Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsara masa.


"Morning!"

Ya fada cikin husky voice din sa, yayi shiru na seconds hamsin duk sun zuba ido da kunne suna jiran yayi magana.



"Ban zan tafi da ku ba, akwai abinda zan yi a nan for some days, already nayi magana da commander, safe trip guys"



Yana gama fadin haka ya juya zuwa cikin gidan, yana mamakin yanda ya kasa sarrafa kan sa, balle ya bijirewa umarnin da zuciyar sa ke ba sa.



Haka ya wuni cikin gidan, ba tare da ya sake fita ba.. ta bangaren sojas dinnan kuwa misalin k'arfe hud'u na yamma suka isa bukavu barracks motocin su a jere reras... Da ihu suka shiga babban gate din *quarter guard* suna buga band, hadi da rera wata waka ta soldiers, gaba-daya Muryar sa ta karade barrack din daya kasancewa shiru, yawancin sojas dake barrack din suka fito waje murmushi dauke a fuskar su suna daga musu hannu, domin wanna ihun da sojas din keyi ya tabbatar da cewa sun samu nasara a fita wannan yakin da suka je.



Commander dake tsaye cikin tsantsar farinciki na kallon su har suka gama faka motar su, kana duk suka zo wajen sa, cikin girmamawa suka kame kam kana suka tsara masa...

Hannu ya dora a kansa yayi musu alamun jinjina, wanda hakan yayi nuni da cewa ya jinjina wa jarumtar su, ya kuma ji dad'i, bai wani tsayar da su ba ya sallame su domin su huta gajiya...




*NASARAWA GRA SULTAN ROAD*
"Falmata! Wai har yanzu wannan gantalafaffen inuwar yakuwar Hamdan din bai dawo ba? Bayan ga shi mun samu labarin sauran sojojin sun dawo, duk da bai da kirki, amma Ni na damu da shi saboda banda bakin hali irin nasa, yadda nake fara a fuska haka zuciya ta take tas, na rantse da Assamadu da ina nan lokacin da Yaron nan zai tafi soja da ban bari ba, yo ya lafiyar kura ma, ace banda bakin hali da murtuke fuska babu abinda ya karo" Ayiyah ta karasa cikin kumfan baki, kai kace zata rufe Mutum da duka.



Su kabeer dake zaune a wajen dariya kawai suke ba ma kamar kalmar gantalafaffe inuwar yakuwa da ta ce.


Ammi dake zaune ta kalle ta kana ta ce "Ayiyah bari na kara kira number'n sa, Ni kaina na damu da rashin dawowar ta sa wallahi".
Ammi ta karasa tana latsa tsad'ad'iyyar wayar ta wanda hamdan ya siya musu iri Ι—aya.



*HAMDAN*
Zaune yake ya jingina kansa da bangon dakin, idanun sa a lumshe, Muryar ta dake rera waka na amsa kuwwa a kunnen sa tamk'ar yanzu ne ta ke yi, ringing din wayar sa ne ya dawo da shi duniyar tunanin daya fada, rikitatun idanun sa da suka dan Sanja launin ya ware kana ya latse kore hadi da karawa a kunnen sa...




"HAMDAN!"
Ammi ta kira real name din sa wanda zai yi wuya ka ji ta kira shi da suna sa.



"Yes first love, good evening?"



Bata tsaya amsa gaisuwar ba tace "Are You okay? talk to me kana lafiya dai ko?"



Murmushin da iyakar sa labb'a ya saki, yana matuΖ™ar kaunar Ammi fiye da zaton mutum, ita din rayuwar sa...

"Ammi ina lafiya"


"Then meyasa baka dawo da sauran sojas dinnan ba, am pretty sure baka dawo ba, na san da ka zo gida".



"Dan taune lips din sa yayi, cikin yanayin sa na rashin son magana yace " ina Kogi..., amma zan dawo soon, wani abu zan yi ne, amma karki tambaye ni please Ammi nah"



Jikin Ammi ne yayi sanyi, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "kana boye min wani abu ne?"


"Not at all first love"



"Hmmmm..." Ammi tace tana sauke numfashi, kana ta kara da cewa "i wish you all the best son"

"Thank you first love, how are my siblings doing?"


"Fine alhamdulillah" daga can ya ji muryar Ayiyah na cewa

"ka ji dan k'wal uban yaro mara kirki, ina nan na tada hankalina a kan ka amma ko kace a bani way..." Ai bai jira yaci karshen maganar ba ya katse wayar, domin Ayiyah zata iya saka masa ciwon kai da surutun ta.



*******

*BAYAN KWANA DAYA*
da misalin karfe shadaya ya shirya cikin polo T-shirt black sai wando ash color, kasancewar akwai dan rana yau sai ya sanya facing cap, fess da shi looking handsome sai tashin k'amshin sanyayyar perfume yake na company'n D&G.



Hannun sa duka biyun soke Cikin aljihun ya fice daga gidan, cikin kauyen oguma ya nausa, bai san abinda zai kai shi, sai dai zuciyar sa na mamari da kwadayin zuwa kauyen.....



Bai wani hadu da mutane sosai a tafiyar sa ba sai jefi-jefi, kasancewar yau talata ranar cin kasuwar su ce, yawanci suna kasuwa yayinda wasu ke gona, daidai yazo Kofar gidan da ya ga Hoorain na shara sai ya kasa cigaba da tafiya, kamar an rike kafafun sa, mamakin yake, yadda gaba-daya ya fara sauyawa daga ainahin HAMDAN MALEEK BUMSA zuwa wani daban....✍️




_manage Please, yau nayi busy da yawa_...




Share share share fisabilillahπŸ™




NoorEemaan
07082281566



Thank you for reading my novel πŸ₯°



Ga mai son shiga group din Hoorain mai kusumbi ya danna wannan link dinπŸ‘‡
https://chat.whatsapp.com/JxzoG62bUENBfExeNPbRSu
[14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡





*Korafi ya karbu, zan kara yawan typing. Ina godiya sosai masoya da yanda kuka karbi littafin Hoorain, ku cigaba da bin alkamina domin jin yadda labarin zai kaya, wannan littafin ya sha bambam da duk wani Novel nawa, sosai na jima da son yin book din nan tun a Novel din papi, Amma Allah bai nufa ba sai yanzu, Muje zuwa... Noor na muku sahihiyyar kauna*πŸ’•πŸ˜˜



_written by NoorEemaan_✍️



Chapter 1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣



_________Mintuna goma masu kyau ya dauka a tsaye yana murza hannun sa cikin na juna, duk wani tunanin sa ya tsaya cak, zuciya da idanun sa ke son ganin ta, duk yanda ya kai ga son bijirewa zuciyar sa ya kasa... Kamar wanda ake bawa umarnin haka ya ga yana jefa kafar sa cikin gidan, sautin bugun zuciyar sa na sauyawa...


Sai daya tsinci kansa a dan soron gidan su kana hankalin sa ya dawo jikin sa, a ransa ya furta
"Hamdan me hakan kake yi akan mace? Please come back to your normal self, this is not you"...



Cikin sauri ya juya domin barin gidan... saura bai fi taku uku ba yace an ce

"waye nan?"

Runtse rikitattun idanun sa yayi, kana ya ware su ya juyo ga Mami dake tsaye, duk da yanayin mai wuyar fassaruwa da yake ciki ba zaka taba fuskantar hakan a saman fuskar sa ba.


"Me zaka ce kazo yi cikin gidan su?"
Wata zuciyar ta tambaye sa.

A hankali ya tako ya zo gabanta, cikin girmamawa ya dan dukar da kan sa yace

"Good morning ma" domin a lokacin sha biyu saura.



" Good Morning, lafiya dai ko?" Mami ta fada Cikin sakin fuska, a ranta tana mamakin Meye kawo shi gidan su?


Ta bangaren hamdan ma ya dan yi mamakin jin Mami tayi Hausa, kasancewar kallo daya mutum zai mata ya gane cewa ita din Ζ™abilar igala ce, amma bai nuna ko alama ba.


Kamar yadda ya saba yake kuma dabi'a a gareshi ya buΙ—e bakin sa kamar bayason magana yace "nazo ganin ta ne"
ya ji ya fadi maganar da bai san ta ina ya fito ba.
A ransa yana fatan kada ta kara masa wata tambayar, domin wanna karon bai da wata sauran amsa.

Dariya ya bawa Mami, amma bata yi ba, ta maimaita abinda ya fada " nazo ganin ta ne" ta lura kamar bai da son yawan magana,
"shigo daga ciki" Mami tace yana yin gaba, ta san cewa bazai cuce su ba, domin yanayin sa bai yi kama dana mugu ba, duk da ance mugu bai da kama. ga agogon soja dake hannunsa wanda ya tabbatar mata da cewa yana daga cikin sojojin da Allah ya aiko suka kawo musu karshen azzaluman yan ta'addan nan.


****

Da kallo Hoorain dake zaune kan yagagiyyar tabarman su ta bi su da kallo, hannunta cikin sakin masara da man ja Sai yaji... Kasa hadiye na bakin ta yi sakamakon ganin Mami da wani Balarabe a tunanin ta sun shigo...
Da kallo ta bisu, mamaki fal fuskar ta, cikin Yaren Igala tace Mami tace "Hoorain wajen ki yazo"
Duk da tayi mamakin abinda Mami tace amma bata nuna ba, cikin ladabi tace

"toh Mami".

Daga haka Mami ta shige daki abun ta.

Sauke idanun ta kasa tayi, cikin rashin sanin abinyi ta cigaba da taunan abincin ta a hankali...


*HAMDAN*
Tsurawa k'ananan labb'an ta masu kala biyu yayi, wanda ya kasance pink sai zagayen baki kamar ta zana da eye- pencil sai dai ba haka bane, naturally haka lips din ta yake...

Yanda take taunan yafi komai tafiya da shi, idanunsa ya kai kan sakin masara da yayi fari kamar ma ba a sa masa manja ba, alamun bai ji ba.

Ya kasa yarda cewa mutum ke cin irin wanna abincin da a wajen shi sai dai ya kira shi guba, domin a tunanin sa zai iya sa mutum rashin lafiya, saboda ganin da yake wa abincin yanzu wani tashi zuciyar sa ke yi, dauke idanun sa daga kan abincin yayi, a fakaice ya kalli tsakar gidan su, a rayuwa bai taba ganin gida daya lalace irin wannan bare har ya shiga, amma saboda bawa abinda zuciyar sa ke so yau gashi a cikin gidan da a wajen shi gwara kwalta a kan sa.



"Tsawon wani lokaci suka dauka cikin irin wanna gidan? Allahu Akbar and they survive" Ya fada a ransa, yana jin wata matsananciyar tausayin su, dama akwai mutane da suke cikin zallan talauci haka?
Bayan ga masu hali bila adadin suna facaka da kudi kan abu mara muhimmanci.....

Ajiyar zuciya amma boyayye ya saki a Lokacin da ya ji melody voice din ta.

"Good afternoon, Please sit" tace tana nuna masa tabarman bayan ta dan matsa.


Kallon tabarman daya yayyage ga jan kasa duk ya cika shi, kamar mai tsoron kar wani abu ya cije shi haka ya fara kokarin zama, cikin sauri Hoorain ta zabe dankwalin atamfar kanta daya sha ruwa ya kode ta warware kan tabarman, ta kuma yi hakan ne gudun kada wandon shi ya bace, kana ta yafa wani bakin dankwali dake gefen ta, wanda ya dawo ruwan kasa-kasa saboda tsabagen d'ad'ewa.

Ajiyar zuciya ya sauke, kana ya zauna, amma kafafunsa na kasa, bai cire takalman sa ba.

"Bismillah"
tace tana dan turo masa kwandon samiran da duk jikin sa ya gama tsatsa.



Can kasan makoshi ya girgiza kai hadi da furta "Thanks" kasa cigaba da ci tayi, sai wasa take da hannun ta cikin abincin.


Cikin tausaya wa ya kalle ta, a ransa yake fadin abincin ba dadi shiyasa ta kasa ci, shi a hakan ma ya ga kokarin ta, domin a cewar sa ko dabbobi aka bawa bazasu iya ci ba, zuciyar sa ce ta kasa hakuri ya ce "ba dad'i ko" da dan mamaki ta kalle shi jin yana Hausa, amma bata ce komai ba, cikin murmushi daya taho da cikowar kwalla tayi, wanda ya lo6a one side dimple dinta tace "tun ina shekara biyu na fara cin irin wanna cimmar, kaga ya zame min jiki, kawai nayi loosing apatite ne"


Lumshe rikitattun idanun sa yayi kana ya bude su, Muryar ta na matukar tasiri a jikin sa...

Haka suka yi zaman kurame babu wanda ya Ζ™ara magana, can Hoorain tace "kana cikin sojas da kuka taimaki kauyen mu ko?"


Jinjina mata kai yayi, ba tare da yace komai ba, murmushi tayi tace "mun gode kwarai, may Allah reward You guys"

"Ameen" ya amsa slowly.
Daga nan babu wanda ya kara magana cikin su, kallon hunch back din ta yayi, abinda yake ji a labarai yau gashi ya gani a bayan Hoorain, tausayi take bashi sosai da wanna abu dake bayan ta, can ya kalle ta yace


"I shall take my leave, take care"


"Toh sai anjima" hoorain replied tana kallon sa har ya fice...

Haka kawai taji ya burge ta, baya ga Mami da Aramani shine mutum na uku da ya zo kusa da ita haka ba tare da kyama ba, komai na shi ya burgeta, musamman tsananin tsafta da iya gayun sa, ajiyar zuciya ta sauke kana ta kalli dakin da Mami take, cikin siririyar Muryar ta, sannan a ladabce tace


"Mami! Bacci kika yi?"



"A'a omami" (a'a diyata) Mami ta fada tana fitowa.


"Ya tafi kenan?"


"Eh Mami, yana da kirki sosai, amma baya son magana" ta fada cikin yanayi mai kama da shagwa6a...



Murmushi Mami tayi ganin Hoorain ta sake sabanin dazu da take zaune shiru, tana son yarta, burinta ta kasance cikin farinciki a kullum, shiyasa a kowacce sallar ta Hoorain take Fara yi wa addu'a.



"Dama kin san shi ne?" Mami ta jefa mata tambayar.


"A'a faa, yana dai cikin soldiers da suka yi mana maganin yan ta'addan nan"


Jinjina kai Mami tayi cikin gamsuwa, lallai wannan yaro da abin mamaki yake, ta san dai dan mai kudi ne, domin yanayin sa ya nuna hakan baro-baro, amma gashi yazo har gidan su wajen Hoorain wanda Bata gama sanin dalilin zuwan sa ba,amma ko ma menene dai zai bayyana, domin yaron ya kwanta mata a rai..
Haka suka cigaba da hirar su gwanin sha'awa.


*BUKAVU BARRACKS KANO*
Zaune commander yake a tsararren office din sa, wayar sa ce ta dauki kara, hannu ya kai ya dauka hadi kara wa a kunne su....

Daga can bangaren field Marshal ke tambayar sa " wai har yanzu Captain Hamdan Maleek Bumsa bai dawo ba, domin na kira wayar sa bata shiga ba".


Nan commander ya sanar da shi cewa "Yes sir! har yanzu dai"

marshal yace "Yakamata ya dawo hakan nan kusan sati kenan, sunyi namijin kokari a aikin da suka gudanar, gashi ya yi shekara biyar a matsayin Captain, matsayi za a kara masa, and we can't do nothing tunda baya nan"



"Haka ne sir! Nima zan gwada kiran layin sa, idan ya shiga zan sanar da shi lalle ya dawo cikin gaggawa" cewar commander, nan suka yi sallama da Marshal.


*********


*Kogi state*
(Kauyen Oguma)
Kwance yake a kasa ba amma duka ba, domin hannu da kafafunsa ba a kasa suke ba, cike da jarumta yake yin kasa da sama, a turanci dai ana kira shi da presa up, ya riga daya saba kullum sai yayi wannan excerise din yake jin dadi...



Cigaba da yayin excerise din yayi, fuskar Hoorain na mai yawo ciki idanun sa, komai na yarinyar na yayi masa, a ganin farko ya kamu da son ta, Abinda turawa ke kira love at first sight .

Yana jin zai iya rayuwa da ita a ko wani yanayi da ko wani hali, ta samu matsayi mai yawa cikin zuciyar sa, baya ga tsananin son da yake mata, yana mata kallon kanwa, wanda bai da shi, hakika ta samu matsayi wanda babu wata mace data taba samun irin shi a zuciyar sa...

Ammi ce ta fado masa, ya san cewa matukar ta samu labarin cewa yayi masoyiya zata yi farin ciki, domin abinda ta dade tana so kenan, ko kusa bai taba kawowa zai fada so mai zafin gaske haka ba, abinda yake ji a kan Hoorain bazai fadu a baki ba. Amma babu wanda zai gane hakan saboda dakiya, jarumta, da zurfin cikin sa...


Ya jima cikin tunanin Hoorain din sa, kana ya mike, ya nufa toilet domin yin wanka, saboda a kage yake da son ganin ta, tun yana mamakin sauyawar halayen sa har ya daina, Hoorain has totally changed him from Captain Hamdan to another new person duk da ba sa wani hira, amma ganin ta kusa da shi na sanya zuciyar sa yin sanyi...




_nayi alkawari gobe
in Sha Allah zan yi update_



Share
Share
Share
Please as much as you canπŸ™



NoorEemaan
07082281566


Thank you for reading hoorain the hunch back girl.πŸ™πŸ₯°


*(Not edited)*
[14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡




_written by NoorEemaan_πŸ“šβœοΈ




ELEGANT ONLINE WRITER'S πŸ“šβœοΈ




Chapter 1️⃣7️⃣⏩1️⃣8️⃣


Daga can bangaren Ammi kuwa a zafafe ta daga wayar domin sauke masu tsananin fushin da take dashi, saboda kullum cikin damuwa take, musamman data daina samun sa k'watak'wata a waya... Sabanin fadan da take da niyyar masa, sai jikin ta yayi laushi sak'amak'on muryar sa da ta ji yayi kasa sosai ya furta

"my first love".

Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tana jin fushin da take da shi na raguwa, sosai take son Hamdan, amma ta rasa meka damun sa gaba-daya ya sauya mata, kamar ba zakin sojan ta ba, duk da babu gazawa a muryar sa amma ta66as akwai canje-canje a tare da shi.


"Captain dina, ka Ι—auke ni matsayin ammin ka kuma first love dinka kamar yadda kake fada?"


"Of course yes Ammi" ya fada yana mikewa zaune, domin da kamar bacin rai Hadi da damuwa a tattare da Muryar ta.


"Then why kake boye mun damuwar ka, ko ban cancanci sani ba?".


"A'a Ammi, kin fi kowa dacewa ki sani" ya fada cikin wata murya daya kashewa Ammi jiki.


Amma ta daure tace "in hakane then tell me, me kake a kogi bayan ba dangi uwa bare na uba a can, meyasa bazaka dawo ba, na kasa gane maka fa, You re behaving strange these days, ko so kake ka samun damuwa a zuciya, baka bani ciwon kai kana yaro ba sai yanzu daka mallaki hankalin ka Hamdan? answer me am taking to you" wanna karon a dan tsawace tayi maganar domin she can't take it anymore.



A Zuciyar sa yaji wani daci sosai, idanun sa ya runtse da karfi, abu ne wanda kowa na gidan su ya sani, matuΖ™ar Ammi ta kira real name dinsa toh lallai fushi take da shi, boyayyen ajiyar zuciya ya sauke kana cikin Muryar sa da yayi bala'in yin kasa yace "Am sorry Ammi, please karki yi fushi dani, You know I have you first love, bana kaunar ganin fushin ki..."



Numfashi ya dan sauke yana datse jajayen labb'an sa da jerarrun hak'oransa sannan ya cigaba da cewa "as soon as na dawo zan baki labari mai dadi wanda kika jima da muradin jin shi daga bakina"



Sanyin sosai Ammi taji a ranta, fuskar ta dauke da murmushi.

Hamdan ya dan yi gyaran murya yace " pray for me, ki sa ni a addu'ar ki, Allah ya bani ikon yin abinda ke raina, kinji first love?"


"My handsome son, a kullum ina maka, sannan zan dage da tashin dare domin yi maka addu'a, Allah ya tsare mun kai a duk inda kake, ya baka Sa'a, Please do take care of yourself for Ammi ok, i love You"



"I love you too first love" yayi mata reply.


"Yawwa nace yaushe zaka dawo ne?"


Shiru yayi na yan Mintuna sannan yace
"Ammi ban sani ba, but a kodayaushe zaki iya gani na, just pray for your son"


Jikin Ammi ya fara sanyi da lamarin Hamdan. Definitely something is fishy somewhere, amma bata matsa masa ba, addu'a ta k'ara masa, da haka suka yi sallama.



Ya jima zaune idanun sa a lumshe yana tunani.. can hoton fuskar Hoorain ya mamaye idanunsa, ajiyar zuciya ya sauke kamar ita din ya gani a gabansa, tuno halin daya barta a ciki ne yasa shi mikewa, yayi kewar ta ba kaΙ—an ba, musamman zazzak'ar Muryar ta da murmushin ta dake sanya zuciyar sa yin sanyi, mikewa yayi ya shirya, kana ya nufi cikin kauyen nasu....



*******


Kansa tsaye cikin gidan bakin sa dauke da sallama kasa kasa kamar yadda ya saba, dan tsakar gidan nasu shiru, babu motsin kowa.

Mami data ji Muryar sa kasa_kasa ta fito tana amsa sallamar, cikin girmamawa ya dukar da kansa ya gaishe ta, Mami ta amsa fuskar ta a sake, kana ta warware masa matacciyar tabarman su dake nannad'e sakamakon hakan k'urar jar dake jikin tabarman ya tashi, kawar da kansa gefe yayi, juyowa Mami tayi ta ce "zauna ko, bari na taso Hoorain, tun jiya taki bacci sai dazu na samu baccin ya d'auke ta"


Sabon tausayin ta ne ya kamashi, so yake ya ce wa Mami ta barta tayi bacci amma ya kasa magana saboda miskilancin sa da rashin son maganar sa.



*Hoorain*!
kwance take kan kafita wanda sabagen yanda kafitar ta dade gaba-daya ya cinye, har gwara tudun wani tabarman a kan shi.


Gaban kafitar Mami ta karasa hadi da tattaba Hoorain a hankali, a dan zabure ta farka, ganin Mami yasa ta saki ajiyar zuciya hadi da k'amk'ame hannun ta, cikin kulawa Mami tace

"Hoorain tashi, Hamdan yazo"

Lumshe ido tayi cikin baccin da bai ishe ta ba, amma ta ji sanyi a ranta a dalilin zuwan ya Hamdan dinta.



A hankali ta tashi, bayan ta gyara dankwalin kanta ta nufi waje...ido suka hada tayi masa Murmushi, zura mata ido yayi baya ko kiftawa, wajen da fashashen butar su yake ta nufa, ta zuba ruwa cikin tafin hannun ta ta kuskure bakin ta, sannan ta kara diba ta wanke fuskar ta, tana juyowa suka hada ido, saurin Ι—auke kanta tayi ta zo gefen sa ta zauna.



Cikin siririyar Muryar ta daya dan tsarke da bacci ya kuma bada wani amo na musamman tace
"ya Hamdan! Ina kwana"


Lumshe ido yayi, kana ya ware su a kanta, kasa tayi da kanta, a ranta tana mamakin wanna yawan kallo da yake mata a yau, Hamdan kuwa abubuwa da yawa yake ji a kanta wanda baki bazai iya fada ba, sai dai a bar wa zuciya, ga wani mugun kyau da ya ga ta kara masa a yau, musamman manyan idanun ta da suka kara haske tarrr...


Dankwalinta daya dan zame kadan, wanda ya bawa gashin gaban kanta bayyana. Abin kafita ya gani makale a gashin ta, hannu yasa ya cire hadi da nuna mata sannan ya jefar, kunya taji ya kamata.

Haka suka yi zaman kurame a wajen, daman yawanci ita ke magana, amma damuwa dake manne a ranta yasa ta kasa magana a Yau din.


Bayan azahar sai ga Aramani yazo, Hoorain ta ji dadin ganinsa, tana son Aramani domin Allah, tana jin shi kamar wan ta.

Hira ya dinga janta da shi, abin ka da mai barkwanci nan da nan Hoorain ta Ι—an saki jiki tana murmushi.


Hamdan yaji dadi ganin babe dinsa ta fara walwala sak'amak'on labaran barkwanci da Aramani ke bata, although Yana Jin kishin Aramani a ransa duk da yasan babu komai a tsakanin su, amma tsananin son da yake mata yasa baya kaunar ko wani da namiji ya rabe ta, amma bashi da zabi da ya wuce ta kasance cikin farinciki.


Sai bayan la'asar aramani ya tafi, duk da ba a samu cikon na bakwai ba, domin babu wanda ya yarda zai kara bin su, saboda tsananin hadarin duniyar mutuwa.



Sai bayan magriba Hamdan ya yafi cike da kewar Hoorain.
haka ma ta bangaren Hoorain sam bata ji dadin tafiyar sa ba, ga damuwar da take ciki ya dawo sabo saboda gobe ne su Aramani zasu tafi, a ranar bacci ya kauracewa idanun ta, kuka mara sauti ta dinga yi...



WASHEGARI

*5:55am*
Zaune yake kan sallayar dakin da yake kwana, ya gama addu'o'in sa da azkhar. Yayi shiru tunani mabambamta na zagaye brain din sa wanda yasa jijiyoyin kansa suka fito, wayar sa ya janyo ya rubuta wa Ammi text kamar haka...



_saba'ul khair ya Ammi, ki min addu'a kinji yau ne zamu_........
sai kuma ya kasa karasa wa ya tura mata. Dalili kuwa shine bayason ta shiga damuwa, infact ya yi imanin cewa idan tasan inda zai je bazata taba amincewa.



Kara rubuta mata yayi

_i love You so much Ammi, you re the sweetest mum ever, ki yafe min if I have ever offended you in any way_


Ganin massage din ya shiga, sai ya kashe wayar da sauran 2percent ya jefa cikin jakar sa irin ta sojoji da ya so da ita, toilet ya shiga yayi wanka hadi da brush wanda ya dauk'esa Mintuna ashirin sannan ya fito, goge jikin sa yayi da mini towel, ya shafa mai hadi da fesa body spray, wasu bakakken kaya riga da wando body hug na kamfanin DOLCE AND GABBANA (D&G) ya sanya, hair cream dinsa na kamfanin XPEL ya shafa bayan ya cire dan rubber band din, ya jefar, tajewa yayi, sannan ya kara kamawa da sabon rubber banda kamar yadda ya saba a kasan keyar sa, jelar har wuyan sa.

Wani turare mai sanyin k'amshin na kamfanin Christian Dior ya fesa sama-sama, sannan ya rufe gidan ya fito...cikin tafiyar sa ta sojojin masu ji da jarumta hadi da cikakken lafiya ya fara lafiya.


Kusan a tare shi da dan baiwa suka zo kofar gidan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment