Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za su shiga dajin suka soma jiyo gurnani mai tsanani a kunnuwansu nan suka soma waige-waige, shiru na yan da’ki’ku can wani duhu a wata irin iska mai tsanani ya mammaye saman dajin, ba su yi aune ba sai ga wata hallita mai fuka-fukai ta bayyana suffarta abun tsoro. Ta dinga nufosu tana da kai guda huɗu da jela a bayanta nan suka soma artab babu ji babu gani cikin shammata ta wage bakinta ta suri Hamu ta jefa shi a baki ta la’kume kamar mage da ɓera. Al’amarindaya ɗaga hankalin abokin tafiyarsa kenan ya kuma fusata shi koda ganin hakan sai Samu somankai mata sara da suka ya kuntatta ta al’amain daya usatata kenan ta yi kansa ya kwasa da matsanancin gudu yana mai falfalawa kamar zai taɓo keyarsa da kafarsa don tsananin gudu. Nan fa suka kasa gudu yake ya galabaita ya sadaka mutuwa kawai zai yi tuntuɓe ya yi ya kifa ta bishi ta dakeshi da jelarta take hannunsa ya karye ya kwala kara mai amo ta wage baki zata hadiyeshi cak ya ga ta tsaya tare da sakin wata kara mai karfi data haddasawa jejjn girgiza duk da radadin da yake ji saida ya ya ɗago yaga daliin tsayawarta take ya yi arba da Alhussain takobinsa na digar da jini ga kuma fuskarsa duk jinin ya falatsa.

Rikica ta fadi gefe wajan ya zurma rabinta ya rufta da hannu daya ya ɗagoshi suka ‘karasa ya zauna Aisha ta tsaya tana shawagi da takobinta, tambayarsa ya yi ina abokin tafiyarsa ya bashi tabbacin ya rasa rayuwarsa, jim ya yi daga bisan ya gyara masa karayar suka mike da niyyar tafiya ya bisu da idanu,

“yanzu tafiya zaku yi ku barn wata hallitar ta cinyeni kai kaicona dana sani banyo wannan tafiyarba”.

Cikin tausayi Alhussain ya kamo hannunsa suka cigaba da tafiya tafiyar sa a daya suka soma jiyo ihu da kida kide na tashi nan fa hankalinsu ya dugunzuma domin suna da tabbac suna gab da shiga garin tafiya suke cikin taka tsantsan koda suka kara gaba sai suka hangi mutane biyu daure jikin itace kimanin mutum dubu zagaye dasu suna kida take suka gano ko suwaye komawa da baya suka yi suka sami mafaka suka zauna tunanin abin yi.

***

Al amarin Sarki Sharmil kuwa kullum cikin tunan yake ga Zajlat jiki kara rikicewa ya ke yi sossai kulum Sharmila bashi baki take takai ta kawo dakin bauta ya yi kaura ya daina zuwa al ammuran masarautar duk sun lallace a ɓangare guda kuma sarki Sharbusa na masa barazanar ɗaukar fansa mudun ya rasa tilon ɗansa ga yawan mafarkai da yake yi masu ban tsoro da firgtarwa. Ga yawan mafarki da yake da Samaratu tana barazanar ɗaukar ran Zajlat.

***

Cikn dare Alhussain ya faki ido ya shiga cikin garin suna bacci ya kashe mutum uku ya dauko kayansu bayan ya binnesu suka saka kayan awashegari suka shiga garin gefin asuba suka saje da mutanan komai iri daya.
Mazauna garin arnan daji ne masu cin naman mutane, a tarhin garin shekaru hamsin kenan raban da su sami naman mutum sai tarkon da suka kafawa su Sham unu shi yasa suketa murna da tsale da kude-kide safiyar ranar ita ce safiyar da zasu yanka su daya aba sarkisu daya su kacaccala. Sarkinsu wani basamude ne mai katon tumbi ga katon hanci da idanu manya kofar hancinsa a zura irinsu Rash da Avv guda biyu ko huɗu, iin su Kamala ɗaya n kawai zasu iya shiga ba sauran waje Dr Mubara kuwa sai asa shi sau uku. Bakinsa kuwa tamkar kofar gari guda haka take.
Lokacin da aka soma hararramin yankasu sai hankalin Alhussain ya tashi zuciyarsa ta dugun zuma ya soma huci gashin jikinsa duk ya mimmike ya mummurde kamar wani gawurtacan zaki bai aune ba ya afka musu dasara da suka Samu na saman bishiya yana tayashi da kibau a daya bangaran Aisha na tayashi da zarge musu wuya da igiyoyi nan da nan waje ya hautsine suka rikatasu kadin sa a daya sub karar da rabin mutanan al amarin daya dugunzuma hankalin shugabansu kenan ya shammace Alhussain ya lafta masa wani kashin kwarangwal a tsakiyar ka take ya fadi bab numfashi Aisha data hango ta kwala wata giggitaciyar kara ta yo cikinsu tana sararsu da iya karfinta sarkin yawa yafi sarkin karfi dukda asarar data yi musu sun sami nasarar cafketa sanan suka kama Sam suka hadasu suka daure acikin keji su biyar har zuwa lokacin Alhussain baya numfashi…
ku biyoni dojin Alhussain ya mutu ne ya makomarsu masarautar sarki sharmil? Shin Zajlat na samun lafiya ne? Ina burin Sarki Sharbusa na daukar mataki idon ya rasa yaronsa? Shin yana rasawa da gaske?.

BABI NA SHA BIYU
Lokacin da aka kwashi su Alhussain basu riskikansu ko ina ba sai cikin wani wawwakekken keji mai faɗi da tsayi. Babban tashin hankalinsu yadda Alhussain bai farfaɗo ba har tsawan rabin sa a hakan ya dugunzuma hankalinsu. Hamu ne ya dubi Jardus da tsananin takaici,

“ya aka yi suka kamaku”.

Koda ya zauna a zancansa sai takaici yasa ya ki tanka masa al’amarin daya fusata shi kenan ya soma huci, kamar daga sama suka hango tahowar wani katon basamuden gwaggwon biri cikin hanzari Aisha ta mike ta jijjiga kejin ya juyo sabida jin mitsi. Da hannu Aisha ta yafito shi ganin mace ce yasa ya taho hada tsale-tsalensa ganinta cikin keji yasa ya dinga tamola da kejin kenan al’amarin daya farkar da Alhussain kenan daga dogon suman da ya yi, jikisa duk ya yi tsami koda ya yi arba da abinda yake faruwa sai hankalinsa ya ta shi kafin ya yi wani yunkuri birin ya hankaɗa kejin ya tafi ya gangara nan suka soma gware da juna, bai faɗa ko ina ba sai gasu a wata alkarya suna faɗawa bamuɗin yana buɗewa sai gasu ga wasu wadannin mutane masu katon kai da ido ɗaya kunuwansu kuwa falka-falka kamar na Dr.

Karfin dakuwar da kejin ya yi yasa ya buɗe suka yo waje, kamar an watsosu. Koda birin ya yi aba da Aisha sai ya kwarara ihun murna yana tsale yana buga kirjinsa cike da iza. Kamar daga sama suka yi arba da wadannin nan suna fiffitowa da wasu irin makamai suka yi wa birin k’awanya nan kallo ya koma kansu aka soma artabun gumurzu.

Cikin matsanancin artabun yaki,birin ya dinga makasu da kasa ya dakewa suna ɓalewa, cikn shammata wani wada ya yi tsale tare da caka masa wani kakkauran itace mai tsini a idanu take ya ɓingire yana mata gugu yana kai duka ko ina al’amarin daya haifar da cakuɗewar wajan kenan su Alhussain suka sulale suka nausa cikin daji.

Tafiya kwana ɗaya da yini suka riski kansu a kofar kogon darl ukub, nan fa zuciyar ‘yan maza ta motsa kowa na neman ace shi ne gwanin iyawa lokacin da suka kutsa kai cikin kogon sai hankalinsu ya tashiwasu ‘kayoyine suke sukar ‘kafafunsu suna hudowa ta saman ‘kafar da ‘kyar da siɗin goshi suka ‘karasa akingaɓar kogon suka zauna da niyyar hutawa. Zamansu keda wuya waubirin hallitu masu suffar doddani suka dinga fitowa suna kewayesu, al’amarin daya ɗaga hankalinsu kenan suka shiga damuwa mai tsanani, nan suko soma yunkurin kai musu hari da faratansu masu tsananin tsini kama mashi. Duk wanda suka tsira sai ya kwala kara sabida tsananin zafi sai da suka shafe sa a shida sanan suka sami nasarar kashe hallitun suka shiga kogon. Koda shigarsu sai suka cika da tsananin mamaki ganin sa faffaɗa mai haske ga wani kwantacan yanayi a shimfiɗe a kasansa, daga nesa da shi akwai wani tudu mai kama da rijiya a samansa a kwai wata wuta tana ci ga ruwa na zirarowa ta samansa amma ruwa bai kashe wutar ba. A gefan rigiyar akwai wata kwalba ta dinare tana ta kyalkkyali da ɗaukar idanu a cikinta koda suka yi arba da ita sai Jardus ya zabura da karfin gaske ya nufi wajan, takunsa ɗaya biyu wasu kibau suka dinga fitowa ta wasu sirarran kofofi suna sukarsa take ya faɗi matace.

Al’amarn daya ɗaga hankulansu kennan, koda ganin haka sai Alhussain ya yi bisimillah ya yi taku ɗaya sai ya lura duk inda ake s ka taka ga shatin ‘kafa nan amma ba a ganinta sossai cikin sauri-sauri ya dinga bi, koda ganin haka sai Sham’unu da Aisha da Hamu suka bi ta sauran rukunnan hanyoyin guda uku suna bin yadda ya ke fi, al’amarn daya haifar musu da ruɗani kenan cikin ci da zuci kowane keson kai wa ga gaci, da karfn sihiri Hamu ya fara isa karshan wajan al’amarin daya dugunzuma hankulansu kennan suka tsaya cak! Cikin keta da nuna iya wa ya furta,

“dama nasai ni zanyi nasara”,

ya dubi Alhussain,

“ina bin dogaran naka? Yau ya gaza taimakonka ne?”.

Koda ya zauna a batusa sai Alhussain ya yi murmushi,

“ubangijina mai jarrabtar bayinsa ne”.

Dariya ya kyalkkyale da ita tare da juyawa ya ɗora hannu da niyyar ɗaukar kwalbar take hannunsa ya daskare ya soma komaa dusar ‘kan’kara a hankali har zuwa gaɓar hannun, ya cika da tsoro ya soma kwarara ihu, suka yi zugum suna dubansa har ya gama zama dusar ‘kan’karar baki ɗaya jikinsa daga nan ya tarwatse a wajan ya bi iska. Gaba ɗaya suka tsaya cike da mamaki cikin azama Aisha ta ‘karasa ta yi basmallah ta sa hannu ta ɗauka tare da juyowa ta soma tafiya murmushi ɗauke a fuskarta.

Shu! Wata macijiya ta taso sama bakikirn da ita, bakinta yana zubar da wani bakin dafi mai tsananin tururi ta nufi Aishan gadan-gadan.

*BABI NA SHA UKU*
Cikin tsananin tashin hankali da damuwa suka maida dubans kan macijiyar, gaba ɗaya ta wage bakinta tana neman haɗiye Aisha cikin sufa Alhussain ya daka wani wawwan tsale ya ɗare bisa wuyanta ta yi matagugu ta wurgar da shi gefe ta sa jelarta ta fyaɗeshi take ya faɗi magashiyan ganin haka sai Aisha ta kara tsorata hankalinta ya yi mugun ta shi, gata ta nufota da karfinta kafin ta karaso Alhussain ya sake sufa ya makyalkyale wuyanta suka soma artabun gumuzu hohoho in baka yi bani waje, waniaikin sai Jarumai masu tsagwaran karfin damtse da jarumtar nunawa sa a. Haka sukaita gumurzu Aisha da Sham’unu suna kallo.

***

A can birninsu Gimbiya kuwa duk abin da ke faruwa suna kallo ta madubin tsafin bokanya Sharmila kamar wani majigi, kofar fada cike dam’kan da jama’a suna kallon avɓbin mamaki sananin jarumtar Alhussain ya fi komai birgesu har sun soma yi masa al’kakancin cin gasar, al’amarin daya fusata bokanya kenant janye hoton tare da korar kowa ta shige fadarta koda ganin hakan sai Sarki Sharmil ya bi bayanta fuskarsa cike da damuwar da ya kasa tantance ko damuwar mececce. Samun waje ya yi ya zauna a gefe tare da dubanta,

“ya ke abar dogaranmu me kike tunani akan wannan al’amari?”.

Koda ya zauna a batunsa sai ta yi shiru ta shiga dogon tunani mai zurfi.

***

Lokacin da gumurzu ya yi gumurzu, gumu ta gumu harta kai ga macijiyar ta ciji Ahussain a sassa biyu a hannunsa sai lamarin ya tsananta ya zama baya iya kai hari sai dai ‘ko’karin kare kansa da yake yi. Ana haka kwatsam wani haske ya ratso cikin kogon a hankali ya cur guri ɗaya ya rikiɗe ya koma Sarauniya Samaratu cikin mununar shiga ta yaki.

Dariya ta soma kyalkkyalawa ta nufi Aisha gadan-gadan. Nan da nan Aisha ta bude batar jikinta ta saka kwabar maganin ta nufeta suka soma gwabza yaki cikin tsananin gwanancewa. Sham’unu sai ya zama ɗan kallo ya rasa tantance waye yafi wani tsananin jarumta tsakanin Aisha da Alhussain.

Cikin shammata Alhussan ya faki idon macijiyar ya caka mata wuka a ciki take ta saki ‘kara ya ‘kara cakawa ɗayan idon take wani tafashasshan ruwa ya soma ambaliya a tsakar wajan yana ɓulɓulowa ta idanunta kamar famfo cikin tsananin zafin nama Alhussain ya finciki hannun Aisha daga ri’kon da Samaratu ta yi mata suka yi gefe kusa da Sham’unu faruwar hakan keda wuya ruwan ya gangaro inda ta ke take ta kwala kara ta soma zagwanyewa a wajan kamar darma suna kallo harta gama zagwanyewar ɗif kogon ya ɗauke tsit! Sai kuma ya soma ‘kara yana girgiza kamar ana jijjigashi wani fanni na kogon ya soma zaftarewa yana faɗowa cikin kicima suka nufi hanyar fita duk inda suka ɗauke ‘kafa sai ya zurma ya yi wawakekken rami da ‘kyar da siɗin goshi suka fito ‘kofar kogon suna maida numfashi.

Kwanansu bakwai suna tafiya basu haɗu da komai ba na mugun abu, kwanci tashi suka shafe kwanaki goma cif suna tafiya, ɓangaran Sham’unu ya gama cika da mamakin su Aisha kwaɗayin shiga addinnin musulunci ya ɗarsu a zuciyarsa amma ya yi shiru bai nuna ba. A ranar kwana na sha biyar ne suka iso birnin Sambusa cike da farin ciki ga mamakinsu tn daga harabar ganuwar garin suka hango dandazon dakaru an zo taryarsu cike da farin ciki aka wuce dasu fada, bayan komai ya lafa Alhussain ya fito da maganin ya mikawa Sarki Sharmil shi kuma ya mika wa Sharmila ta buɗe tare da kura masa idanu, koda faruwar hakan sai ta turɓne fuska ta furta,

“wannan ba tsumin dodo kiryanu ba ne, da alama ba can kuka je ba”.

Gaba ɗaya fadar ta hautsine da maganganu kowa na faɗin albarkacin bakinsa, al’amarin daya dugunzuma hankalin Aisha kenan ga mamakinta sai taga Alhussain ya mi’ke yana dubanta,

“ta shi mu tafi Aisha”.

Babu musu ta mi’ke ta na mai bin bayansa, tun mutana garin na hangosu har suka ‘kulle aka daina ganinsu. Fuskar Sharmila ta washe ta mi’ke tare da sallamar mutanan garin gaba ɗaya.

Koda ta shiga ciki sai ta haɗa maganin ta bawa Zajlat, ta dubi Sarki Sharmil,

“nan da kwana uku zata koma dai-dai”.

***

Tsayin kwanaki huɗu kenan da faruwar al’amarin, amma *GIMBIYA ZAJLAT* ko motsi bata yi bale asa ran tashinta. Lamarin daya ɗaga hankalinsu kenan.
SHIN DA GASKE NE ZAJLAT BATA WARKEWA?.

INA LABARIN ALHUSSAIN DA KUMA JARUMA AISHA?.

SHIN SHAM’UNU YANA KAR’NBAR MUSULUNCI?.

WAYE YA KE SAMUN NASARAR WARKAR DA GIMBYA ZAJLAT?.
Dukkanin amsoshin ku naga ɗiyar Katsinawa jikar Katsinawa ‘yar asalin garin Matazu, Mata kuɗi Mata imani Mata gasu da albarka, Matanmu namu abincinmu da gonakinmu na ba’kinmu.Rainan ta dikko ɗakin kara kunya garesu badai…….lol😜
BABI NA SHA HU’DU
Gaba ɗaya Sharmila ta shiga damuwa da tashin hankali mai tsanani game da rashin mik’ewar Zajlata. Hakama mahaifinta.
***

Al’amarin Sham’unu kuwa tunda ya koma gida ya kasa taɓuka komai, hatta horan yaki da yake ba wa mayak’an garinsu ya yi sanyi. Hakan ya ɗaga hankalin mahaifinsa sossai ya zaunar da shi yana tambayarsa dalilin damuwarsa. Bai ɓoye masa ba ya nuna masa yana sin karɓar musulunci ne, koda ya zauna a batunsa sai ya bushe da dariya daga bisani ya furta,

“ya kai ɗana menene ya baka sha’awa da wannsn addinni?”.

Koda ya zauna a tambayarsa, sai ya gyara zama ya bayyana masa komai daya faru kama daga tafiyarsu zuwa dawowarsu.
Koda ya zauna a batunsa sai ya cika da mamaki zuciyarsa ta cika da farin ciki, nan da nan ya amince da bu’katar ɗansa ya tashi dakaru bisa jagorancin ɗansa aka shiga daji neman su Alhussain.

***

Al’amarin su Alhussain nuwa tunda suka nausa cikin daji, sai suka sami gari nesa da birnin Sambusa kaɗan da tafiyar sa a biyu suka yadda zango. Kwanansu ukuba wajan babu wanda ya sake magana game da batun su Sharmila, bayan sun yi sallahr la asar ne Aisha ta dubeshi.

“ya kai ɗan uwana, wana mataki ka ke ganin zamu ɗauka game da wannan cin amana da aka yi mana?”.

Koda ta zauna a batunta sai ya yi murmushi ya buɗa baki zai yi magana kenan suka ga wani tsoho ya bayyana a gabansu yana nishi da ‘kyar. Da sauri Alhussain ya ɗagoshi tare da bashi ruwa ya sha baya sha ne ya dube Aisha da ido ya yi mata nuni ta bashi gurasa tana mi’ka masa ya bashi ya soma ci. Yun’kurawa Alhussain ya yi zai mik’e ya hango tashin ‘kurar dawakai tuni ya mi’ke tare da zare takobinsa yana jiran kota kwana.Koda isowarsu sai ya hangi tawagar su Sham’unu nan ya maidata kufenta ya nufi Sham’unu suka rungume juna.

Bayan ya janye ne ya dubeshi,

“ya kai Jarumi Sham’unu menene ke tafe da kai?”.

Koda ya zauna a batunsa sai ya sanar masa da yadda suka yi da mahaifinsa take fuskarsa ta washe ya yi kabara yana mai nuna godiyarsa ga ubangiji. Aisha kuwa jikinta ya yi sanyi sossai. Tare da su suka koma garin Samuwaru a ranar suka karɓi addinnin musulunci Alhussain ya soma koyar dasu yadda addinnin gaskiya ya ke cike da ‘kwarin guiwa, da fari Aisha ta’ki sakin jiki dasu tsoranta kar a aha’ince su daga bisani saita saki jiki sossai ita take koyawa mata ababban da suka shige musu duhu. Kwananki kaɗan suka rushe ganuwar garin aka sake sabuwa mai ɗauke da kalimatushahada suka rushe duk wasu ɗakunan bautar gumaka. Sham’unu aka sauya masa suna da Muhammad mahaifinsa kuma Abdallah mahaifiyarsa Khadija.

***

Lokacin da Sarki Sharmil da bokanya Sharmila suka sami labarin abin da ya wakana ba ‘karamar kaɗuwa suka yi ba. A ranar suka tura da Manzo kan mutanan Sarki Abdallah su bar addinnin gaskiya, Alhussain ne ya sa aka yi musu martani da cewa su ya kamata su dawo addinnin gaskiya ko kuma su ya’kesu nan da tsawan kwanaki bakwai masu zuwa, lokacin da sa’kon ya isa fadar Sarki Sharmil take ya harzu’ka yasa aka soma shirin ya’ki ganga-ganga.
***

Lamarin masarautar Sarki Abdalla kuwa bayan tafiyar Manzo birnin Samuwaru sai Muhammad ya dubi Alhussain,

“ya kai wannan Jarumi ina so kasani har yanzu ina mamanin rashin warkewar Zajlat bayan kuma zahiri maganin ka ɗauko”.

Koda ya zauna a zancansa sai ya ga ya bushe da dariya, al’amarin daya ba shi mamaki kennan wannan ne karon farko daya ga dariyarsa kodayaushe murmushi ya ke yi.

“Muhammad kasani cewa, banyi mamaki ba da maganin bai ba domin har abada ɓata-ɓata ne. Dana so zan zauna a garin Sambusa in ro’ki ubangijina ya bata lafiya kuma cikin amincewarsa zai bata lafiya amma don in nuna musu ubangijina mai iyawa ne mai taimakon bayinsa ne a kowane yanayi sai naje na samo maganin da suka yi imani shi zai warkar da ita kuma ya ‘ki yi musu aikin”.

Koda ya zauna a batunsa sai ya cika da mamaki ya ‘kara gasgata hikimar ubangiji.

Cikin kwanaki uku masarautar Satki Abdallah cikin shirin ya’ki suke da horo na musamman daga Jatumi Alhussain bisa ɗabarun ya’ki kala-kala don jiran kotaɓkwana. Haka Aisha ta dage tana koyawa mata tsagwaran jarumta da juriyar ya’ki. A gefe guda kuma soyayya ce ta ‘kulu tsakanin ɗan Sarki Abdallah da Jaruma Aisha.

Ranar kwana na biyar ne kwatsam suka soma jiyo karar sukuwat dawakai, da busa alamun zuwan dakarun Sarki Sharmil nan da nan suka hau shiri. Kamar wucewar sa a ɗaya suka yadda zango a bayan gari suka aiko da Manzo zuwa cikin gari. Koda isarsa sai ya mi’ka sa’kon Sarkinsu take maga takarda ya mi’ke ya soma karantawa.
_”Sa’ko daga Sarki mai daraja Sarki Sharmil bin Markahu, na birnin Sambusa. Mun gargaɗinku da komawa addinnin iyaye da kakkani, ko kuma fushin abin bauta JARBUBA ya hau kanku. Mu shigo mu ya’ke ku mu kama matayanku da dukiyoyinku_”.

Koda ya zauna a karatunsa take Alhussain ya rubuta martani ya tashi Manzo da sa’kon martani,

_”Sa’ko daga maɗaukakkiyat masarauta, masarautar Sarki Abdallah mun ga sa’konku mun kuma karɓa amma kusani cewar. Ha’kika addinnin musulunci shi ne addinnin gaskiya kuma muna kan turbarsa baza mu sauka ba, mun amince zamu fito mu ya’ki juna amma da sharaɗin idan muka yi nasara zaku karɓi addinninmu”._

Koda ya zauna a batunsa sai Sarki Sharmil ya kwarara ihu mai firgitarwa. Take suka rubuta radin amincewa aka hau kafa tantuna.

👑
Washegari aka shiga gabza ya’ki, tsayin kwanaki uku ana ya’ki babu hutawa a ranar kwana na huɗu ne su Alhussain suka yi nasarar kama Sarki Sharmil hannu-da hannu bayan aɓ kadhe mutane da dama ciki hada bokanya Sharmila.

Cikin murmushi Alhussain ya dubeshi,

“ka amince addnnin musulunci ne addinnin gaskiya?”.

Take ya zube yana kuka yana neman yafiyar su Alhussain, bayan komai ya lafa suka yi masa rakiya masarautarsa a washegari birnin Sambusa suka sake karɓar addinnin musulunci karo na biyu cike da ‘karfin guiwa da kyautattawa. Tsahin kwanaki bakwai Alhussain yana yi wa Zajlat tofi a ruwa ana bata a ranar kwana na takwas ne ta mi’ke ‘kyam da ‘kafaffunta babu wanda ya sani sai Alhussain ya gargaɗeta kada ta fito sai an zauna fada. Kaya ya sa aka kawo mata mai mata hidima ta yi mata wanka kamar yadda aka saba.

Da yammaci fada ta cika ma’kil ana zaune saiga Gimbiya cikin shigarta ta alfarma take mahaifinta ya mi’ke yana faɗin,

“tsarki ya tabbata ga ubangijin addinnin gaskiya”.

Suka rungume juna cike da farin ciki suna godiya ga Allah. Bayan wasu kwanaki aka ɗaura auran Aisha da Muhammad Gimbiya Zajlat da Alhussain, kwanaki huɗu tsakani aka naɗa Alhussain Yariman birnin Samuwaru. Burinsu Alhussain ya cika ya ‘kaddamar da burin mahaifinsa daular musulunci ta kafu a birnin Sanbusa wanda ya maye gurbin sunan Baitul ƁNur.

Masha Allah.

TAMMAT BI HAMDULLAH!.
Godiya ga ubangijin daya bani ikon farawa da ‘karewa cikin iko da hikimarsa, abinda muka yi dai-dai da kuskure ubangiji ya gyara yasa mu amfana da abinda muka ji mai kyau mu watsar da marasa kyan mu haɗu awani sabo mai zuwa insha Allah cikin yardar mai duka……
YARDA CE SILA……..!

Al’kalamin Ummu Beenah.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment