Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa da zuciya idan yyi zuciya abun ba kyau, har zai tashi ya bishi daddy yace ya tsaya karya soma binsa. Haka ya hakura, mutane kuwa sai tayasu murna suke, haka taron ya watse.
"Dakyar farooq ya samu ya sulale yabar wajen, shima wata motar ya shiga sannan ya karbi key gun wasu abokansu, ba inda ya nufa sai gida. "Tun abakin gate yyi parking sannan ya wuce side dinsu direct, dakin omar ya nufa ya Ganshi a bude, alamar be ma dawo gidan ba kenan. Zai fito kenan suka hadu da mummy fuskar nan tata a tamke 6acin rai qarara a fuskar ta, abinda ya sake hargitsa tunanin farooq kenan, cikin tsawa tace ina omar din yake?




Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] ‪+234 813 725 2431‬: [8/27, 12:50 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓



82_83



Zanyi amfani da wannan dama wajen bawa masoyana hakuri bisa jina da kukayi kwana biyu banyi posting ba, ba komai yaja ba sai lectures da mukeyi sosai ga exam da muke shirin yi, abin dai sai du'a'i, Amman dai insha Allahu yanxu komai normal. Ku kasance tare da mai kaunarku a koda yaushe _*Nuceey*_ _*luv*_.


**************


"A rikice yace nima shi nake nema mummy, mummy tayi kwafa sannan ta juya batare da tace masa komai ba.shima farooq sake ficewa yyi a gidan dan Neman inda Omar ya shiga.

***
Tunda ya fito a taron yake ta falfala Gudu kamar zai tashi sama idon nan nasa sun qanqance sakamakon 6acin rai da yake ciki zuciyar nan kuwa sai tafasa take tamkar ruwan da aka Dora kan gas. "Ikon Allah ne kawai ya kawo omar gidan shi, Wanda daddy ya Gina masa idan yyi aure saiya tare aciki, dake gidan babu gateman dolen sa ya sauko a motar, sannan ya bude gate, unguwar shiru kamar ba mutane saidai daka ga ginin gidajen wajen zaka tabbatar wa kanka ba qananan mutane ne suke rayuwa aciki ba. "Bayan yyi parking motar sa sai ya wuce falon sa direct, abunda yyi matukar bashi mamaki shine bai wuce ganin yanda aka gyara main falon ba, dake gidan me hawa biyu ne, yanda aka sa colours din komai red& ash shiya tabbatar masa da lalle wannan auren fa dgske ake masa, saidai ba laifi ya yaba da tsarin colours din, qarshe kuma ya ta6e baki ya haura sama da sauri, dakin shi ya wuce batare dya duba dayan dakin dake wajen ba, "yana shiga ya cire duk kayan jikin sa sannan ya fada toilet ya sakar ma kansa ruwan sanyi, kusan 15mins ya dauka sannan ya fito, kamar dai tsarin dakinsa na gida, saidai wannan yafi kyau sosai, ran nan nasa saikace ana qara masa fetir a ciki sai tafasa yake, farin idon nan ya koma red, "duk yanda yyi ya mance sunan yarinyar da aka daura masa aure abin ya faskara,tunawa da sunan ta kuwa shike qara tunzura 6acin ransa, a fili yace kai anya daddy yasan waya aura masa? _Fateema_ fah? Mtwss gaskya an gama dashi wallahi, an cuceni toh ma me zaiyi da wannan tatsitsiyar yarinyar? Dayaga dai tunanin sa zai sake birkitashi yasa ya mike kan gado rai a 6ace da wannan tunanin bacci yyi gaba dashi.


"Farooq duk inda yasan omar zai shiga yaje Amman babu labari, kwata2 be kawo gidan omar a ransa ba. "Haka ya koma gida, mummy kam ranta yyi mugun 6aci bata ta6a zaton omar zai watsa mata qasa a ido ba gaban dubban jama'a, Amman koda ta shiga cikin mutane sai tayi kokarin 6oye fushin ta.
"Koda farooq ya dawo, mummy yaja gefe zuwa side dinsa sannan ya sanar mata shifa began omar ba, cikin 6acin rai mummy tace toh shi yaro ne? Yaje duk inda zaije karka qara Neman sa, tana kaiwa nan ta tashi da nufin tafiya, farooq yyi qasa da murya sannan ya shiga lallashin mummy dan ya lura tana cike da 6acin rai sosai, "dakyar ya iya calming nata, sannan tabar side dinsa, a zuciyar ta tace dadin yara dayawa kenan idan wani ya bakantaa maka sai wani ya faranta maka. "Haka biki ya watse batare da omar ba, 'yan gulma sunyi abunsu har sun gama, amarya ameera ta tare gidan angon ta farooq, "koda akace za'a dau amaryar omar, mummy hanawa tayi tace a kyaleta a wajen ta. "Amarya _Imaan_ kuwa hankalin ta kwance batasan wainar da ake toyawa ba, dukda basa shiri da omar Amman kwana biyun da bata ganshi ba ta danyi kewar sa, farooq ta tmby, farooq yace yyi wata 'Yar tafiya ne, imaan ta tabe baki tace shine ko salllama babu, farooq ya kalleta da mamaki tunda yasan bata shiri da omar ai ba yanda za'ayi ta damu, kasa shiru yyi yace a'a kodai kin fara son bro dina? Ya fada yana murmushi, imaan tace cabdin Allah ya sauwake me zanyi da tsoho, farooq ya zaro ido yace Ashe nima kallon tshoho kikemin, imaan tayi dariya, tace lah ya farooq Allah banda kai, farooq yace toh yanzu akace ki auri omar zaki auresa? Imaan ta zaro ido tace dan Allah ya farooq ka rufamin asiri ko maza sun qare bazan auresa ba. "A razane yace what? Imaan tace umhu ai kaima kasan Kaine mijina, farooq ya girgiza kai yana tunanin hadin gambizar da su mummy sukayi, *OMAR* bayaso *FATEEMA* Tace tsoho, _daddy_ da _mummy_ kuma sun ```hada```.





Nuceey luv😘
[8/27, 2:23 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓



84_85



"Haka omar yake rayuwar sa cikin wannan gida shi kadai, saikace maye, farooq kuwa yana gidan shi anacin amarci dukda yana cikin tunanin dan uwansa, kamar daga sama ya tuna da gidan omar, ai ko minti daya be qara ba yabar gidan shi, direct gidan omar ya nufa, "a tura kofar gate din yyi ga mamakin sa yajita a bude, hakan ya tabbatar masa da akwai mutum a ciki, yana shiga kuwa yaga motar omar aciki, hamadala yyi, sannan ya kutsa kanshi cikin falon, sallama yyi yaji shiru, dan haka ya haura sama, dakin omar ya gwada budewa yaji ta budu, dan haka ya tura, bayan yyi sallama, nan ma shiru, mamaki ne ya kasheshi ganin omar sai baccin sa yake hankali kwance, saidai da mutum ya lura zai tabbatar wa kansa ya danyi rama. "Matsawa yyi yadan bubbuga kafar sa, omar dake bcci yaji ana bugun sa a razane ya tashi yana kallon farooq da mamaki, "farooq ma mamakin yake dukda yadan daure fuska, atake baccin omar ya washe sannan yace malam lpy? Farooq ya nemi bakin gadon ya zauna, sannan ya kalli omar yace haba bro abinda kayiwa su mummy kayi adalci kenan? Yanzu kusan 4days baka je inda suke ba just bcoz sunyi maka gata? Haba bro. "Omar ya tabe baki yace kaga malam gidana kazo ba dandalin wa'azi ba idan shi kkeson yi kaje ka masallaci ko inda akeyi kayi inaga zakafi samun lada. "Da mamaki farooq yace bro ni kke fadawa haka? Akan an baka imaan? "Cikin tsawa yace ni nace inason ta? Cewa nayi a auramin ita? Bana sonta, bana qaunar ta har abada baxan ta6a sonta ba. "Farooq yace bekai ga haka ba ai, abinda nake jiye maka shine ranar da zakayi nadaman wannan kalaman da kake furtawa.. Omar yace ya isheka haka farooq tun muna shaida juna ka daina min mgnr jaririyar, farooq ya cije baki cike da takaici yasan hakane ai da tun farko ya sanarwa mummy zai auri imaan da duk hakan bata kasance ba, a fili yyi murmushi sannan ya fara mgn a nutse, yace sorry bro, Amman inaso ka gane fushin iyaye kan 'ya'yan su ba karamar masifa yake jawowa ba, duk abinda iyaye zasuyi wa yaransu bazasu taba yin abinda zai cutar da su ba, abinda iyaye sukayi mana bazamu ta6a biyansu ba biyayya itace tamu duk abinda sukace muyi zamuyi matukar be kauce addini ba, koda bama son Abu yakamata mu tausasa zuciyar mu muyi na'am da za6in su sai kaga qarshe mune dacin moriyar abun, INA rokon kayi kr2n ta nutsu kaje ka bawa su mummy hakuri dan Allah. "Omar yyi shiru shi kansa yasan be kyautawa su mummy ba, Amman harga Allah beji zai iya aminta da imaan a matsayin Matar sa ba. "Tabe baki yyi sannan yace sai nayi tunani. "Farooq yyi murmushi sannan yace ohk no prob, ahankali abinka da tsakanin twins, ba wani bata lkci farooq yyi ta Jan omar da hira har saida ya tabbatar ya ware daga bacin ransa sannan yabar gidan zuciyar sa wasai.


"Tunda yabar gidan omar yake ta tunani qarshe dai ya yanke shawarar komawa gida dan bawa mummy hakuri. "Cikin shirin sa ya fito na T shirt da wando, kwalliyar tayi matukar amsar jikin sa, yyi kyau sosai. "Motar sa ya shiga sannan ya kama hanyar gida, a hankali yake tuki harya isa gidansu. "Ya Dade cikin mota sai yanxu ma yakejin tsoron haduwar sa da mummy, dole dai ya fito a motar qirjinsa na bugawa dafdaf yasan mummy idan ta fara masa fada sai ikon god, gefe guda kuma tsanar imaan tana masa yawo a kwanya.

"Ahankali ya tura kofar falon hade d sallama, jin shiru ya tabbatar masa d ba kowa a falon. Qarasawa falon yyi Da nufin sake yin wata sallamar tarrrr idanun sa suka sauka kan wani photo dayayi bala'in yi masa kyau dake maqale jikin bango, idan bazai manta ba wannan shine hoton da akayi masa shida imaan lkcn data rungume shi, sosai ya shagaltu da kallon hoton, dan ba qaramin kyau sukayi ba. Mwtsssss yaji anja tsaki, juyawar da zaiyi yaga mummy ce data fito a dakin ta, da sauri ya sunkuyar da kansa, mummy kam juyawa tayi dan komawa dakin ta. "Ganin haka yabi bayanta da sauri, har dakin ya bita batare da tace masa komai ba tayi zaman ta tana duba wata jarida. "Mummy, omar ya kira sunan ta, mummy tayi banza dashi, kusan sau uku ya kira Amman ta share shi. "Omar yace dan Allah mummy kuyi hakuri akan abinda nayi muku sharrin zuciyane ya debe ni har na aikata abinda nayi, tsaki mummy ta sake ja cikin kunan rai tace ka tashi kabar min daki inada abinyi, omar ya rike kafar ta yace mummy dan Allah kiyi hakuri bazan sake ba insha Allah. "Mummy tace ka bani mamaki omar, ko a mafarki ban zaci akwai ranar da zamuyi maka kyautar Abu kayi watsi dashi ba, bama a iya gaban mu ba aa a gaban duniya ka nunawa duniya iyayen ka basu isa da kai ba, omar ya sadda kansa qasa ko kusa baison bacin ran iyayen sa, da kyar da sidin goshi ya lallaba mummy harta yadda, "qarshe mummy tace naji abunda nakeso kasa aranka shine auren ka d imaan babu saki, a rikice ya kalleta saidai ya kasa cewa komai dan bayason ya qarawa kansa wani lefin dakyar ya iya gyada kansa a matsayin ya yadda, mummy tace duk lkcn daka musgunawa imaan ta sanar min ko na gani da idona sai nayi mummunar sa6a maka, nan qirjinsa ne ya bada darararam, a fili kuwa yace insha Allah mummy zanyi yanda kikace, mummy tace gud, next week zaka dau Matar Ka. Omar yace Allah ya kaimu. Yana fadin haka yabar dakin sannan ya nufi side dinsa. "Mummy kuwa addu'a tayi Allah ya hada kan omar da imaan. Allah kuma ya sanyawa auren Albarka da daurewa har abada, nima dai nace ameen.





Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] ‪+234 813 725 2431‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓



86_87



"Imaan CE ta shigo gidan a gajiye sai kwala sallama take ta dawo daga skul, dake kwana 2 mummy ke kaita skul, lkcn tashi kuma farooq ya kawo ta kafin ya wuce nasa gidan tunda basu koma aiki ba sakamakon hutun amarci da suka dauka. "Dakin mummy ta wuce tayi sallama, tana shiga ta tarad d mummy tana salla, "ajiye skul bag dinta tayi sannan ta fada toilet, wanka tayi, sannan ta fito, "lkcn mummy harta idar da sallah, imaan tace mummy sannu da gida, mummy tayi murmushi tace ya skul. Imaan tace uhum sai du'a'i, can kuma tadan 6ata fuska. "Mummy tace mekuma ya faru? Imaan tace mummy kinga fah kullum naje skul, sai a dinga nunani anacewa wai ga amaryar DR omar. "Mummy tace ke share su, imaan tayi narai2 da ido tace dan Allah mummy wai dgske ne? Mummy tayi shiru itama ta gaji da 6oyewa imaan batun auren ta, "can tace eh ba qarya bace, a rikice imaan tace whattttt??? Mummy ta girgiza kai alamar confirm, "imaan ta durqushe a wajen tana rusa kuka kamar wacce akayi mata rasuwa, "mummy tashi tayi ta isa gareta duk ta rikice da kukan imaan, lallashin ta tafara yi, Amman kamar ana angiza kukan imaan. "Mummy ta rasa abin yi, imaan kuwa bata daina kukan ba, mummy tace kinga imaan bakyason omar din ne? Idan bakyaso sai a raba auren karki cuci kanki ki sanar min, dan banaso naci amanar ki, cakk kukan imaan ya tsaya tayi shiru tana tunanin maganganun mummy, idan akwai abinda zata sakawa mummy tasata farinciki shine ta amince da auren yaranta, rashin amincewar kuwa kamar tayi mata butulci ne, "karki takurawa kanki wajen amincewar abinda bakyaso ke dasu farooq duk daya na dauke Ku cewar mummy, imaan ta dago kanta tana goge hawayen ta tace aa mummy ba nufi na ba kenan, duk abinda kika zabamin wallahi INA maraba dashi Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, da farinciki mummy ta rumgume imaan tana fadin ameen 'yata na gode na gode Allah yyi miki albarka, Imaan ta kwakwulo murmushi tace ameen, mummy tace toh Amman meya saki kuka dazu? Imaan tayi shiru dalilan kukan ta ai sunada yawa barkatai, abinda yafi daga mata hankali be wuce wai da omar aka daura mata aure ba, mutumin data fara tsana a rayuwar ta kenan, kuma itama tana da tabbacin ba wacce ya tsana kamar ita toh taya zaman su zai kasance da wannan hadin gambizar?....mummy ta katse mata tunani da fadin kinyi shiru. "Imaan tayi murmushi sannan ta sunkuyar da kanta kasa dan wasu hawayen ne ke Neman zubowa kan kumatun ta, a hankali tace sbd ya farooq, mummy tace farooq kuma? Imaan ta gyada kai, mummy tace meya miki? Imaan ta sanarwa mummy alkawarin auren ta da farooq yace zaiyi. "Mummy tayi shiru a zuciyar tace itama kanta taso hakan Amman data ga baice komai ba shiyasa taja bakinta tayi shiru, a fili kuwa ta furta tace don't worry, shi daman haka Allah yake ikon sa, kana naka ne shima yana nasa, Amman idan akabi nasa sai aga daidai. Imaan ta gyada kai cike da gamsuwa. "Mummy tashi tayi tabar dakin, imaan kuwa na ganin ta fita ta kifa kanta a jikin gado tana rera kuka yyinda zuciyar ta take ci gaba da tafasa, d wannan kukan bacci ya kwashe ta, kasancewar ba sallah take ba. "Sai da mummy ta shigo dakin sannan ta gyara mata kwanciyar ta.



*******
Tun daga wannan ranar mummy take gyara diyar ta, omar kuwa ko kadan bayason ma ya hadu da imaan, haka zalika itama bata kaunar su hada hanya duk mummy na lura dasu saidai kawai ta basar taci gaba da bawa imaan abubuwan daya kamata, tsumi na musamman mummy tasa aka kawo wa imaan, imaan kuwa sai sha take abunta dan taji shi da zaqi, hadin kankana kuwa ba'ace komai, imaan bata ta6a kawo komai a ranta ba dan haka take shansu hankali kwance. "Imaan tayi bulbul abinta sai qara kyau take tamkar ba itace jaririyar da omar yake ambata ba.

****""
Yau data kasance Friday sati biyu da auren omar da imaan kenan, yau kuma mummy take son damkawa omar Matar shi a hannun sa.




Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] ‪+234 813 725 2431‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓



88_89



"Imaan CE durkushe gaban mummy, a dakinta sai wa'azi take mata na zamantakewar aure, "mummy tace yi nayi, bari na bari imaan shine ribar aure, banban abun kuma shine hakuri, duk yanda masoya suka kai da soyayyar su, har sukayi aure toh INA tabbatar miki abinda zai biyo bayan zaman nasu shine hakuri., dukda na sanki ba baya bace wajen kwalliya da tsabta, toh inaso ki kara zage damtsen ki domin ita mace 'Yar kwalliya CE,... Wa'azi sosai mummy tayi mata, imaan kuwa ba abinda take sai kuka. "Mummy tashi tayi ta kaita falo, alkcn daddy ya fito shima, mummy ta danna kiran omar be Dade ba shima sai gashi, a wannan wajen daddy shi yaja musu kunne sosai a karshe yyi musu fatan Alkhairi, imaan dai kuka take kamar an bude famfo a idon ta, "mummy CE ta rike hannun ta lkcn har omar ya fice a falo, "yana cikin mota mummy ta iso da imaan wajen sa. "Da kyar mummy ta iya cire imaan jikin ta dan wani irin kuka da takeyi kamar anyi mata mutuwa Sam batason rabuwa da mummy. "Haka ta ajiyeta gaban mota, mummy ta leko tana kallon omar daya juya kansa gefe ransa sai tafasa yake dan jin kukan imaan da yake tamkar qara masa guguwar tsanar tane, "mummy ta kira sunan sa, da murmushin yake ya juyo yana kallon mummy, na'am ya amsa, mummy tace ga fateema nan na damka maka amanar ta, Ka kulamin da yarinya ta karka soma cutar da ita. "Omar yace insha Allah mummy zan kiyaye, ohk batun skul, ka dunga kiyaye lkcn tafiyar ta da kuma dawowar ta, omar ya gyada kai alamar ya amsa. "Mummy ta shafi kumatun imaan dake kuka sannan tabar wajen. "Tana barin wajen omar ya fisgi motar a guje Wanda har yasa imaan ta dago tana kallon sa a razane, ganin fuskar sa tayi a murtuke kamar an aiko masa da sakon mutuwa, sunkuyar da kanta tayi a sanyaye a zuciyar tace ni daman nasan za'a Rina Allah kadai yasan irin zaman da zasuyi, take kuma ta kece da wani irin kuka, da sauri omar ya daka mata tsawa yace ya isheki kukan kuma haka, be qarasa bama imaan tayi saurin kama bakin ta wani mugun tsoron sa ya dirar mata lkci guda.

"Gudu yake tamkar zai tashi sama, har ya iso unguwar su, yana zuwa gate, aka bude masa dake ya samo me gadi tun jiya. "Gate man sai daga hannu yake yana yalla6ai sannu da zuwa, inaa ai omar ko kallon sa beyi ba, wani wawan parking yyi, bayan ya tsaya sai yyi shiru, imaan dai kanta a qasa batasan ma a'ina suke ba. "Omar cikin daga murya yace jirana kike na fitar dake ko me? Imaan najin haka tayi saurin bode motar batare da ta kalleshi ba. "Tana fita omar ya sake fisgar motar a guje, kadan ya rage ya buge imaan dam ma ta matsa da sauri, baki galala ta tsaya kallon sa hanyar waje ya nufa, har ya fice a.gidan gaba1 bata daina kallon sa ba. "Wasu zafafan hawaye ne suka sake zubo mata, yana nufin anan zanyi ta tsayuwa kome? Wai wannan wanne irin aure ne? Imaan ta tambayi kanta. "Jikin wata fulawa ta matsa sannan ta samu wani waje tayi zaman agun, tana zaman jiran tsammani.





Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] ‪+234 813 725 2431‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓



92_93



"Da wannan tunanin ta shige dakinta, ko d tazo bcci ma gagarar ta yyi tunanin Abinda omar ya fada mata take.
"Da safe ya kasance Saturday, tunda imaan tayi sallar asuba wani wahalallan bacci ya kwashe ta sbd bata samu tayi jiya ba dalilin tunani data sa a ranta, "omar kuwa yana dawowa a masallaci har zai wuce dakinsa sai kuma ya bude dakin imaan, kwance ya ganta tana sheka bcci, "ruwa dake cikin roba a dakin ya dauka ya yayyafa mata, a matukar firgice imaan ta tashi sakamakon jin ruwa a jikin ta da taji, ga wani nauyi da kanta yake mata hade da Sara mata, "cikin tsawa yace ke uban wa ya baki izinin komawa bcci? Imaan tayi zuru tana kallon sa itafa har yanxu mamaki omar yake bata dan bata taba zaton zaiyi rabin abinda yake mata yanzu ba saikace me aljanu?.... Omar ya katse ta da fadin kin zubamin wannan idanun naki masu kama Dana ungulu bazaki amsani bane? Imaan ta sadda kanta kasa wasu zafafan hawaye na Neman zubo mata ita batasan amsar da zata bashi bama. "Omar yace well, tashi ki biyo ni, yana fadar hakan ya juya zuwa falon kasa. "Imaan ma binshi tayi tamkar jela. "Saida ya zauna sannan yace, zaki fita waje akwai tsintsiya a inda ake ajiyewa, kullum zaki dinga share gidan nan sau uku, imaan ta dago kanta da sauri tana kallon sa qirjin ta sai dukan 3,3 yake, omar ya sake daure fuska yace safe, rana, yamma kenan, haka zalika duk wata fulawa dake gidan nan zaki dinga bayin su suma sau uku a rana, falo da dakina ma, suma sau uku har mopping, imaan tun tana daure zuciyar ta qarshe saida ta 6alle da kuka, "cikin kuka tace dan Allah ya omar kayi hakuri wallahi bazan iya dukkkanin abinda ka zayyano ba dan Allah, ko kuma ka sauwa kemin auren dan Allah, omar yyi murmushin mugunta yace a gidan ubanki Zakice bakya aiki? Ai bari kiji baki da Mara da mai aiki a yanzu, sannan ki sani banason wasting time a aiki na, so jeki fara tun yanzu. "Yana kaiwa nan ya tashi ya haura sama, yana shiga daki ya kwanta yabi lafiyar gado.
"Imaan a nan ta durkushe tana kukan bakin ciki, ita gaba1 ma rayuwar ta isheta, "jiki ba kwashi jiki ta fita waje, ga wani irin sanyi da ake busawa kasancewar sanyi asuba dake kadawa, dakyar ta iya fita wajen, wani irin tashin hankali ne ya bayyana kan fuskar ta, ganin yanda fadin gidan yake, gashi kota INA ganyen flowers sun bata wajen, wani hawaye ne dumi suka gangaro kan kumatun ta, "jikin ta na rawar sanyi, ta qarasa inda aka tanadar dan zaman tsintsiya, idan zata iya tunawa tofa rabon ta da shara tun umman ta nada rai, dan a gidan mummy akwai masu aiki, abinci ne kawai sukeyi tare da mummy dan mummy batason me aiki tayi mata abinci ta gwammaci tayi da kanta, bayan wannan saidai taci ta kwanta ko tayi kallo, ko kuma taje farooq ya koya mata kr2, wasu hawayen ne suka sake zubo mata lkcn data tuno da ya farooq dinta shikenan yyi mata nisa. "Hawaye na ambaliya kan kumatun take sharar ta, tun wajen 6 ta fara shara ba ita ta gama ba sai 8. Duk jikin ta yyi laushi ga gajiya, haka ta kwashe sharar ta zuba a dustbin, tana gamawa ta koma kan flower, nan ma dakyar da sidin goshin ta kammala bayin flowers din. Hannun ta kamar ya cire a jikin ta, sai to 9 ta gama da gyaran waje, "tana komawa falo, daidai lkcn omar ya fito cikin shirin sa yadau wanka yyi kyau fuskar nan kam kamar an aiko masa d sakon mutuwa, shi haka omar yake idan tun farko ya nuna bayason Abu to kada a takura sa akai, dan koda yanason abun idan aka takura masa zai tsaneshi, shiyasa tunda aka tilasta masa auren imaan yaji babu halittar daya tsana tamkar ita dan ko kadan baida burin aure a yanzu. "Har zata wuce yace kee, imaan ta juyo tana kallon sa, omar yace a gidan Ku ba'a koya miki yanda ake gaisuwa bane? Imaan ta sadda kanta qasa tace kayi hakuri dan Allah sannan tace good morning, omar ya tabe baki sannan yasa kai ya fice, ita kuma imaan ta fara haurawa sama, har zata bude kofa taji ance kee, a razane ta juya, yace zonan, imaan ta tafi da sauri har tana hada stairs wajen sauka. "Tana zuwa omar ya jawo hijab dinta suka fito waje, suna zuwa wajen omar yace haka ake shara a gidan Ku? Imaan ta juya tana kallon wajen cike

Please Login or Register in order to submit comment