Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce tayi mishi albishir ranar ina kwance
kan doguwar kujerarta ta kra su suka gaisa dashi
ke tasa waya inaji yana ce mata ina a amanata?
hope tana lfy? tace kwarai lfyr ta lau,yace bana
samun wayarta dukna damu,anty. asmy tana da
rigima sosai gashi yanzun ta shiga rayuwata
sosai amma ita bata sona, anty ta kalle nicikin
murmushi sannantace yanxun ma na kiraka ne in
maka albishir yace dabino da zam zam ina jin ki,
tace mun samu karuwa yar rgimarka tana dauke
da juna biyu don haka sai ka siyo mana kayan
beby yanda ya rikice a waya abinhar mamaki ya
bani,fadi yake don Allah antynah da gaske?
Alhmdl anty zanje inyi dawafi zanyi sallah in gode
ma ubangijina,sannan inrokesi ya sauke ta lfy,
don Allah anty kice mata ta bude wayarta,
zucyata tanamatukar son jin muryarta, ya kashe
wayar.
Farida ya isko tana cikin daki tanata sheka bacci
tafi mai da kai ga bcci fiye da aikn data zoyi, ya
rungume ta sannan ya girgiza ta yana fadin tashi
my farida kiji abin farin ciki daya sameni, da sauri
ta tshi ga zatonta training din da yaketa addu'a
Allah yasa yana ckn wadanda za'a tura ne ya
samu lbrn sunanshi yan ciki,tace menene sojana?
yaceasmy tana da ciki ,haba wani mummunan
faduwar gaba taji nan take kishi ya dirar mata
tamaimaita kalman ciki? yace wlhyanxunnannty
nah tayo min way, tayi kokari ta danne kishinta
tace Allah ya bamu masu albrka, yace
amin.hakika ya jima yana rokon Allah ya inganta
mishi ya kuma roki Allah ya cusa sonshi a zuciyar
asma'u da sukazo batun tsaraba kuwa nan farida
taga hauka, kaya yayi ta lodnamata da maza har
sai da tanuna jin haushinta sannan ya lafa
takano suka sauka kaitsaye kd suka nufo a jirgi
lokacin ina bacci cikin baccin nake shakar
kamshin wani daddadan turare, sanda na farka
sai nagaya umar sanye da fara jallabya kara kar
Da hula itama fara sai yayi minkama da larbawa,
domin sajanshi yayi kama kawai dasu , ya umar
yana da kyau namijine cikinmaza, yaana
cikinmaza masu wuyar samu,irinsu ne one in
town amma a zuciyata ba sonshi, kamshin
turarensa yayimindadi yasaki murmushi sannan
ya zauna kusadani ya dubimomy cike da fara'a
tafarka,momy taceka tshe ta dai ya tsura min
nikam kamshin turerenshinake shaka ji nake
tamkar in tashi in shigejikinshi inta shakar
kamshin momy tace ina farida fa?yacetanadakin
anyna ta mike bari insaantyn taka ta shirya muku
abinci ko? taana fita ya dube ta da murmushi ni
kam har da kra shigar da fuskata tsakiyar
kirjinshi kamshin nan ina sonshi shi kam yaji
dadin yanda nayi lamo a jikinshi ya saka murna
kuma yanazaton Allah ne ya amsa addu'arshi na
fara sonshi ne tunda yaga in ya rungume ni
tureshi nakeyi ko in ta mutsu mutsu amma
yaunice da kara kankame shi, bmu sanmomy ta
shigo ba saimgnr ta mukaji tana cewa, farida
shigo mana da sauriyaa sake nini ko sbd kunya
sai na koma na kwanta shima ya dan sosa wuyar
shi irinna wanda yaji kunya din nan, sannan ya
zauna .
[7:45PM, 17/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu 2----10
Farida ta shigo muka gaisa tace yaya jiki?nace
jiki da sauki na dai ki tashine ya samu tafi tare
ko dankaratuna ammaa naki yarda,nace ni gurin
momy zan zauna momy tace ya brni , ina kara
warwarewa sai yazo yaa tafi dani, yanda farida
taga kowayana lallaba ni musamman shikanshi
sojan ta hankalinta faya tashi sannan ta soma
tunanin ciki itama suka tafi bayan ya roke nikan
cewa kada na kashe waya na barta a bude domin
yana son jin muryata ,har ma yace yana tayi ni
murna, mun kusan rabuwa cewar shi ina haihuwa
zai bani takardata,hakanyasani murmushi
donmurna. bankokashe wayata ba kamar yanda
yaroka, sun isa ya kirani asmy mun isa gida da
fatankna lfy dababyna?nace um yace ki dinga
min mgn mana,ni dai shiru namishi , yace toki
shafa min baby na na tura baki duk na kosa
yagama mgnr ,kamar ya sani yace to shi kenan
sai anjim. na riga shi kashewa, sannanna kwanta
wanina me cikiwai yanzu babu abin danakeson ji
irin kamshin ya umar, hak na kwana da safe
mana samu turarukana inata shaka amma daga
wanda yakusan amai saime son sani ciwonkai
donhakana tarkata su na'aje kayan da na cire na
daukana kara shakar kamshin.
Yau kwanan shi 3 da tfy cikin dare na kasa bacci,
qamshin turaran nan nake matuqan so na
shaqa,nunfashina har yi yake tamkar xai
dauke,kunsan mai ciki in taso abu ga kayan da ya
rungumeni dasu neke dan shaqa momy ta saka
su cikin wanki an wanke su an goge na dauki
wayata na shiga neman layinshi wani abin haushi
saida ta soma ringin sannan wata xuciyar tace
me xaki ce masa? nan take na yanke sannan na
koma na kwanta.shi kan lkcn yama kan sallaya
yana miqa godiyarsa gun ubangiji ta wannan
baiwa da ya mishi, bayan ya kammala ya miqe
sai daya xauna a bakin gado sannan ya dauko
wayarshi dake aje gefen gado ya duba ga
mamakinsa sah yaga no ta da sauri ya soma
neman layina,har na fara bacci naji ringin da
saurh na duba shine araina nace me xance mishi?
amma sai na dake na dauka, yace asmy me ke
faruwa? nace name fa? ya qara saisaita murya
yacf naga call dinki ne,nace ni kuwa?na dan ja
tsaki gsky bani bace yace hope kina lfy.nace
lau,amma kuma nayi shuru, yace fada mana me
nene?
Nace kodai ma bar shi,ya tausaya murya plx
asmy gayamin mana, nace to yaushe ne xaka
xo? yace cikin sauri kina san gani nane? nace a'a
dama xance ina san turare ne nawa duk basamin
dadi yace shi kenan xan xo miki da shi cike da
haushin kana na kwanta a raina ina cewa qilan
ma ya xata na damu dashi ne.shi kan cike da
farin ciki ya kwana xuciyarsa ta rage xugi yana
ganin ta soma damuwa dashi.sati daya da
yamma lkcn mun gama dramer dasu jamila xata
dora shinkafa da miya nace miyar nafi san asa
ganda maimakon kifi da nama xa-a sa,momy
tace to maxa jamila taxo jaje kasuwa ta siyo
ganda, haushi ya cikata tace wlh momy kina
shagoba asma'u yanxu sbd ita xa'a canxa abin
da akai ninya? momy tace ki dau kudi ki wuce
banasan dogon turanbi nafisa dake nhnke kaya
tace ai ita anty arma'u ta cika saka mutane aiki
kamar kanta aka soma cikin sai dana bari momy
ta fita nace kema yanxu xan qirqiro mikh
naki.tace wlh babu abinda xan maki tunda yau
bani ce da aiki ba,nayi dryr mugunta,momy na
shigowa nace ...
Nace nafisa ina xan sami xobo mara suga sosai?
tace oho miki,momy tace baxa a rasa xobo anan
gidan ba tashi ki hada mata nafisa,tace wlh
momy dama tace sai ta sani aiki ne ba wani
xobon da xata sha, na dake nace in baxaki yi min
ba to siyo min gun maman walida,momy ta ce
a'a ta tashi ta hada da yawa kowa yasha nafisa
ta fita rai bace na shige bedroom ina dry.sai
kawai na tsinkayi sallamar ya umar cikin
muryansa mai saka mara jin magana natsuwa, na
xauna gefen gado, naqi fitowa, take raina ya
soma tuno min da daddadan qamshin turaranra ji
nayi tamkar in fita in rungume shi,duk da rashin
ran da nake mishi amma sai na dake,sun gasa da
momy ta tambayi farhda yace tana gaishe ta,sun
dan taba hira kafin ya tambaya ina nike? momy
ta ce tana nan ciki yace ba wata damuwa ko?
momy tace da sauqi damuwar nan ka shiga dai
tana ciki ua tambaye ta, jin haka yara nayi shiqu
tamkar mai bacci na kwanta, ya shigo da sallama
yatsaya akaina yana kallan fuskata,ina jin sautin
murmushin shi.
Sannan ya tsugunno saitin kunnena yace asmy na
sani idonki biyu,yanda ya kusanto ni sosai yasa
qamshin shi ya kai ma hancina xiyara,na bude ido
a hankali na sauke su fes akan fuskarsa, yasa
hannuwanshi ya dago ni xaune shima ya xauna,
ban ankara ba naji tafin hannunsa akan marata
yaya bebyna? na runtse ido tare da daure fuska,
sam bana san tuna cewa inada ciki, ya rungume
ni tsantsan na qara nutsa kaina cikin qirjinsa
qamshin shi nake shaqa tamkar naga turaren, ina
qara manne mashi ya shafa ni a kunnena ya ke
tambayata kina san babynmu? na girgixa kai
alamar aa ya dan sausata riqona yana duban
fuskata baki san babynki? na bata rai nace ni fa
ba babyna bane,yace to yanxu ke ba kya sanshi
kenan nace allah ni ba ruwana da shi, na miqe
ina qoqarin qwacewa yayi wata sansanyar ajiyan
xuciya sannan yace to ki kawo min wani abu inci,
na fita shikuma ya bini da kallo a ransa fadi
yace,sam batayi kama da mai ciki ba, ya qosa
yaga cikin nata ya tsufa, tafiyan kasaita ta masu
ciki tana birge shi.
Tafiyan masu ciki tana birge shi,amma ita sai
qirjinta ya ciko yayi dam, sannan hips dinta suka
qara fitowa.wata sha'awa ce ta motsa mishi
dama yayi mssng dinta da yawa yana so wasu
halittunta.na dawo yace to xauna ki xuba min,ya
kalmashe kan bapet nima na xauna ina xuba misii
na tuna nace yauwa em ina turaren? yace ok
yana gidanmu can gwamna rd, kin san can na
fara sauka na manta da shi,yayi murmushi xa
muje ki dauko ai ko?na kalle shi a raina nace shi
wannan ya umar din ya cika wayau, a fili ko sai
nace a'a in kaje ka kawo min. bayan sallar isha
nayi mugun ci sbd miyar gandar tayi min dadi
sosai ga kuma xobon da nafisa ta hada ina ci ina
musu dry da gwalo jamila tace Allah yasa yau
mijinki ya kwashe ki mu huta.nafisa tace Allah
yasa su wuce abujan tare xaki be, waya ta ta
soma ringin na dauka ya umar ne nace slm
alkm,ya amsa da kema amincin Allah ya tabbata
agare ki, asmy shin kina buqatar turaranki? nace
eh yace ki same ni nan qofar gida cikin mota, na
tashi ina neman mayafi,momy tace ina xaki?
Nace ya umar ne xai bani saqo,nafisa tace ba
wani ke dai sai da safe. jamila tace ana san miji
amma ana kai wa kasuwa, tsaki kurun na musu
na wuce, momy ko dry take mana,xaune a
maxaunin drb yace shigo mana ina shiga yaja
mota muka soma tfy nace ina xamu jene? yace
gidanmu ki dauko yanxu nan xan dawo dake,
nace ban fa yi shirin fita ba,yace ai ba wani
baqon guri xamu je ba gidan mu xamu je shiru na
mashi.bayan mun tsaya ina qoqarin fitowa shi ya
fito ya rufe gefen xamanshi ya xagayo sai kurum
naji anyi sama dani haka ya rungume ni tamkar
ya rumgume jaririya, da qafa ya rufe motar
sannan yayi sama dani laf nani a jikinshi ina
shaqar qamshin turaranshi.idanuna a lunshe dan
tsabar mugunta irinta ya umar sah jina nayi cikin
bahon wanka,cike dam da ruwa da sauri na tashi
xaune tare dayin wata shegiyan ajiyar xuciya,shi
kam dry yake min na saka mishi kuka,wanda ni
kaina na san na tabara ne.ya soma lallashina wai
bari yayi min wankan,banxa na masa ya cuda ni
ya wanke tamkar jaririya.
Ya nado ni cikin tawul, ina mamakin ya umar in
yana soyayya tamkar a india shi yasa wani lkcn
ban sani ba nake biye masa sai daga baya inxo
ina jin haushin kaina. kan gadon shi ya sauke ni
sannan ya warware tawul din ya barni wai xai
shafa min mai,daga shafa man ne ya xarce da
min kalolin wasannin shi masu sakani cikin
shagala, kada kuga laifina bansan yanda xan
fassara maku ya umar ba,bangaran soyayyar
auratayya, da ace ina san ya umar to dana ce
babu wanda ya kaini dace kaf fadin duniyar nan,
yana sani in mance so ko qi in mance k6ai da
kowa nakan dauka duniyar daga ni sai shi aka
halitta,lkcn da natsuwa taxo mana sai ma rinqa
jin takaicin kaina ni da ba sanshi nake yi ba me
yasa xan ringa biye mashi, shin na manta
wulaqanchn da ya min can baya? shiko dadi tare
da farin ciki ne ya cika xuciyasa yariyan tana da
bahwar ni'imar da ba kowace mace ce take dashi
ba, sannan ya san dama mace mai yaron ciki
abin bukatar kowane namiji ce sbd wasu dalilai,
cyan haka tana gamsar dashi.
Da asubahi kam naji haushi sosai sbd yaji qe min
kayana gashi ba dakina muke ba babu kayana
kuma a dakin shi jallabiyarsa mai gajeran hannu
ya bani gashi ta min tsawo cikinta nayi sallah ina
ta fushin me yasa na biye mashi nan ya kuma
lallaba ni har da cewa in tausaya mishi da fa na
haihu shi kenan, xai bani takarda, nan dai nuka
sake lulawa ,da safe anty ta aiko mana da break
nace ya kamata mu soma shirin komawa gidansu
momy tunda nifa banma xo da shirin kwana ba,
yanxu ma kunyar momy xanji, yace menene na jin
kunya bayan gidanki kika xo kuma tare da mijinki
kike,nace mijina fa kace mijin sharadi? yace ok
yes haka ne,amma yanxun sai yamma xan tafi na
fasa tafiya da wuri shiru na mishi domin ni kaina
ban gaji dajin dadin qamshinshi ba.yinin raran na
murwu gun ya umar dan haka na gaji iya gajiya
bayan bacci babu abin da nake sanyi.nan na
matsa mashi ya maidani gidan su momy,muka
shirya muka fito.na shiga gidan fuska daure ni a
dole ban so na bishi ba.jamila tana xaune qofar
momy tana yanka kubewa.
Nafisa tanayi ma anty amrya kalaba, dukansu sai
nagasun kalle ni sun kuma kalli junansu sun
kwashe da dariya har anty na tsaya raina ya kara
baci ina harara jamila sallamar ya umar sai
sauka nutsu illa anty dake ta dariyart, shima
wata 'yar dariya yayi tare da nuna ni da baki ina
waigawa sai ya wayance sannan ya dake, na dubi
jamilaa cike da masifa nace me kuka gani na
dariya a jikina? jamila tace dole ne muyi miki
dariya amma salon takusoyayyar tana birge mu,
bakin ciki ne yasani saka kuka musammanganin
yana su duka suka saka dariya da jamila ta gama
mgn na shige daknmomy da kuka da sauri ta fito
daga bedroom a rungumeni, lfy 'yar gidan momy
sallama da kuka? cikin shesshekar kuka nace ba
su ba suke mindarya, ta kamo hannuna zo inji
waye kemiki dariya? sanda muka fito sai daryar
sukeyi da lama mgn ta suke yi.momy tace dariyr
me kuke mata kun sanillar dariya kuwa?jamila
tace momy da. wasa mukemata fa,mu dariyr da
mukeyi tace baa son yayanmu amma in yayi
wayahar wani canza murya takeyi, dagazanje in
amso sako shikenan shiru, sai yanxunzata shigo
tana mana fushi? suka sake kwashewa da dariya,
nace dukabin da kikeji zaki same shi jamila ai ga
ya umar din nan ki tambayeshi in son shi nake ba
dan ya matsa min ba wlh bazan bishiba har
zakigaya min mgn momy. ta fara ma jamila fada,
ya umar yace tokuina ruwanku ne? ance
mukutana sona ne? yna mgn yanamurmushi
sumasai guntse dariya sukeyi na
[7:46PM, 17/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu 2----11
Ance mukutana sona ne? yna mgn yana
murmushi sumasai guntse dariya sukeyi na kula
ma sun maida ni wawaiya donhaka sai na wuce
daki ina kuka momy ta shgo tana lallashina ,
gado na haye nata fushina har bacci ya kwashe
ni ban sanlkcn dayaa tafi ba tun dani sai
damagrib sannanmomy ta tasheni na farka naga
turare a gefen amma dana sunsunabaya wancan
kamshin dana sani,bayan isha'I na kira shi toilet
na shige sbd su jamila 'yan sa ido nace mishi shi
ne zaka ajemin wani turare ba wanda nace bako?
yace to wanne kike so? na ce irin wabda kake
sawa nace fa yace ai shi ne na aje miki nace
bashi bane daka sanbaza kabani ba dabakamin
alkawarin ba, na kashe wayr ya kira haba asmu
bbu binda zaki nema gurna inki baki wlh wannan
ne turaren danake sawaki yarda nace shi kenan
yace kn yarda shine? nace eh sai anjima na
kashe ina fadinbakasonbani kawai zakace shi ne.
ina fitowa nafsa tacemanya, yanzun kuma wayar
ma a boye akeyi? dama haushinsu nakeji gashi t
kara tsokanata, nace duk abinda kike ji in jin shi
nima zamuyi bala'I inbaku fita harkata ba, nafisa
tace mu ma ki fitaharkarmu ki daina sa momy
tana samu aiki tsaki naja
Sannan na bangaje tana wuce, tayi dariya tace n
son yayanmu ammaanki yarda sonshiake yi, cikin
kwanakin ban da fushi bna komai, kafin daga
baya na huce.wannan kron satinshi 3 snnan yazo,
kila tun subahi ya fto don na farka dagabacci ne
naganshi yace da yamma zaikoma,tare dani zai
tafi tunda naji sauki nace ba zanje ba momy tace
inyi hkr in bi shi sai zanzo hihuwa sannan gama
bikin jamila nn da wata 3 ,haka nan na hkr na
soma shiri su ko su jamila is tsiya sukemin wai
dama momy ta daina bata bakinta dama sunji
inacewa da zarn mijina yazo binshi zanyi, banza
nayi musu sbd inji da takura min ma da batun tfy
da ya umar yayi, munyi sallama dasu mama
saurn dangi da nce banmusu sallamaba, saiya
samin 2000 cikin waya wai na ma kowa
sallama,abba ya shgo momy take gaya mishi zan
bi mijina nan fa ya ringa wa ya umar kashedi a
kula dani kada ya barni ba"a bani abin da nakeso
ba, sbd abba kullum zai fita sai ya tambaye ni me
nakeso? me zanci yazo min dshi? duk abin da
nakeso sai naci shi ya hau minute ki. turaren ya
umar shi ne kawai matsala ta yanzun son shi
nake ammana rasa yaumr yaki y bani.
Ina jin nty tana yima ya umar gargadinkad ya
matsa min, dominhakan za iya kawozubewar
cikin,n tuna rhma tace min snd tayi bari dr yace
sbd yawan kusantar ta da mijinta keyi ne ya
kawo zubewar cikin, a raina yandabanason cikin
nan dama zai zube da naji dadi sanda muka isa
gidnbabu kowa, na bude kofata na shga da
addu'a bayanna danyishare share da goge goge
nayiwanka da alwala hakazamna yaci gaba da tfy
a gidanyaumar ina zuwaskul. farida sune suka
gama yanxun. harkar kasuwanci yana bunkasa
harma tanason ya umar yabart ta rnga xuwa
dubai saro kayashi kam yace ya yarda da ita
yasan Allah ne mai tsarewa,amma yasn xatakula
dakanta, sbd tsoron Allahnta, sannan zai kara
matajari . zuwan farko tare da ahj jamlu sukaje,
sida suk gamahlewarsu satun ta 3 snnan yajibgo
matakaya ta dawo kayanyaranajarira tajibgo
waiya sya , jki na rawa ya biya tare da zuga mata
albarka shi sarkin son yara.
Bikin jamila ya matso lkcn cikina wata 6 ya fito
ga cikin kato haushin ckinnakeji sbd hanani
baccinda yake yi ga kafafuna duk sun kumbura
kayan sun min kadan. bubuwan da ada nake son
su yanzun duk bana sonsu. kamar su danwake,
dudu madara da zuma da dai sauransu yanxun
sai kamshin makiyana ya umar shi na fiso wta
rigima ta ciki ashe turaren daya bani gashe shi
neturaran a haka sai jikin shi d wannan damar
shikuma yake samuna a cikin duk rana kun
girkina, yjuy ni yanda ranshi ke so , ya kashe ni
da soyayyarshi gefega kamshinshida nakeso fiye
da komai. maltina bin shan ya umar ko yaushe
yanxun nima tazamemin abin sha safe da rana.
farida ko harkar kasuwancinta yasa bata cika
zama a 9jaba wannan wta dama ceta hutawa da
abokan harkarta. ya umar ya shgo ya sameni
zaune turus a bakin gado yace a'a har yanxun
baki shirybgashi harfarda ta dawo ta shiry.na
dubi kayana cike da takaci sai hawaye na soma
kuka, ya rude, lfy asmy ya taso ya tsugunn a
gabana nace cikin kuka yanxun duba ka gani ji ba
kayana kowanne yayi kadan da wane kay
Wani kaya zanje kenan? ku tafi na fasa zuwa ya
kunshe dariyar dakeson fitowa yasan inyayi ta ya
tokano rigima,sabuwa yace kidansamu wani ki
saka in yso da munje saiku shiga kasuwa da anty
ki siyo zannuwa miki wasu, nace ni bazan iya
zuwa kasuwa ba wannan cikin ne zai bar mutum
zuwa kasuwa?yce to ni zanbar komai inje in
kasuwar na saka jallabiya sai kayan kwalliya. ana
saran kwana 2 zamu kadunan faridace a gaba ya
umar ke jan motor ina jin su suna hirar cikin tana
cewa ya ddace y bata duk babyn dana haifako?
yace sosai ma ai danki ne ko 'yarki tace Allah
yasa a haifamin 'ya mace mai kma da kai , mu
gani wani suna ma zan sa mata? ta daga kai
alamar tunani, can tace yauwa zansa mata ikram,
inko na mijine insa mishi ikra'a, yace nafison
fatima inko namiji ne muhd, haka suke ta zancen
su inajin su, don tani dama zai cire cikin ya bata
yanxun da nayi farin ciki burina ya sakeni, muna
isowa da kyar na fito daga motar dama idan na
zauna na dade haka kafata ke kumbura,kuma
tashisai da dabara, da tamakon ya umar na fito
daga mota muka shiga kowa sai sannu yake min.
A tsakar daki na zauna na mike rashe rashe. mun
gama cin abinci na watsa ruwa sannan nayi
sallar azahar da la'asar. su shem'u da hadiza su
rahma suka shigo kowa sanye da ankon lunching
nace ina nawa ko baku dinka min ba? rahma tace
mun isa maman 2,wane mu,na bata rai nace kada
kimin mugunfata rahma biyun lfy? jamia ta shigo
tace yawwa antyna ga kayanki da fatan kinzo da
direbanki muna son yin amfani da motarki nace
ya umar ya kawo mu fa. banzo da direba ba, na
tash insaka kaya amma kaya sunki shigata da
kyar siket dinya shiga amma riga taki bansan
sanda na saka kuka ba sbd takaici na zauna
bakin gado. su jamila da farko suna min dariya
amma ganin abin nawa da gaske ne sai suka kra
momy take ta saka gyalenta ta amshi kayan ta
fita dasu takai ma teloli tana tsaye aka bude su
ba laifi tunda sun shiga amma sun matse ni haka
nan dai na daure daga gurin lunchingnace ya
usman dayaje daukar rahma yakaini gidnmu
gwamna road, sbd gadajan nan na su momy dana
su mama dam yake da baki banyi mamakin ganin
gida ta ciki a bude ba sbd
Sbd nasan ya umar yana gidan, na hau sama duk
daba son ya umar nake ba,naji zafin yanda na
same su cikn gidan da ya umar kekira nawa shi
da faridarshi suna minsoyayya cikin falosun
shagala da shafar juna dogon tsaki danaja ne
yasa suka dube ni na shige dak na ina zama
bakingado ya shigo meyasa bakice min zaki
zonan in zo in dauko ki ba? na dube shi gefen ido
danme zance kazo ka dauke ni kana tare da
matarka? na ci gaba, ba zaka tuna dani ba irin
wannan lkcn ban damu daka tuna dani kokada ka
tuna dani ba domin ba kai ne a gabanaba, burina
in rabu da wannan kaddararran cikin inhuta. ya
zauna kusa dani ko dai kina kisihina ne? nayi
murmushin takaici kishin w? na nunashi kishinka?
na juya na kwanta tare da fadin abinda kakeso
shi zakayi kishi ni ka sani ban sonka da safe ban
sonka, da rana haka da dddare baxan soka bane.
ka sanini da kai ba zamuso juna ba domin tun
farko in harakace ki ba zai taba zama so ba kaje
kayi nazari ya kara matsowa kusa dani tare da
tursasa murya kinyi kuskure asmy so yna zamaki
tamkar yanda ki ke rikidewa ya zama so, na gani
akan kaina domin ada naki ki asma'u amma a
yanzun ya matso da bakinshi cikin kunnena,you
are the one I love, Allah shine shaida ta yanzun
ne nasan meneneso, koda baso nayi ba,ya mike
zaki yarda nan gaba ya fita. farida ta koma
mazauninta cikin sauri daga leken da takeyi taso
taji menene ya umar ya gaya ma asma'u cikin
kunne?
Akwati guda haka ya umar ya ciko min da
atamfofi,shaddoji da material suka kaima tela
daga buba sai play da xani aka min sauran anko
din ma duk manyan dinki akai min. ya umar xasu
tafi da faridanshi washe garin daurin aure, dama
yace ni inyi sati 2. ya kira momy falan abba
sannan ya kira ni cikin waya, na same su yace
ma momy kingan ta nan ta qi muje asibiti su yi
mata awo dana mata magana sai ta saka min
kuka, ga kumburin da take yi,na rasa yanda xanyi
da ita gata nan xan barta sai ki kaita asibiti,ya
ciro rafar yan dari biyar guda biyu gashi nan duk
yanda akayh momy kin min waya, momy ta dauki
kudin sannan tace shi kenan Allah ya kiyaye
hanya ina faridar? yace tana dakin anty,momy ta
fita nima na miqe xan fita ya kamo ni ya saka a
jikinshi yace haba asmy ki bari muyi sallama da
bebyna mana. nace daka sani tun kafin inxo kd
ka gayamin cewa in mun xo xanga doctor
mana,ka sani inhar ka gaya min baxan xoba, ka
dinga tunawa sharadinka babu tursarawa, yace
haka ne husna amma dan lfyrki da beby xaki
asibiti
Ke matsalarki daya ce baki san allura,tuncan
abuja nace baxan bari a miki allura ba kinqi
yarda dani na cire jikina daga nashi nace har
abada baxan yarda da kai ba, ka tuna har qofar
gidanmu ka dauke ni da sunan xan gwada
takalmi ka kaini asibiti suka caka min allura da
nufin xa amin gwajin HIV,ni xa ama gwajin HIV
ka cuce ni, jikin ya umar yayi sanyi ya durqusa
gabana gwiwa 2 yace ba kya yfy ne asma'u? ki
xama daga cikin masu yfy ga yan uwansu a yayin
da aka bata musu na sani na cuce ki ni mijinki ne
amma kalleni gwiwa 2 aqasa ki yafe min ina so ki
sani inna tuna abubuwan dana miki ina jin
haushin kaina nasan laifukan dana makh ne ya
hana ki sona, na kuma shaida ki na da haquri. na
dube shi ya ban tausayi amma na dake na ce xan
yafe makd ya umar amma sai randa ka sake ni
na fita na barshi a gun.tsakar dare ya umar ya
kasa runtsawa yanda ya tsani ciwo haka ya tsani
asma-u ta furta kalmar saki, kana ya tsani ya
xauna da laifin wani kanshi domin bai san ranar
mutuwanra ba,
Sakin asma'u baya cikin tsarin shi wayo kurum
yake mata saidai yanxun yana ganin dole ne ya
sake ta ko dan ta yafe mishi laifukanshi, wata
xuciyar tace yaya xaka yi da santa? ya miqe yana
xaga dakin ya dubi farida dake ta faman shirga
bacci, ya sani yana san farida so na yarda da
ganin girma da kuma mutunci amma san asma'u
daban ne a hankali ya shige shi kuma har yau
yana shigarshi kadan ya rage ya gama xagaye
dukkan jikin shi ya xauna bakin gado tare da
furxar da xaxxafan huci,sai yace menene maganin
xuciyarshi can sai tabi amsa da cewa Allah,da
sauri ya miqe tare da dauro alwala nan ya duqufa
neman mafita gun Allah.Diamand hospital muka
je da momy sunmin awo tare da dubani sunce
baby lfy amma jininta ne ya dan hau, wannan
kuwa ba wata matsala ce mai xafi ba yawancin
masu ciki kan sama haka

Please Login or Register in order to submit comment