Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kirjinsu suka sauke ajiyar Zucıya, sannan suka shige cikin turakar suka kulle kofar.
Bayan sun zauna ne Rasimat ta kawowa Sulaisa abinci da abin sha ta ci ta koshi sannan ta dube ta ta ce "Tabbas idan kika kảl ni cikin kuyangin dake yi wa Sarki hidima da zarar ya kalli idanuwana zai shaida ni, ni kuma a ƙalla ina bukatar kwana bakwai kafin na gano abin da nake son na gano."
Sa'adda Rasimat ta ji wannan batu sai ta kyalkyale da dariya ta ce "Kwantar da hankalinki ya shugabata. Dabara ba ta karewa mai neman tsira. Na san yadda zan yi ke dai kawai ki zuba ido ki sha kallo."
Kafin sa'a guda ta cika Rasimat ta zabo kuyangi guda goma sha daya sai ta yi musu ado iri daya da na Sulaisa sak, sannan kafin ta fito da Sulaisa daya cikin furakarta sai da ta sauya mata launin gashin kanta na ainihi daga baki zuwa ruwan kasa yadda babu wanda zaigane cewa launi aka sauya masa, sannan ta bata wani abu ta sanya shi cikin kwayar idanunta.
Take kalar idanunta suka sauya Sulaisa ta fito daga cikin turakar Rasimat ta jero acikin kuyangi goma sha daya suka tsaya reras a sawu guda Rasimai ta zo ta tsaya á gabansu sannan ta sanar da su yadda za su tafiyar da ayyukansu a turakar Sarki daga nan ne ta wuce gaba suka bi ta abaya har cikin turakar sarki.
Sarki Marhat na zaune bisa wata shimfida ta alfarma a tsakivar turakarsa sai ga shi an shigo da kuyangi guda goma sha bivu suka jeru a gabansa suka risina suka kwashi gaisuwa sarki Marhat ya mike tsaye ya fara kalonsu daya bayan daya yana matsowa gaba a hankali har ya zo daf fa Sulaisa wacce ita ce ta biyun karshe a layi. Ya dubeta da kyau amma sai ya wuce gaba ya kurawa ta karshen idanu sannan ya juyo ya dubi Rasinat ya ce "Aikinki ya yi kyau su fara nasu aikin."
Ba tare da bata wani lokaci ba Rasimat ta raba kuyangin gida uku ta nuna musu irin ayyukan da za su gabatar. Shi kuwa Sarki Marhat sai ya koma kan shimfidarsa ya kishingida aka kawo masa kayan ciye-ciye da na shaye-shaye amma ko kallonsu bai yi ba sai ya daga kansa Säma yana kallon rufin falon. Ga dukkan alamu dai tunani yake yi, kuma yana cikin damuwa mara misaltuwa.
Ku da ganın haka sai Rasimat ta taho gareshi ta zauna a gefen hagunsa ta dube shi ta ce, Ya shugabana kamar kana cikin damuwa da rashin walwala, shin akwai wata matsala ne?"
Sa'adda Sarki Marnat ya ji wannan tambaya sai yayi murnushin yake ya ce 'Ya ke shugabar| kuyangi ki yi sani cewa tun daga ranar da aka nemi masoyiyata Sulaisa aka rasa a cikin gidan nan sai farin ciki da walwala suka kaurace mini. Na tura yan leke asiri izuwa duk biranen dake nahiyar nan su gano min ko wane ne ya Saceta amma ko duriyarta ba ajii ba. Nayi amfani da karfin sihirin tsafina don gano inda take duk a banza. Ni dai
zaton da nake yi wanda ya saceta ya kasance gawurtaccen matsafi kuma babban makiyina."
Lokacin da Rasimat taji wannan batu sai ta yi ajiyar numfashi ta ce Ya shugabana ga yadda soyayyarku ta kasance ta gaskiya kai da Gimbiya Sulaisa babu wani mahalukin da ya isa lya raba ku face mútuwa."
Da jin haka sai Sarki Marhat ya bushe da darıya al'amarin da ya yi matukat baiwa Rasimat mamaki kenan Kawai sai ta ga $arki Marhat va murtuke fuskarsa ya dubeta ya ce, "Ba ki san sharrin makiya ba.
Yanzu haka wanda ya saceta ya gaya mata gaskiya da karya kuma ya nuna mata hujjojin da zai sa ta gamsu cewar ni ba mutumin kirki ba ne, don haka za ta iya tsanata a rana kuma a lokaci guda."
Rasinat ta ce Haba ya shugabana ai ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi, kuma so ba karva ba ne."
Cikin fushi sai Sarki Marhat ya mike tsayesayd zumbur ya dubi Rasima ya ce Tabbas So gaskiva ne amma yana |ya juycwa ya zama kıyayya. A halin vanzu Suiaisa ta daina sona tunda har ta amince da maganar da makiyi na Gadaraz wanda ke shirin daukar fansa a kaina ya fada mata.'
Ko da jin wannán batu sai zuciyar Rasimat ta buga da karfi jikinta ya kama tsuma. Ita ma Gimbiya Sulaisa da ke cikin bayi ta yi bad-da-kama tana ta aiki såi Zuciyarta ta kama daka. Kawai sai suka ga Sarki Marhat ya baro inda yake ya durfafo inda Suiaisa take, Yana zuwa sai ya cafkk kevarta ta baya da hannunsa, ta kurma ihu sannan ya dube ta kuma ya waigo ya dubi Rasimat ya ce, "Ke munafuka kina zaton za ku iya yaudarata ne? Na karfinku kuma na fi karfin makiyana. Tabbas ni azzalumi ne, na kashe talakawan da ba su da laifin komai, haka ma attajirai da masu mulki don kawai na mallake abin da suke da shi, ko kuma domin jin dadina da nishadina. Ke Sulaisa ki sani cewa Babanki ma yaudararsa na yi da batun neman aurenki ba shirya gasar dukiya ta hakan ne na sace dukkan dukiyar da aka tara a wajen gasar da kuma ta 'sa wacce ya boye a įnda ya ke zaton babu wanda ya sani. Yanzu na mai da shi matsiyacin Sarki bai sani ba.
Aurena da ke kuma ya zama wajibi gobe-goben nan za a sha shagalin bikinmu."
Yana gama fadin hakan sai ya tafa hannunsa sau biyu Nan take wasu dakaru guda biyu suka shigo Cikin falon, ya dube su ya ce, Ku kama munafuka Rasimat ku kai ta kurkuku, gobc bayan an gama shagalin bikina da Sulaisa za a yanke mata hukuncin rataya."
Ko da jin haka sai Rasimat ta kurma ihu, ai kuwa sai dakarun suka kamata da karfin tsiya suka fice da ita daga cikin falon, Ita kuwa Sulaisa sai ta doke hannun Sarki Marhat daga jikin keyarta ta waigo, ta dube $hi a fusace ta ce Tabbas abin da Gadaraz ya fada mini a kanka gaskiya ne. Ka tabbata azzalumi kuma butulu, ma ci amana To ka $ani zalunci baya dorewa kuma ina mai tabbatar maka da cewa sai dai ka zauna da gawata a gidan nan."
Sarki Marhat ya kyalkyale da dariya ya ce "Duk abin da na shiryawa rayuwata shi ke faruwa. Ba a sarrafa ni sa dai ni na sarrafa wanda na so."
Nan take Sulaisa ta yunkura cikin zafin nama ta ciro wata takobi da ke rataye a jikin bango ta daga sama da rufin ta caka a cikinta amma sai hannunta ya kame a saman ta kasa motsa shi.
Sarki Marhat ya kyalkyale da dariya sannan ya sa hannunsa va karbe takobin daga hannunta, ya dube ta ya ce "Ai jikinki namu ne sai dan haka babu wani abu zai same shi face da yardarmu.
Şhige ki tafi turakarki ki kwanta ki huta. Ba zan zo miki ba sai gobe đa daddare bayanan gama shagalin biki."
Ai kuwa sai Gimbiya Sulaisa ta juya ta fice daga falon Sarki ta nufi tata turakar kamar yadda ya umarca ta. Tabbas tsafi gaskiyar mai shi ne. Gabadayan kuyangi da hadirnan dake cikin wannan falo na Sarki Marhat sai da suka cika da tsananin mamakin karfin sihirinsa þisa yadda ya gano duk irin shirin da Rasimat da Sulaisa suka şhirya da kuma yadda vake sarrafa Sulaisa tamkar rakumi da akala.
Wannan Shi ne abin da va faru a birnin Misira bayan Gadaraz ya mayar da amarya Sulaisal ainihin ga masovinta Sarki Marhat wanda a halin yanzu ya babban makiyinta a duniya.
A can fadar Sarki Zarmal na birnin Kisira kuwa yana zaune ana tafiyar da harkokin fada cikin nishadi, wasu yan mata na rawa a gabansa ana buga wani kidan taushi sai ga Sadauki Bartus ya shigo da sauri fuskarsa cike da alamun damuwa Da zuwansa kusa da karagar Sarki sai va zube kasa bisa guiwarsa guda lokacin da masu kida suka dainab'yanmatan dake rawa suka tsaya cak, fadar ta yi tsit tamkar babu mai rai a cikinta.
Sadauki Bartus ya budi baki kansa na sunkuye ya ce Ya shugabana. Gadaraz yaci amanarka. Ya kashe dakarunmu kuma ya taimakawa insam Barsad sun sami nasarar guduwa daga kurkuku. Koda jin wannan batu sai sarki Zamral ya bushe da dariyar farin ciki al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan a fadar, sannan Zamral va murtuke fuska ya mike tsaye daga kan karagarsa ya dubi sadauki Bartus ya ce ai dama wannan ranar nake jira ya kai Bartus kasance wa wani lokaci yazo wanda zan mallaki birnin Misra. A duniyar nan kaf bani da makiyin da yafi sarki Marhat na binin misra ni da shi munyi kunnen doki a karfin mulki arziki da kuma karfin sihiri tsafi. Kowannan mu so yake ya kawar da daya domin va mallake komai nasa, tun tsawon shekaru bakwai baya amma mun kasa Gadaraz shine mutumin da zai tai maka mini na sami lagon sarki Marhat, na sata amarya Sulaisa daga hannun sarki Marhat shi kuma Gadaraz va saketa daga hannunsa na mayar da ita wajen marhat matar Gadaraz wato jaruma Ilaila itace kadai wadda tasan inda littafin sarki Marhat yake kuma itama ta manta inda yake, amma zata iya tunowa idan wani abu ya faru makanancin wanda ya bata labari inda aka ya boye littafin. Ya zama wajibi nayi gagarumin shirin yaki nabi bayan su Gadaraz ba tare da sun san da cewar ina biye da su ba har sai sun đanko wannan littafin daga nan naje na yaki sarki Marhat
na kasha shi na mallaki kasar sa, dukiyarsa dama amaryarsa sulaisa, matsala ta guda daya ce yanzu, gobe daura aurensa da Gimbiya Sulaisa lallai ina son na tsayar da wannan daurin auren domin bana son ya kwanta da ita kafin na gama dashi, lokacin da sarki Zamral yazo nan a jawabinsa sai fadar tayi tsit aka rasa wanda zai kala. Daga can sai wazirin sarki zamral yayi gyaran murya ya dube shi yace ran sarki ya dade ai wannan abu ne mai sauki, kawai rundunar yaki zaka tasa ta isa kofar birnin misra a gobe da sassafe a aikawa sarki Marhat takardar yaki, kaga kenan batun bikin aurensa ya rushe tunda tashin hankali va zo sannan kai da wasu dakarun daban sai kabi bayan su Gadaraz a sirrance. Koda jin wannar shawara sai sarki Zamral ya sake bushewa da dariyar farin ciki sannan ya dubi wazirin sa yace tabbas duk wanda yariga ka kwana dole ne ya riga ka tashi wannan shine amfanin zama da manya, ga shi a cikin kankanin lokaci ka bani shawarar da itace kadai mafita. Sarki zarmal ya dubi sarkin yakin sa dake tsaye a gefe guda yace ya kai dirka birnin kisira maza kaje ka shirya dakarun yaki kaso biyu, kaso na farko kaine zaka jagorance su izuwa kofar birnin misra ku vaki Sarki Marhat kaso na biyu kuma ni zan jagoran ce su Mubi sahun su Gadaraz sarkin yaki Darkis yace angama ya shugabana.
A can daji bayan su Gadaraz Sun gama yarjejeniya akan dayansu bazai ci amana ba sai Gadaraz ya dubi Ilaila yace lokacin da kina yarinya karama wane abu kika fiso, kuma wane abune yafi baki tsoro?
Koda jin wannan tambaya sai mamaki va kama Ilaila ta dube shi tace saboda me kayi min wannan tanbayar?
Gadaraz yace dole a cikin wannan abubuwan guda biyu zaki iya tuno labarin da mahaifin ki ya baki dangane da inda aka boye Iittafin sirrin sarki Marhat. Ilaila tayi shiru tana tunani har izuwa tsawon yan dakiku sannan tace a rayuwa ta ina son hawa tsauni da shiga cikin kogon duwatsu abin da yafi bani tsoro a cikin wannan duniya shine nayi arba da aljani ko dodo mummuna. Gadaraz yace da kyau mun sami mataki na farko na ga0e inda zamu sami wannan littafin, dole ne muje inda kogon duwatsu suke da kuma tsaunika mu shigesu mu kuma hau kansu, wannane kawai hanyar da zai sa ki tina inda aka ajiye littafin sirrin da muke nema, tabbas inda aka ajiye littafin aljanu
da ko dodanni ke gudinsa. Ku sani bamu da wani isashen lokaci don haka kuzo muyi sauri mutafi izuwa wannan wurare. Gama fadin hakan keda wuya sai Gadaraz ya mike tsaye ya kama dokinsa ya hau, cikin sauri sauran yarana masu shigar bakaken tufafi kimanin su dari suka yi koyi dashi, ai kuwa sai Insam, Barsad da Ilaila suka mike suka kamo nasu dawakan suka hau aka dunguma gaba daya aka nausa cikin daji. Gadaraz ne akan gaba yana yi masu jagora.
Al'amarin sarki Marhat na binin misira kuwa ashe kifi na gani ka mai jarkoma. Duk abubuwan da suka faru a fadar sarki Zamral da wanda suka faru a daji tsakaninsu Gadaraz sarki Marhat ya gani a madubin tsafinsa, don haka sai ya kyalkyale da dariyar farin ciki. Lokaci guda sai yace ai ni murucin kan dutsene ban fito ba sai da na shirya, tabbas sarki zarmal yayi kuskure da kake tunanin cewa zaka iya yaudarata da yaki sannan ka tafi izuwa inda littafin sirrina yake ka dauko shi, duk da cewa nima kaina bansan inda littafin yake ba amma ai gashi a saukake za'a kaini inda yake, naga ta yadda ko su Gadaraz zaku iya mallakarsa alhalin ina wajen. Koda gama wannan batu sai sarki Marhat ya tura aka kirawo sarkin yakin birni nasa mai suna sadauki Inzan ya dubeshi ya ce ya kai Inzam dama ka kwana biyu baka motsa jiki ba.

AlhamduLillahi naga addu'o'inku yan uwa, kuma ina godiya matuka Allah Ya saka maku da alheri ga karin kumallo nan.

Allah Ya cika mana burikanmu na alheri 🙏🙏🙏
GWARZON SADAUKI
Littafi Na Biyu (2)
Part E
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey

To ka sani abokin hamayarka sadauki Darkin na birnin kisira ya đebo dakarun yaki sun taho izuwa nan birninmu domin su yake mu, so suke su iske mu has nan kofar gari, abinda nake so da kai shine kaima ka debi dakaru masu yawa kaje kutaresu a can daji kuma ku dana musu mugayen tarkuna da zasu hallaka kafin ku hada jiki dasu, ma'ana kuyi musu yakin sumame da mamayar bazato, koda jin wannan koda jn wannan batu sai farin ciki ya lullube sadauki Inzanu saboda damá ya dade yana so yayi ramuwar. akan sadauki Daskin na kisira bisa dan uwansa uwa daya uba daya daya kashe a wani yaki da akayi shekaru biyar baya, don haka ya dubi sarki cikin murna ya ce ya shugabana ina mai tabbatar maka da cewa zan shiryawa dakarun birnin kisira tuggun yakin da dayan su bazai tsira ba kuma wannan sine karo na karshe da zamu yi yaki dasu domin birnin nu ya zama namu. Koda jin haka sai sarki marhat ya bushe da dariyar farin ciki yace maza kaje ka fara shiri nima.yanzu Zanyi nawa domin bin bayan $arki Zamral izuwa inda littafinsa na sirri yake domin kawo karshensa gaba daya.
Sadauki Inzam ya risina yace angama ya shugabana, nan take ya juya da sauri ya fice daga cikit dakin. Sarki Marhat sai ya fara kira sunayen wadansu aljanu, kwatsam sai ga wasu zaratan matasan aljanu acikin shigar yaki dauke da makamai masu ban tsoro, suna ratsowa ta saman gini suna sauka a gaban sarki Marhat suna masu kwasar gaisuwa.

A can sai da su Insam suka shafe kwanaki biyu da yini guda sannan suka iso wannan daji mai dauke da manyan tsaunika da manyan kogunan duwatsu, da iso warsu wannan waje sai sai suka tsayar da dawakansu suka sauko suka daure su a jikin bishiyoyi, faruwar hakan keda wuya sai suka ga Ilaila ta kama kallon wani guri ta hanga can ta kalli nan, daga can kawai sai ta durfafi wani tsauni kai tsaye, koda ganin haka sai Gadaraz yabi bayanta da sauri ai kuwa sai Insam da Bushrad ma suka biyo su, yayin da Ilaila taci gaba da tunkarar tsaunin sai kuma ta kara sauri | daga bisani ma ta fita da gudu hart a isa kan tsaunin suma su Gadaraz suna biye da ita, koda isa kan tsaunin sai ta tsaya cak ta kura wa wasu duwatsu guda biyu idanu wadanda aka ajiye a wajen nan take sai hawaye ya zubo mata ta tsuguna bisa gwiwoyinta ta shafa dutse daya a cikin duwatsun, koda ganin haka sai Gadaraz ya tsugunna kusa da ita ya dubeta yace shin kin tino da wani abu ne?
Ilaila ta dubi Gadaraz lokacin da hawaye ya ci gaba da zubo mata tace ni da mahaifina mun ta6a hawa kan tsaunin nan har muka zauna a kan duwatsun nan guda biyu.
Cikin murna Gadaraz ya ce ina son to ki kurawa duwatsunan biyu idanu ki yi kokarin tino da duk abin da ya faru tsakaninki da mahaifinki lokacin da kuke zauna a wannan wuri.
Koda jin baka sai Ilaila ta dafa dutsen da mahaifinta ya zauna sannan ta rintse idanuwanta ai kuwa nan take tafada kogin tunani.
Suna zaune akan duwatsun biyu sai mahifinta ya dauko salkar ruwa ya samata a baki ta sha, sannan shima ya sha sakamakon kishit ruwal da kuma da gajiyar tafiya da suka sha, sa'adda idanunsa suka ciko da kwalla yace yake yata ki sani inda zamų yanzu wajene mai hatsarin gaske, zan iya rayuwa kuma zan iya mutuwa amma bamu da wani zabi wanda ya wuce muje wajen, in ba haka ba wanda ke biye da mu zai riskemu koma yakashe ni ko ya rabani da wannan littafin, nan take mahaifin Ilaila va sa hannu cikin aljihun rigarsa sai ya dauko wani dan karanin jan littafi ya nuna wa Ilaila inda sarki Marhat ya boye dukiyarsa mai tsananin yawan gaske kuma yana dauke da sirrin sa na tsafi wanda dole saida shi da shi ne kadai za'a iya hallaka shi, kuma duk wannan dukiya daya tara nine sanadinta Hakazalika duk sihirin daya samu nine sanadi kuma nine kadai na sani a fadin wannan duniya. Bisa wannan dalili ne yake so ya kasha ni kema kuma kama ki zaiyi yanzu daga nan zamu je kogon badarel anwar inda zan boye wannan litattafin a gaban idonki idan kin rayu zaki iya zuwa ki dauki littafin domin ki kawo.karshen sarki Marhat bisa cin amanata da yayi, idan kuma baki rayu ba shikenan shi ma har abada ba zai sake mallakar littafinsa ba kuma sai ya mallaki littafin a hannusa sannan zai iya samun nasara akan abokan gabarsa har ya cika burikansa. Lokacin da mahaifin Ilaila yazo nan jawabinsa sai ta dube shi tace,
Yakai Abbana to akan me kake fadamin cewar ba zaka rayu ba, alhalin gaka yanzu a raye ina tare da kai? Mahaifin Ilaila yace ka'idar wannan littafi shine duk wanda ya kai shi cikin kogon Hadara aswar ya ajiye shi indai ba mamallakasaba rmutuwa zai yi, kuma ba bu wanda zai iya sake daukoshi face jininsa. Amma ke zaki iya dauko shi nan gaba babu abi da zai sameki. Sa'adda mahaifin Ilaila yazo nan a jawabinsa sai Ilaila ta fashe da kuka kuma ta rungumeshi tana mai cewa ya kai Abbana saboda me zaka sallamar da rayuwarka don kawai kakai wannan littafi kogon Hadaru Aswar. Dajin wannan tambaya sai ya janye jikinsa daga ciki nata sannan ya dubeta cikin nutsuwa yace nayi hakane domin ceto rayuwar miliyoyin jama'ar da sarki Marhat yake zalunta. Idan ban rabashi da wannan littafi ba to nan gaba sai ya mallake nahiyarnan gaba dayanta, kuma mulkin zalunci zai yi ta dorarwa kema ba zakiyi rayuwa mai kyauba. Kafin Ilaila ta budi bakin ta kara cewa wani abu sai kawai suka hango sarki Marhat bisa doki tare da wasu dakarun yaki acan nesa kadan sun darfafo wannan tsauni da suke kai! Nan take Mahaifin Ilaila ya mike tsaye zumbur ya suri Ilaila ya goyata a bayansa yasa Mayafi va daureta ta tamau sannan va falfala da gudu yana mai sakkowa daga kan tsaunin ya nufi wata hanya da tanufi çikin kungurimin daji mai dauke da manyan duwatsu, koda su sarki Marhat suka hango mahaifin Ilaila goye da 'yar sa ya tunkari cikin wannan daji a guje sai suma sukal karawa dawakan su.kaimi domin su cin musa, amma sai suka kasa saboda gudun nasa na sihirine. Ai kuwal sai shima sarki Marhata ya fara amfani da na shi sihirin na tsatin ya zamana dawakansu na iya tsallake duwatsu da bishiyoyi tamkar kibiyoyi ake harbowa, $ai da aka shafe rabin sa'a ana wannan tseren gudun tsakanin mahaifin Ilaila da sarki Marhat amma basu riske shi ba, gashi suna harbo masa kibiyoyi sai dai sun kasa samunsa har suka isa bakin| kogon| Hadari Aswad. Da zuwa sai mahaifin laila ya kunna kai cikin kogon ba tare da tsoron komai ba yana goye da Ilaila.
Mutum na shiga wannan kogo zai ga wani katon rami a kasansa mai tsananin zurfin gaske dauke da wata gadace a saman ramin wacce aka yi ta da itatuwa, dole sai mutum yabi ta kan wannan gadar sannan ya wuce kana ya isa cikin wannan ainihin kogon dutsen inda aka ajiye kayayyaki na dukiya da sihiri marasa adadi, ba tare da shakkar komai ba mahaifin Ilaile ya wuce da gudu takan wannan gadar yana kallon kasa kuma yane tsalake wasu itatuwa wanda ba a takasu, domin idan mutum yayi kuskuren ta kasu zai subuto kasa gadar ya halaka saboda wata irin gagaruma wuta ce a kasan ramin take zabalbala har da narkeken dutse a cikin ta.
Mahaifin Ilaila na cikin yin gudu akan wannan gada sai yaga sarki da dakarunsa sun shigo a guje sai suka tsaya a bakin gadar wace aka yi tada itatuwa, kuma itatuwan sun tsufa ga dukkan alamu baza suyi kwari ba, sai hankalinsu ya dugunzuma jikinsų va kama kyarma kawai sai sarki Marhat ya ratse gefe guda ya dubi badakaren dake bayansa sai yace
maza ka ruga ka riske su ka kasheshi ka dauko min wannan yarinyar da littafin dake hannunsa, ciki tsoro bisa dole badakaren ya ruga kan gadar aikuwa taku na uku sai icen da ya taka ya karye ya sullubo kasan gadar yana mai kurma ihu. Koda ya isa can kasa cikin wutar nan sai suka ji kara soyewarsa tamkar anjefa nama a tafasashen man girki, nan fa saurar dakarur suka fisgita ainur suka fara Kokarin jada baya amma sai Sarki Marhat ya daka musu tsawa tare da cace duk wanda ya yi yunkurin guduwa zan kure masa kudunsa kuma in halakashi da hannuna, sajin haka sai dakarunsa suka tsaya kawai sarki Marhar ya ci gaba da umartarsu suna rugawa kan gadar har saida mutum tara suka hallak sannan ya tsayar da sauran ashe yana lurane da abinda yake sasu Hallaka, wani farin ice ne ba'a takawa daga cikin itace, idar kuwa mutum ya takashi take -zai sullulibo kasan ramin, nan take sarki ya sanar da sauran dakarunsa wannan matsalar sannan ya fara wuce wa da gudu ba tareda ya taka farin ice ba ya nufi inda su Ilaila suke, aikuwa suma sauran dakarun sukayi koyi dashi, koda mahaifin Ilaila ya hango su sarki Marhat sun biyo su sai yakara karfin gudun har ya įsa karshe gadar ya dira cikin kogon hadari Aswar. Yaci gaba da gudu a cikin kogon bai tsaya ba, ga tsubi tsubin dukiyoyi nan kamar su Zinare, luu u'u, jauhar da sauransu ko kallonsu bayi ba har $aida ya iso gaban wani teburi na karfe wanda a tsakiyar sa akwai wani dan karamin rami sannan ya
tsaya ya kwanto Ilaila daga bayansa ya ajiye ta a gabansa ya kalleta kallon karshe a lokacın da hawaye ya zubo masa yace yake 'yata anan nake miki ban kwana domin ni nazo inda mutuwa zata rabamu da zarar kin ga na sa wannan littafi a wannan raminki gudu ki nufi can kudu karshen sa akwai cibiyar ruwa ta kogi kawai ki yi tsalle ki fada ciki, nasan tun kina yar shekara hudu na fara koya miki iyo a ruwa kiyi iya yinki har ki isa gabar rowan idan kina da rabon rayuwa zaki rayu har ki dawo nan ki dauki wannan Iittafi idan kuma baki da rabon rayuwa to shi kenan koba komai mun hana sarki Marhat cika babban burinsa a rayuwa, yana gama fadin hakan sai ya zura wannan littafin cikin wannan ramin dake kan wannan tebur din adaidai wannan lokacin sarki Marhat suka

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment