Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mishi ba, duk da kyanta nashi
gurin kyawu inya cika yawa hadari ne.***
hafis lady ta dubi farida amarya tace in fata kin
gama amfani da duk kayan da inno ta hada miki?
farida tace ke dai bari,kinsan Allah , saida na
gama komai dan iskan nan ahj sambo ya rusa
komai, da sauri hafsi lady ta mike tana fadin
amma ke farida Allah yayi 'yar iskar baiwa,
yanxun dan jaraba da rashin hakuri ke da za'a
kawo gidan miji sabon jini shine kikaje kika mika
kanki ga wannan tsohon ya shanye duk dan
tattalin da tanajin da aka ma ango? farida ta dubi
aminayarta ta cikin damuwa tace wlh kawata ba
da son raina bane bana ce miki yana ta damuna
da waya ba? tace bana ce miki kada ki daga
wayar ba? tace in ban daga damun da yakemin
dole na daga, cemin yayi in har banzo munyi na
bankwana ba , zai min tuggun da soja zai gane
kinsan ko ba zan so haka ba. hafsi lady tace me
ya hana ki kira ki sanar dani? yanda kike son
soja haka yake son mulki sai kice mishi kema zaki
fito ki fada ma 'yan jarida alakarku tace kash,
duk tunanin baizo min ba , to yanxu na danyi
amfani da wasu, tace inma ya gane ki hada da
kissa da kuma kisisina, sai kice fade aka miki tun
kina karama, inko bai gane ba ki share shi. farida
taja filo tace aiko kin kawo shawara kawata
nasan zai gane yanda yake kurin ya auri salihar
mace ya sameni fanko dole hankalinshi ya tashi
sukayi dariya sannan suka tafa
hafsi lady tace sauaran yanda kike son shin nan
ki nuna zakewarki da zalamarki zai iya ganewa,
kiyi ta nokewa kina....sllamarango da abokanshi
ya katse hirr tasu, nan take farida ta ja gyale ta
rufe fuskarta,sun gais bayan barkwanci aka sai
baki haka ango ya raka abokanshi sannan ya
dawo. sun gabatar da sallar ma'aurata yayi 'yan
tamboyoyi game da addini babu (not clear) dama
ya zaci haka kasancewar ta kamila a nashi
tunanin. soyayyarshi ya shiga nuna mata tare da
wasanni tana nokewa tare da nuna tsoro hakan
yasa shi binta a hamkali, yana da ilmi
musamman na fikihu yasan sirrin mata da yanda
halittarsu take hakan ya shiga bin komai a sannu
amma sanda ya kai kofar da ya jima yana raya
ma ranshi yanda zai bude ta, sai kawai yaji ta a
bude, hakan ya saka jikinshi sanyi take komai ya
lafa, ruf da ciki ya kwanta sai yana ji tamfar
mafarki, kuka ta saka tana fadin innalillahi wa
inna ilaihir raji'un dama nasan haka zata kasance
a kaina, ya daure ya dube ta amma ya kasa
magana, ta mike tare da neman kaya tasaka
sannan ta dauki gyalenta ta rufa ta tsugunna
gaban gadon inda yake kwance ka yafemin kuma
Allah ya baka hakuri nasan ban caacanci ka zana
dani ba ta mike zata fita yayi karfin hali ya tashi
zauna a kua bakofayc z n,ta jyo fuskashi tamkar
bai taba dariya ba gaban ta ya fadi.
[1:56PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----17
Yace xonan ki gaya min dalilin bada kanki ga
wani,ta soma kuka, ban bada kaina ga kowa ba,
ta xauna ta daga kai tamkar mai tunani hawaye
na xuba kan kumatunta,tun ina yar shekara
takwas wani mlmnm bayan mun tashi mkrnt ya
amshi jakata sannan ya bani wasu takardu ya ce
in kai mishi su ofis.bayan na dawo yana qofar
ajinmu sai yace in shiga cikin ajin in dauki
jakata,ina shiga sai ya biyo ni ya rufe qofa....ta
rushe da sabon kuka tankar gaske,taci gaba da
fadin ya min fyade yayi kaca kaca dani ya gudu
sai da aka min dinki a asibiti,ta kifaka kai tana ta
kuka mai ban tausayi,uaji makira,ya taso da sauri
yaxo xa rungume ta,tausayinta ne ya kika ranshi
yana ji aranshi da yaga wannan tsinannan mutum
babu abin da xai hana shi saka bindiga ya harbe
shi,daga lallashi ya xarce soyewa,ranshi fes.duk
da yaji haushin yanda ya sameta amma haka ya
daure bai nuna ba tunda ba laifinta bane,soyayya
suka shiga xabgawa a satin inda yaga shi
qaramin dan wasane a wannan fannin itace take
nuna mai salosalo na soyayya.
Abin ya ta bashi mmk hr ya kai ga tambayarta a
ina ta koyo wadannan salon,sanar da shi ta yi ai
ma'abociyar karance-karancece, dan haka sai ya
yi murna da jin haka ta mantar da shi komai.
dani da ke mkrnt muka gama jarabawa a ka
bamu hutu. kamar nasan ba zai zo dauka ta ba
na ce Balkisu in direban ku yazo daukarki zai sa
min hannu ku sauke ni kaduna.Ta ce in an zo
daukarki fa? Na ce bros dina na Abujan nan ne
zai zo daukata,kuma gidan shi zai kai ni ni ko ina
son ganin Momy,Mina ta ce kai Queen ki tsaya a
Abuja nan basa sai muna ziyartar juna ba? Na ce
kin sani ne? ba ma shi da shi ne sosai zai matsa
min gara in je gurin Momy haka ko direba su ya
zo suka sauke ni har gida Murna gurin Momy
kamar me musamman ganin yanda na koma.Sun
gaisa da Balkisu sannan suka dauki hanyar
jigawa ko na ce Kano,Momy ta ce me ya hana
Soja yaje ya dauko ki? Na ta6e baki sannan na
ce kila ya manta,ta ce wane irin ya manta? Na ce
ina wayata ne? Ta ciri min ta ce gata sai kin
saka a caji na ce zan kira Rahma ne ta san na
dawo.
Momy ta ce ina ruwan Rahma in taje gaida Mama
ta kan shigo mu gaisa ai Usman ya yi sa'ar
mata,na ce sosai ma ita ce dai ba ta yi sa'ar miji
ba,Momy tana dry ta ce shima ai ba ruwanshi na
ce ni kam gare ni ba shi da kirki,Anty ta shigo ta
ce 'yan mkrnt hr kin iso? Na ce eh ina yini Anty?
Muka gaisa ta ce ke da maigidan ne? Na ce a'a
kawata ce suka rage min hanya,Momy ta ce shi
ne zai zo ya dauko ta yana fama da Amarya? Ai
zai zo ya same ni, Anty ta ce a"a Momy kin san
ko bayan ta taho yaje? Ta ce ba wani zuwa da
zai yi wannan kawar tata da suka kawo ta tun da
daga jigawa aka je dauko ta amma na cikin Abuja
bai je ba ki ce yana da niyya.Tunda nazo kaduna
bai ta6a zuwa ba,Momy kuma bata neme shi ba
don koda ya yi mata waya bata ta6a mishi
zancena ba, Ko ta ce yaya ba muyi hutu ba? Ko
kuma nazo bai zo ba sannan ta lura bai ta6a
kirana ba, don haka ta ce ta san maganinshi.
Abbada ya nemi ba'asin zamana a kaduna,Momy
ta ce nazo ganin gida ne.Hutun mu na sati 4 ne
saboda SS2 zamu shiga rannan na shiga gidanmu
mun gaisa da su Mama,sai ga Rahma.
Na ce yauwa kawata,dama ina ta jiranki ne kizo
ki raka ni saloon,ta ce muje nima ki biya min na
wanke nawa na ce lallai Momy zata ba ni sai dai
kije gurin Ya Usman ko ke ma Mama ta baki?
Mama ta ce zo gashi Rahma,Rahma ta fita tana
dry tare da fadin wasa nake Mama,gidan su
Momy shiga na yi wanka ina kwalliya muna hira
da Rahma muka ji sallama gabana ne yayi wani
mugun faduwa ban san mai sallamar ba,na gama
na saka riga da siket na atamfa 'yar Holan mun
fito falo Momy ta ce ga kudin gyaran kan na ce
dari biyu ma za ki ban. Ta ce rike dari biyar din
na amsa zamu fito kenan akayi sallama kofar
Momy gabana ya sake faduwa ta daga labule ta
shigo,Nan take na gane ta. Faridar Ya umar don
bayan hotonta da na gani hr da kalandar su na
gani dakin Mama hr da agogon su sanye take da
wani shegen leshi wanda kyawunshi ya nuna
tsananin tsadar shi. Ruwan madara ne da ratsin
ja dan gyalenta shi ma ja, Haka takalmi da jaka
na dauke kaina daga dubanta duk da ba son
mijinta nake ba sai na ji kishinta yana yin kallon
da take min tana tunanin nice matar mijinta
tunda duk sauran taga su lkcn bikinta,sannan
taga idon da yake ce mata yarinyae ba kyau
ba,sai ido kamar na mujiya....
Ni dai muka fita kofar waje muka yi kici6is da Ya
Umar ya dube ni cikin mmk ba komai ya ba shi
mamaki ba yanda ya manta dani har ga Allah ya
manta da wata matarshi a mkrnt yanzu mai zai
ce ma Momy ban ko kuma kallon shi ba na sa
kai na fita abina,Rahma ce ta tsaya gaishe shi ta
biyo ni me yasa bako gaida shi ba? Na ce yanzu
ba da ba ne,ba zan dauki wulakanci ba ko dama
don ni sane na jur wani abina. Shi kam da ya
shiga gurin Momy sai ya shiga kame-kame yana
cewa shi sam mkrntr ba su mishi waya su anyi
hutu ba,Aliyu ne. ya dauko ta ba shi ba ne amsar
da Momy ta bashi kenan,ta fita daga dakin,Farida
ta dube shi Soja na wadda tafi ta yanzu ita ce
Asma'u din? ya ce eh kawai shi yasan Momy
tana fushi dashi ne don ko gaisawa sama-sama
suka yi ta,Ya kai Farida dakin Antynshi sanda na
dawo daga saloon na gansu zasu shiga
gidanmu.Yanayi tamkar ban gansu da na wuce
abina,na samu Momy tana yanka Alayyahu na
amshi yankan Anty Amarya tana ciki tana tuka
tuwan shinkafa,dama su baka gane mai girki
komai tare suke yi.....
Gefen baki suka kwana da farko neman masauki
ya ce zai yi a hotel,Momy ta ce duk gidan nan ko
can gidan Alhj ba gurin kwana sai ka kaita hotel
saboda ta raina mana arziki? To kuje sai da safe
a gabn Farida ta fadi haka,nan yake ya gyara
musu gefen baki tunda Aliyu baya nan haka nan
su Jamila.Jamila da Nafisa suna gidan Anty
Salima shi ko ya Aliyu sunyi tafiya da Abba ni dai
ina can kuryar dakin Momy koma falo na zauna
ba zan ta6a gyara musu gurin kwanciya ba,da
safe ma sanda suka shigo na gama karyawa
kawaye da Mina Turaki ina jin sanda suka yi
sallama yi na yi tamkar ban san suna yi ba,Suka
zauna Momy ta fita suka gaisa ya Umar sai
hararata yake,na mike na shige cikin daki,ina
amsa wayata,dakin Anty suka yada zango karfe 2
suka tafi bai ce ma momy komai game dani ba
haka nan nima ban ce kala ba dama bana so ace
in bishi Momy ma ba ta ce komai da hutun mu
yana karewa ta mishi waya bai zo ba ba ya turo
kudi wai Aliyu ya yi min shopping sannan yajw ya
biya kudin makaranta hakan ce ta kasan ce muka
koma makaranta......
Tun daga wannan ganin ban kuma ganin ya Umar
ba,har muka gama SS2 muka shiga 3 duk hutu
Momy zata aiko a dauke ni ta ce ma Abba ita ce
na dinga zuwa kaduna saboda in an gama gini
shi nan zan zauna, ko da Abba ya tuntua6e shi
da wannan batun sai ya ce haka ne don haka ya
saka shiriritar gama aikin nima haka na ke so,
domin yanzun shi kan shi da zai ganni ba yabon
kai ba yasan na fi karfin wulakanci daga shi har
matarshi basa gabana na samu labarin an ce
tana da ciki amma watan cikin hudu ya zube
yanda nake ji gurin su Jamila tamkar zai yi kuka
saboda zubewar cikin na ce su karata. Duk da
matsatsin fiar da ya Umar ke ma Farida hakan
bai hanata hulda da abokan shashancin ta ba,ta
kan fake da zuwa gidan Yarta dake nan Abuja
cikin ta ma cire shi tayi saboda yana bata
matsala da abokan harkarta. Alhj Sambo shi ne
ya hada ta da likitan da ya cire mata cikin.
********** cikin Yardar Ubangiji muka kammala
karatunmu bayan kammala komai aka bamu
kyautuka kowa ya kama gabanshi sai dai abn
farin ciki ina daya daga cikin dalibai uku da
makaranta ta za6a don daukar nauyinmu,muyi
karatun Likita saboda hazakarmu in ka ji ana
Asma'u to a kaduna ne Amma Abuja har gobe
Queen suke kirana.....
Sai da muka dawo gida na samu Momy zata biki
jos danginta na bita muka tafi ansa bikin Hadiza
da Shema'u Sai na Ya Usman da Aminiyata
Rahma,Hadiza da na Ya Aliyu ne haka Shema'u
yaron yayan Mamanta ne Sadik. Tun da biki ya
matso ba mu da sukuni kawayena su Mina duk
na gayyace sy kuma nasan za su zo. Biki ya yi
biki kenan,na musu ankonmu duka don har da su
cikin kawayen aana gobe daurin aure suka iso
Mina tariga su isowa saboda tafi kusa,sannan
Balkisu sanda Fatima shehu ta iso mun gama
shirin tafiya lunchen ko hutawa bata yi ba ta yo
wanka muka fito,muna ta shakiyancinmy da
muka saba,Kowace direbansu ya kawo ta, don
haka muka shiga motar su Mina muka shiga
tunda shi direban su ya huta haka muka kayata
gurin tamkar taurari gaba kin su Mina baya
gajiya da fadin Queen duk in da na bi nan sauran
mutune suka dauka Queen-Queen,duka amaran
lunchen gurin daya muka hada tunda duk gida ne
har angon shema'u tunda ya saba dama dasu ya
Usman ni da Jamila mun dauki kwalayan
abubuwan da zamu raba ma mutane muna kaiwa
gurin ajiye wakafin mu sona rabawa,Anty Saluna
ta kira ni nazo ta ce ina aurans Na ce wane aure
kuma?Har ga Allah ni ina mantawa wai ni matar
aure ce,Har mijin kanshi na manta da batunshi.
Ta ce iye lallai Asma'u kin hadu shi yasa ko dan
gyale ba ku saka ba,na ce share kin ji har zan
tafi Anty Fatima ta ce kishiyarki ta ko zo? Na ce
tazo bata zo ba ban sani ba,anty Aina'u ta ce na
ganta gab da zamu zo nan na ce ita ta sani ni
ina ruwana......
Guri ya yi guri,na rasa duk inda nayi jama'a
kallona suke,ga mai wakar ya kama Asma'u
Queen ban san da wanda ya sanar dashi sunana
ba,Har da fadin Queen din Umar Soja marmari
daga nesa,naja tsaki na ce bar hada ni da wani
Soka,Jamila ta dauki kafadata ta ce dama tun
dazun nake son in ce miki duk wanda ya kira ki
zamu dau mataki kanshi,na ce jacan ki bani
guri,yanzu nake tashena wannan Sojan ya min
Tsufa,don haka duk wanda ya kira ni zuwa zanyi
muka saka dariya ni da su,gashi dama muna da
wata sara ni da su Mina,in munyi abin dariya
mun dara sai muce wa ya dukanmu Jamila ta ce
Allah ya shirye ku,Haka aka sha lunchen muka
taso muna mota su Mina suka dame ni wai
wanene Umar Soja? na ce don Allah ku bar
zancan shi nima ban san shi ba,Fatima shehu ta
ce ba wani ba ki so nw musan Saurayinki kawai
Queen.Jamila zata yi Magana na toshe mata baki
amma sai da ta ce musu mijinta ne,na ce kunha
nayi kama da matar aure? Muna tsayawa kofar
gidanmu Anty Salima ta miko min yaronta Muslim
ta ce don Allah Asma'u ki kai danku gurin
Momy,na ce yaron nan kato da shi yana tafiya ga
surutu amma sai kuyi ta daukan shi? Ni dai ba
zan dau ke ka ba sauka ka taka da kanka.Anty
Aina'u ta ce dama ke ai ba ki san yara na ce ku
ai yaranky sun cika kuya Anty Fatima ta ce kema
in ki haifa kin rike naki na ce ba konai suka shige
gidanmu mu kuma muka nufi gidan Abba da
kawayena ina rike da muslim sam ban kula ba
she su Ya Umar da ya Abubakr ne a gurin tare da
wasu daban ban san su ba.Muslim ne naga ya
kwance hannunshi ya ce ga Dadyna ya nufi gurin
Ya Abubakar.Mina ta ce la ji yaro da wayi yasan
Babanshi ko ba Babanshi ba ne?? Na ce
Babanshi ne mana Bilkisu ta ce yayanki ne, Na ce
shi ne Na farkonmu a dakin mu muka zo gota su
yi nayi tamkar ban gansu su ba saboda ya Umar
dake gurin sai naji su Mina suna gaishe su, har
mun gota naji muryar ya Abubakar yana cewa kE
Asma'u zo nan na juya na zo shi nake duba na ki
kallo gurin Ya umar, na ce gani ya ce ke har
yanzu.....
Kanki bai dana hayaki ba ko? Na 6ata rai ya ce
gaba kina kallonmu kin wani dauke kai sama
sannan dubi shigarki babu ko dan gyale kin daura
gwargwaro a kai gashi a waje tamkar ba matar
aure ba ko?Na dubi sasheb ya Umar da gefen ido
waya yake amma na kula da kallom da yake min
da gefen ido, na wuce ban ce komai ba, Fatima
Shehu ta ce wai da gaske kina da aure ne? Na ce
don Allah muje ciki. Falon Momy na bar su na
shiga dakin Anty Amarya dan na dan watsa ruwa
kasancewar gidan bai cika kamar gidanmu ba,tun
da nan gidan Maza ne wanka nake na tuno ya
Umar da na ganshi yau in har ba zan manta ba
yau shekara biyu da wata shida kenan rabona da
na sa shi a idona. Ya Allah sam ban ji zuciyata
tayi farin ciki da ganin shi ba,duk da cika da kyau
da kwarjini da na lura ya kara,sannan ga kudi da
ya zauna. Can waje kam ya Umar ya dubi Muslim
sannan yasa hannu ya dauke shi tare da fadin zo
nan big boy,yayi sha'awar yaron kwarai da
gaske.Yanzu kam ya matsu yaga dan kanshi.
Farida ya lura abin bai dame ta ba,in yayi la'akari
da yanzun makarantar da ta koma tafi dauke
mata hankali,ko dai zai............sai kuma yaja
tsaki yayi shiru,yana son yin shawara da Anty shi
ya dubi Abubakar ya ce bari na ga Antyna,Muslim
ya ce zanje gurin Dadyna,ya Umar ya ce nima
Dadynka ne ai ya ce a'a ga Dadyna nan Ya Umar
ya mika shi suna dariya ya ce jeka gurin Babnka
ya nufi cikin gidan ma ba mutune sosai kamar
yanda ya zara ya shiga gefen Antynshi babu
shamaki,ko ina shiga yake kai tsaye ya shige
bedroom yana fadin ina Antyn tawa take? Ni
kuma na fito daga ni sai wani dan tawul wanda
iyakarshi cinyata,kallonaya tsya nayi wani abu ne
yaji shi tub daga yatsun kafarshi har kanshi
idunanshi sun kasa daukewa daga kaina.
[2:07PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu 1----18
Ganin yana min kallan qurilla na juya na koma
toilet ya bini da kallo har na shige na kulle qofar.
ahankali ya kulle ido ya sake bude su sannan ya
jingina da bangon dakin a hankali ya furta ya
salam.jikinshi babu qarfi ya fita xuwa falon anty
ya xauna kan kujera wani abu yana mishi yawo
aranshi yayi ajiyar xuciya tare da jingina bayanshi
da kujerar,lkc guda ya kwantar da kanshi,yarinyan
nan ce haka? daman haka qiranta take?wata
xuciyar tace ko dai kaji sha'awanta ne?kafin ya
samo amsa sai yaji maganan anty,ta dubeshi dan
gidana,yayi dan murmushi ya ce ina kuka jene?
tace munje kai abincin biko mana,yace kai mata
kun cika bidia,yanxu tsakanin gidannan dana
baba alhj har akwai wani biko ne ko bai kone ma
kika ce? tayi dry tace hakama mama tace,yaja
murmushi yace ina farida ne? tace aini tunda
muka gaisa tace min xataje gurhn wata qawanta
gashi har magariba bata dawo ba, ya ja tsaki
yace tasan inta fadamin baxan barta ba shine
watan ta tafi?yace anty matsaloli sunyi yawa
dama ina san mu xauna....
Ya dubi agogo ga lkcn sallah yayi bari ayi isha'I
cewar anty daidai nan nazo na wuce su ya dube
ni sannan ya dubi anty yace yarinyar nan ta samu
daurin gindi wurin momy ko gaeshe ni batayi ba .
anty tace harda kai dangidana , da ace tana
gidanka dole ta gaishe ka . yace bari naa dawo.
mukam gidansu rahma muka nufa inda za'aje a
kwashe mu xuwa zuwa gidan kanwar momy da
take u/dosa , dan can xa'aa sa lalle. lkcn da ya
umar ya samu xama da antynshi ya dube ta kin
san anty meke damuna? na farko kamar yanda
kika sani inason yara kin sani anty sannan naa 2
farida tunda ta koma makranta bataso ina mata
xancen haihuwa , ga shegen yawo, look at, lkc
yanxu kusan 9 bata dawo ba haka in taje
makaranta bata dawowa akan lkc ga matsalar
abinci saidai muci na kuku ga yawan zuwa yola
suna yau suna gobe biki na gaji. anty tayi shiru a
ranta tana nazarin me xatace dashi in kuma ta
fad xai yarda? amma duk da haka sai tayi kuru
tace umar yace naaaam tace mexai hana ka
dauki matar ka asma'u ?ya dube ta da sauri tace
kwrai, tana da kyau tana da diri inda bata da
kunya yanxun tana dashi hakanan bata duk
halayen ta daka santa dasu duk ta daina koh
masifa dama sai an tabo ta, snnan zata iya
haihuwa, shiru yayi yana nazarin maganar anty,
ta sake dubanshi sannan kuma xakasha fama da
momy . shiru yayi yana tunanin maganar anty ,
yasan tabbs shi bayason yarinyar saidai zata iya
haihuwa amma ya zai cema momy
Ya dubi anty me zance wa momy? gaskiya don
son yarinyar nan banayi na tsane ta saedae don
son haihuwa , xan nemi komenta ko nace zan tafi
da ita saidai momy ce matsalar. dan na kula
yanxun ban cikin yan harkokinta kuma duk akan
yarinyar ne. anty tace ta baya xaka biyo wato
wurin abba, kafin yayi magana farida ta shigo da
sallama, tare da fadin anty kin ganni sai yanxun
koh? ganin soja yasa tayi tsit tasan tayi laifi tun
xuwan su ta kama gabanta ta zauna ta fadin
danAllh kayi hkr sojana na kir wayar ka taki shiga
ya dubi agogo 9 daidai sannan ya dube ta ina
kikaje? kafin ta bashi amsa wayar ta tafara ruri,
ta duba ta ganin ahj sambo ne yasa gabanta ya
fadi, ta dauka cikin tsorofuskarta daure tace lfy?
yace na kiraki ne naji kin kai gida lfy? tace eh
yace kin manta pant dinki anan , tsaki taja
sannan tace sai anjim, ya kwshe da dariya ta
kashe wayar, yarda duk ta tsargi kanta yasa ya
umar tunanin batada gaskiya, yace ina kikaje
nace? nan ta soma shiryo karya , wlh wta 'yar
set dinmu ce a skul dama nan suke da mijinta ke
aiki can shi ne ya samar mata skul dinmu , jiya
na kirata nace mun zo kd.
Shine tace itama tana kdsai tamin kwatance naje.
yaja tsaki yace wa kika tambaya ya baki izini ?
tace yi hkr , bai kuma magana ba ya dubi anty
xan tafi masaukina , don masaukin gidan nan xai
cika yau.farida ta tashi bari naje ya daga mata
hannu alamar kada ta bishi sannan yace inaso na
samu rest of mind, ba tare da ya jira komai ba ya
tafi , anty tace meyasa xkiyi gngancin nn kinsan
mijinki bayason yawo? tace soja ya cika kishi ne
anty, anty tace ai duk namijin da baya kishn
iyalinshi jaki ne, saidai na wani yafi wani, nan
suka kwanta tna tunanin yanda xata shawo
kanshi dan tasan sojan bai iya fushi ba.kwance
yake rigingine fuskar shi tana kallon
sillntunaninshiyana kan yarnyar ,ganinta yake
cikin slow tana tafiya lkcn da suka wuce da
kawayenta , sannan tazo mashi rai sanda ya
ganta daure da towel santla santalar cinyoyinta
da kogunta ya tuna, nan zuciyarshi ta raya kwarai
xata hafa mishi yara, saidai yasan xai fuskanci
matsala wurin momy , ga yarinyar fa?
Ranar daurin aure gidajan kam da jama'a Mu dai
wannan lkcn muna gidan su Rahma Muna ta
shirya yanda zamu gabatar da walima anjima
bayan dauren aure.Lkcn daurin aure ya karato na
ce kuzo muje gida muyo wanka kunga in gidan ya
dinke da jama'a ba zamu samu gurin shiga
ba,abokana ya Usman suka zo suka kawo mana
drnks wanda zamu yi amfani da su gurin walima.
Na ce su sauke mu gida,suka debe mu wajan har
ya soma cika da mutane,gasu Ya umar da
abokanshi irin su Al-Amin,da sauran su,ban da su
ya Abubakar ga sunan.Muka sakko daga mota
tun kan mu shiga cikin gida Mina ta dame ni da
tambaya don Allah wancan yayanku ne? Mai
sanye da farin boyl din can? Na dubi gurin ya
Umar take magana amma sai nayi tamkar ban
gane shi ba na ce wa kenan? Bilkisu ta ce wanda
jiyan nan muka ganshi cikin kakin Soja, na ce
sunanshi ya Umar shi ne babban yaron Momy,
Fatinma shehu ta ce suna kama gaskiya,yana da
kyau gayen na ce wane kyau anan? Bilkisu da
Mina har suna hada baki gurin cewa ko ke ya fiki
kyau Queen duk da kina mace, Na ce Allah ya
kyauta,MINA ta ce yana da mata? Na ce kilama
tana nan cikin gidan nan suka dage kan in tana
ciki don Allah na nuna musu ita....
Tun daga nesa na hango dakin Momy fal da
mutane haka falonta, haka muka ja birki kofar
Anty falon ta da mutane ba su da yawa ban tsaya
dubansu ba na ce ku zo nan dama kayanku na
ciki.Bedroom din Anty muka shige,duk muka zube
mata kan gado,na ce bari na debo mana waina
ko tuwo? Suka ce wainar dai na dibo na shigo
saina ga ashe harda Faridan ya Umar a cikin na
zauna a falon Anty. Na shiga ina cewa kai 'yan
iksa ga to matar da kuka ce in nuna maku Bilkisu
ta ce matar Sojan nan? Na ce eh wata fara, duk
suka tashi da gudu.Suka je suna lekenta. Suka
dawo suna fadin tana da kyau gaskiya na ta6e ba
ki na ce suyi ta kyansu,Fatima Shehu ta ce
Amma dai ba mamnku daya ba? Nan na ce
musu,nifa canne gidanmu,maman can gidan ce
Mamana,ba Momy ba, yanda muke dasu yasa na
basu labarin na amma ban sanar dasu yanada
akayi auranmu ba na dai ce ba ma son juna aka
hada mu,sun sha mamaki sannan suna ta min
korafin me yasa bana sonshi dan Allah in yarda
Mina cewa tayi wlh ban da ke da kike tsakani da
sai na ce ina sonshi na ce ki ce mana,aini ba fa
zan zauna da shi ba,ina samun wanda na ke so
wlh dole ya bani sakina, Nan dai muka ci muka
sha muka yi ta shakiyancin mu,sai dai kiji muna
ihu muna cewa waya kwashe da dariya don ko a
school in muna sama mutum iddo ya bani
damu......
Wayar anty dake kan mirror ta soma kuka na
duka naga ansa dan gidana nace a raina ya umar
ne na aje hak yayi ta kira su mina suka ce na
dauka nace a'a sojn nan ne suka ce na dai dauka
don Allah tunda ta tana can cikn mutane , ina
dauka ya soma fadin antyn, cikin masifa nace ba
ita. bace tace to ko wcece tce frida tazo, na kshe
wyar sannan nce ina ruwana

Please Login or Register in order to submit comment