Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

_Typing📲_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_Shafi na ɗaya_



*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._


........“Ango! Ango!! Ango!”. Itace kalma mafi rinjaye da tafi fita a bakunan taron matasan dake cike da ƙofar gidan. Yayinda wanda suketa faman kira da angon bakinsa ya kasa rufuwa dan farin cikin da yake a ciki a wannan rana data kasance ta aurensa da masoyiyarsa mafarkinsa. Magana da ɗaya daga cikin abokansa ya gwargwaɗa masa a kunne ta saka shi jan hannunsa suka koma gefe. Cikin ɗan nuna yanayin damuwa da hasala ya ce, “MB ya akai haka kuma? Nifa bana son matsala wlhy, duk abinda zan ɓatama Love rai bana son shi musamman a wannan ranar ma data kasance mana ta daban.....”
      “Na sani kwantar da hankalinka, kaima kasan dai bazan bari wani abinda zai ɓata farin cikinka faruwa ba JJ. Na faɗa maka ne kawai dan kar kaga an samu canji, dan yanzu haka ma nariga na daidaita matsalar, wajen da aka samu yanzu ɗin ma yafi wancan komai...”
     “Amma karka manta wajen farkon muka saka a invitation card”.
    “Hakan bazai zama matsala ba shima, dan kusa-da-kusa suke, dabarar da zamuyi zamu ajiye su Nure a ƙofar wancan hall ɗin duk wanda yazo sai su turosa inda aka canja ɗin. Yanzu sai ka sanarma amarya kawai, ko hakan baiyi ba?”.
          “A yayi, kunyi ƙoƙari, ALLAH ya bar zumunci bari na sanar mata”.


     *_DINNER HALL_*

       Matuƙar ƙyau da ƙayatuwa wajen yayi tamkar dama tun farko nan suka shirya yin shagalin. Kalar decoretions ɗin wajen kalar ankon ƴammatan amarya da suka sha ƙyau har suka gaji, haka suma abokan ango shar da su. Shigowar ango da amarya ta shafe duk wani ƙyawun kowa a wajen, dan adonsu na musamman ne. Atake hasken flash ya shiga tashi tako ina, tsakanin wayoyi da camaras, a gefe mc na faman kwarzantasu, yayinda dj ya saki wani cool music mai ratsa zuciya. Ta ko'ina dai taro ya cika taro kam sai masha ALLAH, abokan ango da ƙawayen amarya nata taka rawar gani irin na bajinta tare da dangi takowace ɓangare. A yanda aka tsara komai zaka iya saka masu bikin a layin masu hannu da shuni, sai dai sam ba haka bane ba, ana dai tsaka tsaki, wato babu tsiya babu hamshaƙin arziƙi. Sai dai akwai rufin asirin ALLAH ta kowanne ɓangarorin guda biyu. Anyi taro an tashi lafiya kusan ƙarfe ɗayan dare, ango na son maida amaryarsa gida da kansa yayarta tace karya damu yaje gida ya huta zasu wuce da ita. Babu yanda ya iya dole ya haƙura suka dunguma shi da abokansa zuwa hotel da suka kama. Amarya da danginta suma suka wuce nasu gida dan sai gobe in sha ALLAH za'a miƙata gidan mijinta.....

           *_WASHE GARI_*

   A kaf ƴan rakkiyar amarya babu wanda baiyi santin gidan da aka kawota ba. Dan kuwa dai gida ya cika ya tunbatsa komai zam. Tabbas angon yayi ƙoƙari sai kuma fatan a zauna lafiya. Bayan kammala ƴan kai da kawo na al'ada da rabe-raben kayan gara kowa ya kama gabansa aka bar amarya da ƙawayenta. Sune suka sake gyare mata gida ana faman raha da wasa da dariya komai ya koma kan saitinsa. Sai dai amarya bata da wani kuzari tattare da ita, ba komai ya jawo hakan ba sai ƴar fargabar da aka san duk wata amarya kamila da ita a irin wannan ranar, dama ita gata bamai yawan hayaniya bace, ko ƙawayen ma ba wasu ne daban ba, daga ƴan uwa sai maƙwafta da aka tashi tare. Bayan idar da sallar magrib kowacce ta shiga sake gyara kwalliyarta sukai zaman jiran abokan ango. Ƴan halak ɗin kam basu taushe hannu ba, dan idar da sallar isha kaɗan suka iso gidan. Amarya dai na lulluɓe, yayinda ango yay tsallen turare ɗan goma zuwa inda take ya zauna kusa da abarsa kamar zai rungume, itako tana ta faman matse jiki waje guda abinka da farin shiga ga kunyar baƙunta. Suko abokan ango nata faman masa shaƙiyanci da ido yana musu daƙƙuwa ta ƙasan riga da sakin murmushi. A haka dai akai ƴan abubuwan daya dace tsakanin abokan ango da na amarya, zuwa tara da rabi ango da yaga basu da niyyar basu filin ya murje idanu ya korasu waje. Sun fito suna dariya, yayinda MB babban amininsa ya sinna masa wasu ƙwayoyin magani tare da miƙa masa gorar ruwan hannunsa yana faman ƙyafta masa idanu da masa magana a hankali. “Adai yi tuƙi a hankali, dan wannan motar ƙirar larabawa ce, idan bakai wasa ba amaimakon horn ƙira'ar Alkur'ani zakaji”. A tare suka kwashe da dariya tare da cafkewa bayan ya afa maganin batare da tambayar na miye ba ya kora da ruwa. Ango JJ ya ce, “Shege abokina, kune malaman duniya, dan shugaban mai jan ƙyalli ma a ƙarƙashin koyarwarku yake baza komarsa”. Dariyar suka sake kwashewa a tare, MB yay gaba yana saɓa babbar riga da faɗin, “Idan da matsala kai dai kai kirana da wuri na turo makanike dan ka samu damar fita shan iskar yammaci, na barka lafiya a tuna da maƙota kar'a ishesu da...” bai ƙasa ba ya wani kashe masa ido ɗaya yana ficewa a gate ɗin. Shi dai ango JJ rufe gate ɗin yay yana cigaba da dariyarsa. Kafin ya juya cikin gidan ransa fes yau ranar baje koli ta duniya a cikin rayuwar sa...
     Shuuu!! Aka gitta kamar ta gefensa a dai-dai yana kai hannunsa ga handle ɗin ƙofar, kamar zai share da tunanin iskar sanyi data fara kaɗawa ce sai kuma dai ya ji an sake gitta masa yana ƙoƙarin tura ƙofar. Wawwaigawa yay damansa da haggu sai dai kuma babu kowa, cikin nuna halin ko'in kula ya ɗage kafaɗu da taɓe baki ya ƙarasa shigewa a falon.
     “Amarya kin sha ƙamshi, amarsu baƙya laifi koda kin kashe ɗan masu gida!”. Ya jero kalaman kirarin tamkar shine ya fara ƙirƙirarsu saboda tsaruwarsu a bakinsa kai kace waƙace a bakin shata ko barmani coge. Bai damu da jin ba'a amsa mar ba, ya murzawa ƙofar key harda gyara labulaye da ƙyau. Turus yaja ya tsaya ƙirjinsa na bada wani irin turururumm tamkar sautin gangar Ado gwanja a tsakkiyar filin biki. Wayam falon babu komai, duk kayan alatun nan da aka ƙawata falon da shi  tamkar wata almara babu su babu alamar su. (Kai ina, wannan almara ce JJ dawo hankalinka) wata zuciya ta ayyana masa. Yawu ya haɗiye da ƙyar, tare da sakin murmushi mai kama da kuka shi adole yana son dawo da hankalinsa jikinsa. Bakinsa na rawa da karkarwa ya furta, “L-o-v-e!” a rarrabe yana runtse idanunsa da ƙarfi. Ba'a amsa mar ba yanzun ma dai, dan haka ya sake ƙarfin halin buɗe ido ɗaya da ƙyar, da sauri ya sake buɗe ɗayan ma ya shiga waige-waige yana haɗiyar yawu da sauri-da-sauri. Yanzu kam falon komai ya dawo kamar yanda yake a da, sai dai kuma kalar kayan ta canja. (JJ! Farin ciki fa ke neman juyar maka da brain, ka daidaita kanka mana). Kansa ya shiga gyaɗawa kamar tsohon ƙadangare cike da son gamsar da kansa akan dole, sai kuma kamar wanda aka ingiza ya nufi bedroom da sassarfa, yana tafiya yana waigen falon. Har ɗan datse hannunsa yake wajen ƙoƙarin rufe ƙofar bedroom ɗin da danna mata key saboda yanda jikinsa ke rawa. Cikin dauriyar azabar dake ratsa masa hannun da ya datsa ya jingina da ƙofar yana sauke nannauyar ajiyar zuciya irin ta na sha da ƙyar ɗin nan. Yakai minti ɗaya a haka kafin ya dai-daita kansa da ƙyar yana sauke ajiyar numfashi a jajjere. Kasancewar sai ka ratsa ɗan lungu daga jikin ƙofar kafin ƙarasawa tsakkiyar bedroom ɗin sosai saboda bathroom dake a wajen ya bashi damar share gumin ɗaya tsatstsafo masa da dai-daita yanayinsa da ƙyar sannan ya cigaba da tafiya a takun da bai gaza huɗu zuwa biyar ba. Bedroom ɗin ƙato ne, ga kayan gado yaji masu ƙyau dan iyayen amarya sun taka rawar gani suma. Ƙoƙarin hana kansa kallon komai yake saboda abinda ya baro baya, dan haka ya nufi gadon kansa tsaye dan yasan dai anan zaiga amaryar tasa sarkin kunya da nutsuwa. Sai da ya kai zaune yana faɗin, “Afuwan Love na barki ke ɗaya, na sallami waɗan nan ƴan matsalar ne, kin san in su MB na waje bakin mutum baya hutaw......”
     Ya kasa ƙarasawa sakamakon abinda idonsa ya gane masa. Wata irin murɗaɗɗiyar macijiya ce baƙa ƙirin an mata wata kwalliya da kalar jaja-jaja mai haske kamar ƙwan lantarki. Ba'a labaran tatsuniyoyi da wasanni ba, ko'a film ɗin ƴan India da suka sabayin na macizai bai taɓa cin karo da irin wannan maciji mai girma ba. Rawa jikinsa ya farayi kamar mazari, har takai yana zamewa a saman gadon zuwa ƙasa batare daya farga ba. Gab ya kusa kaiwa ƙasa daɓar yaji an riƙoshi...
       “D lafiya kuwa? Miya faru kake irin wannan kakkarwar har kana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa?”.
   Nutsatstsiyar muryar amaryarsa ta ratsa masa kunne, yayinda lallausan tafin hannunta da tunda ya riƙesa a wajen dinner jiya abin ya kasa barin ransa ke riƙe da shi a yanzu ma. Kusan a tare ita da shi suka zube a ƙasan, dan ya riga ya taho gaba ɗayansa, sannan ya fita nauyi. Faɗowarta jikinsa ya sakashi sakin wani irin ihu tamkar wanda aka farkar a barci da ruwa mai sanyi. Yay wani irin mamuƙeta illahirin jikinsa na rawa. A hankali ta saki ƙara da faɗin, “Wayyo D zaka karya min awazzu.”
     Kafin yau idan yaji wannan zazzaƙar muryar tata ji yake yafi kowa sa'a a duniya. Amma a yau maimakon hakan wani irin rawa da kakkarwa jikinsa keyi, ga zufa ta wanke masa illahirin jikinsa tamkar wanda yay wanka. Zumut ya miƙe tamkar wanda aka zabura ya shiga waige-waige, sam babu komai a gadon, sai ma gyaran da yasha na musamman ga filos da aka jera a kansa tamkar an zana a takarda. Sake juyowa yay da sauri yana kallonta da nuna gadon da yatsa, sai dai bakinsa ya kasa furta komai, sai ma rawa da pink lips ɗinsa sukeyi. Cikin rashin fahimta take kallon gadon itama, sai kuma ta dubesa da alamar tashin hankali a tattare da ita. “D! dan ALLAH miya faru, wlhy kana sake rikitani nikam. Jibafa yanda kake zufa. Kana nuna min gado kuma ni banga komai ba a wajen.”
        (JJ ka nutsu, karfa ka ɓata wannan daren mai muhimmanci a gareka mana) wani ɓangare na zuciyarsa ya faɗa cikin tsawatarwa. Kansa ya shiga jinjinawa tamkar zuciyar tasa na kallonsa ne, ya haɗiye busashen yawu tare da sakin murmushin yaƙe ga amaryar tasa. “B..ba komai Love, dama fa ina gwada ki ne kawai naga amaryar tawa jaruma ce ko matsoraciya.” ya ƙare maganar yana damƙo hannunta cikin nasa da ƙyau. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, sai kuma ta duƙar da kanta tana ƙoƙarin janye jikinta daga nashi dan kunya. Yanayin nata ya sake sakashi dawowa hayyacinsa da tuna masa shi ɗin fa ango ne. Ƙoƙarin haɗiye komai yake yi, duk da hakan abune mai wahalar gaske a garesa, amma dai zai gwada yin wannan jarumtar ya gani. Ayatulkursiyyu ya karanta a zuciyarsa yana tattofawa a kaikaice. Sai da ya tabbatar ya ɗaure ɗakin ɗamm acewarsa, kafin ya ƙara ɗan samun nutsuwar sake maida hankalinsa ga amaryar tasa da kanta dai ke a sunkuye.
      A karo na farko ya jawota jikinsa ya rungume tsam yana sauke tagwayen ajiyar numfashi, yayinda ita kuma ta shiga masa rawar jiki irin na farin shiga, sai dai bata hanashi ba ko yunƙurin janye jikinta har kusan mintuna biyu daya saketa dan kansa. “Yau dai ga ni ga Love a gida ɗaya, ɗaki ɗaya a matsayin ma'aurata”. Ya faɗa yana sake riƙo hannunta duk biyu cikin nasa da ƙyau tare da gyara zamansa ya fiskanceta. Murmushi ta saki tana ƙara ƙasa da kanta tare da jan mayafinta ta rufe fuskarta. Shima sai ya saki wata ƴar siririyar dariya cike da nishaɗi, hannu ya kai ya yaye mayafin yana mai ɗago haɓarta ta yanda zaiga fuskanta da ƙyau.. Wata muguwar zabura yayi baya yana mai waro duka idanunsa waje jikinsa na karkarwa batare da ya ma sani ba ya furta, “Anoosha!!”.
       Cike da salo tai masa luuu da idanu tare da sakin sassanyan murmushin da a fuska ɗaya ya sanshi kuma ya taɓa ganinsa, bai kuma sake ganinsa ba. Tsabar kiɗimewa da shiga ruɗani har yana bugewa da gado wajen zabura da ƙoƙarin tattara babbar rigar jikinsa alamar zai kwasa a guje yaji caraf an riƙesa.......✍️


       *_😂😂Tofa babbar magana, wai ango JJ mijin amaryar da ko sunanta bamu sani ba mi shika hwaruwa ne hakanga kuma? Anya kuwa ba....🥱Bara dai na iya bakina abinga walle bana hiɗi bane🤣🤣._*

   _Alhamdullahi inata alƙawarin gareku na yin free book ALLAH bai ƙaddara hakan ba sai yanzu. To Amin afuwa gani zan cika alkawarin in sha ALLAH. Ina fatan wannan littafi zai ƙawatar da ku tako wace fiska, cakwakiya, nishaɗi, ƙalubale, ƙaddara, son zuciya, kai abubuwane da yawa ya wawuso tako wace fuska, zakuma ku fahimci saƙon da yake son isarwa, dan salon na musamman ne, idan nace na musamman ina nufin na musamman a gaba ɗaya musamman ɗin😉👌.

     *Kumuje zuwa gidan ango muji yaya zai ƙare da wannan daren farko nasa, dan naga na musamman ne fa 🚴🚴🚴😆😆🤫🤫.*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_Shafi na biyu_


........“Ai babu gurin zuwa, saboda da hannunka ka rufe duka ƙofofin guduwar Mr JJ ango mijin amarya Alimah”. Muryar da baya jin zai manta a rayuwarsa ta ratsa kunnuwansa. Dauriyarsa ta ƙare, hakama ƙarfin halinsa ya kai ƙarshe. A take jikinsa ya fara rawa kar-kar. Gashi an riƙesa irin riƙon da ko numfashin kirki ya gagara yi. Jin saukar numfashin mutum a fuskarsa ta saka shi buɗe idanunsa da sauri. A matuƙar razane ya fasa gigitacciyar ƙarar data ɗauke numfashinsa gaba ɗaya sai gashi ƙasa wanwar a sume.....

A firgice ta buɗe idanunta itama tamkar wadda aka farkar da ga nannauyan barci. Waige-waige ta fara ƙirjinta na wani irin luguden daka. To ita yaushe ma barci ya ɗauketa ne, ba yanzu babu jimawa suka shigo ɗakin nan tare da angonta JJ ba. Dan fitarsa babu daɗewa rakkiyar abokansa ko cikakken minti biyu baiyi ba ya dawo, batama jin yabar jikin ƙofar falon. Cike da zumuɗi da aka san duk wani ango da shi ya koma ya zauna inda ya tashi a kusa da ita. Batare da yayi magana ba kawai ya jawota jikinsa ya rungume yana shinshinar wuyanta. Kunya ta sakata shiga wani yanayi, a take jikinta ya fara mazari ta shiga noƙewa. Dariya ya sakar mata cikin kunne da faɗin, “Ai yau dai kunya ta ƙare Love, miya rage kin zama matar JJ, JJ ya zama mijinki. Please ki ajiye wannan kunyar da safe ƙya maidata dan kin san yau ɗin ta musamman ce fa”.
Bata iya tace da shi komai ba, dan a matsanancin tsorace take ga kuma kunya. Sai dai hakan baisa ta hanashi yin yanda yaso da ita ba. Bayan ya gama shinshinar ta ne da rungumeta ya ɗakkota cak zuwa wannan ɗakin yana faɗin, “Yanzu dai muje muyi sallah kafin komai ko. Dan nasan matar tawa ustaziya ce”.
A karo na farko ta sakar masa murmushi, tare da tura kanta a jikinsa dan kunya takeji matuƙa kamar me. Dan tunda take a rayuwarta bata jin wani ya taɓa riƙe mata hannu, sai a jiya wajen dinner da JJ ya aikata hakan gareta. To ita dai tasan sun shigo ɗaki, daga haka kuma bata san miya faruba sai ƙarar ihun nan da bata san daga ina ya fito ba da ya farkar da ita, a yanda kuma taga kanta alamu sun nuna barci tayi. Gadon ta sakko da sauri, sai kuma tai tsamm ta dakata saboda jin motsin ruwa a toilet ɗin ɗakin, hakan na nufin JJ na ciki kenan. Numfashi ta ɗan sauke a hankali, tare da komawa ta zauna tana gyara mayafinta, zuciyarta na tabbatar mata wanka ya shiga kenan, ita kuma barci ya ɗauke ta, ihun da taji kuma maybe a maƙwafta ne. To amma abin mamakin anan taya tayi barcin? Haka cikin ƙanƙanin lokaci? Rashin amsa ya sakata ɗan sauke numfashi kawai.. dai-dai nan JJ ya fito a toilet ɗin babu alamar wanka yayi sai dai ko alwala. Kanta ta duƙar ganin ita yake kallo, shi kuma ya saki murmushin da har ta iya jiyo sautinsa da ga inda take tare da faɗin, “Naga a takure kike, jeki falo ki jirani”.
Kamar mai jiran jin hakan ta mike zumbur, har harɗewa take wajen fita tana mai sauke ajiyar zuciya, sai dai mamaki fal kanta dan sai take jin kamar wani banbarakwai hakan nan....

(Bake kaɗai ba amarya, ni kaina fa man kai na ya tsiyaye. Dan na gagara fahimtar komai, shin JJ ɗin ne ba mutum ba ko ke kanki? Masu karatu ko akwai mai amsa min?🥱😆🚴).

★★.....

A ɓangaren JJ ango kam zubur ya miƙa tare da sauke nannauyan numfashi alamar farfaɗowa da ga sumar da ya tafi. Gaba ɗaya jikinsa babu wani ƙarfi a yanzu, dan tun bayan numfashin da ya kawo cikin zabura sai kuma ya koma laƙwas kwance yana maida idanunsa a hankali ya sake lumshewa. Falaƙi da Naasi ya fara karantawa a zuciyarsa yana ɗan buɗe ido kaɗan, shiru babu motsin komai, sai wata iska mai daɗi dake ƙaɗawa. Kamar wanda aka bama ƙarfi ya miƙe zaune dingangan, waige-waige ya shigayi idanunsa a buɗe sosai mamaki fal kansa na ganinsa a baranda kwance wanwar, tabbas a waje yake, ya kuma kasa iya tuna komai da ya faru. Babu alamar akwai wani abu da zuciyarsa ke ayyana masa kuma, sai ma wata nutsuwa da yake ji ga zuciyarsa na tabbatar masa faɗuwa yay kenan bayan yama abokansa rakkiya, dan abinda ya fara tunawa kenan kafin gittawar da akai masa lokacin da yake ɗaura hannunsa saman handle ɗin ƙofa, sai kuma abinda ya faru na shigarsa falo dama ɗaki, hakan na nufin komai daya faru a mafarki ne ba zahiri ba dai kenan. A take ya gamsu da hakan, dan kamar an masa wanki ƙwaƙwalwa ne ma ya kasa tuna komai a yanda ya kamata balle yayi tunani irin na mutane masu hankali. Sai ma amaryarsa da ta zo masa a zuciya. Miƙewa yay tamkar wanda aka tsikara, ya gyara zaman babbar rigarsa da hula sannan ya ɗaura hannunsa a handle ɗin ƙofar ya murza a hankali yana sakin wani murmushin farin ciki.
A inda ya barta nan ya sameta, tana lulluɓe dai har yanzu cikin mayafinta. Sai ƙamshinta daya gama gauraye falon mai shegen daɗi. Taku ya cigaba dayi cikin shauƙi da bajinta zuwa gareta. Kusa da ita daf ya tsaya batare daya zauna ba ya zuba mata shu'uman idanunsa da suka sake ƙanƙancewa. Tsahon mintuna biyu kafin ya kai durƙushe ƙasa tamkar ɗa a gaban uwarsa. Hannu biyu ya saka ya ɗaga mayafinta ƙyaƙyƙyawar fuskarta mai alamun rashin yawan hayaniya ta bayyana. Ga kwarjini irin wanda aka san amarya da shi tattare da ita. A hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da kamo hannayenta da take matsewa cikin juna ya riƙe, sun sha jan lalle da baƙi sai sheƙi suke. Ɗagosu yay zuwa bakinsa ya sumbata tsakkiyarsu ɗaya bayan ɗaya. Sosai ta sake ƙanƙame jikinta da sinne kanta na kunya...
“Babu gaisuwa Love?”.
Ya faɗa cikin wata irin siririyar murya. Kanta ta sake sinnewa cikin tata muryar da ke rawa ta ce, “Kayi haƙuri ina yini”.
“Ai baƙya laifi amarya koda kin kashe JJ ne ma. Dama wannan golden voice ɗin nake son ji ne. Ina miki Barka da zuwa gidanki, fadarki. Alƙawarin ALLAH ya cika yau gani ga Love ɗina a gida ɗaya matsayin ma'aurata. Babu abinda zance da UBANGIJI sai godiya. Kisa a ranki har abada bake ba kishiya, ko'a aljanna ke kaɗai ce”.
Murmushi ta saki a karo na farko, sai dai bawai ta amshi kalaman nashi bane da muhimmancin riƙewa, dan duk da ƙananun shekarunta kuma ita bamai yawan hayaniya bace da taron ƙawaye tanada iliminta. Tasha jin yayunsu na faɗin yarda da irin waɗan nan kalaman a bakin namiji yaudarar kaine kawai..
Shiko tuni murmushin nata ya kashesa, dan a tunaninsa kalamansa sunyi irin tasirin da yake buƙata. Tashi yay daga ƙasan da yake ya koma saman kujera kusa da ita, gaba ɗayanta ya jawo ta koma saman cinyarsa ya rungumeta tsam-tsam yana sauke numfashi da sauri-sauri. Dan maganin da MB ya basa ya fara aiki. Itako gaba ɗaya ta gama rikicewa da kunya da tsoro, sai dai batai yunƙurin jaye jikinta ba kamar ɗazun. Tsahon mintuna uku suna a haka kafin ya ɗago fuskarta, kallonta yake

Please Login or Register in order to submit comment