Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

https://chat.whatsapp.com/F1uZsFAFSUI6dIRXSQ1niH

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F1uZsFAFSUI6dIRXSQ1niHhttps://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

A'ISHA LABIBA 🌺❤️

LOVE AND REMONTIC

SHORT STORY 📚✍️

MALLAKI N

MEERAT UMAR ❤️💞

AUTAR JAJIRTATTU 💪 CE

.

Ya Allah yan da na fara littafinan lafiya Allah ka sa na gama lafiya Allah ka sa darasin da ke ciki ya amfani yan uwa musulmai Ameen,

Bismillahi rahamani Rahim,


Ban yarda wanni ko wa ta ya juya min labari ba ba tare da izzinina ba ko a karanta mun ta YOUTUBE ba tare da an tambaye ni ba idan kuma hakan ta kasan ce na bar mutum da Allah,





1,.
ina zaune cikin bedroom ɗina naji kamar ƙara Mota tsaki na yi dan na san babu wanda zai shigo cikin gidanan ya na gudu da mota,sai ya Ayan, ta shi na yi na leƙa ta window dan na tabbatar wa da idona Ai kuwa ina leƙawa na gan sa
Ganin ya yo hanyar part ɗin mu ya sa na yi sauri na koma kan bed na kwanta dan na san dole ne sai ya zo ya ta kuramin,

Ji na yi am buɗe ƙofa, da sauri na ja belanket na rufe har kai na kamar mai bacci Mami na ji ta na magana "ai kam ka ganta nan ta na baccin, da ta sa ba ayi mutum kullum shi ya yi ta zaman ɗaki," ni dai ina jin su, munshari ƙarya na fara dan su tabbatar da gaske bacci na ke,

Ina ji Mami ta fita ta bar ya Ayan acikin ɗakin, wajan bed ɗin ya zo ji na yi an ya ye min belanket ɗin shafa gefan fuska ta ya yi " My "A'ISHA LABIBA 🌺 ta Allah ya mallakamin ke ki zama uwar ya'yana ina sonki sister amma ban son dalilin da ya sa ki ka tsaneni ba why LABIBA 🌺" na fashewa ya yi da kuka,duk da wannan abun da ya ke hakan bai sa naji tausayin sa ba , ni kai na shedace akan yadda ya Ayan ya ke sona amma ni kwata- kwata ba na sonsa kuma babu abin da na tsana Kamar na wayi gari na ga wannan mutumin, a raywata,

Bayan ya gama sambatu sa ya fita, ta shi na yi ina jan tsaki haba mutum kamar wanni maye, na ce ba na sonka ba sai ka ƙyale ni ba mtsss na ƙara jan tsaki


Bayan tafiyar ya Ayan part ɗin su futowa falo na yi Mami na gani zaune ta na kallo "auta kin ta shi ɗaga ma ta kai na yi Alamar eh yanzu ya yan ki ya fita har ɗaki ya shiga ki na bacci" turo baki na yi ban ba ta amsa ba" ko baki ji mi na ce ba" " naji Mami Ai tin da ya tafi wanni lokacin ma haɗu", "hmm Allah dai ya shirya min ke wai ace mutum ya ce duk Duniya babu wan da ya tsana Kamar ɗan uwan sa to idan baki sani ba ki sani Ayan tin ki na yarinya shine ya yi rainon ki ya ci kashin ki ya ci fitsari ki sai yanzu da ki ka girma ki ka ga kin zama mace sannan zaki ina wulaƙan ta shi to wallahi a hirr ɗin ki LABIBA ba zan ɗauki hakan ba sakarya kawai"

Haka Mami ta ƙaraci faɗan ta ban ce ma ta komai ba ni dai kawai abu ɗaya na sani shine na tsani ya Ayan kuma ba na son ganin sa ko mutuwa zai yi ba zan taɓa auransa ba Ahh,

Washegari da wuri na ta shi dan ina da lector kuma ba na so na yi late fitowa na yi harabar gidan mu zaune na ganshi acikin mota da alama kuma ni ya ke jira ban bi ta kansa ba na ni fi in da idi drive ya "ke kai idi ta so ka kai ne school kar na yi let,"

"Idi I zaman ka idan ba za ta zo ta shiga mu tafi ba to sai dai ta fasa zuwa makaranta" ya faɗa a hassale sani idan ban shiga ba sai dai na haƙura dan na san halinsa buɗe ƙofar baya na yi na zauna be cemin komai ba ya ja motar'sa,


Mu na isa na sauka ko godiya ban ma sa ba fatima na hango da alama ita ma ba ta daɗe da shugowa ba rungume juna mu ka yi mu na murna dan Allah ya sani duk duniya ba ni da wa ta aminiya Kamar Fatima,

Ya na komawa gida kai tsaye part ɗin sa ya wuce ya na da fe da ƙirjin sa" wai shin yaushe ne LABIBA za ta gane abin da na ke ji a kanta? "

Wanni babban bedroom ne mai Kyau da girma ga wasu kayan na alfarma Royal bed ne shin fiɗe a ɗa ki ga ba ɗaya ɗakin pic LABIBA 🌺ne tin da ga saman bangon ɗakin har zuwa jikin derowa ɗin, ɗakin, wa ta durowa ya jawo mai ɗauke da muhimman ta kadun sa buɗe ta ya yi akwati ya ciro yar ƙarama mai kyan gaske abin da ya ba ni mamaki gaba ɗaya pic LABIBA 🌺 ne a ciki har da wan da su ka yi ta na yarinya, Alokacin da ta ke ji da shi komai ta ɗauko ya Ayan ɗinta ti na wa da haka ya sa ya fashe da kuka mai tsima rai, Ayan jarumine amma akan LABIBA 🌺


jarumatar duk ta gudu ya na ji kamar in ya rasa ta wanni abun zai faru da shi,

To fa a kwai chakwakiya shi fa Ayan ya na tsananin ƙaunar LABIBA 🌺 to amma fa in da matsalar ta ke ita ba ta san sa kuma ba ta ƙaunar ta buɗe ido ta gansa anya kuwa bai ɗaukarwa kan sa wahala ba,?

Ma su tambayar littafin rayuwar mafarkina payment ne idan kin yi shirin biya kimin magana karki ba ri ayi tafiya babu ke dan yanzu ma aka fara wasan ayanzu ne zamu ji yadda a ka haifi Afaf da kuma yadda wainan sheɗanu su ke bi biyar rayuwarta ki biya ki sha karatu sister, 500 amma na yi duba da yan da mu tane su kace na rage mu su hakan ya sa na mai da shi 400, domin jin daɗin ku shine na mu

AUTAR JAJIRTATTU 💪 ce

Comments and share,
https://chat.whatsapp.com/F1uZsFAFSUI6dIRXSQ1niH

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F1uZsFAFSUI6dIRXSQ1niHhttps://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

A'ISHA LABIBA 🌺

LOVE AND REMONTIC

SHORT STORY 📚✍️

MALLAKI

MEERAT UMAR

AUTAR JAJIRTATTU 💪 CE

____________________________________
BISMILLAH I RAHAMANI RAHIM,

2,

Bayan na dawo da ka school wanka na yi na shirya tsaf cikin doguwar riga mai kyan gaske fake kai na na yi wan da kullum ya ke ba ni wahala fakin wani sain ma sai dai Mami ta fakemin shi dan Allah ya sani ina jin wahala ba yan na gama shiryawa part ɗin su ya Ayan na wuce saboda na je na ga Momy samun ta na yi zaune ta na waya da alama kuma wayar mai mahimmanci ce ji na yi ta ce "ka ganta nan ga ta ma ta shigo bari na baka ita" miƙa min wayar ta yi duk da ban son wanene ba amma sai da naji faɗuwar gaba

Murya ya Ayan ce naji ta doki dodon kune na "hello Angel" naji ya faɗa a kasale ban ba shi amsaba kuma bai damu ba ya cigaba da min magana eh kawai na ce ma sa na kashe wayar, Yusra ce ta shigo cikin palon ta na murna rungumeni ta yi "sister Albishirinki goro na ba ta amsa da ma Uncle Jabi ne ya ce gobe in Sha Allah I yanzu sun sauka" ni ma murna na shiga yi dan mun shaƙu da Uncle Jabi sosai ga shi ya na shagwaɓɓa mu dan idan ya na ƙasarnan tofa ko tsawa ba ya bari amana wannan dalili ya sa ba ma so ya tafi ƙasar faris

Momy ce ta dube mu ta na dariya "ai dole kuji daɗi tin da mai goya mu ku ba ya ku yi abun da ku ke so zai dawo ba"

Banbar part ɗin Momy ba sai kusan 9:00pm dan Allah ya sani ina son Momy sosai kuma ita ma ta na sona ina shiga na tarar da Abbana su na kallo shi da Mami da ya sauban wata uwar harara ya sauban ya watsamin ni dai ban san mai na yi ma sa ba haka kawai ya ɗauki karan tsana ya ɗoramin saboda na ce ba na son ya Ayan

"Mamana kin dawo "eh Abba na ba shi amsa " "to zonan maza ki zauna miyi kallo" babu mu su na je ku sa da shi na zauna ya Sauban ne ya dubi Abba "wallahi Abba har da ku ku ke ja yarinyar nan ta ke abun da ta ga dama ace yarinya ai ta shagwaɓɓa ta kamar wa ta baby"

"To ban da abun ka Sauban ni a gurina ai yarinya ce to wai ma da zaka bi ka takurawa Mamana nawa ta ke ko dan kun ga ta girma da wuri" ni dai ina jinsu faka idon Abbana na yi na wa ya Sauban gwalo "kagani ko Abba gwalo fa ta ke min " "ban so sharri Sauban ya zaayi ta maka gwalo ni na san halin Mamana ba zata maka gwalo ba Ko Mamana" ɗaga kai na yi Alamar "eh Abba ni ya za'a yi na yiwa ya Sauban gwalo kawai dai ya tsaneni shiyasa idan fa ba kanan har hantara ta ya ke" na fashe da kuka kamar da gaske faɗa Abba ya dinga ma sa kwafa kawai ya Sauban ya yi ya ta shi da ga falon,

Mami ce ta yi magana " A'a Alh ya kamata fa ka dai na biye yarinya nan yanzu ka ga kasa yaro ya ta shi kuma bayan ni ina ganin duk abun da ta ke masa " " ban da abunki Maman Sauban ya za'a yi Mamana ta ma sa gwalo ke dai kawai ki ce kin goyi bayan ɗanki" "to ai shikenan Allah ya kyauta" Ameen Abbana ya ce mu ka cigaba da kallon mu muna yi mu na hira abun mu gwanin ban sha'awa,


Wacece A'ISHA LABIBA 🌺,

Family ɗin Alh mubarak family ma su ban sha'awa dan su na da haɗin kai sosai ga tarin dukiya uwa uba kuma ilimi wan da ya ka san ce jigon rayuwa, tun san da kakan mu ya ke da rai ya gina wanni ƙaton gida wan da duk ya'yan sa idan su ka yi aure za su zauna acikin sa, kakan mu ya na da ya'ya Uku a Duniya Alh Muhammad shine babba wan da mu ke kira da daddy sai kuma Alh Ahmad shine Abbana sai ɗan Autan su sadeeq wan da ake kira da Jabi Uncle Jabi shi ba anan ya ke da zama ba amma ya kan kawo mana ziyara shida matar shi Aunty Ruƙayya shekarasu uku da aure kuma har yau Allah bai ba su haihuwa ba ,

Sai Abbana ya na da yara biyu ni da ya sauban sai da ya sauban ya shekara biyar duniya sannan Allah ya ba su ni,

Daddy ya na da yara biyu ya Ayan wan da ya ci sunan kaka mu shine a ke kiran sa da Ayan sai ya Farhan wan da ya ke Sa'an ya sauban sai kuma Yusra ita kuma ta ba bi wata biyu aduniya mun ta so cikin ga ta da soyayya duk da soyayya da iyayen mu su ke nu na ma na haka bai sa sunƙi ba mu tarbiya ba tin ina ƙarama ya Ayan shine ya ke raino na ka sance war Mamina ita ce uwa a gare sa ko bacci ya Ayan
zai yi sai tare da ni haka ni ma ba na yadda na yi bacci in ba da shi ba a da san da ya ke karatu a UK tare mu ka tafi saboda ya ce ba zai iya tafiya ya barni ba haka ni ma tin san da zai tafi na fara rashin lafiya dole aka shirya ni mu ka tafi tare cen na gama pramary school na yi secondary School ɗina ina J s 2 ya Ayan ya gama karatun sa muka dawo Nigeria,

Mu ka cigaba da rayuwar mu haka kurum wata rana na wayi gari na ji na tsani ya Ayan ba na son ganinsa kuma ni ban son dalili ba kawai abun da na sani shine na tsane sa

Wannan shine ta ƙaitacen labarina,




Sai mu tara a wani page ɗin dan mu cigaba da jin yadda zata kaya,

Karku manta Autar jajirtattu 💪 ce

Sannan ma su tambayar littafin rayuwar mafarkina har yanzu ƙofa a buɗe ta ke ga wan da su ka yi shirin biya su min magana dan yanzu ma a ka fara wasan yanzu ne za mu shiga cikin tsagwaran labari a da mun ɗan taɓane

Wan da su ka shirya biya sumin magana ta wanan Number

09165855674

https://chat.whatsapp.com/F1uZsFAFSUI6dIRXSQ1niH

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F1uZsFAFSUI6dIRXSQ1niHhttps://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

A'ISHA LABIBA 🌺

LOVE AND REMONTIC


SHORT STORY


BY MEERAT UMAR 💋


AUTAR JAJIRTATTU 💪 CE
___________________________________

3,


Yau ne ranar da su Uncle Jabi za su dawo duk mu na ta aiki ka san cewar yau ba ma da school Mom ce ta shigo " a'a wai har yanzu ba ku ga ma ba? ni fa daɗina da ku ba kwa abu da wuri" turo baki na yi na ce haba Momy tin ɗazu fa mu ke ta aikin nan kuma ma ai ya kamata ace anzo an karɓe mu " kaji ni da yara to idan ku ka yi aure wazai karɓe ku" " yauwa Momy faɗa mu su dai" naji murna ya Ayan ya na magana ta baya turo ba ki na yi "to kai kuma ina ruwan ka" na faɗa a hasale koma mai ya sa ya zo in da mu ke kawai mutu ya yi ta takurawa mutane ina juyowa na ga Momy ta fita Yusra kuma ta na store jawoni ya yi na ku san faɗawa jikin sa "ma ki ke faɗa? " wai mai ya sa ki ka tsanani LABIBA ni dai na san LABIBA 🌺 ta ba haka ta ke ba why LABIBA ko dai wanni abun na damunki?" ni babu abun da ke damuna kawai dai na tsani.... Kafin na ƙarasa maganar na ga ya Ayan ya tafi baya ji na yi ya faɗi ya na dafe ƙirjin sa lokaci ɗaya kuma Numfashinsa ya ɗauke ihu Yusra ta rusa dan duk abun da ya faru a gaban idon ta ya faru.

Ni ma tsugunawa na yi ina jijiga shi Mamy ce ta shigo cikin wajan " a'a lafiya Yusra kike.. ba ta ƙarasa maganar ba ganin ya Ayan a ƙasa babu lamar rai a jikin sa Mamy fita ta yi da sauri ita da ya Sauban su ka dawo gun ɗaukar sa ya yi ya ni fi wajan aje motoci idi na ganin su ya buɗe ma sa mota Mamy ce ta shiga ya ja motar aguje ya bar gidan

Likitoci sun yi iya bakin ƙoƙarin su dan shawo kansa to Alhmdllh an samu damar dai-dai ta Numfashinsa amma har yanzu babu lamar far faɗowa ta nauwar kawai su ke ganin ya na yi bugun Numfashisa,

Likita ne ya kirawo Mamy cikin office ɗinsa a nan ya ke ta batar ma ta da ɗan su ya na fama da ciwo zuciya kuma ahakin da ake ciki yanzu ya na mataki ƙarshe na ciwo mudum ba a bashi abun da zuciyar sa ta ke so ba to fa za su iya rasa shi.
Godiya ta masa ta fita ta na mai saka abubuwa da yawa a ranta.

Agida kuma hankali kowa ya ta shi ni kaina kuka na ke musamman idan na tina ni ce sanadin ciwo ya Ayan gashi Yusra taƙimin magana Allah sarki Momy duk da ta san ni ce sanadin ciwo ɗanta amma haka bai sa taƙi rarashina ba.

Su Uncle Jabi su na iso wa yaji abun da ke faruwa dan Yusra ta faɗa ma sa komai ina kwance a ɗaki ina kukan danasani naji an bugo ƙofar Abbana na gani idon sa ya yi jajir ni foni ya yi da sauri na ja baya dan ban taɓa ganin shi cikin wannan ya na yin ba. Ke dan ubanki wato sakarci na ki harya kai ki faɗawa ɗan uwanki munan kalamai ko to wallahi yau sai na lahira ya fiki jin daɗi da sauri Uncle Jabi ya sha gabansa haba yaya idan rai ya ɓaci hankali shike dawo da shi kuma idan ka dubeta ai zaka ga alamar da na sani a fuskarta

Juyawa ya yi ya kalleni ki samani a part ɗina LABIBA uncle Jabi ya faɗa ya na jan hannun Abbana sauke Ajiyar zuciya na yi ina tinani ya Allah ka kawomin mafita,

Yau dai LABIBA ta ɓatawa Abba rai kowane wukunci za su ɗauka a kanta oho, kudai ku biyoni

Sannan da Comment ɗin kune ka ɗai zan ga yadda kuka karɓi labarin karku manta

Labarin A'ISHA LABIBA 🌺 SHORT STORY ne

AUTAR JAJIRTATTU 💪 CE


https://chat.whatsapp.com/F1uZsFAFSUI6dIRXSQ1niH

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F1uZsFAFSUI6dIRXSQ1niHhttps://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

A'ISHA LABIBA 🌺

LOVE AND REMONTIC

SHORT STORY 📚✍️

BY MEERAT UMAR 💋
___________________________________

BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM
____________________________________
page,4 and 5,

Gasky ba zai yuwu na din ga zama ina muku typing ba amma ku ku kasa ba da lokaci kaɗan kumin Comment dan naji daɗi,

Idan da Comment da typing,
____________________________________


Ban ta shi daga in da na ke ba sai ku san magrib wanka na yi nai sallah na nufi part ɗin su Uncle Jabi da salama na shiga samun sa na yi zaune ya na waya sai da ya gama sannan na gaida shi "yanzu baby abin da ki ka yi kin kyauta kenan haba ban taɓa tinani zaki aikata haka ba ka" " yi haƙuri Uncle Wallahi da na san haka za ta faru da ban faɗa ma sa maganar da na faɗa ba " na faɗa ina kuka Aunty Ruƙayya ce ta jawoni jikinta ta na rarashina " ishiru baby Uncle kin ji ni na san ba zaki faɗawa ya'yan ki maganar da za ta cutar da shiba ki na sane in Sha Allah komai zaizo da sauƙi kin ji " ɗaga kai na yi ina kuka "to yanzu ki dai na kuka" ta faɗa ta na share min hawaye Uncle Jabi ya ce "sai ki bari gobe idan ya'ya ya wuce ki je ki ba sa haƙuri kuma duk hukuncin da su ka yanke a kanki ki karɓa hannu bi biyu saboda ni na san ba za su taɓa cutar da ke ba" " to Uncle in Sha Allah zan yi ƙokarin haka" Allah ya yi miki albarka" Ameen na amsa Aunty Ruƙayya ce ta kama hannuna muka shiga ciki


Washegari tun safe su ka shirya dan tafiya asibiti na so na bi su amma Uncle Jabi ya hanani babu yan da zan yi dole na zauna acikin gida da gani sai Ma su gadi Fatima na kirawo a waya ina kuka na faɗa mata abin da ke faruwa hankalita ba karamin ta shi ya yi ba ta ce min gatanan zuwa gidan naji daɗin zuwan ta sosai duk da ko da ta zo faɗa ta dunga min kamar wadda zata dakeni "wallahi LABIBA ko kaɗan ban zaci haukan na ki ya kai haka ba kirasa wan da zaki cutar sai wan da ya ke sonki ya baki gata da ko ƙanwarsa da su ke uwa ɗaya uba ɗaya bai bawa kin bani mamaki LABIBA kuma ki sani ba na goyan ba yanki akan wannan lamari sakarya kawai wai shin LABIBA ina iliminki ya tafi"? "haba Fatima na kiraki ne dan na samu sauƙi amma kema kina tamin faɗa ni fa ban yi haka da gangan ba kuma wallahi Fatima ni ma ban son mai ya saba na tsani ya Ayan har yanzu da na ke miki maganar na na tsanesa kuma ina kuka ne kawai saboda sanadina ya kamu da ciwo da kuma halin da su Momy su ka shiga "

Su na cikin haka haka Mamy ta dawo ita da ya Sauban daya ke su acen su ka kwana shiyasa su ka dawo dan su huta ko kallona ba ta yi ba ta wuce ciki bayan sun gaisa da Fatima "ya Sauban ya jikin ya Ayan ɗin?" na tambaye sa " au tambaya ta ma kike Okay ki na so ki ji ya mutu kamar yadda ki ka so ko to ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment