Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa takan rasa ɗanta ɗaya amma abun da ya ɗaure musu kau gugguwar bata taɓa ɗaukar Zajlat ba, lamarin daya haddasa kiyyayarta a zuciyar Samaratu kenan matar mahaifinta take kokarin hallakata ta kowa ce hanya.

Zajlaht ta taso yarinya mai wayau da saurin shiga rai ga saurin rike abu, tana da som bincikeda zaga arurruwa amma mahaifinta baya barinta sabida gargaɗi da bokanya Sharmila ke masa a kodayaushe kan kula da ita. A wata rana Sarki ya shirya mata fita randagi a tare da ita dakaru goma ne, lokacin tana da shekara goma sha huɗu a duniya a wannan tafiya ya shirya ta ne don zuwa ta gaishe da amininsa Sarki Sharbusa amma sai Zajlat ta ɗauke hanya bisa umarnin data bawa umarnin da ta bawa dakarunta, koda wasa ta tsani zuwa MASARAUTAR SAMUWARU sabida mutanan garin basa tausayin matansu ko kaɗan har sunfi masarautarsu bakin mulki tana yawan kawowa mahaifinta korafi kan hakan amma ba wani mataki da ya ke ɗauka. Babbar damuwarta yadda karfi da ya ji Yarima Sham’ unu ke sa a ɗauko masa matasan yan mata ya yi lallata da su da sanin mahaifinsa kuma babu wanda yake da karfin ikon tsawatar masa, sunyi nisa da garinsu sossai suka riski kansu a wata alkarya mai cike da yayyan itattuwa da buka guda biyu. Zaljaht ta yi umarni ga dakaru kan tana so ta shiga babu musu suka amince da umarninta su kansu sun yi mamaki kuma al’amarin ya burgesu har suka soma sha’awar shiga wannan waje harma suna ayyana yin rayuwa a cikinsa.
GIMBIYA ZAJLATA

4
Lokacin da suka shiga wajan sai suka cika da mamaki ganin koramu da shuke-shuke. Daga gefe ga wani matashi mai sufar sadaukantaka sunkuye a gefansa matane guda biyu suna lullube da farin mayani ba a ganin komai sai fuskarsu Zaljat ta zubamusu idanu tana tunanin mai suke yi ta rasa mai bata amsa?.
Basu kai rabin sa a da tsayuwa ba, suka juyo zuba garesu namijin mai kirar sadaukantaka ya furta,

“ya ku waɗanan mutane meke tafe da ku?”.

Koda ya yi shiru sai dakaru biyu suka nufi hanyar da wata itaciya take babu magana suka hau tsinka, lamarin daya fusatashi kenan ya daka musu tsawa take jijjiyoyin hannuwansa suka murɗe suka kumbura har tufafinsa suka soma yayyagewa cikin fushi ya ɗaga hannnunsa ya gabzawa badakare ɗaya naushi take ya faɗi sumamme koda ganin hakan sai wasu mutum goma suka yo kansa take ya dinga watsi dasu kamar kararre na shawagi kan iska cikin dakika kadan ya gama dasu. Ganin hakan wasu suka sake kukan kura suka yi kansa take Zajlat ta daka musu tsawa suka dakata ta dubeshi,

“ya kai wannan ma abocin karfi wanene kai, kuma menene addininnka?”.

“Ni bawan Allah ne, kuma addinni na addinnin musulunci ne”.

Koda ya zauna a zancansa sai ta yi jim tana mamaki, ta ɗauke idanunta daga kan dakarunta da suke kwance magashiyan cikin raunka ta furta,

“sunan Gimbiya Zajlat Sharmil bin Markah ni yar sarki Sharmil ce, na futo zagaye ne na hangeku alkaryarku ta birgeni shi ne na shigo don ɗebe kewa”.

Koda ta zauna a zancanta sai ya yi murmushi ya basu dama suka ɗibi abinda suke bukata suka yi nufin fita har sun kai bakin kofa ta juyo tana mai tambayar sunayansu kamar ba zai tanka ba ya dubeta,

“sunana Alhussain ibn Tahir wannan kanwata ce Zahra wannan kuma mahaifiyata ce”.

Koda ya zauna a batunsa take dakarunta suka tsorata matuka, harda masu fitsarin wahala juyawa ta yi suka fice daga wajan. Sinyi nisa sossai ta dubi amintacan badakaranta,

“ya kai Lamrisu ina dalilin tsoratar ku yayin da kuka ji sunan wannan jarumi?”.

Koda ta zauna a tambayarta sai ya buɗa baki ya bayyana mata waye Alhussain lokacin daya kare a batunsa saita fashe da kuka tana mai la antar mahaifinta da mummunar manufarsa.

***

Tun daga wannan lokacin Zajlat ta soma zuwa tana kaiwa Alhusain ziyara, sun shaku da su Aisha sossai mahaifinta bai taɓa sanin abin da ya ke faruwa ba sabida ta gargaɗi dakarun rakiyarta kan duk wanda ya tona zata kashe shi.

A haka aka ɗauki lokaci tana zuwa wajan, mu amalasu da yadda suke bautarsu ya burgeta sossai wata rana ta kawo musu ziyara ta samu suna sallah bayansun idar ta kasa jurewa ta tambayi Alhussain,

“ya kai wanna jarumi me nene wannan kuke yi haka?”.

“Ya ke Gimbiya wannan ita ce ibadat wato sallah”.

Koda ya zauna a batunsa sai ta dubeshi da alamun mamaki,

“Sallah? Ya kai wannan jarumi mecece sallah kuma menene dalilinku na yinta?”.
Jim ya yi daga bisani ya dubeta.

“Gimbiya sallah da kike gani aba ce mai matukar muhimmanci ga musulmi. Ita Daya ce daga cikin rukunnan musulunci guda biyar, wanda Allah maɗuakakin sarki ya wajabtata guda hamsin a kan bayinsa yayin da Manzan Allah S.A.W yaje mi’iraaji (wato Sama) ya karɓo ta yayi ta neman ubangiji da ya ragemana ita har aka rageta zuwa guda biyar.

Kamar yadda take a yau saboda tausayin Manzan Allah S.A.W. Kuma Manzan Allah S.A.W ya ce,

“Itace farkon abinda za’ayi wa bawa sakamako (hisabi) da ita ranar k’iyama. Idan ta yi kyau dukkan sauran aiki zasu yi kyau bawa ya samu tsira kuma idan ta yi muni to dukkan sauran kafin Sallar da bawa yake yi ta sami karɓuwa sai idan tadace da yadda Manzan Allah S.A.W ya yi ta kuma ya karantar domin fadar Ma’aiki “Kuyi sallah kamar yadda kuka ina yin Sallah”.

Sannan an wajabta yinta acikin jama’a (wato Jam’i a masallaci ga maza mata kuma suyi ta a gida a ɗakunansu). Kuma wanda duk yabarta to yabar musulunci kamar yadda ma’aiki tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi yace ” Alkawarin dake tsakaninmu dasu shi ne Sallah duk wanda yabarta to ya kafirta”.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “An gina musulunci a bisa ginshiqai guda biyar, shaida wa babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, kuma Muhammad bawansa ne Manzonsa ne, da tsayar da sallah…..” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce,

“Mafi falalar ayyuka sallah a farkon lokacinta” [ Tirmizi ne ya rawaito shi] .

Annabi (S.A.W) ya ce, “hakikaa tsakanin mutum da shirka da kafirci barin sallah” [Muslim ne ya rawaito shi] .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku bani labari da ace akwai qorama a qofar xayanku, yana wanka a cikinta a kowace rana sau biyar, shin wani abu zai ragu na dattinsa, sai suka ce “Babu wani dattinsa da zai ragu” sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Hakanan misalin salloli biyar suke, Allah yana goge zunubai da su” [Bukhari ne da Muslim ne suka rawaito shi]”.
Koda yazauna a batunsa sai ta dubeshi cikin mamaki ta furta.

“Ya kai wannan jarumi me yasa mu bama yi, kenan muma mun kafurta?”.
5

“Mu me yasa bama yi?”.

“Ba kwa bautawa ubangiji waninsa kuke bautawa….”.

Take dakaru biyar suka zuciya suka zuciya suka saken yo kansa a fusace ya mike ya buɗe hannunwansa wasu murɗa-murɗan jijjiyoyi ne suka bayyana a dantsan hannunsa har saida tufaffinsa suka soma tsattsagewa ya dunkule hannu ya kai musu naushi take ya sumar da mutane shida huɗun suka yi baya suna makyarkyarta sai abin ya birge Zajlaht ta gyara zamanta a kan doki,

“ya kai wannan ma abocin karfi kaimin bayanin wannan kalma yadda zan fahimta”.

Ya zuba mata idanu yana kisima shekarunta bazata kai sa ar Aisha ba amma a kiyasinsa Aishan ta girmeta sai dai girman jiki sai ya sami kansa da jin wani nishaɗi mara tushe ya dubeta,

“”Hakkin salla shi ne ka san cewa ita salla neman kusaci ce da Allah Mai Girma da Daukaka, kuma yayin da kake yinta kana tsayuwa ne gaban Allah Mai Girma da Daukaka. Idan ka san haka to zaka yi tsayuwa irin ta makaskancin bawa mai tsammani, mai tsoro da kaskantar da kai, mai natsuwa domin girmama wanda yake tsaye a gabansa (wato Allah), kuma zaka fustantar da zuciyarka gareta sannan zaka kiyaye iyakokinta ka bata hakkokinta”Karkata zuwa ga ibada lamari ne da ya samo asali daga fidirar mutum wato dabi’ar da Allah ya halicce shi da ita tun fil azal. Wasu mutane da dama wurare sun kasu daban daban dan Adam ya kasance yana bautawa ababen bauta daban daban, ko dai Ubangiji makadaici ko kuma gumaka da halittun da suke cikin sararin samaniya kamar rana da wata da taurari. Wannan yana nuna mana cewa dan Adam, bisa dabi’arsa, yana bukatar abin bauta kuma Alkur’ani mai girma ya yi baiyana cewa mutane gaba dayansu suna tareda wannan dabi’a kuma an haliccesu ne da ita. Allah madaukakin sarki yana cewa: “Sannan kuma ka tsayar da fuskar ka ga addini ɗoɗar, wannan addini dabi’a ce da Allah ya halicci mutane a kanta, ba wani canji ga halittar Allah. Wannan shi ne addinin mikakke, sai dai kuma yawaicin mutane basu san haka ba.” Suratu Rum aya ta 30.Manufar addinin Musulunci shi ne mutane su gane wane ne abin bauta na gaskiya, kuma su san shi gwargwadon iko, ta yadda zasu biya bukatar su ta yin bauta ba tareda sun fada tarkon ababen bauta na boge ba.
Addinin Musulunci yana sifanta Ubangiji wanda ya cancanci ibada da cewa shi rayayye ne, mai dukkan daukaka, mai hikima, masani, mai ji da gani da kudura. Shi ne mai gudanarda lamuran dukkan talikai kuma shi ne mai taimakon bawa idan ya fada halin kaka ni kayi. Addinin Musulunci ya baiyana cewa hanyar da bawa zai iya kulla alaka da mahaliccinsa ita ce ya yi masa ibada, wanda kuma salla ce mafi girma daga cikin ibadu. Mafificin tafarkin da zai sada mutum da Allah shi ne salla, domin salla wata irin ibada ce mai game dukkan sassan mutum, jikinsa da tunaninsa da kuma ruhinsa. Dukkan wadannan suna gurfana gaban girman Allah, tareda hushu’i da kankan da kai. Manzon rahama Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) yana cewa: “Ko wani abu yana da fuska, fuskar addini ita ce salla, saboda haka ku yi kokarin kiyayeta.” A wani hadisi kuma Ma’aikin Allah yana cewa salla ita ce ginshikin addini, duk wanda ya tsai da ita ya tsai da addini, duk kuma wanda ya wulakanta to ya wulakanta addini.
Wato idan mutum ya kasa tsai da salla alakarsa da Ubangiji zata yi rauni, idan kuwa alakar mutum da mahaliccinsa bata da karfi to imaninsa zai raunana, shi kuwa raunin imani yana sa sauran aiyukan ibada su kasa bayar da tasirin da suke da shi. Salla ce take tallafawa sauran ibadu take basu kima, domin ita salla ta kunshi aiki da fadi da tsarkin niya, ta yadda idan mutum ya doge kanta dare da rana zata dasa masa son kyautatawa a zuciyarsa, sannan kuma ta tsarkake masa ruhinsa.Imam Sajjad (a.s.) yana kiran masallata da su kula saboda girman wanda suke tsayawa gaba gare shi, sannan kuma su yi kokarin amfana da falalar da Allah (swt) yake lullube mai salla da ita, saboda su kyautata aiyukansu na kwarai su kuma bar ta aikin assha. Imam din yana fadakar da mu cewa idan mutum bai yi sallarsa kamar yadda ya kamata ba, kuma yayinda yake tsaye gaban Ubangiji masani mai iko, bai ji kaskancin kansa ba, sallarsa ba ta wuce sunkuyawa da tsayuwa ba, wanda kuma ba shi da wani tasiri a rayuwar mutum ta yau da kullum. Sai dai ya kamata mu sani cewa mai salla yana kula da hushu’i da tawalu’u da kankan da kai gaba ga Ubangiji yayin salla ne saboda ya fahimci girman Allah mahalicci, amma ba wai Allah yana bukatan hakan ba, domin kuwa shi Ubangiji baya bukatan komai daga bayinsa. Yayin da mutum ya fahimci cewa a cikin salla, yana magana ne da Allah mamallakin dukkan iko da hikima, to zai sami dammar sha daga tafkin falalar Ubangiji (swt). Saboda haka ne ruhin salla da kashin bayanta shi ne tara hankali da natsuwar zuciya yayin munajati da Ubangiji.
Tasirin wannan tara hankali a lokacin da mutum yake ibada shi ne samun kariya daga aikata munanan aiyuka da kuma samun karfin aikata kyawawa. Allah madaukakin sarki ya baiyana wannan lamari a cikin littafinsa inda yake cewa: “Ka karanta abinda ake yo maka wahayinsa na Alkur’ani, ka kuma tsai da salla; hakika salla tana hana alfasha da kuma abin ki. Kuma hakika ambaton Allah shi ne mafi girma, kuma Allah yana sane da abin da kuke aikatawa.” Suratul Ankabut aya ta 45.”

Koda ya zauna a zancansa sai jikinsu gaba ɗaya ya yi sanyi bakinsu ya yi nauyi zuciyarsu ta cika da imani, take suka nemi karin haske kan addinin musulunci babu jimawa ya yi musu basu gushe ba dukansu su goma sha ɗayan suka nemi shiga addinin musulunci, take ya biya musu kalma shahada suka maimaita, ya yi musu bayanin muhimman abubuwa kan addinni suka yi masa godiya Zaljat ce ta cire sarkar wuyanta wadda ta kasance ta zinare ta mika masa ya ki karɓa ya girgiza kai,

“ya na baka abu ka ki karɓa”.

“Kin fini bukata yake ma abociyar rauni”.

Jinjina kai ta yi suka juya suka tafi.

Tun daga wannan lokaci Zajlata ta karɓiadddinin musulunci, haskensa ya ratsata take gudaar dashi a asurce a gidan mahaifinta cikin fadarta kuma cikin kariyar ubangiji babu wanda ya taɓa fuskanta har mahaifinta. Haka Zaljah ta kasance tsayin shekara ɗaya tana ziyartar Alhussain sun saba sossai da dattijuwa Khadija da kuma Aisha haka Alhussain tare da amintattun dakarunta sunyi zurfi cikin sannin addinnin Allah tare da sannin ilmi mai yawa musamman ita tamkar wata Malama haka ta kasance cikin dakarun. Mahaifinta bai san badakalar da ake yi ba sai a wata safiya da bokanya Sharmila ta fito cikin halwar tsafi cikin matsanancin tashin hankali, ga wani ammo mai karfi yana fitowa daga ɗakin abin bauta JARBUBAmai barazanar fasa kunnuwa, fuskata bau annuri ko kaɗan ta shigo kamar an jehota. A lokacin bai fi sa a biyar da tafiyar Zaljay rangadi ba.

GIMBIYA ZAJLAT
6

***

A ɓangare guda bayan fitarsu Zajlat da sa a biyu sai garin ya haɗe ya yi wani irin ja mai ban mammaki ga wata kara da take tashi mai firgitarwa nan mutan garin suka soma guje-guje da iface-iface lamarin daya ɗaga hankalin sarki Sharmil kenan ya soma tunanin in da Zajlat ta ke. Harya janyo mudubin tsafinsa zai fara dubawa sai ga bokanya Sharmila kamar an jehota tana huci idanunta kamar zasu zazzago sai huci take bakinta na fida wani irin tururi mai koran launi.



Lokacin da bokanya Sharmila ta shigo faɗar ɗanta Sarki Sharmil bin Markahu ba karamin kaɗuwa ya yi ba, domin a iya saninsa ta shiga halwar zafinta kuma kwana casa in take sai gata ta fito a kwana goma yasan tabbas da walakin. Gaba ɗaya aka mike alamun girmammawa ta dumfaro wajan tana hucci idanunta sun yi gwalo-gwalo sun yi ja ga wani hayakin sihiri da ya ke fita ta kofoffin kunnuwanta da kafar sadarwar numfashinta.

Zama ta yi tare da takarkarewa ta kwarma ihun da ya hadasawa masu nakuda haihuwa, masu karamin ciki kuwa suka hau yin ɓarin da basu shirya ba daga bisani ta kyalkkyale da wata shu umar dariya irin ta takadirai makiya Allah dariya mai cike da kekashe zuciyar imani. A fusace ta juyo ta daka masa tsawa,

“kaicon ka ya kai Sharmil, ka yi wauta mai girma wadda zata kai kai ga nadama!”.

Koda ta zauna a zancenta sai ya ɗago a razane yana dubanta fuskarsa cike da tsananin mamakin furucinta,

“yake Ummina ina dalilinki na yin wannan batu?”.

“Ina Zajlat ta ke?”.

Ta faɗa murya a kausashe, sai ya dirirrice ya hau kame-kame ta daka masa tsawa,

“ina take!”.

“Ta ta fi faɗar Sarki Sharbusa”.

Koda ya kai karshe a batunsa sai ta wanka masa mari, lamarin daya girgiza ɗaukacin fadawansa kennan bata tanka ba ta yi nuni da hannunta sai ga wani haske mai launin rawaya ya bayyana a jikin bango wani duhu ya rufeshi daga bisani kuma ya yi haske, tiryan-tiryan sai ga farkon zuwan Zajlat wajan da kuma yadda komai ya gudana. Sai ya ɗauke wani ƴya kawo sai ga inda ta dinga kai musu ziyara duk fitar da zata yi harda wajan koya mata karatu take ya kwala kara yana gurnani kamar wani tsohon zaki.

“Yake Ummina ya aka yi hakan ya faru?”.

Kallon data watsa masa ne ya sa ya yi shiru daga nan ta dinga zazzaga faɗa fadar ta yi tsit, sai da ya tabbatar ta gama sannan ya buɗe baki ya yi magana.

“Ya ke Ummina yanzu menene abin yi?”.

Koda ta ji batunsa sai ta kyalkkyale da dariya ta mike ta yi tafiyar rabin sa a sannan ta juyo,

“zamu hallaka waɗanan mabiya addinni domin fanshe fushin abin bauta, zamu bada jinninsu su sha”.

Koda ta kai karshe sai ta sake nuni hotan su Alhussain ya bayyana, koda ya yi arba da hotan idonsa ya sauka kan Aisha kanwar Zahra take gaban Sarki Sharmil ya faɗi sabida karo da ya ƴyi da fuskarta take fuskar tsohuwar matarsa ta faɗo masa sai kuma ya rikice yadda ya gansu jere da Zajlat tamkar wasu tagwaye kafin ya yi wani yunkuri bokayan Sharmila ta ɗauke hotan tana ɓaɓɓaka dariya.

Gaba ɗaya gumi ya gama jikashi, hannunta ta runtse katamau tana karanta wasu dalamusan zafi take faɗar ta fara girgixa cikin gari aka soma iface-iface da guje-guje bata gushe ba wasu manyan hallitu masu kama da ɓatoyi suka dinga bayyana ta karkashin kasa, girman hallitun ya kai girman bishiyar kuka katuwa suna da kafaffu guda hudu da doguwar jela jikinsu kuwa wasu kayoyyine masu tsananin kaifi da tsini bakinsu wakekkene zasu iya haɗiye mutum uku lokaci guda suna da fuka-fukai masu tsayi da idanu kwala-kwala suna fitar da feshin wuta. Su goma sha biyu ne suka yi jerin gwano tare da sirrina a gabanta alamun girmamawa.

Daya bayan ɗaya ta bisu tana shafa wuyansu daga bisani ta yi wani irin yare da ita kaɗai tasan abin da take nufi, take suka yi juyi da wani irin gurnani suka ɗaga fuka-fukansu suka tsaga ginnin masarautar suka wuce ɓat, take ginnin masarautar ya koma kamar ba shi ne ya dare ba ya koma man ya manne.
Koda ɓacewarsu basu bayyana ko ina ba sai anahiyar su Alhussain bayanarsu keda wuya kasa ta soma girgiza koramar wajan ta kafe kaf bishiyu suka soma zubewa kamar lokacin hamada babu wanda bai tsorata ba cikinsu sai Alhussan jarumin maza da ya tsaya kyam yana hucci.Gaba ɗaya jijjiyoyin jikinsa sun mummurde a sukwane wata hallita cikin hallitun ta kawo masa bahagon sara ya sunkuya cikin gwanintar iya salon yaki ya kauce ta karci kasa take wajan ya bada wani wawwakeken rai tamkar rijiya gaba biyu hucin giftawar halitar ya hada karamar gugguwar data turnuke wajan ya yi bakikkirin. Sai bayan lafawar iskarne Alhussain ya hangi gawar mahaifiyarsa yashe a kasa cikin jinni hankalinsa ya yi matukar tashi ya daddage ya kwarara kabara take tsuntsaye suka soma shawagi suna faɗowa kasa ya yi kukan kura ya fada cikin hallitun suka soma gabzawa yaki yake yana kukan rashin mahaifiyarsa shikenan ahalin ƁMarkahu sun yi nasarar watsa ahalinsu sunyi nasarar watsa a halinsu?.

Bai gama dawowa tunaninsa ba wani cikin hallitun ya shamace shi ya laftamasa ya kushi a kaucin cikinsa ta ke ya kwalla kabara ya zube kasa yana numfarfashi tuni suka suri Zajlat suka yi sama da ita.Duk abinda yake faruwa Sharmila da Sarki Sharimil na kallo ta madubin tsafi koda faruwar hakan sai suka takarkare suka kece da dariya dakaru da fadawan Sarkin suna masu tayasu kafin kiftawar ido sai gasu a gaban gidan sarautar dauke da Zajlat tana kuka.

7
Da gudu Aisha ta karaso daga maɓuyar da ta boye tun sa ada aka fara gwabza yakin ta yi yunkurin ɗaga Alhussain duk da kasancewarta jaruma kuma gwana a fagen yaki amma ya hakan ya gaggara . Ruwa ta ɗebo ta yi bisimillah ta shafa masa a jikinsa da ikon Allah sai ya yi zumbur ya mike yana layi kamar wanda yasha banju rike shi ta yi suka som tafiya fahimtar inda yake son nufa wato kan gawar mahaifiyarsa. Hakan yasa ta nufi can, koda zuwansu sai ya fashe da kuka sun jima sua kuka daga bisani ya mike shi ya yi mata wanka ya sallaceta ya buneta sai bayan komai ya lafa ciwan kuiɓin cikinsa ya soma uzura masa da kansa ya ɗinke ya shafa wani koran magani haɗe da zuma bayan ya yi basmallah kafa tara. Zuciyarsa ta dinga zafi musamman da ya kali Aisha ya ga ita kaɗai ta rage masa a duniya zuciyarsa ta yi zafi bai aune ba ya tsinkayi muryar Aisha tana fadin:-

“Hakika duk abinda ubangiji zai kaddarowa bawansa, to hakika yana cikin kaddarar rayuwarsa idan kuma ya yi hakuri yana da lada ma dumbin yawa”.
Koda ta zauna a zancanta sai idanunsa suka ciko da kwalla mai zafi ya share yana mai tasbihi ga ubangiji.
Lokacin da waɗanan hallitu suka kai Zajlat fadar mahaifinta sai gaba daya fadar ta yi tsit take a wajan kakarta Sharmila ta hukunta ta tare da sa a kaita gidan a zaba mahaifinta yana ji yana gani ya kasa hana aikata hakan. Tun daga ranar duk lokacin da aka je kai wa su Alhussain hari ba a ganinsu sai dai sautin muryoyinsu hakan ya dagulawa Sarki da bokanya hankali. Haka aka cigaba da azabtar da Zajlat duk sanda ta saci jiki ta je wajansu Alhussain.

A bangare guda kuma matar Sarki Sharmil bata da burin da ya wuce kashe Zajlat, yayin da soyayyar Zajlat ta yi wa dan Sarki Sharbusa wato Sham unu kamun kazar kuku. Daga wannan ranar ya zama ansawa Zajla takunkumin fita babu inda take zuwa kwatsam ranar Talata an shiga ɗakin bauta ta saci jiki ta tafi basu ankara ba sai da abin bautasu ya fusata ya soma haufar datsawa da girgiza katangun birnin hakan ya fusata Bokanya Sharmila tasa aka bi sahunta aka kawota shi ne dalilkin kaita ɗakin azaba.

CIGABAN LABARIN
Dakin da aka kai Zajlat kuntattacan dakine mara yalwa gashi mai tsaanin duhu, ko mikewa gaba daya bata iya yi a gefan dakin an yi wani rami da aka hura wuta a cikinsa wadda ta kasance ta zafi ce tana ci kodayaushe bata yankewa gata jajjur tana fitar da shud shudin haske mai tsoratarwa.
Tsayin kwanakinta biyu da ta yi a dakin cikin mawuyacin hali ta yi su. Domunzafin wutar yabfara y mata illa sossai a ranar kwana na uku ne ta shiga mawuyacin hali sabida galabaita harta kaita ga faduwa magashiyan a hankali bacci ya ɗauketa ta yi mafarki da Alhussain yana karanta mata kalmar, innalillahi wa inna ilaihirraji un tare da la ilaha ila antassubhanaka inikuntuminazalimun take ta mike a firgice tana maimaita kalmar take wutar ɗakin ta mutu wani haske ya gauraye ɗakin saɓanin duhu mai tsanani ta rarrafa ta sami kasa ta yi taimama kamar yadda Alhussain ya koyar da ita a wani zuwa da ta yi, ta yi jim tana tunanin yadda lamarin ya kasance.

Wani yammaci ne mai cike da ni ima Zajlat ta kaiwa su Alhussain ziyara koda ta je sai ta samu basu da ruwa gashi lokacin ibada ya karato sai ta ga duk sun tsuguna sun ɗora hannuwansu kan kasa ta zuba musu idanu tana kallo bata gaza ba ta furta,

“ya ku ma abota karamci menene wanan ku ke aikatawa?”.

Koda ta zauna a zancanta sai Aisha tace,

“wannan ita ce taimama”.

Cike da mamaki take maimaita kalmar ta sake furta,

“ki gafarce ni ya ake yin wannan ibada kuma baku koyamin ba?”.

Murmushi suka yi dukkasu daga bisani Khadija ta furta,

“yadda ake gabatar da taimama shine; zaki wara yatsun hannayanki biyu ne sai ki buga a kasa, sannan sai ki shafi fuskarki da cikin tafikan hannunki, sai kuma ki shafi hannayanki zuwa wuyan hannu (Ku’i), zaki yi ko kari ya tabbata ya game ko’ina na fuskarki a lokacin da kike shafar kar ki manta da karkashin haɓarki da kuma hannayanki idan kina da zobe sai kin cire domin shafar ta game ko ina, idan lokacin da kika shafo kasar ba’ace dole sai mutum ya sa kasa a fuskarsa ba.

Idan kuma ya ga dama sai ya yi shafar sau biyu to tafarko sai ya shafi fuska da ita ta biyun kuma ya shafi hannuwa zuwa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment