Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita filin
gasa inda ya sanya kayansa na yaki
kuma ya daukil takobinsa da garkuwarsa
ya fice da sauri.
Shi kuwa sarki Taryan ba komai
ne ya hanashi fitowa ba da wuri izuwa
filin gasa face rashin jin sakamakon abin
da ya faru tsakanin bokayen birninsa da
sarki Gurzalu.
Al'amarin da ya yi matukar
dugunzuma hankalinsa kenan ya kasa
zaune ko tsaye kuma ya rinka kai kawo
a cikin turakarsa yana jiran dawowar
sarkin yakinsa Zamaru wanda ya turashi
yaje ya yi leken asiri don ya gano duk
abin da sarki Gurzalu ke kullawa a
sirrance. Ba don komai yake son ya
gano wannan sirri ba sai don ya ts erar da
rayuwar "yarsa gimbiya Sbumaira don
kada ta rasa saurayin da ta kamu da
tsananin Sonsa fiye da komai
rayuwarta.
Sarki Taryan ya san cewa tabbas
idan aka kashe jarumi Imhal a wannan
gasa za ta iya rasa hankalinta koma ta
rasa rayuwar ta ta gaba daya.
Sarki Taryan na cikin wannan hali
na damuwa sai ga gimbiya Shumaira ta
shigo a gigice tana kuka.
Cikin sauri sarki Taryan ya tareta
yana mai rike hannayenta ya dubeta
cikin firgici ya ce, yake 'yata wai shin
me ke faruwa ne naga har kina yin kuka
haka?
Shumaira ta rungurne sarki Taryan
ta sake fashewa da matsanancin kuka
sannan ta ce, ya ya ba zan yi kuka ba ya
Kkai abbana alhalina yau ne masoyina zai
yi wasa mafi hadari a cikin wannan
gAsa. Ka yi sani cewa yau fa kowa yana
tsoron wannan gurnurzu da za a yi
tsakanin jarumi Imhai da sarki Gurzalu
Saboda babu wanda ake da yakinin
cewar shi ne zai lashe gasar. Matsafa
sun yi iya yinSu kan su gano wanda
Zai yi nasara, atlajirab Caca sun Zuba
Gaba dayan dukiyarau akan wannan Wasa kuma na san cewa kai ne Wanda ya
zuba dukiyarsa mafi tsoka daga cikinsu
tabbas idan jarumi Imhal ya fadi ba
kararmar mummunar asara Zaka yi ba
Yanzu ta yaya zasu iya kubutar
da rayuwar Inhal daga sharrin sarki
Gurzalu?
Ko da jin wannan tambaya sai
sarki Taryan ya rasa abin da zai gaya
mata, ya dan juya mata baya sannan ya
waigo ya dubeta Cikin tsananin damuwa
ya ce, yake yata kin sani cewa duk
yadda zan yi naga rayuwarki ba a
salwanta ba zan yi don haka ki kwanta
da hankalinki dan jirani akwai abin da
nake jira kafin mu fita izuwa can filin
gasa..

Nima kuma AA Misau kudan jirani abu Kadan nake jira naa cigaba muku da typing......

WhatsApp group
https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q

Facebook page
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295

Facebook page
https://www.facebook.com/AlaminGuyson?mibextid=3amO3DAFELuS4Abp

Saikunzo

Admin
AA Misau ke MaganaRIJIYA GABA DUBU 💕
Littafi Na Shida (6)🩸
Part C. 💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
AA Misau ke Magana
✍️⭐⭐⭐

(Kamar yadda mukayi korafi akan kuna son litattafan da muke dorawa amma bakwa Nuna Kuna so a Yanzu Nake Ga Kamar kun gyara Ta hanyar maida hankali Akan goya mana baya SABODA HAKA idan yau kun Samar mana da LIKES SOSAI gobe ma zamu dora cigaban) 🥰

Labari Ya Isowa Shagala Cewa
Marubucin Yaci gaba da cewa...
Kafin sarki Taryan ya gama rufe
bakiisa sai ga sarkin yaki zamaru ya
shigo cikin dakin da gudu. Yana isowa
gaban sarki Taryan sai ya yi masa rada a
kunne.
Nan take sarki Taryan ya cika da
tsananin mamaki kuma ya yi shiru yana
tunani har izuwa tsawon yan dakiku
sannan shima ya yiwa Zamaru radar a
kunne sai Zumaru ya sake ficewa da
gudu shi kuwa sarki Taryan sai ya karma
hannun gimbiya Shumaira ya jata da
sauri yana mai cewa, zo mu karasa filin
gasar domin lokaci na neman kurewa.
Da isowar sarki Taryan da gimbiya
Shumaira cikin filin gasar sai jama'a
suka rude da shewa gami da tafi da
murna saboda sanin cewa nan ba da
dadewa ba za a fara wannan babban
wasa na manyan giwayen da ake shakka
da tsoro.
Bayan sarki da gimbiya sun je sun
zauna a inda suka saba zama sai aka
buga tambari sannan mai gabatar da
gasar ya fito tsakiyar- fili ya fara jawabi,
bayan ya yi gaisuwa da bayanin barka
da zuwa ga manyan baki sai ya ce, ya ku
jama'a ku yi sani cewa a yau din nan
wani bakon jaruni ya zo kuma ya
bukaci shiga wannan gasa duk da cewar
a yau ne za a yi wasa na karshe wato ya
amince ya fafata da jarumin da ya lashe
gasar ta yau a gobe ko a lokacin da ya
kama.
Wannan bakon jarumi ya biya
harajin da ake biya kuma ya cika duk
gasa bisa
ka'idojin shiga wannan
wanda shima
wakilcin maigidansa
bakon attajiri ne mai yawo da jarumai
izuwa kasa don halattar irin wadannan
wasanni. Bisa dalili ne yanzu wannan
bakon jarumi zai fito yayi wasa don mu
ga irin jarumtakarsa kuma ya amince a
hadashi fada da jarumai ashirin
Duk attajiran da suke da sha'awar
yin caca akan wannan bakon jarurni da
jarumai ashirin da zai fafata da su sai su
kai kudadensu ga wakilin caca.
Ko da jin wannan sanarwa sai filin
gasar ya dada kaurewa da shewa gami
da tafi da hayaniya. Attajiran cacar da
suke da sauran 'yan kudi a jikinsu suka
shiga wannan sabuwar caca.
Bayan jama'a sun dan sami yar
nutsuwa ne aka kirawo wadansu zaratan
jarumai su ashirin suka shigo cikin filin
sanye cikin kayan yaki.
Komai jarumtakar mutum idan ya
ga wadannan jarumai sai ya tsorata
saboda irin kirar da Allah ya yi musu ta
mutanen farko. Sun kasance dogaye
kuma kaurara kuma gaba dayan jikinsu
a murde yake cike da jijiyoyi da kwanji,
kai da ganinsu kasan babu tambaya dole
ne su kasance sadaukai.
Ko da "yan kallo
suka ga
wadannan manyan sadaukai
ashirin sai suka firgice
guda
suka firgice suka kama
sumbatu wasu na cewa shi kuma
wannan bakon jarumi wane irin
ne haka mara hankali har da yake
tunanin cewa shi kadai zai iya da
wadannan samudawan mutane.
wawa
Wasu kuma sai suka rinka cewa ai
karar kwana ce kawai ta kaishi ga yin
wannan furuci.
Abin da ya kara daurewa mutarne
kai shine yanzu ashe akwai sauran irin
wadannan mutane dama a duniya amma
ba a ganinsu? Menene dalilin da ya sa
tuntuni ba a sasu cikin wanann gasa ba
Ana cikin wannan kace kace ne
aka kirawo bakon jarumi Salmanu bin
Usmanu. Nan fa filin agsar ya yi tsit
kowa ya zuba idanu izuwa kofar da
jaruman gasa ke fitowa.
Wata rigar fata ce da wandontaa
jikinsa. Rigar mai yankakken hannu ec
iya hammata don haka ta baiyana surar
kwanjinsa da murdewarsa, Salmanu ya
bar fuskarsa a bude bai rufe ta ba don
haka yana shigowa cikin filin gasar sai
tsananin kyawunsa da kyawun surar
jikinsa suka dauke hanklain kowa maza
da mata, musamman ma matan domin
dìmaucewa suka yi saboda babu wata
ya mace da zata ga jarumi Salmanu ba
la ji tana sonsa ba.
Nan fa aka rude da yi masa tafi da
jinjina tamkar dama can an sanshi kuma
ana kaunarshi fiye da fima.
Ko da gimbiyahumaira ta yi arba
da jarumi Salmanu shima ya hada idanu
da ita sai duk su biyun suka ji zukatansu
sun bugad a karfi kuma suka kasa gane
dalilin faruwar hakan.
Jarumi salmanu ya nufi tsakiyar
filin mai gidansa na take masa baya
wanda ya yi shiga irin ta manyan
attajirai ababan kwatance, domin
alkyabbar da take jikinbsa da rawaninsa
da takalminsa sun isa su gina fadar wan
AA Misau ke Magana
sarkin, fuskarsa cike take da kasumba.
gashin baki da gemu.
Ba wani ba ne wannan mutum ba
face gimbiya Lamrita wacce tayi 6ad da
kama. Sai da ta raka jaurmi Salmanu har
izuwa tsakiyar filin gasar sannan ta juyo
ta barshi tsaye cikin tsakiyar
wadannan samudawan jarumai guda
ashirin.
A daidai wannan lokaci ne filin
gasar ya yi tsit tamkar mutuwa ta gifta.
Mutnae suka bude idanuwansu sosai
suna kallon tsakiyar filin, domin su ga
yadda wannan bakon jarumi shi kadai
jal zai fafata da jaruman guda ashirin.
Ai kuwa nan take aka buga gangar
fara yaki, sai jaruman guda ashirin suka
zare takubbansu suka afkawa jarumi
Salmanu suka haushi da sara da suka ta
ko ina da dukkan karfinsu.
Nan fa jarumi Salmanu ya rinka
kare duk hare haren nasu ta duk inda
suka kawo ya zama kamar mazari a
sakiyarsu ya rinka yin wata irin
cstantawa a Kasa da sama wacce tasa ya
zame musu alakakai kuma ta burge gaba
dayan yan kalon har sai da kowa ya
Kama yi masa tafi, filin ya dada rudewa
da shewa fiye da koyaushe saboda ba a
Taba ganin jarumin da ya taba yin irin
Wannan gwaninta ba.
Jarumi Salmanu ya ci gaba da kare
kansa kawai ba tare da ya maida
martanin sara ko suka ba amma sai ya
Rinka naushinsu da hannu da kafa Nan
fa ya fara hada musu jini da majina a
hanci da baki.
(Kai nima fa abin ya fara bani mamaki AA Misau ke Magana)
Al'amarin da ya fusta jaruman
kenan surma suka fara kai masa wawan
duka gami da wawan saran amma duk
sa Suka zamo na banza saboda tsananin
Zafin narmansa ya wuce tunanin mai
Tutani kai kace jkinsa na karfe ne bana
Jini da tsoka ba.
Sai da aka shafe kusan rabin sa'a
ana wannan bakin artabu amma jaruman
ashirin sun kasa ko da kwarzanar jikin
jarumi Salmanu shi kuma sai ya kasa kai
mutum daya kasa a cikinsu duk da
cewar shi ne yake yi musu lugudan duka
saboda tsananin juriyarsu da nacinsu.
Ko da jaruman suka fusata ainun
kuma suka rasa yadda zasu yi da shi sai
kawai suka ja da baya gaba dayansu a
lokaci guda suka rabu izuwa kaso biyu
wato suka rabu mutum goma goma
Lokaci guda suka rugu da gudu cikin
tsananin zafin nama da shammace
goman farko suka danki hannayen
Salmanu, ragowar goman kuma suka
kama kafafunsa suka kana ja suna tale
shi da nufin su tsinkashi. Saboda
tsananin azabar da Salmanu ya ji bai san
sa'adda ya kumma uban ihu ba tunda
shammatarsa suka yi bai san manufarsu
Amma da yake shammatarsa suka
yí bai san manufarsu kenan ba, amma
da yake Allah ya bashi karfin Allah ya
isa sai shima ya dage ya hanasu samun
damar tsirkashi.
Nan fa kwanjin Salmanu ya fara
kumbura, rigarsa ta fara yayyagewa sai
gashi yana janyo jaruman ashirin
gabansa wato ya zamana cewa kartin
damtsnsa ya fara rinjayar nasu.
Nan fa filin gasar ya sake rudewa
da shewa aka shiga yiwa jarumi
Salmanu kirari da jinjina, kawai sai gani
akayi ya janyosu su duka da karfin tsiya
ya gwara fuskokinsu.
Cikin bakin zafin nama ya mike
tsaye zumbur ya rinka naushin
Hannayensu da kafafunsu ya rinka
kakkaryasu suka rinka yin ihu suna
zubewa kasa.
A cikin abin da bai wuce dakika
ashirin ba ya zubar da su kasa su duka
suna iface-iface aka rasa dayansu da zai
iya mikewa tsaye.
Ko da ganin haka sai filin gasar ya
kaure da tsananin ihu da shewa
Attajiran cacar da suka zabi Salmanu
kuwa rawa da tsalle suka kama
wasunsu kuwa suka kamna zuba ruwa a
kasa suna sha su ma suna birgima a
Rasan tamkar wadanda suka zautu.
Al'amarin gimbiya Lamrita kuwa
saboda tsananin farin ciki da kidimewa
bata san sa'adda ta mike tsaye ba
zumbur daga cikin yan kallo ta ruga
izuwa cikin filin gasar ta daka tsalle ta
rungume jarumi salmabu. Saura Riris
rawanin kanta ya kwance a ga gashin
kanta sai jarumi Salmanu ya yi sauri ya
gyara mata rawanin.
A lokacin ne sulka hada idanu taji
ta kamu da tsananin kunya amma sai ta
wayance ta ci gaba da tsallen murna don
kada jama' a su gano wani abu
Yan kallo da yawa suka fado
flin gasar suka daga jarumi
Salnanu sama suna tayi masa jinjina har
Sai da dakaru suka rugo suka tarwatsa su
Aka fitar da jarumi Salmanu daga cikin
flin kuma aka kwashe wacannan
Karyayyun jarumai sannan wuri yayi
daidai jamna'a suka utsu.
Ba tare da bata wani lokaci ba aka
Sake buga tambarin ci gaba da gasar in
da alkalin gasar ya fara kirawo jarumi
mhal ya fito daga cikin dakin jaruman
Yan kallo na ganinsa sai aka rude
ihu gami da shewa, tafi, jinjina da
A daidai wannan lokaci ne sarki
Taryan ya dubi gimbiya Shumaira ya ce
yke yata yanzu ke a ganinki tsakanin
Jarmi Imhal da wannan bakon jarumi
Waye ya fi kyau da jarumtaka?
Sa'adda Shumaira ta ji wannan
tambaya sai ta yi ajiyar numfashi sannan
ta ce, ai ni kaina ma ya juye. Ya kai
abbana kayi sani cwa babu wanda zai
iya tantancewa tsakanin Imhal da
wannan sabon jarumi face kawai idani
sun fafata a zahiri an gani.
Sarki Taryan ya yi murmushi ya
ce, hakika zancenki dutse ne 'yata.
Gama fadin hakan ke da wuya sai
suka ji an kirawo sunan sarki Gurzalu, ai
kuwa sai filin ya sake yamutsewa da ihu
da hargowar mutane fiye da koyaushe
har sai da aka rinka toshe kunnuwva da
tafin hannaye don ji zaka yi kamar
kunnenka zai dode saboda karfin ihun
mutane.
Sarki Gurzalu ya nufi cikin filin
gasar yana tafiya cikin takama da izza
irin ta manyan sadaukai kuma nanyan
sarakai masu ji da kansu.
Nan fa murokansa suka shiga yi
masa kida da kirari irin wanda suka saba
yI masa na musamman.
A wannan lokaci jarumi Salmanu
da gimbiya Lamrita na zaune a waje
guda tare a inda manyan attahirai ke
zama.
Ko da sarki Gurzalu ya taho zai
gifta ta gabansu sai Lamrita tayi sauri ta
a sunkui da kanta kas saboda tasan cewa
a da zarar sun hada idanu ita da sarki
Gurzalu sai ya shaidata, Shi kuwa
Jarumi Salmanu sai ya kurawa sarki
a Gurzalu idanu, ai kuwa shima yana
ganinsa sai ya kura masa idannun har
yana waigensa. Duk su biyun sai sukayi
ta kokarin su tuno da inda suka taba
haduwa arnma sai abin ya gagara har dai
sarki Gurzalu ya isa tsakiyar filin ya
kusanci jarumi Imhal ainun yadda suna
Ajin mum fashin juna.
AA Misau ke Magana
A daidai wannan lokaci ne zuciyar
gimbiya Lamrita ta kama tafarfasa
kamar zata kone saboda tsananin bakin
ciki da kuma jin kiyayyar mahaifinta a
cikin ranta a sa'adda ta ganshi daf da
Imbal.
rinka
Nan fa ta
tuno da
maganganun da sarkin yaki ya gaya
mata bisa irin cin amanar da sarki
Gurzalu ya yi ya kashe mahaifin Imhal
dan uwansa kuma jininsa da yadda ya
kashe matarsa da duk zuri'arta. Nan take
jikin Lamrita ya kama tsuma ta yunkura
zata mike tsaye ta ruga izuwa cikin filin
domin taje ta gayawa jarumi Imhal,
Salmanu ya riko hannunta a karon farko
tun da suka hadu. Cikin sanyin jiki ta
koma ta zauna.
Cikin rada Salmanu ya ce da ita,
me za ki je ki yi a cilin flin gasar wanda
ba ki sanar da ni ba tun kafin mu iso
nan?
Ko da jin wannan tambaya sai
Lamrita ta wayance ta kama yake ta ce
babu komai.
Sarki Gurzalu ya dubi jarumi
Imbal ido da ido ya ce, to Imhal yau ne
fa ranar karshen numfashinka a doron
Rasa. ldan kana da wata wasiya ka bar
mini ita nayi alkawari zan cika maka ita
bayan mutuwarka.
Sa'adda jarumi Imhal ya ji wannan
batu na sarki Gurzalu sai ya yi
murmushi ya ce ko kadan bana ji a
jikina cewar zain mutu a wannan gasa da
za mu yi ni da kai. Idan har ban vi
nasara kanka ba sai dai mu yi ragas
amma kasan cewa da hannuna ba zan
iya kasheka ba saboda ina yi maka
kallon ubana mahaifi a matsayinka na
uban masoyiyata wacce na kamu da
tsananin sonta, son da ba zan iya
kankareshi ba daga cikin zuciyata
Ko da jin wannan batu sai jikin
sarki Gurzalu ya yi sanyi har ya ji
Kwalla na neman zubO masa sai ya yi
sauri ya sunkui da kansa kas ya juya da
baya yayi taku bakwai sannan ya zare
takobinsa ya gyara tsayuwarsa.
Ko da ganin haka sai shima jarumi
Imhal ya zare tasa takobin kuma ya
gyara tsayuwa suka fara kallon kallo.
Ba wani abu bane ya sa kwalla ta
zOwa sarki Gurzalu ba face sanin cewa a
badini fa shi uba ne ga jarumi Imhal
mutane ne basu sani ba amma kuma
gashi a zahiri ba shi da makiyin da ya
fishi a doron kasa.
Nan take sarki Gurzalu ya ji ya
tsani jarumi Imhal fiye da koyaushe don
haka ba shi da wani burin da ya fi ya
gaggauta kasheshi domin ya daina tuno
da cin amanar da ya yi a baya.
A wannan lokaci gimbiya Lamrita
na zaune na cikin van kallo cikin
shigarta ta attajiri kuma jarumi Salmanu
na zaune a gefan damanta daf da daf
Ko da jarumi Salmanu ya karewa
sarki Gurzalu da jarumi Imbal kallo na
natsuwa sai ya dubi Lamrita ya ce,
haikka wadannan jarumai ne na gaske,
samun nasara a kansu sai sa'a da rabo ba
wai tsagwaron karfin damtse ba da 1ya
yaki.
Ko da jin wannan batu sai nankalin
Lamrita ya sake dugunzuma ainur fiye
da koyaushe ta sake rudewa har shi
kansa jarumi Salmanu ya fahimci cewar
lallai Lamrita ba ia son wannan gum urzu
da za a yi tsakanin mahaifinta da jarumi
imhal kuma nan take ya gane cewa lallai
akwai soyayya tsakaain ta da jaruni
Imhal.
Salmanu na cikin wannan tunani
Ne ya lura da cewa ashe gaba dayan
matan dake cikin filin gasar hankalinsu
kansa suke, kai hatta matan aure ma sun
kasa kau da idanunsu a kansa, al'amarin
da ya sa yaji gaba daya ya tsani filin
gasar kenan, har ya janyo rawaninsa zai
rufe fuskarsa kuma sai ya hada idanu da
gimbiya Shumaira, yana yin arba da ita
yaji nan take ya kamu da tsananin sonta
kuma itace kadai bata kallonsa a filin,
idanun ta suna kan jarumi Imhal kuma
kwalla ta ciko mata, hawayen na shirin
zubowa.
Kawai sai ji akayi an buga gangar
fara gumurzu, ai kuwa sai jaruman biyu
suka rugo izuwa kan juna suka kacame
da azababben yaki suna masu kaiwa
juna sara da suka cikin tsananin zafin
nama, juriya da bajinta ta ban al'ajabi.
Nan fa yan kallo suka rude da
shewa, tafi, kowa na yiwa gwaninsa
kirari, makada da mawaka ma suka
kama aikinsu.
Sai da jaruman biyu suka shafe
sa'a daya da rabi suna wannan bakin
artabu suka tashi hankalin kowa a filin
gasar amma dayansu bai sami nasarar ko
da kwarzanar jikin daya ba. Al'amarin
da ya sa 'yan kallo suka kagauta kenan.
Bisa dole jaruman biyu suka ja da
baya suka yi cirko cirko suna kallon
juna suna haki.
Ba komai ne ya sa suka ja bayan
ba sai domin su baiwa kansu dan hutu
kuma su yi nazari akan irin salon fadan
da ya kamata su sauya don samun lago.
Ai kuwa sai da suka shafe kusan
dakika dari a tsaye sun kurawa junansu
idanu sannan suka sake tasowa da gudu
iZuwa kan juna. Ko da ya rage saura
baifi taku hudu ba su hadu sai
kowannansu ya daka tsalle sama tamkar
kibiyoyi, kowannansu ya kaiwa dan
uwansa mugun hari cikin shammnace.
Cikin nasara sarki Gurzalu ya
yanki Inhal akan damtse hannunsa na
dama....

Topah nima AA Misau ganin wannan galaba da. Sarki Gurzalu ya samu yasa zan dakata anan sai wani lokaci kuma

Admin
AA Misau Ke Magana
WhatsApp group

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QRIJIYA GABA DUBU 💕
Littafi Na Shida (6)🩸
Part D💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
AA Misau ke Magana
✍️⭐⭐⭐

(HAKIKA KUN NUNA MANA KUNA SON LITTAFIN NAN SABODA HAKA GA ALKAWARI NA NAN NA CIKA😎 kucigaba da nuna mana goyon baya kusha LABARAI)

Labari Ya Isowa Shagala Cewa
Marubucin Yaci gaba Da cewa...
Sarki Gurzalu ya samu nasarar yankar imhal a damtsen sa na dama
shi kuma Imhal sai ya sami
nasarar yankasarsa akan cinyar kafarsa
ta hagu. A tare su biyun suka kwala ibu
sakamakon tsananin zafi da zogin da
sukaji suka rikito kasa, jini na diga a
jikinsu kowannansu na dafe raunin
kuma suna hararar juna.
Kai da ganin wannan abu da ya
faru akasan cewar karfi ya zo daya.
Hakan ce ta sa gimbiya Lamrita tayi
murmushin farin ciki ta sami nutsuwa da
kwanciyar hankali, bisa ganin cewa abu
ne mawuyaci sarki Gurzalu ya sami
nasarar kashe Imhal.
Da zarar dayansu ya sami nasarar
saran dayan ko yankansa sai kaga shima
dayan ya samu.
Nan fa jini ya rinka zuba a jikinsu
a wurare da dama har jiri na dibarsu
amma saboda bakin naci da juriyar
bala'i sun ki faduwa kasa kuma basu
daina yakin ba.
A haka ne kuma suka hada da
gabzawaunansu
j naushi da bugu. Nan fa
fiuskokinsu
da idanuwansu
kumbura suka yi suntum.
suka
Haka dai suka ci gaba da wannan
bakin artabu suna layi kamar zasu fadi
Kasa, kai hatta 'yan kallo sai da suka
kamu da tausayinsu amma ko kadan su
jaruman basa tausayawa kansu.
Tun suna tsaye sai da suka tsugune
kasa a sannan ne kuma suka kama
komowa, wannan ya shake wancan
wancan ya shake wannan suka yi ta
birgima a kasa kuma suka ci gaba da
naushi da bugun juna a lokacin da
takubban hannayensu suka subuce daga
bannayensu.
Babu abin da ya dada baiwa 'yan
kallo mamaki face ganin yadda da zarar
dayansu ya cutar da dayan sai shima
dayan ya rama yayi masa irin abin da
yayi masa.
Tun da aka fara Wannan gasa ba a
taba yin jaruman da suka yi irin wannan
dadewa ba suna gumurzu a cikin filin
gasa ba tare da daya ya samni nasara ba.
A daidai wannan lokaci ne
hankalin atajiran caca ya dugunzuma
ainun saboda kowa yana ganin cewa za
a iya cinye jaruminsa.
Lokacin da jaruman biyu suka
kwamarzu sosai kuma suka galabaita
ainun sai suka saki juna suka zube kasa
wanwar suna haki da numfashi sama
Sama.
Da kyar da sidin goshi suka mike
tsaye suka skae daukar takubbansu suka
ja da baya taku biyar biyar suka dada
kurawa juna idanu suna tunanin karshe
na samun nasarar lashe gasar.
Tsawon 'yan dakiku suna tsaye
kikam, a lokacin ne filin gasar ya yi tsit
kamar mutuwa ta gifta saboda kowa ya
zuba idanu ya ga yadda wannan haduwa
Ta karshe zata kasance.
Kawai sai aka ga jaruman biyu sun
taso da gudu izuwa kan juna suna ihu da
kururuwa mai tsananin firgitarwa wacce
ta razana kowa, mutane suka mimmike
tsaye daga zaune ana dafe kai da bude
baki, kawai jira ake a ga jarumin da zai
fadi kasa idan aka yi wannan mugun
gamo.
Ba zato ba tsammani sai aka ga
jaruman biyu sun daka tsalle sama,
kafafunsu sun rabu da kasa tamkar an
barbosu daga cikin baka suka luluka can
sama tamkar kawunansu zasu tabohadari Ai kuwa suna haduwa
kowannasnu ya sami nasarar sokar dan
uwansa da takobi da gefen ciki. Kowace
takobi sai da ta hudo ta gadon baya.
Take suka rikito kasa suka baje wanwar
suna kakarin mutuwa.
Ko da ganin ahin da ya faru sai
gimbiya Shumaira da gimbiya Lamrita
suka dimauce suka kwala ihu. Take
Shumaira ta sulale kasa daga kan kujerar
da take zaune ta sume, ita kuwa gimbiya
Lamrita bata san sa'adda ta mike tsaye
ba zumbur har rawanin dake kanta ya
tuje sai gashi gashin kanta na ya mace
ya zubo kasa. Kawai sai ta ruga izuwa
cikin filin gasar. Maimnakon ta wuce
zuwa kan sarki Gurzalu wanda shi ne
mahaifinta sai ta wuce zuwa kan jarumi
Imhal.
A daidai wannan lokaci ne alkalan
gasa da dakaru suka ruga izuwa kan
jaruman gasar domin a gane halin da
suke ciki, idan basu mutu ba a basu
agajin gaggawa.
Da yake fuskar gimbiya Lamrita
cike take da gashi ba a shaida kowacece
ba ammna kuma da aka ga gashin mace
ne da ita sai rashin yadda ya fado dakaru
suka sha gabanta domin su hanata isa
inda jarumi Imbal yake, ai kuwa sai ta
tarwatsasu da Rarifn tsiya inda ta zarc
takobinta ta hau kare harinsu tana
makesu suna faduwa kasa.
Nan fa filin gasar ya yamutse, 'yan
kallo suka kama iface-iface da guje guje.
A lokacin ne aka yi sauri aka
đauke sarki Gurzalu aka shige da shi
cikin gidan sarautar likitocinsa na biye
da shi da gudu babu tabbacin cewar za a
iya ceto rayuwarsa.
Gimbiya Lamrita ta isa har inda
jarumi Imhal ke kwance cikin jini male
male yana ta kakarin mutuwa amna sai
ta kasa daukeshi saboda dakarun dake
tare ta kara yawa suke kuma sarkin
yawa yafi sarkin karfi.
Ko da jarumi Salmanu ya ga cewa
lallai gimbiva Lamrita ba za ta iya
dauko jarumi Imhal ba kuma in dai ta ci
gaba da kokarin daukoshi sai asirinta ya
AA Misau ke Magana
tuno sai ya yi sauirI ya batar da
kamanninsa ya ruga izuwa inda take ya
taimaka mata suka bazar da duk dakarun
dake gabanta suka dauke jarumi Imhal
suka hau doki da shi suka fice daga cikin
birnin gaba daya da karfin tsiya.
Ai kuwa sai dakaru sama da
mutum dubu uku suka hau dawakai suka
bi sawunsu.
Ko da jarumi Salmanu ya waigo
yaga dumbin dakarun da suka biyo su
kuma suna kokarin cimmasu sai ya
shiga addu'a yana mai neman taimalkon
Allah.
Faruwar hakan ke da wuya sai
yaga sun baiwa dakarun tazara mai
yawa, kafin a jima kuma sun bace musu
da gani.
Su kansu dakarun sai suka cika da
tsananin al'ajabi bisa ganin bacewar
barayi biyun da suka sace jarumi Imhal
tunda da suna hangensu daf da daf.
Bisa dole dakarun suka yi turjiya
suka kama kalle kalle da
ddawakansu suka
waige waige suna kallon
kudu da arewa ko zasu gansu
amma ko duriyarsu babu.,
gabas da yamma
Nan take suka kada linzamin
dawakansu suka koma da baya domin su
kai labari.
A can cikin birnin Misra kuwa gari
ya hautsine hankalin kowa a tashe yake.
Shi sarki Taryan hankalinsa na kan
"yarsa gimbiya Shumaira. Dama yana
ganin ta suma ya kwalawa likitansa kira
suka dauketa suka shige da ita cikib
gidan sarautar a dimauce amma har
tsawon sama da sa'a guda ba ta farfado
ba, al'amarin da ya kara razana sarki
Taryan kenan ya kama kai kawO a
lokacin da kwalla ta cika masa idnau.,
shi kuna likitan yana ta aikinsa.
Bayan jama'a Sun gama
tarwatsewa daga filin gasar ya zamana
cewa filin yayi wayam tamkar dama dan
adam bai taba wanzuwa ba a cikinsa sai
mutane suka ruga izuwa cikin gidajensu
a cikin gari suka kukkulle kofafi domin
gani suke yi kamar yaki ne ya barke a
garin.
Sai da aka dan jima ba a ji
hayaniya ta ci gaba ba sannan hankalin
mutane ya fara kwantawa har suka fara
bude kofofin gidajensu suna lekawa
waje don suga abin da ke gudana.
Babu abin da suka gani face
dakarun sarki Taryan suna ta kai kawo
alamar cewar suna neman wani abu.
A wannan lokaci ne mutane suka
sami damar tattaunawa akan abin da ya
faru.
Nan fa kowa ya rinka fadan
albarkacin bakinsa. Wasu su ce ai sarki
Gurzalu da jarumi Imhal sun mutu wasu
kuma suce ai basu mutu ba, zama su iya
idan likitoci suka yi gaggawar
cetonsu,
yanzu
menene
To wai shin
matsayin wannan gasa? Tsakanin sarki
Gurzalu da jarumi Imhal wanene kenan
zqi lashe wannan gasa? Shin sunyi ragas
kenan ko kuwa zasu sake fafatawa ne
jdan har sun rayu basu mutu ba sannan a
tantnace zakaran gasar? To ai ga shi ma
an sace jarumi Imhal kuma ba a ma san
wadanda suka sace shi ba, don haka
babu tabbacin ma za a sake ganinsa.
Haka dai mutane suka yi ta kace
nace ba tare da an san takamaiman halin
da ake ciki ba.
Sai bayan sa'a daya da rabi sannan
gimbiya Shumaira ta dawo cikin
haiyacinta ta farfado. Tana bude idanu
sai ta mike zaune zumbur tana mkai
anbaton sunan jarumi Imhal kuma ta
yunkura zata sauka daga kan gadon da
take zaune sai sarki Taryan ya yi sauri
ya riketa ya ce, ki yi hakuri yake 'yata
ba za ki iya ganin Imhal ba a yanzu
domin yana cikin wani irin nugun
yanayi wanda in kika gani kema za ki
iya komawa cikin halin da muka cetoki
da kyar. A yanzu haka likitoci

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment