Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba”.
  Dariya suka kwashe da shi a tare har ɗakin na wani irin jijjiga suka kuma tafa. Tsuuuu kakejin JJ na sakin gudawa a wandonsa. Fitsari kam dama tuni shi ya fara yin gaba. Kallon wandon nasa sukai a tare suka sake kwashewa da dariya. Sai da sukai mai isarsu Anoosh ta kalli Alimah. “Amarya! Ya kamata ki kawoma angonki abinci yunwa yake ji”.
      “Hakane fa”.
  Alimah ta faɗa tana juyawa ga kulolin abincin. Daga inda take ta miƙa hannunta sai gashi yayi dogo ziriri har inda kayan abincin suke. Yatsanta manuniya ta dangwala a samansu tayo baya da hannunta sai gasu sun biyota ta dire a gaban JJ da ya sake diriricewa. Ƙular data buɗe a ɗazun yaga shinkafa a yanzu data buɗe sai ga kunamu baƙaƙe kirin na motsi da ransu cike da kular. Kula ta biyu mai ɗauke da miya kam wani irin abune kore shar baima san yanda zai fassarashi ba. Kofi mai ɗauke da zoɓo kuwa ya koma jini. A yanzu Anoosh ce ta zuba kunamun a plate, tare da koren abunnan, Alimah kuma tasa jini a kofi. Jikinsa suka sake matsowa gab suna wani irin mugun murmushi.
        “Haaah!”.
   Cewar Anoosh tana ɗebo kunamun nan da wani irin zabgegen cokali zuwa bakin JJ. Kansa ya shiga jujjuyawa hawaye na zubo masa. Tsawa mai firgitarwa Alimah ta daka masa, tuni ya wangale bakin yana fashewa da kuka. Anoosh ta zuba masa kunamun a bakinsa. Cikin sauri ya fara taunawa yana wani kalar ɓarkewa da kukan azaba dan suma kunamun kamar jira suke ana zubasu suka fara ɗalla masa harbi a bakin.
        Cike da shaƙiyanci Alimah ta kai hannunta saman kansa tana shafawa. “Yauwa My D maza kaci mana kasha magani, ko kanaso Yaya Mujee ya ɗauka banji maganarsa ba. Haba ɗan sumilmilin mijina ƙyaƙyƙyawa tauraron ƴammata moouuch!!!”. Takai masa wani irin kiss mai shegen ƙara a gefen kumatu tare da ɗaura masa kofin nan mai ɗauke da jini cikin baki. Wata iriyar gigitacciyar ƙara ya saki na azaba. A take ya fara zazzago harshe waje zufa na wanke masa jiki. Sai kawai yay baya zai sume musu..
         
       Saukar ruwa mai masifar sanyi a jikinsa ta sakashi buɗe idanunsa a hankali. Zumbur ya miƙe yana ware idanunsa, sai kuma ya ƙwalla ƙara da faɗin, “Na shiga uku na lalace ni Jazool. Dan ALLAH dan ALLAH azo a taimaka min. Wayyo Baba. Na roƙeku ku faɗa min ku su wanene? Dan ALLAH Alimah ina kika san Anoosh, ta mutu fa ta mutu, kice min ba ita bace wannan, zaku haukatani wlhy na haukace kodai mafarki nake.....”
      “Ai baba bazai taɓa jinka ba anan. Bama shi ba ko maƙwaftan da ke katanga ɗaya da kai bazasu taɓa jinka ba JJ. Ka ɗauka nan ɗin lahirarka ce, kasan kuwa ai duk wanda ya tafi lahira ba'a sake jin labarinsa kuma. Anoosh kuwa ashe baka manta da ita ba hhhhhh” Ƙatuwar magen dake a saman kujera zaune baƙa ƙirin da jajayen idanunta tamkar wuta ta faɗa cikin muryar Alimah.
        Gaba ɗaya ƙarfinsa ya gama ƙare wa. Ga harshensa dake masa wata irin azaba dama bakinsa gaba ɗaya. Mugun ƙanƙame jikinsa dake karkarwa yake waje guda ko kaɗan baya fatan ƙadangarun dake yawo cike da falon su taɓashi. Dan a rayuwa JJ na matuƙar tsoron ƙadangare da mage. Suko sai su taho kamar zasu taɓashi, sai kuma su zagayesa suna kaɗa kai. Gasu wasu irin tuma-tuma babu ko ƙyan kallo.
     “Dan ALLAH ku kasheni kawai na huta. Ku kasheni zaifi min sauƙi da wannan azabar da kuke min”.
         “Hhhh mutuwa kuma. Ai idan ka mutu a yanzu JJ kaci riba kenan. Dan koba komai ka kuɓuta da ga tari-tarin buhunan azaba dake zaman jiranka. Yanzu lokacin ɗaukar darasin rayuwane bana mutuwa ba.” sai tai wani irin kuka na maguna da ya sashi fashewa da kuka. A take ƙadangarun nan suma suka shiga rige-rigen nufar JJ. Ihu yake sosai yana ƙanƙame jikinsa. Suko suka shiga hayesa yuuuuu kamar an kori tururuwa da ga rami. Tsaff suka yanyamesa yanda kiyashi ke yanyame abu mai maiƙo. Wasu har cikin wandonsa da rigarsa. Harsunansu suka shiga zarowa suka fara lasheshi. Yayinda wasu ke ƙoƙarin shiga masa cikin bakin daya wage yana ihu iyakar ƙarfinsa. Miƙewa yay ya shiga zagaye falon yana tsalle-tsalle da ihu da ƙoƙarin kakkaɓesu a jikinsa. Da ƙayar ya iya kama rigarsa ya saɓule ya watsar ƙasa. Wandon ma ya saɓulesa. Cigaba yay da dire-dirensa yana kaɓar dana jikinsa. Sai da ya gama galabaita da jigata ƙarfinsa ya ƙare tasss ya zube ƙasa yaraff sannan magen nan tai kuka ƙadangarun suka ɓace ɓat. Gaba ɗaya jikinsa raɗaɗi yake masa na bala'i. Dan duk sun karceshi da jikinsu da farcinansu. Da ƙyar yake numfashi idanunsa nayin kamar zasu rufe sai dai sun gagara rufuwar. Sai buɗesu yake da rufewa kamar mai shirin suma. Ji yay ana wani kalar siɗeshi tun daga yatsan ƙafarsa. Yunƙurin zabura yayi sai hakan ya gagara. Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa da sukai masa masifar nauyi da ƙyau kan abinda ke suɗesan.  Wata irin mummunar hallita ce da tunda uwarsa ta haifesa bai taɓa gani ba duniya. Jikinta tamkar jan nama, kai irin na jaki, fuskar mutane da ƙahuna irin na shanaye. Tayi wani kalar tsaho mara misali da daɗin kwatamtawa. Idan ta lashesa ta lasa ta lasa saita fesa masa wani irin ruwa a bakinta mai azaba da raɗaɗi aka ciwukan nashi kamar ruwan attaruhu. Azaba ta hana JJ ko kuka. Jikinsa kam ya gagara koda motsawa. Sai hawaye da ke rige-rigen sakko masa a idanunsa. Zuciyarsa na addu'a da zuwan mala'ikan mutuwa ko hakan zai zama sauƙi a gareshi. Ji yake inama uwarsa bata haifeshi a wannan duniyar ba. Inama ya mutu kafin ya girma.....


(JJ na buƙatar malamai a gidansa🚴🚴🚴🤣)

       ★★★★....

      “Dan ALLAH ka taimakeni ka faɗamin yanda akai Husby. Wlhy gaba ɗaya zuciyata ta kasa samun nutsuwa, a tsorace nake, a firgice nake.”
         Sai da ya haɗiye laumar shinkafa da waken da ya zuba a bakinsa sannan ya saki ƴar dariya idonsa a kanta. Cikin nuna alamar rashin damuwa ya ce, “Tsoro kuma Dijoh, minene abin tsoro ko firgita anan. Gida fa nace miki an bamu halak malak da motar hawa ga kuma aiki da za'a dinga biyana albashi mai tsoka. Ai nakega abin muyi farin ciki ne mara misali”.
     “Dafeeq wake garemu a garin nan dazai mana duk wannan? Sannan karka manta iyakar karatunka secondary ne kawai balle muce ko girman takardunka zai baka wannan nasarar. Dafeeq ka faɗa min gaskiya mana!”.
     Yanda ta ƙare maganar kamar a tsawace ya sashi tsayawa cak da ga yunƙurin kai abincin da ya ɗibo bakinsa ya kalleta. Spoon ɗin ya ajiye a hankali yana mai harɗe hannayensa a ƙirji ya cigaba da kallonta. “Khadijah!” ya kirayi sunanta a hankali idanunsa na sake tsatstsareta. Nata idanun ta rissinar ƙasa, sai kuma ta amsa shi a hankali.
          “Ihu fa kike min kamar?”.
       “Kayi haƙuri. Wlhy hankalina ne a tashe. Ina jin tsoro Dafeeq matuƙar tsoro. Karka manta nabar komaina da kowa saboda kai tsahon shekara uku batare da nasan yaya suka kasance ba. Taya kake tunanin bazan shiga ruɗani ba a lokacin da naga sabon abu a wajenka tunda nasan mun bar komai namu ne a yanzu kuma bamu da komai sai kammu.”
     “Humm hakane, na fahimce ki. Sai dai ki sani barin komai da mukayi bashi ke nufin bazamu samu komai ba a gaba. Itafa duniyar nan da kike gani Khadijah tamkar tsanin hawa gini take. A lokacin da kika bar step 1 zaki ci karo da step 2 ne har zuwa ƙarshe kafin ki kai ƙarshen ginin da zai kaiki rufin soron. Naji bamu da wani karatu mai zurfi da zai iya bani aiki mai girma haka, amma kada ki manta mutanen kirki basa ƙarewa, sannan nasan abinda nakeyi fa ni ba shahsha bane.....”
       “Miya kawo zancen shashanci anan kuma. Indai maganata ce nikan ta ɓata maka rai ALLAH ya baka haƙuri. Gida da mota kuma bazan sake magana a kansu ba ALLAH ya sanya alkairi. Ya kuma sa matakin nasararmune su ɗin”.
    A ɗan gatsine ya ce, “Amin”. Da ga haka ya ɗauka spoon ɗin ya cigaba da cin abincinsa fuskarsa a ɗaure, bai kuma sake kallonta ba duk da ita yana jin idanunta a kansa alamar shi take kallo. Tsaff ya cinye abincin dan yana cin abinci sosai dama shikam. Batare da ya sake mata magana ba ya miƙe ya haye doguwar kujera ya kwanta ya lumshe idanunsa. Nata idanun kawai ta zuba masa zuciyarta na rawa sosai....

      ________★

    “Wai mi kike shirin yi da wannan yaron da kika danƙarama wannan ƙyautar haka? Kainaat!. Ni gaba ɗaya kin birkita min lissafi wlhy”.
         Murmushi ƙyaƙyƙyawar matar da zata iya kaiwa shekaru talatin da huɗu ta saki. Sai kuma tai wani irin juya lafiyayyar kujerar office ɗin nata da salo irin na isa da ƙasaita tana kai bayanta kwance da lumshe idanu. Tsahon mintuna biyu kamar bazatace komai ba sai kuma ta buɗe idanunta a hankali akan wadda tai mata tambayar. Murmushi ta sake saki da motsa lips ɗinta dake ta shining na jambaki maroon ta ce, “Nadwa!”.
       “Na'am”.
   Nadwa ta amsa mata idanunta ƙyar a kanta.
     “Auransa zanyi”.
  Ta faɗa kanta tsaye babu shakku ko nuna damuwa balle kwana-kwana a zancen nata.
    A zabure Nadwa ta ce, “Aure!! Fa Kainaat? Da wannan abun dana tabbatar kin girma da kusan shekara goma? _Don_ ma da kuke shekarunku dai-dai da shi an miki sutu balle wannan jaririn. To ke da baki gama idda ba ma miya kawo miki wannan tunanin haka?”.
        Murmushi Kainaat ta saki tana wani limshe idanunta da sake buɗesu cike da yanga da ƙasaita. “Nadwa kenan, ai ƙarancin shekarun nasa ne suka ja hankalina da yin hakan garesa. Dan zan samu damar tafi da shirina yanda nake so. Rashin gama iddata kuwa ba matsala bace tunda ba yau nace a ɗauran aure da shi ba. Ina yin sharar fage ne kawai yanzu dan so nake ina gama idda a washe gari a ɗaura min aure da shi”.
     “Hummm wannan wane irin tunani ne yazo miki na rashin mafaɗi Kainaat? Kamarki matar riƙaƙƙen attajirin matashi ɗan ƙwalisa irin _Don Abaan_ ki rasa a inda zaki ƙare sai auren wannan gajan yaron da ko shekarun balaga bai gama cikawa ba. Anya duniya bazata miki dariya ba da kallon kinyi faɗuwar baƙar tasa kuwa? Ai shi kanshi Abaan zai sake jin izza da yarda ya fi ƙarfin naki kamar yanda yay iƙirari. Uwar tashi da ƙanwarsa da suka zama sanadin rabakun kuma sunci riba.”
       Murmushi Kainaat ta saki saki mai faɗi har ƙyawawan farare haƙoranta dake jere reras na bayyana. Idanu ta zubama aminiyar tata cike da ƙasaita. “Nadwa kenan, na fahimci har yanzu baki gama haddace ilimi akan halayena ba kenan. Ban so nace miki komai ba a wannan gaɓar amma ya kamata nace mikin domin ki tabbatar da ni Kainaat ba shasha bace. A tunaninki zan iya haƙuri da 1-0 a fagen wasa ne? Ai in har ba'ai 2-0 ba sai dai ayi draw wlhy, ko kuma a tashi babu ko ɗaya zai fi sauƙi ga abokin karawa. Bari na fito miki a mutum, saki ukun da Abaan yay min zan gyara na sake komawa gidansa dan aure ni da shi yanzu ne zai fara. Wlhy wlhy kinji na rantse, sai na raba Abaan da uwarsa da wannan shegiyar ƙanwar tasa mai kama da aljanu har abada. Sai na sakashi ya wulaƙantasu fiye da yanda suka sa ya wulaƙantani. Sai na shafe babinsu a zuciyarsa fiye da yanda ruwa ke shafe garin da aka gina akan hanyar wucewarsa. Zan ɗanɗana musu azaba sannan na wawashe kaf abinda ya mallaka a duniya ta yanda almajirin saman titi sai ya fisa kima da darajar kallo. Zan tabbatar musu ni Kainaat annoba ce a rayuwarsu. Talauci ga talaka kuma ba tambari bane adone”
       “Kin daina son Abaan ke nan?”.
   Wata siririyar dariya ta saki mai faɗin gaske. Kafin ta furta, “Bazan taɓa daina son Abaan ba har ranar mutuwata, sai dai kuma hakan bazai hana ni ɗan ɗana masa hukuncin laifinsa ba da na uwarsa da ƙanwarsa dan sabo da kaza a wajena baya hana na saka mata wuƙa a maƙoshi na yanka banza nai farfesunta na cinye”.
       “Humm amma kin san shi wannan yaron da kike son aure yana da mata? Sannan ba ɗan garin nan bane zuwa sukai nan aka ɗaura musu aure a gidan hakimi saboda mugun son da sukema juna shi da matar tasa”.
     “Wannan dalilinne yasa na zaɓesa ai. Batun matarsa kuwa idan ta kwantar da hankalinta ƙaruwarta ce. Dan bani da wata matsala da ita sai idan ta shiga gonata ne fa tabbas bazan barta ba koda ace zaman sati ɗaya nayi niyyar yi da mijin nata kuwa. Soyayya da kike magana kuma ni ban yarda akwaita ba. Dan naga abubuwa masu yawa a cikin idanun wannan yaron na hatsabibanci. Inda ace sonta yake da gaskiya bazai rabota da iyayenta ya kawota nan ya aura ba. Da sonta yake bazai dinga zubar mata da ciki ba a duk sanda ta samu....”
       “What! Zubar mata da ciki fa kika ce? Ke ko ina kika san duk wannan Kainaat?”.
     Wani shegen murmushi Kainaat ta saki tare da maida bayanta jikin kujerar ta wani kwanta........✍️



        _(Tofa wata sabuwa. Khadijah da Dafeeq laila da majnoon yaya dai?🚴🚴)._

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

   *_Typing📲_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_Shafi na bakwai_



INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN, DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

MAZA KU GARZAYO "UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN "TA TANADAR MUKU DA HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.🥰🥰🥰

KAMA DAGA
*FLYER
*3D MOCKUP LOGO
*2D MOCKUP LOGO
*NORMAL LOGO
*IMAGE LOGO
*BANA
*STICKERS
*ADVERT VIDEO
*PROFESSIONAL INVITATION
*INVITATIONS CARD
*BIRTHDAY VIDEOS
*POSTER
*CERTIFICATE.AND MORE......

CONTACT ME ON
👇
09035390383

____________


.......“Please Kainat yaya kika san duk wannan wai?”.
     “Humm Nadwa kenan. Na faɗa miki Kainaat ba shashasha bace ba ai, kin san dai bazan jashi jikina ban san wanene shi ba. Inama da fiye da wannan game da shi, sai dai lokaci ne zai sa ki san sauran gaba ɗaya ba yanzu ba”.
Idanu kawai Nadwa ta zuba mata cike da mamaki da tsoro. Maganar gaskiya bata son ƙawar tata tace zata shiga tsakanin waɗan nan ma'auratan dake tsaka da cin ƙuruciyar soyayyarsu. Amma ta santa tasan halinta, in har tace tana son abu sai ta cimma burinta a kansa, dan ita shaidace ko akan Don Abaan da yanda ya fara sonta har sukai aure shirine babba...
     
       ★★★.....

“Ina ganin zuwa jibi zamu koma sabon gidan can dan mu samu albarkacin juma'a”.
Da wani irin razana Khadijah ta jiyo tana kallon Dafeeq da ke magana a dake hannunsa riƙe da rigarta data miƙa masa zai shanya a igiya. Babu alamar wasa a kan fuskarsa ga shi ya wani tsareta da idanu. Nata idanun ta rissinar ƙasa tana ƙoƙarin saita rawar da jikinta ya fara. Sai kuma ta shiga jinjina masa kanta dan in har tai magana sai hawayen da take riƙewa sun zubo mata.
“Miye wani ɗaga kai baki da bakin magana ne wai? Khadijah nikam wlhy na gagara gane miki gaba ɗaya. Da ace wani kemin wannan sabon halin naki sai na ɗauka baƙin cikine ko hassada. Gaba ɗaya kin hana kanki zama lafiya. Ki duba fa jiya na shigo da waya gidan nan amma koda na nuna miki baki ko taɓata ba a tsatstsaye kika wani ce ALLAH ya sanya alkairi kika kwanta...”
Duk yanda taso riƙe kukan ta gagara yin haka a wannan gaɓar saboda yanda yake mata magana a zafafe kamar ba Dafeeq ɗinta ba. Miƙewa tai da sauri daga gaban kayansu da sike wankewar ta nufi ɗaki da gudu hannunta toshe da bakinta. A zafafe shima Dafeeq ya miƙe, tana shiga falon yana shigowa shima. Wani kalar fisgota yay baya tai taga-taga zata faɗi ya hankaɗata saman kujera. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa sun gama kaɗewa, cikin nunata da yatsa tamkar zai mareta ya ce, “K! Wai mi kike nufi dani ne? Dan Kinga ina lallaɓaki kike ganin kin samu hanyar wulaƙantani da jana a ƙasa. Ubanmi na miki ba dai-daiba anan?”.
Kuka sosai Khadijah ta sake fashewa da shi, sai kuma ta kai hannu ta hankaɗashi baya iya ƙarfinta tana ƙoƙarin miƙewa. Taga-taga yay zai faɗi ƙasa ALLAH ya taimakesa ya dafe kujera.
“Taauuu!!”.
Kake jin wani lafiyayyen mari a fuskarta. A gigice ta dafe kuncinta tare da fashewa da wani sabon kukan. “Dafeeq ni ka mara?!”.
“An mareki ko zaki rama? Ke har kin isa ki dinga jana a ƙasa kamar wani yaronki! Har kina da ƙarfin min wannan abun. Ko kuma dole sai nayi abinda kike so saboda haihuwata kikayi ƴar marasa tarbiyya”.
“Dafeeq nice ƴar marasa tarbiyyar?!”.
“Kina da ita ne. Ko ƴa mai tarbiyya ce zata bar uwarta da ubanta ta biyo namiji wata uwa duniya. K! Nifa na fiki iya iskanci. Har ni zaki dingama baƙin cikin cigaban rayuwata saboda ke butulu ce. To bari kiji ki kama kanki kafin na sassaɓa miki kamanni a gidan nan. Dan wlhy kaɗan da ga aikina ne na haɗa miki jini da majina wawuya kawai...” fuuu ya fice kamar zai tashi sama.
Ragwaf Khadijah ta zube ƙasa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya.. Tunda ta baro gidansu ta biyo Dafeeq yau itace rana ta farko datai mahaukacin kuka na tashin hankali da har ya saka mata masifaffen ciwon kai tare da jin wani abu kamar nadama nasan ɗarsuwa a ranta. Dan ko daren farkonsu tayi kukan azabar da taci a hannunsa amma baiko kai kwatankwacin wannan ba. Ita yau Dafeeq kema gorin bijirema iyayenta ta biyosa nan?, ita Dafeeq ya ɗaga hannu ya mara. Mari fa, mari mai suna mari da har take iya jin sayin yatsunsa biyar akan ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta. jama'a Dafeeq fa, Dafeeq ɗinta data zaɓa akan iyayenta da karatunta. Dafeeq data yarda ta bar komai ta koma mara komai ta ɗaukesa. ya arrahaman wannan wace irin rana ce haka da bata taɓa lissafawa a ciki lissafin rayuwarta ba. ya ALLAH kasa mafarki takeyi ba a zahiri bane ba. Ta sake fashewa da sabon kuka mai tsananin ƙona zuciya.....

(Hummm Khadijah kaɗan daga illar bijirema umarnin iyaye kenan. Ƴammata a dinga sassauta soyayyar da har zata iya saka ido rufewa a bijirema iyaye🤦🥲 dan zancen malam bahaushe nan fa na NAMIJI BA ƊAN GOYE bane gaskiya ne akan wasu mazan).


★★★......


Iya jigata da galabaita JJ yayi a wannan dare zuwa safiya. Dan da salo-salo su Alimah suka dinga firgitashi. Gaba ɗaya ya gama fita a hayyacinsa tamkar wani sabon kamu a hauka. Babu abinda yake iya ganewa tsakanin rayuwa da numfashi. Rana da duhun dare. Duniya da lahira, fari da baƙi. Abinda kawai ya sani a garesa komai ya gama ƙarewa kawai. Yayi masifar zama zuru-zuru cikin ƙanƙanin lokaci. Ba shi kaɗai ba hatta gidan kansa ya gama fita a hayyacinsa tamkar ba sabo ba, wanda aka ƙawata da kayan alatu.
Dukan gate da akeyi da ɗan ƙarfi ya sashi buɗe idanunsa da sukai masa matuƙar nauyi. Wani irin zafi da haske suka ratsa idanunsa da jikinsa a lokaci ɗaya. Tamkar wanda aka bulbulama wani irin ƙarfi ya miƙe zubur. Waige-waige ya fara, tabbas a tsakar gidansa yake kusa da gate gab. Idanu ya sake warewa na tabbatarwa. Farin ciki ya sake ratsashi ganin fa da gaske ƙofar gate ɗin ce dai. Ihu ya kurma na tsabagen jin daɗi mara misali, batare da tunanin komai ba ya miƙe a 360 zuwa jikin gate. Ƙofar ya shiga ƙoƙarin buɗewa yana waigen bayansa tamkar mai tsoron a biyoshi, yanda yake karkarwa da ƙyar ya iya buɗe ƙofa. Ko kallo bai yima wanda ke tsaye gaban gate ɗin ba alamar suke knocking ya wani kwasa a bala'in guje ji kake fiyyy-fuyyyy yana dukan iska, sai ya tafi gaba zai faɗi sai ya damƙi ƙasa ya miƙe yana waigen bayansa....
Tuni yara da ke wasa a tsakkiyar layin suka fara kwasa a guje suma suna ihu dan ganin ƙatoton mutum tsirara haihuwar uwarsa na gudu jikinsa yay wani irin butsaaa da ƙuraje ƙanana tamkar jikin kada. Cikin ƙanƙanin lokaci anguwar ta ruɗe, yayinda JJ ke falfala gudun ceton rai da iyakar ƙarfinsa. A haka ya kai har titi, bai damu da tare abin hawaba ya ɗauki titin da ƙafa. Sake ruɗewa mutane sukai ana kiran mahaukaci-mahaukaci. A tare a tare. Sai dai ina babu mai tarewar sai ma darewa da ake ana bashi hanya a guje. Duk da wahala da jigatar da yay gudunsa yake sosai batare da nisan hanya da yanda mutane ke ƴar tsere akan ganinsa ya damesa ba. Sai dai duk mai hankalin daya gansa yasan wannan gudun bana lafiya bane, sannan ba a cikin hayyacinsa yake yinsa ba dan a haka ya isa har gidansu.
A anguwar tasu ma tunda ya shigo ta rikice da iface-ifacen yara da mata da matasa. Dole akai dafifi wajen masa tara-tara da ƙyar aka iya kamashi. Ƴan gidansu hankalinsu yay masifar tashi, wasu ma kuka suke dan tun fitowarsa gida su Rabi'ah dake knocking gate yazo ya wuce su suna kuka sukai kiran iyayensu suka sanar da su. Tuni wasu sun nufo gidan nashi, sai dai a hanya suka gamu da shi, dole suka juya gida dan ganin komi zasuyi bazasu taɓa samun kanshi ba, ALLAH ma ya taimakesu hanyar gida ya dosa ba wani waje daban ba.....

(🤦 Uncle JJ badai kuma ka haukace ba😩😩😫).


...★...★...★....

Duk yanda ya fito da ga gida da tsananin ɓacin rai gaba ɗaya yaji zuciyarsa tai masa sanyi a dalilin shigowar kiranta. Cike da girmamawa ya ɗaga tare da kai sabuwar galleliyar wayar tasa iphone 14 data bashi shekaran jiyannan saman kunne yana ɗan murmushi. Sallamarsa kawai ta amsa da faɗin “Kana ina ne babban mutum”.
Wani irin murmushi ya saki mai faɗi, dan yana matuƙar jin daɗin sunan nan da take kiransa da shi. Cike da girmamawa ya bata amsa da “Ina gida ranki ya daɗe”..
“A to bara na haƙura wannan lokacin uwargida ne ran gida ai. A gaidamin ita sai da saf......”
Cikin sauri ya katseta da faɗin, “A haba hajiya, ai ko'a gidan giya akwai babba. Dan ALLAH kada ki katse ki faɗa min komi kike buƙata zan miki shi yanzun nan”.
“A'a ai ba'ayi haka ba Dafeeq. Ka bari kawai gobe ma haɗu” Kainaat ta faɗa tana danne murmushin ta.
“Hajiya bazanyi jayayya da ke ba, amma dan ALLAH ki bani umarni kawai ni mai biyayya ne a gareki”.
Ajiyar zuciya

Please Login or Register in order to submit comment