Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

RIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Shida (6)
Part A.
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Labari Ya Isowa Shagala Cewa
Marubucin Yaci gaba da cewa.....

Badakaren ya kawo
gwauron numfadhi ya ajiye sannan yace ai
muna rabuwa da kai na taho iZuwa nan
dakina domin na yi shiri na tafi izuwa
cikin gari don cika umarninka. Na juya
baya ina sa tufafina sai na ji an turo
kofar dakin nan an shigo. Katin na
waigo naga mai shigowa sai ji nayi an
gabza mini naushi a kan kunnena na
hagu. Daga nan ban san abin da ya faru
ba sai farkawa nayi na ganni a kwance
da rub da ciki kuma a daure.
Kafin badakare ya gama rufe
bakinsa tuni Zamaru ya nike tsaye ya
ruga waje da gudu. Wannan shi ne abin
da ya faru a cikin gidani sarautar sarki
Taryan bayan dare ya raba a ranar da
jaruni imhal ya lashe gasar lambun
jarumta a zagaye na hudu,
Al'amarin jarumi Imhal kuwa sa
da ya shafe kwana biyu a kwance yana
cikin natsananciyar rashin lafiya da
jinya ba tare da ya ma san wanda ke
kansa ba.
A tsawon wadannan kwanaki babu
mai shiga cikin dakin da aka ajiyeshi
face sarki Taryan da likitansa. Ita kanta
gimbiya Shumaira babu yadda bata yi ba
akan sarki Taryan ya amince mata ta
shiga taje ta ga lafiyar Imhal amma ya ki.
Babban abin da ya dada dugunzuna
hankalinta shi ne gaba daya ta daina
ganin Muzaira a tsawon kwanakin biyu
bare ta toketa ta shigar da ita inda aka
6oye jarumi Imhal kuma bata san dalilin
bacewar Muzaira ba.
A wannan dare na biyu ne kafin
daren ya raba jarumi Imhal ya dawo
cikin haiyacinsa har ya bude idanunsa.
Yana bude idanun nasa ya yi arba da
sarkí Taryan da likitansa zaune a
gabansa kawai sai ya yunkura ya mike
Zaune, yana shirin mikewa tsaye kenan
sarki Taryan ya ce, kada kayi
Kwakkwaran motsi domin dinkin da na
yiwa raunikan jikinka zai iya farkewa kuma
kaga raunikan basu gama
warkewa ba.
Ko da jin
wannan batu sai kwallar
takaici ta zubowa jarumi Imhal ya du
ikitan sannan ya dubi sarki Taryan ya
ce, na gaji da wannan gasa haka kuma
na gaji da irin bakar wahalar da nake sha
don baka lallai gobe da safe nake son na
yi wasan karshe da sarki Gurzalu domi
na kawo karshen komai, ko ni ko shi
Ina son na sami'yancin kaina haka na
gaji da ganin jinina na zuba.
Ko da gama fadin haka sai jarumi
Imhal ya yunkura cikin zafin nama va
hankade sarki Taryan da likitansa daga
gabansa suka zube kasa sannan
takarkare ya kwarara uban ihu wanda ya
sannan ya
Cika gidan sarautar gaba daya da amsa
kuwa. Hatta sarki Gurzalu dake tsaye a
Can cikin turakarsa sai da zucivarsa ta
buga da karfi sakamakon jiyo wannan
sautin ihu domin ya gane muryar mai
ihun ba ta wani bace face ta jarumi
Imhal. nan take ya cika da tsananin
mamaki bisa yadda akayi jarumi Imhal
ya
Sami lafiyar da har zai iya yin
Wannsn uban ihu a vanzu
Saboda ihun da jarumi Imhal ke yi
sai dinkin raunikan jikinsa suka rinka
farkewa amma kuma sai gashi raunikan
sun warke babu inda jini ya tsattsafo.
Al'amarin da ya yi matukar baivwa
sarki Taryan da ikitansa mamaki kenan
Imhal ya ci gaba da kwarara ihu
yana zarya. a cikin dakin tankar
mahaukacin tsohon rikakken zalki
wanda ya fusata ainun a cikin daji.
Sai da sarki Taryan ya taso da
sauri ya kama jarumi Imhal da karfin
tsiya ya zaunar da shi kasa sannan ya
shiga rarrashinsa yana bashi baki amma
Imhal bai nutsu ba sai da sarki
Taryan ya amince da batun cewar
gaba da gasar kambun jarumta gobe da
safe.
A cikin wannan dare kuwa aka
yada labarin ci gaba da gasar kamnbun
jarumta gobe da safe.
Ai kuwa nan da nan labari ya bazu
a ko ina birni da kauye, mutane suka
rinka cewa lallai jarumi Imhal ba mutum
ba ne, aljani ne shi don babu yadda za a
yi ace mutum ya warke daga iin
mugayen raunikan da ke jikinsa guda
shida.
Al'amarin gimbiya Lamrita kuwa
tun daga lokacin da ta sami nasara
kufcewa daga hanun su sarkin yalki acan
birnin Kisra ta fada cikin daji. bata
saurara ba da gudu akan doki don gudun
kada su sarkin yaki su biyo bayanta su
cimmata saboda ta san cewa sarkin yawa
yafi sarkin karfi. idan suka yi mata
rubdugu zasu iya cafketa su je su jefataa
cikin kurkukun da ba za ta iya guduwa
ba.
Lamrita bata yada zango ba sai da
ta ga dokinta ya gaji likis kuma itama ta
gajin kuma yunwa da kishirwa sun fara
galabaitar da ita sannan ta tsaya a bakin
wata korama ta sauko daga kan dokin
suka kama shan wannan ruwa ita da
dokin nata.
Da yake tana tsoron kada cikinta
ya kulle sakamakon yunwar da take ji
sai ta sha ruwan dan kadan.
Ita dai wannan korama tana da
zurfi amma bata da fadi sosai kuma
mahada ce ta ruwan wani katon kogi da
ke can gaba a cikin daji.
Kash rashin sani yafi dare duhu.a
she dai dai wurin da gimbiya Lamrita ta
tsuguna tana shan ruwa akwai wata
murtukekiyar macijiya mai kauri da
tsawon gaske wacce ta yi lambo a
AA Misau ke Magana
Karkashin ruwan, kawai jira take Allah
ya kawvo wata dabbar mai tsautsayi
shan ruwa ta yi kalaci da ita saboda
tana cikin matsananciyar yunwa. Ko do
Lamrita ta gama shan ruwa ta mike zata
kama dokinta su bar wajen sai kawai taji
an fincikota izuwa cikin ruwan da Karfin
tsiya, kafin tayi wani yunkuri macijiyar
ta fara kanannade kafafunta ta kasa
zuwa kugunta ne ta sa hannayenta ta
tokare macijiyar.
Nan fa suka kama kokowa suna
nutsewa izuwa kasan ruwan Suna
dagowa sama Suna ta birgima,
Sakamakon nutsewar da suke yi izuwa
kasan ruwan sai Lamrita ta fara
galabaita saboda daukewar numfashinta,
gashi dai suna ta fafatawa ita macijiyar
ta kasa karasa kanannadeta ita kuma ta
kasa samun damar zare wuka ko
takobinta ta cutar da ita.
A daidai wannan lokaci hankalin
gimbiya Lamrita ya dugunzuma ainun
domin karfinta ya fara karewa ta san
cewa da zarar macijiyar ta karasa
kanannadeta zata karya gaba dayan
kasasuwan jikinta ta hadiye ta.
Nan take Lamrita ta cire kai ga
samun tsira ta saddakar da cewa lokacin
mutuwarta ya yi.
Kwatsam sai ga wani matafiyi bisa
wani dogon rakumi sanye da fararen
tufafi ya zo giftawa. Matafiyin ya rufe
fuskarsa, idnaunsa ne kadai ake gani.
Ko da ya ga abin da ke faruwa sai
ya dako tsalle sama daga kan rakumin,
tun kan ya fado kan macijiyar ya zaro
wata sharbebiyar wuka kawai sai ya
sokawa macijiyar wuka a idonta guda
Take idon ya fashe, macijiyar ta yi wani
uban ruri saboda tsananin zafi da zogin
da taji a sa'adda iini ya kama shatatowa
kasa, ba ta san sa'adda ta saki Lamrita
ba saboda dimaucewa, ai kuwa sai ta
koma kan wannan bakon matafiyi shima
ta fara kanannadeshi amma sai ya yi wuf
ya kama jelarta da hannu guda kuma ya
wuyanta da daya hannun ya
warware nadewar da tayi masa a hankali
da karfin tsiya.
Nan take kwanjin hannayensa suka
kumburo har hannun rigarsa ya yayyage
saboda tsabar karfin damtse nasa. Tuni a
wannan lokaci gimbiya Lamrita ta fito
daga cikin koramar da kyar tana jan ciki
saboda tsananin galabaitar da tayi.
tana numfarfashi
Ko da ta ga irin tsananin karfin
wannan matafiyi da ya kawo mata dauki
sai ta ci gaba da kura masa idanu tana
kallon gumurzun da yakeyi da wannan
katuwar macijiya a cikin ruwa. Tun da
gimbiya Lamrita ta zo duniya bata taba
ganin mutum mai kirar sadaukai ba da
tsananin karfi kamarsa domin duk
girman macijiyar sai ga ta hannunsa ta
kasa kufcewa.
Ana cikin wannan artabu ne taga
jarumjin ya daga macijiyar sama ya tabe
hannayensa yana mai kwala kabbara.
Nan take ya tsinke macijiyar ta dare gida
biyu ya yi jifa da gawarta a cikin ruwan.
Saboda tsananin mamaki
gimbiya Lamrita ta sandare kamar
gunki, baki a bude, idanu a kafe ta kura
masa idanu ko kiftawa ba ta yi har ya
fito daga cikin koramar ya zo daf da ita
ya tsuguna sannan ya kwaye rawanin da
ya rufe fuskarsa da shi suka yi arba da
juna yana mai yi mata murmushi.
sai
Ko da gimbiya Lamrita ta ga irin
tsananin kyawun fuskar saurayin sai ta
sake dimaucewa har yayi mata kwarjini
ainun ta kasa ci gaba da kallonsa ta dan
sunkui da kanta kas, a sannan ne ya
dubeta ya ce, ina fatan dai babu wani
rauni a jikinki?
Ko da jin wannan tambaya sai
gimbiya Lamrita ta mike tsaye ta duba
ko ina a jikinta ta tabbatar da cewar
babu wani rauni sannan ta dubi saurayin
ta ce, ina godiya a gareka mara adadi
bisa ceton rayuwata da ka yi daga
sharrin wannan katuwar macijiya.
Sunana gimbiya Lamrita 'ya ga sarki
Gurzalu na birnin Kisra kuma ina kan
hanyata ne ta zuwa bimin Misra don
hallarar gasar kambun jarumta, wanene
kai, daga ina ka fito kuma ina ka dosa
yanzu?
Sa'adda kyakkyawan saurayin ya
ji wannan tambaya sai ya cika da
mamaki amma sai ya dubi gimbiya
Lamrita cikin murmushi ya ce, ni sunana
Salman bin Usman kuma na fito daga
wata kasa da ake kira Madinatul Ansar
dake kudancin nahiyarku. Babu inda na
nufa face birnin Misra inda ake wannan
gasa ta kambun jarumta domin nima n
AA Misau Ke Magana
shiga gasar amnma da wata manufa. Na
dade ina jin labarin wannan gasa da
yanayinta irin yadda ake fafatawa da
manyan jarumai na duniya ana yi musu
kisan gilla. Lallai idanuna sun kagu da
su ga yadda ake wannan bakin gumurzu.
Yake yar sarki ki yi sani cewa
kafin anzo nan na sauka a cikin birninku
na Kisra har na kwana biyu kuma na
sami labarin cewa mahaifinki sarki
Gurzalu shi ne zakaran wannan gasa ta
kambun jarumta kuma yanzu haka yana
can birnin Misra yana yin gasar. Menene
dalilin da ya sa baki bishi kun tafi tare
ba izuwa birnin na Misra, kuma ta yaya
kina matsayin 'yar sarki guda za ki
shigo cikin wannan daji mai hadarin
gaske ke kadai?
Ko da jin wannan tambaya sai
kunya ta kama gimbiya Lamrita ta
dabarbarce ta kama in ina, shi kuwa
jarumi Salman sai ya tari numfashinsa
ya ce, bana son karya a rayuwata kuma
bana tafiya tare da makaryaci. Kawai ki
fito fili ki gaya mini gaskiyar
tambayoyin da na yi miki, idan kuma
kin san cewa ba za ki iya gaya mini
gaskiyarki ba to ki yi shiru da bakinki
ina ganin cewa zai fi alheri a garem
ubaki daya.
Ko da gama fadin hakan sai jarumi
Salman ya mike tsaye ya je inda
rakuminsa ke tsaye ya dauko wata jaka
tasa ta guzuri gami da battar shan ruwa
ya dawo wajen Lamrita ya baje jakar
guzurin ya fiddoa gasasshen namna
tsuntsu nannade a cikin wani ganye ya
ajiye a gaban Lamnrita ya yagi cinyar
tsuntsun guda daya sannan ya dubeta ya
ce, ki cinye wannan naman duka don
naga akwai alamun matsananciyar
yunwa a tare da ke. Dan wannan da na
yaga ya isheni.
Yana gama fadin hakan sai ya
koma can inda rakumin nasa yake ya
shimfida buzu a kasa ya zauna a kansa
yana mai juya mata baya ya cinye dan
guntun naman dake hannunsa sannan ya
mike tsaye ya fuskanci alkibla ya kama
sallar nafila.
Al'amarin Lamrita kuwa ko da
jarumi Salmanu ya ajiye wannan
gasasshen tsuntsu a gabanta sai ta cika
da murna, Nan take ta kama Cin nanan
har sai da ta ci ta koshi ta taune kashin
duka sannan ta dauki battar ruwan shan
nasa ta kwankwada har sai da taji tayi
Byatsa.
Tana ajiye battar ruwan ne ta
hango jarumi Salman yana sallar nafila,
a sannan ne ta gane cewar lallai shi
ma'abocin addinin musulunci ne addinin
da yake da tsananin bakin jini a
nahiyarsu gaba daya.
Nan dai ta ci gaba da kallonsa tana
mamakin irin yanayin aikin bautar da
yake yi har sai da ya kammala ya shafa
addu'a sannan ya juyo ya dubeta ya ce,
ina neman alfarma a wajenki guda daya.
Ina son ki nema nini damar shiga
wannan gasa ta kambun jarumta idan
mun isa birnin Misra.
Ko da jin wannan tabaya sai
mamaki ya kama gimbiya Lamrita ta
dubeshi ta ce, tabbas kai bako ne baka
san dokokin wannan gasa ba. To ka sani
cewa yanzu saura zagaye daya kacal a yi
gumurzun karshe na wannan gasa a
wannan shekara, babu mamaki ma a yi
fafatawar ta karshe a cikin wannan sati
da muke ciki. ldan har kana son ka
fafata da jarumin da ya lashe gasar dole
ne ka fara kafsawa da wadansu manyan
jaruman guda hudu kuma sai ka biya
dinare dubu dari biyu da hamsin sannan
za a yarda ka kafsa da jaruman dake rike
da kambun gasar.
Sa'adda jarumi Salman ya ji
wannan jawabi na bimbiya Lamrita sai
ya yi murmushi ya ce idan da mutum
dari zan kafsa kafin na hadu da mai
kambun jarumta babu matsala kuma
batun kudin ba matsala ta ba ce ko
dinare miliyan daya ake bukata zan
biya.
Ko da jin wannan batu sai gimbiya
Lamrita ta karewa jarumi Salmanu kallo
daga sama har Raş cikin raini domin
bata ga alamar yana da ko dinare dubu
ba bare miliyan daya.
Ko da jarumi Salnanu ya fahimci
cewar kallon rauni take yi masa sai ya
dauko wata katuwar jakar fata a kan
rakuminsa ya ajiye a gaban Lamrita ya
budeta sai ga dinare cike fal. Take
gimbiya Lamrita ta dimauce ta kidime
saboda mamakin ganin wannan dukiya

Ni kaina AA Misau saida naa dimauce har na kasa cigaba da wannan rubutun kuma na dakata anan

Saikuma wani lokaciRIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Shida (6)
Part B.
Na Abdulaziz Sani M Gini
Typing By
AA Misau ke Magana

(Rashin Sakin Litattafan da muke kawo muku akan lokaci daga gareku ne domin muddin zaku dinga nuna kuna so a cigaba ta hanyar LIKES & COMMENTS bamuki kullum mu kawo muku cigaban ba)

Labari Ya Isowa Shagala Cewa
Marubucin Yaci gaba da cewa....

tsananin mamakin wannan dukiya
mai yawan gaske a hannun mutum daya
mugayen
kuma matafiyi mai ratsa
dazuzuka haka.
Nan fa ta fara aiyanawa a ranta
cewar anya kuwa wannan saurayin ba
dan sarki bane ko wani mashahurin
attahiri? Amsar da ta kasa baiwa kanta
kenan.
Ko da jarumi Salmanu ya ga
gimbiya Lamrita ta tsaya tana tunani sai
ya katse mata tunanin ya ce, ai sai ki
tashi mu hanzarta zuwa birnin Misra don
ka da a yi wannan fafatawa ta karshe ba
ma nan.
Lamrita ta yi ajiyar zuciya ta ce, na
yarda zan taimaka maka ka shiga
wannan gasa amma bisa sharadi biyu.
Sharadi na farko shi ne dole ne ka zama
kamar yarona, ma'ana za mu shiga cikin
birnin Misra kana matsayin sabon
jarumina wanda na kawo na shigar da
shi gasar kuma ina matsayin bakon
attajiri daga wata nahiyar, kaga kenan
babu abin da zaka yi sai bisa umarnina.
Ko da įin wannan batu sai mamaki
ya kama jarumi Salmanu ya ce yanzu
kina nufin kice za ki boye siffarki ta 'ya
mace kenan ki yi shigar mata, sannan
kuma ni na zauna a matsayin bawanki
• alhalin na fiki ma arziki?
Ko da jin wannan tambaya sai
gimbiya Lamrinta ta yi murmushi ta ce
kwarai kuwa abin da nake nufi kenan
kuma in dai baka bi wannan umarni
nawa ba ina tabbatar maka da cewar ba
zaka taba samun damnar shiga wannan
gasa ba.
Sa'adda Lamita ta z0 nan
jawabinta sai hankalin jarumi Salmanu
ya dugunzuma ya dubeta cikin matukar
damuwa ya ce haramun ne a addinina
mace ta yi shiga irin ta maza ko kuma
namiji ya yi shigar mata.
Kafin ya gama rufe bakinsa sai ta
ce, ai ana iya hakuri da wata dolen bisa
lalura, kuma a kowane addini akwai
lalura.
Ko da jin haka sai jikin jarumi
Salmanu ya yi sanyi ya yi shinu yana
tunani da nazari daga can sai ya numfasa
ya ce, shi kenan na yarda da duk
sharadin da kika zo mini da shi.
Cikin tsananin farin ciki gimbiya
Lamrita ta mike tsaye ta kimtsa kayanta
ta hau dokinta shima jarumi Salmanu sai
ya hau kan rakuminsa, har ya yunkura
zai wuce gaba sai ta sha gabansa ta ce,
saboda me zaka wuce kan gaba alhlain
ni ce na san banya fiye da kai?
Salmanu ya yi murmushi ya ce, ai
dole ne na wuce kan gaba ke ki tsaya a
baya saboda haka dokar addinina ta ce,
in ya so idan na kauce hanyar sai ki
saitani.
Lamirat ta jinjina kai ta ce, shi
kenan amma ka sani cewa dole ne ka
Boye addininka idan mun shiga birnin
Misra, in ba haka ba kuwa duk shirinka
sai ya wargaje.
Salmanu ya sake yin shiru yayi
dan guntun tunani da nazari sannan ya
saki rakuminsa ya yi gaba itama Lamrita
sai ta sakarwa dokinta linzami ta bishi a
baya dá sauri suka nausa cikin daji.
A can birnin Misra kuwa kafin gari
ya waye filin gasa ya cika ya batse, duk
inda mutum ya hanga sai dai yaga
kawunan bil adama rututu babu masakar
tsinke. Kai ba ma akan katanga ba hatta
akan benayen gidajen birnin mutnae ne
maza da mata suna kallo tsakiyar filin
gasar domin su ga yadda wannan
gagarumin wasa na karshe zai kasance
saboda an san cewa wasa ne wanda babu
mai kyansa da hadarinsa tunda za a
fafata ne tsakanin tsohon jarumin dake
rike da kambun gasar da kuma sabon
jarumin da babu kamarsa.
Bayan filin gasar ya gama cika, ga
alkalin gasa su duka sun gama hallara
kuma ga attajiran caca sun taru su da
yawa kuma sun zuba kudade mafiya
yawa a duk kwanakin gasar da akayi sai
kuri da cacar baki suke. Makada da
mawaka kuwa tuni sun fara aikinsu tun
kafin ma a fito da jaruman gasar.
Nan fa mutane suka kagu su ga
fitowar sarki Taryan domin dole sai ya
fito sannan za a fara gasar kuma a ka
rinka mamakin abin da ya sa ake ta bata
lokaci haka.
A can cikin gidan sarautar kuwa
sarki Gurzalu bai fara shirin fitowa filin
gasar ba sai da ya gama kimtsawa a
hankali cikin nutsuwa. Abin da ya fara
yi bayan ya tashi da safe shi ne wasa jini
ta hanyar yin wasa da takobinsa. Sai da
ya shafe kusan sa'a guda yana wannan
wasa jini sannan ya je ya yi wanka ya
zauna yana buda baki cikin janjani
tamkar ba shi da wani uzuri a gabansa.
Yana cikin wannan hali ne ya tuno
da batun 'yarsa gimbiya lamrita, nan
take takaici ya turnuke shi saboda ganin
yadda rashin jituwa ke neman shiga
tsakaninta da shi kuma bai san hanyar da
zai bi ba ya shawo kanta ba tunda ba shi
da amsar tambayoyin da ta yi masa akan
zafafa kiyayyarsa da yayi akan jarumi
Imhal.
Ko da sarki Gurzalu ya zo nan a
zancensa sai hawayen bakin ciki ya
zubo masa gami da nadamar abin da ya
aikata a baya wanda bai taba zaton
cewar zai yi nadamarsa ba kuma ba
wani abu bane face nadamar kashe dan
uwansa wato mahaifin jarumi Imhal da
dukkan iyalansa saboda kawai ya karbi
karagar mulki.
AA Misau ke Magana
Yanzu dai gashi ya sami mulki.
daukaka da dukiya mara adadi kuma ya
yi suna a duniya amma ya rasa abu daya
wanda har abada ba zai sameshi ba.
wato rashin dan uwa na jini.
A halin yanzu sarki Gurzalu ba shi
da sauran dan uwa a duniya ko guda
daya face jarumni Imhal wanda ya
kasance dan uwan dan uwansa da suke
uba daya.
Babban abin da zai rasa kuma anan
gaba shi ne soyayyar 'yarsa gimbiya
Lamrita a duk ranar da ta gano cewar shi
ne ya kashe mahaifin Imhal kuma ta
gano cewar Imhal dan uwanta ne na jini
Ko da sarki Gurzalu ya zo nan a
zancensa sai hawvayen bakin cikı va sake
subuto masa.
A daidai wannan lokaci ne yaji an
kyalkyale da dariyar mugunta. Dariyar
ta cika cikin dakin nasa da amsa kuwa
Take ya shaida muryar mti cdariyar, ba ta
kowa baee face ta Muzaira.
Ko motsawa sarki Gurzalu bai yi
ba sai ya gyara zama akan kujorar da
yake zaune ya dauki kofin ruwan inibi
ya kai bakinsa zai kurba,
Caraf sani yaji an karbe kofin daga
hannunaa sai ga Muzaitn ta baynna
tsulum a gefe daya kusa da shi ta sa
kofin a bakinta ta kwank wacde ruwan
inibin dake ciki kuna tayi jifa da kofin
Sannan taje ta zauna akan kujerar da ke
fuakantar ta sarki Gurzalu wacce tazarar
dake tsakaninsu bata wuce taku bakwai
ba ta dubeshi cikin mumushi ta ce
hakika sannu bata hana zuwa sai dai a
dade ba a je ba,
Yau kusan shekaru ashirin da biyar
kenan da cin amanar da ka yiwa dan
uwanka wanda a sanadiyar haka ne ka
kashe yar uwata da duk zuri ar mu
Ni kadai ne na tsira ka jeda rayuwata a Cikin
kunci da rashin 'yanci da sakewa tunda
koyaushe a cikin buya nake don gudun
sharrinka. Yau gashi ranar daukar fansa
ta zo. A gaban idanuna dana zai yi maka
kisan gilla. Babban bakin ciki na shine
ba zan iya gayawa dana sirrinka ba a
yanzu ya san cewa kai ne ka kashe masa
mahaifi. ldan har na gaya masa hakan
jikinsa ne zai yi sanyi ya kasa yin yakin
da kai da kwarin guiwa saboda sanin
cewa kai dan uwansa ne na jini kurna
uban macen da ya kamu da tsananin
sonta.
AA Misau ke Magana
Ko da Muzaina ta Z0 nan
zancenta sai sarki Gurzalu ya bushe da
dariya, al 'amarin da ya baiwa Muzaira
mamaki kenan domin a tunaninta
maganganun da ta gaya masa zasu sa
zuciyarsa ta karaya. Lokaci guda kuma
sai ya turbune fuskarsa ya daka mata
tsawa ya ce, ke yarinya ki yi sani cewa
kafin giwa taje kasa sai anyi da gaske.
Kuma mushen zaki, kuda ma baya binsa
bare tsuntsaye da sauran dabbobi. Ni a
rayuwata duk abin da na sashi a gabana
sai naga bayansa kuma makiyina bai
taba samun nasara ba a kaina. Ina so ki
sani cewa bukatata tana gaba da komai
nawa. Kar ki taba zaton cewa soyayyata
ga 'yata zata iya zama lagon da za a iya
sarmun galaba a kaina. Ki bar ganin cewa
kina tare da guurun sihirina ki yi zaton
cewa hakan zai sa ku sami nasara a
kaina.
Muzaira ta yi murmushi ta ce, ai ni
ban sa ce gurun sihirinka don na cutar da
kai ba sai don na tserar da rayuwar dana
daga sharrinsa tunda kaima kasan cewa
ban san yadda zan iya sarrafa gurun na
ka ba har na yi amfani da shi.
Kafin Muzaira ta gama rufe
bakinta tuni sarki Gurzalu ya yunkura
cikin tsananin zafin nama ya daka tsalle
sama ya zaro takobi daga cikin wani
kufe dake rataye a jikin bangon dakin a
sama ya taho shu... sama ya sokawa
Muzaira takobin a kirjinta, ya duro kasa
bisa kafafunsa ya kura mata idanu.
Kawai sai yaga ashe gaba dayan
jikin Muzaira na haske ne don haka
takobin bata yi mata illar komai ba duk
da cewar ta lume a cikin kirjinta ta faso
gadon bayanta.
Muzaira ta kyalkyale da dariya
sannan ta zare takobin daga cikin kirjin
nata tamkar ta zare silin gashi daga cikin
tandun mai ko alamar kwarza ne babu
akan kirjin nata, (topah ni kaina AA Misau abin ya bani mamaki) tayi jifa da takobin can
gefe daya ta sake bushewa da dariya ta
ce, wai shin so kake ka kasheni ka
dauke gurun sihirinka ne? To idan ma
mafarki kake yi ka farka. Idan kaga
wannan gurin sihiri ya dawo hannunka
tabbas ka sami nasarar kashe jarumi
Imhal a filin gasa. ldan kuwa shi ne ya
kashe ka to fa gurin sihirinka zai koma
kogonsa a ranar da ya hau karagar
mulkinka.
Ko da jin wannan batu sai jikin
sarki Gurzalu ya kama tsuma saboda
tsananin fishi, fuskarsa ta kama gatsine
kamar zata zazzago ta zabtare kasa.
Kawai sai ya sake yunkurawa cikin
shammace a karo na biyu ya watsowa
Muzaira wutar sihiri daga cikin tafin
hannunsa.
Kafin wutar ta zuba a kanta tuni ta
6ace 6at tana mai kyalkyala masa
dariyar mugunta gami cewa, mu hadu a
filin gasa zan gani idan sauran sihirin
tsafin naka da ya rage zaisa ka sami
nasarar kashe dana.
Nan take muryar Muzaira ta dauke
dif tamkar bata taba wanzuwa ba a
wajen kuma bai Rara jin wani motsi ba a
cikin dakin.
Cikin tsananin fishi sarki Gurzalu
ya mike tsaye ya fara shirin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment