Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hadi da saka matacciyar hijab dinta da shi kadai ta mallaka ta toshe bakin ta dashi ....


Muryar ASHIMI dan baiwa daya cigaba da tashi ya sa wurin ya dawo so slient kamar ba hallitu a wajen duk suka kasa kunne suna sauraron sa


"Alhamdulillah! Allah ya nuna min maganin, wanda maganin warakar kusumbi Hoorain yana world of dead (duniyar mutuwa)"



Salati aka kara saki, wasu har da dora hannu a kai.

Ashimi dan baiwa ya cigaba da cewa "world of dead na da matuƙar hatsari fiye da tunanin ku, mugayen Aljanu, mayu masu shawagi da rana hadi da wasu hallitu marasa kyauwu ne suka cika duniyar mutuwa, duk mun san cewa babu wanda ya taɓa zuwa ko yin hanyar duniyar mutuwa. Toh anan maganin warkar da kusumbin Hoorain yake cikin wata kwarya a karkashin bishiyar kuka..."


Shiru ya dan yi yana bin mutane da kallo kana ya cigaba da cewa "zaratan samari bakwai ne zasu yi wanna tafiyar zuwa duniyar mutuwa domin dauko kwaryan nan, ba karya zaku hadu da miyagun hallitu da zasu yaudare ku, domin da siffa mai kyau zasu zo muku amma kada ku yarda da su daidai da ƙwayar zarrah, ku karfafa zuciyar ku, ku rike addu'a, ga wadanda suka shirya wannan tafiya zan baku wasu addu'o'i domin kare kanku, Hoorain na da kyakkyawar zuciya, ga duk wanda ya ga zai taimaka mata Allah ya biya shi, jibi ne tafiyar, na barku cikin aminci" yana kaiwa nan ya juya cikin tafiyar sa ta sauri_sauri ya bar wajen...



*HOORAIN*
Kamar wacce aka datsa haka ta cigaba da tsayawa idanunta kurrr kan dan baiwa Ashimi har ya tafi ta kasa kyafta idanun ta a wajen da ya tsaya, tsananin shock yasa ta kasa motsi, sai ruwan hawaye dake bulbulowa daga idanunta kamar an kunna famfo...



*HAMDAN*
Kallo daya zaka masa ka hango tsantsar damuwa daga cikin blue eyes dinsa daya Sanja launi, gaba-daya ransa a bace yake, duk da kasancewa mushkaf ba a jinsin bil'adama yake amma wani mugun kishi ke caccak'ar zuciyar sa game da shi, tausayin babe din sa ya kara yawaita a zuciyar sa.



Mutane ne suka fara watsewa kowa da abinda yake cewa, cikin sauri Hoorain ta fada cikin gidan tana kara sakin kuka mai tsuma zuciya, Mami ta biyo bayanta, kana Hamdan ya mara musu baya... hannunsu zube cikin aljihun wandon sa ya kafe ta da idanun sa masu ɗauke da tausayi, tsananin so, zallan kishi, hadi da bacin rai amma bai ce komai ba.



Abin tausayi haka Mami ta zube gaban Hoorain hadi da dafa ta, cikin sauri ta dago, ganin Mami ce yasa ta fada jikin ta hadi da kiran "Mami mie" cikin kwarewar zuciya.



Hugging dinta back Mami tayi tana rarrashin ta, kana tace "Hoorain haka Allah ya ƙaddara Maki, amma har da laifina ciki domin tabbas kina yar karama ban fiye son saka Miki kaya ba, ki yafe....."



"A'a A'a Mami, wallahi bazaki taba Zama mai laifi a gareni ba, ke ce duniya ta, ke kika kila da Ni har na kai iyanzu, Mami kada ki ci komai dan Allah, ina son ki Mami mie"



Kuka Mami ta sa, kauna da tausayin tilon yarta na kara mamaye zuciyar ta.

Hamdan kuwa bai taba ganin abinda ya ta6a zuciyar sa hadi da bashi tausayi kamar Hoorain ba, karamar innocent girl da take cikin K'addarar rayuwa.



Kasa jurar kallonsu yayi ya fita waje ya samu wani benchi na karfe a dan nesa da gidan su Hoorain ya zauna hadi da nausa hannunsa cikin sumar kansa yana mai rufe idanun sa.



****************


Da misalin K'arfe biyar din yamma, sai ga Aramani tare da wasu samari biyar sun zo gidan su Hoorain.

Abin mamaki suka sanar cewa zasu je duniyar mutuwa domin dauko maganin nan da zai warkar da kusumbin ta, sun kuma sanar da su cewa zasu Yi wannan sadaukarwan domin son fisabilillah da suke wa Hoorain, hakika ta sha gwagwarmayar rayuwa da tarin kalubale, ya kamata zuwa yanzu ta ji dadi ko yaya ne. Suka kara da cewa suna saka ran in Sha Allah su samu cikon na Bakwai din zuwa gobe tunda jibi ne tafiyar.



Mami tsabagen al'ajabi yasa ta kasa magana. Hoorain kuwa kuka ta samu musu tana cewa "Aramani, Danjuma, salihu, yakubu, oshimana, Abu, dan Allah karku je, bana so ku mutu, karku jefa rayuwar ku cikin hadari saboda Ni, ina farinciki da godewa Allah a yanda nake, dan Allah bazan iya jurar rasa ku baaaaaa" ta ja karshen maganar sakamakon mugun kukan daya kufce mata.



"Tafiya babu fashi Hoorain yar'uwar mu, matukar kana son mutum zaka iya sadaukarwa mai girma domin shi, ki mana addu'a kin ji ko? In Sha Allah zaki mike kina tafiya kan kafafunki kamar kowa"


samarin suka hada baki wurin fadin haka, daga nan suka fice a gidan.



****


A ranar kam har dare Hoorain idanun ta jike suke da ruwan hawaye, ta kasa daina kukan, Mami kallon ta kawai take cikin tausayawa domin babu wani karfin guiwa a tare da ita, jikin ta gaba-daya ya mutu, a ranar sun manta sunan abinda ake cewa *YUNWA* saboda tsananin damuwa daya cika zuciyar su, ko lokacin da Hamdan ya tafi ma basu sani ba.





Ta bangaren yan kauyen Oguma kuwa, ko wani gida da ko wani majalisa hirar Hoorain ke tashi kowa na fadin albarkacin bakin sa.


*WASHEGARI*


*HAMDAN*

Tun ranar da suka gama chat da Imran bai kara kunna wayar ba sai yanzu, kallon percentage din wayar yayi ga sauran masa 10% a hakan ma ya ga kokarin ta, domin iPhone baya mugun rikon chargi, gashi tunda yazo kogi bai yi mata chargi ba.



Contact list ya shiga, inda ya tsayar da idanun sa kan number'n Ammi, wata karfafar ajiyar zuciya ya sauke, kana ya danna number'n ta hadi da kara wayar a kunnen sa yan sauraron ringing din da yake...







*Mun fara shigowa cikin labarin, i swear basan yadda zan kwakwanta zafin book din nan ba. Abubuwan ciki na daban ne, just continuing following my pen, sahihiyyar kauna Noor ke wa masoyan ta na fili dana boye*


*Naso kara yawan typing amma banda a enough charge*


*_guys Meye ra'ayinku kan page din yau_?*





*Two free page left karku ji dif*🤸💃



NoorEemaan
07082281566



Thank you for reading my story
🍇#Hoorain the hunch back girl🍓



Share
Share
share

Please🙏



9:07
26/5 2022
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇




_written by NoorEemaan_ 📚✍️




Chapter 1️⃣9️⃣⏩2️⃣0️⃣


Hannun Mami ta rungume gam tana cigaba da kukan, ga muryar ta ya fara dashewa... haka ta cigaba da kallon su har ta daina ganin su.



Mami ta kamata da k'yar domin ita ma babu karfi a jikin ta suka nufi dan gidan su.


Mami ta shigar da ita daki, Hoorain ta sulale kan yoluluwar kafitar su ta kwanta, babu jimawa wani zafaffan zazzab'i ya rufe ta, jikinta ya dau zafi, hak'oranta na had'ewa dana juna yayinda jikinta ke rawa kamar mazari...

Hankali tashe Mami ta dauko yan jike-jike irin na su na kauyen ta bata ta sha, sannan ta dauki zanin ta ta rufa mata, bayan Mintuna talatin wani bacci mara dadi ya dauke ta cike da mafarkin su Hamdan.



*********



*NASARAWA GRA SULTAN ROAD*
_10:00am_

A dai-dai lokacin Ammi ta tashi daga bacci, domin raba dare tayi tana ibada, bayan tayi sallar asuba kuma bacci ya dauke ta, sai yanzu ta tashi.



Mikewa tayi tana dan yamutsa fuska abinka da jikin tsufa, toilet ta nufa tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin had'add'e kuma tsad'add'en atamfar *English gold* ta shafa humra da wasu turaren ta masu dadin k'amshi.
Ammi macece mai son gayu, tsafta, hadi da k'amshi, a takaice dai a wurin ta y'ay'an ta suka gado hakan.


Bakin gado ta zauna, ta latsa wayar ta, inbox dinta ta gani ya nuna an turo message, hakan yasa ta shiga, ganin number'n Hamdan ne yasa ta danna da sauri...



Sau uku ta maimaita abinda ya rubuto mata, jikin ta yayi sanyi sosai kalaman sa sun ratsa zuciyar ta, tausayin sa da son sa sosai taji ya kara shigar ta har hakan yasa wasu hawaye Masu dumi suka biyo kuncin ta, hannun ta daga sama a fili tace "ya Allah ka fini sanin abinda yarona ke yi, ya Allah ka bashi Sa'a, ka zaba masa abinda yake mafi alkhairi, ka tsare shi da tsarewar ka ya Allah, ka kiyaye shi da kiyayewar ka, mugun ji, mugun gani ya Allah ka raba shi da su, sharrin mutum sharrin Aljani ya Allah ya kiyaye shi, Allah ka dawo min dashi cikin koshin lafiya" ta shafa addu'ar wasu hawayen na kara zubo mata.



"Falmata! Falmata!! Wai baccin ne yar yanzu? inci dai Lafiya ko?" Ayiyah data zo bakin kofar yanzu ta fada.



Cikin gaggawa Ammi ta share hawayenta, sannan ta dai-dai ta Muryar ta ce
"gani nan Ayiyah" ta fada tana nufar bakin kofar, ta bude, ta wani dogon corridor ta bi sai ga ta a babban falon ta wanda ya kasance kamar general falo domin duk a nan suke jin abincin.


Ayiyah ta gani zaune ta kurawa tv ido, kamar idanun ta zasu fado ciki, jin takun tafiyar Ammi yasa ta waiwayo, ta zubawa Ammi idanunta da ta rambada musu kwalli har yaso yayi yawa, tace "Falmata! wanna wani irin Bacci mai nauyi kika yi haka? Hankalina ya tashi ba shiri na kwashi kafafuna nace bari na dubo ko lafiya, yo Allah na tuba kana zaune da mutum yanzu, daya shiga daki babu jimawa sai dai ka ji ya zarce lahira, su Anas ma sun tambaya nace baki tashi ba, har sun wuce aiki domin sun ce basa son tashin ki"



Murmushin k'arfin hali Ammi tayi a ranta tana jinjina surutun Ayiyah ko full stop babu, rissinawa tayi kamar yadda ta saba ta gaishe da Ayiyah, cikin kulawa Ayiyah ta amsa tana sa mata albarka, domin ta kasance mace mai son a girmama ta, sannan tana yawan yabon Ammi a ranta domin duk da danta Wanda shine mijin Ammi ya rasu, amma hakan bai sa ta fasa girmama ta ba.



"Kiyi karin kumallo ko? yau kin makara... Nace wai ya wanna dan fadin rai da miskilancin tsiya, ince kun yi waya mara kirki ko neman kakar sa baya yi"



Danne damuwarta Ammi tayi sannan tace "eh Ayiyah yana lafiya, yace ma ce na gaishe ki" ta karasa domin faranta ran Ayiyah.



Ta kuwa washe hakoran ta tace "Masha Allah, dan k'wal uba yau ya ga daman tambayata kenan" ta karasa tana sakin dariya irin nasu na tsofaffi.


Ammi bata kuma cewa komai ba ta nufi kan dining table, tea da Irish kaɗai ta ji domin sam bata jin yunwa, haka ta wuni curr jikin ta ba dadi, Mintuna kadan sai tayi wa Hamdan addu'a a ranta.



***********




*KOGI STATE*

Sunyi tafiya mai nisan awannin goma kana suka shigo *land of death (duniyar mutuwa)*.
Ko gida daya babu bare ka saka ran ganin wata hallita, sai ciyaye hadi da bishiyoyi, kasan wajen tsaf kamar akwai masu sharewa kullum, da shigar su duniyar mutuwa komai ya sauya, ita kanta duniyar abar tsora ce ga duk wanda ya kalle ta, sai kukan wasu abubuwa kamar na tsuntsaye marasa dadin amo ke tashi.



Yamma sosai yayi domin duhun almuru ya fara, sam babu gazawa a tare da su duk da dare ya fara amma basu fasa tafiya ba, bare Hamdan sam babu alamar gazawa a fuskar sa bare gangan jikinsa su gaji.

Da sun daidaita lokacin sallah sai suyi taimama su gabatar da sallar su.
Ga yunwa ga k'ishirwa daya fara sanyayyar wa su Aramani jiki, amma haka suka daure, domin babu ruwa balle ka saka rai da samun abincin.

Har taran dare suna tafiya, wanda zuwa wannan lokacin Danjuma da Ya fi kowa gajiya cikin su ya tsaya, hakan yasa sauran dakatawa fuskar su cike da karin bayani.



Cikin Muryar galabaita yace "wallahi na gaji, har jiri ya fara diba na, dan Allah ku bari da asuba mu cigaba da tafiya, bazan iya ba, yunwa sosai nake ji"


Cikin tausaya wa duk suka kalle shi, ko wa yasan Danjuma baya wasa da cikin sa, Hamdan dake jikin su ya ɗan kalli Danjuma sannan ya motsa bakin sa a hankali yace
"mu huta zuwa asuba sai mu cigaba" yana fadi hakan ne domin saukaka musu, dan ta shine bai gaji ba, kuma baya jin yunwa ko dan bai damu da abinci bane...
Tabbas yasan akwai sauran lafiya sosai a gaban su, tunda ko alamar bishiyar kuka basu gani ba.

Gwara su huta domin kada karfin su ya ƙare, ya aiyana hakan a ranshi, sannan ya cire takalmin kafar sa ya zauna a kai yana mai lumshe idanun sa.



Su Aramani ma zama suka yi, bayan sun ajiye addinan su a gefen su, aramani Sarkin barkwanci kuwa ya dasa hira, nan suka saka bak'i aka cigaba da hira.



Hamdan kuwa sam bai san abinda suke cewa ba, domin ya zurfafa kogin tunanin Hoorain din sa, a ransa yana addu'ar Allah basu nasara....Tuno yanayin daya barta dazu ya sa zuciyar sa sosuwa, kukan da take yi hadi da kiran sunan su a lokacin da suka fara tafiya sai amsa kuwwa take a kunnen sa tamkar yanzu ne take yi, iska mai zafi ya furzar daga bakin sa, yana fatan ace ta daina kukan yanzu.



Sai sha biyun dare su aramani suka hakura da hiran da suke, Sakamakon baccin daya fara cika idanunsu, nan duk suka kwanta a kasa babu jimawa bacci ya dauke su...


Hamdan karewa wajen kallo yayi baya iya ganin ko tafin hannunsa ne, sakamakon tsananin duhu daya kara mamaye wajen, ga wasu Kuka iri daban-daban marasa daɗin amo daya cika kunne sa...


Da misalin ƙarfe dayan dare wani irin dariya mai matuƙar tsorata rai hadi da sanya Mutum cikin rudu da tashin hankali ne ya cika kunnen su tamkar zai fasa musu dodon kunne...


A firgice su Aramani suka farka daga nannauyyan baccin daya d'auke su, a tsorace suka fara kalle-kalle amma basu ga komai ba, sai can suka kalli sama inda suka ga wasu hallita masu tsorata ruhi suna shawagi a sararin samaniya tamkar suna tseren jirage yayinda kawunan su ke kallon kasa...


Hamdan ya bude idanun sa ya kalli saman sannan ya dawo da kansa kasa, sam babu wani tsoro a tare dashi, domin a cewarsa bai ga amfanin tsoro ba, addu'a kadai ce babban muk'amin mumuni.


Addu'a ya fara a ransa, cike da nutsuwa, a tsorace Danjuma da yafi kowa tsorata ya dawo gefen sa ya rakube, kallon sa hamdan yayi ya dauke kansa, gaba-daya Danjuma ya jike da gumi barin ma fuskar sa.



"Kuyi addu'a kada ku bari tsoro yayi tasiri a zuciyar ku"

ya fada hankali a kwance cikin k'asaitacciyar Muryar sa.


Nan suka samu sukunin fara addu'a, Danjuma saboda sabar tsoratan da yayi har addu'an shiga banɗaki ya dinga karantowa da karfi cikin fitar hayyaci, abin so Funny da a ce suna cikin yanayin mai kyau babu abinda zai hana su Aramani dariya.


Bayan kamar mintuna arba'in dif suka ji dariyar ya daina kana wadannan addu'an suka bace. Still hakan bai hana su shiru ba, addu'a suka cigaba da yi...

Babu wanda ya ƙara gingin komawa Bacci cikin su, har asuba ta gabato suka yi taimama, Hamdan ya ja su sallah, bayan sun iddar suka cigaba da tafiya domin haske ya ɗan fara bayyana kadan-kadan.




HOORAIN!
Zaune take ta kurawa waje daya ido bata ko kiftawa yayinda hawaye ke sauka a k'yak'yawar fuskar ta, da alama ta zurfafa a kogin tunani.

Ammi data fito a sanyayye ta zauna kusa da ita, sannan ta ɗora hannun ta kan kafad'ar Hoorain trying to comfort her, Wani sabon kuka Hoorain ta fashe da shi tana shigewa jikin Mami gaba-daya...



"Ya isa Hoorain! kuka baya magani, addu'a zamu dinga musu kinji"



Cikin Muryar kuka tace "Mami ina tsoro ne, banason wani abu ya same su, a wani hali suke ciki oho? Na san ko abinci basu ci ba mami, ga ya Hamdan bai saba da wuya ba amma saboda ni yasa kan sa a hadari, ina tausaya musu Mami, fatana su dawo cikin koshin lafiya bana son rasa masoyan asali masu nagarta kamar su mamiiiiiiiii" ta ja sunan cikin kuka.


Bubbuga bayanta Mami ta dinga yi tana rarrashen ta kan tayi shiru. Ta b'angaren Mami ma tana cikin damuwa kawai dannewa take a zuciyar ta.




*BUKAVU BARRACKS KANO*


Cikin yanayin mai nuni da fushi FIELD MARSHAL ke wa commander magana kan rashin dawowar Hamdan wanda ya saba ka'ida da doka.


A tausashe commander'n Wanda ya kasance dan kabilar Nupe ya dinga bashi hakuri hadi da tausar sa cewa jiya ya ce gidan su dake Nasarawa GRA ya kuma tattauna da Ammi inda tace a kara masa hakuri soon zai dawo, domin yanayin ta ya nuna cewa akwai wani Abu a kasa kan rashin dawowar Hamdan din.



"Zan kara masa wasu kwanaki matukar bai dawo ba, he will be punished, domin ya saɓa dokar aiki" Marshal ya fada yana katse wayar sa, duk da kasancewar yana son Hamdan domin Allah ya had'a jininsu, amma baya so sam a dinga wasa da aiki...



Commander numfashi ya sauke yana son gano menene ya hana Hamdan dawowa, amma ya kasa, domin abu ne wanda kowa ya riga ya sani cewa baya wasa da aikin sa, kara kiran Ammi yayi ya sanar mata abinda Field Marshal yace, kana ya dora da cewa idan ta same shi a waya ta sanar masa, shima zai dinga gwad'a kiran nasa, idan hakan ma bai yu ba sai a aika wasu soldiers din chan kogi a dubo shi.


Da haka suka sallama Ammi tayi masa godiya, jikin ta ya kara sanyi sosai, sam bata so damuwar ta yayi tasiri a kan Hamdan balle har ya kasa samun sukunin zuciya a duk inda yake, hakan yasa take kai zuciyar ta nesa tana masa addu'a.



*DUNIYAR MUTUWA*
(Land of death)


Tun suna tafiyar marmari har gangan jikinsu ya fara gajiya, kafafuna su ya yi tsami, ga yunwa ga ƙishirwa.

Hamdan shine karfin guiwan su, domin ganin babu gazawa a tare da shi yasa suma suke bada himman wurin bin sa, tafiya suke amma ko alama basu zo inda kwaryan maganin kusumbin Hoorain yake ba...


Sai da suka daidaici lokacin magriba yayi sannan suka tsaya domin yin Sallah.



Taimama duk suka yi, amma banda Danjuma dake zaune yana sauke numfashi daidai alamun yunwa na k'walk'walan sa gwanin tausayi.



Bayan sun daidaita tsaho Hamdan ya juyo ya kalleshi, tsaf Danjuma ya gane Meye ma'anar Kallon, marairaicewa yayi yace "zan yi sallah amma bari na huta kaɗan wallahi na gaji" ya karasa kamar numfashin sa zai dauke saboda tsabar yunwa da gajiya.


Hamdan bai ce komai ba ya shiga jansu sallah, Danjuma ya kafe su da ido yana kallon su....Can yaji alamun mutum a gefen sa, a dan firgice ya juyo, wata k'yakk'yawar budurwa ya gani zaune gaf dashi tana sakar masa Murmushi mai sumar da mutum, dan zabura yayi zai mike tayi saurin riko hannunsa, lumshe idanunsa yayi saboda tsananin taushin hannun ta, so yake yayi addu'a amma kamar an sa kwado an rufe mai baki.


Cikin wata murya mai dadin gaske budurwan nan tace "kar ka ji tsorona, naxo taimaka maka ne, kaji" ta karasa da mayaudariyar muryar ta.



Zuciyar Danjuma ta kasu kashi goma, yakasa tsayar da ita wace daya, before he could think of any other thing yaji ta kama hannunsa cikin wani salo ta fara cewa "ka yarda dani, bazan cutar da kai ba, abinci na kawo maka, kasan yunwa kake ji" ta karasa tana mika hannun ta bayan ta take wani bowl mai sheke da lafiyayyen abinci ya bayyana, ta dawo da shi gaban ta hadi da jefan sa da wani kallo mai kona ruwan ƙwaƙwalwar mutum sannan tace

"kaci, idan baka koshi ba zan kara maka kaji" ta fada calmly.


Wani dunk'ulallen yawu Danjuma ya hadiye, yayinda cikinsa yayi kiran ciroma, yunwar da yake ji ta karu sosai, lashe baki yayi, duk da yanda ran sa ya biya da abincin, amma kasan zuciyar sa yana tuno maganar dan baiwa inda yake cewa


_Kamar Yadda na fada zaku gamu da mugayen Aljanu, mayu, Hadi da Wasu hallitu marasa kyau a tafiyar ku da dawowar ku, ina so ku karfafa zuciyar ku, kada ku bari yayi rauni, duk wata yaudara da zasu muku kada ku amince_



Numfashi ya sauke ya kalli su Hamdan dake sallah cike da nutsuwa, da alama basa jin Muryar budurwan, wanda hakan ya bashi mamaki.



"Ka ci ka ji kada yayi sanyi, har ruwa mai sanyaya makoshi zan samo maka" ta fada tana mika masa abincin.
Hannu yasa ya karba Kamar wanda aka umarta, cikin gaggawa ya sa hannun sa cikin bowl din ya dibi abincin fuskar sa kuri kan na budurwan dake ta faman jan hankalin sa cikin salon k'issa da kisisina.



Bakinsa na rawa tsabar yunwa ya kai loma daya bakin sa, ya ma manta bai yi bismillah ba, wani lumshe ido yayi domin tunda yake bai taba cin abinci mai dadi dandano irin wanna ba...



Cikin sauri-sauri ya dinga ci... ya kusan gama cin abincin ya ga budurwan ta dawo wata mummunan hallita mai tsoratarwa, ta jefa masa wani kallo da jajayen idanunta kana ta bace bat.



Wani tashin hankali yaji ya shiga, abincin bakin sa kuwa ya kasa hadiye wa, bowl din hannunsa ma ya bace kamar a mafarki, wani sabon tashin hankali ya shiga, tamkar an yaye masa komai sai yanzu ya dawo cikin hankalinsa...

wata mahaukaciyar murdawa Cikin sa yayi, ya dinga ji kamar ana saka mashi ana huda masa cikinsa, zubewa kasa yayi ya rike wuyan sa da yake jin wata azaba a cikin ta, yayinda kumfa ya dinga bulbulowa daga bakin sa, tsananin azaba ya sa ya dinga shure-shure da kafafun sa.... Daidai lokacin ne su Hamdan suka sallame sallah idanun su ya kai wajen Danjuma da har ya daina shure-shuren, jikinsa ya saki alamun rai yayi halin sa, da wani mugun sauri suka yi kansa hankalin su a matuƙar tashe......




*Alhamdulillah!*
_*A nan na kawo karshen free pages na Hoorain mai kusumbi, ga mai son cigaba da karanta wa ya biya #300 ta wannan asusun 2261488155 Rukayya haruna zenith bank. Marasa bakin kuma zaku iya zuwa pos ku biyani #250 sai ku bawa mai pos #50 kuɗin charges din sa, na yi wanna ragin ne saboda mutanen da suka min maganar cewa basu da banki, idan kun biya sai ku nuna min shaidar biya ta wannan number'n 07082281566*_

_*Yan nijer kuma su min magana domin na gayamasu yanda zasu biya*_.



_*fadin zafin littafin nan bata lokaci ne, ya kunshi abubuwa da dama wanda baku saba gani a novels ba, wandanda suka sanni sun san salon rubutu na, sai dai wannan ya sha bambam, ina kaunar baku dukkanin littafina a kyauta, sai dai tanadin daya yi Hoorain yasa bazan iya sakin sa a free ba, dan haka ku hanzarta biya. Mu hade a original group Habibte's wanda a nan ne zan cigaba da posting ga wandanda suka biya*_



*Shin zaratan samarin nan zasu dawo da ransu*?


*Shin kusumbin Hoorain zai warke ta dawo cikakkiyar mace kamar kowa*?


*Shin akwai sauran kalubale da ƙaddarar rayuwa da zai sake shigowa rayuwar Hoorain*?


*Da sauran wasu tambayoyi dake zuciyar ku, inda duka amsoshin ku na tafe a paid book*.




_Sai na jiku, soyayyar da zasu nuna min kadai shine ku siyi littafin HOORAIN THE HUNCH BACK GIRL_.

_i love all my fans, known and unknown_💖🔐



Thank you for your patronage🙏🥰



NoorEemaan
07082281566





I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment