Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya isa ya cimma an ana kokarin tada iqamar sallar magrib ne,ah daidai kofar gidan yayi parking sannan ya nufi masallacin gidansu don sauke farali,yana lure da yadda Kasim keta kauda fuska don karsu hadʼa idanu,murmushi kawai ya saki ya kuma nuna kamar besan dashi awajen ba,ya gaisa da samarin gidan da kuma yabbaninsa waʼenda keta mamakin saurin dawowarshi,ce musu kawai yayi sun kammala abunda yakaisu da wurwuri ne,har aka idar da sallah Kasim be bari sun hadʼa idanu da Gidado ba don har sauri saurin saka takalmi yake yabar wajen,waigowar da zaiyi sai ganinshi yayi abayansa yana jiran fitowarshi,gabansa yayi wani irin tsalle kamar zai fado waje,jan hannunsa Gidado yayi suka koma gefe yasa hannunsa yana dan bugun kafadarshi yace''Clever boy kwantar da hankalinka ni bata naka nake ba yanzu ta budurwarka nake,wato ka koya mata rashin kunya sannan kuma kace tamun ko..?toh dafatar ka shirya cetonta don yau mai kubutar da ita ahannuna sai Allah...!ʼʼ

Ya fadʼa yana nannade hannun rigarsa tamkʼar wanda ke shirin dambe da saʼansa,ya kada kai ya shige cikin gida yabar Kasim tsaye anan da tsananin mamaki da takaicinsa,Part dʼin Yumminsa ya nufa straight ya tarar tana wanka hakan yasa ya nufi dakinsu Ramlah direct,suna can suna kallon wani india film ah system dʼin Hamma Aliyu wanda dʼa ne ga goggo Boddiya yakanzo ya yini agidan lokaci zuwa lokaci,Gidado be shaidashi awaje ba if not tare ma suka jera wajen sallah,Aliyu nada shekaru 35 aduniya kuma maʼaikacine awani industry na raw materials,daga shi har Gidado basa wani shiri don kowannensu naji da girman kai,shine jikan tsoho na biyu agidan amma ya kasance ta bʼangaren yʼa mace ne,tunda ya kyalla idanu akan Baddo yaji ta mishi kuma yanason ya aureta tunda dama can bashi da auran,be damu da kankantar shekarunta ba hankalinta ya yaba mawa,ammh sedai ko kadan be beri ya fallasa mata sirrin zuciyar tasa ba,zai samu tsoho ne da zancen,tunda su Ramlah suka dawo daga gidan Gidado suka cimmasa shine fa suka hanashi sukuni sai fira don tanan ne yadan banbanta da Gidado akwai sakin fuska ga kannensa ammh bandasu OA😅,dazai tafi sallah shine Ramlah suka kwace system dʼinsa dake su mayun kallo ne suka nufi daki dashi,aka baje saman gado ana kallo,ita dasu Hanifa da Baddo,su wajen biyar,suna tsaka da kallon sai ganinsa sukayi ya fadʼo dakin tamkʼar an jefoshi.............✍

_*Wayyo Allah Gidado meh kayi haka ne?😭 tofa ga wani Aliyun ya danno fa kuma wai shima din baddon yakeso😳koya zata kaya..?muje zuwa...*_



_*4 extra free pages remaining purchased by Nanarh Ayeesha buh mind you registration is still goin on😜*_

_ku nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_

*🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
     _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

_*💍NANARH AYEESHAʼS PAGE..!😘*_

  _*💫BABI NA SHA HUDU..💥*_

!...Ramlah ce tayi saurin shutting dʼin system dʼin jiki na rawa ta sakko kasa tana hawaye,sauran ma suka mara mata baya ammh banda Baddo wacce tayi kokarin danne tsoronsa taki sauka,koda taga yana kwance belt kin motsawa tayi ammh badon bata tsoron bane kawai kʼarfin hali da kuma kokarin nuna jarumta mutuniyar take,rinannun idanunsa kʼyam akanta yana mamakin sabon sauyin da aka samu atattare da wannan yarinyar wai kwata kwata ta dena tsoronsa,taya ma akai yayi sakacin da har hakan ya faru ne..?ammah ai babu damuwa yanzun nan kuwa zai maishe da tsoron nashi cikin zuciyarta ya zamana ma ko karo taci da mai kama dashi saita firgita,su hanifa ne suka kawar mishi da gajeriyar hirarshi da zuciyarsa,hawaye duk ya gama wanke musu fuska sukace cike da tsoro''Hamma...plsss..kayi..hakʼuri..bazamu..sake..ba..wallahi...ʼʼ

Hannu yasa ya datse lips dʼinsa yace''shhhhh...! Kumin shiru anan..duk saina ci ubanku dama kunyi complete basai naje neman wata awani wajen ba,yadda kuka hargitsa mun gida dazu toh billahil azimu kuma sekun jishi ajikinku..!ʼʼ yana ida magana ya nufi bed inda Baddo ke kwance ta sake budʼe system din da Ramlah takashe ta cigaba da kallonta tamkar bbu abunda ke faruwa ammh deep inside her tsoro ne fal ranta tana kokarin dannewa ne kawai hakan kuma ya dadʼa fusatashi,bata ji zuwanshi ba sai kawai jin saukar belt ajikinta,zaffffff! kakeji kʼarar dukan kenan,wani irin hantsilawa tayi sai gata akasa ta fadi timmm! kusa da yanʼuwanta ta dʼaya bʼangaren gadon,afusace ya sake tunkaranta yake fadin''Shegiya wato kece meh bone head baki tsorona shiyasa kika cigaba da kallonki ko...?inason ki gayamun ko yaushe wannan rainin ya shiga tsakanina dake in ba haka ba kuma yanzun nan zan farfasa jikinki...!ʼʼ ya ida magana yana karkada belt dʼin,tuni su Ramlah aka fashe da kuka har ita Baddon ammh sai ta runtse idanu taki kallonsa don kallonshi kawai na tsinkar mata da gaba balle yakai da tabʼa lafiyar jikinta,''budʼe baki ki soma bayani or else iʼll disform you,sake maimaita abunda kika fadʼamun awaya dama kince na addana duk wani kalma har sai mun hadu gaba da gabanta,toh gani ina jinki yi bayani,can you die of constipation..?I asked becuz am worried about how full of shits youʼre...!ʼʼ

Sake zabga mata belt din yayi yana fadi cikin daga murya''kin tuna ko kuwa saina kʼara miki..?i dnt want to die of constipation so can you help me..?tukunnah ma dai uban waya koya miki irin wannan dirty insult dinne haka..?abokin cin mushen naki right..?

Afusace Ramlah ta mikʼe zatayi waje tace''wallahi saina hadaka da Yumma kazo kawai kana cin zalinmu...ʼʼ wani irin fuzgota yayi ta dawo da baya sai saman gado ta fada,ya shiga tsula mata belt tana ihu yace''Bari na soma cin zalin naki dakyau kinga kin samu kwakkwaran hujjar gaya mata,ina ganin daga rana irin ta yau ko amafarki bazaku sake zuwa gidana bama balle ku hadʼa fada..!ʼʼ

Bulala shidda masu lafiya yayi mata sannan ya koma kansu Hanifa suma irin nata dai yayi musu sai ya rage Baddo akʼarshe...

     **********

Yabban Gidado ne ya jero da Aliyu bayan sun idar da sallah,sai tsokanarsa Yabba yake akan shi dai yaki aure,''Ko kuwa so kake ne sai mun bayar dakai sadaka tunda kayi kwantai..?ʼʼ Yabba ya fada yana fadada faraʼarsa,susa kai Aliyu yayi kan yace cikin kasaitacciyar muryarsa''haba dai yabba da ajina da komi na sai ace zaʼa badani sadaka..?ai abune wanda bazai tabʼa yiwuwa ba...ʼʼ

Saurin taran numfashinsa yabba yayi''Toh Aliyu ruwan idon meka tsaya yi ne harna tsawon shekarun nan bayan ga yan mata nan birjik agari sai wanda ka zabʼa..?ga kannan bayanka ma nan duk sun gama aure sun barka,daga mai yaʼya biyu sai fiye da hakan ko kuwa so kake ne muzo muna daura auren baba da yaʼyansa arana guda nan gaba...?ʼʼ

Dariya ya fashe dashi don maganar ta daki zuciyarsa ba kadan ba,shi kansa yabban dariyan yake mishi yace''Eh man gaskia na fada ai,azo ana daura auren uba da yaʼyansa arana guda,ai kuwa da mun buga abun ajarida duniya ta gani,idan har bakason hakan ta faru toh ina son acikin kwanakin nan ka kawo mana mata kace wannan nakeson na aura kana jina ko..?in ba haka ba sadaka zamu bada kai...ʼʼ

Murmushin kasaita Aliyu ya sakar gami da sosa kʼeya yace''Yabba basai ma ankai nan ba don ayau naga wata fure acikin gidan nan kuma harga Allah da aure nakesonta....ʼʼ cike da farin ciki yabba ya washe hakʼora yana fadin''Tofa masha Allah kai kuma anan Allah ya hadaka da taka furen yʼar dangi..?abu yayi dadi wallahi kuma sosai zaka kafa tarihin da baʼa tabʼa bari ba acikin wannan zuriʼar wato auren dangi,na tabbata ba tsoho ba har sauran iyayen naka zasuyi matukʼar farin ciki da wannan dadadʼar zancen,ammh kayi hakʼuri ban tari numfashinka ba wacece halan..?

Adaidai lokacin suka shigo katafaran falon,bekai ga bashi amsa ba suka jiyo kururuwa,saiga Yumma ma ta fito agigice da daurin kirji sai hijab data zura don wanka ta fito,kallonsu tayi ganin sunyi cirko cirko suna mamakin inda iface ifacen ke fitowa,Yumma tace''ku baku jin ihun yara na tashiwa ne kuma ina tsammanin su Ramlah ne Allah dai yasa ba fada suke atsakaninsu ba yadda ma naga sun wani likʼewa juna yau,ina tsammanin wani sabon yʼan matancin ne ya taso musu...!ʼʼ ta fada tana nufar dakinsu Ramlar ayayin dasu yabba ma suka rufa mata baya,Aliyu na lazimi da counter dʼinshi,

''Get down on ur knees karki nuna mun taurin kai donni kai biyu nake dashi masu taurin balaʼi...ʼʼ Gidado ya fada tare da shaudawa Baddo belt,ita kuwa ta tsaya atsaye kyam kamar an shukata tana kuka taki bin umarninsa,har ya daga hannu zai kara mata saiga Yumma ta fado dakin tana salallami ganin yara na kuka ga Baddo kuma yana kan cin zalinta ne..Su Ramlah na ganinta suka nufeta suna cizgar kuka,Ramlah ta kwashe labarin komi ta gaya mata,bata karashe ji ba ta kwasheta da wawan mari tana nunata da yʼar yatsa''wato ke Ramlah bazaki dena debomun magana bako..?ko dukan dayake miki ne bai isheki ba shine harwa yau kika kasa nesanta kanki da shiga gonarsa..?meye na zuwa ki hada fada agidanshi..? kije ki cigaba idan ya kasheshi abanza babu abunda ya dami Ummerherny..!ʼʼ

Gidado kuwa tunda Yummin tasu ta soma magana ya sauke hannun belt kasa wanda ada yake shirin zabgawa Baddo shine ta shigo,nufanshi tayi adaidai lokacin kuma su Yabba suka shigo suke tambayar abunda ya faru su Ramlah da aka samu freedom aka shiga bayani,Yumma kokarin fuzge belt dʼin hannun Gidadon tayi ammh sai ya hana,azuciye ta daga hannu ta kifa mishi wawan mari tace''zaka cikamun ko kuwa sai ranka yayi mugun bʼaci tukun...?ʼʼ ta fadi da jajayen ido,dasauri ya cika mata yana jin wani irin tukukin bakin cikin yummin tashi,yarasa meyasa akomai take ganin laifinsa,shi da kannensa sam beda right yace ya hukuntasu atake sai ta dizgashi agabansu,yana cika mata ta daga hannu iya karfinta ta zuba mishi cikin daga murya take fadin''maza get down on ur knees ina jin mantuwa kayi dana ce maka duk randa kasake dukan wani yaro agidan nan saina rama mishi,karka manta har yanzu mahaifiya nake agareka don haka ba fin kʼarfina kayi ba..ʼʼ

Sake zuba mishi belt dʼin tayi tana fadin''Taurin kai kakeson ka nuna mun ko..?get down in ba haka ba zan sake zuba maka..ʼʼ ta fada tana nuna mishi gabanta,wasu kwallar bakin ciki ne suka tarun mishi acikin kwarmin ido,dasauri ya kʼarya gwiwowinsa zuwa kasa kamar yadda ta umarta duk kunya ta cikashi wai agaban kannen kannen bayansa ake hukuntashi,saurin kafe hawayen dake shirin gangarowa yayi gudun raini (yo! raini na nawa kuma Gidado..?😜)

Su Baddo sai mamakin wannan alʼamarin suke wai Gidado ne ayau dashan bugu,har yumma ta daga hannu zata sake zuba mishi belt sai ji tayi yabba yayi saurin rike hannun yana magana cikin bʼacin rai''haba ummerherny wannan wani irin abun kunya ne haka kikeyi ne..?dukanshi agaban idon kannensa..?yanzu shikenan shi bashi da damar ya hukunta kannensa idan sunyi laifi saidai ya zuba musu idanu yana kallo babu kwabo..?ʼʼ saurin taran numfashinsa tayi''Yo! haka ake kwabo..?ah iya sanina idan kanason ka nunawa na kasa dakai kuskuren dayayi toh kamata yayi ace ka zaunar dashi ka fahimtar dashi cikin lumana,tanan sai kaga ma yafi daukawa da kuma ganin girmanka ammh yawan dukan yaro ba komi yake jawowa ba illa zubʼewar girma da kʼara maida yaro gagarabadau,abu nanan ma haka ai sai ya kawo kara wajenmu,ansan sunyi laifi ammh bai dace yayi musu irin wannan bugun ba,dake yana jin kanshi shi din wani ne mara imanin dan sanda kawai an saba bugun masu laifi shiyasa abun yabi mishi jiki,ka bari in sake ji ko in gani ka tabʼa wani yaro agidan nan saina tabbatar dana kunyataka fiye da wannan mutumin banza kawai...!ʼʼ

Tana gama jawabinta ta hada kan yara sukayi waje ahanya tana ta musu fada kan abunda sukayi basu kyauta ba musamman ma Baddo,akace karsu sake sannan kuma kada suce zasuyi amfani da wannan damar su rainashi don sunga ta hukuntashi agabansu,idan hakan ta faru saita dauresu,jin hakan yasa tsoro kamasu dukah,suka dau alkʼawarin bazasu tabʼa gigin rainashin ba,bayan fitarsu yabba ya matsa kusa dashi yana bashi hakʼuri yace''kaima babana ka cika zuciyar tsiya ne,,ka sani ba kowani abu ake tankawa ba ka koyi shanye wasu abubuwan balle kai meh mata biyu dole fa sai kaci hakʼurin zama dasu,,kowacce zata dunga nuna salon makircinta ne don ta bʼata dayar awajenka,idan kuma kace zaka cigaba da tafiyar da rayuwarka akan dokin fushi,ana kawo maka kananun magana kana hawa ka zauna akai tofa zaka bata rawarka da tsallenka acikin gidanka,don haka tun wuri ka sauya taku banason yawan fushin nan Gidado...ʼʼ

Hawayen bakin ciki ne suka wanke masa fuska yace''Buguna tayi fa agaban kannena yabba...!?ʼʼ hakuri yabba kawai yayi ta bashi,Aliyu kuma ya watsa mishi harara don dama akwai wasa atsakaninsu yace''Women beater kawai,,malam kana bada maza idan zuciya kakeson nunawa toh kaje kayi dambe da yanʼuwanka maza ba kazo nan kana dukan kannenka ba ni wallahi harka bani kunya..ʼʼ ya ida magana akufe yana kwasar system dʼinshi,dariya yabba yayi kan yace''Aliyu gaya mishi dai ga maza yanʼwansa nan ya fita yaje yayi dasu mana ammh yazo nan yana cin zalin kannensa...!ʼʼ

Hakʼika kalaman Aliyu sun sake tunzurashi ammh kala bece mishi ba sai binsa da kallon ka kama kanka yayi,ko kallonsa Aliyun ma beyi ba ya fice yana fadin''yabba bari na sallami Tsoho nazo na kama hanya...ʼʼ yabba ya bishi da ''Toh nima gani nan tafe..ʼʼ shida Gidado suka mikʼe atare yana fadi mishi cewa shi zai tafi gida,yabba ya dubeshi yana girgiza kai yake fadin''wato don an maka fada shine bazaka je ka gaida mahaifina ba donna tabbata baku haduba kayo nan,kai idan ma aka bibiya babu wanda yasan da shigowarka,wallahi Gidado ka canza hali ina dai gaya maka...ʼʼ

Susa kʼeya yayi yana fadin''ayi hakuri yabba zan canza insha Allahu,muje na gaidashi...ʼʼ bayan sun isa falo kuma yabban yace mishi maza yaje ya bawa mahaifiyarsa hakʼuri don ranta yayi mugun bʼaci da abunda ya aikata,beci musu ba ya nufi dakin nata ammh ko kallonsa batayi ba sai cewa tayi ma ya bace mata daga gani kafin ranshi ya kuma bacewa,dasauri yabar dakin rai duk babu dadi ya sami yabbanshi ya fada masa yadda sukai da ita,girgiza kai yayi yace''kai ummerherny itama dʼin akwai zuciya kamar farar kura kuma ada ba haka take ba watakila kaine ka canzata da fitinarka...ʼʼ


     ******
Bayan Hafsa ta fita sai ta samu wani wuri ta rakubʼe toh shiyasa da Gidadon ya fito be ganta ba,tana ganin wucewarsa ta barke da kuka tana fadin''insha Allahu Jameelah idan kika sake na dawo gidan nan saina hana miki kwanciyar hankali acikinta,yadda kika sa aurena ya samu targadʼe toh naki rushewa zaiyi gabaki daya,zan tafi gida in sake sabon shirin sannan in dawo miki,kince am qualify amma on trial toh ni Hafsa inamai tabbatar miki da cewa zan komo ne with full qualification dʼina....ʼʼ tana gama fadar hakan ta nemi Nabeelah awaya wacce ta tafi yawon gantalinta tun safe kuma bata dawo ba,tana dagawa ta rufeta da zagi''Don kutumar ubanki kina ina yʼar iska kawai kina can kina biye biyen maza ni kuma anan shegen ya sakeni...ʼʼ kuka yaci mugun kʼarfinta,akidime Nabeelah dake kan cinyar saurayinta Andrew suna zukʼar shisha ta mikʼe har tana neman kwarewa tace''what...?Anti Hafsa saki kuma..?meh kika masa har ya sakeki ne bayan ko sati biyu baku rufa ba da auren...?ʼʼ ta fada cike da tashin hankali,dkyar hafsah ta iya cewa''kedai duk inda kike ki taso ki sameni ina kʼofar gidan...ʼʼ tana gama fadar hakan ta yanke call dʼin,cike da tashin hankali da dubi Andrew tana shafa kumatunsa tace''baby i hav to get going my sister juz got divorced...ʼʼ

Cike da mamaki yace cikin harshen turanci''kina nufin wacce kikace anyi aurenta last week shine har ya saketa..?meh tayi..?

Daga mishi kai tayi''yes itafa wallahi nima ban san abunda tayi ba ammh na tabbatar makirar kishiyar nan tata nada hannu aciki...ʼʼ waro eyes waje yayi yana fadin''you mean tana da kishiya dama..?

''Of cours tana dashi,plsss baby idan mukayi aure karkamun kishiya wallahi bani sonta...ʼʼ ta fada gami da rungumoshi tana kuka,hannu yasa ya shiga bugan bayanta yana fadin''Swthrt Allah dai yasa abarki kikoma christianity don kinji dai na gaya miki ni bazan iya musulunta akanki ba saidai ke ki komo addinina kokuma kowa yayi nashi idan zaʼa bari ki aureni,sannan kuma inason ki kwantar da hankalinki mu ah addininmu an haramtawa namiji auren mace fiye da daya,duk wanda yawuce against law tofa ya fita daga addini...ʼʼ sake kankameshi tayi tana kuka tace''wallahi idan akaki bari in aureka zan bika ne mu gudu zuwa kasarku cuz i cnʼt live without you babyy..ʼʼ

Shidai yana mamakin yadda baiwar Allahn nan ke masifar kʼaunarsa har take tunanin rabuwa da kowa nata akanshi bayan addininsu ba daya ba haka kuma kabilarsu ba daya ba donshi dʼin dan bature ne wani aikin contract ne yakawoshi Nigeria kuma agarin abuja har watarana suka hadu awani wajen party shine tabi ta likʼe mishi wai tana sonshi don taga fine boy,shi kuma harga Allah baya jinta aransa yana da wacce yakeso yʼar kasarsu wato Antonia,kuma shekara daya zaiyi sannan ya koma kasarsa ta haihuwa da zarar ya kammallah abunda ya kawoshi,saida ya durjeta dakyau sannan suka shiga wanka ita tayi wankan tsarki shi kuwa ko oho,akarshe sukaje daukar Hafsa wacce ta gaji da jiranta,taso rufeta da fada ne ammh data ganta da saurayi kuma acikin mota saita shanye,Sun gaisa da Andrew ah mutunce har yake mata jajen abunda ya faru,tunda suka hada idanuwa da juna sai da gaban kowannensu ya buga ina nufin Hafsan dashi Andrew dʼin,bayan sun shiga mota,Hafsa take bawa Nabeelah labarin abunda ya faru da batanan wanda har yakai ga saki,Andrew ya gyara madubin motar daidai saitin fuskar Hafsa dake baya,lokaci zuwa lokaci yake kallon yadda lips dʼinta ke motsawa ayayin da take bawa Nabeelah dake zaune ah gaba labari,dan bugan sitiyari yayi yace aransa''owh lawd! diz woman is damn cute..! Wannan ai tawa ce kuma ya zama dole na sameta,,God so kind ma sheʼs being divorced don haka komai zaizo mun da sauki...ʼʼ

Karaf! ta kamashi yana kallonta da ocean blue eyes dʼinsa ta madubi,ya sakar mata wani irin lallausan murmushin daya fadar mata da gaba,ba shiri ta dauke kallonta tare dayin shiru da labarinta,Nabeelah kuwa wacce batasan wainar da ake toyawa ba ta hau masifa''lallai Gidado ya kunnowa kansa wuta daga shi har munafukar matan nan tashi,sai sun gane cewa shayi ruwa ne,ita kuma Ramlah ta bani mamaki don ban tabʼa tunanin hakan daga gareta ba,ashe dama kʼaunar gulma ce take mana bamu sani ba sai yau..?ammh babu damuwa bashi taci..............ʼʼ

Adaidai wannan lokacin suka iso kofar gidansu............✍


_*Manage pls yau busy day dina...!*_


_*Tofa! ana wata ga wata,dan bature shima ya shigo😳,nake gaya muku ba karamin cakwakiya bane yake acikin wannan littafin ammh sai kun biyoni sannu sannu don nishadantar daku dakuma fadakar daku😘*_




_*3 extra free pages remaining purchased by Nanarh Ayeesha buh mind you registration is still goin on😜*_

_ku nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_

*🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
     _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

_*💍NANARH AYEESHAʼS PAGE..!😘*_

  _*💫BABI NA SHA BIYAR..💥*_

!.......Har suka isa kofar gidan koda wasa bata bari sun sake hadʼa idanu dashi ba,shi kuwa babu takun da beyi ba don kawai hankalinta ya komo gareshi ammh hakan be samu ba,bayan ya paka motar ta masa godiya,,bata jira taji amsawarsa ba ta budʼe ta fice,amsa mata yayi akasan mokoshi don kwata kwata bashi da sauran kuzari,ah daidai gate ta dakata tana jiran fitowar Nabeelah wacce ta tsaya sallamarsa,jawota yayi ta fado jikinsa ya mata radʼa akunne cikin kwararren harshen turancinsa yace''Swthrt sister dʼinki ta fiki haduwa sosai..ʼʼ

Dasauri ta fuzge jikinta daga nashi tana mai bʼata rai tace''owh haka ma zaka ce ko baby..?nasan ta fini kʼyau ammh banison ana fada don inajin haushin hakan sosai..!ʼʼ aranta tace''Sabida tana dakyau da kuma komi shiyasa kowa yake cewa yana sonta,Gidado ma yakamata ace niche na aureshi ammh Ramlah tamun bura uba tayi saurin hadashi da ita,ai kana naka Allah na nashi ne gashi nan kin fito kuma bi izinillahi bazaki koma gidan nan ba Hafsa,insha Allahu kin gama auran Gidado agidan duniyar nan sai inko ah lahira,ni nasan da cewa bazan iya samun auranshi ba ammh zanyi iyakacin bakin kokarina wajen ganin muna having affairs awaje,kema Jameelah am coming for you soon,am juz 20 buh mind you age are juz numbers,zan baku mamaki ne..!ʼʼ

Andrew ne yadan tabota tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lula hadda sauke wawan ajiyar zuciya,''Babe! tunanin meh kikeyi ne haka gashi sister nacan tana jiranki har tayi flashing naki ma baki ji ba saiku ta saka waya ah silent tamkʼar baku da gaskiya..ʼʼ

Murmushi tadan saki aranta tace''kai dʼan bature nakusa baka red card don dama arashin Gidado ne na likʼe maka sannan kuma don kudinka,ammh yanzu tunda sister ta fito zanyi kokarin maye gurbinta awajensa...ʼʼ

  ''Swthrt wai lafiyarki kuwa.?ʼ ya fada cike da mamakinta,dasauri ta bashi peck ah kumatu tana fadin''goodnyt baby sai munyi waya...!ʼʼ bata jira amsawarshi ba ta fice ayayin daya bita da kallo,can kuma ya maida hankalinsa kan Hafsa dake tsaye da yayansu Muktar wanda yazo shigewa cikin gida yaci karo da ita anan,

Yah Muktar yace''Hafsa tambayarki fa nake nace meya faru kikazo gida ah irin wannan lokacin har kuma shi mijin naki ya kyaleki kika.fito..?

Da rawar murya tace''Sa...sakina yayi...ʼʼ ta fada hawaye na kwaranyo mata,adaidai lokacin Nabeelah ta karaso wajen,cike da mamaki da alʼajabi yace''whatttt...!?saki fa kikace meh kika masa dahar yaga bazai iya hakʼuri ba ya sakeki..?dududu yaushe ma akayi auran..?anya Hafsa kina da gaskiya kuwa...?kar dai ince wani rashin mutuncin ne kika shuka masa don nasan halinki sarai baki da kirki...!ʼʼ

Juyawa yayi ga Nabeelah wacce murna fal ranta yace''Ke! Nabeelah meya faru aka sako yarʼuwarki..?

Kai tsaye tace tana taunar cingam''Rashin kunya ce take yawan mishi,kwata kwata bata darajashi ga kuma yawan neman rigima awajen uwargidansa toh shiyasa yace ya gaji ta tafi gida....ʼʼ

Kallon mamaki Hafsa tabita dashi don bata tabʼa tunanin cewa magana irin haka zai fito daga bakinta ba,ji yadda ma tayi maganar kai kace ko agabanta akayi komi,afusace Yah Muktar ya daga hannu da nufin yanka mata mari,juyawa tayi ta shige cikin gida da gudu tana kuka,yayi hanzarin bin bayanta haka itama Nabeelar wacce bazaʼa iya misalta irin tsananin farin cikin da take ciki ba,duk abunda yake faruwa akan idon Andrew ne dake zaune cikin mota,duk da cewa besan meh suke tattaunawa akai ba ammh yasan bezai wuce akan zancen sakin bane,sosai ya tausaya mata ganin danʼuwan nata ya dauki zafi da lamarin,girgiza kai yayi sannan yaja mota yayi gaba,

Kuka take tamkʼar ranta zai fita ta nufi entrance door aguje tana waigen Yah Muktar daya dauki wani cable akasa yana biyota abaya,Alh.Bilyaminu da matarsa Haj.Amina wacce ake kira da mami suna zazzaune suna cin abinci bayan sun idar da sallar ishaʼi,sai gani sukayi yʼar tasu ta fado falon tana rusar kuka,cike da tashin hankali duk suka mimmikʼe tsaye,Daddy ne yayi kʼarfin halin cewa''ke Hafsah lafiya kuwa..?meya faru kika shigo mana gida ah hargitse ne..?

Kafin ta bashi amsa saiga Yah Muktar ya shigo tamkʼar mayunwacin zaki,nufarta yayi ita kuma ganin hakan yasa ta buya abayan mami,

Mami ta doka mishi tsawa''Dakata muktar banson haukan banza ku natsu ku mana bayani,meke faruwa ne...?

Azuciye yace''Sakinta fa akayi,gata nan dai da ranta ku tambayeta ba kʼarya nake mata ba...ʼʼya

Please Login or Register in order to submit comment