Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa'i-sa-i yake juyowa ya kalleni idon maryam yana kanmu duk abunda yake faruwa tana kallo, yana sauƙemu ya ciro kuɗi yabawa Maryam yace.

"Kada kuzauna da yunwa tunda kunga wuni zakuyi a school yanzuma nasan baku karyaba kuna fita lacture ɗin yanzu kuje ku karya, Maryam ta karɓa mukayi masa godiya Sai mamakin kulawarda yake bamu takeyi. Tanda tambayata abunda yake faruwa na shareta naƙi kulata har muka shiga class muna shiga lecturer yashigo hakan yasa ta sararamim.

Ƙarfe goma yafita 10:10am kuwa saiga kiran Hamma saida nasaki wani murmushi kafin nayi picking. Ina ɗauka yace.

"Baby kunci abinci?" Saida na ɗan rangwaɗarda kaina sannan nace.

" uhm-uhm yanzu muka fito"

"okay toh yanzu kuwuce cafeteria kuje kuci abinci uyum karki walaharminda kinji koh?" saina na shagwwaɓe muryata kamar yanda yake shagwaɓani nace.

"Naji Hamma yanzu zamu tafi" Ina faɗan haka maryam tajuyo ta dubeni tace.

"Tabbas biri yayi kama da mutum gama wayarnan kizo kimin filla-filla yanda zan gane" Ta cikin wayar Hamma yace.

"muje na rakaki toh" kalle-kalle na fara nace.

"Dama baka tafi bane?" dariya yayi sosai sannan yace no natafi zan rakaki a waya sannan kuma a cikin zuciyarki" bansan lokacin dana saki dariya ba maryam dake gefe tatafa hannuwanta haɗeda kama haɓa tace.

"Unbelievable Babe keda Hamma kunada abun Mamaki duk wata Hanya da zakubi kubawa mutum mamaki kunsanta" jin zata cikamin kunne ya sanya na miƙe nafara tafiya, ta ɗaga murya tana faɗin.

"bag ɗinki kuma mawa kika barwa ta ɗaga miki?"
Ban kulata ba nacigaba da tafiya ganin haka yasanya ya ɗebosu ta biyoni abaya har muka shiga ita tabiya kuɗin komai ta zaɓi abunda zamuci nikam ina kan waya har tafara jin abincin nikam cokali kawai nasaka ina caccakar abincin ko sau ɗaya bankai bakinaba ɗaga murya tayi tana faɗin.

" sai yaushe zakiji abincin wai ke?" jin haka ya sanya Hamma yayimin sallama in a ajiyewa tace.

"Wai yaushe kuka jone har haka?"
"Aide kyabari naci abinci koh?" na faɗa ina kaiwa abincin bakina.

"Amma ai yanzu ta kina waya da Hamma bakima saka shekrar cin abincinba" tafaɗa a kufule, bankulataba har saida nagama cin abincina sannan na ɗago nayi mata bayani, Tayi farin ciki sosai zan iya cewa fiyeda yanda ni nayi farin ciki. Tana dariya take faɗin.

"Haba wallh haɗuwarmu dake nayi bala'in mamakin yanda Hamma ya sauƙe girman kansa, kinsan shi baya yarda yakai kowa anguwa. Haka zanyita roƙonsa yaƙi amma kiga yanzu har makaranta yake ɗaukomu Hamma mai abun mamaki tafaɗa tana sheƙewa da dariya." Nima dariyar nayi nace.

"wallh kuma sonsa nakeyi kamar hauka"

"iyyeh ko kunyar idona bakyaji?" Hararta nayi nace.

"ke Ummi ce da zanji kunyarki?"

"Anzaga ɓoyeyyen masoyi ta bayan fage" cewar maryam. Na taɓe baki nace.

"anata Hamma wa yake tawani can kecema naga dama kin damu dashi" tayi saurin girgiza kai tace.

"ke rabani gida bai ƙoshi ba ina za'akai wani waje?"
Na tuntsire da dariya nace.

" kin dawo saiti Yarinya" alokacin na roƙeta akan kada ta faɗawa Ummi dafarko taƙi dan cewa tayi Ummi zatafi kowa farin ciki amma daga Baya ta yarda tunda itama firr taƙi saurayinta ya tura saboda tanaso saita gama karatu."

Ma'akatan cafeteria naga sun nufo wajanmu hannunsu ɗauke da box suna zuwa suka ajiye a table ɗinmu haɗeda faɗin saƙonmu, mukace musu mu bamuyi saƙoba sukace tabbas munyi dan har anyi making payment, zanyi magana maryam ta girgizamin kai sai nabari tace musu mungode sannan suka juya. Saida suka tafi ta kalleni tace.

"Ba shakka Kinsan mai wanna aikin mutumin da zai iya sakawa ayi deleting pictures ɗinmu akafar sada zumunta ta instagram kinsan zaiyi fiyeda haka. Yanzu abunda nakeso dake idan kinaso alaƙarku da Hamma tayi nisa to ki koyi ɓoye al'amura sannan kibi da wannan Ɓoyeyyen mutum a yanda yakeso ina nufin babu gardama kamar yanzu da suka kawo idan kullum zasu kawo babu jan lokaci kikarɓa, sannan Sai yanxu nayi tunanin kinyi hikima da kika hana Hamma zuwa zance dan tabbas BIBIYARKI wannan mutumin yakeyi sannan kuma bamusan WAYE SHI? ba komai zai iya aikatawa idanya ganku tare ki koyi gudun duk wata mu'amala da zata haɗaku awaje har abun ya tabbata sannan karki yarda koda sau ɗaya kuyi waya ko chat da ainihin layinki wannan ƙaramar wayar daya baki komai tanayi dan haka ki buɗe whatsapp da layin daya baki da ita sannan kar Hamma yasan wannan lamari har muga ƙarshensa" tana bayani ina murmushi dan tabbas ta samomin mafita."

Ganin lokaci yana tafiya ya sanya muka ɗauki box ɗin da bags ɗinmu muka fice saida mukaje class sannan mukayi kyauta da snacks ɗin. Sai six muka gama lactures kafin mufito Hamma yazo ɗaukanmu muna fitowa muka taras dashi yafara kaini gida sannan suka wuce."

Duk sanda mukaje wajan wani cin abinci ko wani wajan sayayya kafin na biya zan samu anbiya wasu lokutan ƙin karɓa nakeyi nafice awajan soyayyata da Hamma kuwa tananan kullum ƙaruwa takeyi.

Yau nadawo a school dake yauma nayi Yamma gabaki ɗaya yanayin Anty fadeelah da Aysha ya canjamin saida nakada haƙuri na tambayesu, Anty fadeela ne yake shaidamin Mummynsu ta kafa musu ƙahon zuƙa sai dai su tattaro su dawo, Su fasa karatun kuma su ahalin yanzu basason tafiya,
Jin wannan zancen nasu saida ya sakani a damuwa Domin nasan ba ƙaramin tashin hankali Baba zai shigaba idan suka tafi dan yayi murna da zuwansu sosai a kullum burinsa gidansa su dawo su haɗe yana murma sun fara haɗuwa yanzu yaya zaiji aransa idan akace sun sake tafiya?.

Kwana biyu kenan dagani harsu bbau wnada ya samu kwanciyar hankali sannan bamu iya faɗawa kowa ba, yauma Nadawo daga makatanta na samesu cikin tashin hankali sai kuka anty fadeelah takeyi, dafata nayi nace.

Haba anty fadeela dan Allah kidain wannan kukan in sha Allahu babu wani abunda zai faru bazaku koma ba Baba ma nasan bazai bariba" girgiza kanta tayi tace.

"ke bakisan mummynmu bane ayanda mukaji labari shi Kansa baban shakkarta yakeji kuma idan tace zatayi abu saita aikata, Marmee bazaki fahimci halinda muke cikiba kinsan yanda mukeji kuwa? Kinsa raɗaɗin tashi ba agidan mahaifi ba kuwa? Mahaifinmu ba yana raye amma muna rayuwa kamar marayu shikenan komai zai ƙara tarwatsewa akaro na biyu dukda cewa bawai ya gyaru bane amma zamanmu anan yafi mana kwanciyar hankali"
Ciked kufula Aysha tace.


"ko menene na fitowa kiyita faɗar wannan maganar? akwai wani abunda maganarki zata canja ne? Kitashi ki haɗe kayanki nasan nanda ƙwana biyu dole zatasan yanda zamuyi mukoma koda bamu koma ta daɗin raiba" cikeda tausayi na dafa Anty fadeela nace.

"nima kubani kwana biyu zanyi duk yanda zanyi na tabbatar baku koma ba in sha Allahu" aysha ta taɓe baki tace.

"Kina faɗin haka saboda bakisan Mummy ba" Anty fadeela kuma tace.

"kinyi Alƙawari?" nace.

"in sha Allahu" da sauri tayi hugging ɗina tana murna cikeda tausayinta nima naji idona yanason kawo ruwa."


Ƙarfe sha biyun dare ina cikin bacci naji wayata tayi ƙara. Sautin ƙarar yasa bazan iya haƙuri batareda na dubaba aduk lokacin danaji ƙarar saƙon hankalina yakan kiɗima har sai naga da wani irin al'amari saƙon yazo, ban kaiga buɗe idanuwa na ba Ƙarar wani saƙon ya ƙara shigowa hakan yasa natashi na zauna ya ɗauki wayar nashiga saƙon. Saƙon farko kamar Haka.

عيد مولد سعيد قلبي
أتمنى أن يملأ عيد ميلادك بلحظات ❤️

Abunda wannan saƙon yake nufi shine (Barka da zagayowar ranar haihuwa my heart May your birthday be filled with joyful moment❤️)

Sai na biyun kuma

حان الوقت

Hakan yana nufin(It's time) toh lokacin menene yayi kenan? Ganin saƙon saida ya sanya gaban yafaɗi.
Inata tunani cikin raina ko lokacin menene yayi. he's definitely up-to something.


Kamar nakira Hamma na naji ko ya isa saina haƙura. yayi tafiya zuwa Abuja gabaki ɗaya hankalina yakasa kwanciya inason naji halinda yake ciki haka na haƙura na kwanta washe gari ina tashi d asubahi naji karo da saƙonsa da yayimin nayi murmushi, sai bayan natshi da safe na kirashi harya fita wajan aiki dama yacemin yana isa sassafe zai fice saboda yagama abunda yakaishi, Kusan 1hour kenan daya cemin yana tsaye a titi motarsa ko gotawa batayi tsabar cinkoson ababen hawa, yana zaune a mota nikuma ina tayashi hira."

"Hammana" nakira sunansa yace.
"Na'am babyna" wai meyake faruwa agarinne cinkoso yayi yawa haka?" Na tambayeshi.

"Ɗan wasan kwallon ƙafane zaizo shine gabaki ɗaya garin ya rikice tako'inafa jami'an tsarone ko shugaban ƙasa bana tunanin za'ayi masa wannna tsaron" ya bani amsa.

"Oh tabbs kuwa nasanda zancen zuwannasa dan anata sanarwa a kafafen sada zumunta mutane kamar zasuyi Hauka nima naso naganshi i am his big fan" Dariya Hamma yayi yace.

"kima haƙura dan wannan a manya manyan ƙasarma ba kowa bane zai samu ganinsa ai ba ƙasarmu ba kawai duk ƙasar dayaje saiya rikita ƙasar tunda anyi ittifaƙin babu wanda yataɓa kafa record ɗinsa a yanzu fa shine matshin dayafi kowanne sanuwa a duniya ni bansanma abunda zai kawoshi ƙasarnan ba"

"May be personal issue ne shiyasa ba'a buga dalilin zuwannasa ba" nabashi amsa.

"Eh toh amma inagako shugaban ƙasa yakeda issue dashi zai iya binsa har ƙasarda yake ammma bansaniba basu sanar a media ba" canja zancen mukayi da wani zance daban."

***********

Wani katafaren gini ne mai Hawa biyu kusan gabaki ɗaya ginin da glass akayishi, gini yayi masifar haɗuwa gabaki ɗaya shape ɗin gidan curve yabada daga nesa kyallinsa kawai ake kallo, cikin katafariyar harabar gidan ansake wani katafaren ginin wanda yake kamada ma'aikata sai gefe filin kwallo ne wanda shima aka tsarashi, cikin wannan gini Kama da ma'aikata akwai wani Babban office aciki mai girman gaske yana ɗauke da set ɗin kujeru har guda biyu. Cikekken Balarabe ne matashi kyakkyawan gaske yanada tsayi sannan kuma baida jiki sai dai yanada murɗaɗɗan jiki bazai wuce 30years ba kansa cike take da kwancecciyar suma baƙiƙirin tayi luff yanada dara-daran idanuwa ƙwayar idanuwansa fararene tass yayinda tsakiyan eyeball ɗin yaci baƙi sosai fatarshi har wani tarr takeyi yanada haske sosai cikin larabawanma shi mai haskene, zaune yake a ɗaya daga cikin kujerun yana duba wasu takardu yagama sanya hannu ya miƙawa mutumin dake zaune a kujerarda take facing ɗinsa ya amsa sannan cikin harshen larabci yadubi wannann mutumin Personal Assistant nasa yace.


"Idan mungama zamu iya tafiya" Mutumin yayi murmushi cikin harshen larabcin yace.

"mood sir kanada tabbacin samun abunda zakaje nema? Kamar yanda kafaɗa bazaka taɓa dawowa batareda cika burinka ba, sanya ran cikar burinka yasa kaja tsawon wannan lokacin ka daidaici lokacin daya dace dan aiwatarda ƙudirinka, ina fata Allah yacika maka ƙudirinka duk da abune mawuyaci ace kamar yanda kake wannan ƙudirin yakasa cika" Murmushi yayi saida gefen kumatunsa suka lotsa Ya furzar da iska mai zafi a bakinsa ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗaura kan ɗaya ya jingina ya lumshe idanuwansa ya buɗe hannaye akan saman kujerar yasake furzarda iska mai zafi, mutumin nan cikin harshen turanci yasake cewa.

"are you nervous? jijjiga masa kai kawai yayi alamun eh. Mutumin yace.

"don't be sannnan ya canja harshe zuwa larabci yana faɗin.

bana tunanin a duniya akwai wani wanda zasu ƙi baka aure bana tunanin a duniya akwai macen da zataƙi aurenka, kanada kuɗi kyau suna da komai na maore rayuwa meyasa bazata soka ba?" sai alokacin ya ɗago ya gyara zamansa yace.

Idan har zata soni saboda wannan qualities ɗin menene bambamcinta da sauran matan? Kamar yanda soyayyarda nake mata ta kasance ta daban inaso itama ta kasance ta daban" Ya miƙe yace.

" Zamu iya tafiya yafaɗi haɗeda fara yin gaba wannan P.A nasa yabishi abaya dama an rigada anshirya masa motaci guards ɗinsa suka suka buɗe yashiga sannan suka rufe suma suka shiga dasu aa tada motocin sai airport. Dama da Jirginsa na musamman hakan yasa da gabaki ɗaya guards ɗinsa duka suka tafi."



PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

✔️Ote
Comment
Follow
share


To be cintinued


Zaynab Alabura




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment