Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ake maka na cewa Nafisa ta gama dakai da cewan da ake saboda ita ka kasa zama da Fati.
Akan wani dalili zata fitar dani ta yaya din zata fitar dani yace muje zuwa nan gaba zaka sani idan lokacin hakan yayi yanzo ina zamu ne kadauko ni tunda safe haka.
Wurin ta zamu in gwada mata ita din ba kowa bace ya kwashe mai da dariya yace ta zama kowan ke nan tunda har zaka iya biye ma shirmay ta na mata.
Bai kara magana ba sai juya kan motar yayi zuwa office din su ya shige bai tsaya jiran Yusuf din ba.
Anan malam musa driver ya tsayar dashi yana fadin yana da magana dashi na siri da yake son suyi a tsakanin su yace da malam sani din wani abu ya faru ne yace eh to sai dai maganan nason siri gaskiya yace dashi babu damuwa kasa may ni a gida da yamma idan mun tashi.
Ga haka suka bar zancen da malam sani din sai dai ya barshi da tunane a zuciyar shi ko akan may yake bukatan kebewa dashi bai sani ba ya san dai abune mai muhinmanci sosai.
Shiko gogan acikin office maganan da sukayi da Yusuf ne yake ta mashi yawo arai wai zata zama mai garkuwa a kan matsalan shi da Fati da Nafisa ta yaya ma haka zai faru .
Nan dai ya watsar da maganan ya ci gaba da aikin dake gaban shi sai dai yanayi yana tuna zancen a zuciyar shi.

Kai tsaye da na fito kamar yadda na saba gidan da muke na nufa yau yawan ci basu da lectures sai karan gida ke tashi ko ina a cikin gida.
Yunwa nake ji don ban tsaya nayi karin kwarai ba da safe sallah nayi sana fara hada tea na nasha sai da na dan huta a wurin na mike ina sauya kayan jikina.
Na saka dan guntun rigan da nake zama a daki dashi gyaran dakin nayi na gyaro ko ina na dakin sai na dora girkin dare don shinkafa da miya nake son yi irin na yan makaranta.
Bayan na gama miya na dora shinkafan na koma na zauna a bakin katifa ina tunane zarah ne ta fado min a rai yau in zan lissafa kwananta biyar bata dawo ba.
Zarah tana daya daga cikin "ya"ya dake cin amanan iyayyen su don babu inda suka rageta don koba a fada ba zarah tafi gata don sati biyu bai shigewa iyayyen ta basu turo mata da sako ba.
Amma duk ta watsar da wanan gatan nata tabi ra,ayin kwadan abin hannun samari wanda ya rufe mata ido a yanzu har yakai ga ta watsar da karatun ta.
Ido na lumshe tare da girgiza kaina ina cewa ubangiji katsare mu ka karemu ya Allah kasa mufi karfin zuciyar mu don yanzu rayuwa abin tsorone .
Sai gata washe gari ta dawo dakina ta nufa don karban key din ta koda ta shige ban sake mata fuska ba daga inda nake kwance ta tambayi key din ta na nuna mata da hannu kawai ta nufi wurin ta dauka.
Harara na bita dashi tana ficewa daga dakin andan jima kadan sai gata ta dawo dakin daga ita sai wani dan guntun tawul da ta daura iya cinyan ta tana tambayana wai ban rage abinci ba in bata.
Wani kallo nayi mata nace inda kika fito gantalin ki kwana da kwanaki baki kici abinci bane acan ?
Tace kin san yanzu wata yayi nisa ba wani abin kirki ake samu ba sai maneji nace sai ki je gaba ki nema ni banyi abinci ba yau.
Ta ce khady yaushe kika fara rowa haka ba halinki bane rowa nace ban dafa ba nace maki ashe karyan iskanci kike yi da zaki dawo kwana da kwanaki hannu empty.
Ta dan tsaya jin ganin ban kulataba ina karatuna sai ta fice min daga dakin dagowa nayi nabita da kallon mai kama da harara har tafice daga dakin.

Bayan ya gama saurare abinda malam sani ya gaya mashi jikin shi ne yayi sanyi karshe yayi mai godiya tare da jaddada mashi kan kada ya fada ma Nafisa komai ya dai saka ido ga alamarin ta kawai.
Bayan fitan shi gidan nine na fado mashi a rai wayana ya kira mun gaisa dayake shi mai son wasa ne nan yajani da wasa wanda bai wuce hiran mijin buzuwa.
Yace gobe dai weekend ne ba shiga aji ke nan nace eh sai dai ina son zan fita zuwa wurin wankin kai don ina son gyaran jiki gobe dai.
Yace ashe shi gyaran ma sai anje wani guri yin shi dariya yaban don irin zolayar shi nace ana mace ba gyara ne yace kwarai kuwa har in ta san kanta.
Karfe nawa zaki ya tambaya nace wuraren goma zan tafi nasan zuwa karfe sha biyu ko da rabi na gama yace da safe banda time da nazo na kaiki sai dai ki fada min sallin din da kike zuwa in duba ki idan na rarage abinda nake yi.
Nace No kabarshi kawai ba wani nisa yake dashi da inda muke ba nagode yace aini nace ki fada min ko nace beauty hair drasses na fada mai layin da yake a saman babban titi.
Munyi sallama ina mamikin halin shi da saurin sabo irin nashi na zauna na tsefe kaina a cikin daren nan don kada in makara in samu mutane a wurin.
Washegari da safe na shirya na isa sallon din ba wasu mutane dayawa don haka nabi layi sai da akawanke min akai min drying din shi kafin su fara min kitso.
Ranan nasha gyara sosai na jiki daidai zan fito sai ga wayan Yusuf shigo yana tambayana ina wurin ko wuce nace an kusa gamawa nan da minti talatin zanbar wurin .
Nakashe wayan akaci gaba da min gyara sai yaba yawan gashina da tsayi suke yi nidai murmushi kawai nake masu ban wani dogon magana da kowa a wurin.
Sun fito daga kubuwa duban fili da sukaje gani a hanyansu na komawa gida yaga Yusuf ya dauki hanya bai iya magana ba yana aiki a system din shi kan shi a duke yake.
Sai dai yasan ba hanyan gida Yusuf ya nufa dasu ba aikin da yakeyi ya dauke mashi hankali a lokacin ganin ya tsaya a bakin wani gyaran jiki na mata yasa shi dago kai yana tambayan shi ina ne nan kuma ?
Kafin ya bashi amsa yaji yana fadi a wayan shi fito gamu a kofa idan an gama maki nace gani tafe na fito tun fitowa na ya hango nice tafe kallon mamaki yake wa Yusuf din.
Har na karaso bakin motar nasu sai a lokacin nasan tare suke dashi fadi yusuf ke yi da na karaso wai wanan haduwa haka fa kanwata .
Kaike kara zuzuta yayi maganar kamar bashi ya fada ba yace ba dole ba in zuzuta kanwata yar gidan mama wanan ai kyasa ayi karo a hanya nidai murmushi kawai nayi mashi.
Na fara gaida su yace shigo mu sauke ki mana ba hostel zaki koma ba nace a a nagode yayana ku tafi abinku kawai dakai dayane zan shiga amma dai ku tafi kawai.
Yace au don wanan miin buzuwan da kika gani ai bashi ke jan motar ba ko shiga muje don ki kawai muka biyo nan fa.
Jin haka yasa na bude motar na shiga batare da na sake wani magana ba shiko sai aikin shi yake yi kawai ana tafiya mun kai wurin wani babban shago yace don Allah ku bani minti biyu in dawo.
Ya faka motar yafita sai mu biyu a cikin motar kowa da abinda yake yi a lokacin sai can naji yaja tsuki yana kallon shagon na dauka dani yake yi nace dakata malam bafa kai ka dauko ni ba da zaka ja min tsuki haka.
Da mamaki ya dago kai yana kallo yace ke dani kike nace da wani nake haka kawai zaka kama jamin tsuki a mota da mamaki yake kallo na yace ke wata irin yarinya ce da bata da tarbiya.
Kadai gyara maganan ka malam tarbiya ai ko makaho yasan akwaishi nan sai dai a lalaba a gani ai ba bace marasa tarbiya suke ba.
Bai kai karshen magana ba cikin zafin nama da kunar zuciya ya juyo inda nake yace wa kike nufi baida tarbiya cikin muryan nan nashi mai dadin saurare da yake rowan ta.
Tsoro naji ganin irin kallon da yake bina dashi mai kama da harara ko tsana sai nayi kasa da kaina na kasa furta komai don kwarjin da yai min a idona
Ya nuno yatsan shi daidai saitin fuska na tare da tsure ni da idanuwan shi lumsarsu yana fadin ke in badan Yusuf da bai san ciwon kan shi ba har kucaka irin ki ta isa ta shiga min mota na a tare dani.
Yace kallani nan ko a hanya nagan ki baki isheni kallo ba a cikin mata don banga abin gani a wurin irin ki ba cikin dakiya da dauriya nake kallan shi ina jin kalamin shi har cikin raina sai dai ina tara abinda zan mayar mashi ne a zuciya ta duk da naji tsoran yanayin shi.
Yaci gaba da fadin idan baki hankali da ni ba watarana sai na balbala ki wallahi don ni mace bata kawo min raini nace dashi.
Don Allah malam matsamin bakumayi mamaki jin haka don ba abin mamaki bane don ka fadi hakan tunda dama kai irin maza nan ne dake raina jinsin su sai kai ido ga mata ketere saboda zalama irin na rashin sanin ciwon kai.
Don wanan matar taka abin kyama ga jamma a da kai ka mayar mutum har kake ganin tafi ko wace macen kasan nan dadin abin dai kaima macen kasan nan ta haife , , , ,
Fat naji yakai min bugu a baki don zafi sai da na dafe baki na ina dubawa ko jini yake min ban san lokacin da idona ya fara fitar da hawaye ba na yun kura zan fita daga motar yasa hannu ya danna lock mutar ta rufe kit yace kuma ki saurare ni.
Duk kika sake ganina a mota kikayi gigin shigan shi sai ya jefar dake a waje mota ya take ki kin mutum in kashe ki in kashe bazan .
Nace ni wallahi ba banzan bace sai dai in kaine yace bakin naki bai mutu bako yana kokarin kai hannun shi ya kamo baki na na noke kaina a kafana sai bai samu kama bakin nawa ba.
A daidai lokacin Yusuf ya iso wurin da manyan ledoji a hannun shi yana bude motan zai sa ganin mu haka yasa shi ya sake murmushi.
Ina jin shi nayi saurin dago kai nace mugu kawai azzalumi yace kai yaya haka may kai mata don Allah take kuka kuma ya waigo zai kara jamin baki na noke ina son fita a motan Yusuf ya tare ni yana fadin haba dai yaya zakaci zalun ta kuma haka ?
May tayi maka haka wai kasa ta kuka ya juya yana cewa bakin nan mai rashin kunya na daka ido ya zaro yana cewa ka dake ta Abdul ?
Kadan ma ke nan nayi mata ai fita nake son yi ba hanya don Yusuf dake wurin yayi rufe kofan ya zagaya ya shigo motar sai da muka fara tafiya yace ka bata hakkuri Abdul.
Ina baya ina kuka naji ya fada mai hakan yace nace ka bata hakkuri yace wani zanba wanan yariyar hakuri ko wa yace bakai ka zalunce ta don may bazaka bata hakkuri ba ko kafin ka tafi da hakkin ta ne a kanka ?
Baiyi magana ba sai aikin shi dayaci gaba dayi yace wai may ya hada kune haka da sauri nace zagina yayi na rama.
Motar ya tsaya a kofa gidajen mu na fita da sauri ya biyo ni yana kirana ban tsaya ba wata yar gidan yaba kayan ta shigo min dasu suka tafi ban san yadda suka karata ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: A raina sai mamaki nake wai wanan matashin da nagani wanda bai wuce ace yanzu zaiyi auren farko ba ke da mata har biyu haka.
Buzuwan nan dai da za a zauna a fadi gaskiya tana iya girmay mashi daga shi har matar shi sai idan ance yanayin jikin su kawai da ba a gane hakan.
Ita kuma Fatin baka ce sai dai da zata zauna ta gyara jikin ta banga abinda buzuwan nan zata gwada mata ba sai dai kasshh yanayi irin namu na matan hausawa yana cin rayuwan ta da haka nake hango buzuwa ta kwace mata miji .
Yau da gobe sai Allah dama sati uku zanyi don hutun ba yawa shiyasa ban so zuwa kaduna ba a wanan lokacin amma anty na ta dage sai nazo ita kadai ne a gida mijin ta yayi tafiya.
Ashe kuma da rabon mu kwasa da matar mulki ne a garin ya kawoni don haka shiri nake inda ba komai nake shiryawa sai kayana don ban daukan provition da ga gida sai na tafi can nake saya.
School zan wuce direct sai nakwana biyu zan shigo mina in masu weekend in kwashi abinda na samu in koma bayan kwana biyu don haka nake ta shirin komawa makaranta a lokacin.
Kwatsan da safe muna karyawa saura kwana biyu tafiyana sai ga wayan mommy ta bugo ma anty wai Fati ta dawo gida yanzu haka tana nan gidan su naji anty na fadin o o Allah yanzu matan nan da karfi da yaji sai ta raba wanan auren take nufi.
Banji may mommy ta fada mata ba nadaiji tana fadin gaskiya haka nane idan abu yaki sai ayi hakkuri kada zumunci ya baci idan abin ya sake shi inda rabon komawan ta gidan sai ta koma.
Bayan ta kashe waya tace mummy tace ki shiga kafin ki wuce kada ki tafi baki sallamay su ba nace haba anty may yasa kika fada mata zan wuce ai sai yazama kamar roko idan naje sallaman su.
Kai ta girgiza min tace ba haka halin su yake ba dauka na sukeyi kamar wata ta gida a gurin du duk zuwa kikayi kika wuce sai sunyi min korafin hakan.
Shiru nayi sai tace o Allah sarki wanan buzuwan dai ta hana Fati zama gidan mijin wai yanzu kuma ta kara fitowa tace bazata koma ba.
Dudufa baifi wata da ta koma gidan na yanzun kuma ta kara fitowa jiya wai sai dai na shiga inji may kuma ya hadasu fada yanzu.
Takaici bai barni nayi magana ba sai dai a zuciyana nake bankawa mijin zagi da rana su binta suka shigo gidan mu anan muke jin labari wai tunda ya dawo buzuwa taki bari ya ke be da fati hakan bai isheta taja Fatin da fada har tana fadin sai ta kashe ta.
Shiya ba Fati tsoro tace barin gidan yafi mata nace shike nan ta samu galabanta ai ta kashe ta din idan ta isa mana.
Gaskiya matan nan ta samu wuri da yawa wallahi nace shiko sokon yayan naku fa may yayi a kai tace jiya baban mu ya kirashi sai cewa yayi shi yagaji da halin fati tana bata mashi suna.
Ai wallahi idan da nice tace sai ta kashe ni da na nuna mata hauka ke matsorata ne fa iskancin abaki yake masu kawai Fatin dai ne wallahi she is to slow .
Anty tace khadija baki san aure ba fa shi wanda ake abin a kansa bai nuna wani feeling din shi akan ta gara dai da ta hakkura ta basu wuri.
Zata tafi nace barin bisu daganan in masu mommy sallama tun ranan da mukai fada da buzuwa ban sake shiga sai yau da zan tafi sallaman su da anty ta matsa min.
Tsab na shirya na fito cikin wani dogon riga mai hannu shara shara shara da gyalen shi na yafa akaina sai turaren da na fesa a jikina.
Mun shiga gida inda na fara zuwa dakin mama na gaida ita sai na fito naga anty amarya a waje anan na gaida ita har zan wuce tace khadija ashe haka kike ina ganin ki shuru shiru dake ashe ke ma jaruma ce ban sani ba.
Dan guntun murmushi nayi nayi kasa da kaina kawai dakin mama na nufa ina jin suna maganan a waje da mai masu aiki na shige wurin mama in gaida ita.
Tana zaune a falon ta tana waya haka yasa na samu wuri a kasa gefeta na zauna ta gama wayan ta dago kai cikin fara a tana fadin yau khadija ne gidan nace mama ina kwana.
Ta amsa min fuska a sake nace mama nazo in sallamay ku gobe zan koma school tace a a har hutun ya kare wanan karon nace eh mama.
Ta sake cewa gida zaki ko Abujan zaki wuce aa zan wuce school ne daga nan tace barin baki tsaraban yan makaranta ko nace mama da ki barshi ai ba zan dauki kaya daga nan ba sai naje can saya.
Tace a a wanan kan zaki so dambu ne da akai ma yayan zai tafi dashi kin san yana son dambun nama sosai shine na aikai mashi shima gobe zasu tafi.
Ta mike ta shiga daga ciki sai gata da roba dan madaidaici ta fito da kudi a hannun ta ta miko min nayi godiya namike zan fita ko ba a fada ba yanzu na sheda wanan kamshi ba kowa bane sai dan ta Abdulsamad mijin buzuwa.
Zai shigo ni kuma zan fita ban yi tunanen in kauce mashi ba a lokacin dole suka jaye a hanyan na fita ashe da buzuwa suke tana bayan shi.
Mama ce naji ta kwala min kira sai na dawo wanan karon sai da na bari sun gama shiga na shiga dakin nima na karasa wurin ta gwiwa na biyu a kasa na zube ina fadin mama gani.
Buzuwa ke gaida ita ta tsaya amsawa ta dago tana cewa dan ta gobe ne zaku tafi din ko yace insha Allahu mama yanzu ma mun zo mu sallama ku ne don goben sakko muke son yi dan zan shiga office.
Ta juya gare ni tana fadin gobe sai ki shirya su tafi dake indan zasu wuce gaba na ya ba da damm da sauri nace a a mama ba tafiyan safe zanyi ba ni.
Khadija yayan ku ne fa ki shirya ki bishi yafi shiga motar kasuwa su wuce da ke shidai baiyi magana ba ya rike goshin shin da hannu guda .
Sai buzuwa ne tace motar tamu ai a cike take dayan ni dashi ne sai driver dayan kuma na masu aiki mun ne su larba sai na security din mu .
Naku zata shiga don ita din ba bare bace yar gida ne kaji na fada maka tau mama yace ta shirya da safe din kada ta makara sukuku na mike tare da fadin mama na gode.
Fitana dakin mommy na tafi ina nuna mata abinda hajiya mama ta bani tace ai yaya tafi danan ban fada mata zancen bin mijin buzuwa da tace in yi ba a lokacin itama daki ta shiga sai gata ta fito min da wani bakin dogon riga da takalma cikin na sayarwanta tace ga wanan a samu na sakawa.
Binta ce ta shigo dakin tana dariya mommy tace maynene kuma tace khady nakewa dariya mommy mama tace da yaya gobe su tafi da ita.
Ga buzuwa can tana fada bayan fitar mama daki wai bata yarda ba bata san mama ta jita ba shine mama ta fito tana fadin har ta isa tace ga abinda take so tace ita bata yarda ba yaya ce shi baice ba zata bisu ba ai.
Juyowa mommy tayi ta kalle ni nace nifa ban iya bin su gaskiya don idan tayi min wallahi nima yi mata zanyi gara ko kada in bisu din.
Dariya take min mommy tace akan may kin samu sauki bazaki bisu ba ai shi Abdulsamad baida hakana tunda har yaya tayi mai magana da bai daukan ki tun a nan zaiyi magana balle yanzu da yasan yaya tana hake dashi ai ba zai so ya bata mata rai ba kuma.
Daga cikin dakin mommy anty Fatine ta fito tana saye da wani hijjab har kasa fuskan ta duk ya kode alaman tasha kuka har ta gaji.
Gaida ita nayi ta amsa kasa kasa ta zauna a daya daga cikin kujerun falon mommy tace kin tashi tace eh mommy tace ga mutanen ki can sun shigo sallaman mu zasu koma gobe wai.
Shiru tayi batayi magana ba sai mommy ta kara cewa kin san yaya da son jan magana wai cewa tayi gobe su wuce da khadija da zata koma makaranta goben.
Wai ai ba zata bari ba wallahi bata son kowa ya rabe shi balle wanan da take gani mace haka maikyau kuma gasu da wata a kasa daman.
Aiko banyi niyan binsu ba da amma yanzu sai na bisu tunda abin haka inga yadda zatayi a motan dani idan na shiga.
Murmshi mommy tayi tace ki shirya da wuri don shi da wuri yake tafiyan shi idan zai tafi tashi nayi nayiwa mommy sallama muka fita da binta ta rakani.
Naje gida na nuna ma ya Amina tsaraban da suka bani don da zanfito anty amarya taji zan wuce ta dauko min wani set din turare mai kamshi ummi ce bata ban komai ba a cikin su.
Sai can muna hira nace ya Amina kinsan wai mama cewa tayi in shirya gobe in bi mijin buzuwa da buzuwa idan zasu koma.
Da sauri tace may ne ?
Nace wallahi da banyi niyan binsu ba amma tunda ta nuna bata son haka zan bisu din inga yadda zatayi dani a hanya .
Nidai wanan zuwan wai damay yazo muna haka ne da tarihin buzuwa ko damay yanzu ke binsu din zakiyi, ba zaki hakkura kibi motar kasuwa ba.
Don mama ne kawai zan bisu kada in bata kunya tunda tana sin gwada masu ikon ta ne a kan su da kuma ita buzuwan zantafi.
Da yamma sosai na fito zan shiga gari in karbo dinkina da nakai ina fitowa bakin get sai ga motan shi tundaga nisa na kawar da kaina don ban san wanda ke cikin motar ba sun kawo kusa dani na gane su ne na watsa mai harara na kawar dakai.
Yusuf wacece wanan yarinyar wai da nake gani a gurin mama yarinyar bata da kunya ko yanzu baka ga wanj harara da ta watsa muna ba kullun shi take min fa har a falon mama da muke haduwa.
Dariya Yusuf din yayi yace amma kuma tana da kyau gaskiya koda yake kai yanzu baka ganin kyaun mace gaka da buzuwa a gidan ka.
Wai Yusuf may ya kawo wanan magana haka daga tambayan ka yarinya idan baka santaba kace kawai baka santa ba period.


Please Login or Register in order to submit comment