Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

with our Youths,abu mai had'ari shi suke mayarwa abun adon su,and what really baffle me with them shine duk irin mummunan had'arin da mashin d'innan ke haddasawa hakan bai serving dinsu misali su daina hawan...Alhaji Sa'idu ya kar6e"Sam basu bi dashi yadda yadace ne,haka zaka ga suna ta falla uban gudu kai kace zasu kiyama..."Mutumin na karshe ya katse shi da cewa"Ai wasu kam kiyaman suke tafiya wllh sam basu la'akari da irin titinan mu ba kaman na waje bane,su yi ta tuk'in ganganci,gashi naji ance mashin d'in tsada ne dashi sosae..."Hajiya dake tsaye hannuwanta goye a bayanta ta amsa "tsada kam! Miliyan biyar ya zuba kafin ya mallaki wannan nasan..."gaba daya suka zaro ido a tare suka maimaita kudin da hajiyan ta fad'a,ita kam kai ta jinjina masu Uncle Mani yace "to Allah ya kyauta,Allah ya k'ara tsarewa,gaba d'aya suka amsa da Amin" daga haka ya kalli hajia da d'an murmushi yace "to hajjaju mu zamu wuce sai wani lokaci kuma in Allah yasa rayuwarmu ta kai" hajia tayi murmushi tace"To Allah yasa rayuwar tamu ta kai" ta fiddo hannayenta dake goye a bayanta ta mik'a ma Alhaji Sa'idu kud'i dake cikin hannunta na dama da fara'a tace"gashi ayi ma iyali tsaraba nagode da ziyara,Allah yabar zumunci" hannu biyu yasa ya kar6a harda d'an russunawa suna ta godiya shida dayan,Uncle Mani yace"To ni hajjaju ba'a sallame ni ba" dariya tayi tace banda kai ai sune bak'i na, kai na gida ne" shima dariyar yake ya bud'e mota yace"ba wani abu nasan tawa sallamar babba ce tafi karfin hannu k'ilan,zan turo Account details" daga haka ya shige Abokan tafiyarma suka shiga suna ta kara godiar rafar 50k da hajia ta basu cike da farinciki hannu ta d'aga masu bayan sun fita daga cikin parking space din tace"Agaida Iyali",daga haka ta juya ta koma ciki.

Tunda ta shige gida take kunshe a daki,bayan tayi sallar Azahar bacci yayi awon gaba da ita,ko Uniform d'in bata cire ba,bugun kofar da ake tayi ne ya farkar da ita a tsorace ta fito daga d'akin tana tafiya cikin sand'a har Lokacin kuma ana ta buga kofar da k'arfi,tsayawa tayi cikin zauren tana tunanin waye ke buga kofan haka? kodai mai Motar ne ya kawo k'ara,ji tayi gabanta yayi mugun fad'uwa nan take tsoro ya kama ta tace a ranta "to ya akai yasan gidanmu bayan lokacin da na jefi motan ba kowa wurin..." wani bugu aka yima k'ofar wanda daji mai buga kofan ya k'ule yasa ta tunkari kofar da sauri ta d'an leka idonta d'aya ta ramin makulli nan take ta gane waye da sauri takai hannu sama ta cire sakatan sannan ta d'an ja baya,aikam da karfi aka bugo kofan don da bata matsa ba daba k'aramin buguwa zatai ba,rai a6ace yake kallonta Kawu Amadu ne hannunshi daya rungume da kwali d'ayan kuma katuwar leda ce,Fatuu dake ta faman zare ido tace "sannu da zuwa Kawu Amadu...."da sauri ya katseta da fad'in "sannu da zuwan uwarwa,don iskanci daman kina cikin gidan kika barni inata bugun k'ofa tsawon lokaci,to waima uban me kike a cikin gidan daba zaki zo ki budan ba? d'an turo baki tayi tace "ba komai,bacci ne ya d'auke ni fa" a harzuk'e yace"to miye na kulle kofa don zaki yi bacci" da sauri tace "ina gudun kar a shigo ayi sata ne ina baccin...." "k'arya kike" yace yana k'are mata kallo kafin yaci gaba "fad'a kika jawo ko? Da sauri ta girgiza kai alamar a'a,kwafa yayi yace "ai na dawo gidan inma rigima ki ka jawo zan gani,kuma uban miye na zama da Uniform har yanxu a jiki da alama ma ko wanka baki yi ba,bare kiyi sallah" ya k'arasa maganar yana kokarin aje kayan hannunsa a bakin kofa,d'agowa yayi ya daka mata tsawa"wuce kije ki wanka kafin na buge ki a wurin" juyawa tayi ta nufi cikin gida tana d'an k'unk'uni har ta nufi d'aki taji yace"bakiji mi nace kiyi bane? Da sauri tace "naji.." yace"to wuce ki dau bokiti ki d'ibi ruwa" ta wuce ta xuba ruwan ta shige band'aki,shima yana shiga wankan yayi a d'an band'akin cikin d'akin nasa ya shirya ya kwashi kayan da ya siyo ya nufi shago don jera su.

Sai can bayan Issha gwaggo ta dawo,fatuu dai na k'unk'ume a d'aki cike da zullumin kar akawo k'ararta, koda ta fito tayi ma gwaggon sannu da zuwa dakin ta koma ita kam gwaggo a gajiye take hakan yasa ko ta kan Fatuu bata bi ba balle har ta fahimci wani abu,sai can dare gwaggo tayi bacci sannan ta fito taci abinci tayi sallah ta koma ta kwanta tare da yankewa ranta cewa baza'a kawo k'arar tata ba tunda har aka kai wannan lokacin.

Washe gari asabar da safe Fatuu ce da Haulat zaune cikin ajin su na islamiyya,Haulat ta kalli Fatuu da murmushi tace"sannu hajiyar fad'a" wata yar dariyar iskanci fatuu tayi tace "waya ce maki nayi fada" d'an ta6e baki Haulat tayi tace "har gida akazo aka fad'a mana irin fadan da kuka yi, wai har kin fasa ma Murja baki da hanci" murmura idanu Fatuu tayi tace"Yessss,gobe ma ta k'ara gaya man banzan maganganu harta kirani da yar kauye" girgiza kai haulat tayi tace"ni wllh don kince Gwaggo bata nan amman a lokacin da sai na kai k'arar ki tunda ke dai baki da hakuri" harararta Fatuu tayi tace "aida da ta dawo kinzo kin kawo k'arartawa sarkin masu hakurin duniya" haulat tace "tunda ya rigada ya wuce miye na inzo,Amman ai naji ance wani mutum ne yayi maganinki da ki ka k'i barin fadan ya wanka maki mari" ta kai maganar tana tik'ar daria,wata yar iskar dariya Fatuu ta sake yi tace"hehehe ashe yai maganina,muka dai yi maganin juna don shima yayi asara ehe" haulat ta dakata da dariyar da take tace "what do you mean da ku kai maganin juna?wace irin asara kuma? Fatuu ta gyad'a kai da turancin ta na yar sakandire tace "what u hear" Still haulat tayi tana ta kallonta can tace "don Allah Fatuu fad'a man abunda kika yi masa" fatun na shirin yin magana Malaminsu ya shigo hakan yasata yin shiru daga nan kuma basu sake samun daman yin magana ba don yana fita wani ma ya shigo a haka har aka tashi,akan hanyar su ta komawa gida Haulat tace "d'azun na tambaye ki mi kika yiwa Mutumin baki gaya man ba" banza fatuu tayi mata,haulat ta sake cewa "kinji,mi kika yi masa ne" ba tare data kalleta ba tace"ke dalla bafa komai,wasa nike,ba abunda nayi masa kawai don kar kiyi tunanin yayi nasara akaina ne" haulat tace "kawai dai bazaki fadan bane Amman ko nayi rantsuwa ba zanyi kaffara ba tunda kika ce yayi asara da akwai abunda kika yi masa...." cikin tsiwa tace "ehh d'in nayi, tunda ba ki yarda ba abunda nayi masa ba" shiru haulat tayi amman ba don ta yardan ba,can tace "to ki kar6i jakar ki ko,kince in taho maki da ita kuma kin barni inata kayanta" juyowa Fatuu tayi ta figi jakar ba ko nagode tayi gaba abunta sai wurga kafa take da alama dai ta saba da yin tafiya haka,girgiza kai haulat tayi tace daga abun arziki,tabi bayanta har suka zo bakin lungun da suke rabuwa,haulat ta d'an daga murya tace "sai munhade Anjima hajia Fatuu ikon Allah" Fatuu ta juyo tayi mata kallon up and down ta k'ara gaba,Haulat dai dariya tayi a fili tace"Allah ya shirye ki" daga haka ta nufi hanyar gidansu, adai dai kofar shiga gida fatuu ta waiga tana kallon hanyar da haulat ta bi a fili tace "don ina sakarya Allah ya rufa man asiri in tona ma kaina,don na tabbata na fad'i mata sai ta fad'a ma gwaggo ko kuma tayi ta ma mutane nasihar banza ita ga mai hakuri yen-yen-yen" ta d'age baki daga haka ta shige gida.

Haulat ce keta faman sauri da yamma zata islamiyya don ta makara sakamakon aikenta siyen gero da Innarsu tayi,tana k'okarin shiga lungun da zai kaita har islamiyyar taji daga gefenta ana magana "Ke,ke yar liman wait" da sauri ta juya tana kallon mai maganan,ya nufota yana wata irin tafiya irin ta nigas,da mamaki haulat ke kallonsa tana tunanin ita miye had'inta da Gaye da zai tsaida ta,yana k'arasowa yace"Ke dalla tambayanki zanyi kike ta faman zare ido uwa mujiya" ita dai haulat shiru tayi tana jiran jin abunda zai ce,ya ci gaba "dama tambayanki zanyi k'awarnan taki an kamata tana can cikin cell ne ko har anyi gaba da ita? cikin rashin fahimtar zancen shi haulat tace "wace kawar tawa kuma? Wata yar iskar daria yayi yace "kina da wata k'awa ne bayan Aljanar yarinyar nan mara jin magana, kullum ba tare nike ganinku ba" nan take ta gane Fatuu yake nufi don duk in suna tare suka had'u dashi Aljana yake cema fatun,da sauri haulat tace "to mitayi da za'a kai ta cell kuma? tayi maganar cike da fargaba tana ta zare ido, rik'e ha6a gaye yayi yace "wai kina nufin baki san aika-aikar da aljanar nan ta aikata ba...? da sauri haulat ta girgiza masa kai alamar a'a, jinjina kai yayi yace"tabb,to wllh ruwa ta 6allo ma kanta don ina tabbatar maki sai taje gidan yari..." da sauri haulat ta dafe k'irji tana salati tace"don Allah Gaye ka gaya man abunda tayi,ni sam wllh bansani ba" sai da ya gyara tsayuwa ya karkace baki yace "to bari kiji wani mutum ne jiya hakanan Aljanar nan ta jefar masa glass d'in bayan mota,gaba daya ta dagargaza glass din don wannan glass din yayi konden..." cikin tsananin tashin hankali haulat tasa hannuwanta duka biyu ta rufe bakinta ya ci gaba "atoh kima fad'a mata ta shirya don comfat (confirm) in ba'a biya shi ba har yakai k'ara na rantse da Assamadu sai taje fursun,yo motar fa ba k'aramar mota bace,to tsaya ma kiji,mai motar dan gidan Hajiyar Sanata ne kinsan kuwa ba'a k'aramar harka a gidan nan......" daga haka ya kad'a kai yayi gaba abunshi,

kasa motsawa haulat tayi na tsawon lokaci da k'yar ta juya taci gaba da tafiya a hankali gabanta sai fad'uwa yake tamkar itace akace zata gidan yarin,cikin zuciyarta kam mamaki kawai take na abunda fatun ta aikata,ashe asarar da take nufin mutumin yayi kenan,"tabb lallai Fatuu bata da hankali!" ta fad'a a fili tana jinjina kai.
A daidai bakin ajinsu ta tsaya tana tunanin shiga don tasan ta makara gashi akwae malami cikin ajin,can dai tayi shahada ta kutsa kai tare da yin yar sallama,d'an kallonta malamin yayi yaci gaba da bayanin da yake hakan yasa haulat yin saurin shigewa ta nufi wurin zamansu sai dai ga mamakinta Fatuu bata a wurin,tunani ta fara yi a ranta bayan ta zauna"to Fatuu bata zo bane? Kodai anje an kamata...wani irin bugu gabanta yayi da sauri ta d'ago da kanta a lokacin kuma ta hango fatun acan dayan bangaren,tunda haulat ta shigo ta wuce Fatuu ta ganta a ranta tace "da nice na makara da ya buge ni,ni da kowa ya tsana"ta saci kallon malamin ta d'an hararesa kafin ta juya inda haulat take nan take suka had'a ido don tunda ta hango fatuu take ta kallonta cike da al'ajabin abunda gaye yace zai sameta,murgude fatuu tayi mata ta juya,haulat ta girgiza kai cike da tausayinta,ta kuma fahimci dalilin da yasa fatun ta canja wurin zama don ta saba hakan da d'an abu ya hada su wanda bai kai ya kawo ba sai ta canja wurin zama sai tagadama ta dawo ko haulat taje ta bata hakuri sannan ta dawo,haulat ce kad'ai ke iya jure halin fatuu don ta karanci halayenta tsab shiyasa ma bata biye ta.

Haulat ce keta sauri ta isko Fatuu don da aka tashi ta tsaya copying rubutun da malam yayi bata nan daga littafin wata kawarta da suke zama tare,ita kuwa Fatuu ana tashi tayi gaba abunta don guje ma haulat din take karta k'ara tambayarta game da asaran da tace Mutumin daya raba su fad'a yayi don tasan halinta wani lokacin nacin tambaya ne da ita kuma karshe inta gano tana iya zuwa ta fadi ma gwaggo "Fatuu!fatuu ki tsaya" haulat dake biye da ita a baya tace,ganin bata da niyyar tsayawa yasa haulat yin dan gudu tasha gabanta,cak fatuu ta tsaya fuska ad'aure tace "miye haka zaki wani shage gaba na" kasa magana haulat tayi don k'arfin halin fatun mugun mamaki yake bata ta aikata irin wannan babbar ta'asar amman hankalinta akwance,tsoki fatuu taja tana kokarin bin ta gefen haulat din,taji tace "To ai yanzu nasan abunda kike 6oyewa hajia" da sauri fatuu ta kalleta sama da k'asa tace "ni mi nike 6oyewa? Haulat ta jinjina kai cike da takaici tace "asarar da kika ce mutumin nan yayi na tambayeki wace asara ce kika k'i fad'a man to yanzu nasan komai,ke yanzu fatuu abunda kika yi kin kyauta?hakanan ki jefar ma mutum mota har ki lalata masa glass....."katse ta Fatuu tayi da fad'in "naje na fasa d'in,dama nasan ai sai kin bi diddigi don kin saba sa man ido,to na fasan kuma ko gobe ya k'ara shiga harkata har ya d'aga hannu ya mareni sai na kara ja masa asara don ni ba ai man na kyale ehe" daga haka ta kad'a kai tayi gaba,cikin d'aga murya haulat tace "to kinsan wanene kika fasa ma gilashin mota.....? a fusace ta juyo tace"ina ruwana da ko waye,Allah yasa d'an sarkin makkah ne" ta juya taci gaba da tafiya abunta don ita tayi tunanin tambayarta haulat d'in tayi,cike da takaici haulat tai tsaye tana kallon bayanta a fili tace "lallai Fatuu bata da hankali wllh bata san bala'en da ta jawo ma kanta bane,tama k'i ta tsaya ta saurare ni...." girgiza kai tayi ta fara tafiya tana ta sak'e sak'e a ranta "ko dai inje in sanarma gwaggo don tasan halin da ake aciki..." girgiza kai ta sake yi da sauri a fili tace "kai a'a,bai kamata ta fara jin wannan mummunan labarin daga baki na ba gaskia" can kuma tace "to wai ma ni ina ruwana da zan damu,ita wadda ta aikata laifin ma ko a jikinta,kawai dai ba dad'i ne kana tare da mutum wani mummunan abu ya same shi,to amman tunda ita taja ma kanta ai ita ta sani" ta watsa hannuwa,daina bin bayan fatun tayi,ta canza hanya,lokacin da fatuu zata sha kwana ta juya bata ga haulat d'in ba ta6e baki tayi a ranta tace gwara da nayi mata haka inba haka ba sai tace zata zo ta gaya ma gwaggo,a fili tace "inma tazo ta fadan sai in k'aryata ta tunda dai ba a gabanta akayi ba kuma bata da shaida" tayi k'wafa tace "ta sake ta gaya ma gwaggo wllh 6atawa zamu yi ba ruwana da ita" tayi maganar tana mummurgud'a baki,To hajia Fatuu ba dai yau kika fara fadin haka ba,kuma ko kun 6ata da kanku dai kuke shiryawa don keda haulat sai Allah.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

*Mallakin*
⬇️
*ZAINAB LALUH*🌹
*(Oummu imam)*


Free Page1️⃣8️⃣

Gwaggo ce ta fito daga cikin kitchen lokacin ba'a dade da gama sallar isha ba,hannunta d'auke da d'an kwanon silver madaidaici rufe da murfinsa asaman shi kuma bakar leda ce dauke da wani abu an kulle, tsayawa tayi ta fara kwala ma fatuu kira "Fatuu,fatuu,Worei mi lilma", leko kanta tayi ta jikin labule tace" ina zaki aike ni?" hajia zaki kaima tuwon nan nasanta da son tuwon dawa" da sauri ta fito jin za'a aiketa wurin Hajiyar Sanata,hannunta rik'e da k'aramin bak'in gyale ta fara k'okarin cire hijab d'in islamiyya dake jikinta tana fad'in "dama kwana biyu banje ba wllh...."

Gwaggo tace"to miye na cire hijab d'in kuma,kibarta mana" turo baki tayi tace"ni nafi son in sa gyalen kinga na fi shan iska ma",
gwaggo tace "A daren nan zaki sa wannan figaggen gyalen da iyakarsa kafad'a,to bar aiken ni bari in mik'a mata da kaina..." da sauri tace "a'a to yi hakuri nabar hijab din" tayi maganar tana d'aga hannu alamar ban hakuri,
gwaggo ta mik'a mata kwanon tace "kiyi maza ki kai mata kidawo,sauran kuma ki tsaya shiririta sai tsakan dare ki dawo" dariya tayi ta amshi kwanon ta rungume tana fad'in yanzun nan zan dawo kakus, Gwaggo tace "to ki d'aura akai mana salon miyan ta zubo ta 6ata maki hijab din",
fatuu tace "bazata zubo ba zan kula" abunda gwaggo bata lura ba fatun ta 6oye gyalen da ta hanata sawa a kasan hammata shiyasa tak'i daura kwanon aka don kar ya fad'o ta gani,

A zaure ta aje kwanon k'asa ta cire hijab din ta sagale ta jikin windon d'akin kawu Amadu tasa gyalen kana ta nufi gidan Hajia.

A daidai gate ta tsaya wurin Officer dake zaune shi kad'ai tace"Sannu da gadin gate Officer" ya d'ago ya kalleta yana daria,don maganar tata ta bashi dariya yace "Yauwa kema sannunki yar fillo" tace "kai kad'ai a zaune ina d'ayan Officern yake? Rausayar da kai yayi yace ya tafi yin wani uzuri ne" ta ta6e baki tace "ba wani uzuri wayo yayi maka yanzun haka zance ya tafi wurin Budurwarshi ya barka kai d'aya kana ta aikin tsaro,wllh kada ka yarda ya maida kai sakarai kaima ka rama atoh" jinjina kai yayi yana d'an murmushi jin abunda tace,sam baiji komae ba don yasan ta sam ba datsar k'umba gareta ba duk abunda yazo bakinta fad'i take yace"to yar fillo ya zanyi in rama d'in? turo baki tayi tace "nifa ka daina ceman yar fillo" kyalkyacewa da dariya yayi don dama yasan bata son sunan yace "to ke ba yar fillon bace? tace "to nidai banso ka kira ni da Fatuu na kawae" yace "to shikenan hajia fatuu na bari,sai a fad'i man yadda zan rink'a ramawa nima" tace "yo kaima budurwar zakayi sai ka rink'a tafiya tadi....." katseta yayi yace "to ni ina zan samu budurwa nida kullum ina nan zaune ina tsaron gate" tace "Yo yadda yayi shima ya samu zaka yi" ta juya tana k'okarin shiga gidan yace "to ko ke kizama budurwar tawa kawai ma...",
A fusace ta juyo bayan ta tsaya ta bishi da wani kallo,shi kam sai daria yake,tace" God forbid! ni bazan zama budurwar kowa ba yanzu sai na zama likita,kuma lokacin ni nafi karfin mai gadin gate,tana gama fad'in hakan ta shige sai kuma ta sake lek'owa ta cikin gate din tace "in budurwa ka ke so kaje wurin kawata Haulatu don ita ban ji tana da burin zama koda malamar makaranta ba,kuma nasan zata so ka don sakarya ce" daga haka ta shige tana ta tik'ar daria,shima Officer dariyar yake yana girgiza kai.

A corridor ta tsaya ta cire takalmanta sannan ta d'an lek'a cikin parlon a hankali ta hango hajia dake zaune saman 2-seater ta d'aura takardu saman sofa table tana rubuce rubuce idanuwanta sanye cikin gilashi,cikin d'aga murya Fatuu tace"Assalamu alaikum ga bak'uwa,ga bakuwa daga makkah" hajiya ta d'ago ta kalli entrance tana daria,fatuu ta k'ara maimaita abunda tace,Hajia ta girgiza kai tasan in ba amsa mata tayi ba,haka zatai tayi tace"Maraba da bakuwa mutan makkah shigo" shigowa fatun tayi tana ta kyalkyalar dariya itama hajiyar dariyar take tace "ja'ira",
kusa da ita fatuu taje ta zauna tace"Hajiyar Sanata ina wuni" Hajia tace "lafia lou yar gidan hajiar sanata,kwana biyu baki zo kika gaida hajiyar taki ba, jiya juma'a inata zuba ido banga kinzo yiman barka da juma'a ba" Fatuu ta d'age kai ta kwanta jikin kujerar tace "Ai jiya ban je ko ina ba a d'aki na wuni kamar maijego" ta kai maganar tana ta daria,hajiya dake kallonta tace "hala rigima kika janyo?", "a'a" Fatuu tace tana kunshe daria,
Hajia ta girgiza kai tace"habawa,nida nasan hali,hakanan ba ciwo ba mi zai sa ki wuni a d'aka,har yanzu dai kin k'i daina yin rigima da mutane ko Fatima? dago kanta tayi daga jikin kujerar ta d'an turo baki tace"wllh hajiya mutane ne ke tono na..." hajiya dake kallonta ta katseta"ke kuma ba hakuri ko" dariya kawai fatuu tayi,hajiya tace "gaya man abunda yasa kika wuni a daki" sosae gaban fatuu ya fadi a ranta tace "tabb wllh bazan fadi mata na fasa ma wani glass ba" a fili tace "wata yarinya ce muka yi fad'a na fasa mata hanci da baki" ta kai maganar tana nok'e kai,hajia dake kallonta ta girgiza kai tace "kai jama'a! Yanzu ina amfanin haka fatima,aita gaya maki magana baki ji,ke sam baki da hakuri to kuwa kwanan nan zamu 6ata wllh,6atawa kuma ta har abada kar ma kiyi tunanin zaki ban hakuri in hakura...."da sauri Fatuu ta saukko daga kan kujerar ta duk'a gabanta tace "Don Allah Hajiar Sanata kiyi hakuri wallahi tallahi ita taja ni kinji na rantse,daga nace ta matsa man wuri a Bus din makaranta in zauna bayan an tashi,ta fara gaya man maganganu nai shiru na kyaleta,hakan bai isa ba da muka sauka taci gaba har tana fad'a ma abokanta wai ni daga k'auye aka kawoni..." tayi narai narai da idanu kaman zata yi kuka,
Ajiyar zuciya hajiya ta sauke tana ta kallon fatuu da har kwalla sun cika idanunta, tasan dama hakan sai ya faru don bata son taji tace zasu 6ata,tace"shikenan tashi ki zauna,amman don Allah Fatima ki rika hakuri kinji,yawan fad'an da kike da mutane shiyasa suke tsokanarki ai,ki koyi kauda kai akan abunda bai kai ya kawo ba kinji yar gidan Hajiya" ta k'arasa maganar ta sigar lallashi,
Gyad'a kai Fatuu tayi ta koma kan kujera ta zauna tana murmushin jin dadi,hajiya ta kalli kanta da gyalen ya d'an zame tace "wai har yanzu baki je an kitse kan nan ba? ko rannan ba saida nayi maki magana akan kije ayi maki kitso bane?"
Ta marairaice fuska tace "wllh Balarabar ce zafin hannu ne da ita hajia,in tayi man kitso kaman kan zai tuge gaba d'aya,ni shiyasa banson zuwa" hajiya tace"ba wani zafin hannu,nima ai tana man kitson ko,kawai dai baki son kitson ne,don ma Allah ya taimakeki gashin mai kyau ne ai da tuni ya lalace yadda baki kula dashi d'in nan,bari in Balarabar tazo yiman kitson ai nasa tayi maki shi a gabana kuwa",

ta juya ta kalli kwanon da fatuu ta aje saman carpet da ta shigo tace"mina samu da daren nan haka" Fatuu ta d'ago tace "tuwon dawa ne,Gwaggo tace na kawo maki" fuskar hajiya d'auke da murmushi tace"Aikam nagode wllh,dama kwana biyu banci tuwon dawa ba,gashi Dije badai iya tuwo ba....." Fatuu tace"nikam dai ai ta kusa ta kashe ni da shi" Hajiya tayi daria tace "A ina ki ka ta6a ganin tuwo ya kashe mutum fatima?" Shiru tayi tana ta turo baki,hajia dake ta daria tace"to kinga tashi kidau kwanon miyan nan kije kitchen kisamu bowl mai kyau ki juyo man miyan sai ki daukko man plate in saka tuwon inci abuna yanzu yabi jiki kafin in kwanta,sai ki wanke kwanon ki zubo abinci na nan a kicin d'in kije kici tunda ni dai bazanso tuwon ya kashe ki ba" ta k'arasa maganar tana ta tik'ar daria,

Mik'ewa fatuu tayi ta dau kwanon miyan da ledan tuwon ta nufi kitchen,Hajia tace"ki fara zubo man ruwa a roba in wanke hannuwa",
juyo miyan tayi ta warware tuwon a plate ta kawo ma hajia,har ta juya zata koma kicin don zubo abincin ta waiwayo tace"Hajia ina Aunty Saude ne? Hajiya da har ta fara cin tuwon tace "tana a backyard taje ba su d'awisu abinci" fatuu tace "aikuwa bari inje bayan,dama kwana biyu ban gaisa da mutumina Aku ba...." hajia ta katse ta "A'a kar kije bayan nan,kije ki d'ibo abincin kizo ki tafi kinga dare yayi,na tabbata kika je wurin Aku kuma ai sai an biyo sawunki,ki bari gobe in Allah ya kaimu,ana tasowa islamiyyar safe sai kizo kusha fira dashi,yanzu je ki zubo abincin ki ciko kwanon" Fatuu ta gyad'a kai taje ta zubo abincin wanda dafa dukan couscous ne yaji uban kifi sai k'amshi ke tashi,ta dawo parlon ta aje kwanon akan carpet ta nufi kujerar dake kusa da

Please Login or Register in order to submit comment