Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daddumar tsafi saiya miƙe zumbur ya dubeta yana mai cewa ranki ya daɗe ki ceceni kisa a fitar dani daga cikin wannan mugun wuri,ki
tuna cewa ni ne waziri Kuddaru babban wazirinki.
Koda jin haka sai Gimbiya Sima ta dubi Kuddaru tace,
"Waye kai,a ina kasanni?
Waishin ma a ina muka taɓa haɗuwa har da zakace ka sanni?"
Yayin da Kuddaru yaji wannan batu sai ya cika da mamaki baisan sa'adda ya fashe da kukaba yana mai cewa,
"Yanzu har daɗin daula yasa kin manta dani. Ranki ya daɗe kiji tsoran Ubangijin da kikayi imani da shi ki ceci rayuwata." Girnbiya Sima ta dubi sarki Lu'umanu tace,
"Wannan kuma wane wawan mutum ne haka kamar mahaukaci?"
Lu'umanu ya bushe da dariya
yace,
"Ai kuwa mahaukacine na ƙwarai,asalinsa bawana ne mai kula da bargar dawaki. Rana ɗaya ya sani taɓin hankali ya rínga kashe mini
đewakai. Ni kuma da naji haushin abin daya aikata sai nasa aka kamo shi nan aka ɗaure.
Bazan yi masa komaiba har sai na kama babban maƙiyina da'ake kira Hubairu sannan zan
haɗasu tare nayi musu kisan gilla."
Sima ta sake duban sarki Lu'umanu tace,
"Waye kuma Hubairu,kuma menene ya haddasa muguwar gaba a tsakaninku?"
Lu'umanu ya numfasa yace, "Hubairu wani hatsabibin yarone mai taurin kai da ƙarfin
sihiri bashi đa burin da yafi ya rabani dake kuma ya hallakani." Koda jin haka sai gimbiya Sima a dafe ƙirji cikin alamun razana tace,
"Ya kai masoyina duk wanda ya nemi shiga tsakanina da kai sai naga bayansa. Domin duk duniya babu abinda nake so sama da kai. Duk ranar da ka
kama Hubairu ka bani dama na tsireshi da mashi da hannuna don hankalina ya kwanta na tabbatar da cewa na kashe maƙiyinmu."
Koda jin haka sai sarki Lu'umanu ya bushe da dariya yana mai
cewa tabbas nayi miki alkawarin wannan dama kece zaki kashe maƙiyinmu da hannun ki.
Lu'umanu yaci gaba da rusa dariyar ƙeta har suka bar wannan wuri inda kuddaru ke zaune yana ta faman kuka da mamakin abin da ya faru tsakaninsa da Gimbiya Sima.
Kashe gari da sassafe fadar sarki
Lu'urnanu ta cika ta batse da jama'a. Baƙin sarakuna kuwa suka hallara daga manyan ƙasashe don amsa gaiyatar sarki Lu'umanu bisa ɗaurin aurensa da gimbiya Sima.
Nan take aka fara kaɗe kaɗe da bushe bushe,kayan ciye ciye
dana shaye shaye kuma suka yawaita a fadar fiye da buƙatar Jama'a.
Sarki Lu'umanu da Gimbiya Sima suka fito daga cikin gidan sarauta suka zo suka zauna akan karaga mai ɗaura aure ya fara
aikinsa. Ana cikin wannan haline aka ga aljani Abtarul hudes ya baiyana a sararin sama ɗauke
da jarumi Hubairu.
Koda sarki Lu'umanu ya ɗaga
kai yayi arba dasu sai ya hura musu wata irin iska mai sanyi daga cikin bakinsa,take suka
faɗo ƙasa sumammu.
Sarki Lu'umnu ya bushe da dariya yasa aka ɗauki jarumi Hubairu aka banƙareshi a jikin dirka sannan aka ɗaukeshi da igiya nan take yasa aka dauko kuddaru daga cikin kurkuku aka daureshi kusa da Jarumi Hubairu.
Kuddaru ya dubi jarumi Hubairu yaji daɗi a ransa yace tunda mun sake saduwa babu mamaki wannan karon ka ceci rayuwata.
Maimakon yaji Hubairu yace wani abu sai yaji yayi shiru.
Koda ya dube shi da kyau sai ya fuskanci cewar ai ko motsi ba yayi bare ya taɓuka wani abu.
Nan fa Kuddaru ya rikice ya
kuma firgice ya ƙaddarawa kansa mutuwa. Adai dai wannan lokaci sarki Lu'umanu ya baiwa
Gimbiya Sima mashi yace,
"Ungo kije ki tsire wancan saurayin shine babban maƙiyinmu a duniya."
Take ta karɓi mashin ta nufi inda Hubairu ke ɗauke fuskarta a murtuke ba tausayi.
Wannan shine abin da ya faru a fadar sarki Lu'umanu na birnin teheren bayan ya sami nasarär tsafance zuciyar Gimbiya Sima ta soshi fiye da komai a duniya kuma yayi sa'ar kama jarumi Hubairu da aljani Abtarul Hudes.
Al'amarin su Boka Durfus kowa bayan sun gama tattaunawa dangane da yadda zasu sami nasara akan Boka Shamharu Shahararre sai sukayi shiri suka nufi garin da sarkin ɓarayin
Aljanu yake.
Suna cikin tafiya a sararin samaniya su biyar kawai sai suka gawani abu mai kama da bakan Gizo yasha gabansu kuma abin na fitar da tartsatsin wutane tamkar batoyi ita kuwa wutar ta kasance mai hucin zafi kana doso ta sai kaji kamar ana dafa naman jikinka, cikin tsananin tsoro su duka biyar din suka ja da baya a sararin samaniya. Markahul sabus,bokanya Samaratu,boka Jinshan,boka Sulbaini da boka Durfus su kayi tsuru tsuru kamar jiƙaƙƙen tsumma a rüwa suna masu duban juna
Kowannansu ka duba kasan a matuƙar tsorece suke dan jikinsu ma karkarwa yake yi cikin ƙarfin hali Markahul Sabus ya dubi aljani Durfus yace,
"Yakai sabon boka mai abin al'ajabi mene ne wannan abun da ya sha gabanmu?"
Durfus ya haɗiyi miyau da ƙyar yace,
"Ashsha,kallonmu yake gaba ɗaya. Haƙiƙa daga yanzu tamu ta ƙare,duk wani buri da muke da shi cewa wannan abin da kuke gani a gabamu ba komai ba ne face boka Shamharu shahararre."
Durfus na gama faɗin hakan suka ji an ƙyalƙyale da mahaukaciyar dariya. Nan take
bakan gizon nan ya rikiɗe ya zama aljani Shamharu yana mai ƙyalƙyala dariyarsa,har wani irin tururin masifa ne ke fita daga bakinsa.
Nan take tsoro ya ƙara baibaye su Markahul Sabus suka ruɗe, suka rasa abin yi.
Shamharu ya daka musu tsawa yace,
"Ku ƙananan ƙwari ku sani cewa kun yi sake na rigaku kwana don haka dole ne na rigaku tashi.
Ina sanar muku cewa a yau ne na fito daga halwar tsafina kuma na gano hanyar da zan bi na zama MATSATSUBI a cikin wasu 'yan shekaru. Duk wani shiri da kuke yi a kaina na san da shi.
To ku sani cewa na gaba yayi gaba na baya kuwa
sai labari. Ni Shamharu shahararre na gama da duniya, don na san gaba dayan sirrin cikinta.
Da sannu zan mallaki komai da da kowa.
Ku kuwa ba zan hallaka ku ba, yanzu zan tafi da ku ne izuwa kurkukun fadata da ke can tsibirin Baharzus na ajiye ku a matsayin fursonini.
Ba zan sake ku ba har sai na zama MATSATSUBI nan da shekara goma sha tara da wata shida masu zuwa."
Koda jin wannan batu sai su Markahul Sabus suka yunƙura suka juya da baya don su gudu, amma sai suka ji wata irin iska mai ƙarfin tsiya ta tsaida su a waje daya,sun kasa yin gaba
ko baya.
Shamharu ya dube su ya sake ƙyalƙyalewa da dariya,kawai sai ya buɗe tafin hannunsa guda.
Take su Markahul Sabus suka zama 'yan ƙanana,mini mini suka faɗa tafin hannun Shamharu,shi kuwa sai ya buɗe aljihun rigarsa ya watsa su ciki.
Suka ji kamar an jefa su cikin rijiya gaba dubu. Take Shamharu ya rikiɗe ya zama bakan gizo sannu a hankali bakan gizon ya ɓace ɓat a sararin samaniya.
Wannan shi ne abin da ya faru ga su boka Jinshan bayan sun yi mugun gamo da boka Shamharu a sararin samaniya yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin sarkin ɓarayin
aljanu.
Aljanin dashi kaɗai ne zai iya zuwa fadar boka Shamharu ta tsibirin Bahar Zus ya sato addar tsafi.
A can fadar sarki Dujalu kuwa, jim kaɗan da aika bafade cikin gida,sai ga kuyanga ta fito ɗauke da butar sihirtaccen shayi.
Koda shigowarta cikin fadar sai sarki Dujalu ya dubeta yace, "Maza ki zuzzuba mana shayin nan mu sha har kowa ya gamsu."
Cikin sauri kuyanga ta cika aikinta. Tana gamawa ta shige cikin gida riƙe da butar shayin
wacce babu ko digo guda a ciki. Sarki Dujalu yayi murmushi gami da gyaran murya yace,
"Shin akwai mai buƙatar ƙarin shayin ne?"
Gaba ɗayansu suka ce, "A'a."
Sarki Dujalu ya sake yin murmushi a karo na biyu,yace,
"To sai ku nutsu da kyau domin
yanzu zan baku labarin Hikayar wata azzalumar boka da ake kira Tazibul Luhucul da manyan
sarakunan duniya guda shida. Wannan al'amari ya faru ne a birnin Sin. ldan kuka nutsu sosai zaku ji abubuwan al'ajabi da kuma tsabar tuggu da kisisina waɗanda za su amfani rayuwarku wajen kare kanku daga sharrin maƙiya da mahassada......

A wani zamani mai tsawo da ya shuɗe a cikin ƙasar Sin an
yi wata gagarumar bokanya
mai suna Tazibul Luhucul. Masu harsashe a wannan zamani na ta babu wata 'ya mace mai yawan shekarunta a duniya,domin a ƙallah bata bar duniya ba sai da ta shekara ɗari da saba'in.
Har ta mutu ba ta taɓa yin aure ba,kuma ba ta taɓa haihuwa ba.
Tazibul Luhucul ta fara bokanci ne tun tana da shekara bakwai sa'adda ta yi ƙawa da wata aljana 'yar sarkin birnin Sin wadda ake kira Saubatul Azwas. An haifi Tazibul Luhucul da Saubatul Azwas shekara ɗaya, rana ɗaya,kuma lokaci guda. Tun sa'adda sarkin aljanun ya fuskanci baka sai ya ƙudure a ransa cewa sai ya haɗa ƙawance tsakanin 'yarsa da wannan bil'adama wadda aka haife su rana guda.
Saboda haka tun Tazibul Luhucul ba tafi shekara biyu a duniya ba ya zamana ya buɗe
mata idanu tana iya ganin kowanne irin aljani ba tare da ta tsorata ba. Kuma kullum sai ya kawo mata Saubatul Azwas sun yini suna wasa tare.
Tun mahaifiyar Tazibul Luhucul ba ta fuskanci abin da ke faruwa ga 'yar ta har ta fara ganin abubuwan al'ajabi a tare da ita. Sau tari sai ta ga Tazibul Luhucul ta ɗauki abu mai nauyi wanda sai ƙarti arba'in sun taru za su iya ɗaukarsa.
Haka kuma duk maganar da za ta yi sai ka
ji cewar magana ce ta babbar mace mai hankali da nutsuwa. Daga nan kuma sai ta fara faɗin
abubuwan da zasu faru a gaba a birnin Sin. Duk abin data faɗa kuwa sai a ga ya tabbata.
Haka ma duk irin cutar da mutum ke yi in dai aka ɗauko shi aka kawo shi gaban Tazibul Luhucul a bashi magani take zai warke. Yayin da jama'ar birnin Sin suka ga baiwar Tazibul Luhucul ta yi yawa sai suka shiga girmamata ainun,har ta kai
cewa ma ana bauta mata,kuma duk dokar da ta kafa kowa na binta,har shi kansa sarki Alyasil
buhus wanda ke mulkin jama'ar kasar Sin gaba ɗaya a wannan lokaci.
Lokacin da sarki Alyasil Buhus ya ga irin girmamawar da akewa Tazibul Luhucul ya zamana an bata matsayin abin dogaro sai
hankalinsa ya dugunzuma ya fara tunanin cewa lallai da sannu wannan bokanya za ta raba shi da karagar mulkinsa.
A bisa wannan dalili ne ya tara 'yan majalisarsa a ɓoye don su tattauna wannan matsala a keɓaɓɓen wuri.
Bayan dukkanin 'yan majalisar sun hallara sai sarki ya miƙe ya gaishe su sannan yace,
"Yaku 'yan majalisata kun sani cewa a halin yanzu wannan sarauta tamu ta shiga wani mugun hali na rashin ɗorewa domin kuwa yanzu
talakawan mu basa jin maganar kowa face ta bokanya Tazibul Luhucul.
Tabbas al'amarin wannan bokanya da ban tsoro yake,kun sani cewa ba zamu iya yin yaƙi da ita ba,kuma ba zamu iya korarta ba daga cikin ƙasar, yanzu mene ne abin yi?
Ban tara ku anan ba dan komai sai don mu yanke shawarar da za ta fishshe mu don mu tsira da mutuncin mu,kuma mu tsira da
mulkinmu."
Yayin da sarki Alyasil Buhus ya zo nan a zancensa sai gaba dayan 'yan majalisar suka ruɗe, hankalinsu ya dugunzuma. Tsawon daƙiƙa ɗari da sittin ɗayansu bai ce uffan ba. Daga can sai waziri yayi gyaran murya yace,
"Ya shugabana ka yi sani cewa idan har muna so mu tsira da mutuncinmu da mulkinmu dole ne mu cire tsoro daga zuƙatanmu,walau dai mu je mu
zauna tare da wannan bokanya mu nemi sulhu ta fita daga ƙasar nan ko kuma mu yi tarar aradu mu koreta da ƙarfin tsiya,tun da dai bamu jarraba yin hakan ba mun kasa. Kasan ance a rashin tayi ake barin araha."
Caraf sai Galadima ya tari numfashin waziri yace,
"Haba waziri ya za'a yi mu yi irin
wannan gangancin. Ai shi yaƙi ɗan zamba ne,idan har muna son haƙanmu ya cimma ruwa dole
haɗa da yaudara. Tabbas za mu yi nadama idan muka ce za mu yi fito na fito da bokanya Tazibul Lubucul."
Koda galadima ya faɗi haka sai sarki Alyasil Buhus yayi ajiyar zuciya,sannan ya dubi kowa yace,
"Haƙiƙa kai ma ka zo da uzuri
babba. To wai shin me zai hana mu je mu nemi sulhu da ita?"
Kamar haɗin baki sai gaba ɗayan 'yan majalisar suka amince da wannan shawara ta sarki Alyasil Buhus,kuma aka tsaida magana akan cewa gobe da safe za su ɗunguma gaba
ɗaya su je kogon tsafin bokanya Tazibul Luhucul don warware wannan matsala.
Kash rashin sani yafi dare duhu. In da sarki Alyasil buhus da 'yan mjaitsarsa sun san abin da zai biyo baya da basu yanke wannan shawara ba.
Kashe gari da hantsi sarki Alyasil Buhus da 'yan majalisarsa gaba ɗaya suka yi hawa suka tafi izuwa kogon tsafin bokanya Tazibul Luhucul. A wannan lokaci Tazibul Luhucul ba tafi shekara tamanin ba a duniya.
Koda zuwan su sarki Alyasil Buhus bakin kogon sai suka ja dunga,suka yi crko-cirko,suna masu kallon kogon wanda ya kasance a
rufe ruf babu wata ƙofa ko kafar shiga.
Nan fa suka yi tsuru-tsuru suna kallon juna,suka rasa abin yi. Suna cikin wannan hali ne suka ji wata irin mahaukaciyar dariya ta cika jejin gaba daya cikin amo da amsa kuwa.
Ba zato kuma ba tsammani sai ga wani murgujejen aljani mai ɗan ƙanƙanin kai da tsawo kamar shantu ya bayyana.
Yana da faffaɗan ƙirji cike da gashi,mai faɗin kamu ɗari. Hannayensa dogaye ne zanƙala
zanƙala,kuma sirara tamkar wuyan zalɓe.
Ƙafafunsa kuwa guda huɗu ne murtuka-murtuka kamar bishiyar kuka.
Saboda tsananin ƙarar dariyar wannan aljani sai da su Alyasil Buhus suka ji kamar kunnuwansu za su toshe.
Ba shiri suka faɗo daga kan dawakansu suna masu tohe kunnuwansu da hannuwansu. Iskar bakin aljanin kuwa ta tashi
hankalin komai da ke wajen hatta duwatsun wajen sai da suka kama girgiza.
Lokaci guda aljanin yayi tsit, komai ya tsaya cak. Kafin su
sarki Alyasil Buhus su buɗi baki su ce wani abu tuni aljanin ya feso musu iskar bakinsa,take
suka rikida suka zama guguwa. Aljanin ya cire wata battar fata dake ɗaure a ƙugunsa ya buɗe sai guguwar ta shige ciki,sannan ya rufe.
Kawai sai ya ɓace ɓat,bai bayyana a ko'ina ba saí a
tsakiyar cikin kogon bokanya Tazibul Luhucul.
Babu yadda za'a yi mutum ya tsinci kansa cikin wannan wuri ya yarda cewa a cikin kogo yake,domin kuwa gaba ɗayan wajen a gine yake da dutsen lu'u-lu'u. Kayan ƙawa kuwa gasu nan iri-iri birjik iyakar ganin mutum.
Zaune akan wata karagar zinariya kuma riƙe da gajeriyar sandar tsafi tsohuwa Tazibul Luhucul ce.
Tazibul Luhul ta kasance 'yar tsarmurmura kamar a hureta ta faɗi,duk da ta kasance tsohuwa tana da kyawun fuska,kuma babu wani abun muni a jikinta. Ko yaushe fuskarta a cikin annuri take kamar ta mai tausayi da imani,amma kuwa al'amarin ba haka ba ne,domin zuciyarta baƙinƙirin ce cike da mugun nufi da rashin tausayi.
Koda bayyanar aljanin sai ya yi sujjada a gareta ya miƙa mata battar tsafin. Ita kuwa sai ta miƙe zumbur ta karɓi battar ta ɗaga ta sama,sannan ta kece da dariyar mugunta. Sai da ta jima tana dariyar sannan ta dubi aljanin tace,
"Gaishe ka Haddagul Gubur. Haƙiƙa yau kayi mini kyakkyawan aiki."
Haddagul Gubur yayi murmushi yace,
"Godiya nake uwar bokaye."
Ba tare da ta ce komai ba sai ta sake buɗe
battar fatar nan. Tana buɗe wa guguwar ciki tayi fitar burgu ta zuba ƙas ta rinƙa katantanwa
waje ɗaya. Tazibul Lubucul tayi nuni ga guguwar da sandarta ta tsafi,tana mai cewa,
"Gaa ɗayanku ku zama naƙasssu masu mutuwar ɓarin jiki."
Rufe bakinta keda wuya sarki Alyasil Buhus da 'yan majalisarsa suka bayyana gaba ɗayan su a kwankwance kowannansu rabin jikinsa a shanye. Koda suka dubi jukunansu suka ga halin da suka kasance,sai duk suka fashe da kuka suna masu tuba ga bokanya Tazibul Luhucul.
Ita kuwa sai ta ƙyalƙyale da dariya lokacin da suke ta roƙonta. Lokaci guda kuma ta daka musu tsawa ta murtuke fuska tace,
"Kaicon ku waɗannan sarakuna. Lallai ba zan taɓa yafe muku ba,domin kun kawo matuƙar raini a gareni. Shin kuna tsammanin har akwai wani abu da za ku ƙulla a sirrance wanda ban sani ba?
Duk abin da kuka shirya a majalisa jiya na gani,kuma na ji. Ina tabbatar muku da cewa sai na nuna muku cewa ni Tazibul Luhucul nafi gaban raini. Kai bama ku ba gaba ɗayan manyan sarakunan duniyar nan kun jawo musu bala'i.
Na rantse da darajar ƙarfin tsafina,duk waní sarki mai ji da kansa dake cikin duniyar nan da 'yan
majalisarsa gaba ɗaya sai na maishe su Naƙasssu kamar yadda na maida ku yanzu.
Yayin da Tazibul Luhucul ta zo nan a zancen ta sai sarki Alyasil Buhus ya yunƙura da ƙyar ya jingina kafaɗarsa jikin wata kujera yana mai fuskantar Tazibul Luhucul yace,
"Yake wannan matsafiya naji duk abin da kika faɗi,kuma na tabbatar da cewa ba za ki yafe mana ba,amna ina son na nemi alfarma guda biyu a wajenki saboda albarkar darajar ɗaukakarki da girmanki a wajen al'ummar ƙasar nan,ina son duk abin da za kiyi mana kada laifinmu ya shafi zuri'armu. Alfarma ta biyu ita ce ina son ki sanar damu yadda zamu samo maganin da zamu warke daga wannan cuta,don ya zamana koda ba kya raye a doron ƙasa zamu iya ƙoƙarin nemo maganin,duk da cewar kuwa mun san cewa ba za mu iya samo maganin ba,amma ai mai rai baya fitar da rai da samun rabo."
Koda jin wannan batu sai bokanya Tazibul Luhucul ta ƙyalƙyale da dariya har sau uku sannan tace,
"Yakai wannan sarki ka yi sani cewa ba'a taɓa neman alfarma ba a wajena na ƙi yi,face abin da dama na yi rantsuwa akan ƙin yinsa. Bisa wannan dalili na rantse da darajar tsafi ba zan taɓa cutar da iyalanku ba,kuma zan
sanar da ku yadda za'a samo maganin da zaku sha ku warke daga wannan cuta gobe daddare,ku yi sani cewa bayann zai riskeku cikin gidajenku."
Tana gama faɗin hakan ta dubi aljani Haddagul Gubur tace, "Maza ka kwashe su ka maida kowa gidansa,domin iyalinsu su cigaba da yin jinyarsu bisa wannan cuta ta ajali domin kuwa ita ce sanadiyar mutuwarsu.
Tabbas babu wanda zai ƙara shafe sama da shekara uku nan gaba a rayuwarsa. Kuma kayi sauri ka dawo nan domin ina son ka kirawo min gaba ɗayan hadimaina domin muyi shirin zagaye duniyar nan a cikin kwana arba'in don yaɗa wannan cuta ga dukkanin manyan sarakunan duniya da 'yan majalisarsu."
Kafin Tazibul Luhucul ta gama rufe bakinta tuni aljani Haddagul Gulbur ya kwashe su sarki Alyasil buhus su goma sha ɗaya ya kai su cikin gidajensu ɗaya bayan daya cikin abin da bai wuce daƙiƙa biyar ba.
Yayin da iyalan sarki da iyalan 'yan majalisarsa suka ga abin da ya faru sai hankalinsu ya dungunzuma,gari ya ruɗe, ko'ina ka gifta babu zancen da ake yi sai na wannan annobar
cuta data samu sarakan gari. Nan fa jama'a suka yi ta shawarwari iri-iri har ma aka haɗa kai aka ƙudiri niyyar zuwa kogon Tazibul Lubucul don a roƙeta gafara.
Bayan jama'ar gari sun yi dandazo da niyyar tafiya sai kawai aka ga aljani Haddagul
Gubur ya bayyana a sararin sama. Nan take tsoro ya baibaye kowa.
Jama'a suka firgice suka kama iface-iface da guje-guje. Cikin kakkausar murya Haddagul Gubur ya daka tsawa yana mai
cewa, "Yaku jama'ar birnin Sin na umarce ku daku tsaya waje guda ku saurari saƙo daga mai girma uwar bokaye ko kuma yanzun nan nayi fishi da fishinta."
Koda jin wannan batu sai kowa ya tsaya cak a inda yake. Gaba ɗaya garin ya yi sit tamkar babu wani mai rai. In ka ɗauke kukan ƙwari dana tsuntsaye da kuma sautin iska dake kaɗawa ba ka jin komai.
Haddagul Gubur yayi gyaran murya yace,
"Mai girma uwar bokaye tace a gaya muku cewa ba ta da buƙatar ganin ɗayanku don neman gafarar ta bisa abin da ta yiwa sarki da 'yan majalisarsa. Kuma tace tana
mai yi muku gargaɗi cewar duk wanda duk ya kuskura yaje gareta akan wannan batu abin da ya sami sarki da 'yan majalisarsa shine zai same shi."
Koda Haddagul Gubur ya zo nan zancensa,sai ya bace ɓat. Nan fa gari ya ruɗe masu kuka na yi masu faɗin albarkacin bakin su na yi.
A can cikin gidan sarki kuwa,gaba ɗayan iyalansa sun taru a cikin turakarsa sun kewaye shi,yana kwance bisa gado sai kuka suke gaba ɗaya. Babban ɗansa kuwa a tsaye yake gefe guda ya yi jugum fuskarsa a murtuke babu annuri,haka kuma zuciyarsa cike take da tsananin baƙin ciki. Idanunsa sun kaɗa sun yi jawur, amma ba sa zubar da hawaye. Shi kaɗai sai huci yake kamar macijin da ya fasa kai zai yi sara. Kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da cewa jarumi ne na gaske,domin yana da ƙirar ƙarfi. Ya kasance saurayi ɗan kimanin shekaru ashirin da biyar,kuma ana kiransa da suna
Sammaru.
Sammaru kyakkyawan saurayi ne,kuma mai kyawun hali,domin yana da tausayi da taimako ga talakawa,to amma ta yana da matuƙar fushi,domin ba wuya ya zare takobi ya ƙaddamar da mutum musamman mazalunci.
A rayuwar Sammaru babu abin da ya tsana sama da zalunci.
Sarki Alyasil buhus ya ɗaga kai yana duban iyalansa ɗaya bayan ɗaya,sa'adda hawaye ke zuba a idanunsa,amma bai ga Sammaru ba sai yace,
"Ina yarima yake?"
Mahaifiyar yarima Alfisa tace, "Ai gashi can a gefe guda."
Sarki ya kira Sammaru yace, "Yakai ɗana zo nan gareni mu gana."
Sammaru ya tako ƙafafunsa cikin karayar zuciya,ya iso gaban gadon ya durƙusa,sannan ya kama hannun mahaifin nasa ya sumbata kawai sai hawaye ya zubo masa yace,
"Yakai Abbana ina so ka sani cewa zuciyata na faman zogi da raɗaɗin baƙin ciki bisa wannan hali da ka shiga. Ina son ka yi mini izini yanzu na tafi kogon uwar matsafa na sare kanta."
Koda jin wannan batu sai gaba ɗayan iyalan sarki suka firgice suka faɗi ƙasa suna masu dunƙule jukunansu cikin tsananin tsoro don gani suke tamkar hallakarsu ta zo.
Shi kuwa Sammaru ko gizau bai yi ba.
Kawai sai sai ya zare takobinsa yayi tsayuwar shirin ko ta kwana.
Sarki Alyasil Buhus ya ɗaga hannunsa na dama wanda bai shanye ba,ya kamo hannun Sammaru yace,
"Yakai ɗana ka yi haƙuri ka sanyawa zuciyarka ruwan sanyi, ka
sani cewa ba za ka iya ba da uwar matsafa,domin tafi ƙarfin ka. In ba don ta ɗauki alƙawari cewar ba za ta taɓa iyalannmu ba,da tuni wannan farucin da kayi ya zamo ajalinka.
Ina roƙonka a bisa ƙaunar da ke tsananina da kai da ka janye nufinka na son yaƙar uwar matsafa,abin da nake so da kai shine ka saurari bayanin da zai zo mana akan yadda za'a samo maganin da zamu sha mu warke daga wannan cuta.
Yakai ɗana na sani kai jarumi ne mai dakakkiyar zuciya da tsagwaron ƙarfi da jarumta. Bana shakkarka bisa kowanne irin hali da za ka tsinci kanka a
ciki.
Na sani cewa komai nisan wuri da kuma masifun dake kan hanya za ka iya ke tasu ka kai ga biyan buƙata.
Ina son ka jajirce a ranka cewa
za ka iya zuwa inda wannan maganı yake ka samo shi."
Yayin da yarima Sammaru ya ji wannan jawabi daga bakin mahaifinsa,sai ya ji wani sabon ƙarfi ya zo masa tamkar zai iya y yaƙar duniya shi kaɗai.
Cikin zafin nama ya miƙe zumbur ya juyawa mahaifin nasa baya sannan lashi takobinsa yace,
"Yakai Abbana ka yi sani cewa na rantse da darajarka da kuma kaifin wannan takobi tawa duk inda wannan magani yake sai na je na
nemoshi. Haka kuma komai daren daɗewa sai na tsinke kan Tazibul Luhucul da wannan takobi,domin kuwa ta kasance azzaluma. Lallai ba ni da abokin gaba a doron ƙasa wanda yafi azzalumi."
Koda Sammaru ya zo nan a zancensa,sai suka ji ɗakin ya cika da dariyar Tazibul Luhucul.
Al'amarin da ya firgita sarki da sauran iyalansa kenan. Shi kuwa Sammaru sai ya gyara tsayuwa gami da ƙara riƙe takobin sa hannu biyu.
Dariyar ta ci gaba kamar ba za ta daina ba. Daga can kuma sai wani irin haske ya fara bayyana dishi-dishi a cikin siffar bil'adama.
A hankali surar ta haɗu gaba ɗaya sai ga Tazibul Luhucul tsaye a gaban Sammaru riƙe da sandarta ta tsafi,kuma fuskarta a murtuke.
Koda Sammaru ya yi arba da ita sai ya kai mata wawan sara a tsakiyar kafaɗarta da niyar tsargeta gida biyu,kawai sai yaji takobin tasa ta sari iska.
Sammaru ya ci gaba da saranta amma iska yake sara.
Tazibul Luhucul ta ƙyalƙyale da
dariya a karo na biyu al'amarin da ya sa Sammaru ya ja da baya kenan ya sauke takobinsa ƙas.
Tazibul Luhucul ta nuna shí da
ɗaya hannun nata mara sanda tace,
"Kai yaro tsaya iya matsayinka domin na gaba ya yi gaba,na baya sai labari.
Ina so ka sani cewa duk
duniyar nan babu wani mahaluƙi da zai iya kashe ni.
Ba don na yi rantsuwa ba akan cewa ba zan taɓa iyalan sarakan garin nan ba da tuni ka daɗe da zama gawa. Ban zo nan dan komai ba sai don na tabbatar maka da cewa ni walki ce daidai da gindin kowa. Matsayina ya wuce yadda kake tsammani.
Shawara ɗaya zan baka ka

2 Comments On MATSATSUBI Book 2
avatar
idris-idris-abubakar

10 months ago

Reply

Hausa

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to idris-idris-abubakar

Eh na hausa ne

Please Login or Register in order to submit comment