba anty tun ina jaririya nake kuka bansan ranarda hawayena zai daina zubaba.nan kukan datake yakara tsanan ta snann tacigaba da magana dan Allah anty kitaimaka kisiyomin abinda zansha wanda ko minti 1 bazan kara aduniyaba inbar wannan duniyar mecike datarin azaba inje nahadu da yar uwata nuoriyya inama ace wanan dureban da yabige nuoriyya tare yabigemu datuni nahuta da yin RAYUWAR KASKANCI .auzubillahi nuor menakeji daga bakinki haka haba nuor karkizama mace mara dangana mana saikace bakisan jarabawar ubangiji ba please kidaina cewa zaki kashe kanki kosokike kimutuyar wutane ko bakison mushiga aljanna tare .ko kinason fishin ubangiji ya tabbata agareki . nuor ce tace a,a anty inason ganinmu tare a aljanna. To kitsaya kisaurareni kiji manzon Allah saw yace duk mutumin da ya nasane yakashe kansa makomarsa itace wuta .yanxu nuor zakiso kishiga wuto .aa to kidaina tunanin zaki kashe kanki kinji kicigaba da hakuri .tom antyna cewar nuor murmushi aisha tai sanan tace Kinga nuor kayannan naki ya yage gasu sun kode anaganin jikinki gobe in Allah ya kaimu zan debomiki wasu kayana dasuka mun kadan .

To haka sukacigaba da hirarsu harsuka sayarda abincinsu kowa yatafi gida .
Ayshat tana komawa gida tatararda babanta yana zaune gaishesa tai sanan tashiga gidan ashe itamadin marainiyace dan mahaifiyata tadade da rasuwa daga ita sai mahaifinta da kannanta guda biyu mace da namiji suke yaruwa agidan.to shigatai taci abinci sannan ta dauro alwala tai salla tashiga yin adduoi tanacewa ya ubangiji ga baiwarkanan kataimaki rayuwar nuor karkabarta tashiga wani hali kasamata dangana azuciyarta ka rabata da innarta lpy ya Allah ka saukakamata rayuwarta ya allah duk wanibawa da yake cikin irin halinda nuor take ciki Allah ka cireshi daga wanan alin .sannan tace Allah nakawo kukana gareka kataimakeni karufamana asiri Allah karka barmu da iyawarmu kataimakeni na iya ruke marayun kannena sanan ta shafa addu ar .tatashi

Niko nace ameeen

Abangaren nuor kuwa tana komawa gida tabawa inna kudinta sanan taceinna yunwa nakeji.tsawa ta daka mata kinkawo min kudin cefanen to bangirka da keba .tashitai takoma dakin ummanta tazauna tazabga tagumi tanatuna rabanta da cin abinci tunjiya da safe tunani tafarayi yanzu haka rayuwarta zata kasance nan gaba yaushene zatasamu yanci yaushene zata fita daga RAYUWAR KASKANCI ahaka bacci yadauketa .cikin dare tanabaccin cinnaku suka shigemata riga inda suka samu daudai gurinda inna tafasamata sukadinga gasamata cizo a cikin ciwon ai dasauri ta tashi zaune tamakale ajikin bango tafara gurza gurin abangon sabida azabar radadin da gurin keyimata waiyazubiyyahi duk jini gurin sabida bayanta datake gurzarsa abangon saida taji yaragemata zafin tukunna ta zabga tagumi nafa tashiga tunanin kawai gora yakashe kanta ta huta tinawatai da rijiyar datataba fadawa mikewatai zumbur kamar an tsikareta tanufi kofa kawai sai tatino da maganar da aisha ta fadamata mundum takashe kanta zata mutu yar wuta .komawatai ta zauna tana kuka tana ambaton sunan Allah ya kawo mata dauki.tafita daga cikin RAYUWAR KASKANCI.atake agurin zazzabi mai zafi ya rufeta nandanan tafita daga hayyacinta .amai tafaraji aguge tafito tsakargida tana kakarin amai amma ba abinda yafito sakamakon babu abinda ta saka abakinta tun jiya sai ruwakawai da yawu haka tacigaba da kakarin amai abin tausayi Allah sarki baiwar Allah.innace kamar amafarki taji ana amai futuwatar hannunta dauke da wanan zabgegiyar bulalar tana zuwa tafara zubamata ajikinta hargurin ciwonta daya ke jini nan tafara masifa karuwar banza karuwar hofi kinje kinyi cikin shege kinzo saidamunmu kikeyi muna bacci.budebaki nuor tayi daker tace wlh inna banida lafiya na baciki.kafin takarasa maganar wani wawan naushi takaimata abakinta harsaida nuor ta hantsila bakinta ya fashe sai gini atake agurin nuor ta sulale kasa jikake temmm komotsi batayi .innakam hucewa daki tai tacigaba da baccinta hankalinta a kwance .to ita kuwa nuor tunda tafadi agurin ta kwana .innace da sassafe ta fito tasamu nuor ainda tatafi tabarta .ita tama manta da wata nuor tasuma .


Kujifa wani zalinci to idan yartace zata mantada itane .Allah sarki baiwar Allah


Komawa daki tai ta debo ruwa mai sanyi ta watsawa nuor afurgice ta bude ido hawaye nazuba a idonta dotake tatashi amma takasa tashi komawatai takwanta a gurin tarutse ido zuciyarta na tafarfasa kamar wuta .inna ce takoma ta dakko abincin da suka agiyemata tunna shekaranjiya takawo ta ajiye agaban nuor ai batasan sanda tatashi tafara zuba laumaba harsaida ta cinye shi tass .saida nagaba ci tukunna na ga abincin bayan wani wari dayakeyi har yafara tsutsa ba abin na amayo dashiba bansan me zankara ciba dan inaga daga yau sai jibi nida nakaracin abinci .ga umman hasina sun tashi bansan Inda suka komaba ga anty Aisha tadaina zuwa gurin talla kwana biyu daman ita nake gani naji dadi to itama nadaina ganinta wayyo Allah na ni nuor Wana sabo na aikatawa ubangiji sannan takalli sama tace ya ubangiji dan Allah dan darajar annabi muhammad saw idan nayilaifi koda bansaniba ubangiji kayafemun kafitardani daga kuncin rayuwa sannan tatashi tana share hawaye.

To yauma kamar kullum babu anty Aisha ba labarinta haka nasiyar da abicina yauda wuri nakoma gida tom haka nacigaba darayuwa cikin kunci da tashin hankali tafitafi yausati daya kenan anty Aisha bata zoba gashi bansan gidansuba wayyo Allah na ni nuor

To

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment