Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tafka jiya din akan bakin kishin dake damun zuciyar ta akan mijin ta wanda take mashi son daba taba yi ma wani abu ba sai dai kuma a kasan zuciyar ta ba so bane can na har abandan don da zai iya shiga wani halin jarabtan rayuwa a yanzu tsaba zata iya gudun shi ta koma wa mai maski.
Wayan nata aka kira ya hanata karasa muna jin birnin zuciyar sai ta dan sake guntun murmushi tana daukan wayan nata tare da fadin Aloh ina kika shiga nake ta kiranki baki daga waya ba.
Cikin muryan barci madam din tace tana hamma baki hangale bata fasa magana duk da tana hamman tace wallahi barci nakeyi tunda rana.
Tsuki Nafisa taja tare da fadin barci sai kace wata mai ciki ko kasa ni don Allah watseke fuskan ki kiji ni magana nake son muyi dake ki ban shawara.
Madam tace ina jin ki matar manya dadi Nafisa take ji idan su madam na fada mata wanan sunan madam din ne tace ke nake sauraro fa.
Wallahi ke dai madam kin san ko sai da munafukar tsohonwan nan ta hadamu da yarinyar da nake fada maku tace mu rage mata hanya ?
Don Allah ki bari madam ta fada itako tace sosai kuwa ai saida muka dauke ta a mota daya mukai tafiyan.
Tace yaya kika bari haka ya faru don Allah kin ko san iein mijin ki neman su mata keyi ido a rufe nasha fada maki ki nisanta shi daga ko wace mace in ba muraharamin sa bace har kika yarda hakan yafaru dake.
Ke dai bari madam nanu mashi rashin yarda na ga hakan amma ya rufe ido yace shi yace umurnin mahaifiyar shi ce dole ya bi.
Madam tace yaya kukayi a motar injin baki basu daman sakewa da juna ba a motan ?
Tace ai in fada maki ban yarda ko daga kai yayi ya kalle ta ba kuma nima ban sake ayi hakan ba sai dai mun kwashi rikici dashi sosai da muka iso gida wai zai tafi office a sauke shi sai a wuce da ita.
Bude mashi wuta nayi sosai in fada maki sai da mukayi kaca kaca dashi na kuma hana shi fita sai da aka kaita a ka dawo san nan ya tafi.
Da haushi da bakin ciki ya kamani duk na farfasa kayan falon nan gaba daya don in nuna mashi bacin raina don gobe kada ya kara min haka.
Madam tace kash aike kinji matsalan ki ke da zaki bishi da lalama ki nuna mai ba wata mace sai ke a duniya daga baya sai mu sake shirya wa tace.
Madam idona ya rufe a lokacin da kishin ganin wanan yarinyar a kusa dashi amma da ya fahintar dani shi irin su ba su gaban shi shi yanzu wace mace zai kalla ta bashi sha,awa sai naji hankalina ya dan kwanta a lokacin.
Madam tace amma kin so ki bada mu wallahi kai kin ma dai kwafasa wallahi yanzu ke ko irin matan abujan nan ya lalubu maki har ki ta da hankalin ki haka mudake da wuka a hannun mu nama kawai muke jira.
Kawai yanzu idan ya dawo kije ki bashi hakkuri akan abinda kikai mai din don kada ya zarge wani abu a gare ki.
Kin ga zaki ji a bakin shi ko ita wanan yarinyar wacece a garesu kin dai san yadda zaki bugi cikin shi ai muji komai a saukake.
Tace zanyi kamar yadda kika ce din amma ba yanzu ba zan dai saka ido in gani idan suna tare ko basu tare sai musan abinda zamuyi daga baya.
Sun dauki lokaci suna maganan akaina ana ta kulla sheri da tugu akan mazajen su kafin suyi sallama madam tace zata kira zuwa gobe taji indan da wani matsala kuma.

Na gama shiga da komai daki na da taimakon wata yar gidan namu da ta dawo tagan ni da kaya ta tsaya taimaka min.
Kayan jikina na fara cirewa san nan na fara gyara kayan ina aje komai a inda nake bukatan shi na gama na zauna ina tunane a raina.
Bakomai nake tunane ba sai mijin buzuwa da Allah ya jefo a rayuwana a dan lokaci ya taimaka min yau gani da kudi a hannu na wanda yakai dubu dari ta dalilin mijin buxuwa da iyayyen shi duk na samay su.
Waya na dako a cikin handbag dina ina neman layin ya Amina don in fada mata abinda ya faru don komai ya faru dama nakan kirata in fada mata.
Kira uku ta daga wayan ina ji bata kusa da wayan ne a lokacin mun gaisa nake tambayan yaranta tace suna lafiya sun tafi islamiya.
Nace anty kin san wani abu da ya faru yau tace ina zan sani Khady nidake kaduna zaune kina abuja ke.
Nace anty yau na hadu da mijin buzuwa danaje sayayya tace kun sake haduwa kuma again nace wallahi anty wai duk wanan uban kayan da na sawo nazo biya sai ake ce min ai ya biya bayan da suka sauke ni ranan ya ba driver dubu hamsim ya bani.
Kai da gaske khadija nace wallahi anty kuma su suka kaini gida sai dai shi bai so su dauke ni ba sai abukin shi ne yace saboda mama ne suke min haka.
Dariya tayi tace to Allah ya saka da alheri ki dai bi a hankali inda duk kuka hadu don buzuwan nan ba imani ke gare ta tana iya komai akan mijin ta.
Ya Amina ni inama zan kara ganin shi kuma Allah dai ya tsaga rabona daga Aljihun shi wanan karon mutumin da ko yaushe take a cikin hade fuska banda gaisuwa may zai hada ni dashi kuma.
Daga haka muka kawar da zancen shi muka dauko na iyayyen take fada min cewa sunyi waya da baba yana fada mata kudin su na ritaya ya kusa fitowa kwanan nan.
Ihun jin dadi nayi don murnan iyayyen mu zasu fita acikin hali talaucin da suka shiga na ritayan da mahaifin namu yayi muke cikin halin kaka nakayi.
Tace ai zan riga ki ji idan kudin sun sauka don haka sai abinda kika samu daga baya nace ai ni indai daddy zai samu bukata na ya biya ke nan.
Yanzun ma shawara nakeyi inje banki gobe in tura mai kudin da mijin buzuwa ya bani don akwai kudaden da zasu isheni a hannu na tunda ina da abinci waddatace .
Tace haka akeso mutum idan ya samu ya tuna da iyayyen shi dama dako kin kyauta wallahi dama sallaman ki ya hanani tura mashi kudi wanan watan.
Haka dai mukai ta hira da ita daga karshe mukayi sallama na kashe wayan tare da mikewa na jona electric dina don in dafa dan abinda zanci da dare.
Kira, a na saka a wayana ina aiki ina bin kira a don ni gwanace a wurin iya hadda tun ina yar shekara sha hudu na sauke alkurani mai girma na sake maimaitawa yakai kashi uku yanzu don duk wanda yasan yaran minna ya sansu da ibada da kamun kai ga girmama na gaba dasu a duk inda suke.
Da wanan halin namu nake shiga ran mutane farat daya kowa tsakani na dashi gaisuwa ne na mutunci da sani girman wanda ya girmay mun.
Na gama na zuba a plate na dauko ledan ruwa guda cikin wanda na sayo na aje a dakin na zauna don in fara cin abincin sai ga kiran waya ya shigo min.
Binta ce ta kirani a lokacin na dauka kafin wayan ya tsunke hiran mukayi sosai ranan da ita har nake mamakin ko nawa ta sa awayan ta haka don da mun sake wanan hiran take dauko min wani.
Har take fada min yadda akayi ranan da zamu wuto da buzuwar yayan su tace bazata shiga mota dani ba mama ta dage daya zo mata da maganan kan lalai sai sun tafi dani.
Nace kin ko ga tunda muka kama hanya batai min magana ba nima ban masu ba daga ita har mijin ta.
Tace wanan ai dama shi miskili ne magana kamar aiki yake ganin sa a gare shi zai iya zama da kai kuyi awa daya baice uffan ba haka kuma matar shi anty fati itama take shiru shiru bata magana.
Nace aiyanzu sun samu mai magana a tsakanin su haka yasa ta samu daman musguna mata yadda take so ai.
Tace ke kin ko san halin wanan matar shu,uma ce wallahi ta karshi da farko da tazo boye halin ta tayi kamar wata mutumiyar kwarai da ita.
Sai daga bayane ta fitar da kalar ta kowa ya sani bata kaunan ko dan uwan yaya ta ganshi a gidan nan wallahi.
Nace wuri ta samu wallahi ni kar nake kallon ta don banga abin tsoro ba anan ku dai na fahince ku kuna bata girma ne don mijin ta yana da hali a cikin ku.
Tace ga tsiya nace eh mana haka din ne amma in bashi ba ta yaya zaku zauna wanan matar ta dinga raina maku hakali har tace wai idan tana wuri kada ayi dariya .
Tace ina ma kika sani khadija ai sai wani lokaci da mukaje hutu wurin su a abuja ba girma muka dawo gida kwanan mu biyar ko sati bamu kai ba matsi yai muna yawa a gidan.
Muka matsa ma yaya zamu dawo ga yan uwanta nan muna ganin yadda take ji dasu amma mu ko falo ta hana mu fito muka koma kamar wasu bare ba yan uwan maigidan ba.
Dariya nake mata sosai tace Allah ko magana mai karfi wai ba ai mata a gida tace ba kallo ba komai sai zagi da hattara ga anty Fati damu da ita duk muka koma daya.
Bayan mun dawo sai ga anty Fati ma ta dawo wai a kaduna zata zauna bata iya zama da buzuwa a abuja bata bari ko miji ta gani idan yana gida.
Nace ke ki bari don Allah ashe ba karamar shuuma bace tace baki santa bane Khady wanan fa ko kashe mutu tana iyawa fa.
Nace wanda Allah yabata ikon kashewa ba wani kan ai yafi karfin ta wallahi ba abinda zata iya wanda Allah bai tashi yi da bawan shi ba.
Ni don Allah har kin ban haushi da wanan maganan naki don ba a gidan ku nake ba wallahi da taga tsiya a guri na nifa irin matan barikin nan haushi irin su nake ji.
Zako kiji nata don bata da hali mai kyau ko kadan akan mijin ta zata iya yiwa mutum komai musan man ma ce ko waya tayi da wata ranan sai sunyi jidali sosai da ita ke ta zama mai kaya ko shi yanzu bai da yadda zaiyi da ita ne kawai wallahi.
Nace ya dai ga dama ne Binta idan ka ganshi ga mutum har mutum amma baida kuzari gun mace tir yayan ku ya zama mijin hajiya wallahi.
Haushin abinda na fadi taji da fada muka karasa wayan a rana na kashe ina mata dariyan shakiyanci na gama na wanke kayan na samu wuri na kwanta.
Washe gari da wuri na fita don ban yarda in makara in ba wani dalili ya tsayar dani ba mai karfi shi kadai zai sani makara kawai.
Ban da yawan kawaye sai mutum biyu yan department din mu kosu shirin mu dasu don sun ga nafisu kawo wuta sosai a class din shine likewan su dani.
Banda wasa ga abinda ya kaini abujan daga school sai gidan mu sai ko idan wani dalili zai sa na fita a ranan zan fita.

Yau ya dawo a gajiye don daga wurin aiki ya wuce wuri wasan polo da suke yi don dan wasan ni ne sosai wanda yana daya daga cikin abinda ke kawo mashi kudi a lokacin bai dogara ga aikin shi ba yana buga buga irin na maza gida da waje shike sa yana samun mahaukacin kudin da yake riko.
Wanka yayi yana saka kaya a jikin shi ta shigo dakin dan juyawa yayi ya kalle ta ya kawar da kan shi yaci gaba da abinda yake yi.
Karaso wa tayi gare shi tana wani rangaji na daukan hankalin shi ta sake abinda yake so ya sauko mata har mazaunan ta.
Cike da sallo ta iso gare shi sai dai tsiyan shi da ita duk gayun ta bata damu da saka kamshi ba kuma har yanzu ba gwanewa tayi ba da iya kwalliya shine ma yake kokarin wurin gyara mata idan tayi wani kwaliyan zasu fita.
Gata da son karya sai dai ko bokon kasar su bata samu ba kuma babu na Allah a tare da ita abin ya taru yai mata yawa amma hakan bai hana shi son abin shi ba.
Rungumoshi tayi ta bayan shi ya sauke wani ajiyan zuciya yana dan murmushin jin dadin ganin ta tace yau ina ka shige haka ne ta dawo ta gaban shi suna fuskantar juna.
Bai ce komai ba yadan jajeyeta ya dauko turare yana fesa ma jikin shi tace har da daren ma sai an feshe jiki da turare ko fita zakayi ne haka ?
Sai lokacin yayi magana yace sai zan fita ne zan saka kamshi a jiki na ke baki son kamshine ashe yasa baki sakawa .
Taji zafin maganan amma ta daure don in da sabo ta saba da gorin saka kamshin da yake mata din ko yaushe kuma hakan bai sa ta saba da sakawa ba.
Tace muje kaci abinci yace na koshi ta dubeshi da sauri tace tare da fadin ban gane ba yace mun ci abinci da Yusuf kafin in dawo.
Juyawa yayi ya nufi saman gadon su yana jawo laptop din shi tasan idan ya fara dakilan laptop sai ranta ya baci kafin ya gama.
Idan tayi magana kuma yace business yake a ciki shi ko wani abin dariya tayi ya dago yana duban ta na lafiyan ki kalau kuwa ?
Sai yaji tace maganan turaren da kayi ne dai yaban dariya har na tuna da yarinyar da mama ta saka mu dauko ranan.
Bakaji wani irin kamshi tiraren da takeyi ba kamar tayi wanka dashi yace tasan kan ta ne yasa ta saka turaren haka don kada a raina ta.
Tace shi saka turare kuma har wani sanin kai ne dashi wai ma may ye alakan ta da mama ne data nace sai mu dauko ta wai ?
Yana bude laptop din yace sai yanzu kike son jin halakan su da mama da kishi ya rufe maki ido baki tsaya tambayan ta ba da farko.
Tace kayi hakkuri cikin yanayin tausasa harshe tace nasan ban kyauta ba kishin ganin ka kusa da wata mace nakeyi tundai irin wanan yarinyar dake cikin ganuwan kurciyan ta ga kyau kuma da gani tana kuri da ilimin ta.
Ina tsoron ka hango kyawon tane wallahi kazo kace zaka dauko min ita a gidan nan wata rana son ka nake har karshen zuciya ta ka sani.
Ya tsaya yana mata wani irin kallo yace don kina kishina sai ki min hauka mata nawa nake gani a rana da ina raayin mata ne zaki san lokacin da zan nemay su ne.
Har kina fada min cewa mahaifiya ta da biyu ta hadamu tafiya da yarinyar don in so ta kika haukace har kina fashe fashe a gida.
Kwantowa tayi a jikin shi ta dan shafi kan shi tace kai min afuwa don Allah haka ba zai sake faruwa ba a tsakanin mu.
Yaji hakkurin da ta bashi har cikin ranshi yace ki rage kishin nan nake don ni din mijin mace hudu ne watarana.
Da sauri ta rufe mai baki tana fadin don Allah ka daina fadin haka don kana sa zuciya ta tana bugawa da wanan zancen kishiyar da kake min.
Yace idan lokaci yayi ai yi zanyi sai dai ki tausasa zuciyar nan naki bakiga mahaifina matan shi hudu ba kin sani ko in gado shi nima ?
Kuka ta soma mashi tana fitar da hawayen munafunci a idon ta dariya yayi mata yace akan kishiya kike wanan kukan haka fati fa ba kishiyar ki bace kin ga ai ko yanzu kina da ita ke nan.
A bar maganan Fati tace don ni kaina ma kunya nakeji ace wai ita din kishiya ta ce balle kai ace matar ka ce Fati ta sunna.
Ohh kin fison indan zai ne ma yanzu in nemo wace idon ta ya bude sosai don itace ta dace dani tace ba haka nake nufi ba don Allah mu bar zancen kishiyan nan haka na.
Tambayan ka nayi cewa wacece wanan yarinyar ne sai ka dauko min wani dogon zance kuma akan kishiya ?
Yace nima ban san ta ba a gurin mama wanan zuwan da nayi na fara gani ta koma waye dai ita nasan alakar ta da mama mai muhinmaci ne sosai.
Shiru tayi tana nazarin maganan shi daga karshe dai data ga ya fara aikin shi ta kwanta tana ci gaba da tunane kala kala a zuciyar ta.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Maryam kamar jirana take in gama debe kayan a jikina ina zama tace amma friend zurinfin cikin ki yayi maki yawa wallahi.
Ashe wanan guy din da ake nema ruwa a jallo dan uwan ki ne ban sani ba saurin kallon Maryam nayi nace ruwa a jallo ake nemas may yayi.
Tace tsadan ganin gare shi mana gashi dai matashi ne amma Allah ya kai shi ga babban matsayi nace wani matsayi ne gare shi wanda kike zuzutawa haka wai ?
Kai haba friend zakice baki san koshi waye ba kina tare dashi haka mutumin nan fa na hango tsatsan son ki a kwayar idon shi.
Nace baki hango gaskiya ba idon ki bai hango maki gaskiyan alamarin ba kuma koda kin hango ma bai taba zama gaskiyan magana.
Mutumin da gidan shi yafi karfin shi a karskashin mulkin ki mace yake wanda baida mutucin duban yan uwan shi tunda na fara magana ta kafe ni da idanuwan ta.
Shiru nayi don na farga na fara sakin layi dariya tayi tace min kin dakata kuma mana nace barni da abin haushi don Allah kwantawa nayi rigingine ina tune a raina sai kuma na bushe da dariya ni kadai.
Kallo na tayi tana mamakin abinda nakewa dariya haka ni kadai nace yau akwai bura uba a gida Samad tace akan may kuma nace ke dai bari.
Buzuwar matarshi ta bugo waya tana tambayan shi na dauki wayan nace mata gashi nan wuri na baida lafiya.
Ido ta zaro waje tace kika amsa kiran matar tashi khadija nace kwarai kuwa ina dariya nace zata gane shayi ruwa ne maryam.
Ba gani take ta mallake shi ba ba macen da ta isa tazo kusa da shi hatta uwar shi ta raba shi dasu duk yan uwa ganin su take muggaine bata yarda dasu ba.
Kirikiri ta hana matar shi zama a dakin ta dole yanzu saida ta koma gida take zaune ba ruwan shi da yaran da ya haifa da cikin shi.
Tace khadija kina nufin wanan guy din yana da iyali haka dama idan ka ganshi sai ka dauka ko auren farko baiyi ba a rayuwan shi.
Nace wa mai iyali ne da kike ganin shi wurin nan auren gata ya samu ga iyayyen su shine kuma bai iya riko ba saboda buzuwar matar shi.
Nace Wasa farin girki yanzu muka fara wasan da ita sai na manna mata karamin hauka a zuciyar ta tunda tace bata son hurdan shi da ko wace mace.
Haduwa goma zamuyi dashi sako goma zan tura mata muje zuwa indai nice ko wace mace da dabaranta ake haihuwan ta sai dai na wata yafi na wata kissan.
Khadija kin ko san kisan macen buzuwa macen buzuwa fa duk inda take shu,uma ce bata bari miji ya zauna da matar shi lafiya sai ita.
Nace maryam kin san ko matan minna ko waye su ba buzuwa ba ko tsakiyan matan maradi za a kaini na shirya mata indai akwai ayar Allah.
Zan bi dare in bi rana sai na nuna mata muma matan Nigeria akwai shu,umai cikin mu ai banda matsala tunda na san lagonta ta .
Allah ya bamu saa tace nace amin sai na girgiza kai nace bawai da manufar yaso ni har cikin ranshi nake wanan abin ba yi dai nake in nuna mata boka da malam karya ne.
Tace yanzu yaya kuka kare dashi nace korata yayi daga motar shi kai tsaye dariya ta kwashe dashi tace ai ba zaki kara ganin shi ba ko.
Nace gobe ma yayi nesa ki gan shi nan ai ni abin har mamaki nake ji wallahi tace don dai kince buzuwa ce matar shi amma da sai in ce wani namiji zai samay ki ya bari ki kufce mashi khadija.
Kyau Allah ya baki tsayi da gashi ga ilimi addini dana boko kin tara ranan da naji kina karatu wallahi har rudewa nayi na raya a raina da naje gida komawa zanyi makaranta ni ma na samu in sauke.
Tun ina karama fa na sauke maryam yanzun haka ban bar karatu ba don ina nan ne bana zuwa amma a gida ban wasa da karatu ko kadan kinga yayata malama ce sosai wallahi.
Tace ai naga alama tun haduwa na dake idan kuna waya da ita zata tana makaranta ko gata tana shiri fita makaranta may yafi wanan dadi ga mace.
Nace kinga mu zama yakawo kakannin mu zama garin minna amma aslin mu yan wani gari ne da ake kira ka,oje tun ana hade da sokoto da Niger yanzun haka mu bamu san gida ba mu filani ne na asali wallahi.
Mahaifiyar mu ce kwarin minna amma saboda zama muka juye muka zama mutanen minna baki sanin mu baki ne idan ba mun fada ma ba.
Haba nature din ki yayi kama sosai da na fulani ashe ma ke ruwan su ne nace ada ke nan ina so zuwa garin mu sosai inga yan uwana wallahi.
Don ance har yanzu yan uwan mu suna garin don daddy din mu shi yasan gari har yakan je lokacin da bai tara iyali haka ba.
Tace ya kamata ku nemi gida su san ku fa nace muna da burin haka nida ya Amina ai sai dai kin san abin sai an shirya ne .

Dakin shi ya nufa ya fara cire kayan shi zuciyar shi yana mai soya yana jin kamar ya ganin a gaban shi ya shake ni don haushi da takaicina da yake ji.
Nafisa ce tazo dakin har lokacin a hasale take daidai ya fito daga wanka ta yi mai wani mugun kallo tace yau sai ka fada min gurin wace kaje har ta dauki wayan ka ta kirani dashi.
Baiyi magana ba sai kokarin saka jallabiyan da yake yi a jikin shi ta karaso tana ce mai wata yar iska yar kasada ke son shiga rayuwan ka Samad ?
Ido kawai ya tsura mata yana kallon ta batare da yayi mata

Please Login or Register in order to submit comment