Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gwuiwar hannu.

Cikin mamaki Zajlat ta ce,

“shin ita ma tana ɓacci kamar yadda kuka yimin bayanin alwala?”.
Alhussain ne ya amshe batun,

“Zajlat hakane taimama tana baci da duk abinda yake bata alwala babbane ko karami, kamar tusa fitsari. Fitar maniyyi, jinin al’ada, sannan kuma idan uzurin da ya sa aka yi taimama ya gushe to taimama ta gushe.
Duk wanda ya yi taimama domin ya yi sallar farillah to ya halatta ya yi nafila da wannan taimamar. Idan mutum ya yi taimama ya yi sallah da ita sai kuma lokacin wata sallar ya yi kuma gashi ba abinda ya karya mishi taimama to sai ya sake wata taimamar kafin ya yi sallar, domin abin nufi anan sai ya sake neman ruwa idan bai samu ba to sai ya yi taimama.
Koda ya zauna a batusa sai ta yi murmushi ta ce,

“Yakai wannan jarumi mai cikar kamala me ya ke kawo ayi wannan ibada ta taimama?”.

A wannan karon Aisha ce ta amsa da cewa:-

Rashin ruwa, idan ya kasance matafiya suna cikin tafiya ko suna zaune a gida sai suka rasa ruwa sun nema iya yadda za su iya basu sami ruwan ba, to anan tunda sun nema basu samu ba ba za su bari lokaci ya wuce ba su ce sai sun je gida sai su gabatar da taimama su yi sallar su, ko da a cikin su akwai masu janaba, ko matan da al’adar su ta dauke. Kuma da zarar sun gabatar da wannan taimama to sun sauke wajibinsu ko da an sami ruwa ba za su sakeba. Wato shi addinin musulunci gwargwadon yadda ka gane shi a yadda yake gwargwadon yadda yake da sauki a gareka.
Rashin wadatar ruwa Idan kuma a tare da ku akwai ruwan amma kuna da matukar bukata domin shi zaku sha da shi zaku yi girki ko shi za ku ba dabbobi yadda idan ku ka yi alwala da shi ba zai ishe ku wadancan bukatuba, asalima za’a iya tagayyara, ko kuma ga ruwancan kuna hangowa to amma miyagun namun dajine a wurin ko kuma matattarar barayine wurin to anan fa hukunciku duka shine wadanda basu da ruwa, saboda haka wadanda suke dashi kadan domin bukatunsu sai su sha su yi taimama. Idan ga ruwan, amma ka ji tsoron cuta a jikinka ko kuma ciwon zai sami jinkirin warkewa, sai ka yi taimama. Idan ya zamana yana fama da rashin lafiya amma zai iya alwala sai dai ba zai iya motsawaba domin ya debo ruwan alwalar kuma bai sami wanda zai debo mai ruwanba ko babu wanda zai yi mishi alwalar kai tsaye sai ya yi taimama. Idan yana matukar jin tsoron sanyi idan ya yi amfani da ruwa, kuma ga shi yana son yin alwala ko wankan tsarki ga shi bai sami abinda zai dumama ruwanba to kai tsaye sai ya yi taimama.

Wadannan bayanan suna nuna mana cewa rashin lafiya bata dauke sallah, domin koda ba zai iya alwalaba saboda tsoron sanyi ko jinkirin warkewa ko dai daya daga cikin abubuwan da aka ambata to sai ya yi taimama, abin takaici shine sai ka ga dazarar mutum bashi da lafiya to abu na farko da zai ajiye shine sallah.
Hakanan inda mutum za’a tsare shi, ba zai bada hanzarin ai lokacin da suke a tsare ba’a barinsu su yi alwala to ba sai ya yi taimamaba. Idan mutum yana da ciwo a gabban alwalarsa kuma ba zai cutuba idan ya shafa hannunsa a kan ciwon to sai ya yi alwalar idan ya zo wurin sai ya shafa kawai ba sai ya wankeba.

Idan galibin jiki ya zama ba lafiya kamar ya zama ba inda ya raje sai hannu ko kafa to anan kai tsaye sai ya wuce zuwa taimama. Shi bayani akan abinda ya shafi wanke wasu gabobi sannan ayi shafa akan wasu gabobi sabo matsanancin rashin lafiya daya shafi gabban alwala ko taimama darasine mai zaman kansa, a littafin Iziyyah shine fasali na gwoma sha-daya, malamin ya ware fasalinne domin bayanin cututtuka da zasu sami gabban alwala, kuma ya kawo fasalinne bayan ya kammala bayani akan taimama a fasali na goma, Allah ya saka masa da alkhairi.

Ya halatta ka yi taimama a duk inda yake doron kasa kamar inda yake; rairayi ko jangargari ko dutse ko kamfa ko kasar gishiri ko ta kanwa ko inda yake dusar-kankarace.

: Allah ya yi bayanini shar’antuwar taimama a cikin Alkur’ani mai girma a Suratun Nisa’I, aya ta 43, da kuma Suratul Ma’idah aya ta: 6. amma ayanzu zamu kawo bayani akan ayar suratul ma’idah, wato aya ta shida kenan, Allah madaukakin sarki yana cewa:
”Ya ku dukkanin wadanda su ka yi imani! Idan kun tashi za ku yi sallah to ku wanke fuskokinku da kuma hannayanku zuwa gwiwar hannu, ku kuma shafi kawunanku kuma ku (wanke) kafafuwanku zuwa idon sawu, idan kun kasance masu janaba to ku tsarkaka (ku yi wanka), idan kuma kun kasance marasa lafiya ko kuna kan tafiya ko kuma daya daga cikinku ya yi bayan gida, ko kuma kun taba mata (janaba) baku sami ruwa ba to sai ku yi taimama a wuri mai tsarki sai ku sahfi fuskokinku da kuma hannayanku daga wurin, Allah baya nufin ya sanya mukun kunci ko kaka, saidai yanason ya tsarkake ku kuma domin ya cika ni’imarsa a gareku domin ku gode masa. (Ma’idah, aya ta:6).

Wannan ayar babbar ayace, ta kunshi hukunce-hukuncen Alwala da abinda yake karyata, da kuma janaba da yadda ake wankan tsarki, da kuma taimama da abinda ke sawa ayi taimamar da kuma yadda ake yenta, sannan da manufar da tasa Allah ya shar’anta taimamar.
Ma’aikin Allah –Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- yace: ”An bani abubuwa biyar da ba’a ba wani ba kafin ni; An taimakamin da tsoro (ma’ana sanya tsoronsa a zukatan makiya) na tafira tsawan wata guda, kuma an sanya min kasa ta zama wurin sallah da kuma tsarki, duk inda wani mutum daga cikin al’ummata sallah ta riskeshi to ya yi sallar shi” a wata riwayar ”To anan inda yake masallacinsa yake da kuma abin tsarkinsa”.

Bukhari, Hadisi na: 335 , Muslim Hadisi na: 521.

Wannan hadisin ba karamin hadisi bane, domin ya yi bayanin gatan da Allah ya yi wa wannan al’ummar gatan da bai yiwa wata al’ummaba, a ciki ya ambaci cewa an sanya masa kasa ta zama wurin sallah, al’ummomi da suka gabata basa sallah a ko ina sai a inda aka kebe musu, amma mu ko atsakar da ji ne sai ka tsaya ka kallaci alkibla ka yi sallar ka, kuma yace an sanya masa kasa ta zama wurin tsarki, za ka yi tsarki da ita.

Taimama matsayine na musamman da wannan al’umma ta kebantu da ita, Allah bai sanya taimama ga wata al’ummaba kafin wannan al’ummar domin yalwatawa ga wannan al’ummar. I jima’i: Malamai duk sun yi ijima’i akan tabbatuwar taimama. Ita taimama tana tsayawane matsayin ruwa a shar’ance lokacin da rowan ya faskara, dukkan abinda kasan ba’a yi said a ruwa to ana yi da taimama, kamar sallah, dawafi, karatun Alkur’ani da dai sauransu……”.

Koda ta zauna a tunaninta sai ta fashe da kuka tana mai yi wa mahaifiyar Alhussain fatan dacewa a lahira.
SHIN DAN SARKI SHARBUSA YANA SAMUN SOYAYYAR ZAJLAT?.

SAMARATU NA SAMUN NASARAR KAWAR DA ZAJLAT?.

SARKI SHARMIL DA BOKANYA SHARMILA NA SAMUN NASARAR KAUDA ALHUSSAIN?.

INA BURIN AISHA DA ALHUSSAIN KE TSAYAWA NA KAFA DAULAR BAITUL NUR A DORAN KASA?.
GIMBIYA ZAJLAT
8
Cikin tashin hankali ta kai mari ta kai gwauro, fuskarta ta yi jajjur har wani jajja ta ke yi ga wani gumi da ke keto mata tamkar fanfo ta numfasa kanan ta sauke idanunta a kan amintaciyar Baiwar tata,

“ya ke Juda ki sani bani da burin da ya wuce in kauda Zajlat a doran kasa amma hakan ya ci gagara, ina son in saki wani aiki mai matukar haɗari amma an tabbatarmin ke ce kaɗai zaki iya aiwatar dashi amma kain nan zan fara ganawa da boka Samus”.
Koda Samaratu ta zauna a zacanta, sai ta kyalkkyale da wata shu umar dariya lamarnin kenan daya haifar da kaɗuwar karamar iska, ta ke ta jawo wata kwataniyya ta runtse idanunta tana karanta waɗansu dalamusan tsafi faruwar hakan keda wuya wani hayaki mai launin ɗorawa da fari ya dinga fitowa daga kwatanniyar a hankali ya cuɗe waje ɗaya ya zama wani launi mai kala-kala sai ya zama wata irin hallita akan kwataniyar shi ba mutum ba ba aljani ba yana da motsewar fuska da katon kai ga idanunsa manya da sirarran hannuwa.Hancinsa katoto a bayansa akwa fuka-fukai kamar Malam buɗa mana littafi ya risina yana mai alamun girmamawa.

“Me ki ke so ya shugabata?”.

Ya.yi furucin da wata murya mai firgitarwa, cikin ɗaurewar fuska ta furta,

“ina son abinda zan nakasa rayuwar Gimbiya Zajlat ta daina amfanuwa daga nan gaba ɗaya a rasata sai dai inasan komai cikn tsari yadda Sarki da bokanya Sharmila ba zasu fuskanta ba”.
Koda ta zauna a zancanta sai ya kyalkkyale da dariya ya yi nuni da hannunsa take hotan Zajlat ya bayyana tana kwance tana bacci hannu yasa ta yi nuni zuwa gareta take wani haske baki ya fito ta yatsansa manuni ya daki kafaffunta faruwar hakan keda wuya ta kwalla giggitaciyar karar data karade gidan azaba gaba ɗaya a hankali kafaffunta suka hau nannaɗewa tamkar roba tun tana ihu da karfinta har ta hau shure-shure gaba ɗaya dakarun gidan na zagaye da ita sun zare makamai suna muzurai sun kasa kataɓus har ta daina motsi. Yana sauke hannunsa ya kyalkyale da dariya mai karfi tare da furta,

“daga yau ba ita ba taka doron kasa, kuma baza a taɓa samun maganin warkewarta ba har sai anje dutsan darul ukub shi kuma wannan gida shigasa babban haɗarine dai-dai yake da nemo jaki mai kaho a doron duniya”.

“Godiya na ke ya shugabana”.

Bat ya ɓace suka hau kyalkkyala dariya mai karfin gaske.
Boka Samus amintacen bokan Samaratu ne a ɓoye, babu wanda yasan yana yi mata aiki daga ita sai amintaciyar baiwarta Juda.
***

Lokacin da Zajlat ta kwala kara mai firgitarwa a firgice dakaru suka rugo suka zagayeta suna mazurai duk sun zare makamansu amma basu ga kowa ba sai shure-shure da take yi tana fitar da wata kumfa mai yauki take suka ruga aka sanar da Sarki abinda ke faruwa a kidime ya taho yana huci karan farko a rayuwarsa daya taka gidan Azaba da kafaffunsa halin daya sameta ya yi matukar daga masa hankali kai tsaye aka sureta sai fadar bokanya Sharmila suna shiga Sarki ya shimfiɗeta tare da zubewa yana rokonta wata mahaukaciyar tsawa ta daka masa tare da yi masa nuni daya fita ya bata waje yana ji yana gani ya fito yana kallon yadda kwalin ɗiyarsa ta koma tashi ɗaya. Fitarsu keda wuya ta kule fadarta tare da bada umarnin kada wanda ya sake shigowa sai nan da kwanaki uku, lokacin da labari ya kai kunnan Sarki Sharmil ba karamin tashin hankali ya shiga ba.
Al’ amarin ciwon Zajlat ya damu kowa a gidan sarautar kasanewarta mai tausayin na kasa da ita ba iya masarautar ba har ilahin mutanan garin kullum cikin bauta suke suna nema mata lafiya sai ya zamana ɗakin bauta bashi da shamaki da kowa kulum cikinta suke yi.



***

Kwana biyu tsakani Sarki ya shiga matsananciyar damuwa ga Sharmila ta hana a ganta bai san halin da take ciki ba, hakan yasa ya rame ya fita hayyacinsa ko abinci baya ci bashi da cikakkiyar nutsuwa. Al’ amarin Samaratu kuwa komai da yake faruwa tana hangensa ta madubin tsafinta komai na tafiya yadda take so. Ranar da Zajlat ta cika kwanaki uku a wajan bokanya Sharmila a ranar garin ya tashi da wani rin bakon al amari. Garin ya yi jajjur sossai daga yamma daga gabas kuma ya yi wani irn duhu ga zafin rana tamkar zai fasa kwanyarsu ga rijiyoyi duk sun kafe al’ amarin daya dugunzuma hankulan mazauna garin kenan suka fara iface-iface ana haka bokanya Sharmila bude fadarta tare da bada sanarwar tana son ganin kowa na garin manya da yara.

9
Koda fitowata sai daukacin mutanan garin suka sunkuyar da kai alamun girmamawa, ta bude baki cikin izza da takama,

“ya ku jama ar wannan gari a halin yanzu gimbiyarku na cikin mawuyancin hali wanda take bukatar magani a gaggauce. Sabida haka zamu sa gasar nemo mata magani bisa sharaɗin duk wando ya kawo maganin shi zai aureta…..”.

Koda ta zauna a zancenta sai mahaifinta ya yi zumbur ya mike yana muzurai, zuciyar Samaratu kuwa ta cika da bakin ciki, mahaifinta kuwa hankalinsa ta she ya buɗe baki zai yi magana sai suka yi arba da Zajlat cikin wani abu ana turata kafaffunta sun sirrance kamar na jariri koda suka yi arba da ita sai jikinsu ya yi sanyi masu kuka na yi masu hawaye na yi mahaifinta ma jiki a mace ya koma ya koma ya zauna yana maida numfashi da kyar. Kamar an tsikare shi zumbur ya mike,

“ni zan nemo mata magani!”.

Koda ya zauna a zancansa sai wajan ya i tsit, Samaratu kuwa ta cika da farin ciki ta sami hanyar kauda Sarki da Zajat cikin sauki. Tsawa mai karfi bokanya Sharmila ta daka masa, shi ma ya maida mata martanin tsawa karan farko kenan a masarautar ganin sa insa tsalaninsa da mahaifiyarsa.
Haka taran ya watse, tsayin kwana uku ana bada sanarwar samowa Zajlat magani ga garurruwan dake kusa dana nesa dasu a ranar kwana na hudu ne aka gama haɗuwa harabar masarautar ta cika makil yayan sarakuna da wazirai da sauran masu mukamai da dama ciki hada SHAM UNU da tawagarsa. Lokacin da aka bada sanarwar isowar bokanya Sharmila sai suka sake nutsuwa ta fito ɗaya bayan ɗaya take dubansu daga bisani ta buɗe baki zata yi magana.
Kamar daga sama suka hango wani ingarman doki fari tas yana haninniya ya nufo taron mutanan bayansa mutum ne a goye mahaya dokin dukansu fuskarsu a rufe take da wani mayani baki dashi suturarsu ta bambanta da ta mutanan gari take dakaru sama da hamsin suka yo kansu cikin gwanan cewar yaki kafin kiftawar ido dukkansu mahaya dokin suka diro tare da zare takubansu suka soma artabun yaki cikin gwaninta da tsagwaran jarumta kafin cikar sa a daya sn karar da dasu a haka saida suka karar da dakaru dari da hamsin a sanan bokanya Sharmila ta yi wa dakarunsu tsawa suka tsakaita dai-dai lokacin ne mayanin fuskokunsu ya zame suka bayyana tsananin mammaki y bayyana ga daukacun fuskokin mutanan wajan sabida ganin mace da namiji ga macen karama bata fi sa ar Zajlat ba take wajan ya kaure da hayaniya Sharmila ta yi tsawa aka dakata daga bisani ta bude baki kamar haka.
“Yaku waɗanan ma abota karfin meke tafe da ku?”.

Koda ta zauna a zancenta sai matashin ya buɗe baki ya ce,

“mun zo ne shiga sahun masu bawa Gimbiya taimakon magani amma da sharadi ni ba auranta ne muradina ba muradina shi ne ku karɓi addinina bayan na samo maganin idan kuka saɓa alkawari zan yake ku!”.

Koda ya tsaya da batunsa sai akai kalon kalo tsakanin Sarki da bokanya,

“menene addinin naka?”.

“Addinn gaskiya wato musulunci”.

Take zuciyarsu ta tsinke amma Sharmila ta dake,

“an yarje maka ku shiga sahu”.

Take suka shiga layi Sharimila ta kara nanata gasar da dalilinta ta ɗora da bayanin inda za a samo maganin.
10

Daya bayan ɗaya tadubesutare da furta,

“Darul ukub shi ne inda za a samo maganin gimbiya, daga nan zuwa darul ukub a binciken alkalumana tafiya ce ta tsawan sati biyu tae da tsayawa da hutawa idan kuma babu tsayawa tafiyar lwana tara ce. Daki ne da ke da nau in abubuwa kala-kala akwai haɗarurruka da masifu masu tarin yawa a wannan hanya. Hanya ce mai cike da sarkakiy an tabbatar babu hallitar data taɓa shiga wannan daji ta fito da ranta face ta mutu maganin da gimbiya take bukata yana tsakiyar wannan daji na darul ukub a wani kogo mai suna kogon mutuwa”.

Koda ta zauna a zancanta sai mahalata wajan suka soma zarewa a hankali a hankali har gun ya rage daga Sham unu sai wannan matashi da matashiyar budurwa da wasu jarumai uku Samu da Hamu da kuma Jurdas al’amarin daya bawa kowa mamaki kenann bokanya Sharmila kuwa dariya ta hau kyalkkyalawa take aka sallami mutan gari gaba ɗaya ta karasa yi musu bayanin garin ta sallamesu har sun juya zasu tafi matashin ya sake juyowa ya yi murmushin daya sa gaban sarki da bokanya cikin dakiyar zuciya ya sake maimata sharadinsa suka wuce, Sarki Sharbusa yana kuka ya yi sallama da ɗansa suka nausa suka soma tafiya.

***

Haka aka tura Zajlat cikin kekenta zuwa cikin gidan sarautar bata ko motsi, al amarin mahaifinta kuwa yana shiga ya nufi bokanya Sharmila yana huci,

“haba ya Ummina ya zaki min haka ki amince da sharadinsa?”.

Koda ya zauna a zancansa sai ta tuntsure da dariya lamarin daya bashi mamaki kenan daga bisani ta furta,

“nasan abinda kai baka sani ba ina so a yau ba gobe ba kasa a kashe matarka Samaratu”.

Cikin firgici ya soma motsa baki, bai samu damar tankawaba ta yi masa nuni da bango take komai ya bayyana jikinsa har tsuma yake ya suri takobi tsirara ya nufi cikin gidan sarautar yana huci bai yi wata-wata ba ya sare kan Samaratu ga mamakinsa sai kan ya koma daidai ta mike tare da nunashi da izgar hannunta ya yi sama ya daki bango ya faɗo a sume ta kyalkkyale da dariya ta bace ɓat daga gidan sarautar.

Hankalin Sharmila ba karamin tashi ya yi ba ta soma buga bincike don gano ina Samaratu ta nufa amma duk iyakar kokarinta ta kasa gano komai karshe ma madubin tsafinta bunduga yayi ya tarwase gaba ɗaya. Nan da nan ta baza dakaru nemanta amma tsayin kwana bakwai babu labarinta.

Lokacin da sarki Sharmil ya farfaɗo ba karamar buguwa ya yi ba, saida Sharmila ta gyara masa kashin guiwarsa nan hankalinsa ya tashi ya shiga neman mafita.

***

Al’amarin Samaratu kuwa bata bayyana a ko’ina ba sai gaban boka Samus a galabaice cikin dugunzuma take faɗin,

“ya kai amintacen bokana menene abin yi?”.

Koda ta zauna a zancanta sai ya sheke da dariya mai amo ya furta.

“Mafita ɗaya ce zaki bibbiyi sahun waɗancan jarumai yayin da suka yi nasarar ɗauko magain gimbiya ki karɓa da karfin jarumtarki ki shanye maganin ta nan kaɗai zaki sami tsagwaran karfin jarumtar bokanya Sharmila ki kwace masarautarsu”.

Koda ya zauna a batunsa sai tsoro ya bayyana a fuskarta, amma data tuna kudurinta saita hau shirin binsu hanya cike da muguwar manufa a ranta.



***

Lamarin su jarumi Sham unu wucewar sa a biyu suna tafiya wannan matashi yaja dokinsa ya tsaya koda ganin haka sai sauran suka dube shi ware mayaninsa ya yi tare da furta,

“lokacin ibadarmu ya yi zamu bautawa ubangijinmu”.

Koda jin hakan sai Samu da Hamu da Jardus suka kaɗa kawunansu suka yi gaba abinsu Shamunu kuwa sai ya sami waje ya sauke dokinsa ya tsaya yana kalo suka gabatar da ibadarsu. Ya dinga kallonsu cike da sha’awa har suka kammala suka mike suka cigaba da tafiya, babu mai kula wani a haka suka yi ta tafiya har kwana hudu amma basu hadu da kowa ba. Idan lokaci yayi Sham unu kan tsayasu suyi ibadarsu sossai babu abinda ke burgeshi face kyawun matashiyar yana son ganin fuskarta wadda ta kadance kullum a rufe cikin mayani bata buɗeta sai zata yi ibadarta.

A ranar kwana na tara ne ya kasa jurewa ya tambayi sunayansu babu jinkiri suka bayyana masa sunayansu na ainihi sossai ya yi mamaki da jin sunayansu ya tabbatar suna da manufa kan samowa gimbiya magani da kuma sharaɗinsu domin yana da tarihin yadda aka kashe mahaifansu ta hanyar haɗin bakin mahaifansu.
A ranar kwana na goma ne suka shigo wani daji mai tsananin sahara tafiyar sa a ɗaya suka riski su Samu kwance magashiyan koda suka karasa sai Sham unu ya kada kai zai wuce amma ga mamakinsa sai ya abokan tafiyarsa sun tsaya tare da basu taimakom ruwa suka sha suka dawo hayyacinsu cikin mamaki ya ce,

“yana ga ya kai wannan jarumi ma abocin karfi ko ka manta baro mu suka yi a baya basu tsaya mu ba?”.

Koda ya zauna a zancansa sai ya yi murmushi tare da furta,

“musulmi mutane ne masu tsarkin zuciya da kyakkyawan tunani. Daya daga cikin halayen musulmi shine ba sa kallon sauran mutane ta mahangar jinsi ko al’ada, addinnina ya yadda in taimaki wanda ya ke cikin halin neman taimako”.

Koda ya zauna a zancansa sai suka cika da mamaki a zukatansu haka suka cigaba da tafiya babu mai cewa ufan har tsawa sa a ɗaya. Sunyi tafiya mai yawa Sham un ya kasa jurewa ya dubeshi,

“wai menene addininka?”.

“Addinnina shi ne addinnin musulunci. Asalin addini a duniya shi ne musulunci. Mutum na farko da Allah ya halitta, Annabi Adam (alaihis salam), ya rayu ne bisa tafarkin musulunci. Dukkanin manzanni tun daga Annabi Nuhu (alaihis salam), zuwa Annabi Ibrahim, da Annabi Musa , da Annabi Isa , alaihimus salam, musulmai ne ma su kadaita Allah. Sai dai gaba dayansu Allah ya aikosu ne zuwa ga al’ummominsu kadai. Annabi na karshe kuma cikamakin tsarin annabawa shi ne Annabi Muhammadu (yabo da amincin Allah su tabbata a gareshi). Allah ya aiko Annabi

Muhammadu (SAW) da sako zuwa ga daukacin al’ummar duniya, mutane da aljannu. An haifeshi a birnin Makkah da a yanzu ke kasar Saudi Arabia. Annabi Muhammadu (SAW), bakureishe ne, dan Abdullahi da Amina daga tsatson Annabi Isma’ila (AS) dan Annabi Ibrahim (AS).

“Shi ya ake shiga wannan addinni naka?”

Koda ya zauna a batunsa sai ya dubeshi,

“ana shigasa ne ta hanyar kalma shahada ita kuma kalma shahada na cikin sharaɗan musulunci”.

“Ko zaka iya bayyana min su?”.

“Kwarai kuwa dan uwa. Shika shikan musulunci guda biyar sune ne kamar haka :- Kalmar shahada (TAUHIDI), Sallah, Azumi, Zakkah, da Aikin hajji ga wanda ke da iko. Kalmar Shahada

ma’anarsa shine shaidawa babu abun bauta bisa cancanta sai ALLAH (SWT), sa’annan Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne.

Sallah sallah na daga cikin shika shikan Musulunci mai mahimmanci matuka bayan Tauhidi, ana bukatar kowanne musulmi yayi Sallah sau biyar a rana, yana mai fuskantar Ka’aba dake kasar Saudiya . A kasashen Musulmai, za’a ke jin kiran Sallah daga Masallaci mafi kusa a yayin da lokacin Sallah yayi.
Sallah ana yinta ne cikin Natsuwa, domin a samu kyakkyawan lada. Azumi : Wannan rukuni ne wanda ake nufin barin ci, da sha, da yin jima’i daga fitowan alfijir har zuwa faduwan rana. Dukkan musulmi tilas ne da ya/ta azimci watan Ramalana (watau wata na tara a kalandar musulunci).

Zakka shi ne cire wani kayyadadden kaso, daga cikin wasu kayyadaddun dukiyoyi, a cikin wani kayyadadden lokaci ga wasu kayyadaddun mutane, domin Allah (SWT). Hajji shi ne zuwa ziyartan dakin Allah Mai Alfarma ga wanda keda iko da nufin Ibada. Imani ma’anan Imani shi ne : abun da zuciya ta kudurta, harshe yayi furuci da shi, sa’annan gabban jiki suka yi aiki da shi. Imani yana da shika-shikai guda shida (6) kamar haka : Imani da Allah, da Mala’ikunsa, da littafansa, da Manzanninsa, da Ranar karshe, da Imani da kaddara mai dadi ko marar dadi”.
Koda ya zauna a zancansa sai jikinsa ya yi sanyi dai-dai lokacin suka kawo hanyar data rabu gida uku wadda daga itane za su shiga dajin darul ukub bayan sunyi tafiyar sa a huɗu cif. tsayawa suka yi suna shawarwarin abin yi……

GIMBIYA ZAJLAT

BABI NA SHA DAYA
Koda suka tsaya sai Samu ya kama hannun Hamu suka nufi hanyar da ta yi yamma da ganin haka sai Jardus ya kama Sham’unu suka nufi hanyar kudu take Alhussain da Aisha suka nufi hanyar da ta yi gabas suka nausa. Sham’unu yana ta waigensu har suka ɓacewa ganinsa gaba ɗaya tafiya suke cikin tsanain sahara ga zafin rana takai gaba ɗaya ababan hawansu sun galabaita sun faɗi haka suka barsu suka cigaba da tafiya.

***

Lokacin da Hamu da Samu suka nausa cikin dajin tafiyar sa a daya suka riski kansu a wata faffaaɗar hanya mai cike da kwazazzabai ga duwarwatsu, haka suka dinga bi har suka wuce duwatsun. Cikin hanyar suka dinga gamuwa da namun daji masu haɗarin gaske suna artabu. Kwatsam ranar kwana na ukun gab da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment