Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko daidaita zama batayi ba ya fisgi motar a guje, imaan dai cikin sai kadawa yake tsabar tsoro. "A wani katafaren store sukayi parking, bayan yyi omar yace jeki na baki 10mins kiyi sauri. "Imaan ta kalleshi d sauri tace toh kaxo mu tafi mana. "Omar ya watso mata wani mugun kallo, ai batasan lkcn data fice a motar ba. "Shiga tayi sannan ta fara daukar kayan kwalliya a gurguje d turaruka, saida tayi kusan 15mins a ciki sannan ta fito, kasancewar omar ya shigo ya bada ATM dinsa akan duk abinda ta dauka, a ciri kudin. "Lkcn da imaan ta kusan zuwa jikin motar, mamaki ne yasa ta tsaya cakkk, wata siririyar mata ta gani tare d ya omar, suna gaisawa sai murmushi yake mata abunda bata taba gani ba kenan. "Dan a zaton ta baya kula kowacce mace. "Ta dayan 6angaren tabi ta sanya kayan ciki sannan ta shige mota zaman jiran sa. "Omar kuwa sai alkcn ya lura d zuwan imaan, lekowa yyi yace ke fito, imaan tace na gama ai. Omar yace ki fito nace, imaan ta fito sannan ta zagayo inda yake, wannan matar tace woow omar wannnan sister dinka CE? "Omar yace yes, da murmushi a fuskar ta tace no wonder naga kuna kama kaii ta fika kyauma ta karasa mgnr tana dariya. "Omar kuwa dariyar da yake dazu ta tsaya tsakk ji yyi tamkar ta watsa masa garwashin wuta, kai a duniya ma ba'a ta6a ya6a masa mgn ba irin ta yau taya zata hadashi d imaan? Sannan harda qarin ta fishi kyau??? Kai Amman ta cuceshi wallahi. "Imaan kuwa dadi taji har cikin ranta taji ance ta fishi kyau, take ta dago ido ai tsarab suka hada ido dashi dan haka tayi masa gwalo sanna ta sunkuyar d kanta kasa, ran omar ne ya sake 6aci wannan Matar ta katse shi d fadin yadai Omar? Naji kayi shiru. "Omar yyi murmushin yake yace am.. Muna sauri ne Meenat.sai mun hadu next time. Meenat tace oh sorry, buh kadan bani number ka, so dat mu dinga gaisawa. "Omar yace ohk a gurguje ya bata sannan ya tisa keyar imaan suka bar wajen. "Meenat course mate dinsa ce.a inda sukayi makaranta a america.
"Koda suka shiga mota ba me cewa kowa ci kanka. "Saida suka isa gida, bayan yyi parking, sannan ya riko kunnen imaan, imaan ta kalleshi a tsorace, omar yace uban wa kikema gwalo dazu? "Imaan tayi shiru. "Omar yace karkiyi zaton abinda tace gsky ne, dan babu inda kika baro a kamannin gwaggwon biri, imaan ta zaro ido. "Omar ya gyada kai yace yes kamar ki sakkk data gwaggwon Biri.
"Imaan ta ture hannun ta sannan ta bude kofar da Sauri ta fita tana goge hawaye, a daidai bakin kofa sukaci karo da farooq, farooq yace mekuma ya faru? Imaan ta bare baki ta fara kuka dan takaici ta kasa cewa komai. "A haka ya jata falo. "Mummy ta kalleta d sauri tana tmbyr ta abinda ya faru, imaan kuwa ta sake barke baki, mummy tace yimin mgn mana, imaan cikin muryar kuka ta sanarwa mummy abinda omar yace mata. "Atake mummy tahau salati sai alkcn omar shima ya shigo. "Mummy tace wai omar yaushe ka baci da shirme ne?




Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] ‪+234 813 725 2431‬: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓


72_73


"Farooq ya zaro ido waje cike da mamaki yace, imaan shekarun ki nawa? Imaan tace 16yrs, farooq ya girgiza kai yace kina wannan shekarun harkin fara tunanin aure? Imaan tace naga dai zamu cusawa suhailat haushi ne kaga idan ta qika akwai me sonka. "Farooq yyi murmushi yace na gode Amman nikam baxan aureki ba. "Imaan ta zaro ido tace bakaso na nima kenan. "Farooq yace ah Nina isa? Inason ki mana imaan, "am tukunnan ma meya kawoki nan kina kuka? ( yyi tmbyr dan kawar d wancan zancen.) "Imaan ta tabe baki ta Shiga sanar masa abinda ya faru. "Farooq ya girgiza kai yana mamakin rashin jituwa irinta imaan d dan uwansa ya rasa me imaan ta tarewa omar, "can yace kinci abinci? Imaan tace aa, fatooq yace ohk. Anan yasa aka kawo mata abinci tanaci suna hira abinsu.

"Omar kuwa jin shiru bata dawo ba sai ya fito waje dan dubata. Iya duban sa ya rasa inda imaan ta shige kwatakwata besan imaan tasan wajen zaman farooq ba shiyasa be kawo zataje wajen ba, sosai hankalin sa y tashi lkcn daya tuno fadan dazai fuskanta wajen mummy matukar be samu imaan ba, haka yyi ta zagaye yana duban ta Amman be sameta ba, "har lkcn tashi yyi baiga imaan ba. Jiki sa6ule ya koma gida yana tunanin abinda zai tarad. "Farooq kuwa lkcn tashi nayi ya kama hannun imaan suka dawo gida. Koda mummy ta tmbyesu yace mata shi ya dauko ta sakamakon aiki d yyiwa omar yawa be samu tym ba. "Omar kuwa yana bakin gate ya kasa shigowa gidan, can d tsayiwar ta ishesa yyi ta maza ya shiga gidan. "Yana shiga ya tarad da mummy a falo, d murmushi ta amsa sallamar sa, omar dai mamaki ne ya isheshi kodai imaan din ta dawo d kanta ne? Ya tmbyi kansa, ai koda ta dawo ma saita hadashi d mummy, hakadai yyi ta tunani har mummy ta katse shi da fadin lpyr ka kuwa yau? Omar yyi murmushin yake, yanason tmbyr ta imaan Amman yana tsoron yanda tmbyr zataje ta dawo dan haka yaja bakinsa yyi shiru. "Na gaji ne, ya bawa mummy amsa. Mummy tace eyya jeka huta mana. Ai kamar jira yake ya mike d sauri yabar wajen. A hanyar sa ta komawa side dinsa can ya hango farooq d imaan sai buga kwallo suke suna dariya mamaki ne kurum ya isheshi na yadda imaan ta dawo gida.

"Farooq ya dauki ball da niyyar cirata sama, imaan tace Allah ya farooq nice d bugawa, farooq yahau dariya, aiko ba zato ba tsammani yaji tayi tsalle ta makale a qirjinshi tana kokarin kwace ball.... Ai baisan lkcn data fadi kasa ba, omar kuwa yana kallon su ya tabe baki da qarfi ya furta girma dai ya fadi. Sai alkcn suka lura dashi, farooq yyi murmushi, imaan kuwa harara ta wurga masa. "Omar ya zaro ido yace ni kike harara? Imaan ta murguda baki, tahowa yyi d niyyar dukanta, d karfi tace Allah ka tabani saina fadawa mummy yauma yaddani kayi, omar ya tsaya cakk dan bayason fadan mummy, dan haka yyi kwafa ya nufi 6angaren sa. "Su kuwa sukaci gaba da wasan su.
"Farooq ne kwance kan gadon sa sai juyi yake tunanin sa cak ya tsaya kan imaan, tun mgnr da tayi masa a office yake ta juyasa, a zuciyar shi yace na amince da zancen imaan ko na barshi?



Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] ‪+234 813 725 2431‬: [8/23, 6:49 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓


74_75



"Duk wani tunanin sa yarasa menene mafita. Qarshe tashi yyi daga kwanciyar side din omar ya nufa. "A falo ya tarad dashi. "Omar yana zaune kan kujera yana kallo. "Farooq ya qarasa da sallama sannan shima ya zauna yana kallo suna hirar su jefi2, can farooq yace bro wata shawara nakeson ka bani, omar ya tattara nutsuwar sa ga farooq yace INA jinka. "Faroiq yace kasan daddy ya matsa mana da zancen auren nan ko? Omar yace eh, farooq yace hala ka samu matar da zaka aura? Omar ya tabe baki yace kyale dadday ni ban shirya yanxu ba, farooq ya zaro ido yace sai yaushe kenan? Omar yace sai lkcn da nayi niyya. "Farooq ya girgiza kai yace kasan halin daddy fah kada ya kawo mana wasu matan Wanda ra'ayin mu baya wajen su. "Omar yace kaga malam idan auren nan zakayi kaje kayi danni ban shirya ba., bayan haka kaida kacemin na baka shawara meya kawo wannan zancen auren? Farooq yyi murmushi yace kwantar da hankalin ka, kasan shawarar da zaka bani? Omar yace saika fada. Yyi mgnr a takaice dan ya kosa yaji abinda zaice. "Farooq yace inason na auri _Imaan_ shin meka gani a kai? Whatttt.....ido wuru wuru omar ya zaro yana me kallon dan uwansa, can kuma ya kwashe da dariya yana nunashi da yatsa yace ah lallema bro, shin INA dukkannin 'yan matan ka suke? Masu ji da class? Manya dasu? Ka rasa wacce tunanin ka zai qare sai kan wannan tatsitsiyar yarinyar? Yaushe aka gama tsigeta daga shan nono?.... Farooq ya katse shi d fadin haba bro shawara nace ka bani bawai ka tsaya muzanta imaaa ba, omar da kyar ya tsaida dariyar d yake yace, kasan Allah wallahi ka cire zancen imaan a ranka dan Sam yarinyar nan ba class dinka bace, haba karka bamu kunya mana, kuma kasanme? Daddy bazai aminta da auren Ku ba kwatakwata sbd asalinsu bamasu hali bane, kaifa da kanka kke bani lbrin da kyar daddy ya amince da zaman yarinyar nan a gidan nan fah? Wallahi tun da sauran mutuncin ka wajen daddy ka janye wannan zancen inaga shawarar da zan baka kenan. "Farooq yyi shiru d alama zancen omar na ratsa kwanyar sa. "Can ya nisa yace shikenan na gode da shawarar ka. Omar yyi murmushi yace u r wlcm. "Anan sukaci gaba da hirar su.

****""
Bayan sati biyu, farooq ne ya samu daddy har dakinsa ya sanar masa zancen auren sa, daddy da murna yace wacece? Farooq yace amira 'Yar alhji mukhtar. Daddy yyi murmushi yace good naji dadi sosai, ai namiji idan yyi aure yafi martaba. Farooq dai ya sunkuyar da kansa, mummy dake gefe itama tayi murna tasa albarka. "Daddy yace toh dan uwan naka fah shi be fitar da matar bane? Farooq ya Sosa kai, yace be sanar dani ba daddy, daddy yace turomin shi. Farooq yace toh. "Bayan minti biyar yyi omar a falon daddy, daddy yace kai kuma fa ya mgnr naka auren? Omar ya Sosa kai yace emm daddy har yanxu ban samu wacce ta dace dani ba. "Daddy yace haka kace? Omar ya girgiza kai. Daddy yace ohk zaka iya tafiya. Omar ya tashi cike da farinciki ganin daddy be dau abun da zafi ba. "Bayan fitar sa, daddy ya kalli mummy yace yaronki yana wasa da mgn ta. Mummy itama da damuwa ta kalli daddy dan ta kosa ta fara ganin jikokin ta, tace toh Amman baka CE masa komai ba ya tafi, daddy yace shi yarone? Akanme zanyi ta maimaita mgn? Ga dan uwansa nan ya samawa kansa lpy ai. "Mummy tace yanxu wanne hukunci ka yanke next? Daddy yace akwai mata dayawa d suka nuna suna sonsa acikin su zan sama masa wata saidai yaji anyi masa aure, mummy ta nisa sannan tace Allah ya zabar da abinda yafi alkhairi daddy yace ameen.




Nuceey luv😘
[8/23, 8:24 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROO* ❓



76_77


"Omar kuwa yana fitowa a dakin daddy ya samu imaan a main falo tana kallon wani Indian film. Omar har zai wuce sai kuma ya dawo da baya ya rankwashi kan imaan, "imaan ba zato ba tsammani taji rankwashin har tsakiyar kanta. A razane ta juya tana kallon sa idon sa duk ya ciko d kwallah, "yah omar menayi maka dan Allah? Omar yace ban hanaki kallon Indian film ba? Imaan tace toh dannan kalla meye aciki? Omar ya zaro ido oh wato tmbyta kike miye aciki koh? Imaan tayi shiru, omar yace shikenan zan fadawa mummy kina koyon yanda kiss dan kiyi wa gateman, imaan ta zaro ido tace na shiga uku ya omar yaushe nace maka haka? Omar ya daga gira yana murmushi burinsa ya cika tunda ya sata kuka. "Imaan kuwa tashi tayi daga zaman da take ta kama rigar shi tace dan Allah ya omar karka Sanar wa mummy ni wlhy ban taba yima kowa kiss ba. "Omar yace kinaso na yadda? Imaan ta gyada kai, omar yace ohk biyoni, imaan tace toh. Haka tabishi kamar jela, side dinsa suka nufa, bayan sun shiga falon sa, yace jeki dakina ki gyara ki wanke toilet sannan kizo kiyi mopping, imaan ta kwalalo ido tace haba ya omar banyi maka komai ba fa, kawai ma shrrin k...da sauri omar ya kalleta yace sharri na miki. Tayi saurin girgiza kai, omar ya daka mata tsawa oya je kiyi abinda nace or na je na sanar mata, jiki a sabule ta tafi dakinsa tana mgn ciki2 Allah wannan yah omar din mugune, omar yace kikace me? Da sauri imaan ta qara saurin tafiyar ta fatan ta Allah yasa beji abinda tace ba. Shikuwa omar kallo ya kunna yana ganin news, "saida tasha wuya sosai kafin ta iya gyara gadon omar dan ma Allah ya sota, mummy tana koya mata badan haka ba ai da wuyar saitafi haka. "Saidai ta gama sannan ta komai toilet dinsa, komai tsaf2 yake a zuciyar ta tace mutum har mutum Amman sai mugunta data cika masa kwanya fisabilillahi meye abin gyara anan? Haka imaan ta cika kunfa a katon boket, sannan ta kwara duka toilet din, sannan ta Debi wani ruwan ta kwara haka tayi tayi har kumfan ya tafi, ganin haka ta lall6a ta fito a toilet din kadan ma ya rage santsi ya kwashe ta. "Falo ta tana haki, omar ta samu ya fara bcci, hamdala tayi sannan ta la6a6a tabar falon, tana fitowa ta tafi side din mummy a guje.


*****
Daddy ne ya tara su a falo yake sanar musu sun gama mgn d Abban amira zuwa nan d 2weeks za'a daura aure, mummy tace da wurwuri haka? Daddy yace toh me za'a jira ai idan akwai kudi sai ayi komai akan lkci basai an ja ba. Mummy tace Allah ya sanya Alkhairi daddy yace haka nakeson ji, "farooq dai yyi murna abinsa, shi kansa omar ya taya dan uwansa murna. Haka sukaci gaba da hirar su har farooq ya mike da nufin tafiya side dinsa dan kiran mutuniyar sa, Imaan CE ta tashi tabi bayansa, omar ma tashin yyi. "Lkcn da duk suka fita, mummy ta kalli daddy, tace alhji yanxu ya mgnr da mukayi ranar? Daddy ya hade girar sama data qasa yace zainab abinda ya Dade be kira ba kenan, yace tun muna shaida juna kada ki sake min wannan mgnr Sam banji zan iya ba, mummy ta sunkuyar da kanta tace Allah ya huci xuciyar ka banyi hakan dan 6ata maka raiba, Amman INA rokon ka da kasake tunani akai dan Allah, daddy ya 6ata rai batare d yace komai ba.
"Imaan har falon farooq ta nufa, saida suka zauna farooq yace my sisi yadai? Imaan ta 6ata rai tayi shiru. "Farooq da damuwa yace imaan yimin mgn mana. "Imaan ta fashe da kuka a rikice yace ya salam wani Abu aka miki? Imaan ta daga kai. Farooq yace waye? A hankali tace kaine ya farooq. "Farooq ya zaro ido yace ya salam menamiki? Imaan tace yah farooq ka daina sona gashi nan daddy yana mgnr auren ka da wata Amman bakace dani zakayi ba. "Dariya, mamaki, tausayi sukayi masa durar makiyiya a lkci daya, kwantar da murya yyi yace sorry my sis ba nufina haka ba, kinga yanzu kina Ss1 going to ss2 yaushe kika gama skul kikayi university kafin muyi aure? Ai kinada lbrin yanda daddy yace dole mu kawo mata a yanxu ko. "Imaan ta girgiza kai. "Farooq yace toh kiyi hakuri idan kika gama skul, a shekarar zamuyi aure, d gske? Ta tmbyeshi farooq yace yes, imaan sai alkcn ta saki ranta tana murmushi. "Shima farooq mutmushin yyi yana me mamakin wautar imaan, shi abin nata da wasa ya daukeshi Amman ga dukkan Alamu ita da gske take, wata zuciyar tace Allah ya kaimu lkcn saika aureta as second wife. Da wannan tunanin ya ajiye a zuciyar sa. Sannan sukaci gaba da hirar su yama manta da kiran wata Ameera.


*****
Shirin biki sosai akeyi yyinda aka shiga sanarwa a gidajen radio da talabijin, mutane sai mamaki suke wai duk yanda suke twins Amman wai daya ne zaiyi aure, haka dai masu surutu nayi, 'yan mata kuwa sai haushi sukeji duk Wanda sukayi dating da farooq zataso ace itace Matar sa, sai sukaga duk cikin su sun kasa gano wacece wannan amirar?
Toh nimadai nace wacece amira?
"Aisha ( ameera) kenan ya ga alhji mukhtar yarinya CE ajin farko, ga kamun kai da hankali, babanta yana daya daga cikin Wanda za'a jerasu a masu kudi, sun hadu da farooq ne lkcn data je hospital tana me ciwon Mara period dinta zaizo kenan, Amman yana wahalar da ita, koda taje a kunyace ta iya yiwa farooq bayani, shikuma farooq tunda ya kyalla ya ganta, yaji ta kwanta masa a rai, har ya kasa hakuri da dabara ya samo asalin inda take, cikin ikon Allah kuwa ya samu soyayyar ta, takaitaccen bayanin ta kenan.





Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] ‪+234 813 725 2431‬: [8/24, 5:56 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓


78_79



"Shirye_shirye ake, both gidansu ameera da farooq, farooq har gida ya kawo ameera suka gaisa d mummy, sosai mummy tayi farinciki dan ta lura yarinyar tanada hankali da nutsuwa, imaan kam ta saba da Anty ameera kamar sun dade, har gidan su tana zuwa tayiwa farooq rakiya, dake imaan sun sami Hutu sai bikin yazo mata a daidai, yawo sosai suke zuwa ita da farooq da ameera, itakam burge ta suke yanda suke tafiyar da soyayyar su. "Akwana a tashi babu wuya a wajen Allah, yauta ta kasance Friday inda dubban jama'a suka taru domin daurin auren farooq, 6angaren omar ma sosai yake taya dan uwansa murna, kowa sai mamakin sa ake shine babba Amman beyi aureba. "Shadda wacce tasha dinku ubansu, na hango taurarin sun fito daga side dinsu, duk yanda kaso ka banbanta omar da farooq, bazaka iyaba sbd tsantsar kyaun da sukayi, dinkin sosai ya amshi jikin su, abunka da basu saba sa babbar Riga ba, sai abin ya zama gwanin sha'awa son kowa kin Wanda ya rasa, cikin takun kasaita suka fito a side dinsu fuskarsu dauke da murmushi, "daidai lkcn imaan ta fito a dakin mummy, kwalliya sosai mummy tasa akayi mata, ba karamin kyawu tayi ba, make up dinnan yahau, ga daurin da akayi mata ya matukar karbar ta, saikace itace amaryar, fitowar kenan isowar su omar da farooq me camera na gefen su, masu kirari nayi, imaan na ganin su tayi sauri da nufin hugging din farooq, saidai ta kasa banbanta su, haka ta qarasa wajensu inda zuciyar ta ya bata, ba zato ba tsammani omar yaji imaan tayi hugging dinsa, dagowa tayi tana dariya tace kagani nayi kyau? Omar shime besan lkcn da yyi dariyar ba ai kamar jiran sa ake sai ganin hasken camera suka gani, dukkansu suka juya da sauri dan ganin Wanda ya daukesu camera man suka gani da farooq da shima yake riqe da waya yana, daukar su pic, juyowar su shiyayi daidai da qara musu pic din, raf-raf-raf aka hau tafi, wasu sai fadi suke ko sune amaren? Dan sun rasa waye farooq din. Hotunan da akayi musu ba qaramin kyau sukayi ba. Omar dai yyi murmushi batare da yace komai ba ya kama hannun imaan da take ta washe baki jin ance sunyi kyau duk azaton ta da farooq akayi mata photo. "Har dakin mummy ya kaita still ta sake cewa ya farooq bakace nayi kyau ba? Omar yyi mata shiru, sannan ya fara tafiya, imaan tayi saurin tashi kamar zatayi kuka tace nayi kyau? Kai ya daga mata da murmushi sannan ya wuce da sauri, imaan a zuciyar ta tace haladai yau axumin mgn kke. "Shikuwa omar yaso ya disga ta da niyyar sa ya tureta, Amman yana tsoron fadan mummy dan a falon ta abin ya faru, shiyasa ya samawa kansa salama bayan haka sosai ransa ya 6aci haddai ma hotunan da akayi musu saikace sune amaren, mwts yaja tsaki, mota guda suka shiga shida farooq dan zuwa daurin aure, abokansu suka hau wata motar, wasu kuma suka hau tasu omar, ma'ana daya yyi driving daya ya zauna a kujera me zaman banza. "Koda suka shiga be tankawa kowa ba sa6anin da dayake murmushi, farooq yana lura dashi saidai shima ya basar yana hira da abokan su. "Wanda yake driving din babban abokin farooq kenan, yace kai Amman fa omar kunyi bala'in kyau d wannan yarinyar fah, omar yanajin sa ya share shi, farooq yace kaifa dan iskane wannan sister mu ce, da sauri yace kai dan Allah? Farooq yace dgske, abokin ya kalli wanda me kujerar me zaman banza yace Yusuf d alama na samu mata a gidan su farooq fah. Sai alkcn omar yaja tsaki yace malam kayi abinda ke gaban ka bawai surutu ba ka wani cika mutane da surutu akan wannan yarinyar, wanda yake driving din yace aa kace rowar sister Ku zakumin, farooq yace ah karka damu idan imaan CE zamu baka, omar ya sake Jan tsaki a karo na biyu, shi haushin sa daya yarasa me suke gani jikin imaan da kowa zaice yana sonta, baya manta lkcn daya kai imaan skul, bayan ya ajiyeta har zai tada mota wani dake cikin mota ya fito da sauri yana masa alamar ya tsaya, "lkcn daya tsaya mutumin ya tmbyeshi imaan ko sister sa CE? Yace eh, bawani 6ata lkci ya fada masa tunda take zuwa Skul din yaji yana sonta kuma da aure, ya yaba da hankalin ta da nutsuwar ta da kuma kokarin ta. "Sosai omar yyita mamakin wannan mutumin, qarshe yace yyi hakuri kr2 zatayi, mutumin yace shi zai jira ko shekara nawa zatayi, cikin tsawar d be shirya yinta ba yace malam anyi mata miji, ai d sauri mutumin ya bashi hakuri ganin yanda ransa ya 6aci sannan yabar wajen., da wannan tunanin kala2 suka isa babban masallaci na Kano inda za'a daura auren farooq da amaryar sa ameera.







Nuceey luv😘
[8/24, 6:41 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓



80_81




"Tunda suka isa taron ake busa saikace 'yan'yan sarakuna kai duk wanda ya halarci bikin zai tabbatar was kansa lalle wannan auren bana wasa bane, manyan mutane harda shugaban kasar america ya hallaci wannan hamshakin daurin auren, makada da mawaka kam ai sai abinda yyi gaba, dan sun sami sun baje kolin su, "ba'a dau wani lkci ba aka fara sanarwa kamar yadda al'ada ta tanadar a musulunci, kowa ya shaida daurin auren _FAROOQ_ _DA_ _AMARYAR_ _SA_ _A'ISHA_ akan sadaki me inganci, habawa nan aka fara tafi da Sam barka abindai ba'a cewa komai. "Bayan minti biyar dakyar aka yi sanrwa a lasifiqa akan a saurara, "abinka da dubban mutane baka gane abinda ake cewa,
"Sanarwa aka sake yi, bayan haka mutane da shaidu sun shaida an daura auren farooq da a'isha haka mukeson su shaida an daura auren omar da amryar sa.... Arazane omar ya mike da sauri ya matsa kusa da daddy dake suna kusa, ya rike hannun sa cike da tashin hankali, bakinsa na rawa yace dan Allah daddy, kayi hakuri dan Allah karkamin haka daddy, daddy yyi murmushin sa irin na manya, sannan ya kalli me sanarwar yace ci gaba da abinda kke, farooq yana gefe shi kansa ya tausayawa bro dinsa dukda dai basusan dawa daddy zai hada auren ba. "Me sanarwa yabi umarnin dadi, ya cika aikinsa. "A firgice omar yake kallon daddy da matukar mamaki, anya yasan wacce ya aura masa kuwa? "Ba'a iya tantance yawan tashin hankalin da suka bayyana kan fuskar omar, mikewa yyi yabi cikin mutane fuskar nan babu alamar annuri, haka yyi ta keta mutane har yaje inda sukayi parking, toh Allah yaso shi akwai extra key a hannun sa, hakan ya bashi damar tuka motar a guje, "mutanen dake wajen kuwa sai mamaki suke, sundai ga an sanar frooq za'a daurawa aure Amman sai sukaga sa6anin haka, haka taro ya watse, farooq dai yaken dole yakeyi burinsa yaje ya duba inda omar ya tafi, yasan

Please Login or Register in order to submit comment