Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

įso ya zamana cewa tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku hudu ba gama zura littafin a cikin ramin keda wuya sai mahafin Ilaila ya daskarc ya zama kamar kankara sannan ya dinga ruburbushewa yana zama gari. Koda ganin haka sai laila ta kurma uban ihu kuma ta fashe da kuka amma da taga Sarki Marhat ya nufota sai ta juya da gudu ta nufi inda mahaifinta ya umarceta saura taku daya ja!
Marhat ya cafkota da hannunsa sai ta daka tsalle ta fada cikin wannan ruwan daya kasance cibiyar wani kogi kuma daga inda tayi tsallen ta fada kasa çikin kogin ramine mai zurfin gaske wanda ya firgita sarki Marhat ya kasa yin kundunbalar ya bita.
Lokacin da llaila ta fada cikin wannan kogin tuni ta suma, cikin sa'a sai ta taso saman ruwa kuma igiyar ruwa ta nnga hankadota har ta isa bakin gaba indal wadandu masunta keyin su, anan sarkin masuntan kauye ya tsiceta inda yaga wata laya a wuyanta, koda ya bude layar sai vaga wata wasika a ciki, a cikin wasikar ne yaga wasiyyar da mahaifin Ilaila ya bari a gare shi daya ɗauki Ilaila sai ya kaita wajen wani mashahurin mayaki domin a bata horo ta jarumta da iya yaki
Koda Ilaila tazo nan a tunanin ta sai ta fashe da kuka. Cikin hanzari Gadaraz ya shiga rarrashinta kuma ya rungume akan kirjinsa, daga can sai ýa janye jikinsa ya dubeta yace nasan yanzu Kin gama tino komai kisani yanzu bamu da warni isasshen lokaci don haka kitashi mu hanzarta muje inda aka ajiye wannan littafin sirrin mu dauko shi saboda shi babban makamin da zai kaimu ga nasara. Koda jin wannan batu sai Ilaila ta mike tsaye zumbur ta্|juya da baya ta sauko daga kan wannan tsaunin da gudu ai kuwa sai Gadaraz, Insam da Barsad ma suka yi koyi da ita suna saukowa daga kan wannan tsaunin kowannan su ya kama dokinisa ya haye suma dakárun Gadaraz masu bakaken tufafi sai suka bisu a baya aka sukwani dawakai da guda aka nufi kogon hadaril Aswad, dayake Ilaila ce akan gaba suna isowa gaban kofar kogon sai ta tsayar da dokinta ta sauko kowa ma sai ya tsaida nasa dokin ya sauko kai tsaye ba tare da wata fargaba ba Ilaila ta kunna kai cikin kogon ta tsaya a bakin wannan gadar ta itace har sai da su Gadaraz suka žo suka risketa sannan tayi musu bayanin yadda za'a haye gadar ba tare da dayansu va fadđa kasa cikin wannan gagaruma wuta ya hallaka ba, tana gama yi musu bayani sai ta wuce da gudu ta kan gadar kamar yadd mahaifinta ya wuce da ita tana goye abayansa shekarun da suka gabata sa'adda tana yarinya karama, hatta gwarzon sadauki wato Insam saida ya firgital da ya kalli wannan gada.wadda wannan narkakken dutse ke
fasa acikinta da kuma nisa gami da zurfin dake tsakanin gadar da kasanta amma sai yavi ta maza yabi bayan Ilaila da gudu yana ma kiyaye taką wannan fararen itatuwan. Gadaraz ne ya zamo na ukun su sannan Bursad ya biyo su suma dakarun Gadaraz sai suka saida rai suka biyo su amma saida tsautsayi ya ritsa da mutum uku suka fada kasan gadar suke narke a ciki wutar ruwan dutsen, kai tsaye Ilaila ta nufi inda wannan teburin yake wanda mahaifinta yazura wannan jan littafin a cikinsa, da zuwanta sai ta iske littafina wajen kamar yadda suka barshi duk tsawon wadannan shekaru bai motsa daga inda yake ba amma kura da yana ta lullibe shi, batare da wani bata lokaci ba ta zura a cikin wannan ramin da littafin yake ta dauko shi, a wannan lokaci dakarun Gadaraz sun rude kuma sun Zauce bisa ganin Irın tarin dukiyar da ke cikin wannan kogon dutsea don haka basu san sa'adda suka fara bude rawaninsu ba suna zuba zinaren ba suna daurcwa gami da azawa a kansu, ilaila na gama zaro wannan littafin daga cikin wannan ramı da yake sai wasu irin munanan aljanu masu manyan bakuna da manyan jiki suka bayyana a gaban dakarun Gadaraz suka dinga yimusu hadiyya daya kamar mutum ya jefa gyada daya a bakinsa ya lunkume, kuma nan take dutsen ya fara tsatsagewa daga sama yana rushewa gami da zubowa kasa, da kyar da sidin goshi Ilaila, Gadaraz, Insam da Barsad suka ruga izuwa inda cibiyar ruwanan yake nan take, bayan duwatsu sun farfado musu sún sami raunika a jikinsu, suna isa wajen suka daka tsalle su fadawa cikin wannan kogi a matukar galabaice, nan fa suka yi yita iyo har suka kai gabar wannan kogin. Suna fitowa ne sai suka ci karo da sarki Marhat tare da dubunnan dakaru bisa dawa kai dauke da makaman yaki a gabansu. Sarki Mahat ya dubi Gadaraz da su insam ya bushe da dariyar mugunta sannan ya mikawa Ilaila hannu yace bani Littafina, tabbas duk wahalar da kuka kun sha ta zama a banza, domin nahiyar nan gaba daya ta zama tawa dan haka dukkanin ku kun zama bayina.

AlhamduLillahi Yan Uwa da abokan arziki Allah Ya nufa mun kammala exam lafiya sai kuma jiran sakamako, ina matukar godiya da addu'o'inku a gareni Allah Ya bar zumunci da kuma kauna. Sannan wannan shine page na kusa da karshe inda daga next page Littafin Gwarzon Sadauki na biyu ya kare sai kuma mu shiga wani littafin amman kasancewar zamu shiga azumi sai mu bari sai bayan sallah sai na baku jerin Littattafan dake gareni sai ku zabi daya daga ciki.

Na gode maku Allah Ya biya wa kowa bukatarshi ta alheri, AminGWARZON SADAUKI
Littafi Na Biyu (2)
Part F
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey

Ilaila ta tari numfashinsa tana mai cewa idan kaga na baka wannan littafin to sai |dai idan bana numfashi a doron kasa. Sarki Marhal ya ce ai kuwa yanzu zaki daina numfashi.
Tsulum sai Gadaraz ya shiga gaban Ilaila ya dubi sarki Marhat ya ce ba sai ka kashe taba da hannunka za ta baka wannan Littafin. Gadaraz ya dubi Ilaila yayi mata wata inkiya, batare da wata gardama ba sai ta nufi inda sarki Marhat ya ke rike da littafi da nufi zata mika masa, saura baifi taku uku kacal ta isa gareshi sai aka gaan harbor wata kibiya daga can samar wani katon dutse, kibiyar tazo ta cake a tsakanin Sarki Marhat da Ilaila take kowa ya dago kai ya dubi inda kibiyar nan fa suka hango rundunar sarki Zarmal bisa dawakai a sukwane sun durfafo su, babu wanda yayi wani motsi har rundunar ta iso kusa da su suka yi turjiya aka fara kallan kallo, daga nan sai sarki Zarmal va dubi sarki Marhat yace yau ne rańar raba gardama ranar da Karshen gaba zata zo, ranar da daya daga cikin mu zai mallaki wannan nahiya gaba daya, tabbas dole ne a yau daya daga cikinmu zai cika mafarkinsa, yanzu haka ana can ana yaki tsakanin sarkin yaki na da naka, kai a zaton kun shirya dabarar da zuku iya karar da mutanena cikin kankanin lokacin? To ina so ka dauko madubin tsafinka ka ga qbinda ke faruwa domin kare jin biri akeyi, duk tarkunan da dakarunka suka danawa dakaruna ba su afka ciki ba. Koda jin wannan batu sai sarki Marhat yayi sauri ya dauko madubin tsafinsa daga cikin aljihunsa ya shafeshi nan take yaga abinda sarki Zalmar ya fada shike faruwa, al'amarin daya daure masa kai kenan amma sai ya bushe da dariyar mugunta, sannan ya ce koda mayakanka da nawa sunyi ragas, to kayi sani cewa anan ni ne zanyi nasara akan ka, maza ku shiya ga maza nan bisa kanku. Nan take sarki Marhat ya zaburi dokinsa da gudu izuwa tawagar sarki Zalmar, ai kuwa sai sauran dakarunsa suka rufa masa baya, nan ta aka hade aka cakume aka kuma ruguntsume da azababben yaki, karar karafa da ihun mazaje gami da haniniyar dowakai ta cika dodon kunne, yayin da kura tatashi ta turnike sararin samaniya Ilaila, Gadaraz, Insam da Barsad kuwa sai suka dunga yaki da kowanne bangare saboda sukare kansu kuma su tsirar da littafn dake hannun Ilaila, nan fa suka fara kokari ficewa daga cikin taron yakin amma sai abu ya gagara, domin duk inda suka nufa sai suga ambisu du... ana yan yame su ana kawo musu sara da suka ta ko ina, idan da ba kowannensu ya kasance gawurtaccen jarumi ba da tuni an gama dasu, sai da aka shafe rabin sa'a ana wannan bakin gumurzu sannan da kyar da sidin goshi kuma da karfin tsiya Gadaraz, Insam da Barsad suka budawa Ilaila hanya ta fita daga cikin taron dakarun da ake yakin dasu ta gudu tare da nausawa cikin daji.
Koda sarki Marhat ya kyalla idanu ya hangota sai kawai ya tashi sama kamar tsutsu ya biyota, kwatsam sai yaga Sarki Zarmal ma a sama ta gabarsa, tare da tare masa hanya kai kace fuka-fukai ne da dasu, nan fa kowannansu ya daga takobinsa ta yaki suka hade a sama suna masu kai wa junan su sara da suka cikin bakin zafin nama da jarumtaka, duk sa'adda ta kubbansu suka hadu sai kaga tartsatsin wuta na tashi gami da Karar saukar aradu, kasa kuwa ta ringa jijjiiga tana tsawa saboda karfin sihirin tsafinsu, duk sa'ada da dayan su yayi kokarin yabi bayan Ilaila da gudu ya kamo ta don ya karbe littafin sihirin sai dayan ya sh gabansa suci gaba da yaƙi. Gadaraz, Insam da Barsad kuwa sai suka kara kaimin yaki suka ci gaba da bazaar da dakarun dake gabansu, a haka har suka samu suka kwace dawakai suka haye nan fa suka zaburesu da gudu izuwa inda Ilaila ta nufa. Ilaila na cikin gudu ne sai ta hango Gadaraz bisa doki a guje ya tabo garetal kawai sai ta tsaya tana jiiran isowarsa, koda ya karaso sai ta daka wanki wawan tsalle ta haye bayan dokin nasa suka cigaba da gudu su Insam na biye dasu haka suka baro rundunar yakin Sarki Marhal da ta Sarki Zarmal ana ci gaba da fatatatawa.
Su Gadaraz basu dirfafi ko ina ba sai birnin Misira inda a hanyarsu ta zuwa sunzo wani dajı nan ma suka ga anata artabu gami dq azababben yaki tsakanin rundunar sadauki Darkis da rundunar sadauki Inzam, a wannan lokaci yakin ya dau zafi sosai babu abinda ido ke gani face zubar maza a kasa jini kuwa na malala tamkar idaniyar ruwa ce ta balle. Ba tare da jiran komai ba su Gadaraz suka ratsa cikin sansanin yikın da gudu bis dawakai suna masu kai sara da suka ga dakarun birnin kisira, take kuwa suka murkushe dakarun birnin kisira gaba daya ya zamana cewa babu mutum ko đaya da ya rage a cikinsu. Bayan kurar ta lafa ne sai aka zauna ana jiran dawowar $u sarki Marhat, ana cikin wannan jira ne kwatsam sai ga wani ragowar yaki ya dawo jina jina akan doki, yana mai fitar da numfarfashi da kyar, to daman a wannan lokacin da su Gadaraz suka kawowa su sadauki Inzam dauki, koda suka ga su Insam sai suka zata cewa sarkin sune Marhat ya kawo masu dauki kasancewar kammaninsu iri daya ne, don haka suna cike da kwarin gwiwa gami da farin ciki suka karasa wannan yaki, inda ba a dauki wani dogon lokaci ba suka murkushe dakarun birni kisira, da isowar wannan ragowar yakin sai ya fado daga dokinsa sa Inzam ya ruga gareshi tare da dago kansa ya dubeshi ya ce me ake ciki acan fiIin yaki?
Ragowar yakin ya bude baki dakyar yace sarkin mu da sarkin birnin kisira sunyi ragas, sunyi ragas, sun zama gawa.
Inzam ya dakawa ragowar yakin tsawa yana mai cewa shin kayi hauka ne, ai ga sarkinmu can ya dawo a raye zaka ce ya mutu.
Ragowar yakin nan ya dubi Inzam yace wancan ba sarkin mu bane, kama dai suke yi da shi.
Kafin Inzam ya juyo yayi wani abu tuni Gadaraz ya harbo masa kibiya ta sokeshi a wuya ta bullo ta keyarshi, take va fadi kasa matacce. Koda ganin haka sai ragowar dakarun Inzam suka mika wuya tare da zubar da makamansu na yaki.
Batare da 6ata lokaci ba su Gadaraz su ka dunguma izuwa cikin birnin misira suna zuwa gidan sàrautar aka bude musu kofa suka kunna kai ciki, basu tsaya a ko ina ba har cikin turakar gimbiya.Sulaisa inda suka isketa tana ta faman sharar kuka.
Ko da Sułaisa ta dago kai ta ga Insam, Gadaraz, Ilaila da Barsad tsaye a gabanta sai ta firgita kuma ta kamu da matukar mamaki.
Da ta ga Insam ta zata Sarki Marhat ne amma kuma me ye gaminsa da wanda ya ci amanarsa ya gudu da me laifi Ilaila? Gimbiya Sulaisa tayi wa kanta tambayar da bata da amsarta.
Ko da suka fahimci halin da take ciki sai Insam ya dubeta cikin murmush ya risina gami da girmamawa ya ce, "Ranki ya dade sunana Bawa Insam, kiyi sani cewa azzalumin Sarkin da yake son ya aureki tuni ya dadc da zama gawa a filin yaki.
Sa'adda Sulaisa taji wannan batu sai ta murtuke fuska ta ce Ta ya ya zan aminta da ku, tun da babu mamaki kaine Sarki Marhat kana so ka yaudare ni ne kawai?"
Gadaraz ya ce Ai ko zai yaudareki ba za iya tare da ni ba, tunda kin san ko wayel ni? Gaskıya ya gaya miki Shi ne Bawa Insam mai kama da Sarki Marhat wanda ya lashe gasar jarumtakar da aka yi a tsakanin bayin ranar da aka vi shagalin bikin aurenki a birnin Kisira. Yanzu zan nuna miki cikakkiyar shaidar da za ta tabbatar miki da cewa Sarki Marhat ya mutu".
Yana gama fadin haka sai ya juyo ya dubi Ilaila ya yi mata inkiya. Nan take Ilaila ta zura hannunta a cikin aljihu ta dauko littafin sirrin Sarki Marhat ta nunawa Sulaisa.
Nan fa Sulaisa ta kama yin murmushin farin ciki. A daidai wannan lokacin ne daya daga vikin amintattun dakarun Gadaraz ya shigo cikin turakar ya risinawa Gadaraz ya ce, "Ya shugabana komai ya kammala na zo da abin da ka umarce ni, kuma gabadayan 'yan majalisar garin nan ga su can sun taru a kofar fada ku kadai ake jira.
Ko da jin wannan batu sai Gadaraz ya yi murmushi, sannan ya dubi su Insam ya ce Ku zomu je can." Nan take suka dunguma gabadayansu suka nufi kofar fadar birnin.
Da zuwa suka iske gabadayan fadawan Marigayi Sarki Marhat da jama'ar gari a tsaitsaye an yi cirko-cirko cikin halin jimami da wasu-wasi. Wasu suna tunanin cewa Sarki Marhad ya mutu tunda labari va zo cewa gabadayan dakarun da va fita da su an kashe su babu daya a raye, amma kuma da aka ga Bawa Insam sai mutane suka shiga rudani.
Nan take su Gadaraz kuka zo gaban jama'ar gari suka tsaitsaya. Kawai sai aka ga dakarun yakin Gadaraz kimanin su dari biyar a saman katangar gidan sarautar a tsaitsaye sun kewaye gidan gabadaya, kuma sun dana kibiyoyi a kan baka sun ritsa kowa.
Kawai sai Gadarad ya dubi fadawan tsohon Sarki da kuma mutánen gari ya ce, "Ya ku jama ar birnin Misira kuyi sani cewa sarkinku ya dade yana tafiyar da mulkin zalunci a kasar nan. Yana sa muku haraji mai yawan gaske yana kuma kwace muku amfanin gona. Ya tara dukiya mai tsananin yawan da babu mai kamarta a nahiyar nan gaba daya. Amma wannan dukiya ba ta amfanarku da komai. To ku sani daga yau karshen wannan zalunci ya zo. Sarkinku Marhat ya mutu ga shaida zan nuna muku.
Gadaraz ya dubi wani Badakare dake kusa da shi sai Badakaren ya miko masa wata jaka.
Take Gadaraz ya bude jakar ya ito da abin da ke ciki ya daga sama kowa ya gani.
Ba komai ne wannan abu ba face kan Sarki Marhat".
Nan fa jam6aa suka dimauce aka kama ka-ce-na-ce. Gadaraz ya yi tsawa aka yi tsit sannan ya nuna Insam ya ce.
Wannan shi ne Bawa insam mai kama da sarkinku Zuciyarsa ta adalci ce yana kuma da tausayi, ba shi da komai hakazalika shi ba dan kowa ba ne talaka ne kamar kowa. Daga yau shi ne Sarkinku, don haka Sabon sarki sabuwar rayuwa."
Ko da jin wannan batu sai suka rude da shewa gami da tafi. Gadaraz ya daga hannu sama aka yi tsit sannan ya dubi fadawan Sarki.Marhat ya ce 'Duk wanda baya goyon bayan wannan sabuwar daula yana da zabi biyu ko ya hada kayansa ya bar gari ko kuma ya fito fili yana nuna adawarsa. Idan kuwa ya Munafurce mu hukuncin kisa ne a kansa.
Da jiin wannan batu sai gabadayan fadawa gami da yan majalisar tsohon sarki suka daga hannayensu Sama suka ce "Muna goyon bayan wannan daula ta adalci."
Nan take wuri ya hargitse da sowa aka fara kade-kade da raye-raye. Asannan ne su Gadaraz suka koma cikin gidan Sarautar suka Zauna.
Gadaraz ye dubi Sulaisa ya ce, "Shin kina son sabon Sarinku a daura maku aure da shi"
Sulaisa ta yi murmishi ta ce Ai yanzu șhi ke da zabi tun da shi ne Sarki.
Insam ya yi murmushi ya ce, Tun ranar farko sa'adda aka kawo ki a cikin keken doki kika zuro santala-santalan kafafuwanki waje, sannan na yi arba da kyakkyawar fuskarki sai ji da ganina suka dauke, zuciyata ta kama bugawa da karfi yanayina ya sauya, na nemi yawun da zan hadiya a bakina na rasa. Ba komai ne ya haddasa hakar ba face tsananin sonki da na kamu da shi farat daya. Ina mai neman amincewarki da ki yardarki domin mu zamo miji da mata.
Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye, yana mai kallon Sulaisa cikin murmushi kuma ya mai bude hannayensa. Kawai sai Sulaisa ta mike tsaye tana kallonsa daga can kuma sai ta ruga gareshi ta fada kan kirjinsa suka rungume juna.
Take Gadaraz, Barsad da Ilaila suka kama yi musu tafi. Ana cikin haka ne Gadaraz ya kama hannun Barsad ya ja shi gefe daya ya dube shi ya ce "Birnin Kisra ya zama naka. Yanzu za ku tafi kai da dakaru kaje, ka kar6i karagarka. Bayan daurin auren Insam da Sulaisa da kuma bikin sarauatrsu za mu halacci bikın naka sarautar. Ka sani ba ka taba yin abin kirki ba a rayuwarka sai.wannan karon da ka yaki zalunci ka kafa adalci. Lalla adalcin za ka ci gaba da yi a kan karagarka idan kuma ka yi sabanin hakan ni da Insam zamu hada kai mu hambarar da gwamnatinka."
Barsad ya yi murmushi ya ce "Ba zan taba kaucewa umarninka ba ya shugabana, tun da ba don kai ba har abada a kurkuku zan gama rayuwata. Yanzu ga shi ka mayar da barawo ya zama Sarki kuma adali. Ni da Insam duk ka mai da mu sarakuna kai kuma me ye makomarka?"
Sa'adda Barsad ya ji wannan tambaya sai ya yi murmushi ya ce, 'Ni ba ni da sauran wata bukata a duniya tun da in tare da matata muna zaune lafiya. Burina daya ne jal daga nan har mutuwata na ga zaman lafiya da adalci ya tabbata a tsakanin al'umma a wannan nahiya. Duk sarkin da ya kau daga kan umarninmu zamu kawar da daularsa. "
Ko da jin wannan batu sai Barsad ya yi murmushi ya ce "Na rantse da darajar iyayena da kakannina zan vi mulkina bisa gaskiya, adalci da tausayin talakawa".
Cikin murna Gadaraz ya rungume Barsad suka yi bankwana. Sannan Gadaraz ya janye jikinsa daga cikin na Barsad ya juya wajen Insam shi ma ya rungume shi suka yi sallama yana mai dagawa amarya Sulaisa hannu.
Nan take ya je ya kama dokinsa ya hau, dakaru dari biyu suka yi masa rakiya suka fice daga cikin binin Misira.
Kashegari aka daura auren Sulaisa da Sarki Insam aka sha shagalin bikin aure gami da nadin sarauta.
Kamar yadda aka yi wannan biki na sarauta a birnin Misira haka aka yi na Sarki Barsad a birnin Kisira cikin kwanciyar hankali da lumana.
Daga wannan rana zaman lafiya, gaskiya da adalci ya wanzu a wannan nahiya gabadaya, har izuwa tsawon wadansu shekaru masu dan yawa. Daga bisani bayan shudewar dattawan kwarai irin su Sadauki Gadaraz sai al'amura suka sauya aka samu azzaluman Sarakuna suka fara hawa kan karagar mulki.
A birnin Misira wani gawurtaccen sarki ne ya kwace karagar mulki da karfin tsiya ya kashe sarkin dake mulki da dukkanin ahalinsa sannan ya kashe gabadayan yan majalisarsa ya nada sababbi wadanda yake so, sannan ya fara tunanin hanyar da zai bi ya mallake manyan kasashen dake nahiyar.

AlhamduLillahi Anan muka kawo karshen wannan littafin sai kuma mun hadu da ku a wani sabon Littafin na Abdulaziz Sani Madakin Gini Mai suna Birnin Sadaukai Ko kuma Taskar Tsafi zuwa bayan sallah idan Ubangiji Ya nufemu da kaiwa.

Domin sauke cikakken Littafin a Wayoyinku na hannu ko kuma karantawa sau ku danna bulun Rubutun dake ƙasa ko kuma hoton 👇👇👇👇

https://aihausanovels.com.ng/litattafan-yaki/gwarzon-sadauki-littafi-na-1-complete-document-by-abdulaziz-sani-madakin-gini

Ga masu son dauko Littafin Complete ga link dinsa nan a sama ko kuma ku tuntubeni ta wannan Number 08138873799

Ku huta lafiya Masoya 🥰🥰🥰
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment