Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anti kudi ta sai
duk abin da ya dace, cikin farin ciki abba ya
samai albarka.
Abba yace dama nasan baxaka watsamin qasa a
ido ba, yarinyar ma ta gida ce, asma'u ce yar
gidan babanka alhj ahmad, gabanshi ya fadi da
sauri ya dubi abba, abba ya ce yaya? ya umar
yace a'a ina mamakin ta isa aure ne? abba yace
qwararai shekara sha biyar ina laifi? takaici ya
cika ya umar amma babu dama ya nuna, yace
a'a babu laifi amma inaga gobe xan koma sad
muna da training jibi. abba yace to kaje ku gana
da matarka sannan abokanka su xama wakilanka
anandin, yace shi kenan abba xan yi duka, daga
nan dakin momy ya wuce ya sa mata rigima shifa
baya san wannan yarinyar yar iska ce, momy tace
kai na gari ne? yace Allah ya sani ni momy ina
qoqarin kiyaye dokokin ubangijina, momy tace to
kasa ma ranka ka auri mata ta qwarai, shiru yayi
yana mamakin yanda su momy da abba basa
kishin dansu. sunfa san halin yarinyar nan,amma
sun nace,itama cewa tayi yaje ya gana dani
sannan tace yasa abokanshi cikh kan ya tafi. ba
ya iya ja da iyayanshi dan haka yace to momy,
amma Allah yarinyar nan batada kunya.
Ya umar yace kinsan fa ta taba watsamin ruwan
datti? momy tace ai yarinya ce quruciya ke
damunta, yace haka xanje ina fama da ita? tace
ai xata daina ba xama tayi ba tunda taga daga
kai sai ita, ya fita ranshi bace,kofar gida ya tsaya
ya kira aminu, amininshi ne yace aminu ina
jiranka nan kofan gidanmu, aminu yace captain
umar kana kd kenan? yace eh dan allah kaxo ina
cikin damuwa. kafin xuwan aminu sai ga ya aliyu
yayi mamakin ganin ya umar dan ya kan kira shi
ya sanar da shi xuwanshi, yace yaya yanxun
kaxo? ya umar yace bari kaidai aliyu sai addu'a
ba dadi ya kawo niba, amma shiga gun anty ka
ce ta rbt abubuwan da ake so game da lefe da
sauran abubuwa sai kaje ka cire kudi kuje
kasuwa da anty, yace auran wa xa ayi? yace
shiga kaji gun anty ko momy? aisha ta sameshi
tsaye ta rusuna ta gaidashi sannan tace mama
tace kaxo,yace to kice gani nan xuwa, tun dama
shi dan dakin mama ne girma ne da kuma yawon
aiki ya sa ya rage shiga gunta.ya shiga gefen
mama ya nufa ya same ta xaune duk bata cikin
walwala.
Yayi sallama tace shigo faruk, ya umar ya shiga
tare da fadin mama kina ciki? tace uhum ina ciki
faruk, dama ina tunanin yanda zan ganka sai
aina'u tace minute gka. waje shine nace Aisha ta
kiramin kai, yace jiya nazo abba ne ya kira ni kan
zancen aure, tace nima neman da nake ma kaa
kenan , shawara zan baka kar ka amince da
zancen auran nan, don yarinyar nan llaataccya ce,
cikin mamaki ya dubi mama tace kana mamaki
ne? nasan ba xan boye gaskiya ba in goyi bayan
karya, ji nayi yana jin kunyar mama domin mace
ce mai mutunci ba zai ya nuna bayason jininta a
gabanta ba, domn ba zai manta lbrn da momy
take bashiba takan ce haihuwrka kaawai nayi
amma mama itace ta rene ka taci kashi da
fitsarinka, lokacin bata haifi abubakar ba. haka
sanda ta haifi abubakar din ma sai ta'aje shi ta
dauke ka , shi kansa sanda ya taso yasan shi
dan gidan mama ne sai shi ne ma yasa mata
mama ya bita, tuna wannan da yayi shine yasa
ya kara sadda kai kasa sannan yace mama ai
yarinyar nan kanwata ce, kada ki damu mama
tace kaima baza ka bani goyon baya ba? na
sankaa faruk tund ka taso baka da mugun hali ita
fa? ga rshin kunya a gunta kwani fatima tace min
har ruwa ta watsa maka? yace ai wannan ya
wuce mama kada ki damu, yanxu ina take dama
dan ita nazo in hada ta da abokaina,ni muna da
training jibi gobe znbi jirgin safe ne,
Shiru mama tayi harga Allah bata so haka ba, don
tasan ko itace ce abubakar zai auro mai irin halin
asma'u baza ta yarda ba, kudi ya zube mata
sannan ya fita, tace ai ni daka barsu faruk tunda
momyn ka ta hana ka yarda da batuna, yana fita
yaga aminu yazo sun gaisa sama sama sannan
ya shiga rattafama aminu halin da yake ciki
saidai bai sanar dashi yawon da asma'u keyiba,
ya dai ce mishi bata da kunya, kuma yarinya ce
karama. amma ko me kenan su hadu da dare.
bayan sunyi sallama yace ta shiga gidan alhaji ta
kiramai mara kunyar gidan yana fadin haka tasan
asma'u ce, don haka saita wuce. a dakin hajiya a
same ni muna kallon tashar MBC2 tace asma'u
ya umar yana kira na dafa kirji
[1:39PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Biyu1-----10
Nayi shiru hjiya tace naje bansan me kiran ke nufi
ba, don haka yanda nake haka na fita hijabi kadai
na saka sanda naje yana waya da faridanshi ne
don naji yana cewakada ki damu farida ki sama
ranki wannan auran dashi bababu duk daya ne
zan kuma kira ki ya dan jima yana bata baki kafin
daga baya sukayi sallama, ni dai ko a jikina tunda
ban sn me ake ciki ba, yamin rin kallon dana
tsana, tamkar yaga kashi, yace ke karama jeki
canza kaya ba zaki shigar minute mota da datti
ba, ban fahimce shi ba, don haka nace ni ban
gane ba, yace ai ba zaki gane ba ya shiga
gidansu nima na wuce gida,
har naje daknmu na kwanta sai kuma nayi wani
tunani kadanayi laifi ni 'yar sarkin laifi don haka
sai naje na samu mama, nace ya umar yacena
canja kaya na same shi, ni kuma ban gane nufin
shi ba, harara ta sakar min sannan tace ai da
wanda zakuje party ne baza ki zo ki gayanba,jin
haka yasa na fita. shadda na saka riga da siket
green , na saci hijabin hadiza na saka,saboda yafi
nawatunda ni duk cikn hijabaina babu dogo. dga
cikin zauran gidan mu ina kallonshi yana waya, a
raina nace Allah mutumin nan mugu ne ,jibi
yanda yake wani shan kamshi yana waya ma
kenan shiyasa na tsane shina tsaya a kofar
gidanmu ,yana gamawa ya dube ni cikin hada rai
a raina nace donka ganni da kananan kaya ai ba
wani ka gnni ba, na isa gurin yana kokarin bude
mota ya shiga, sai ga abba ya fadada murmushi
ganinmu tare yace sai ina haka umar?
yace zan kaita ne abba ta gwada wasu takalma ,
abba yace to Allah ya shi muku albarka , gabana
ya fadi na dai durkusa na gaida abba ya amsa
sannan ya isa gurin motarshi ni kam kaina ya
daure da yawa, ya umar ya shiga motarshi nima
na kama gaban xan shiga yace karki yarda ki
shigo min nan ni sa'an ki ne shiga baya, na shiga
na zauna, Allah ba don ina tunanin kada na koma
gida inyi laifi ba, Allah bazan bishi ba, don dai ni
a gidan mu bani da 'yanci yin abu komai
kankartar sa, shi kenan nayi laifi, don kuturun
wulakanci muna cikin tafiya sai cemin nayi maza
in saukar mishi daga kan seat in tsugunna kada
agan mu tare sunan shi ya baci, raina yayi
mugun baci har kwalla suka soma zubomin haka
na tsugunna gurin aje kafa.
Bansan ina muke tafya ba saidai naji ya kira
farida, suna hirar soyayya, a raina nace har na
tausaya miki ko wacece wannan faridar baki san
shi bane shiyas, aini dan auri y umar gara na
mutu b mji, can naji ya kira doctor hassan yana
fada mishi gashi nan zuwa koda mottar ta tsaya
ina nn inda nake nafi minti 30 kafin naji an bude
min kofar motr yace fto daa Allah I ni wannan sai
na kaita wurin car wsh, ni dai na fito kafafuna
duk sunyi tsaami yace wuce muje sai kace ya
Allah tasha wani zunbulelen hijabi, fir'auna a zuci
musa a baki, ban dai tanka ba yayi gaba na bishi
a rana nace to wanene aka kwantar a nan
asibitin,, dan naga an rubuta (dirman hospital).
office din da muka zauna ba kowa, can lkitan ya
shigo wani dan dogo fari, yace ku shigo? ya umar
yace eh gatanan ya nuna ni ina zaune can gefe
likitan ya dubeni ya jima yana kallona tamkar mai
nazari, har dai na gaji na mishi kallo da yake nufn
kallon fa? yako gane sai yace captain umar
kanwar nan taka ta cika tsiwa, ya umar cikin
daurewar fuska yacekayi abin da muka zo y , ai
da'a tsiwa ta tsaya da sauk, na dubi ya umar
abin shi ya soma isata, ya ballo min harara na
sunkuyar da ka, in ya hade rannan tamkar zaki
nake ganinshi. likita yace to ina zuwa nidai
sauraron abin da za'ayi , fita likitan yayi bai dade
ba ya dawo dauke da allura da sauran tarkace,
ya tsaya kana kawo hannunki? ni uwar tsoron
allura don da amin allura gara na mutu da
ciwona, haka nakan fadi in bani da lfy, ance muje
asibiti amma yau gashi dan kuturun wulakanci lfy
ta lau an sako ni a mota gurn sa kafa za'a min
allura, tsawa ya umar ya min ki ba da hannu
akace, nace to ni me za'a min ? kai tsaye ya
umar yace gwajin kanjamau, na mike tsye da
sauri saboda sai naji kamar nima a nan za'a sa
min ciwon.
ya umar ya kuma daka min tsawa ina zaki? na
soma kuma ni bani da koma ban karasa ba naji
saukar mari, tuni na nutsu. likitan yace bi ta a
sannu , ya kama hannuna yasa allura ya cako
jinina, suka fa tare suka barni ina ta faman kuka,
a raina nace kila ma sbd ya tsaneni ne shine zai
kala min sharrin cuta,kusa awa daya ya umar ya
fara shigowa yace in naji kin fada ma wani inda
mukazo, Allah sai kin gane kuranki, ni dai ban
tanka ba sanda likitan yazo ya umar yana waya,
don haka ya shiga 'yan rubuce rubuce bayan ya
gama lkitan yace captain munyi gwaje gwaje
kamar yanda kace bamu samu cuta ko daya
ba,wato captan yarinyar tana da lfy sosai, a
wannan zamanin damuke ciki samun yarinya ko
ince a dari da kyar a samu goma, don haka bata
da kanjamau kuma bata da sauran kananan
ciwuka. y umar ya harare ni, wuce ki zauna inda
kika zauna dazun, Allah ya taimake ki ya jima
sannan ya fito ina da gangan yayi ta wani shegen
gudu sai bigewa nakeyi da kujeru, naji mun tsaya
sannan fa ya leko yace in fitar masa daga mota,
daknmu na shige na kwanta kan gado na
darsawa a raina bani da babbanmakiyi nan
duniya kamarya umar ina ruwanshi dani don bin
diddigi zai kaini gwajin kanjamau? a fili nace
Allah ya isa. sam koda wasa ban sani wai ana
shirin aurena bane , har sauran kwana hudu
amma duk 'yan gdanmu da yaran sun sani sai dai
ance kar su gayamin, don kar mu gudu da suraj ,
basu san yau rabona da suraj din ba tun ranar
partyn nan.
yau dinnan rahma tazo muna hira ina bata lbrn
musanyar jakar da mukay da samir ban gama
bamukaji sallama, ni dama ina daga ciki gurin da
muke sallah kan sallayan ma nake. rahma tana
daga bakin kofa tana kallon waje sanaj tace ka!
akwatunan wanene wannan? waye zaiy aure a
gidanku? nace nan gidan kuwa? tace ga
akwatuna gud 6 rabin dozin? na mike na leka na
koma na zauna hadi da tabe baki nace oho ,kila
nasu anty aina ne kinsan ni yanxun a gidan nan
agola ma ya fini daraka, komai sai dai inga anayi
bana sani.rahma tace ba haka bane Allah suna
sonki, sunf son suga kin canza ne nnace ba wani
so dai ai sha'ani tsan ce kawai tunda in dan kaya
ne tun yaushe na daina sawa? amma ko da safen
nan sai da ya usama ya rarrankwashe ni sai kace
nayi mishi wni laif, wai fa don kawai munyi karo,
tace ni kin tuna min sai ga ya usman a gidanmu
jiya wai yazo mu gaisa ,ni sai naga tuntuni kamar
zaice yana sona nace tab ai wlh ki ka yarda kika
auri ya usman shi kenan ni da ke danba zanje
gidanshi ba, tace kai don Allag sbd me? nace allai
ashe sonshi kikeyi? tace bai dace ba? naja tsaki.
canja min lbr ni yan gidannan saida na kalle su
kawai. rahma tace har mamaki kike bani, yayama
za'a ce 'yan gidanku sanan su tsane ki ko ka
kuma suki ki? nace duk abin da akemin a gidan
nan haka ke miki a gidanku? kafin ta bani amsa
Aisha tayi sallama muka amsa , tace anty asma'u
kije inji wani mutum. nace kn san shi? tace a'a
nayi shiru can nace ba suraj bane? tace a'a nace
jeki. ce wanene? jim kadan ta dawoyace sako zai
baki na mike rahma zo muje tace sai kin dwo
nace don Allah ke da zo muje ta mike muka fita.
yana tsaye jikn gidanmu sanye da jeans da shirt
ban gane shi ba amma saimuka karasa, muka
gaishe shinace kine kake nema na? yace eh sai
na ke gann kamar na sansh, yace kn sann? nay
dan murmushi sannan nace eh to na dai ganinna
taba ganinka yace ok to n abokin captan ne nace
wanene kuma cptan yace umr,nay wani bala'in
hada rai, yanzu na gane shi shine wanda na
watsa ma ya umar ruwa suna tare,cikinmasifa
nace to lfy malam? yace kwantar da hankalin ki ,
sunana Al-amin nazo ne nagana da kawayanki
don musan shirunku da abubuwan da zakuy,naja
tsakinace kayi kuskure don ban gane nufinka ba,
zo muje rahma nayi gaba. yace da rahma, zo ke
,tace Asma'u zo kiji nayi tafiyata, yace ke
kawarta ce? rahma taceeh yace maganan bikinta
kinsan angon baya nan. shine nazo naji
bukatunku, kan rahma ya daure tace auran
asma'u dawa to? yace da ya umar baki sani ba?
rahma tace itama banyi zaton ta sani ba, yace
shi kenan yanxu kije ku rubuto abubuwan da kuke
bukata, tace anyaba kuskure bane? malam ina ga
ba asma'un gidan nan bace, yace zan dai dawo
anjiman. ni kam ina shiga cikin gdan naci karo da
su anty amaryar gidan su ya umar ita da
wa'yansu mata sai naji tace yauwa gama
amaryar nan, ta nuna ni na kalle su cikin rashn
fahimta, su kam sai kallona suke suna fadin
tubarakallah masha Allah, gata yarnyar 'yar
karama zai more aure,na wuce ni fa abubuwan da
suke faruwa 'yan kwanakinnan suna daure min
kai. na shiga cikn dakin umma na jiyo
hayaniyarsu ina isa naga duk daukacin 'yn
gidanmu ne illa mama. kadai ce bata gurin.
[1:41PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: uska Biyu1----11
Duk suna kallon kayan a akwatina shiga ina fadin
kayan wanene? duk suka duben, umma tace
kayan ki ne shigo ki gani. na dafa kirji naceni?
tace kwarai. anty aina'u tace wasa ake dake da
za'ayi miki karya? nace to wa zan aura? shema'u
cikin doki tace kinji dadinki yaya umar fa soja kai
dama nce? ya umar fa kika ce ? fatma tace ki
godema Allah kike wani ya umar,nace na shiga 3
ni asma'u , na mutu. fatima tace shegiya a irin
wannan halinnaki ma ya rufa miki asiri da gudu
na nufi daknmama tanakrga kudi na shiga a
firgice nace mama wa ni za'ama aure da da yaya
umar? don Allah mama banason shi ki taimake ni,
tsawa ta daka minute yi min shiru har kna wani
baki son shi an gaya miki shima sonki yke? to
bari kji rokonshi akayi ya aure ki dan ma kada
kije kina daga mishi hanci ki dube shi da kyauba
ajinki bane. mamkn mama ya cikani,nasha zata a
zuciya nake magana ashe ba hka bane, nace anya
mama ku ne ku ka haife ni? saukar mari naji tare
da fadn , tsinto ki mukayi, da gudu na fita dama
ni uwar kwakwazo gashi ta same ni gurin ido , ihu
na saka ba kukan mar ba sai na kin auran nan
yau kam na kara yarda ba'a kaunata,ba'a sona
na shiga 3!! haka nake fada da gudu 'yan gidan
suka fito daga falon umma, hajiya da umma suka
kama ni.
Rahma ce me tambayataa rude menene asma'u?
asma'u meya faru? umma tace kinji halinki aike
asma'u sai kwakwazon tsiya baza ki fadi magana
ba, cikin kuka nace don Allah umma ku taimako
banason ya umar mugu ne Allah gara k kashe ni
da kanku, anty aina'u tace dubi yar iskar yarnyar
nan zai rufa mikiasiri da wannan mugun halin
naki ya aura amma har kike fadin baki son shi
ban sanlokacin dana ke meyasa baki aura ba
za'abani, don ba'a sona ....duka suka rufeni dashi
ita daant aina'u da anti fatima , da kyar su hjy da
umma suka kwace ni, sunamusu fadan meyasa
zasu duke ni na kufce nayi waje da gudu zan fita
mama tana cewa kada ki fita gidannan,kcibis
mukayi da yaya usman,nabi ta gefenshi zan shara
da gudu ya damko ni. gidan uban wa zakije haka
sa kace mahaukaciya?nace da dai ku barni in
tafi, ya wurgoni cikin gda, mama da kanta ta
dauki ice ta shiga muka min . rahma ta rungume
ni tana kuka, mama tace matsa ko kema inmaka
miki, su hjy suka shiga ssai kuka nake . hjy tace
kin ja ma kanki duka a banza, cikin kuka nace
ba'a sona hjy wlh an tsane ni. hajya tace ba
tsana bace ke ba abin alfahari bane a gurnki?
nace haba hjy wane alfahari? dubi yanda aka bar
su anti aina'u sukayi ta karatunsu, sai ni ce za'a
ma aure kuma maimakon aban wani sai a ban ya
umar , wlh nasan kashe ni zayayi.
Hjy tace wanene mugun?Umar din?Ban bata
amsa ba na ci gaba da kukana.Rahma ma kukan
take tana bani hkr,kafin wani lkc zazza6i ya rufe
ni fuskata ta kumbura.Rahma ta ce bari taje gida
ta sanar ma Momynta,ni dai ina kudundune ban
san ma lkc ya yi nisa ba,ashe hr dare yayi.
Muryar Momyn gidn Abba na jiyo wato Maman su
Ya Umar,ta shigo suna cin abnci a barandarta da
su Umma,na ji tana cewa Hjy Saude dk naji abn d
ku kai ma Asma'u dan cin zalin a bi yarinyar da
lalama abu ya faskara,sai ku taru kuna shigarta
sai ka ce jaka?Umma ta ce to ai a gaisa tukunna
ko? Momy ta ce ba ita na zo ba, Mama ta ce
kina take sani ne yarinyar nan Umar sa'anta ne?
Ai shi aka cuta ga mugun hali yayi biyayya ya hkr
shi ne ita da zai rufamawa asiri zata ban da she
shi ana kallonta? Momy taja tsaki yanzun ina
Asma'un take? Hjy ta ce tana can dakin a nan
Momy ta same ni ina ta rawar sanyi ga fuska
suntum.
Da sauri ta fita ta samu Ya Ali ta ce ya dauko
motar Abba muje asibiti bn san asibitin da muka
je ba na dai ji ana gungura ni akan gado,allurar
da bana so yau kam na sha ta,Likitan ya ce zamu
kwana don dan karamin ruwa , sannan da safe in
ga Likitan ido Momy ce Ta kwana a guna duk d
Momy ta aiko masu Mama cewa anbani gado,sai
Mama ta ce ai ta bani mana ba ta zo ba. Da safe
Anti Amarya suka zo da Abba,ya yi fada kamar
me? Su Umma d Hjy sun same shi yana fadan ya
ce shi ne sai a samu yarinya ai mata irin wannan
duka sai ka ce jaka? Ai zanga Alhj Ahmad din
zuwa yamma Likitan ya Sallame mu muka nufo
gida, tun a hanya na ce Ma Momy ni fa wlh ba
zan koma gidanmu ba,ta ce ai nima ba zan kai ki
gidan Abba muka wuce dakin Momy muka shiga
na kwanta akan gadonta tasa Anti Salima ta dafa
min wake da hanta na danci. Da dare ta kira Ya
Umar a waya landline ta ce bn d lfy mun kwanta
a asibiti, ya ce Allah ya sawwak'e yanzu ina ina
ne? ta ce gani sai na amsa nasa a junne Momy
ta fita tana Murmushi ina dauka ya ce ai ni sun
min dai-dai,Sun ma miki kadan sai ma kin yarda
kin shigo hannuna..
Tun jiya na samu lbrn lugudan da aka miki, ki
shirya zaman uk'uba,ya kashe wayar,na koma na
kwanta kuka na saka,san da Momy ta shigo ta
same ni ina kukan ta zauna ta dago ni me ya faru
ne? Gaya min me ya ce miki? Cikin kuka na ce
Momy don Allah ki taimaka min a fasa Auran
nan,Wlh Yaya Umar ba ya kaunata don Allah
Momyna,rumgume ni tayi tana fadin "kwantar da
hnklnki Asma'u in har naga abn ba mai yiwuwa
ba ne ba zan bari ba, ke ko anyi naga da kwara
zan san yanda zan yi a kai,na ce Momy Yaya
Umar ba shiri muke yi ba,ta ce ki bar ni da shi
bana son kina mgnr kada ki kara cewa komai ba
na so kowa yana cewa ba ki da kunya.kiyi shiru
duk abin d aka ce ki ce to kin ji?Na ce to.Tunda
muka yi haka da Momy bn kuma mgn ba,sai
kuka. Rayuea kenan,yau ni Asma'u ni ce zan auri
Ya Umar mutumin da na tsana ya tsane ni,Rahma
da wasu kawayena sune Momy ta sa su samu
abokanshi lis din komai,ita ce in bar su ai raba
mugu da makami ibada ne,sun shirya Sister day
saiwalima don ni da don ta ne ni da sun bar shi.
Ana gobe da daurin aure a kayi sister day din,kin
yin wanka ma na yi sai da Momy ta sa baki ta ce
in yi wankan tunda shi ba ya garin ma,,,,
[1:42PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----12
Dakyar dai momy ta lallabani nayi wanka ba don
raina ya so ba, na danyi kwalliya amma raina a
dagule yake, haka dai ake abubwan amma ina
cikin damuwa a wajen sister day gaba daya
hankalina yayi gida kawai dan sarari nake nema
na samu mai machine ya kaini gida, Rahma ce
take ta lallaba ni akan nayi hakuri har a tashi, sai
da aka kusa tashi sanna Al-Ameen yazo shida
wasu abokansu, bayan mun gaisa
Rahma ce ta ce Munyi fushi sai yanzun hr an
gama suka ce haba dai ta ce Allah munan ni gida
zamu je ya dube ni to Amaryammu ya gaji ya?Na
sakar mishi harara ya dubi sauran abokan ya ce
kunga amarya tayi fushi ko ya matso kusa dani
ya ce kada ki damu ya kara yin kasa da Murya,
don Allah ba don ni ba kada ki bari wadannan
abokan namu su gane halin da ake ciki.sbd basu
san me yake faruwa ba.Hakan yasa na da daure
na ce ina yininku?Suka ce lfy Amarya yaya jiki?
Na ce da sauki Al-Amin ya gabatr dani
Abdulmalik,Hasim,Sani,Sale sai Muhammad, na
ce sannuku suka ce yauwa.Al-Amin ya ce me
yasa zaki hau mashin?Rahma ta ce kasan bata
jin dadi shi ne take so taje ta kwanta. ya ce to
shiga mota mu kai ku,na ce ku bar shi ai kuma
naga kun cika motar,ya ce bari wasu su sauka
haka dai dole muka shiga.
Muna isa bn jira komai ba na shige gidan Abba,
na bar su suna mgn d Rah,a.Momy tana ta
kiciniyar shigar ma d baki wadanda suka iso
yanzn nan da abinci sai ta ganni tayi turus yaya
dai 'yar gidan Momy? Na ce kaina ne ke ciwo
gajiri,ta ce tofa,ina zuwa ta shiga da abinci
dakinta ta fito,ta kira Anti Amarya ta ce bani
makullin dakin Soja (Haka take kiranshi) ta ce
Momy me za ki yi a dakin?Momy ta ce kwanciya
matarshi zata yi ni dakina cike ke ma haka,Kin
san kuma ba hayaniya take so ba,Ni ina cn ban
son ma kome akeyi ba sai dai naga Momy ta
bude kofa ta ce zo ki shiga 'yar Momy,ni dai bn
ma san dakinshi ba ne tunda ni dai wayona ban
san shi ba,daga baya nake ganinshi gwanin
Kamshi na leka bedroom din naga ashe hr d Kofa
ina zaton kofar ita ce ta 6ulla waje kusa d ta Ya
Aliyu,na kwanta kn duguwar kujera idanuna fes
suka sauka kan hotonashi sanye cikin kaki,na
tsura ma fuskarshi ido yanayin hoton ya burhe ni
hannunshi yana gefen kanshi alamar sarawa,na
sani Ya Umar yana da kyau sai dai bana son
shine na rumste ido ina tunanin zamn doya da
manja da zanyi. Na tuna jiya jin wasu kawayena
suna min murna nayi dacen mijin nunawa
sa'a,sai wata ta ce ai bana sonshi,nan suka cika
da mmk. Samira ta ce ke ko me yasa ba ki san
shi gashi mai kyau gashi Soja mai mukamn
Captain Samun irin su locky ne ke da ba kya
gurin in kin tanka to na tanka,ina jin Rahma
Momy tana cewa ina nan dakin,muna nan kwance
muna hira jife-jife hr magrib tayi munyi sallah hr
da Isha'i ai bacci ma ya soma dauka na sai
kawai naji ana fesa min nono (wato salalle)ya
Allah bakin ciki kamar me? Na saki kuka Momy
ce ta zo ta hana,ta ce su fitar mata a gida nan ta
lallashe ni bata so in wannan kukan nawa samin
jikina ya tashi,tana dakin naji Abba ya kira ta
tana fitowa naji yana ce mata nayi waya da Umar
dole yazo daurin auranshi gobe in ma zai zi ne ya
koma shi ya sani amma lallai ina son ya zo cikin
jin dadi Momy ta ce hakan yayi in baya yazo ya
tafi da matarshi,kwana nayi babu bacci addu'ata
daya ita ce Allah ya dauki raina kafin gari ya
waye a daura min aure da ya Umar,da safe
zazza6i na tashi nayi kuka na gaji.rayuwa kenan.
Misalin goma naji ana ga Ya Umar tamkar in bar
gidan haka naji nan akayi ta shigowa da
abubuwan tsaraba,su katan katan na drinks tun
daga kan ruwa C way,hr zuwa kalolin Juice
hakan ya faranta ran Momy da Abba hr Momy
take tambayarshi ya sanar a gurin aikin nashi?
Ya ce wlh Al-Amin ne ya dinga tura ma abokan
mu da message ta waya,wadanda yasan Number
dinsu,ta ce ai Aminu yaron yana kokari ko nan
yana ta hidima da ita da kawayenta.ya mike yana
cewa Anti Fa? ta ce tana can tana fama da baki
'yan Bauchi d Gombe duk sun zo ya ce bari in
rage zafin nan ya dan tsaya ganin dakinshi a
bude kamar kar ya shiga sai dai ya auno kai. lkcn
ina kwance,Rahma d Jamila kanwarshi suna
kallo.Ya tsaya yana kallonmu,ya ce kai waya ce
ku bude min daki hr d kunna min TV? Cikin in ina
Jamila ta ce Momy ce ta ce mu zo nan ta kashe
TV ta mike Rahma

Please Login or Register in order to submit comment