Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡




_NoorEemaan_





_*hoorain zai zo da wani salo na daban wanda baku taba gani ba, novel din na daban, ya sha bambam da duk wani Novel nawa, ban ce alkamina yafi na kowa ba, amma alkalamina na daban ne, just follow my pen, and i assure you that you Will never regret*_




In the name of Allah, most gracious, most merciful.




Chapter 1️⃣⏩2️⃣


*BUKAVU BARRACKS KANO*

Babban barikin sojoji ne mai matukar girma, yana Ι—auke da waje je daban-daban, yayinda kabilu mabambamta hadi da addinin ne a cikin barikin, sosai suke zaman lafiya ga hadin kai gwanin sha'awa.


Ko wani soja da iyalan sa da area da suke zama, ya danganta da ranka(muΖ™amin) Mutum.

Misali akwai officers mess, batcher, White House, da sauran su, haka ma akwai asibiti da suke kira MRS duk a cikin barikin.



Zaune yake a officer dinsa, in da aka kawata office din da kayan k'awa irin na sojas...
fuskar sa a murtuke yake amma hakan bai hana kyawun sa buya ba.

Kyakkyawan matashi ne mai shekaru talatin da biyu a duniya, sanye yake da kakin soldier da yayi matuΖ™ar yi wa farar fatar sa kyau, duk da a zaune yake amma hakan bai hana mutum ya gane cewa shi din dogo ne ba, mai fadaddar kirjin, a takaice dai giant wanda ya sha training sosai.
Gashin kansa mai tsayi ne, har parking yake, domin yazo masa har saman kafadun sa, sai dai bai barin shi a baje, always Yana parking gashin.


Sajen sa mara yawa kwantacce ne daya kara masa wani sirrin kyau, zagayayyen fuska ne dashi mai dauke da cikakken gira hadi da eyelashes masu yalwa, hacin sa dogo ne mai tsari, idanun sa madaidaita ne masu Ι—auke da eyeball sky blue, sai bakin sa madaidaici red color, a takaice dai he's damn handsome!


System ce a gaban sa yake operating da hannu biyu at the same time cike da kwarewa, yayinda lokaci zuwa lokaci yana Ι—an sipping coffee dake kan table din shi, sam bai damu da abinci ba, mafi yawan lokuta yafi gane wa coffe.


Alamun sako ya gani an Turo ta Gmail din shi, hakan yasa bayan ya gama abinda yake ya shiga.
sunan field marshal ya gani, wanda hakan ya nuna cewa shine ya Turo masa sakon, a nutse ya karanta komai in less than five minutes duk da yawan rubutun...

Hannu ya sa ya shafa kwantaciyyar sumar sa, sanan ya furzar da iska daga bakin sa hadi da lumshe rikitattun idanun sa.

Amsa ya rubutawa marshal da cewa ya gan sakon, sannan ya kashe system din gaba daya

mikewa yayi tsaye... Masha Allah dogo ne sosai wanda ya dace da tsarin halittar jikinsa, hular sa ta sojas ya saka wanda ya Ζ™ara masa kyau sannan ya saka wani brown sunscreen (gilashi) ya dauki wayar sa ya nufi hanyar barin officer Ι—in cikin tafiyar sa mai cike da izza, takama, hadi da burgewa...



Jefi-jefi yana haduwa da sojas daya girma a rank suna gaishe shi cike da girmamawa, hannu kawai yake daga musu ba kuma Ι—an wulakanci ba, sun san halin shi na rashin son magana shiyasa basa damuwa.



Haraban office din na da matukar kyau an kawata shi da flowers masu ban sha'awa green sai kamshi furanni suke ga Nigerian flag da wasu tambari na sojas da aka kawata Haraban da shi...

Wajen hadaddiyar motar sa kirari Bugatti ya nufa, ya buΙ—e murfin ya fada ciki, har ya ta da motar ya ji an K'wank'waso glass din motar.

Zuge Glass din motar Ζ™asa yayi, kasancewar ya rufe kuma tinted ne...

a hankali, ta tsakankanin lips din shi ya furta "Imran" ta yanda babu wanda ya ji, shi ma Imran lips din shi ya karanta da bazai ji ba.

murmushi yayi, domin tun yana mamakin abokin shi ya gane cewa haka halin sa yake sam baya son magana, domin da fari ya dauka wulakanci da girman kai ne, sai da ya zauna dashi har suka kulla abota sannan ya gane cewa halin shi mai kyau ne.


"Yes Captain, ina zaka je ne haka?"


Saurayin nan da aka kira da Captain yace "Ammi.... I wanna see her" ya fada yana jan sunan Ammin.


"Uhmmmm mummy's boy" Imran ya fada cike da tsokanar.


Murmushin da iyakar sa lips kaΙ—ai yayi.

"Sai ka dawo toh, ka gaishe min da ita please" Imran ya fada.

Jingina kai Captain yayi yana rufe Glass din motar, kana a 360 ya bar haraban office din.



*Nassarawa GRA Sultan road*

Had'add'en unguwa ne mai dauke da had'add'un gida irin na masu hannu da shuni, ko ina shiru kowa na cikin gidan sa.


A gaban wani babban gate mai ruwan goro ya danna horn, mintuna biyu kacal aka wangale masa gate din... a guje kamar yadda ya saba tuki haka ya yi parking motar a parking space dake gidan sannan ya bude kofar motar ya fito.


Part hudu ne a gidan, wanda daya na Ammi ne, daya nasa duk da baya zama a gidan, daya na yan'uwan shi, daya kuma babu kowa wanda hasali na mai gidan ne da Allah yayi masa rasuwa.


Part dake tsakiya wanda ya kasance na Ammi ya nufa, gaban hadaddiyar kofar ya tsaya, inda da kansa kofar ta bude ya shiga bakin sa dauke da sallama, da bana tunanin akwai wanda zai ji shi, saboda yadda ya furta sallamar kamar wanda aka yi wa dole.



Macece mai shekaru 50 a duniya, Zaune take cikin shigar less buba Mai kyau da tsada irin na mayan mata, ta sanya medicated Glass, kyakkyawa ce sosai domin kamanin su daya da Captain, kamilalliyar fuskar ta dauke da murmushi mai kyau ganin yaron ta da take matukar so.


"Welcome home My Captain" ta fada tana ware masa hannu.


Cikin tafiyar sa ta lafiyayyen namiji ya karasa gaban ta ya rungume ta, yana fadin

"i miss You first love" hadi da zame kanshi ya kwantar kan cinyar ta.

Murmushi Ammi tayi, ta cire hular kansa, shafa kansa tayi, kullum sai yazo ya ganta amma hakan baya hana shi cewa he miss her.


"Miss you too my jarumin jarumai" ta kira shi da sunan da takan kira shi a wasu lokuta.


Dakin ya dauki shiru kamar ba mutane a ciki, hannun Ammi daya sha jan kunshi ya kama yana kallo, murmushin da bai fito ba Ammi tayi, domin ta fuskanci yayi masa kyau ne amma fada ne ba zai yi ba, girgiza kai tayi, kaf yaranta halin shi ya sha bambam da sauran, komai nasa na daban ne, tun yana karami ta lura yana son kunshi musamman ja. burinta Allah ya bashi mace ta gari, ita kuma tayi alkawarin sai ta sa wa matar ra'ayin kunshi ko da bata da ra'ayin hakan.

Amma abin da kamar wuya domin ko budurwa bai da shi, baya kula kowa, ga kannen shi suna da budurwa amma shi kam sam ba ya son maganar ko wacce mace, duk da kawo kan su da suke gareshi.

Tun Ammi na yi masa magana har ta gaji, domin har cikin dangi ta zabar masa ya nuna baya ra'ayi, haka ta cigaba da yi masa addu'a da fatan Allah ya bashi mace ta gari.


Can ta dago kan shi tace "ka ci abinci?"


Yamutsa fuska yayi, cikin yanayi mai kama da shagwaba daya saba yi wa Ammi yace

"Am full Ammi..."


"Ba wani You re full, kullum haka kake cewa, banason wanna rashin cin abincin naka fa, Ni har mamaki nake duk da baka cin abinci amma ko rama baka yi, oya tashi mu je lemme give you something to eat" ta karasa tana rike hannun shi suka nufi dinining table.


Zaunar da shi tayi kamar karamin yaro Sannan ta shiga serving din shi hadaddiyar fried rice Daya Sha namomi da coslow a gefe, da kanta ta shiga bashi a baki, a hankali ya dinga bude bakin sa yana karba ba dan kuma Ι—an yana jin yunwa ba, sai dan farincikin Ammi, a rayuwar baya kaunar Ι“acin ranta.


Samari uku ne suka shigo cikin falon suna surutai da alama musu suke a tsakanin su, sai dai ganin Captain a zaune Ammi na bashi abinci sai duk suka nutsu kowa ya tsuke bakin shi domin sun san baya son hayaniya, domin yanzu ne zai yi kasa-kasa dasu.



"Ya Hamdan sannu da zuwa" duk suka hada baki wurin fadin hakan.


Kai ya jinjina musu ba tare da ya ce komai ba, cikin kasa da murya daya daga cikin su mai suna Anas yace "kabeer, Omar, ku kalli yadda Ammi ke bawa ya Hamdan abinci kamar jariri"


Dariya ya bawa su Abbas amma babu halin sakin ta, haka suka kunshe abin su, sannan suka sanar da Ammi zasu fita dubiyan abokin su da bai da lafiya, adawo lafiya Ammi ta musu sannan tace su yi masa sannu...



Ganin Ammi bata da niyyar daina bashi abincin sai ya kama hannun ta ya na yamutsa fuska, yace "Please Ammi"sarai ta fahimce shi, sai ta ajiye cokalin ta zuba masa ruwan gora a Glass cup ta bashi, ya Ι—an sha sannan ya ajiye, kan kujerar falon suka dawo...


"Ammmmiiiiiii...." ya kira sunan ta da husky voice din shi.


"Na'am"

Ammi ta amsa tana kallon shi hadi da bashi hankalin ta, numfashi ya furzar ya ma rasa ta yanda zai yi mata wanna bayanin mai tsaho da marshal ya turo masa, domin shine abin da zai bashi wahala.


Wayar sa kirar iPhone 12promax ya mikawa Ammi bayan ya shiga ta Gmail din.

Karban wayar Ammi tayi kana a nutse ta shiga karanta inda karatun ya dauke ta tsahon mintuna bakwai kafin ta gama.


Gwauron numfashi ta saki a lokacin data gama karantawa, hannun Hamdan ta kama cikin nata, tace "na karanta, kai ne zaka jagoranci wasu sojas zuwa kwantar da tarzoma, sam bana kaunar ka zuwa duk wani abu da ya shafi yaki, duk da nan cikin Nigeria ne, zuciya ta cike take da tsoro, amma bani da zabi daga wuce ka je din..."


Kara rike hannunsa da kyau tayi tace "ya Allah! Ka tsare dana daga mugun gani, ka raba tsakanin shi da mugaye azzalumai, ya Allah ka dawo min da shi lafiya, ka basu nasara kan wanna aikin da zasu je yi, ya Allah ka tsare shi da sauran sojoji" ta karasa kwalla na cika idanun ta, amma bata bari ya gani ba, domin ta san cewa matukar ya ga kukan ta, zai ce ya fasa zuwa, ba kuma ta so ta ruguza mafarkin shi, domin tun yana dan karamin yaro yake kaunar zama soja da kuma yi wa Ζ™asar sa hidima.

Rungume ta Hamdan yayi, har abada yana alfahari da Ammin shi

"Ameen ya rabb! thanks Ammi, i love You so much"


"I love you too my captain" ta faΙ—a tana shafa bayan sa.



Haka ya cigaba da zama da Ammin har yamma ta yi sosai, ya kuma ji dadi kasancewar su tare, Domin itace mutum mafi soyuwa a duniyar sa, bai san so ba sai a kanta, hakan yasa wasu lokutan yake kiranta da First love.



Sai bayan magriba ya yi mata sallama cike da kewar ta ya tafi, a hanya Isha tayi masa, sai kawai yayi sallar sa a masallacin gadon k'aya sannan ya cigaba da tafiya har ya shigo cikin barracks... bangaren da gidan sa ya ke ya nufa ya faka motar sa, sannan ya shiga cikin gidan, wayar hannun sa kawai ya ajiye ya cire duka kakin jikin sa ya jefa cikin laundary basket, towel ya daura a jikin sa sannan ya shiga had'add'en toilet din sa.



Shower ya sakar wa, kansa, yana dafe da bango inda ruwan ya shiga dukan sa, ya dauki mintuna goma sannan ya fito, short nicker mai zanen soldier ya saka, sannan ya fada kan gado, lumshe ido yayi, iska mai dadi dake kadawa yana shigowa ta window'n sa, hannunsa kan six packs dinsa Yana shafawa, ya dauki mintuna biyar a haka sannan yaji wayar sa na ringing, bude lumsassun idanunsa yayi da suka yi nauyi saboda gajiya da yake tattare da ita kana ya mika hannu ya dauki wayar....





07082281566




NoorEemaan loves you all habibte'sπŸ’ž


Tue, 17 2022.
7:38am
[14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡



# _NoorEemaan_




The writer of
Rayuwar faheemah
Mijin Ammina ne sila
Papi ne
Kyautar koda
Abraham
And nowπŸ‘‡
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)






Chapter5️⃣⏩6️⃣


D'ago fararren idanun ta masu d'auke da brown eye ball tayi, kana ta kalli wacce ta kira ta.

murmushin da za a kira shi na yake matar ta sakar wa hoorain, martani hoorain ta mayar mata har jerarrun hak'oranta suka bayyana, a hankali matar nan da a kalla zata yi shekaru talatin da tara ta karaso ta zauna a gefen ta, cikin kauna mai tsanani da take wa yarta tace

"Hoorain ga abinci a daki, na dauko miki?"


"A'a Mami.... na koshi" hoorain ta fada cikin sanyin muryar ta mai dad'in amon.


"Me kika ci da zaki ce kin koshi, ko bakya son wanna abinci wani kike so?" Mami ta tambaye ta with so much care.


Murmushi hoorain ta sakar wa Mami tana kokarin mayar da kwallar ta, abinda zasu kai baki wahala yake musu, amma domin farincikin ta Mami ke tambayar ta idan wani abu take so, hak`ik`a idan taci abincin nan bata kasance y'a mai jikin kai hadi da tausayin mahaifiyar ta ba.


"Allah Mami cikina a cushe yake, bana jin yunwa, yanzu ma da daga band'aki nake" ta karasa tana sakar wa Mami murmushi domin kwantar mata da hankali.

Jinjina kai mami tayi, kana ta mike ta shige daki...
Yamutsa fuska Hoorain tayi sak'amak'on wani murdawa da cikin ta yayi kamar y'a'yan hanjin ta zasu fito saboda yanda cikin ta yake wayam babu abinci, amma bazata iya ci ba, domin ta tabbatar Mami ta fita jin yunwa, domin a daren jiya dan guntun abinci daya rage musu ita ta cinye, Mami ta ce ta koshi saboda ita ta samu ta ci, cikin dare tana kallon Mami ba tare da sanin ta ba tana murkususu hadi da yin ruf da ciki, a jiya tayi kuka sosai mara sauti domin bata so mahaifiyar ta taji...



⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*HAMDAN*
Da misalin k'arfe uku da mintuna arba'in suka isa kogi kauyen Oguma. Sai dai ba cikin kauyen can ciki ba.
Tunda daga wajen kauyen Hamdan ya fahimci cewa tabbas kauyen nan ba lafiya, haka dai suka nufi inda aka tanadar musu, already an riga anyi musu abinci, nan mutanen da aka bawa contract din abincin suka shiga gabatar musu dashi.


Kallo daya hamadan yayi wa abincin ya dauke kansa, sam baya jin zai iya cin wanna abincin da ya tabbatar hannu da yawa ne ya dafa ta, sannan bai san yaya tsaftar mutanen yake ba.


Nannade hannu rigar shi yayi, sannan ya fara ciri bakin safa da Boot din kafar sa, inda take farar lafiyayyen kafar sa ta bayyana tamkar bai taba taka Ζ™asa ba.

Dan jan wandon sa yayi sama kad'an, ya cire agogon hannun sa ya d'aura kan wani babban dutsen dake gefen wajen, cike da nutsuwa ya shiga yin alwala, bayan ya gama ya mayar da safar sa da takalmi, zai dauki agogon sa dake kan dutse karaf ya kama Godiya tana kallon sa, macen soja ce yar garin Jos, kara daure fuskar nan yayi tamau fiye da baya, sannan ya bude motar su ya dauki sallaya kana ya fuskanci gabas ya fara sallah cike da nutsuwa, sallar daya dauke shi mintuna goma kafin ya iddar, addu'a sosai yayi, kan Allah ya basu nasara a wannan aikin da suka zo yi, wayar sa ya ciro daga aljihun wandon sa, ya danna number'n Ammi.... Bayan ta daga yace

"first love ina wuni, nayi kewar ki"


Murmushi tayi kana tace
"Lafiya Lou Captain, ya hanya? Ina ta son kiran ka amma ban samu zama ba, iyalan baba Dalhat ne suka kawo min ziyara"


Lumshe rikitattun sky blue eyes din sa yayi kana yace
"Mun isa kauyen Ammi"


Ajiyar zuciya ya ji Ammi ta saki, ta shiga fadin alhamdulillah, daga nan suka Ι—an yi hira, yana jin Muryar Ayiyah da su Omar suka hira, kafin su yi sallama Ammi ta jadadda masa lallai ya ci abinci k'ar ya zauna da yunwa, ya dai amsa mata, amma bazai iya cin wanna abincin ba, rather he prefer ya sha coffeen sa.


Bayan sallar Isha ne, duk sojas din sun kasance cikin shiri, dama yan ta'addan nan cikin dare suke kawo farmaki kauyen, cike da k'warewa Hamdan yake basu umarni da nuna musu direction din da kowa zai bi cikin kauyen ba tare da yan ta'addan sun sani ba, sannan wasu sojas din ya basu umarnin zaga gidajen kauyen domin tabbatar da tsoro... haka dai ya rarraba su ta yanda za a samu komai ya tafi yanda suka tsara...


*10:00pm*
Duk da tsoron dake lullub'e a zukatan jama'ar kauyen Oguma, amma hakan bai hana wasu kwantar da hak`ark`arin su domin bacci ba musamman yara marasa wayo cikinsu, Manyan kuma na zaune cikin zullumi da tsoro mai tsanani.


Karan bindigan da kauyen suka ji yayi sanadiyar karin tashin hankalin su, hakan kuma ya sanar musu cewa azzaluman sun shigo...

Masu tsananin tsoro har fitsari suka saki saboda tashin hankali, wasu kuwa cikin su ne ya shiga murd'awa suna shiga ba haya, domin rage ciki, wanda tashin hankali ya haifar musu da shi, masu buyo har a k'ark'ashin gado na yi, wasu na neman hanyar guguwa, wasu kuma sun fito waje, gaba-daya kukan su ya cika kauyen, ga yan ta'addan da suka fara cinna wuta a wasu gidajen...

Ta bangaren Hoorain da mami kuwa suna cikin gidan su basu fito ba, bama zasu iya gudu ba saboda lalurar hoorain bazai bari su tsira da ran su ba tare da an kama su ba, sai dai wani ikon Allah.
Mami baiwar Allah na zaune kan kod'ad'iyyar sallayar su tana rokon Allah ya kawo musu dauki, hoorain dake gefe hawaye na zuba daga idanun ta ma addu'a sosai take a ranta tana fatan Allah ya kawo musu karshen wannan kashe-kashe rayukan da ake a duniya, tana mamaki mutane marasa imani da zasu iya kashe rai da bai yi maka komai ba saboda son duniya, me suka tanada da zasu kare kan su da shi idan Allah ya tambaye su ranar gobe kiyama?


Daga Ι“angaren yan ta'addan nan kuwa, harbi kawai suka fara ji from no where, wanna hakan ya tabbatar musu da cewa sojoji ne, maimakon su yarda makaman yakin su sai ma kara sakin harbin da suke, nan fa zugan soldiers dinnan suka bayyana kansu kana suka cigaba da sakar musu ruwan alburushi... suma yan ta'addan na sakar musu, yan kauyen Oguma suke dawo yan kallo, tsoron daya lullube zukatan su na raguwa, wasu sojas dake tsaye a kofar ko wani gida suka umarci wadanda suka fito waje kan su koma cikin gida gudun kada harbi ya same su, ai kuwa da gudu duk suka shiga har da saka sakata, dama tsananin tsoro, rudu, da rashin sanin abin yi ne ya fito da su.

Nan fada ya dawo tsakanin SOLDIERS da yan TA'ADDA, sai musayar wuta harbi suke cike da kwarewa...
yan ta'addan nan kamar kara tunkudo su ake, ana kashe su suna kara fitowa, abu fa yaki karewa har karfen dayan dare, inda a lokacin shugaban su da wasu zugan suka kara cika kauyen, suna cigaba da harbi.

Al'amarin fa ya girmama tunanin sojas dinnan, domin basu dauka haka abin yayi muni ba.
Godiya soja da itama take cikin masu harbin ta koma gefe ta yanda ba za a ganta ba, wayarta ta fito dashi, number'n Hamdan ta yi dialing wanda Allah kadai ya san ina ta samu...



*******

Safa da marwa yake, cikin farfajiyar gidan da suke, ya kira number'n wasu sojas din da yake da shi, amma basa dagawa, ya tabbata har yanzu basu kamalla bane, gashi manyan sa sun bashi umarnin cewa kada ya shiga yakin, na shi bada umarni ne da jagorantan su kawai. Amma ya fada a ransa cewa dole idan fadan ya Ι“aci zai shiga cikin su... yana cikin wannan tunanin yaji wayar sa na ringing, bakuwar number'n ya gani, latsa kore yayi ya Ζ™ara a kunne sa ba tare da yace komai ba


Cikin muryar ta mai amon sauti da jarumta kamar ba mace ba tace
"sir! Godiya ce, yan ta'addan nan kara yawa suke, domin har sun kashe mana mutane biyar...."


Bai jira ta gama maganar ba ya kashe wayar ya jefa a aljihun wandon kakin sa, cikin zafin nama ya dauki bindigogi bayan ya cika musu bullet, tsakanin cikin kauyen Oguma da gidan da aka tanadar musu tafiyar mintuna talatin ne, ba kuma yaso yayi amfani da abin hawa, saboda hakan zai sanar wa yan ta'addan zuwan sa, so yake yayi musu dirar ba zata, da direction da aka basu ya dinga bi, cikin sauri-sauri gudu-gudu cike da taka tsantsan domin isa wajen...✍️








NoorEemaan
07082281566


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JxzoG62bUENBfExeNPbRSu
[14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡




_NoorEemaan_




Chapter 3️⃣⏩4️⃣



"FIELD MARSHAL"

Shine sunan daya gani a rubuce baro-baro kan screen din wayar sa.

Latsa kore yayi hadi da kara wayar a kunne sa, cikin girmamawa wa marshal yace


"Good evening sir!"


"Evening captain, hope you are good?"


Hamdan yace "very well sir"


"That's nice, am... kan maganar da zaka jagoranci wasu sojas zuwa yaki ya tashi daga sati mai zuwa, domin mun samu labarin yan ta'addan nan sun sake kai farmaki wa kauyen, suna cikin wani hali matuΖ™a, dan haka jibi ne tafiyar ku in Sha Allah, domin gobe za a kamalla muku komai na tafiyar, all the Best captain Hamdan"



"Thank you sir" ya amsa yana taune jajayen labban'sa masu daukar hankali.

Ya jima yana tunane-tunane kana bacci ya dauke sa, kasancewar a matukar gajiye yake.



⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐



*WASHEGARI*
Misalin karfe goman safiya ce, zaune yake cikin motar sa yana sharara gudu kan lafiyayyen kwaltan, sanye yake da three quater

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment