Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ZAYNAB BAWA



Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid 200
*ƘADDARAR RAYUWA*


Ga wanda suke buƙatar siyan wannan litfafi na *BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI?)* ga wata garaɓasa da zanyi muku yau zuwa gobe in sha Allahu akwai discount yau zuwa Gobe in sha Allahu kowanne mutum biyu zasu biya 500🥰 Ga duk masu so ki samu kawarki ko sisternki ku haɗa 500 ku saya ku biyu ko cikin group kuke zaku iya haɗawa sannan idan mutum 4ne zasu haɗa su saya still akwai discount in sha Allahu
Kada kubari wannan damar ta wuceku💃💃

BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI?) da yawanku nasan kun karanta BIBIYATA AKEYI wannan tsohon novel ɗinane BIBIYATA YAKEYI labarine na daban wanda yasha bambam da wancan salon wannan daban tsarinsa ma daban labaraine guda biyu ma bambanta,

Ina fata zakuji daɗin labarin


Ga masu Buƙatar Biya
Ta 0003075326 Zainab M Bawa jaiz bank Ko katin MTN tareda shaidar biya ya wannan layin 08161146563


*HASKE WRITERS ASSO💡*
*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023


*بسم الله الرحمن الرحيم*




BY
ZAYNAB BAWA

PAGE 7


FREE PAGE SUN KUSA ƘAREWA KUSHIGO CIKI DAN AFAFATA DAKU."

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073



*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!

TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).

WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!

BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝



******

Munata shirye shiryen walima dan haka yau ban fita school saura 2days walimar Sauƙanmu gidanmu da gidansu maryam gabaki ɗaya anata shirye-shirye, Baba ya bugamin Memo masu girma guda ɗari sunana da Maryam ne ajiki domin maryam yanzu tadawo ƴar gida agidanmu kamar yanda nima nadawo agidansu, Mama kuma key holder ta buga mana mai suna ajiki anty tayi mana sticker kowanne guda ɗari ne dan haka na rabasu a tsakiya na 50-50 kowanne natafi dan kaiwa maryam nata, Itama nasamu gidansu anata shirye-shiryen walimar, ganin motar Hamma a harabar gidan ya sanyani sakin murmushi dan nasan yana gida ta iya yiwuwa nayi arba dashi hakan kuma zai samamin sanyi acikin zuciyata.

Part ɗin Umminsu Maryam nafara wucewa na sameta da wasu daga cikin ƴan uwanta suna shirin walima domin ita maryam za'ayi mata walima agida.


Shiga nayi muka gaisa tacemin maryam na ɗaki da ƙawayenta suna aiki, miƙewa nayi nashige ciki. A falonda Hamma yake zama natsaya naketa raba idanuwa na ko zan ganshi amma wayam ina tunanin jama'arda suke gidanne yasa bai zaunaba gabaki ɗaya sai naji babu daɗi nan da nan murmushin dake kan kumatuna ya sauƙa jiki a sanyaye nayi sallama na shiga falon maryam, tana jina ta saki ihu tana faɗin ƴar halak kinƙi ambato wallhy babe yanzu nake zancenki,

Raɓawa ta cikin ƙawayenta nayi bance komaiba na isa kujera ma zauna sannan na taɓe baki nace.

"Toh sai me? Ninace kiyi hira tane da zaki cikamin kunne daga shigowata?" harara ta wurgamin tace.

"keh wallh ba'a abun arziki dake"

"saina tsiya" na ƙarasa maganarta.

Cousin sisters ɗintane a falon da wasu daga cikin ƙawayenmu wanda mukeyin nursing tare su biyu ga dukkan alamu sunzo tayata aikine dan dama tun daga lokacin da suka fuskamci babanta hamshaƙin mai kuɗine suke shige mata.

Souvenir ne agabansu dayawa ga dukkan alamu shiryasu sukeyi, Sannu da aiki kawai nayi musu na dubi maryam nace ga aikanki inji mama da Baba da Anty,

Na miƙa mata ƙatuwar jakar danazo dashi karɓa tayi ta buɗesu taciro tafara karanta ihu tasaka tana faɗin.

"Mufa ƴan gatane tako ina taɓe baki kawai nayi danni bana cikin yanayin raha duka abubuwan taciro tana dubawa tana sake faɗin kyawun da sukayi,

Miƙewa tayi tafice ta nunawa Ummi sannan tadawo tana faɗin idan zaki tafi tare zamuje naje nayiwa Su mama Godiya, bance mata komaiba na zame na ƙwanta na lumshe idanuwa na, zuciyata aai azalzalata takeyi ina muradin ganin Hamma ko zatayimin sauƙin abunda nakeji, Ganin haka ya sanya Maryam ta ɗauko ko wata matslarce dan haka tatashi saiji nayi ta riƙo hannuna na buɗe idanuwana tace.


"zo muje" miƙewa nayi nabita muka shige ɗaki baya saki hannuna na ba saida muka ƙarasa Har bakin gado muka zauna, Sannan tace.

"menene yake damunki babe? Kinyi wani iri badai akan Ɓoyeyyen masoyi kika shiga wannna damuwar ba?" kallonta nayi na wani lokaci yayinda a zuciyata nabata amsa da cewar Hammanta ne yake azalzalar zuciyata. Afili kuma banda wani zaɓi face ɓoye abunda yake cikin zuciyata nace.

"waye kuwa zai sani cikin damuwa idanba shiba? Babe anya mutuminnan kuwa ba aljani bane?"

"Wani abunne kuma ya sake faruwa" ta tambaya na gyaɗa kaina sannan nace.

"kinsan mutuminnan har whatsapp ɗina yake bibiya"

"kamar Yaya?" ta tambaya. Dalla-dalla Nayi mata bayanin abu da yafaru jiya tsakanina da Sageer na ɗaura da faɗin.

"Allah ina ganin wannan mutumin aljanine idanba hakaba tayaya yasan cewa munyi chat dashi,

"Toh Babe menene abun damuwa anan?" naɗauka faruwar wannan abin zaisa ki fahimci cewa wannan mutumin masoyinkine na gaske bawai dawata manufa yake bibiyarki ba"

"toh amma WAYE SHI? idan abunda kika faɗa hakane yanzu yaci ace ya bayyana kansa" cikin sigar ƙwantarda hankali maryam take faɗin shikenan dai in sha Allahu zuwa agama hidimar wannan walimat zamusam wanene shi,

"Allah yayarda" kawai nace. Muka tashi mukayi palour, gabaki ɗayansu saida na lura da canji a fuskarsu sunso duk maganar da zamuyi muyita a gabansu.

Ɗaya daga cikin friends namu fadeela wanda muke school tare takasa ɓoye cikinta saida tafito tayi magana, Amma cikin sigar wasa dama kuma wasu lokutan jealousy comes in jokes so ba kowacce dariya bace taketa soyayya, Cikin wasa tace.

"Wato gulmarce dake mu karen ware ne yasa baza'ayi a gabanmu ba. Toh Allah yabaku haƙuri" Ina ƙoƙarin zama nabata amsa da faɗin.

"Dama kin kwantarda hankalinki danmu babu gulmar da mukayi" Dariya tayi alamun itama taɗauki hakan a wasa.

Marairaice fuska tayi dake dama ƴar azabar iyeyice ni haka kawai jinina bai haɗu da itaba gabaki ɗaya kalar tarbiyarmu ba ɗaya ba. Taddubi Maryam tace.

"Har yanzu Hamma bai fitoba, Wallh Maryam Hammanki ya haɗu sosai ajin ƙarshe, nifa danshi nake zuwa gidanku, Ko raina ke ɓace idan nayi arba da kyakkaywar fuskarsa sainaji ɓacin raina ya gushe,
Jin kalamanta ya sanya gabana yafara faɗuwa ji nakeyi kamar ta zubamin garwashi a ƙoƙon zuciyata, ɗaya daga cikin cousin ɗin maryam ta miƙe haɗeda jan tsaki tabi Fadeelah sa harara fuuu tafice aɗakin,

Fadeela ta dubi maryam wacce take kunshe dariyarta tace.

"Maryam kodai budurwarsa ce?" Dariyar da take ɓoyewa ce ta ƙwace tace.

"ni in nasanine? Aida kin tambayeta tun kafin tafita"

"uhmm ai alamu ma yanuna koba budurwarsa bace itama tana sonsa cewar fadeela" jijjiga kai Maryam tayi tace.

"Au kema sonsa ɗin kikeyi kenan?"

"toh idanba sonsa ba me nakeyi Maryam?" ashe kallon sakara kikemin kenan tunda baki fahimci ina sonsa ba"

Kama haɓa maryam tayi tace.

"ni nikuma A'a gaki ga Hamma Allah yabaki sa'a har yanzu ba'a samu macenda ta isheshi kallo ba amma zaki iya gwada sa'arki"

Cikin muryar damuwa fadeelah tace.

"Dan Allah bani numbernsa" inaji maryam ta karanto mata haɗeda faɗin.

"karki cemasa nice nabaki" Jikina yayi matuƙar sanyi Jin maganar Maryam da fadeela sai nakeji kamar wanda zazzaɓi yakeso ya rufeni. Jiki a sanyaye na miƙe nayi musu sallama maryam tace na jirata tagama Mutafi tare ko takanta banbi ba banma fahimci abunda take nufi ba nafara tafiya, jiki a sanyaye. Harna shiga falon batareda na ankaraba, kamshin turarensa ne yadawo dani daga cikin Hayyacina dasauri nayi ƙoƙarin juyawa ko zan kalloshi Bumm naji na buge mutum nayi baya zan faɗi ya sanya hannuwansa ya tallafoni da sauri tsoron kada na faɗi yasa ya haɗa jikina da nasa A tsorace na ɗago da kaina shima niɗin yake kallo yayinda idanuwanmu ya sarƙe acikin na juna, wani irin abune naga yana yawo a cikin ƙwayar idanuwansa wanda nakasa fahimtar abunda yake yawo aciki, Tsawon sanina dashi 2years bai taɓa kallona irin haka ba, Bazan iya juran kallon dayake yimin bah hakan yasa na yi ƙoƙarin Ƙwace jikina batareda wata gardama ba ya sakeni naja baya na sunkuyarda kaina ƙasa harya buɗe baki zaiyi magama amma yaanyin da zuciyarsa take bugawa da sauri ya sanya ya fasa ya raɓa yawuce, Ajiyar zuciya na sauƙe nabi bayansa da kallo bansan lokacin da murmushi ya kuɓucemin yayinda zuciyata take wani irin bugu kamar zata faso ƙirjina ta fito waje.

Jiki a saɓule na isa harabar gidan ina fita wayata ta buga alamun shigowar message, dake na sauya sautin shigowar saƙon wannan lambar ya sanya batareda na dubaba nasan wanda yaturo saƙon, danna canja sautin shigowar saƙonsa saboda kowanne saƙo yashigo saina samu kaina da faɗuwar gaba, jiki a saɓule na ciro wayata dan duba saƙon."


PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

✔️Ote
Comment
Follow
share


To be cintinued


Zaynab Alabura

*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023


*بسم الله الرحمن الرحيم*




BY
ZAYNAB BAWA

PAGE 8


FREE PAGE SUN KUSA ƘAREWA KUSHIGO CIKI DAN AFAFATA DAKU."

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073




*********


Da sauri maryam tafito ta taras dani sauran Friends namu na biye da ita abaya, hakan yasa na maida wayar nafasa duba saƙon, cikeda jin Haushi Maryam tace.

*Inata yimiki magana ki jirani ko ina kika kai hankalinki? Ko saurarona bakiyiba. kuma Bakima yiwa Ummi sallama ba" hatta gama maganar bance komaiba yanayin da nake ciki bazai barni na maida mata da masifa kamar yanda nasaba ba, dan haka na sakar mata murmushi. Sai kawai tasake baki tana kallona, ƙarasowa tayi daff dani yayinda Friends namu suma suka ƙaraso wajan. Cikeda al'ajabi maryam tace.

"lafiya kike kuwa babe?" cikeda nishaɗi nace.

"Me kika gani?" jijjiga kai kawai tayi batareda tace komaiba tayi gaba zuwa parking-lot, ganin babu kowa a wajan yasanya ta dawo wajanmu ta ɗaga waya takira driver ɗin kusan tare suka fito da Hamma ina ɗaga idanuwa na na kalleshi zuciyata tahau bugawa da sauri, Coppee brown Shadda ce ajikinsa ɗinkin jamba kansa hula hannunsa ɗaure da agogon fata shima brown yayi matuƙar ƙyau acikin shaddannan daƙyar na iya saita kaina na ɗauke idanuwana daga kallonsa, yazo dai-dai yanda muke yayinda kamshin turarensa ya rigashi isowa, Maryam na ƙoƙarin ɗaga waya tayo kira mukaji muryarsa yana faɗin.

"kuzo mutafi" batareda ya kallemuba yayi maganar yaci gaba da tafiyarsa. Maryam tayi saurin sauƙe wayar tabi bayansa, nima na rufa mata baya."


Shirune yabiyo bayan zamanmi gabaki ɗaya acikin motan saida mukahau titi batareda ya kallemi ba hankalinsa nakan TiTi yace.

"Ina zakuje?"

"Gisansu Mamee" Maryam tabashi takaicecciyar amsa,

A ƙofar gidan yakaimu ya zubamu yajuya abunsa, ajiyar zuciya na sauke a lokacin dana fita a motar danko kwararren numfashi nakasa jaa gani nake kamar daga numfashina zai iya fahimtar abunda yake cikin zuciyata."

ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin gidanmu na buɗe mana muka shiga, muka ratsa da harabar gidan har zuwa cikin gidan, fadeelah takasa haƙuri tafara faɗin.

"Zainab Ashe kuma gidanku masu kuɗine" Hafsa wacce muka taho tareda ita tace.

"Ai daga gani yanda kawancensu yayi ƙarfi itada maryam kinsan dole sai dai idan matsayi yazo ɗaya"
Fadeelah tace.

"bantaɓa saniba sai yau" murmushi kawai nayi musu, dan Tabbas ga duk wanda yaga gidanmu zaiyi tsammanin cewa munada dukiya sosai, amma mu kaɗai damuke rayuwa acikin gidan mukasan irin halinda muke ciki, Sai dai kawai muce Alhamdulillhi."

Ɗakin mama muka wuce Kai tsaye a falo muka zauna mama na ciki natashi nayi ciki Maryam tabi bayana cikin drinks ɗinda aka siya san walimar sauƙarmu na ɗebo musu haɗeda ruwan pure water na ajiye."

Maryam tafito tawuce ɗakin anty danyi mata godiya Muna zaune tadawo ta samesmu,

Anan muka zauna sai wajan biyu kafinnan suka tafi."

Wunin ranar gabaki ɗaya nayishi cikin farin ciki sakamakon abunda yafaru tsakanina da Hamma iya tsawon samina dashi bantaɓa ganin ya kalli yanda nakeba sai ayai da idanuwanmu suka sarƙe cikinna juna, ba shakka Hamma yanada kwakkwaran dalilinsa daya sanya baya kallon mutane ido cikin ido mai yiwuwa ya gane akwai ƙwayar halittar kyau a cikisu wanda zaija hankali haɗeda fuskar mai kallonsu.
Har ƴan gidanmu saida suka gane farin cikin danake ciki amma sai suka ɗauki hakan A ɗaukin walimar dana keyi.

Ban sake bi takan wayarba barema na tuna da saƙon da aka turo dan wasu lokuta nakanji kamar nadaina buɗe saƙonma gabaki ɗaya, nayi blocking numbern yafi sau babu adadi amma haka zanji shigowar saƙo ina dubawa zanga blocking ɗin dannayi ya sauƙa, shiyasa hankalina yafi karkata ga cewa aljani ke turamin message.

Wajajen la'asar muna zaune nida Anty fadeelah da Aysha mama ta shigo ɗakin. Tana kallonmu cikeda sha'awar yanda ta samemu muna hira tsakaninmu na ƴan uwa, dukanmu mukayi mata sannu ta amsa, sannan ta dubeni tace.

"Mamee kifito kizo ki tafi aikar Habibu shinkafa kam na aika ansayo, nasan yanzu yakusa isowa ko jallof kiyi masa da ƴan haɗe-haɗe.

"Toh Ganinan zuwa Mama yanzu zan fito" mama tajuya tana faɗin.

"Gara kifito dan nasan yakusa sauƙa" bayan fitar Mama Aysha tadubeni tace.

"Habibu ɗan uwanki yayanki ne zai dawo?"
Bankaiga bata amsa ba Anty fadeelah ta jefa mata harara haɗeda faɗin.

"keba ɗan uwanki bane?" Aysha tace.

"maida wuƙar nifa haka nake nufi ba ina nufin Yayanta"

"Kema ai yayanki ne" Cewar Anty fadeelah. Dariya nayi sannan nace.

"Anty fadeelah bazai girmeta ba kota girmeshi ko suzo sa'anni dan immediate nake binsa tsakaninmu babu wani rata sosai."

"Shekarunki nawa?" Suka haɗa baki wajan tambaya.

"19years zan cika this month nabasu amsa atakaice"

"eh tabbas bazai girmeta ba" cewar Anty fadeelah.


"Aysha ce tace. Amma ai akwai wani bayan shi ko? Ina nufin first born ɗin Mamanku" jin zancen nayi yayimin wani iri nayi Murmushi mai cikeda ciwo ban iya bata amsar tambayarta ba, ƙarancin shekaruna bai hanani jin zafi da raɗaɗin irin ahlin danake dashi ba, Mu kanmu bamu gama sanin junanmu ba. Cikin sanyayyar murya nace.

"Bansan wata irin rayuwa muke ciki a ahalinmu ba, ashe damu daku gabaki ɗayanmu rayuwa iri ɗaya mukeyi muna rayuwa batareda munsan junanmu ba, nikaina bansan ku nawa bane a cikin mahaifiyarku haka kuma baku saniba, wannan wace irin rayuwa ce? Koma wace irice bamai kyau bace. Gabaki ɗayanmu nasan bamajin daɗin yanda wannan al'amari yake kasancewa, idan munason gyara mu yakamata mu tashi mu gyara iyayenmu daban muma daban, Abunda yake tsakaninsu bai kamata ya shefemu ba, Habibu shine babban ɗan Mama ƴan uwan Mama ne suka biya masa karatu a ƙasar waje yagama yau zai dawo mu huɗune gabaki ɗaya a wajanta kukam nasan kunada yawa yaya Ahmad Kawai nasani saiku yanzu da kuka dawo cikin rayuwarmu, gabaki ɗaya sauran banace ban sansu ba bakuma zan iya tunasu ba saboda lokacin da tsawo" ƙarashe faɗin hakan ina miƙewa
Jikinsu gabaki ɗaya yayi sany nima jiki a sanyaye nace.

"Bari naje Mama na jirana" nasaka kai nafice.


A ɗaki nasamu Mama tabani kuɗin aikar harna juya zan fita sai kuma na juyo na kalleta nace.

"Mama mai yasa bakwa saka su anty fadeelah aiki?"
Ta ɗauki lokaci tana kallona kamar bazatayi magana ba har ina shirin fita sai naji tace.

"Saboda tsoron abunda zaije yazo" n ajijjiga kai sannan nace.

"ku kawarda kanku kan abunda mutane zasuce komai zakuyi kuyi zuciyarku ɗaya tsakani da Allah koma menene yaje yazo toh zaizo dasauki" gyaɗa kai tayi tace.

"Toh uwar Mata sarkin sanin yakamata jemin aika nikam ki dawo" najuya nifice ban daɗe a kasuwarba nadawo saboda aikar batada yawa. Ina dawowa nacire Hijabi nafito harabar kitchen ɗinmu nahau aiki Anty tazo tazauna tana tayani, Muna cikin aiki Mama tafito daga ɗakin Baba dan batama san da dawowata ba danaga batanan kawai sai nahau yin aikin tunda nasan ko tananan ma ni ce ƙarfin aikin.


Mama tana fitowa tace.

"Mamee jeki kira ƴan uwanki kuzo ku haɗu kuyi aikin" Abun yazomin a bazata tunda ban ɗauka mama taji maganata ba dan haka namiƙe na nufi kiransu Anty ta dubi Mama tace.

"Amma Mama dakin barsu kawai saboda abunda zaije yazo kinga iya zamansu basu taɓa tunanin tayamu aiki ba tunda aikin ba gagararmu zaiyiba kibarsu suyi zamansu ni wallh banason rikici" Mama ta nisa tace.

"Antynsu Lamarin gidannan yana buƙatar gyara zamanda mukeyi da zuba idanuwa bazai gyara lamarinba. Har indai kina tunanin makomar Ƴaƴanki ko bayan Babamu toh ki taimaka wajan sanya hannu a gyara wannan lamari, Abaya munyi kuskure matuƙa da bamu zuba ido munja gefe ba toda al'amarin bai taɓarɓare hakaba"


cikeda Biyyya Anty tace shikenaan in sha Allahu zan taimaka amma bana tunanin sanya hannuna zai gyara lamarin baƙya kallon har yanzu irin gaisuwarda take shiga tsakanina da yarannan? Ko kallon mutumci fa ban ishesu ba" Mama batakai ga tankawa ba muka fito daga ɗakinmu ganin fuskarsu ya nunawa Mama lallai sunji daɗin kiranda akayi musu. Muna ƙarasowa Mama tacewa anty.

"Tashi kibarsu suyi aikin su kaɗai tunda idan gidan miji sukaje babu mai tayasu, mu dukanmu muka saka dariya Anty tatashi mukaci gaba da aikinmu Har aka kira magrib Baba yafito Sallah ya taras damu muna aiki ba ƙaramin daɗi yajiba dan har fiskarsa tanuna farin cikinsa yakasa ɓoyuwa Har yace.

"Mamee" Bayan na amsa mai ya tuna saiya canja yace.

"fadeela a haɗamin baƙin shayi ki kawomin ɗaki idanna dawo sallar isha'i Mamee ta gwada miki irin haɗin da akemin" mu duka muka amsa haɗeda yimasa adawo lpy."

muka tashi Sallah Bayan mundawo mukaci gaba da aiki saida aka kira isha'i kafinnan muka tashi na nunawa anty fadeelah yanda zata haɗawa Baba shayin, yana shogowa tajuye takai masa tadawo mukaci gaba da aiki, adaren sai muka gama aikin tass, Rice and stew mukayi sai vegetable pepper chicken da kajin da Baba yasiyo ƙwara biyu da ƙananun snacks dama Mama tana kunun Ayah na sayarwa kuma yana tafiya sosai dan haka saida mukayi mata muka ɗureshi a gorina Asyha ta jera mata a fridge sauran aikin da mukayi ƙananun coolern da mama takawo mana muka ɗebawa Habibu da Baba nasu sauran muka na cikin gida, Mama tace tunda mu mukasha wahalar aikinmu toh muraba kayanmu, kintatawa mukayi muka raba.

Sai ƙarfe tara sannan Habibu ya iso Kowa yayi murnar ganinsa barinni dukda bawata jituwa bane a tsakaninmu.

Sai kusan sha ɗaya muka shiga ɗaki domin anzauna anata hira da Habibu hardasu Aysha da fadeelah duk da babu wani sabo tsakani,

Hasken da wayata takeyine ya tabbatarmin akwai saƙo akai na ɗauka shaff ni nama manta da saƙon ɗazu gashi har wani yasake shigowa. Sakon farko saƙone kamar haka.

(انت تملك قلبي)


Mtsww naja tsaki afili a zuciyata ina faɗin wannan mutumin yafiya iyaye da kinibibi, saƙo bazai taɓa yinsa da Hausa ba kullum larabci wasu lokutan ya sirka da turanci Ko yana ganin hakan zai burgenine oho masa. Saƙo na biyu kuma

العد التنازلي
hakan yana nufin (countdown )

العد التنازلي

Shine heading na rubutun
Sannan a ƙasansa kullum yana irge bansan irgen menene amma tabbas nasan akwai abunda yake nufi da wannan irgen Nidai na zuba idanuwan dan ganin yaushe wannan irgen zai ƙare.


Fita nayi daga wajan message ɗin na shiga phone na shigarda numbern Hamma danaji dazu Maryam tana faɗawa fadeelah ƙawarmu alokacin na riƙeta akaina. Harna danna calling nayi sauri nayi hanging, nasaka hannu naɗan bugu kaina bansan meyake damuna ba idanna kira ya ɗauka toh me zance masa? Ajiyar zuciya nayi nashiga nayi saving numbern da Hamma❤️ Harda ƴar heart agaba.
Zuciyata cikeda jin daɗin kasancewar numbern Hamma a wayata na kwanta bacci."


Washe gari ma haka muka tashi da aikin walimar sauƙata gabaki ɗaya gidan muka saka Hannu a aikin domin yayi mana sauri amma hakanma saida mukayi dare sosai muka gama muka saba a ledojin da drinks gabaki ɗaya komai yazama intact muna tashi washe gari sai dai muwuce wajan sauƙa da sassafe."

Aysha ce tayimi jan lalle a hannuna daƙafafuna dake dashi na kwana sai asuba nacire kafin gari yagama wayewa yayi maroon yayi matuƙar kyau sosai."

Ƙarfe tara muka wuce wajan sauƙa batareda ɓata lokaciba aka fara gudabarda abunda ya taramu, dake muryata nada sauti ninayi katatu a wajan sauƙan, maryam kuma tana cikin masu gudanarda baiti.

Anan aka fara kiran na ɗaya dana biyu har zuwa na biyar babu sunana kona maryam aciki, ƙunƙuni maryam takeyi inata dariya nace.

"ke babe kiji tsoron Allah wallh kidaina borin kunya kefa kanki kinsan bakida ƙoƙoarin da zaki fito cikin jerim mutane biyar kinga ni bansakawa kaina ba Alhamdulillhi tunda dai nasan na haddace kuma yana kaina in Sha Allahu kuma zanyi aiki dashi toh menene abun damuwa? Ke bakiga suma kansu malamn suna alfahari da karatunmu ba? Tunda dai aka sakamu acikin wabda zasu fitarda makaranta kunya ai Alhamdulillhi" Tsaki maryam taja nace.

"Nace sai kije kiyi tayi banza mai borin kunya" faɗa muka farayi a wajan mukayi baram-baram. Wayata tafara ruri na ɗagota na duba a yanda true caller da tunanin numbern babban wata company ne wanda suke deleveryn kaya ina ɗauka aka sanar dani inada saƙo ƙofar makaranta nafito na karɓa, ina miƙewa Maryama tace.

ina zuwa babe?" harna fara mata bayani saina tuno munyi faɗa dan haka na haɗe rai nace.

" ina ruwanki nayi hanyar fita."



PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

✔️Ote
Comment
Follow
share


To be cintinued


Zaynab Alabura


*BIBIYATA YAKEYI*
_(WAYE SHI?)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




BY
ZAYNAB BAWA

PAGE 9

*FREE PAGES SUN KUSA KAREWA KUSHIGO DAGA CIKI DOMIN AFAFATA DAKU."*

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment