Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace.

"Tashi kisha ruwa" banbi takan ruwanda takawo ba
na miƙe zaune wayarda Baba ya siyomin na ciro ajaka na mika mata dama already nafaɗa mata Baba ya siyamin wayar ina mika mata ta jonata a chargy tafaramin setting dinta,

Instagram da whatsapp ta budemin tadaura pic ɗin data daukeni mai nikab akai. Mikamin tayi tace nayi following wanɗanda nakeso ina karɓa nafara following ƴan wasan kwallon kafa (footballers) Da mamaki maryam take kallona duka takaimin tana faɗin.

"Ke ana folllowing mutanen arziki ke kina shirme" mtsww naja tsaki sannan nace.

"nikuma kinga ai mutanen tsiya nayi" karban wayan tayi tafara searching abubuwa tana nunamin tana faɗin.

"Kingani irin waɗannan ake following kina mace menene ya haɗaki da ɗan wasan kwallo kuma?" Fauce wayata nayi nace.

"Yan wasan kwallon dai su nayi niyya kuma su zanbi. naga wayata ce ba taki ba? ƴan wasan kwallon kaff sunmafi kowa yawan followers"

Bata sake kulani ba nikuwa naci gaba da dannawa pictures dinsu likes, aɗakin ta ɗauko mana abinci takawo mukaci tafita da kwanukan sai wajan Yamma kafin muka tashi tafiya muka fito dan yiwa umminsu Sallama a falon da muka barshi muka taras dashi sai dai da alamu ya tashi danya canja kaya. Munzo daff zamu fita muka tsinci muryarsa yana faɗin.

"Kujirani zan kaiku" toh kawai maryam ta amsa amma abin yabata mamaki dan datsu babu yanda batayi ba yace bazai kaitaba tunda shi ba driver dinta bane amma yanzu bata tambaya ba yana fadin tajirashi yakaita.

Wajan Umminsu Maryam muka wuce danyi mata Sallama Kudi taɗauka tabani naki karba babu yanda batayi na karɓa ba naki bayan hakama ban faɗa agida zanje gidansu naryam ba kuma mama idan taga kudin sai tayimin faɗa, Umminsu Maryam bataji daɗin yanda naki karban kuɗin ba amma nima babu yanda na iya saboda yanayin gidanmu,
Muna zaune a falon munajiransa yashigo Bai kalli yanda muke yace.

"Muje" Nan danan zuciyata tafara bugawa da sauri-sauri jin muryarsa danayi a hankali na daga kaina na kalli fuskarsa farine sol kyakkyawa yanada dogon hanci da manyan idanuwa kana kallonsa kaga sakk bafulatani kamarsa ɗaya sak da Umminsu, Yanada tsayi kuma siririne, Cikin harshen fulatanci naji yana yiwa Umminsu magana itama ta maida masa da harshen fullancin amma naji ta ambaci sunansa Abubakar abunda na iya ganewa kenan acikin abunda suka faɗa bayan sun gama maganar Ummi ta juyo ta dubeni tace.

"ki gaishe da Mamanku" na amsa sannan mukayi mata sallama muka fice. Kafin mu karaso harya isa gaban motarsa yashiga mu kadai yake jira. Maryam ta bude min bayan motar nashiga tarufe sannna ta shiga gaba, tunda muka fara tafiya baice komaiba tuƙinsa kawai yakeyi cikin nutsuwa ganin yanda maryam ta nutsu duk kuwa da rawar kanta ya tabbatarmin da cewa bayason hayaniya saida muka hau titi sannan naji yace.

"ina zamuyi?" yayi maganar ne batareda ya kalli ko daya daga cikinmu ba.

"Kobi" Maryam tafaɗa sannan tayi masa bayani yanda zai gane. tunda muka fara tafiya nake satar kallonsa amma shi gabaki ɗaya hankalinsa ba'a kanmu yakeba. Yanda kikasan bai sanda mutane acikin motar ba. Sa'i-Sa'i maryam take jiyowa tanamin magana ina bata amsa. A dai-dai ƙofar gidanda ta faɗa masa yayi parking motarsa,

Muna isa nayi masa godiya da kayi kawai ya amsa na fice. Inajiyo maryam tana cemasa zataje ta gaida mamana juyawa nayi naga ko ita zai bata amsa sai naga itanma da kayin yabata amsa fitowa tayi muka wuce ciki tareda ita suka gaisa da Mama sanin yana jiranta yasa bata daɗe ba tafito suka wuce."


2YEARS LATER (Bayan shekara biyu)

Sanye nake da farin Uniform ɗina. ɗinkine wanda aka yishi na zamani yayi matukar zaunawa yamin kyau sosai yasha guga dagani har uniform ɗin sheƙi mukeyi. a shekara biyunnan da suka wuce nayi matukar kyau nayi cika har tsayi saida naƙara izuwa yanzu na cika ƴan mata wacce za'a kalla akirata da ƴan mata, baƙar jakace schoolbag maƙale a bayana duk wasu takadduna suna cikinta, muna sanya ƙafarmu cikin school ɗin wayata tayi ƙara. Inajin ƙarar shigowar Saƙo wayata saida gabana yafaɗi. Maryam ta dubeni tace.

"Saƙon koh?" Kai kawai na gyaɗa mata cike da damuwa nace.

"Wallh Babe Yanzu har banaso wayata tayi ƙara har indai nashigo school saina tsinci kaina da faɗuwar gaba" Maryam tace.
"ni abunda yake damuna mun kasa gane waye mai wannan saƙon mai kuma saƙon yake nufi" Nisawa nayi cikeda tabbacin abunda zan faɗa nace.

"inada Tabbacin namijine yake wannan saƙo, saƙone ake yinsa da ƙunshasshiyar manufa, saƙon yana nuni da kumshesshiyar soyayya, ina tunanina yana bayyana soyayyarsa gareni kuma ga dukkan alamu BIBIYATA YAKEYI toh amma WAYE SHI? me yake nema a wajena? Wace irin manufa yake da ita akaina da tsawon shekara biyu yakasa Bayyana kansa gareni?" Dafani maryam tayi tace.

"Khair in sha Allah karki damu inaji ajikina koma wanene yake BIBIYAR rayuwarki toh alkhairine Babu wani abun akasin haka ki kwantarda hankalinki kinji?" gyada mata kai nayi danni dai gaskiya yanzu abun yana damuna dafarko bai dameni kamar yanzu ganin lokaci kawai jaa yakeyi amma har yanzu yaƙi bayyana agareni. Nisawa nayi nace.

"tashi mutafi class kawai kar muyi latti" Dariya maryam tayi tace.

Yawwa Babe tashi mutafi ki share wannna mutumin dannaga yanaso ya maida minke baya" tafiya nafarayi ina faɗin aiya ma maidani bayan, biyoni tayi tana faɗin.

" ko zamuje ayi mana tracing na numbern?"

" Share kawai idan yagaji zai bari"

"Uhm Uhm fa babe shekara biyu tsawon lokacine da idan barine yaci ace yabari. Har indai zakina takura kanki da tunani gara muje ayi amma ni inaji ajikina alkhairinr kidaina matsawa kanki ko wanene shi wata rana zai bayyana a gaban idanuwanki"

"Hmm kawai nace nashige Class."


Bayan gama lactures ɗin lacturen yazo dai-dai zai fita yatsaya yakira reg no na yace mai Reg no ya sameshi bayan yagama lacture, jikina sai ɓari yakeyi domin bansan abunda nayi ba tunani babu irin wanda baizo rainaba,

Yana gama lacture yafita babu yanda banyi Maryam tazo ta rakani ba haka taƙi jiki aɗarare natafi office ɗinsa can na tadda ba wani abun bane ya sanya yake nemana details dina zan cika wanda za'a fara biyanmu, nacika nafito, Maryam tana kallon nafito ta tsareni tana tambayata abunda yacemin ƙin kulata nayi data dameni nace.

"Da kika matsu kiji abunda yacemin mai yahanaki biyoni? Sai dai kije ki tambayeshi abunda yacemin" tasan halina sarai bazan fada ba hakan yasa ta ƙyaleni dan haushinta nakeji da taƙi rakani yanzu da ace wani abunne haka zan shanye baƙin cikina ni ɗaya.

Sai wajan magrib kafin muka gama abunda zamuyi a school ɗin kusan yanzu koda yaushe tare muke tafiya da maryam itake saukeni wata rana ma sai tabi ta ɗaukeni tukunna, amma yau tunda haushinta nakeji na ƙudirta cewa bazan bita ba.

Abaya take bina amma naki saurarenta a bakin gate na makarantarmu mukaci karo da motan Hamma kamar yanda maryam ke faɗa masa ya buɗe motan yana zaune aciki amma ƙafafunsa suna waje yana danne-danne a waya ina kallonsa bugun zuciyata ya sauya tashi daya naji fushinda nakeyi yana neman kaucewa, ganin naja na tsaya ya sanya Maryam tayi sauri ta ƙaraso dai-dai yanda nake tana faɗin wai bana baki haƙuri ba?

Jin maganarta ya sanyashi ɗagowa ya dubemu batareda ya kulamu ba yashige motar ya maida murfin ya rufe mungane abunda yake nufi dan haka batareda na kulata ba na isa wajan na buɗe motar nashiga, itama ta ƙarasa tashiga yaja muna cikin tafiya Maryam tadubi Hamma tace.

"Hamma kaga Mamee fushi takeyi dani tun ɗatsu nabata haƙuri taƙi haƙura" Kamar bazai kulaba sai can kuma yace.


"Kukam ai kullum acikin faɗa kuke. Menene ya haɗaku?"

"Hamma wani lecturer nefa yace taje office ta sameshi dannaki rakata shine fa" yayi sauri ya taka burki gabaki ɗayansu suka razana. Ajiyar zuciya ya sauke sai kuma ya tayarda motar sukaci gaba da tafiya kamar bazai ƙara cewa komaiba sai can kuma yace.

"Me zatayi masa a office daya kirata?"

"nima bansaniba na tambayeta taƙi fadamin" tunda suka fara zancen sai yanzu tasaka baki tace.

"Details ɗinane bai cikaba shine yakira yace na rubuta masa"

Uhmm kawai yace amma jikinsa yana bashi akwai abunda zaiyi da details ɗin idanba hakaba ai sai dai takai aɗaura mata a portal. Suna sauƙeni nafita nayi masa godiya itako ko kallonta banyiba.


Wajajen ƙarfe tara wayata tafara ruri lokacin ina zaune cikin ɗakinmu ina duba littafaina, Ganin baƙuwar lamba ya sanya na ɗauka nayi shiru saida naji Sallama daga cikin wayar sannan na amsa, Sai akaci gaba da magana.

"Nasan baki gane waye ba dan nakiraki babu izini Sunana Salman nine wanda ɗatsu kika bawa lanbarki" cikeda rashin fahimta nace.

"ni banbada lambata ma kowa ba"

"kidaiyi tunani dan nidai nasan da hannunki kika rubutamin" shiru nayi ganin yazo da rainin hankali daga cikin wayar yace.

"sorry Dr salman ne lecturer dinku da yakarɓi details ɗinki recently agafarceni na karɓi number ɗinki da sunan zan cika abu amma maganar gaskiya ma kaina na karɓawa" Nayi shiru ina sauraronsa yacigaba da magana.

"Ba zan tsaye wani raɓe-raɓe ba batun arziki ya kawoni wajanki, Bada maganar wasa nazo ba, kina jina?" ya tambaya jin nayi shiru. Cikin sanyayyar murya nace.

"Eh inaji"

"Yawwa Alhamdulillhi tunda kinaji karki damu da lallai sai kin bani amsata ko tsayawa tunani yanzu ki saurareni kawai zan baki ishesshen lokacin da zakiyi tunani. Nagama settling nayi achieving abubuwa dayawa da nakeso nayi arayuwata, abu ɗaya ya ragemin shine aure, na yaba da hankalinki sosai kuma inaso na aureki idan kin amince kai tsaye magabata zasu shiga zancen idan kuma baki aminceba karkiji tsoron gayamin dan kin ganni lecturer ɗinki zan fahimceki sosai, zan baki ƙwana 3 kiyi tunani acikin wannan 3days bazan nemeki ba har sai yacika idan ke kuma kikaji kin amince kafin time ɗin zaki iya nemana. Mukayi Sallama dashi zuciyata sai bugawa takeyi.

Dr salman bayida wata makusa, amma ni gabaki daya cikin maza mutum ɗayane yake burgeni shine Hamma nakasa fahimtar me yake faruwa dani aduk lokacin dana ganshi koda ambatar sunansa akayi bugun zuciyata sauyawa yakeyi, komai nasa burgeni yakeyi. Nakasa karatun dana keyi gabakai ɗaya juyi Kawai nakeyi narasa da wanne zanji ga wannan mai Bibiyar rayuwata ga Wannan daya shigo dawani batu numfashi mai ɗumi na furzar sannn na lumshe Idanuwanta inaso bacci ya ɗaukeni."

Washe gari muna zaune a school kiran Dr salman ya shigo wayata banyi saving number ɗinsa ba amma ina kallo nagane, Cikin raina nace.

"Toh mai zaiyimin bayan yace bazai sake kiranaba sai bayan kwana uku?" amsa wayar nayi na kara a kunnena haɗe dayin Sallama ya amsa bai jira na gaisheshi ba yacemin.

"Idan babu damuwa kizo office ɗina inaso muyi magana" toh kawai nace, badubi Maryam dama yanzu nagama bata labari tace.

"menene kuma?"

"wai nemana yakeyi a office ɗinsa" Dariya maryam tayi tana faɗin.
" Dr fa yadage baisan an rigashi ba" Hararta nayi nace.
"waye ya rigashin?"

"Ɓoyeyyen masoyi mana Ni Ƴar Team ɗin Boyeyyen Masoyine" Siririn tsaki nayi nace.

"Allah kinsamu matsala ke kam" nafaɗa ina miƙewa
Miƙewa tayi tace.


"Zakice nafaɗa miki Allah kuwa"
Tafiyana farayi batareda na jirata ba, biyoni abaya tayi Mukayi knocking yabamu izinin shigowa, gaisheshi mukayi yace muzauna muka zauna, ya kalleni yace.

"Babu damuwa zan iyayin magana agabanta?"

"Babu komai" nabashi amsa, Saida ya tattaro nustuwarsa gabaki ɗaya sannan ya dubeni yace.

"Zainab dama anyi miki miji agidane? Tun jiya da ina kiranki kika sanar dani" kallon rashin fahimta nakeyi masa yacigaba da faɗin.

"Banji daɗin abunda ya faruba gaskiya, dakin sanar dani zan fahimta tsakanin mu biyu basai kin sanar masa ba"

"Menene yafaru malam?" najefo masa tambaya."


PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

✔️Ote
Comment
Follow
share


To be cintinued


Zaynab Alabura


*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡


*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023


*بسم الله الرحمن الرحيم*




BY
ZAYNAB BAWA

PAGE 6

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073



*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!

TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).

WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!

BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝







Dr Salman yaja numfashi Sannan yacigaba da faɗin.

"Jiya Bayan wayarda mukayi dake nasamu saƙo daga baya kira yashigo, anyimin offering kuɗinda hankali bazai iya ɗauka ba akan narabu dake banaji akwai wani mahaluki da zai iya cire wannan kuɗin yabayar kawai saboda soyayya har indai akwaishi toh son dayake yiwa wannan abu duk duniya baza'a samu wanda zaiyi mata kwatankwacinsa ba, da baki sanar dashi ba ni kaɗai kika faɗawa zan fahimta" Da mamaki nake kallonsa nace.

"Amma ni ai malam babu wanda na faɗawa kuma mutumin da kake referring akansa ni banma sanshi ba" Ya kalleni kallo irinnna wanda yakeson gaskata abunda nake faɗa. ya jijjiga kai yace.

"Amma abun da mamaki dan fa har zuwanda kikayi office ɗina jiya yana sane da hakan dan saida yayi maganarsa kuma maganar da mukayi a waya yayimin ita jiya"

"Wallh Malam ni ban faɗawa kowaba ko zuwan office ɗinka danayi ko agidanmu ban faɗa ba"

"Eh toh zan yarda da cewa baki faɗawa kowaba saboda saida nayi tunani nace idan keda kanki kika sanar masa kiranki danayi awaya da zuwa office ɗina hakan yana nufin kina ra'ayinsa kenan idan hakane bayada buƙatar bani kuɗi kafin narabu dake har indai kina ra'ayinsa keda kanki zakice akwai wanda kikeso, tunda bakisan dashi ba tabbas yana BIBIYARKI toh Amma WAYE SHI?" Shiru mu dukanmu mukayi dan bamuda wannan amsar,

"Malam dan Allah zan iya ganin numbern da aka kiraka?" danno kan number ɗin yayi ya mika min yace.

"Gata nan idan kinada bukata zan iya sakawa a Bibiya miki layin"

"kayi hakan dan Allah malam nagode"

"Babu damuwa zuwa gobe duk yanda ake ciki zan sanarda ke. amma sai dai Kiyi Hakuri na janye zancen neman aurena akanki dan wannan ga dukkan alamu zai iya aikata komai akanki bazan ɗauki wannan risk ɗinba dama ace munsan WAYE SHI? toh da zamusan yanda zamu ɓullowa lamarin amma rikici da abunda baka taɓa kallonsanba ai babban kasada ce" Har wani zazzaɓi nakeyi Jin wannan lamari dayake faruwa koma wanene yanzu yaci ace ya bayyana kansa. Malam yace.

"Bani wayarki nagani" na miƙa masa wayar jiki a sanyaye Ya dudduba sannan yace.

"Abunda mamaki da nayi zaton ana sauraron kiranki amma kuma ya nunamin babu mai bibiyar layinki shikenan dai Zaku iya tafiya in sha Allahu idanna sameshi zan sanar dake Godiya nayi masa sannan muka tashi muka fita"

Masallaci mka wuce kai tsaye saboda bamuda lactures har awa biyu masu zuwa kuma bazan iya shiga library karatu ba, Kwanciya nayi zazzaɓi yanason rufeni. Maryam tace.

"Wai keh meye kikeyi hakane? Wannan fa ba abun damuwa bane dama nafaɗa miki Boyeyyen masoyi ne yake bibiyarki, ki sakawa ranki sanyi wallh jikkna yabani akwai alkhairi mai ɗumbin yawa a wannan lamari" kwantarmin da hankali ta ringa yi har na warware,

"kinsan me" maryam tafaɗi. Na ɗago daga kwancen danake nace "

'A'a"

"Tashi muje mubada layin wajanmu ayi mana tracing ta'iya yiwuwa yakasance mutum ɗaya"

"A'ina zamu bada" na tambayeta bari ina zuwa tafaɗi sannan ta ɗaga waya takira wani saurayinta minti talatin ya'iso tabashi layinda ake turamin saƙo ta nemi yayi mata tracing layin shima cemata yayi zuwa gobe duk yanda ake ciki zai sanarda ita."


Yamma liƙis muka koma gida hakanma saida na gargaɗeta akan kada ta faɗawa kowa abunda yake faruwa tacemin bazata faɗa ba."


Gani nakeyi kamar gari bazai waye naje nasamu Dr salman naji yanda ake ciki a lamarin ba, sassafe na shirya zuwa school ko Karyawa ban tsaya yiba.

Har 12:00pm muna zaman jiran Dr salman bai isoba Maryam takira saurayinta ya sanar mata da cewa zaizo baigama abunda yake yiba,


Dr baishigo school ba sai 2:00pm yana shigowa kuma lactures yashiga mukayita jiransa sai 4 yafito, sannan yakira mukaje muka sameshi. Bayan mun gaidashi ya amsa yafara da faɗin.


"Kuyi hakuri nasan kunyita jirana lamarinne dai ya tsareni maganar gaskiya ba'a gano mai layinba naje wajan tracing amma campaynyn layin sun rufe komai na SIM ɗin sunki bada damar da za'a bibiyi layin naje campaynyn da kaina bansamu wani bayani ba sunmaƙi tsayawa su saurareni daga ƙarshe ma dana matsa duka ma'aikatan wajan sai suka tashi daga aiki. Aka rufe wajan. Abunda zai baki mamaki danaje ina tambaya akan layin costumer care dana samu bai yarda yabani wani bayani ba har saida yatashi yashiga office na manaja, ina iya kallo lokacin da manager ya leƙo yana kallona da dukkan alamu yayi waya wani wajan ya sanar, nakasa samun haɗin kansu atakaice sai babu wani kwararran bayani gameda mai wannan lamba"

"Jikina yayi sanyi matuƙa" Dr salman yacigaba da faɗin ga dukkan alamu wannan mutumin yanada ƙarfin iko na gaske duk yanda muke tunani yawuce nan mutumin da zai iya juya company alokaci guda ya sanya su rufe su tashi kiyi tunanin wani irin mutumne, kinsanda cewa company basa ɗaukan asara, yanzu nasake gaskata cewa kuɗinda yace zai bani akanki zai iya badawa. Saboda yanzu Allah kaɗai dasu kansu sukasan nawa zai biya wannan company" Jiki a sanyaye nace.


"Shikenan malam nagode sosai"

"Amma zan baki shawara why not ki sanarda mahaifanki? Ta iya yiwuwa su zasusan matakan ɗauka" Girgiza kai nayi nace.


"A'a malam mahaifina baida cikekken lafiya banaso yashiga damuwa ta wannan dalilin in sha Allahu komai zaizo da sauƙi"


"shikenan Amma ki kwantarda hankalinki yanyinki ya nuna baki cikin nutsuwa, wannan mutumin ga dukkan Alamu bamai cutarwa bane. da akwai cutarwa a lamarinsa toh daya daɗe da cutar dake tunda yanada ƙarfin ikon yin hakan tako wani hali. Sannan Shawarata ta biyu karki nuna Alamun cewa kinsan yanayi kokuma wannan abun yana damunki, karki nemi sanin ko waye. karkk bari yagane kina cikin wani hali. yin hakan zaisa yaƙara nisanta haɗuwarsa dake karki damu wata rana dole zaizo gareki tunda bazai zauna har abada a ɓoye ba. Na tabbata yana ganin kowane moves ɗinki yasan me kike ciki kwantarda hankali shine zai bashi damar bayyana a ƙaramin lokaci."

"koma wanene inada yaƙinin sonki yakeyi matuƙa abunda zai baki mamaki koni daya kira ba threaten ɗina yayiba roƙon Albarma yayi wajena da tayin kuɗi mai masifar yawa, nima kaina banaji zai cutar dani bare ke wanda duk wasu alamu sun nuna cewa masoyinki ne"

Godiya nayi masa mukayi masa sallama muka fice, Maryam tace.

"muwuce wajan Saurayinta dan yazo tun ɗazu muna wajan Dr salman"

Kai tsaye wajansa muka wuce mun sanya ran samun amsa mai daɗi daga wajansa. da abokinsa sukazo yayi mana bayani yace.

"har yanzu bamu samu mai wannan layin ba har company munje karshe ma sai cemana sukayi babu wannan lamba a jadawalin numbers ɗinsu" murmshi abokinsa yayi yace.

"Kai ka yarda da abunda suka faɗa kenan?"
Mutanen nanfa ba gaskiya suke faɗa mana ba kawai akwai wani abu aƙasa"

"Nima naso na fahimci hakan" kallon Maryam yayi yace.

"Akwai wani matsala ne gameda layin?"

"Ana yawan turowa ƙawata message da layin shiyasa muka nemi sanin mai layin"

Abokinsa yayi dariya sannan yace.

"Lallai wannan ya kwafsawa kansa ai irin wannna matan kai tsaye zaka je musu shi ya tsaya wasa nikuma nagani inaso dan haka yanzu zan shigarda kaina" sunkuyarda kaina nayi dan dama naga take takensa. Saida mukayi exchange phone number dashi kafin mukabar wajan ni saida naji tsoron bashi number ɗinma dan bansan abunda zaije yazoba.
Saina fara tunanin wanann kodai aljani ne?

Ƙarfe takwas na dare muna zaune aɗakin mama muna hira wayata tafara ruri ina dubawa naga mai kiran Sageer kamar yanda nayi saving ɗazu naƙi ɗagawa Mama taɓe baki saidan yakira kusan sau 3 duk ina kallo ban kulaba danni tsoron ɗauka nakeyi dan bansan abunda zaije yazoba.

12:am ina zaune ina karatu Washe gari inada test naji ƙarar messages ya shigo wayata, batareda na dubaba nacigaba da karatuna minti biyu baya wani saƙon yasake shigowa, ɗago kaina nayi na ajiye alƙalamin dake hannuna na miƙa hannu na ɗauki wayar, duka lamba ɗaya taturo saƙon gabaki ɗaya guda biyun dan haka kai tsaye nawuce cikin message ɗin saƙo nafarko yananan kamar haka.


_don't dig too deep_

na biyu kuma aka rubuta.
حظ موفق في اختبارك (Good luck on your test) abunda saƙon yake nufi kenan amma da kalmar larabci aka turoshi Taɓe baki nayi sarai nagane abunda yake nufi da message ɗinsa nafarko wato yana nufin nadaina bincike akansa karna zurfafa bincike afili nace


"Kai kaji wajan"
Wato harma yasan inada test gobe?
"koma wanene kai zaka bayyana lokacine" na ɗauki shawarar Dr salman zan nuna kamar bansan abunda yake faruwa, kunna Data nayi nahau whatsapp naga naga mesaages ɗin sageer yafara shigowa, shiga message ɗin nayi naga yanamin ƙorafi akan rashin ɗaga wayarsa haƙuri kawai nabashi yace zai kirani alokacin nace.

"Dare yayi yanzu kawai lets chat bama daɗewa zanyiba saboda ina karatun test, hira mukayi dashi na ɗan lokaci sannan nayi masa sallama na sauƙa. Saida na taɓa karatu kafin nayi bacci, Sassafe naje na zana test ɗina nadawo dake muna shirin yin walimar sauƙa bazama mukeyi a school kamar yanda muka saba ba,

Dama tun tashina da safe naga kiran Sageer so ban ɗauka wani abun bane ban bi bayan kiranba har saida nadawo yasake kira. Abunda ya faɗamun ya matuƙar bani mamaki. ya tabbatarmin da cewa akwai mai bibiyar chats ɗina kuma yacemin nayi bincike sosai domin sanadin chats ɗinmu najiya an kirashi ana rokonsa daya fita a rayuwata. Mamaki sosai abun yabani wato whatsapp ɗinma bai barmin shiba? yasan duk wani abunda nakeyi chats ma saida ya bibiyeshi, Sageer yacigba da faɗin.

"Bansan WAYE SHI ba amma inada tabbacin zai iya sadaukarda kansa akan soyayyar dayake yimiki daya kira abun kamar almara amma ba abu bane na wasa, na gaskata soyayyarsa gareki Har indai ya bayyana soyayyarsa gareki kawai ki amsa dan yana matuƙar sonki, toh kawai nace masa mukayi Sallama."

"ina sauƙe wayar na luntsuma tunani wato zai iya fitowa ya bayyanawa kowa soyayyar dayakemin nice wacce ake yiwa soyayyar kuma bazai iya fitowa ya nunaminba afili nace.

"Koma wanene kai toh kai kaji wajan."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

✔️Ote
Comment
Follow
share


To be cintinued


Zaynab Alabura


*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023


*بسم الله الرحمن الرحيم*

BY


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment