Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

GWARZON SADAUKI
Littafi Na Biyu (2)
Part A
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
AI'amarin jaruma Ilaila kuwa ko da ta ga an harbo kibiyoyi an kashe abokan tafiyarta guda shida nan take sai ta yi wuf ta suri garkuwarta da takobinta ta shammaci mai hular karfe ta gabza mata naushi a ka da garkuwar dake hannunta.
Saboda karfin naushin sai da mai hular karfen ta hantsila baya ta rinka mirginawa a kasa izuwa can inda koramar nan take. A lokacin ne aka ci gaba da harbowa Ilaila kibiyoyi amma sai ta dunkule jikinta waje daya ta kare jikinta da garkuwarta. Sai da ta ji kibiyoyin sun daina dira akan garkuwar tata sannan ta mike tsaye zumbur ta falfala da masifaffen gudu i zuwa cikin dajin Hairil Salas sakamakon ta fita daga cikinsa ta bi hanyar da Nazima ta bi!
Haka dai ta cigaba da gudu ba waige amma saita ci gaba da ganin ruwan kibiyoyin wasu suna wucewa ta samana wasu ta gefenta. Kawai dai tsananin sa'a ne da nisan kwana suka sa ko kibiya daya ba ta soke ta ba. Ba ta daina ganin ruwan kibiyoyi ba masu kawo mata hari har sai da ta shafe sama da rabin sa'a tana gudu. A wannan lokacin ne ta yi tuntube ta fadi kasa, ta dinga mirginawa a kasan da gudu ba ta ankara ba sai ji ta yi a fado kasa cikin wani rami mai tsananin zurfin gaske don haka sai ta kurma uban ihu lokacin da ta saddakar da cewar ajalinta ya zo.
Ba zato ba tsammani sai ta ji fanjam ashe cikin ruwa ta fado. Ko da tai nutse izuwa karkashin ruwan sai kanta ya bugu a jikin wani dutse nan take ta suma.
Hakika mai rabon ganin badi ko ana daka shi a turmi sai ya gani, maimakon Ilaila ta cigaba da nutsewa i zuwa kasan kogon da ta fada sai gashin kanta ya nannade a jikin jelar wani katon kifi da ya zo giftawa da gudu. Ai kuwa sai ya janyeta ya tafi da ita yana ta gudu har sai da ya iso gabar kogin sannan gashin kan nata ya warware daga jikin jelar kifin kuma sai ambaliyar ruwan ta hankadota wajen cikin rairayi.
A wannan lokaci alfijir ya keto an fara wata irin iska mai karfi da sanyi, wannan iska ce ta sa Ilaila ta fartado daga dogon suman da ta yi ta mike zaune a matukar firgice sannan ta dubi gabas da yamma kudu da arewa. Ko da ta liga inda take ta tund lokacin da tuntube ta fado kasan rami ta kalli kogin dake gabanta kuma ta hango hisan dake tsakanin gabarnkogin da can saman ramin da ta fado sai ta cika da tsananin mamaki
Ya ya aka yi har na iya ketare wannan kogin na iso nan? Amsar da Ilaila ta kasa bai wa kanta kenan amma sai wani abu ya fado mata a rai ta ce duk yadda aka yi suma na yi sa'adda na fada cikin kogin nan kuma akwai yiwuwar cewa wani ne ya kawo ni nan ko kuma wata dabbar ruwan ce ta janyo ni nan.
Gama ayyana hakan ke da wuya Sai ta hango kyallen wuta a can nesa sosai a bayan wani kogon dutse, da yake har a sannan gari bai|yi gaske ba sai Ilaila ta mike tsaye ta kama sanda ta nufi inda wannar hasken
wuta yake.
Sannu a hankali ta kusance wajen sai ta fara jiyo sautin muryar mutane da yawa suna a hira.
Sai da ta matso daf da su sannan ta labe a bayan kogon dutsen ta kasa kunne tana sauraron hirar da suke yi. Kawai Sai ta gane cewa ai wadannan mutane ba wasu ba ne face rukunin dakarun $umame na চiyu, kuma Shugabansu ne yake cewa "Ya zama wajibi mu yi shiri, mu bi bayan mayakan nan mata wadanda suka rage ba su mutu ba. Kun sani dai labarl ya riskenmu cewa a cikin su akwai wata shaidaniyat da ta fi shugaban yan rukunin farko iya yaki har ma ya ajiye mukaminsa ya bar
dajin nan. A halin yanzu yaransa sun kashe mutum $hida daga cikin mayakan matan, an harbi daya da kibIya a kafadarta amma tsere an nemeta an rasa. Ita ma Wannan hatsabibiyar cikin nasu ta gudu ba a ganta ba. Barita ce ta kawo mana wannan labarin kuma tanal cikin dajin nan tare da wasu daga cikin dakarun rukuni na uku suna farautar ta hatsabibiyar jarumar.
"Lallai duk inda take sai sun cimmata. Yanzu tun da mun yi kalaci sai ku tashi mu hau dawakanrnu mu ruga 1 zuwa can wajen dajin nan domin mu cimma mayakiyar da aka harba a kafada kafin ta isa birmin Misira saboda Sarki Marhat ya ce lallail kada a bar a ta fita a raye. Za mu bar mutum daya jal ya yi gadin komai namu da ke cikin wannan kogon dutse."
Gama fadin hakan ke da wuya sai shugaban dakarun sumame na biyu ya mike tsaye suma sauran yaran nasa sa Suka mike gabadayansu.
Nan take Suka debi makaman yakinsu suka hau dawakal suka bi hanyar da za ta fitar da su daga cikin dajin gabadaya Suka bar badakare guda daya jal zaune a kofar kogon dutsen yana gadi.
Sai da Ilaila ta tabbatar da cewa wadannan dakaru sun yi nsia da tafiya sannan ta cigaba da tafiyar sanda har ta iso bayan wannan badakaren da aka bari gadi bai ji motsınta ba, kawai sai ta hannayenta biyu tal kama kansa ta murde masa wuya, ta yar da gawarsa kasa.
Ckin anzari] ta cire tufafin Badakaren ta sauya da nata, kawai sai ta dauki gawar ta jefa bayan wasu duwatsu yadda babu mai gani ta.
Nan take Ilaila ta dauki makaman yakin badakaren da ta kasheh ta kwance dokinsa ta hayenkuma tajuya da baya, ta nufi hanyar da yan'uwansa suka bi!
Maimakorn laila ta bi sawun dawakan dakarun sai a bi wata hanyar daban wacce za ta iya shan kansu ta ci gaba da yi wa dokinta Kaimi. Ashe wannan hanyar da ta bi anan ne ragowar rukuni na hudu na dakarun Sumame suke kuma kowane rukun sansaninsu daban.
Tabbas zakaran da Allah ya nuta da cara ko ana muzuru ana shaho sai
ya yi. Da gudu bisa doki Ilaila rinka wuce sansanin dakarun sumamen har guda hudun sa dai kawai ta daga musu hannu su daga mata amman babu inda aka tsayar da ita. Dalili kuwa shi ne tana sanye da kakin dakarun sumame na biyu da kuma irin kayan yakinsu ajikinta.
Da yake gabadaya tukuni su shidan sun san junansu kuma sun san kalar tufafinsu da makamansu wannan yasa ta tsallake bincike.
Haka dai Ilaila ta ci gaba da gudu bisa dokinta ba sassauci har sai da rana ta kwalle. A daidaı lokacin ne ta iso iyakar daji da birnin Misira, kawai sai ta hango Nazima a guje bisa kafafunta ga dakarun sumame
bayanta bisa dawakai su ma a guje suna kokarin cimmata amma saboda karfin gudun nata sun kasa cimma ta.
Har i zuwa wannan lokaci akwai kibiya soke a kafadar Nazima ba a cire ta ba, amma saboda juri ya da jarumtaka ta kk yarda dakarun Sumamen su ¢immata.
Saura bai taku biyar ba wani Badakare ya cimma Nazima har ma ya kai mata sara da takobinsa ta sunkuya ya sari iska sai ta daka tsalle ta tsallake iyaka ta fada cikin yankin birnin Misira ta fadi Kasa da ruf da ciki.
Ko da ganin haka sai Dakarun Sumamen Suka kada linzamin dawakansu suka juya da baya suka koma inda suka fito.
Duk wannan abu da yake faruwa Ilaila ta buya cikin duhuwar ciyayi tare da dokinta tana kallo. Har dakarun sumamen suka zo suka wuce ta kusa da ita amma ba su ganta ba.
Ita kuwa Nazinma ko da ta ga dakarun sumamne sun hakura sun koma da baya ízuwa cikin daji sai ta yunkura da nufin ta mike sayc ta nufi cikin birnin Misira.
Kawai sai ji tayi an maketa ta baya. Nan take ta sulale kasa sumammiya. Ba wani ba ne ya maketa ba face jaruma mai hular karfe. Kawai sai ta sunkuya ta dauketa ta dora ta a kan wani doki da ta zoda shi sannan ta hau dokin ta kada shi ta nufi hanyar da za ta kai ta inda kurkukun mata yake na birnin Misira
Lokacin da Ilaiia ta ga abin da ya faru ga Nazima sai ta kada dokinta ta
nausa wani bangaren dabaru na dajin. A can cikin daji ne ta rabu da dokin kuma ta cire tufafin da ke jikinta na dakarun sumame ta sanya nata kuma ta rufe fuskarta, sannan ta sake dawowa kofar birnin Misira ta shiga cikin gari.
Sai da Ilaila ta shafe kwanaki goma sha úku tana boye cikin birnin Misira sannan ta yi shiri rana daya ta yi kundumbala ta haura gidan Sarkin Misira da tsakar dare domin ta kashe shi.
Wannan shi ne sanadin da aka kamata aka jefa ta cikin keken doki aka ka ta kurkukun mata na birnin Misira.
Daga wannan rana Ilaila ta ci gaba da rayuwa a cikin kurkukun birnin Misra. Duk bayan kwana bakwai sai Sarki Marhat ya kawo nata ziyara har kurkukun. Abin da yake gaya mata kawai shi ne, "Kin tuno inda mahaifinki ya boye littafin sirrina?" Idan ta ce 'a'a" ko kuma ta girgiza kai alamar cewa bata sani ba to ko kallonta ba ya yi sai kawai lya juya ya yi tafiyarsa.
Sau uku Ilaila tana guduwa daga kurkuku amma shugaban dakarun kurkukun Gadaraz yana bin ta ya kamota, ya dawo da ita kuma duk sa'adda ya dawo da ita sai an yi mata azaba ta tsawon sati guda.
Akaro na ukun ne da ya kamata suka yi kazamin artabu wanda kowannensu ya jigata ainun kuma ya kasa amfani da karfin sihirin tsafinsa a kanta sakamakon a ranar ya manta bai dauko kambunsa na tsafi ba ya daura karfin ya biyo sawunta.
Sa'adda suka yi kare jini biri jini suka zube akasal suna haki da numfarfashi a yanáyin da dayansu ba zai iya mikewa ba sai ya dubeta ya ce Wai ke mene ne dalilin daya sa ba za ki daina kokarin guduwa daga wannan kurkukun ba?
Ilaila ta dube shi ta ce "Saboda na san cewa wata rana zan iya tuna inda mahaifina ya boye littafin sirrin sarki kuma da wannan littati ne kadai zan iya daukar fansa a kansa. Kai kuma mene ne dalilin da ya sa ka tsaya kana bata lokacin ka kana bautar tsaron kurkuku alhalin käna da wannan karfi da jarumtaka kuma da sihirin tsafi haka"
Lokacın a Gadaraz yaji wannan tambaya sai ya yi ajiyar numfashi sannan ya dago kai ya dubi Ilaila ya ce 'Matsalata da taki kusan iri daya ce. Asalin masarautar garin han ta Kakannina ce, kakan Sarki Marhat ne ya kashe Kakana na biyu ya gaje karagar mulkinsa. Ba ni da wani buri a duniya wanda ya wuce naga na dawo da Wannan masarauta hannun zuri'ata to amma na san cewa abu ne wanda ba zai yiwu ba cikin kankanin lokaci.
Bisa wannan dalili ne nima tun ban fishekara tara ba a duniya na rinka
bai wa kaina horona yaki da jarumta kuma na rinka bin bokaye ina yi musu bauta, ina samun sihiri a wajensu domin na yi gagarumin shirin yin juyin mulki a kasar nan. A zaton sarki Marhat babu nutum daya da ya yi saura daga cikin zuri'ata alhalin bai san cewa ni ina raye ba.
Ke ma kin yi ganganci kuma| kin yi gaggawa da ki ka bayyana kanki a a
gare shi domin ba za ki ya samun nasara ba al yanzu. Yanzu idan na mayar da ke kurkuku za aci gaba da gana miki azaba ne irin wacce ta fi ta baya ni kuma ba zan iya jurar ganin hakan ba.
Ko da jin haka sai mamaki ya kama Ilaila ta dube shi tace "Mene ne dalilin da yal sa ba za ca ya jure ganin yi min azabar ba?"
Gadaraz ya ce "Saboda yanzu na gane cewa ciwo na irin naki ne don haka idan ana yi miki azabara cikin jikina zan rinka jin ta.
Baya ga haka tun ranar da kika fara guduwa daga kurkukun nan na biyo ki muka yi artabu na ga irin jarumtákarki sai ta burge ni kawai na ii ina kaunarki. A tsawon zamanki a kurkukun na wata tara kullum idan na ganki sai naji kina dadđa shiga raina, Ayau din nan da na san wace ce ke sai na ji na kamu da tsananin tausayinki gami da matukar kaunarki a zuciyata. Zan so a ce ki zamo abokiyar rayuwata tun da mundace da juna a jarumtaka da kuma kaddarar rayuwa".
Sa'adda Gadaraz ya zo nan a jawabinsa sai |laila ta kur amasa idanu nan take hawaye ya xubo mata Sannan take ta rungume hi tare da fadawa kan kafadarsa suka rungume juna.
Daga can saj Ilaila ta janye jikinta daga cikin nasa ta dube shi ta ce Yanzu mene ne abin yi?"
Gadaraz ya ce "Báza mu koma kurkukun birni Misira ba birnin Kisra za mu tati Sau uku sarkin Kisra yana yi mini tayin na je na kula da kurkukunsa zai rinka biyana albashi mai tsoka ninki ukun wanda Sarkin Misra ke ba ni amma naki saboda mafarkin dake raina na yin juyin mulki. Yanzu zanje na karôi wannan aiki, idan kin amince sai mu yi aure amma burinmu na nan na daukar fansa a kan Sarki Marhat kawai dai za mu cigaba da yin.bincike a kan yadda za mu sami nasarar cika burinmu."
Wannan shi ne asalin haduwan Ilaila da Gadaraz har suka yi aure a birnin Kisrai suka cigaba da rayuwarsu a wannan kurkuku.
Aranar farko da aka kawo jarumi Insam Gadaraz na yin arban da shi sai ya ga ai kamanninsa iri daya ne sak da na Sarki Marhat tamkar an tsaga kara. Hatta tsayinsu da kaurin jikinsu iri daya ne, abin da ya kara daure masa kai shi ne Insam na yin magana sai ya ji muyarsa ma irin ta Sarki Marhat ce.
Nan take wani tunani ya fado a zuciyar Gadaraz ya ce "Wannan mai laifin zai iya zama makamin da za mu ya cika burinmu hi da Ilaila a kan Sarki Marhat.
Lokacin da aka shigo da Insam cikin wannan kurkuku na birnin Kisra har Gadaraz ya zo wajensa ya gan shi Şuka yi magana ya tafi sai ya sami Ilala ya ba ta labarin Insam da ya gani yanzu kuma ya gaya mata cewa za su yi amfani da shi wajen cika burinsu. Nan take farinciki ya turnuke Ilaila ta daka tsalle ta fada kan kirjinsa suka fada kan gado anan barci ya sace su.
Karar wannan kaho da aka busa ne ya tashe su daga barcin. Lokacin da Gadaraz ya fito daga bangarensa na gidan kurkukun dauke dal makamansa na yaki yana mai falfalawa da gudu sai ya nufi inda ya ga dakaru na tafiya al guje, a hanya ne ya yi ta tsallake dakarun da su Insam suka banbanke zube a kasa fululu, wasu ma sun sami raunuka a sassan jikinsu sun kasa nikewa tsaye.
Kuyi hakuri kwana biyu shiru in sha Allahu ba zamu kara daukar long time irin haka ba fatan alheri gareku masoya masu bibiyar wannan littafin.

Ga masu son complete pdf zasu iya tuntubata ta Numberta har ma da wasu littattafan 08138873799GWARZON SADAUKI
Littafi Na Biyu (2)
Part B
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Insam da Barsad suka ci gaba da watsar da dakaru a kasa suna ta falfalawa gudu. Wani lokacin har tsalle suke yi sama suna hayewa kan katangu da rufin dakuna suna dira kasa. Kafin Gadaraz ya riskesu tuni sun iso inda rariyar gidan take wacce aka rufeta da shafen sumunti, cikinta kuma karfe ne na gorar ruwa mai kamar bututu, dogo ne mai tsawon gaske, gami da kauri kuma ya hade da wata korama dake bayan kurkukun.
Ko da su Insam suka iso inda wannan rariya take sai Insam ya dako tsalle sama daga inda yake ya dira a kan malalan sumntin wanda shi ne murfin rariyar sai ya zage iya karfinsa gabadayal ya naushi murfin rariyar. Wohoho! Wanda duk Allah ya bai wa karfi to sai dai Allah ya isa.
Insam na naushin wannan malalen sumuntin sai wajen ya burme ginin ya fashe suka fada cikin rariyar wacce ruwa ke gudu a cikinta.
Nan fa suka yi ta tafiya suluiu a cikin rariyar har zuwa karshenta inda ta watsosu cikin| wannan Korama dake bayan kurkukun. Ko da suka fado cikin koramar sai suka ga wani kwale-kwale karami daure a gabar koramar, ai kuwa sai suka y iyo izuwa wajen kwale-kwalen suka haura cikinsa suka kwance igiyar da ta tsai da shi suka tuka kwale- kwalen da sandunan tukinsu suka yi gaba.
A daidai wannan lokaci ne Gadaraz da dakaru suka fado cikin koramar. Ko da suka hango su Insam a cikin kwale-kwale sun yi nisa sai Gadaraz ya kwarara uban ihu. Kawai sai ya ga Ilaila ta fado cikin koramar daga cikin rarriyar itama.
Ilaila ta dago kai ta hango su Insam a can nesa cikin kwale-kwale sannan ta dubi Gadaraz ta ce 'Maigida yanzu mene ne abin yi?"
Maimakon ya ba ta amsa sai ya juya ya dubi mataimakinsa tare da saurar dakarun dake biye da shi ya ce "Ku koma kudauko dawakai ku je ku Sha kansu a can dajin Farwas. Ni da matata za mu haye koramar nan mubi sawunsu.
Ko da jin haka sai mataimakin gadaraz wato Saduaki Bartus ya dube shi çikin alamun damuwa ya ce, "Ya shugabana ni fa ina ganin cewa akwai lauje cikin nadi. Ta ya ya aka kawo kwale-kwale aka ajiye a nan.wurin alhalin ba a kawowa kuma a koyaushe dakarunmu na gadin har wajen amma yau babu ko mutum daya daga cikinsu. Ga su can ma kwance ga dukkan alamu kashcsu aka yi. Duk yadda aka yi wadannan fursunoni guda biyu da suka gudu sun sami hadin kan wasu murafukai daga cikinmų wadanda suka taimaka masu.
Ko da jin haka sai Gadaraz ya ce "Yanzu ba mu da lokacin yin wani bincike kawai ku je ku zartar da abin da na umarce ku da yi."
Bartus bai yi gardama ba sai ya juya, ya fice daga cikin koramar sauran dakarun na biye a shi suka koma cikin kurkukun domin dauko dawakai.
Gadaraz da Ilaila kuwa sai suka ýi iyo izuwa can gabar koramar $uka riski inda su Insam suka bar wannan kwalc-kwale. Da fitowarsu daga cikin koramar sai suka bi sawur su Insam suna masu falfala uban gudu.
Al'amarin Insam da Barsad kuwa tun da suka iso gabar koramar $uka fito daga cikin kwale-kwalen sai suka ruga izuwa cikin daji. Sai da suka yi gudun sa'a guda ¢ur sannan suka zube kasa bisa guiwoyinsu suka kama haki da numfarfashi sakamakon tsananin gajiya da suka yi a kokarinsu na fitowa daga cikin kurkukun da kuma gumürzut da suka yi da dakaru.
Barsad ya dubi Insam ya ce, "Yanzu dai ga shi mun $ami nasarar fitowa daga cikin kurkukur nan amma daga yanzu zuwa kowane lokacin dakaru za su ya isowa nận su cimmana ka ga kenan duk wahalar da muka sha a baya ta zama ta banza, domin ba za mu iya tserewa ba.
Insam ya ce Kamar yadda na baka nmamakl na cire rodunan tagar dakin da aka kulle mu kurna na gaya maka ta hanyar da za mu bi mu ficc daga cikin kurkukun wacce kai baka taba tunaninta ba a zuciyarka haka ma yanzu zan shirya mana yadda zamu kubuta. Za mu gaba da yin gudu na tsawon rabin sa'a kacal sannan mu tsaya. Shi inda za mu tsaya din anan gaba bishiyoyi ne a wajen ko kuwa duwatsu ne? Ka fi ni sanin haka tun da kai mutumin daji ne".
Barsad ya jinjina kai ya ce, "Bishiyoyi za mu riska masu tsawo da duhowoyi".
Insam ya ce "Da kyau" faduwa ta zo dadai da zama. Lallai a iya Tsawon gudun abin sa'a ne dakarun kurkuku za su riske mu domin a kan dawakai zasu biyo mu. Yanzu dole ne mu hanzarta mu isa inda bishiyoyin nar suke kafin su rigamu zuwa domin mu hau kan bishiya mu
buya inda zamu dinga yi masu daukar daidai. Abin da nakc so ta kal ১hine da zarar mun isa wajen, duk abin da ka ga na yi kai ma ka vi shi.!
Gama fadin hakan ke da wuya sai Insam ya falfala da gudu izuwa cikin dajin, ai kuwa sai Barsad ya yi koyi da shı.
Haka dai suka gaba da gudun babu waiwaye babu tsawa har tsawon cikar rabin saa sai ga shi sun iso wannan wuri mai dauke da dogayen bishiyoyi wadanda suka haifar da duhuwoyil sakamakon fadin ganyayyensu da yawansu.
Da isowarsu wannan wuri sai lnsam ya yi trujiya shi ma Barsad sai ya tsaya cak lokacin da Insam ya kurawa dajin idanu yana kallon gabas da yamma kudu da arewa
sannan ya dubi kasa. Ko da ya daga kansa sama sai kawai ya hango raga ta taho kansu.
Kafin su yi wani yunkuri tuni ragar ta lullube su sai kawai suka ga dakarun Gadaraz suna firfitowa daga maboyansu rike da masu da takubba kimanin su dubu sun kewayesu.
Gashi raga ta kanannadesu kuma g6 shi babu makami a hannunsu ko guda daya Insam ya dubi Barsad cikin alamun takaicj da bakin ciki ya ce Mun yi latti tunda sun rigamu isowa nan.
A daida wannan lokacin ne mataimakin Gadaraz sadauki Bartus ya fito daga inda yake boye yana kyalkyala dariyar mugunta sannan ya murtuke fuskarsa ya dubi Insam da Barsa ya ce, Mene he amfanin gudun da ba tsira. Ku sani cewa hukuncin kisa ne a kan duk wani fursunan da ya yi kokarın guduwa. Yanzu za mu

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment