Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na nan
tsaye a kansa suna aiki.
Ko da jin wannan batu sai gimbiya
Shumaira ta fashe da matsanancin kuka
tana cewa, ya kai abbana kayi sani cewa
ba zan iya yin rayuwa ba muddin ban
sami soyayyar jarumi Imhal ba.
Ko da jin haka sai tausayin
Shumaira ya kama sarki taryan ya
rungumeta a kijinsa kuma ya shiga
rarrashinta yana mai kwantar mata da
hankali kuma yana nuna mata cewar
lallai zai yi iya ko karinsa wajen ganin
cewar ta mallaki Imhal.
Haka dai ya ci gaba da lallabata
har likita ya bata. maganin barci ta sha.
Sarki Taryan na rungume da ita a
kirjinsa yana
shafar gashin kanta barci
ya sace bata sani ba.
Sarki Taryan ya shimfideta akan
gadon sannan ya kirawo wata babbar
kuyangarta ya ce ta kula da ita sosai
Nan take suka fice daga cikin
Turakar ta gimbiya shi da likitan nasa.
Suna isowa kofar harabar turakar ta
gimbiya sai ya dubi likitan ya ce, tsawon
sa'a nawa gimbiya zata yi tana barci?
Likita ya ce a kalla sai ta shafe
sa'a shida tana wannan barci.
Ko da jin haka sai sarki Taryan ya
yi ajiyar numfashi ya ce, dole ne na
nemo jarumi Imhal a duk inda yake
kafin gimbiya ta farka daga wannan
barci in dai ba so nake ta rasa rayuwarta
ba gaba daya. Ya zama dole nayi shiri
da kaina na tafi farautar wadanda suka
saceshi tunda
Cimmasu.Sun kasa
dakaına
Nan take sarki Taryan ya sallami
likita ya tafi sannan ya aika aje a kirawo
masa sarkin yakinsa Zamaru.
A daidai wannan lokacin ne alkalan
gasar kambun jaruntar suka rugo da gudu
izuwa gaban sarki Taryan suka zube kasa
suka kwashi gaisuwa sannan suka mike
tsaye suna masu sunkui da kawunansu
Kas.
Babban cikinsu ya risina ya ce ya
shugabana yanzu menene abin yi, wane
hukunci zamu yanke akan wannan gasa?
Ko da jin wannan tambaya sai sarki
Taryan ya bushe da dariyar mugunta,
al'armarin da ya yi matukar baiwa alkalna
gasar mamaki kenan. Daga can sai sarki
Taryan ya murtuke fuskarsa ya dubi
shugaban alkalan ya ce, ku kwantar da
hankalinku ku sani cewa sarki Gurzalu da
jarumi Imhal ba su mutu ba yanzu nema
za a fara wannan gasa, duk abin da akayi
a baya somin tabi ne. yanzu ne8 a sarmi
kazaman kudade a cacar da akeyi saboda
ma zuwan bakon jarumin da yake son
fafatawa da wanda ya yi nasara tsakanin
Gurzalu da Imhal. Yanzu na gano
wadanda suka tura a kashe jarumi mhal
har cikin dakin da muke tsaresh ida amma
ba zan baiyana su ba yanzu har sai an
gama wannan gasa.
Ko da jin wannan batu sai mamaki
da tsoro ya kara turnuke alkalan gasar,
shugaban nasu ya sake dubna sarki
Taryan ya ce, ya shugabana shin yanzu ba
ka tsoon cewa wadanda suka kaiwa
Imhal hari a wancan karon su ne suka
saceshi a yanzu?
Ko da jin wannan tambaya sai sarki
Taryan ya sake bushewa da dariya a lkaro
na biyu sannan ya ce, ko kadan ba su
bane su ka sace jarumi Imnal ba amma
nasan ko su waye. Abin da zan gaya
muku yanzu shi ne daga yau na sauya
jarumin gasata. Wannan sabon jarumin da
ya shigo gasar shi zan zuba dukkan kudin
cacata a kansa.
Ko da jin wannan bat sau mamaki
ya dada kama alkalan gasar domin gani
suke yi kamar sarki ya saki reshe ne ya
kama ganye tunda ba a san irin sa'ar
ba, jarfin
wannan sabon jarumi
damtsensa kawai aka sani.
Nan dai sarki Taryan ya sallami
alkalan gasar sannan shima ya tafi izuwa
cikin turakarsa da sauri ya kimtsa sannan
ya fito ya hau doki shi kadai jal ya fice
daga cikin gidani sarautar ya nausa cikin
daji ba tare da wani ya shaida shi ba
saboda yayi badda kama yayi shiga irin ta
dakarunsa.
Al' amarin su jarumi Salmanu kuwa
lokacin da suka bacewa dakarun da suka
biyosu bayan sun dauke jarumi Imhal sai
suka ruga izuwa cikin wani dogon dutse
mai tsawo da duhun gaske suka shimfide
jarumi mhal a kasa. Har izuwa wannan
laokaci yana kakarin mutuwa.
Nan fa Lamrita ta dada dimaucewa
ta shiga kokarin zare takobin dake cikinsa
tana kuka.
Cikin hanzari jarumi Salmanu ya
rike hannunta ya hanata zare takobin har
sai da ya yi wata addu'a ya tofa akan
raunin sannan ya sa hannunsa ya zare
takobin.
Nanfa Lamrita ta cika da tsananin
mamaki saboda take jini ya daina zuba
duk da cewar ramin raunin mai Zurfi ne
SOsai.
Salmanu ya bude jakarsa ya debo
wani garin magani ya zuba akan raunin
sannan ya kawo wani farin dogon kyalle
ya daure raunin da shi tamau.
Faruwar hakan ke da wuya sai
Imhal ya daina kakarin mutuwa kuma
barci ya daukeshi. Nan take Salmanu ya
sake karanta wadansu addu'o'in ya
tofawa Imhal sannan ya dubi Lamrita
cikin murmushi ya ce, da izinin
ubangijina wannan rauni na Imhal za
warke a cikin kwankai kadan kuma zai
sami lafiya sosai ya ci gaba da wasansa.
Ko da jin wannan batu sai Lamrita
ta kamu da tsananin farin ciki ta kuma
yiwa jarumi Salmanu tana mai goge
hawayen idanunta sannan ta dubeshi ta
ce, ya kai Salmanu kayi sani cewa ka yi
mini taimakon da ba zan iya biyanka ba
tunda ka ceto rayuwar masoyina wanda
nake kaunarsa fiye da komai a wannan
duniya a yanzu.
Ko da jin wannan batu sai jarumi
Salmanu ya yi murmushi ya ce, ai ba ni
ne na ceto rayuwarsa ba, ubangijin
musulunci ne ya ceci rayuwarsa tunda ni
ba likita ba ne kuma ni ba matsafi ba ne.
ubangijin nawa na roka ya bashi lafiya.
Amma fa yau saura kiris asirinki ya tonu
kuma a hakan ma ina zargin cewa sarki
Taryan ya ganeki.
Kafin Lamrita ta bude baki tace
wani abu sai kawai suka ji motsi
bayansu. Cikin hanzari da firgici suka
waiga da sauri.
Ba wani suka gani ba tsaye
bayansu face sarki Taryan a cikin
gagarumar shigar yaki yana murmushi.
Kawai sai ya dubi Lamrita ya ce, ki dena
zaton ban san duk abin da kike kullawa
ba dangane da mahaifinki.
Ko da jin haka sai Lamrita da
jarumi Salmanu suka mike tsaye suna
masu kurawa sarki Taryan idanu cikin
tsananin mamaki.

ME ZAI FARUYANZU
TSAKANIN SU JARUMI SALMANU
DA SARKI TARYAN?

YAUSHE NE ZA A CI GABA DA
WANNAN GASA TA KAMBUN
JARUMTA, KUMA WAYE ZAI SAMI
NASARAR LASHE GASAR A
KARSHE?

Mu hadu a litafi na gaba don jin
yadda za ta kasance.

Marubucin littafin
Abdulaziz Sani M Gini
Typing by AA Misau
WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment