Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Khadija"


Lawan ya rika salati jikinshi sai karkarwa yakeyi ya bude dakin da Matartashi take kwance,ya ganta a lullube da zani,sai ya tsuguna kusa da ita ya bude fuskar yana kallo tamkar mai bacci haka ya gani innallilahi wa'ina ilayi raji'un kawai yake fada a zuciyara yace"yanzu Khadija kin tafi kin barni,Allahu akabar,zama yayi ya rika yi mata adduoi har a kayi kiran sallah,asubah ya fito ya daura alwala ta nufi masallaci,

Duniya kenan ,haka a kaiwa Khadija suttura a ka kaita gidanta na gaskiya, sai bayan sarakar bakwai ne sannan Alh Bashir yafara shirin tafiya shida iyalinshi a lokacin Ali na Engila karatu,sai waya a kayi masa,gaskiya yaji mutuwar auntyshi sabida yadda jininsu ya hadu da ita in yaje gurin Nene tayi ta hidima dashi ,yana son mace mai hankali da fahinta da tsafta shiyasa suke shiri da ita sosai,nan dai yayi mata adduoi na Neman rahamar Allah

Alh Bashir yayi yayi da Nene tabashi baby su tafi tare da ita ,Ummi ta hadasu tare da yarinyar ta da take goyo a lokacin Fa'iza ta shayar dasu Nene tace Sam a kyale mata ita zata iya kula da ita,babu yadda ya iya haka sukaje asibiti a ka Dora baby kan madarar da ta dace da ita ,sai da ya tabbatar ya ajiye musu komai na bukata sannan suka wuce abuja tare da iyalinshi,

Nene ta dau son duniya ta dorashi kan D'ija bata so ko kuda ya sauka a kanta sabida yadda take rattalinta,lokacin da ta isa shiga makaranta Alh Bashir yazo ya yiwa Nene maganar ya kamata tafara zuwa makaranta ko Ka wai ta bashi yarinyar ya tafi da ita ya hadata da sa'arta Fa'iza ya sakasu a tare,Nene tace Sam bata yadda ba ,ita ya kyale ta,alokacin shi kanshi Lawan yaso Nene ta hakura ta bada D'ijan a tafi da ita abujan amma ganin yadda ta rika fada yasa ,yayi shiru da bakinshi domin dama in Nene tana rigimarta akan "yar tasa yasa yaja bakinshi yayi shiru kawai ya zuba musu ido

Haka Alh Bashir ya kammalawa D'ija komai na makaranta sannan ya wuce ya tafi bayan ya tab star da ya ajiye musu komai Wanda zasu bukata


D'ija ta taso da rigima gami da kwarafniya yarinya mai wayo sosai gata Sam bata barin takwana shiyasa ko a makaranta yara sa'ointa suke shakkarta ,tana da bala'in son girma kamar gyambo shiyasa Sam basa shiri da kawarta Indo sabida itama indo bata son rai ni ko kadan,kullum sai ankawo kararta Nene tayi ta fada tana cewa sun takurawa marainiya kwata kwata D'ija taqi karatu ko taje makarantar ma babu abinda takeyi sai naiman fada ,malamai duk sun San halinta,Lawan in yana mata fada Nene sai tasa kuka tace"yana nuna mata iko dan yaga "yarsa ce"haka yake hakura kawai amma abinda "yartasa takeyi yana bata masa rai


Allah sarki rayuwa,D'ija na da shekara shida a duniya Allah ya karbi ran Lawan sakamakon ciwon ciki farat daya,mutuwar ta girgiza zukatan al'umma mussaman dan uwansa Alh Bashir Nene tayi kuka sosai da sosai ta fawwala wa Allah ikonshi bayan sadakar bakwai nanma Alh Bashir ya rika tausar Nene kan ta bishi abuja ganin yanzu tazama ita daya kadaici zai dameta,Tace Sam bata amunce ba ita dai ya barta a dakinta ai a kwai "yan uwa da abokan arziqi,haka alh Bashir ya tafi badan yaso ba sai Dan gudun bacin ran mahaifiyar tasa


Haka rayuwa tai ta tafiya D'ija Sam taqi karatu yau in taje makaranta gobe baza taje ba ,wannan ne dalilin da yasa makarantar boka suka sallame ta gaba daya Nene tace ta nemi guri ta zauna ai ba dole bane a karatun bokon ,sai na addini,ko isilamiyar ma a makare take zuwa ,shiyasa Sam bata gane karatu sosai.


To a cikin wannan lokacin Ali ya sauka garin bayan ya kammala karatunsa na aikin Soja a kasar Engila


Misalin karfe shida da wani abun ya fito yana sanye da jallabiya ruwan toka tsakar gidan ya rika bi da kallo ganin ko ina a share babu datti ,tsaf iska sai kadawa takeyi gwanin sha'awa ,girgiza kai yayi ,kawai sabida dama tuntuni yasan Nene macace mai bala'in tsafta,kai tsaye kchin ya nufa ,domin bazai iya Wanka da ruwan sanyi ba kasancewar an kwana ana ruwan sama ,duk da yake mutum ne shi Wanda baya kaunar zafi ko kadan hakan bazai sa yasawa jikinshi ruwan sanyi da safiyar nan ba ,Nene na zaune kan kujera "yar tsuguno a kchin din tana joye ruwan zafi cikin fulas ,ya shiga kchin din

Ta dago kai tana kallonshi , yana tsaye jikin kofa sai faman ya mutse fuska yakeyi kamar yadda ya saba


Tace"ka tashi ashe ,ka ganni nan nima sauri nakeyi in kammala hada kayan karin kummalo ,sai muyi wanka domin bana son muyi tafiyar rana"


Gyaran murya yayi kadan ,yace"Nene kin tashi Lafiya"?

Ya share maganar da take masa


"Lafiya kalau na tashi ni kam"
Nene tafada tana juye sauran man kulin da tayi suya da shi cikin wani kwano


Ya mutse fuska yayi yace"kina da ruwan zafi ko"?

"Me zakayi dashi"?
Nene ta tambayeshi kai tsaye
Sabida tasan ba ya wanka da ruwan zafi

"Wanka zanyi dashi naji garin a kwai sanyi"

Cikin mamaki Nene tace"Yau kuma kai ne zaka yi wanka da ruwan zafi,?ashe dai karya ce kawai mutum yace ,shi baya jin sanyi da ko wane lokaci


Babu abinda yace mata ,ya sunkuya yana kokarin daukar fulas din da ta juye ruwan zafin a ciki sabida yaga lokacin da take juyewa

Nene tace"ai ka tsaya na miko maka ko"

Shi dai bai ce mata komai ba ya dauki fulas din zai fita,tace "Muskili kafi mahaukaci ban haushi


Dai-dai bakin kofa suka kusa yin karo da D'ija ta shigo kchin din ,yayi saurin ja da baya yana ai ka mata da banzan kallo fuskarshi a murtuke

D'ija ma tsorata tayi ganinshi ne tsaye a gabanta ,sai jikinta yafara rawa,


Saurin dauke kansa yayi daga kanta ganin kayan da suke jikinta ,riga ce iya gwiwa gashi ta kama mata jiki ,gashin kanta duk a barbaje fatarta luwai luwai , gabanshi ya rika faduwa ,sabida Allah da ya halliceshi yana bala'in son mace mai gashi mai sharp sosai fatar ta tazama kalar coffee ya lura wannan yarinyar duk ta tara abubuwan da yake muradi ga "ya mace duk da take yarinya bata gama cika mace ba amma duk ga alamu nan sun nuna


Ficewa yayi yana jan tsaki ko da wasa bai kara kallon ta ba


D'ija ta sauke ajiyar zuciya tana tabi bayanshi da harara ta zumbura baki , kawai ta wuce ciki gurin Nene

Nene tace "kin tashi ko dube ki don Allah,kai yayi duguzun babu gyara gaki Allah ya baki gashi,amma Sam sai kice baza'a miki kitso ba"
Da zaki daure sai kije gidan Delu tayi miki ko manya ne kafin mu tafi"

D'ija ta karasa kusa da Nene tace"Nifa Nene bana son kitso wallahi kawai ki taje min kamar yadda kike min"

Tabe baki Nene tayi tace"ai shikkenan kanki ne ,ke zai dama, ai


Zumbura baki tayi gami da cewa "Ni dai ki kyale min kai na haka"

Nene tace",to mai kika ji nace dake ne "yannan"?

"Allah ya shiryeki




Tashi tayi daga kan kujerar da take zaune ganin sabon ruwan data daura yana nai man tafasa bandaki tashiga tare da dauko baban bahon dasuke wanka tajuye wa Dija ruwan tace " kimaza kije kiyi kifito kin tsaya surutu da fadi ba,atambayeka ba kinsan in yariga fito zai zo ne ya azzalamana ko"

Fita tayi daga kchin din ta nufi ban daki tana zumbure zumbure na shagwaba




Ita ko Nene kayan Karin nasu ta hau dauka tana shiga dashi daki tana kimtsa gurin da zasu zauna



Ali ne ya fito tsaf dashi cikin wata shadda wacce tai bala,in yi masa kyau ga sumarsa da tayi luf ta kwanta a kansa sai sheki take da ,alama ana kula da ita
Idanunsa sanye da glass yayin da hannunsa yake daure da a gogo as'usuel fuskarsa kamar ko da yaushe ya shigo dakin yana bin ko i na da kallo



Fuska Nene ta hau gyarawa tace " AF ashe kagama kintsawa kaga muma mungama ai ga kayan kari ai yauma mutumin naka nai ma" tafada tana gyara zama itanan lallabashi take karya botsare al halin basugama kintsawaba, bayan hakama tana so tashiga makotan nasu ta yi musu sallama ganin cewar ansaba babu dadi kayi tafiya irin wannan baka sanar da abokan zamanka ba



Ya mutsa fuska yayi yana duba a gogo yace "duba time fa Nene yanzu karfe Tara har da "yan mintoci ummm"! yafada yana kallonta tare da fadin sai yaushe kike so mu kama hanya ne"?


Cikin sauri Nene tace "yanzu nan ai babu abinda zanyi kuma in ba wanka ba Dija nake jira ta gama nashiga naje nai"


Bai CE komai ba ya shige dakin kan kujera ya zauna yana Dada gyara link din hannun rigarsa


Nene kam kunun ta hau zubamasa da zafinsa gashi sai kamshi yake yaji kayan kamshi sannan ta CE "ko in hada ma shayi ne kallonta yai yace "me kika mai da nine wanan dinma is ok yafimin wani shayi ni" amman dan zubamin madara a cikin kunun" ya fada yana dan sakin dariya ciki ciki sabida yasan sai tayi magana


Ai kam harara ta gallamasa tace" baka da hannu ne zuba ma na da kanka ai gatanan kan ta rufe baki Dija tashigo dakin jikinta daure da wani karamin zani kanta duk rabinsa a jike da ruwa kai tsaye jikin siff ta nufa ta na kokarin futu da kayan da za tasa dan tun jiya da daddare ta waresu a gefe


Nene tace "kin fito ba bara nashiga kafin infito sai kihada kayan karin gashinan"


"To Dija tace yayin da take kokarin. Saka kayan ta kwata kwata bata lura da mutum a dakin ba kasan cewar dakin yana da girma Nene kawai tagani wacce take daura da bakin kofa,,


Cire kayan ta tai tana kokarin saka wando bayan tasaka ta jawo rigar tana kokarin sawa rigar taki shiga kasancewar ta mai botora ce irin rigunan ne dogaye odar dubai wanda Alh bashir ne ya kawo musu iri daya ita f'aiza wani zuwa dubai dayayi


Shikam Ali tun lokacin da ta cire kayanta yai saurin dauke kansa abin yana yimasa yawo aka domin dai wata irin hallita ya gani wacce ta bashi mamaki ,,,asace ya kara kallon gefen da take itakam sai kici kicin sa, rigar take takasa gano daga inda rigar takasa shigarta.


Kallon ta yake tagefen idon sa yana dan kurbar kununsa hankali kwance aransa yace dubi ba gidajiya ko tayaya rigar zata shiga bayan bata balle botir din taba



Cire rigar ta yi daga inda ta makale cikin bacin rai tai hanyar fita da rigar ahannun ta gashi daga ita sai karamin wando



Ali kam ganin tayi hanyar fita daga dakin babu kaya a jikinta bai San sanda yace "keeee!! cikin sauri Dija ta waigo cike da tsoro dan batai zaton da mutum a dakin ba bayan Nene


Gyara fuska yayi yana ya mutsa ta yana kallonta kasa kasa dan shikam bazai iya jurar kallonta a haka ba duk da ceawa da glass a manne a fuskarsa

Cikin maganarsa da isa yace "gidan ubanwa zakije haka da riga a hannu"? domin dai shi a zatonsa zata iya fita daga gidan ahaka da nufin taje a sa mata rigar ganin cewar Nene tashiga wanka



Zumbura baki Dija tayi tana kallonsa kai tsaye tace "rigar ce taki shiga jiki na bayan kuma ina sata bata ma tseni ba yanzu kuma nayi nayi ta shiga taki shine zan nunawa Nene



"Dallah zo nan bakiga rigar a kwai botira a jikinta ba, bakicire botir din ba ta ina zata shiga a haka" yafada yana harararta tare dajan tsaki "bagidajiya kawai"


Mika mai rgar tai tayi tayimasa tsaye a ka dago kai yayi fuska a hade yace " wuce daga kaina ni sa,an kine zaki na tsaya min aka ke ku kunya bakyaji kitsaya ahaka shashasha vileger kawai" balle botir din yai mika mata rigar yace "wuce kije can waje kisa acan" yafada tare da jan tsaki ,,karba tai ta na zumbura baki tai hanyar waje da rigar ahannuta


A jiyar zuciya ya saki bayan yaga ficewarta daga dakin ,,yana mamakin yarinyan a ransa yake fadin yarinya karama da wannan dirin.jikin ina ga inta girma kuma huuuuu abin babba ne


Nene CE ta fito da ga bayi taga dija na saka kaya a tsakar gida cikin mamaki tace "wai ke meyake damunki? anan kike sa kayan" tafada tana rike baki!! ,cikin kumbura baki tace "cewa yai na fito waje wai bazansa a dakin ba ,,


"Ya,asalin kifito waje "? Nene tafada har yanzu hannunta na dafe da ha6ar ta!
"Kai wannan yaro Allah ya shiryeshi" tafada tana kokarin daura al,wala domin dai sallar walha bata wuce ta


I ta kam Dija bayan tasa rigar dan kwalin rigar ta daura ta nan nade kanta dashi ta sa wani karamin hijab sai tayi wani uban kyau ga fuskar ta tayi fayau kalar fatarta sai ta kuma fito wa,,yayinda kanta data nan nade sai yayi kamar wacce tayi a cuci irin wanda matan wananan zamani n mukeyi😀


Shiga dakin tai tace "Nene ina kika ajiye man shafawa banganshi ba "



Tana kokarin tada sallah bayan tasa kayanta itama "tace gashi can gefen kujearar can"


Kallon gurin tai still Ali nanan zaune a inda tabarshi gashi man sha'awar yana waje kafafunshi



Shi kam Ali air fic ne mane a kunnensa bai San ma me su ke ba idanunshi a lumshe kamar mai bacci azahiri kam baba bacci yake ba music yake ji cikin wakar silendion mai taken becouse love me" shikam yana San wakokin ta acewarsa ta,iya wakokin soyayya masu ma'ana



Cikin yanayinta na rashin tsoro ta nufi inda ta hangi man shafar can kar kashin kafafunsa sunkuya wa tai zata dauki man ,,yayinda shikuma ya yunkura da nufin mikar da ka fafunsa


Kawai sai ji yai kamar wani Abu a tsakanin kafafunshi cikin sauri ya bude idon sa dake lumshe,,yana kallon gurin me zai gani! Dija CE a tsakanin kafarsa kamar wacce tai wa sarki karya tayi tsilli,tsilli cikin mamaki ya zuba mata idanunsa yana kallonta ,,itama shi take kallo. kallonta yake fuskarsa a hade bai CE komai ba ,,



Itama Dija fuska tadan ya mutse ta zira hannuta da nufin dauko man sha'awar cikin sauri yasa kafarsa ya take hannun still idanunsa na kanta shi so yake ya San meya kawuta har inda yake



Wani irin azaba Dija taji tana kokarin cire hannuta da ya take

Kara mutstsika hannun yai da kafarsa ,,Dija kam jin wani irin zafin a zaba! wani uban ihu! ta kurma,wanda yai daidai da idar da sallar Nene


Cikin Sauri takai dubanta gun me zata gani! kafar Ali CE a kan hannun Dija yana ta mutstsikamata hannu


Cikin sauri Nene ta bige kafar tace "kai kam
Ali muguntarka ta yi yawa wai ko mugunta ka je ka karanta ne"? tafada tana maka maim sa harara!



Ko kallonta baiyi ba yace "kina ban mamaki Nene to taya za,ai ma tazo tashiga karkashina ni sa,anta dan ubanta ?"



Cikin mamaki Nene tace" ya Asalin ta shiga karkashinka"? man shafawa fa zata dauka gashinan a kasan kafafunka" tafada tana nuna inda man yake


Ko kallon gun bai yi ba
Yaci gaba da duba wayarsa ,,


Tsaki Nene taja tace "mugu dai baji da din halinsa ba
"
Man shafawar tajawo daga kasan kafarsa ta mikawa Dija dake tsaye a gun rike da hannu



Shi dai bai ce mata komai ba yacigaba da danne dannensa a wayarsa.



Dija kam zama tai kusa da Nene tafara shafa man. Cikin ranta kuwa in banda tsinewa Ali babu abinda take itakam bataga abin duka anan ba da ga kawai taje dau kar mai



To a gurguje suka karya gaba dayansu sabida ganinin lokaci yatafi tunda har goma darabi ta wuce


Kallon a gogon da ke daure a hannunsa yake sannan ya kalli Nene yace "ni ina waje in kungama mu hadu amma don Allah ku futo yanzu"



Nene kam ko kallonsa batai ba sabida haushin da yabata batace komai ba har ya fice da ga dakin,,


Shashen sa ya nufa loptop dinshi ya dauka da wasu tarkacen sa da yazo da su domin dai baya zuwa da kayan sawa kasancewar akwai wasu kayan nasa a gidan



Fita yai rike da loptop din da sauran kayan inda ya a jiye motar sa ya nufa ya bude ta hade da bubbuge ta da rigarta ,,sannan ya bude ya ajiye loptop din tare da kayan hannunsa a set din gaba


Shiga yai ya kunna motar domin dai yaji lafiyarta duu dacewa kalau take kasan cewar bata wani jima ba, Sabuwa ce da wo warshi daga karatu Abbah ya siya masa to amma kayan nasara bashi da wani tabbas


Sai da yattabatar lafiyan ta lau sannan ya kasheta zama yai a ciki ya zuro kafafunshi waje yana sauraro tambihi daga malam Jafar mahmud adam



To Nene ma cikin sauri takarasa 'yan kaye kayen ta sannan suka futo ita da Dija wacce ke jaye da jakar kayansu,,



Wani katon kwado Nene tasa ta kulle gidan bakinta dauke d ado'o,i iri iri

Gidan baba malam tashiga a gurguje tayi musu sallama sannan suka futo suka shiga gidan inna hajara wacce takasan ce aminiyar Nene ce a unguwar to nan ma a gurguje suka shiga suka fito


Can gefe Nene ta hangi motar dan haka kai tsaye can suka nufa



Ali yana kallon ta wowarsu dan haka ya maida kafafunshi ciki

Bakin shi dauke da ado'a ya kunna motar a karo na biyu bayan ya rage sautin radi'oyn motar



Nene kam murfin baya ta bude takar6i jakar ta fara turata ciki sannan Dija ta shiga ita ma ta bi bayanta,,



Wani irin kamshi ne yadaki Nene ita da Dija da wani irin sanyi sanyi da motar take bayarwa mai dadi ,Nene ce ta kalli Ali yayinda ya ke kokarin juya kan motar tace "barin turare kayi a motor ne? jin irin wanann kamshi da yake tashi"




Kallonta yayi ta cikin mirrow din motar yace "Nene kenan ko daya mota na haka take ke dai kawai kinji kamshi mai dadi ba irin turarki ba dan hamsin". Ya fada yana kanne mata ido daya



Wannan karon dariya Nene tayi har da kyakyatawa tace "dan banza ai duk da tsofa na bazan shafa turaran naira hamsin ba ehee"!


Tace "ka dai jamu a hankali don Allah kar ka fafura mu"


Murmushi yayi bai ce komai ba yaciga ba da tukinsa yayinda suka fice da ga layin


*To Allah y kiyaye hanya su Ali*



Tuki yake cike da kwarewa wayarshi ce tafara kara kallon inda ya ajiyeta yai sunan Abbah ya gani ya na yawo a kan fuskar wayar dauka yai cikin sauri ya makala a kunnesa yayin da daya hannun yake tukin da shi yace "Abbah barka da asubah"

Daga daya bangaran Abbah yace "barka dai Ali kun taho ne?


"Eh abbah gamu akan hanya" yace "to masha,Allah bani Nene ,,


Yace "to tare da dan waiwayawa ya mikawa Nene wayar ya ce "abbah ne


Cikin sauri Nene ta karbi wayar takara a kunneta tana fadin "salamu alaikum"


Cikin sauri abbah ya amsa yace "Nene antashi lafiya"?

"Lafiya lau ai gamunan akan hanya ai kadai matsa bashir to bazan wani da deba zandawo kamar yadda nasaba ,tokaji"!!



Abba ya ce "babu mutsala Nene Allah ya kawuko lafiya "
"Ameen tace tare da mikawa Ali wayar


Dija kam kwanciya tai kan jakar kayannasu tana faman daddana wayar Nene da ke hannuta game take yi da ita



Shiru motar tayi in banda sautin karatun alkur,ani dayake tashi kasa kasa cikin kira,ar malam sulaiman Ahamad



Tafiya tai ta fiya wanda Dija wayar hannuta har ta subuce ta fadi bacci ya kwasheta to itama Nenen gyangyadi take



Ali ya na kallonsu ta mirrow din moto


Dan tabe baki yayi yace "dubi wai bacci suke kamar wa,"yanda basuyi baccin dare ba tafiya bata kai ta kawo ba har za,ayi bacci"



Ana kiraye kirayen sallahr azahar suka isa abuja D'ija "yar kyauye ta zama kalle kalle kawai takeyi domin wannan shine karonta Na farko da ta taba zuwa Ali yana kallonta ta cikin mudubi sai tsaki yake ja yace shashasha "yar kauye kawai


Nene ta bude idonta tare da gyara zama bakinta dauke da salati ta kalli Ali Wanda yake kokarin shiga da motar cikin gidan tace"wato ina can sake da baki kana fafara gudu dani ko"

Shi dai bai ce mata komai ba, can inda suke aje motocinsu ya nufa yayi parking Haruna draver tare da Malam Yahaya mai gadi suka karaso gurin da sauri suna musu barka da zuwa

Ali ya fito cikin gajiya yana mika musu hannu alamun gaisuwa, Haruna murna duk ta isheshi yau yana hannu da hannun da oga yace"Haruna mun same ku lafiya"?


"Lafiya kalau yallabai ya hanya"?

"Alhmdullhi"

Cikin barkwanci Haruna ya karasa yana tsokanar D'ija tare da yiwa Nene barka da zuwa



Nene ta fito daga motar tana amsa gaisuwar Haruna cikin sakin fuska da mutumta dan Adam dama tun asali Nene macace mai sakin fuska gami da wasa da dariya, Haruna ya karbi jakkonan kayansu, yayi gaba dasu,Ali ya kalli Nene yana murmushi yace"ni dai na gama nawa aikin ko"?


Nene tace "kwarai kuwa ka gama Allah mungode ma da ka kawo mu lafiy.. Kafin ta karasa sai ga su Na'ima tare da Fa'iza sun fito da gudu suna ihu ,ga Nene ga Nene ,Na'ima taje ta rungumeta kamar zata kada ita ,sai murna take,ita ko Fa'iza D'ija ta rungume tace"kawata yau gaki kinzo gudanmu gaskiya naji dadi,tun dazu nake jiran zuwanki yau har sai da naki zuwa sukul sabuda ke"


D'ija ta rungumeta tana dariya tace"nima ina ta murna zanzo in ganki ,Fa'iza na

Ali ko tafiyarshi yayi ya kyalesu a gurin ganin abinda sukeyi shifa ya tsani shirme, kai tsaye part din shi ya nufa ,Wanka kawai yakeson yayi sabida yadda yake jin nauyi a jikinshi ,kwata-kwata baya son zafi ko kadan


Nene ko hararar Na'ima take tace"ai sai ki sake ni ko sai ki yadda ni"


Na'ima na dariya tace"wace ni yadda uwar masu gida,gaskiya naji dadin zuwanki Nene nayi kewarki sosai,sabida kinzo kenan ,baza ki kuma ba"

"To ai sai ki rike min kafafu ki hanani tafiya,Nene tafada tana galla mata harara

Dariya Na'ima tasa ,ta kalli D'ija tace "ke wai ba zaki gaishe ni ba"?

D'ija ta kalle ta tana zumbura baki tace"tabdijam ke zan gai sai tab!

Na'ima tace"ni ba yayarki bace to"

Zumbura baki D'ija tayi batare da ta gaida Na'iman ba suka wuce ciki gidan ita da Fa'iza sai karadin surutu sukeyi.

Girgiza kai Na'ima tayi tana murmushi sabida tasan halin D'ija da tsiwa


Gaba dayansu suka shiga babban falon hajiya Zainab tana khicin ita da mai.aikinsu Asabe yau da kanta ta shiga kichin din domin girkin na mussaman ne sabida zuwan Nene bayan hakama tasan Ali bacin abincin masu aiki yake ba duk da cewa Asabe akwai tsabta shikam inda ba ita ce tayi abinci ba to bayaci. Sabida yasan tes din girkin kowa shiyasa babu yadda zatayi take shiga khicin din tai mai dashi da maigidan,, sukuma asabe tayi musu nasu ,,gashi asaben ta,iya girki sosai bata da kazanta ko kadan amman duk da haka Ali bai yadda ba shikam haka Allah ya hallice shi da tsamtsami



Cikin sauri Ummi domin haka suke cema ta ,tafito da ga khicin tana goge hannuta


Cikin fara,a tace "sannu da zuwa Nene kunsha hanya" tafada tana zama a kujarar da,take kallon Nene


"Ai kam dai munsameku lafiya"? "Lafiya lau wallahi ya mutan gida da sauran "yan uwa?


"Nene tace kowa lafiya lau duk suna gaisheku",

"To masha,Allah muna amsawa"


Asabe ce tashigo hannunta rike da wani babban tire ,itama cikin fara,a tace "sannu da zuwa hajiya ,,

"Yawwa sannu Asabe mun sameku lafiya

Cikin sauri Asabe tace "lafiya lau hajiya tana kokarin budewa mata lemo


Cikin fara,a Ummi ta kalli dija wacce suke ta faman surutu ita da fa,iza tun zamansu a gun "tace Dijan Nene babu magana ko?


Cike da kunya Dja ta sunkuyar da kanta tace "ummi inayini"? domin itama da haka take kiranta


Dariya ummi tayi tace "bazan amsaba sai. Da na roka sannan"kara sukuyar da kanta tayi tana murmushi tace "to kiyi hakuri",ummi tace" nakiyi "


"Tace Nene kina jina da mutuniyar taki ko wai sai da na roki gaisuwa sannan"


Dariya Nene tayi tace "ai in suka hadu da wannan berar basa ji basa gani"


Ummi tace "ai kam dai"
"Tace Nene kisauko kasa ma kici abinci

Please Login or Register in order to submit comment