Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gagarumar bajinta a nahiyarsu."
Gaba ɗayansu sun taho nan don na sanar dasu hanyar da zasu bi suje kogon Muddaril Ikisina.
Lallai gobe iyanzu sun iso,sai ku yi haƙurin zuwan goben,domin nayi muku jawabi tare dasu a lokaci guda,kuma na sallameku ku tafi izuwa wannan gagarumar tafiya."
Take wata kuyangar aljana ta bayyana gabansa ta duƙa cikin biyayya da gimamawa.
Hulumul Makahur ya dubeta yace,
"Yake Ikilis na umarce ki daki kai manyan baƙinmu izuwa ga masaukinsu a basu kyakkyawar kulawa domin su sami hutu da nutsuwa.
Gobe iwar haka a dawo mini da su nan."
Ikilis ta ɗago kai tace,
"An gama ya shugabana."
Kafin su yarima Sammaru suce wani abu tuni Ikilis ta shafe su da fukafukanta guda ɗaya wanda ya lulluɓe su tamkar an jefa su cikin rijiya.
Kawai sai suka ɓace,gaba ɗaya tare da Ikilis ɗin.
Cikin abinda bai wuce daƙiƙa uku ba suka tsinci kansu a cikin wani ƙasaitaccen gida mai kyawun gini da abubuwan ƙasaita irin na sarakunan duniya.
Barori da kuyangi na bil'adama kyawawa,kuma tsala-tsala nata kai
komo,suna ta hidima.
Cikin matuƙar mamaki yarima Yauhana ya dubi Ikilis yace,
"Nan kuma a ina muke?"
Koda jin wannan tambaya sai Ikilis ta bushe da dariya tace,
"Ai nan masaukin baƙi ne irin ku sarakai.
Daga can fadar mai girma Hulumul Makahur inda na ɗauko ku zuwa nan tafiyar wata uku ce,amma na gajarce ta izuwa daƙiƙa talatin.
Ga gadaje nan da kujeru,masu taushi,kuma ga abinci nan da abin sha iri-iri,haka kuma ga matanan kyawawa sai kun zaɓi waɗanda kuke so,ku zauna ku huta sai gobe zan dawo na kwasheku na mai da ku can fadar mai girma."
Ikilis na gama faɗin hakan ta ɓace musu ɓat.
Cikin farin ciki Sammaru,Yauhana da boka Karluz suka hau ciye-ciye da shaye-shaye har sai da suka sha giya suka bugu,kuyangi kuwa suka rinƙa yin kiɗa da rawa don ɗebe musu kewa.
Kai a taƙaice dai anan suka shagala da more jin daɗin rayuwa tamkar sun manta da abin da yasa suka baro gida.
Washe gari kuwa Ikilis ta dawo masaukin su yarima Sammaru a daidai lokacin da tayi alƙawarin dawowa.
Koda zuwa sai ta riskesu a kwance su duka suna ta sharar barci.
Cikin
mamaki ta dubi shugabar kuyangin gidan tace,
"Me ya faru naga baƙina suna ta yin barci tun jiya,kawo i yanzu?"
Shugabar kuyangi ta risina tace,
"Ranki ya daɗe ai tun da kika tafi kika bar su suka shagala da ciye-ciye da shaye-shaye,kuma suka far mana basu gushe ba suna more rayuwarsu har dare ya shuɗe kuma alfijir ya keto.
Daga sannan ne suka kama aikin rago har yanzu kuma basu farka ba."
Koda jin wannan batu sai Ikilis ta ƙyalƙyale da dariya,tana mai cewa,
"Tabɗijam yanzu a haka ne waɗannan ragwagen zasu je kogon Muddaril Ikisina.
Ai kuwa da ganan ma sun faɗi jarrabawa.
A yi dai mu gani,kallo ne namu kawai."
Tana gama faɗin hakan ta lulluɓe su da fukafukinta guda.
Take ta ɓace tare dasu bata bayyana a ko'ina ba sai a tsakiyar fadar boka Hulumul Makahur.
Da zuwa ta yarɓar dasu a ƙasa tamkar wadda ta deɓo gawarwaki.
A wannan lokaci gimbiya Ashwarya,yarima Lubaika da yarima Larbuz na zaune a cikin fadar sun harɗe akan kujeru na alfarma suna masu sauraron bayani daga bakin boka Hulumul Makahur bayan ya gama yi musu barka da zuwa.
Bayan Ikilis ta ajiye su yarima Sammaru,sai Hulumul Makahur ya dubi su gimbiya Ashwarya ya nuna su Sammaru yace,
"Yauwa ga abokan tafiyar taku waɗanda naba ku labarin cewa suna can masaukin baƙi."
Gimbiya Ashwarya ta dube su tace,
"Me ya faru gare su suke barci,mai nauyi haka?"
Hulumul Makahur ya bushe da dariya,sannan yace,
"Ai sun sha giya ne mai yawa jiya,kuma sun hole sosai bari na tashe su daga barcin."
Nan take boka Hulumul Makahur ya nuna su da đanyatsansa guda na hagu.
Take wata irin iska mai ɗan karan sanyi ta fito daga cikin ɗanyatsan ta buge su suka miƙe zumbur a firgice,suka hau kalle-kalle tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni.
Koda yarima Sammaru da yarima Yauhana suka yi arba da gimbiya Ashwarya sai suka ruđe,suka kiɗime saboda ganin tsananin kyawunta da kwarjininta.
Yarima Lubaika da yarima Larbuz suka dubi juna suka yi murmushi.
Lubaika ya yiwa Larbuz raɗa a kunne yace,
"Ya kai abokina dubi fa yadda suma suka ruđe,lallaı muma ba mu yi laifi ba,da har muka yi faɗa da juna akan gimbiya domin kyawunta ya kai matuƙa."
Larbuz yayi dariya ya lce,
"Ƙwarai kuwa zancenka dutse ne abokina."
Boka Hulumul Makahur ya dubi su yarima Sammaru yace,
"Ya ku waɗannan 'ya'yan sarakai ku nutsu ku dawo cikin
hayyacinku ku sani cewa in dai kyawun gimbiya Ashwarya ne ke ɗibarku to ku sani zan nuna muku wadda ta fita kyau sau dubu nan ba da daɗewa ba."
Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuƙe 'ya'yan sarakunan nan su duka huɗun.
Ita kuwa gimbiya Ashwarya sai kishi ya kamata tace a ranta,
"Yanzu a cikin duniyar nan har akwai wata mace wadda ta fini kyau?
Lallai zan so na ganta a duk inda take."
Hulumul Makahur yayi gyaran murya yace,
"Kamar yadda nayi alƙawari cewar yau zanyi muku bayanin hanyar da za ku bi ku je kogon Muddaril Ikisina to yanzu zan cika wannan alƙawari,don haka sai ku nutsu da kyau,ku saurareni,kuma ku kiyaye dokokin da zan faɗa muku,domin idan kuka kuskure guda ɗaya ku duka ne za ku hallaka.
Abu na farko shi ne daga nan zaku yi tafiyar shekara bakwai idan akan dawakai ne,zuwa inda tsakiyar wannan duniya tamu
take idan kuwa akan hadiman aljanuna ne kwana bakwai kacal za ku yi.
Zaku keta ta cikin manyan dazuzzuka guda uku masu mugun haɗari kafin ku je wannan wuri.
Daji na farko ana kiransa da suna Baluzul Mahaful.
Babu komai a cikin wannan jeji face tarin dodanni ƙabila-ƙabila har kala bakwai.
Waɗannan dodanni basu da abinci face naman bil'adama.
Lallai a cikin wannan daji sai kun yi tafiyar kwana uku cir in dai akan hadimaina ne,tsafi ba zai ƙwaci rayuwarku ba,a wannan daji face tsagwaron ƙarfinku da kuma iya yaƙinku,lallai anan ne zaku jarraba iyakar jarumtakarku.
Daji na biyu kuwa shi ne wanda ake kira Zamutul Makatul.
Babu komai a cikinsa face mugayen namun dawa,kuma sihirtattu.
Dole ne ku yi amfani da tsafi da kuma ƙarfin damtse a wannan wuri.
Ga wanda ya san sirrin daji daga cikinku zai samu sauƙin kuɓuta a jejin Zamutul Makatul.
Shi ma sai kun shafe kwana uku cur a cikinsa.
Daji na uku kuwa wanda shine na ƙarshe ana kiransa da suna Halalil Masur.
Shi kuwa wannan jeji babu komai a cikinsa face wata gagarumar wuta mai ci a ko'ina sama da ƙasa.
A tsakiyar sararin sama ne kaɗai babu wutar,kuma
dole sai dai ku bi ta kan wata doguwar gada a ko yaushe harshen wuta na lasota.
Wani karon sai tayi girgiza kamar zata faɗo ƙasa cikin wutar ko kuma ka ga iska na majajjawa da ita,kamar zata yi sama da ita,cikin wutar dake sama.
Dole ne ku yi tafiyar kwana guda akanwannan gada.
Yayin da kuka je ƙarshen gadar zaku fita daga jejin Halalil Masur ku tsinci kanku a tsakiyar wani tafkeken jeji wanda babu komai a cikinsa face wata doguwar bishiyar gwanda guda
daya cal,wadda tsawonta ya kai zira'i ɗari uku.
A ƙarshen wannan bishiya ne hanyar zuwa duniyar ƙasa take.
Zan baku wani icen tsafi wanda shine zai huda muku ƙasa ku shige cikinta ku yi ta tafiya har sai kun iso tsakanin duniyar bakwai da duniyar takwas,inda kogon Maddarul Ikisina yake.
To fa daga wannan wuri ban san yadda za ku yi ku iya shiga cikin kogon Maddarul Ikisina ba.
Iyayena da 'yan uwana ma a wannan wuri suka hallaka.
Bayanina na ƙarshe a gareku shi ne a cikin bincikena na gano cewa duk duniyar nan babu wani mahaluƙi da zai iya shiga cikin wannan kogon dutse na Maddarul ikisina a sauƙaƙe face gimbiya Fauwaza 'yar sarki Usman na birnin Misra,wadda ita ce macen da tafi gaba
ɗayan matan duniya kyawu a wannan zamani.
A halin yanzu ta baro ƙasar ta tare da waɗansu dakarun yaƙi,don yaɗa addininsu wanda akewa laƙabi da Addinin Musulunci.
Duk ƙasar da ta je sai ta cisu da yaƙi,ta kuma hana su yin addinin da suka gada tun iyaye da kakanni ta ɗora su bisa tafarkin nata addinin.
Haƙiƙa gimbiya Fauwaza na da tarin baiwa da sirrikan nasara,ba zamu iya ja da ita ba,gaba ɗayanmu nan face mun mallaki sirrikan tsafi adadin wanda Tazibul Luhucul ta mallaka."
Boka Hulumul Makahur na gama wannan jawabi ya yi nuni da hannunsa izuwa ga allon tsafi sai ga gimbiya Fauwaza tare da dakarunta suna gwabza yaƙi da kafirai a cikin birnin
Askandariya.
Koda su yarima Sammaru suka
ƙyallara ido suka ga gimbiya Fauwaza sai kyawunta ya ruɗe su suka shiga sumbatu da koke-koke tamkar waɗanda suka shekara cikin cutar begenta.
Ita kanta gimbiya Ashwarya saida ta raina kanta ta tabbatar da cewa ita kam ba kyakkyawa bace,kyau na wajen gimbiya
Fauwaza domin ita ce ƙurunƙus.

********

Lokacin da sarki Dujalu ya zo daidai nan a labarinsa sai wata baƙar kyanwa ta shigo cikin fadar a guje ta nufi inda karagar sarki take.
Koda
ganin kyanwar sai sarki Dujalu ya miƙe zumbur cikin firgita,saura ƙiris yayi abin kunya ya ruga da gudu.
Kawai sai tsoho Rafkanagu ya cafke magen ya jefa ta cikin bakinsa ya tauneta da ranta ya haɗiye.
Al'amarin da yayi matuƙar razana sarki da sauran 'yan majalisarsa kenan,domin basu taɓa ganin mutumin da ya cinye mage da ranta ba,sai yau.
Nan fa kowa ya sha jinin jikinsa aka fara tunanin anya kuwa wannan tsohon mutum ne.
Rafkanagu yayi gyatsa sannan ya dubi sarki Dujalu cikin murmusi yace,
"Ranka ya daɗe ai sai ka cigaba da bamu wannan labari don mu ji yadda ƙarshen wannan Hikaya ta bokanya Tazibul Luhucul zata kasance."
Cikin alamun rashin yadda sarki Dujalu ya dubi tsoho Rafkanagu yace,
"Kai ba za ta yiyu ba.
Kowa ya tashi ya bani wuri,ba zan cigaba da wannan labari ba
har sai na yi bincike akan wannan baƙuwar mage data shigo cikin fadata tana ƙoƙarin hallakani,kuma sai na yi bincike akan ka kai wannantsohon,tabbas kaima ban yarda da kaiba."
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin su Ruziyal da sarki Dujalu yayin da yake basu labarin Hikaya ta huɗu wacce itace ta ƙarshe sai
dai su tafi wani garin neman sauran labarai don hada rubutun sabon KUNDIN TSATSUBA.

Al'amarin su Jafar kuwa bayan ƙatuwar macijiyar nan ta haɗiye su sai kawai suka ga an jefo su cikin ainihin ta su duniyar ta cikin KUNDIN TSATSUBA aka watsar da su a gaban littafin kundi,har yanzu shafi na goma sha shida ne a buɗe.
Mazalish ta dubi Jafar,Gulzum, Yelisa da Mashrila tace,
"To fa mun gamu da bala'i mara sauƙi da ƙarshe zai fi kyau mu hanzarta ganin ƙarshen sa don mu huta da tararrabi."
Cikin fushi da tsawa Yelisa tace,
"Amma dai ke kin cika mahaukaciya.
Ai da mu kai kanmu cikin bala'i gwara shi bala'in yazo ya same mu da kansa."
Caraf Jafar ya ansa yace, "Haba Yelisa ai Mashrila ta fiki gaskiya me zamu tsaya jira kawai a cigaba da karɓar sakamako tunda dai mu da kanmu muka ɓaro wannan aiki."
Gulzum ya dakawa Jafar harara yace,
"Tabbas ka cika wawa,sususu.
To bamu yarda wani ya buɗe shafin gaba ba.
Kawai bari ya buɗe kansa."
Nan fa aka hargitse da kace-nace.
Ba su ankara ba har lokaci yayi kundi ya buɗe kansa,
izuwa shafi na sha bakwai,sai ga hoton ƙatuwar macijiyar nan,kuma babu rubutun komai a jikin shafin.
Nan take iskar kundi ta zuƙe su suka faɗa ciki.
Sai tsintar kansu suka yi gaban macijiyar a wata duniya dabam,kafin su yi wani yunƙuri tuni macijiyar ta wangame ƙaton bakinta ta haɗiye su gaba ɗaya.
Haka dai su Jafar suka dunga shiga cikin masifu iri-iri har guda dubu,kuma duk guguwar nan ce ta rinƙa kai su cikin masifun.
A cikin shafi na ashirin ne na KUNDIN TSATSUBA suka rabu da wannan guguwar bala'i bata sake ɗaukar su ta kai su wani wuri ba.
Bayan an watso su cikin duniyar su ne suka sami hutun daƙiƙa ɗari da ashirin,sannan KUNDIN TSATSUBA ya buɗe kansa izuwa shafi na ashirin da ɗaya suka yi arba da hoton wata duniyar da ke sararin samaniya.

SHIN GIMBIYA SIMA ZATA TSIRE JARUMI HUBAIRU DA WANNAN MASHI WANDA SARKI LU'UMANU YA BATA?
SHIN SARKI DUJALU ZAI ƘARASA LABARIN HIKAYAR BOKANYA TAZIBUL LUHUCUL?
YAUSHE NE SHAMHARU ZAI ZAMA MATSATSUBI?
INA LABARIN SU MARKAHUL SABUS WAƊANDA SHAMHARU YA MAIDA SU 'YAN MINI-MINI YA JEFA A ALJIHUN RIGARSA?
ME SU JAFAR ZA SU GANI A CIKIN WANNAN DUNIYA DAKE SARARIN SAMANIYA?
Mu haɗu a MATSATSUBI 3.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


2 Comments On MATSATSUBI Book 2
avatar
idris-idris-abubakar

10 months ago

Reply

Hausa

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to idris-idris-abubakar

Eh na hausa ne

Please Login or Register in order to submit comment