Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cire batun yaƙi da ni a ranka ka sanya tunanin nemo maganin cutar mahaifinka,domin kuna da ƙanƙanin lokaci.
Tabbas indai ba ka samo maganin ba kafin shekara uku daidai sai dai ka dawo ka iske gawarsa."
Cikin fushi Sammaru ya dubi Tazibul Luhucul yace,
"Ina ne inda wannan magani yake?
Na rantse da darajar mahaifina komai nisan wajen,komai masifar dake wajen sai naje na deɓo wannan magani."
Tazibul Luhucul ta sake ƙyalƙyalewa da dariya, tace, "Yaüwa haka 'näke sön naji furucin namiji mai zuciyar maza.
Kada ka damu nayi alƙawari zan faɗa sai ka jira zuwa tsakiyar daren yau cikakken bayani zai zo ya riske ka har nan."
Tana gama faɗin hakan ta rikiɗe ta zama wannan haske.
A hankali hasken ya rinƙa disashewa har ya ɓace ɓat.
Wannan shine abinda
ya faru tsakanin yarima Sammaru da uwar matsafa Tazibul Luhucul a can birnin Sin.
A sauran manyan ƙasashen duniya kuwa labari ya iske sarakuna cewa ga wata annobar nan na shirin afko musu,wato gaba ɗayansu zasu zama naƙasssu. Sun sami wannan labari ne daga bakin aljanun da suke bautawa.
Nan da nan hankalin sarakunan duniya ya dugunzuma,suka shiga ganawa da aljanun nasu don neman tsari daga wannan masifa mai shirin afkowa.
Kowa ya tuntuɓi aljaninsa nasa sai aljanin ya ce da shi ai wannan al'amari yafi ƙarfin sa domin kuwa ba kowane zai haddasar dashi ba face bokanya Tazibul Luhucul uwar
matsafa,ita kuwa wannan boka a halin yanzu duk duniya babu wani matsafi ko matsafiya mai tarin sirrikan tsafi kamarta.
An ce tana da sirrin tsafi guda miliyan dubu tara da casa'in da tara guda ɗaya ne kacal ya rage mata ta mallaka,kuma duk ran da ta mallake shi za ta iya mayar da duniya tamkar ƙwan kaza a gaban ta.
Waɗannan sirrikan tsafi data mallaka guda miliyan dubu tara da casa'in data tara ta ɓoye su
ne a cikin wata taska,ita kuwa an ajiye tana a cikin wani kogon dutse.
Shi kuwa kogon yana tsakanin duniya ta bakwai
da ta takwas daga cikin duniyoyin ƙarƙashin ƙasa.
Babu wani abu mai rai da ya taɓa zuwa wannan wuri,kuma ba za'a samu wanda zai iya zuwa ba.
Lokacin da sarakuna suka ji wannan jawabi sai duk suka ɗimauce suka firgice, wasu ma dalilin rikirkicewar al'amuransu kenan.
Wasu suka kama kuka,wasu kuma suka kama ciwo don tsananin fargabar wannan baƙin labari.
Su kuwa aljanun na su sai suka rinƙa kwantar musu da hankali suna cewa su yi haƙuri su saurari jawabin da uwar matsafa za ta yi dangane da inda maganin wannan cuta yake,lallai zasu samo musu shi. A wannan lokaci manya ƙasahen duniya mafi girma guda shida ne,ƙasa ta farko ita ce birnin Sin,sai kuma birnin Hindu sai Rum,Ƙisra,Misra da kuma Farisa.
Ƙasar da ake ganin za ta iya biyo bayan waɗannan ƙasashe ita ce Askandariya.
A can fadar bokanya Tazibul Luhucul kuwa wato cikin kogonta na tsafi gaba ɗaya
hadimanta sun taru sun durƙusa a gabanta yayin da take zaune bisa karagarta ta mulki.
Amma bisa mamaki sai suka ga tayi shiru ba ta ce da su uffan ba,kuma ta sunkuyar da kai ƙasa ta nutsu ainun kamar mai jiran umarni.
Jim kaɗan sai suka ga wani haske mai
launin ɗorawa ya bayyana a tsakiyar fadar yana katantanwa a waje guda.
Koda ganin hasken sai Tazibul Lubucul ta miƙe zumbur cikin farin ciki ta nufe shi.
Kafin ta isa gaban hasken tuni ya rikiɗe ya zama wata kyakkyawar aljana wadda ke riƙe da sandar tsafi iri ɗaya da ta Tazibul Luhucul.
Nan take wannan aljana ta rungume Tazibul Luhucul suka sumbaci junansu,cikin tsananin farin ciki.
Aljanar ta dubi Tazibul Luhucul cikin murmushi tace,
"Gaishe ki ƙawata,haƙiƙa duk abubuwan da na umarce ki da yi kin yi su daidai.
Ina mai yi miki bushara cewa burin mu ya kusa cika.
Tabbas idan muka sanya wannan cuta a jikin manyan sarakunan duniya na bil'adama zamu gano inda wannan sirrin tsafi guda ɗaya yake wanda ya gagaremu samu."
Tazibul Luhucul ta yi murmushi gami da ƙyalƙyalewa da dariya, sannan tace,
"Yake Saubatul Azwas ki yi sani cewa raina cike yake da farin ciki bisa wannan bushara da kika zo mini da ita,kuma dama ke nake jira ki iso,domin na tara dukkanin hadimaina gasu suna jira sai ki faɗa mana yadda zamu kai ga gaci.
Koda yake kin san cewa hadiman nan nawa basu san ki ba ya kamata na gabatar dake a gare su ko
kuma ki gabatar da kanki don ance waƙa a bakin mai ita tafi daɗi."
Saubatul Azwas ta yì murnushi,sannan ta dubi hadiman Tazibul Luhucul waɗanda gaba ɗayansu sun kasance aljanu ne,kuma su talatin da bakwai ne.
Guda talatin mata ne zallah, guda bakwai ne maza. Saubatul Azwas ta fuskance su
tace,
"Ni fitacciya ce a cikin al'ummar aljanu amma ba a sanni ba a fuska,domin ban yarda na bayyana kaina ba,tun ina ƙarama kawo iyanzu saboda wani buri dake cikin zuciyata. Yaku waɗannan hadimai ku sani cewa ni ce SAUBATUL AZWAS 'ya' guda ɗaya ga sarki Kalimul Ifwan."
Koda jin wnanan batu sai gaba ɗayan hadiman nan suka yi sujjada ga Saubatul Azwas cikin girmamawa,ba su yadda sun sake haɗa idanu da ita ba,kuma take jikinsu ya kama
ƙyarma,kamar a ce ƙyat su tashi su ruga.
Ba wani abu ba ne ya sa waɗannan hadimai firgita face sanin cewa sarki Kalimul Ifwan shi ne sarkin da ya zamo abin tsoro ga dukkanin aljanun duniya a zamaninsa,domin ya kasance ƙasurgumin matsafi. Saboda tsananin ƙarfin tsafinsa idan zai yi yaƙi da wata ƙasar yana daga zaune yake yaƙin,kuma yana iya
maishe da garı guda turɓaya har da komai na cikin sa,wato yana iya maishe da aljanu,dabbobi da komai na su ya zama turɓaya.
Kuma wannan turɓaya zata cigaba da wanzuwa abadan-abidina.
Har wannan sarki ya gama zamaninsa ba a taɓa samun wanda ya sami galaba akan sa ba.
An sani cewa yana da 'ya' guda ɗaya kacal a duniya kuma kafin ya mutu ya bata gaba ɗayan sirrikan tsafinsa.
Bayan ya mutu sai aka nemi wannan 'ya' tasa sama da ƙasa aka rasa.
Yayin da Saubatul Azwas ta fuskanci cewar waɗannan hadimai sun tsora ta da ganinta sai ta daka musu tsawa tace,
"Na umarce ku da ku iya bakinku,kada ku kuskura ku sanar da wasu cewar ina nan a cikin duniyar nan.
Ku sani cewa a duk inda kuke ina tare da ku,kuma ina ganinku ina jin ku,koda kuwa kuna ƙarshen bangon duniya ne,ko cikin kuratandu.
Ina son ku nutsu ku tattara
hankalinku waje guda ku saurari jawabin da zan muku bisa gagarumin aikin da ke gabanmu.
Idan har muka yi nasara gaba ɗayanku ku talatin da bakwan nan zaku zama manyan sarakai a cikin ƙasashen aljanu,kuma za
mu ba ku dukiya irin wacce baku taɓa ganin mai yawan taba.
Ina so
ku sani cewa ni da ƙawata Tazibul Luhucul bamu da wani buri wanda yafi na mallakar duniya gaba ɗaya.
Ni ina son na mallaki ƙasashen aljanu,ita kuma tana son ta mallake ƙasashen bil'adama.
Lallai mu biyu kacal ba zamu iya wannan aiki ba,sai da taimakonku.
Zan kasa ku gida biyu,kaso guda zai bini,ɗaya kason kuma zai bi ƙawata Tazibul Luhucul. Mataki na farko shi ne nan da kwana bakwai zamu tafi izuwa ƙasashen sarakan duniya mu zuba musu wanna cuta ta mutuwar ɓarin jiki.
Wannan ciwo zai zame musu ajali,amma sai sun yi shekara uku suna jinya.
Da zarar sun mutu zamu sace gawarwakin su mu zuba a cikin wani sunduƙi gaba ɗaya.
Ina nufin gawar sarakunan aljanu da gawar sarakunan bil'adama za mu gwamutsa duka a cikin wannan sunduƙi ba zamu buɗe sunduƙin ba sai bayan shekara uku,idan muka buɗe zamu tarar ƙasusuwansu,naman jikinsu kuma ya gama ruɓewa ya zama tsutsa.
Haka kuma zamu đebi ƙasusuwan da tsutsotsin mu zuba a cikin wata hodar tsafi mu dama,sannan mu zuba a cikin wata ƙatuwar tukunyar tsafi mu yi ta dafawa har tsawon shekara uku.
Lallai dole ne ku yi ta gadin wannan
tukunya tsawon shekara uku,don kada ɗigo ɗaya na abin dake ciki ya salwanta.
Idan shekara ukun ta cika zamu buɗe tukunyar mu iske abinda ke ciki ya zama salalan tsafi. Zamu ɗauki wannan salala mu tafi da shi izuwa taskar tsafina.
A can ne zamu haska madubin tsafina a jikinsa ya nuna mana inda sirrin tsafi guda ɗaya yake, wanda shi ne kaɗai sirrin da ban mallaka ba a duniya.
Da zarar na je na ɗauko wannan sirri burinmu gaba ɗaya ya cika."
Koda Saubatul Azwas ta zo nan a zancenta sai gaba ɗayan hadiman nan suka cika da mamaki.
Ɗaya daga cikinsu wata mace mai ƙarancin shekaru ta dubi Saubatul Azwas tace,
"Ya shugabata shin za ki iya sanar damu a inda taskar tsafinki take?"
Koda jin wannan tambaya sai Saubatul Azwas ta murtuke fuska,sannan ta dakawa mai tambayar harara tace,
"Wannan kuma wace irin banzar tambaya ce?
Mene ne amfanin sanin wajen da za ki shige shi da ƙafarki idan har buƙatar mu ta biya."
Mai tambayar ta duƙar da kai ƙasa tace,
"Tuba na ke ranki ya daɗe ki gafarce ni."
Wata tsohuwa ta ɗaga hannu tace,
"Ranki ya daɗe a cikin bayaninki na fuskanci cewar sai
mun yi shekara tara muna yin wannan aiki,kuma na ji kin ce dole ne mu yi gadin wannan tukunya don kada ɗigo ɗaya na abin da a ke ciki ya salwanta, idan ɗigo ɗaya ya salwanta me zai faru?"
Saubatul Azwas ta yi ajiyar numfashi tace,
"Ke dakata ki ji bama ɗigo ɗaya ba,idan muka bari ƙuda ya tsotsi ƙwayar zarra daga cikin wannan abu da muke dafawa a tukunyar,gaba ɗayanmu shirinmu ya wargatse sai dai mu dawo da baya mu fara sabon shiri,wato mu samo
gawarwakin sababbin sarakunan duniya,mu sake ɓata wasu shekaru taran,muna haɗa wannan sinadari."
Saubatul Azwas ta a cigaba da cewa,
"Yanzu dai abin da nake so ku fahimta shine,dole ne ku kiyaye wasu abubuwa yayin da zamu je waɗannan manyan ƙasashen duniya guda biyar don yaɗa cutar mutuwar rabin jiki ga sarakunansu da 'yan majalisarsu.
Ƙasashen nan dai da za mu je sune,Hindu,Rum,Ƙisra,Misra da Farisa.
Ni ce zan je birnin Hindu,Rum da Ƙisra.
Ita kuwa Tazibul Luhucul za ta je Rum,Ƙisra,Misra da Farisa. Kamar yadda na fada muku ɗazu,ku kuwa zamu rabaku kaso biyu.
Kaso guda su bini,đaya kason su bi ƙawata Tazibul Luhucul. Ni da
ita mune zamu je gidajen sakaruna,ku kuma kuje gidajen 'yan majalisarsu.
Gaba ɗayan ku zaku tafi da wani bututun tsafi ne,wanda shi za ku hura iskar cikinsa ta zuba kan 'yan majalisar da zarar kun yi hakan take cutar mutuwar rabin jiki za ta kama su.
Ni da Tazibul Luhucul kuwa zamu je ne da sandar tsafinmu kawai da zarar mun nuna su
da ita za su kamu da cutar.
Ku yi sani cewa babu inda zamu je sai da tsakar dare.
Duk inda muka je muka tarar da cewar Sarakunan suna yin wani abu daya danganci tsafi ko bauta kada mu kuskura mu yi musu komai.
Wanda kuwa ya bijirewa wannan doka take zai zama gunki.
Ku sani cewa bai zamo lallai sai suna yin barci ba,amma babu lokacin da yafi kyau face lokacin da suke tarawa da iyalansu.
Ina daɗa tunasar da ku cewa wanda duk ya manta ya kusance su a lokacin da suke aikin tsafi ko bauta zai zama gunki,idan kuwa ya zama gunkin ni kaina ba zan iya dawo
da shi ainihin halittar sa ba.
Da wannan batu nake muku sallama zan tafi ba zan dawo na ba sai bayan kwana bakwai,don mu ɗunguma mu tafi aikatar da wannan babban aiki."
Koda Saubatul Azwas ta zo
nan zancenta,sai ta juya ta fuskanci Tazibul Luhucul
suka rungume juna đa sumbatar goshinsu suka yi sallama.
Nan take Saubatul Azwas ta
rikiɗe ta zama haske mai launin đorawa.
Hasken ya disashe ya ɓace ɓat. Ba tare da ɓata lokaci ba Tazibul Luhucul ta ware aljanu goma sha đaya daga cikin waɗannan hadimai nata ta rarraba musu wasiƙa tace maza su je su kai gidan sarki Alyasil Buhus da 'yan majalisarsa a cikin wannan dare.
Nan take hadiman suka tafi aiwatar da wannan umarni.
Wannan shi ne abin da ya faru a fadar bokanya Tazibul Luhucul bayan ƙawarta aljana Saubatul Azwas ta kawo ziyarar bazata.
A can gidan sarki Alyasil Buhus kuwa da kuma gidajen 'yan majalisarsa har yanzu hankali bai kwanta ba,domin yadda iyalansu suka ga rana haka suka ga dare,wato har dare ya raba basu rintsa ba.
Ba zato,ba zammani sai su rinƙa ganin wasiƙu na dira,kuma ba'a ga wanda ya kawo ba.
Lokacin da wasiƙar gidan sarki
Alyasil Buhus ta faɗo a tsakiyar
turakarsa iyalansa gaba ɗaya na zaune sun yi tagumi.
Wasu suna kuka,wasu kuma suna juyayin wannan hali da sarki ya shiga rana tsaka.
Cikin sauri da zafin nama yarima Sammaru ya yunƙura ya ɗauki wannan wasiƙa ya warware ta ya fara karantawa kamar haka:-
"Daga uwar matsatan duniya Tazibul Luhucul zuwa ga sarkin birnin Sin Alyasil Buhus.
Bayan gaisuwa a gareka gami da jajen wannan masifa da ta same ka ina mai farin cikin sanar da kai cewa idan har kana son ka warke daga wannan cuta dole ne aje taskar tsafina a deɓo ruwan tsumin tsafin da nake sha a baka ka sha.
Da zarar ka sha wannan tsumi take za ka warke.
Ka yi sani cewa taskar tsafina na cikin wannan kogon da ake kira MADDARUL IKISINA,shí kuwa Maddarul Ikisina na nan tsakanin duniya ta bakwai da ta takwas daga cikin duniyoyin ƙarƙashin ƙasa.
Sa'a na ga mai rabo.
Lallai me nema yana tare da samu,amma abin da kamar wuya tsohuwa da tauna ƙwallon
goruba."
Ko da Sammaru ya zo nan a cikin karatun wasiƙar,sai yayi jifa da wasiƙar.
Cikin matsanancin fushi ya zare takobinsa ya nufi ƙofar fita daga cikin turakar sarki Alyasil Buhus,cikin sauri yan'uwansa maza suka ruga suka sha gabansa suna masu bashi baki da lallaminsa,da ƙyar ya haƙura ya dawo ya zauna sannan ya dubi sarki Alyasil buhus yace,
"Ya kai Abbana kayi
sani cewa haƙiƙa wannan matsafiya ta raina mana hankali.
Shin a ina aka taɓa jin cewar wani mahaluƙi ya taba zuwa cikin wata duniya dake ƙarƙashin ƙasa."
Sarki Alyasil Buhus ya muskuto da fuskarsa da ƙyar ya dubi yarima Sammaru yace,
"Ya kai ɗana haƙiƙa akwai wasu duniyoyin a cikin ƙarƙashin ƙasa kuma na sami wannan labarine daga bakin bokana Hulumul makahur.
Na umarceka da kayi shiri gobe da safe ka tafi izuwa jejin Dulmas ka riski boka Hulumul Makahur ka bashi wannan wasiƙar wacce uwar matsafa ta kawo kuma ka buƙaci taimakonsa a bisa wannan al'amari.
Tabbas zai taimaka muddin akwai halin taimakawar."
Koda jin haka sai Sammaru ya miƙe tsaye ya dubi Alyasil Buhus yace,
"Ya kai Abbana kayi sani cewa bazan iya bari sai gari ya waye ba,tabbas a yanzu zanje nayi shiri na tafi jejin Dulmas kuma na rantse da darajarka ko boka Hulumul Makahur ya taimakeni ko bai taimakeni ba,ba zan dawo ba sai da tsumin tsafim uwar matsafa.
In kuwa ban samo shi ba kar kuyi sallama gaba ɗaya sai wata rana.
Idan da rabon zamu sake saduwa zan dawo."
Ko da jin haka sai mahaifiyar Sammaru ta rungumeshi kuma ta fashe da kuka,suma sauran
'yan'uwan na sa duk sai suka matso gareshi suka rungumeshi suna kukan gaba ɗaya.
Sarki Alyasil bubus ya share hawaye a idanunsa yace,
"Ya kai ɗana ka sani cewa kaine babba a gidan nan don haka kaine mai jiran karagata.
Mai zaisa ka yanke wa kanka wannan ɗanyen hukunci yanzu idan baka nan waye zai gaje ni?"
Sammaru ya saki yan'uwansa ya dawo ga mahaifin nasu ya durƙusa a gabansa ya kama hannusa na dama ya sumbata a lokacin da gaba ɗayansu suna zub da hawaye.
Sammaru yace,
"Ya kai Abbana kayi sani cewa ko bana nan akwai ƙanne na don haka sai a zaɓi wanda ya fi dacewa daga cikinsu a bashi sarauta."
Alyasil Buhus yace,
"Ai kaine kafisu dacewa domin ka gajeni a komai."
Sammaru yayi shiru tsawon 'yan daƙiƙu sännan yace,
"Na yarda haka ne amma ina so ka sani cewa nine kuma nafi dacewa da tsayawa tsayin daka don kare darajarka da ƙimarka.
In dai ina numfashi a doron ƙasa bazan taɓa barin rayuwarka a cikin tozarta ba,lallai sai nazo da maganin wannan cuta taka kafin cikar shekara uku,sai na dawo." Sammaru na gama faɗin haka ya miƙe da sauri ya fice daga cikin turakar.
Da yake dama Sarmmaru bai taɓa yin aure ba kai
hasalima bai taɓa son wata 'ya mace ba kuma a gaba ɗayan birninsu bashi da aboki ko guda ɗaya don haka bai sake neman kowa ba don yin sallama nan da nan yasa aka shirya masa guzuri sannan yayi shigar yaƙi ya hau wani baƙin ingarmar doki ya kama hanya ya nufi dajin dulmas acikin wannan dare.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin sarki Alyasil Buhus na birnin Sin tare da ɗansa jarumi Sammaru bayan wasiƙar bokanya Tazibul Luhucul ta riskesu.
A can birnin Hindu kuwa sarki Bahacal da 'yan majalisarsa sun kasance cikin tsananin tashin hankali tun sa'adda boka Kirish ya sanar dasu cewa nan da kwana bakwai annobar ciwon
mutuwar rabin jiki zata same su kuma sai sun shekara uku suna wannan cuta sannan zasu mutu.
Tun a lokacin ne suka tambaye shi,shin babu wata hanya da zasu iya bi su kare kansu daga afkuwar wannan masifa?
Boka Kirish yace ai ba wani bane zai aiko da wannan masifa ba face uwar matsafan duniya bokanya Tazibul Luhucul wadda ke zaune a birnin Sin. Tabbas wannan bokanya tafi ƙarfin dukkanin matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da ita.
Abin da za'a iya yi shine kawai a saurara aji hanyar da za'a bi a samo maganin wannan cuta domin
Tazibul Luhucul tayi alƙawarin baiyana hakan.
A ranar da wasiƙar Tazibul Luhucul ta riski sarki Alyasil buhus da 'yan majalisar boka Kirish yaje fadar sarki Bahacal inda ya iskeshi tare da 'yan majalisarsa gaba ɗaya da kuma sauran fadawa da matanen garı a zaune cikin matuƙar ga zulumi da fargaba.
Da zuwa sai boka Kirish yayi gaisuwa ga sarki sannan ya zaiyana musu batun zuwa kogon maddarul ikisina don đebo tsumin tsafin bokanya Tazibul Luhucul kuma ya sanar dasu a inda wannan kogo yake.
Koda jin wanan batu fiye da kowa ne lokaci,take wasunsu suka kama kuka wasu kuwa suka rinƙa nadamar kasancewarsu a cikin wannan masarauta.
Ana cikin wannan hali ne gimbiya Ashwarya ta shigo cikin fadar bisa wani farin ingarman doki sanye da kayan yaƙi kuma
ta ɗora gawar wani murgujejen zaki akan wuyan dokin. Dawowarta kenan daga farauta sai ta samu labarin cewa ga boka Kirish can a fada zai yi ƙarin bayani dangane da masifar da akace zata zo ta riski mahaifinta da 'yan majalisarsa. Tun sa'adda labarin al'amarin ya fara zuwa kunnenta ta ɗauki abin tamkar tatsuniya don ma har sai da ta yiwa boka Kirish rashin kunya tace taga alama ya fara zautuwa tunda ya fara zuwa da labaru
masu kama da almara.
A lokacin da ta faɗi hakan boka Kirish baiyi fishi ba sai yace da ita ta zuba ido izuwa lokacin da abin zai faru lallai zata gasgata shi ta tabbatar da gaskiyar al'amarin.
Gimbiya Ashwarya kyakkyawar budurwa ce ta kwatance wadda shekarunta baza su fi sha tara ba.
Tun tana ƙarama ta taso da jarumtaka,rashin tsoro da kuma iya yaƙi,tana da matuƙar iya jure wahala,yunwa da ƙishirwa kuma idan ta kece da gudu ko barewa albarka,tana da matuƙar zafin nama kuma ita kaɗai tana iya fasa taron mayaƙa.
Haka kuma tana da yawan shige da fice wajen matsafa don haka ta sami sirrikan tsafi da ɗan dama waɗanda suke taimaka mata sosai wajen fuskantar abubuwan haɗari.
Bisa wannan daliline take shiga daji ita kaɗai tayi farauta sannan ta dawo gida.
Lokacin da gimbiya Ashwarya ta shigo cikin fada ta iske mabaifinta sarki Bahacal da 'yan majalisarsa a cikin halin firgita da damuwa sai ta dubi boka Kirish tace yau kuma da wane labarin ƙanzon kuregen kazo mana dashi.
Boka Kirish ya dubeta cikin fishi ya maimaita abinda ya faɗi gasu sarki.
Ashwarya ta ƙyalƙyale da dariya tace bazan yarda da wannan labarin ba har sai idan abin da ka faɗi ya tabbata wato sai na
gani da idona cewar sarki da 'yan majalisa sun kamu da wannan cuta nan da kwana bakwai,idan kuwa al'amarin ya kasance na rantse da darajar karagar sarki sai na nemo maganin da zasu sha su warke kafin shekaru ukun su cika." Gimbiya Ashwarya na gama faɗin hakan ta kaɗa linzamin dokinta ta wuce izuwa cikin gidan sarautar tana mai tunƙaho da matsayinta.
Gaba ɗayan mutanen fadar suka bita da kallo.
Yana zaune acikin turakar tsafinsa ya runtse idanu,ƙafafunsa a tanƙwashe suke kamar lauje yana mai fuskantar wani ƙaton kaskon wuta wanda aka cika shi da ƙiraren tsafi kala-kala har guda ɗari ba daya.
Gashi babu garwashin wuta a cikin kaskon amma sai wani shuɗin hayaƙine ke ɓulɓula yana tashi sama daga jikin ƙiraren kuma basa ƙonewa.
A dai dai wannan lokacine sarki Jamshul tare da 'yan majalisarsa suka banko ƙofar shigowa wannan turaka suka faɗo ciki,a fusace boka Karluz ya waigo ya dubesu a tsanake ba tare da wata fargaba ba sannan ya kau da kai yaci gaba da yin abin da yake.
Su kuwa sai suka tsaya suka yi
cirko-cirko kamar masu jiran umarni su ƙaddamar.
Boka karluz bai sake waigawa gare su ba sai bayan daƙiƙa ɗari biyu da arba'in,cikin
girmamawa ya risina ya gaida sarki Jamshul yace,
"Ya sarkin sarakai lafiya kazo har nan turakana tare da 'yan majalisarka yanzu alhalin mun rabu akan cewa yau da yamma zan zo fada na riske ku?"
Koda jın wannan tambaya sai sarki Jamshul yace,
"Tun sa'adda ka labarta mana batun bokanya Tazibul Luhucul da kuma masifar da zata jeho mana muka kasance cikin matuƙar tashin hankali,mun kasa zaune mun kasa tsaye haka kuma mun kasa ci mun kasa sha,barci ya ƙauracewa idanunmu don hakane muka kasa jurewa har yamma tayi kazo fada,wannan shine dalilin da yasa kaga mun kawo maka ziyarar bazata,lallai muna son musan hanyar da zamu bi mu kuɓuta daga wannan masifa." Yayin da boka karluz ya ji wannan jawabi daga bakin sarki Jamshul sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubesu ɗaya bayan daya cikin alamun karayar zuciya yace,
"Ya shugabana kayi sani cewa bincikena ya tabbatar mini da cewar ba makawa wannan masifa sai ta sameku acikin waɗannan kwanaki bakwai,dama ɗaya ce a gare ku kuma ba komai bace face tafiya neman maganin wannan cuta bayan kun kamu da ita kafin shekara uku,ku sani cewa shi dai wannan magani wanda zaku sha ku warke ba
komai bane face tsumin tsafin bokanya Tazibul Luhucul wanda ke ajiye acikin taskar tsafinta.
Ita wannan taskar tana can cikin wani kogone da ake kira Maddarul Ikisina.
Maddarul Ikisina kuwa na nan tsakanin duniya ta bakwai data takwas daga cikin duniyoyin ƙarƙashin ƙasa."
Koda boka Karluz ya zo nan a zancen sa,sai sarki Jamshul da 'yan majalisarsa suka firgice suka rasa abin dake musu daɗi nan duniya,gaba ɗayansu suka yi tagumi suna masu juyayin al'amarin cikin zukatansu.
Ba zato ba tsammani sai suka ga yarima Yauhana ya fito daga cikin wani saƙo na wannan turaka shi kansa boka Karluz bai san sa'adda Yauhana ya shigo ba har ya ɓuya a cikin wannan saƙo don haka sai da yayi matuƙar mamaki.
Yauhana ya dubi mahaifinsa sarki Jamshul yace,
"Ya kai mahaifina ina son ku kwantar da hankalinku bisa wannan al'amari domin in dai akwai wannan kogo na Maddarul ikisina nayi alƙawarin sai na riskeshi a duk inda yake na deɓo muku wannan tsumin tsafi kafin cikar shekara uku."
Ko da jin haka sai sarki Jamshul ya fashe da kuka sannan yace, "Ya kai ɗana ka sani cewa duk faɗin ƙasarnan ta Rum babu wani abu da
nake so sama da kai,kai ne ɗana a duniya don haka bazan yarda ka tafi neman wannan abu mai haɗarin ba a sanadıyar hakan rayuwarka ta salwanta.
Ina son ka rungumi ƙaddara daga yau har izuwa ranar da zamu kamu da wannan cuta izuwa lokacin da rai zai yi halinsa domin ka gajeni ka zama sarkin Rum."
Yarima Yauhana ya dubi mahaifinsa cikin dakakkiyar zuciya yace,
"Ni kam na gama zartar da wannan hukunci kuma babu abin da zai hanani zartar da shi face mnutuwa,ba zan cika ɗa a gareka ba har sai na sami nasara bisa wannan buƙata.
Ya kai boka Karluz ina son ka sani akan turba yadda zan iya zuwa wannan wuri inda kogon Maddarul ikisina yake." Sa'adda yarima Yauhana yazo nan a zancesa sai boka Karluz yace,
"Ni kam nayi iyakar bincikena ban gano yadda za'a iya zuwa wannan wuri ba,amma a cikin binciken nawa na gano wani boka guda ɗaya wanda shi kaɗai ne zai iya faɗar hanyar da za'a bi aje wannan wuri.
Shi dai wannan boka sunansa Hulumul Makahur,yanzu haka yana nan zaune cikin wani jeji da ake kira Dulmas a yankin kasar Sin kuma yarima Sammaru ɗan sarki Alyasil Buhus mai mulkin ƙasar Sin ya tafi izuwa gareshi don ya sa shi
akan turbar zuwa kogon Maddarul ikisina."
Koda yarima Yauhana yaji wannan batu na boka Karluz cikin zaƙuwa yace
"Na umarce ka da kasa ɗaya daga cikin aljanunka ya ɗaukeni da gaggawa ya kaini wajen wannan boka a cikin ƙanƙanin lokaci."
Karluz yayi murmushi yace,
"Zanyi duk yadda kace amma nima ina rokon alfarma

2 Comments On MATSATSUBI Book 2
avatar
idris-idris-abubakar

10 months ago

Reply

Hausa

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to idris-idris-abubakar

Eh na hausa ne

Please Login or Register in order to submit comment