Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaje gareta tana jiranka,,yau din darenta ne don haka dnt spoil it for her plsss.....ʼʼ ta ida maganarta tare da rushewa da wani sabon kuka,,da sauri ya dago fuskarta ya hadʼa da nashi,,goshinsu ya manne dana juna,yace in a very romantic voice"Hearthrob ahakan kikeson in tafi ga wata sannan ke in barki cikin damuwa bayan you are d woman dat trully ownʼs me?no wlh bazan iya ba,,gashi tun baʼa kwan ba ta soma gwada mun halayenta wanda na tabbtar da nan gaba bazan iya cigaba da zama da ita ba idan har bata sauyaba,,kai My Jamila i really love youuuu,,believe me ke din ta dabanceʼʼ ya rungumeta sosai ajikinsa yana mai jin tausayin kansu na ratsa bargon zuciyarsa,ita kuwa kuka take rerawa ahankali.....!

     __________★
Hafsah dai daga baya an canza raʼayi an shiga bandaki aka tsalo wanka sannan ta sanya doguwar night gown dinta wanda ko gwiwa bekai ba,mai vest hand gashi kuma shara shara dashi don tsab ake hango pant dinta da kuma shape dʼin nipples dʼinta,,wai ita nan don taja raʼayinsa ne fa😂,ta feffeshe jikinta da turare har kala hudu tare da jefa mint abaki sannan ta zauna abakin gado gami da hardʼe kafafu tana jiran shigowar oga,lokaci zuwa lokaci take tsotsar alawar,can dai taga zaman bazai amfaneta da komi ba don shirun tayi yawa,taja tsoki tare da mikʼewa tayi kofa tana fadin"wai kazar an koma yinta ne ah london dayake neman taking foreva awaje?ji kusan sha biyu ake nema fa?ʼʼ

Ta furta tana duban agogon bango kafin ta murdʼa handle na kofa ta fice take fadin"Ai zai dawo ya sameni ne...!ʼʼ

    Idan ba idanuwanta kʼarya suke mata ba tou kuwa tabbas Gidadonta ne dai take gani yana romancing Jameelah kishiyarta don har nema yake ya fita cikin hayyacinsa,,ita kuma Jameelar nema take ta kwace kanta ammh yaki bata wannan damar sai dadʼa kankameta yayi yana tsotsar lips dʼinta dkyau hadda wasu lumshe idanu,harta matso kusa basu sani ba sai kallon tsantsar mamaki da alʼajabi take binsu dashi baki sake,,bbu abunda kake ji sai kʼarar french kisses da Gidadon ke aikawa Jameelah wacce daga baya ta shiga karbʼa cuz she canʼt reject it anymore...!

      " _Innalillahi waʼinna ilaihi rajiʼun....!_ Suleiman ina can daki ina jiranka ka kawomun kaza ashe wayau kamun kazo nan kana cin taka kazar hankali kwance,,tou na rantse da Allah bazan tabʼa yafe muku cin amanata da kukai ba...ʼʼ ta rushe da kukan haushi,,su kuwa ah firgice suka saki juna tare da dagowa suna dubanta don bbu wanda yayi tunanin zata fito falon,gara ita hearthrob tayi tunanin hakan shiyasa take ta turjewa ammh shi sahibul kalbin he never saw it coming at all😆

  cike da kunya ya shafa kansa yace''Hafsah! am so sorry nayi kuskure...ʼʼ

  kallon rainin wayau ta wulla masa tace''Kamar naji ka ambaci kuskure??tou ka sani wannan ba kuskure bane illah son zuciya,,ayau daya kamata ace ina cikin tsantsar farin ciki ammh gashi u guys hav spoilt my wedding night wanda ya kamata ace nabar dadadʼar tarihi akansa,,ammh ga dukkan alamu sun nuna cewa tarihin nawa daren farkon zai rufe ne da kayan takaici wanda aduk sanda na tunashi zai jefani cikin kunci ne,Allah ya isa tsakanina daku kuma sai Allah ya bi mun hakkʼina,,wayyo kishiya bata yi ba wallahi.....ʼʼ ta sake rushewa da kuka tare da kʼarya gwiwowinta zuwa kʼasa,,jikin Jameelah ne ya dauki rawa sosai sai hawaye sharrrr cuz she felt so guilty,,da rawan murya tace"Haf...sah...don girr..man Allah kiii yaaa...femun wallhiii bazan kuumaaa ciin amanarkii ba...ʼʼ

Adaidai lokacin wayar Gidado ta dauki kidʼa,yana dubawa yaga Sagir ne,bayan ya dauka yace masa"Kai mallam yi sauri ka sameni awaje dare yaja....ʼʼ da tou kawai ya amsa masa sannan ya mikʼe yace da Jameelah"Ke wuce part dinki kuma karki sake na dawo na sameki anan...ʼʼ

Ta amsa masa daa tou,ya dubi Hafsa ransa ah matukʼar bʼace yace"Kema haka...ʼʼ

Tsoki taja tace cike da tsiwa"Anki atafin maci amana kawai...ʼʼ murmushi kawai yyi sannan yasa kai ya fice don yasan bbu yadda zaʼayi Hafsah ta taka matsayin Jameelah ah zuciyarsa,,rashin kunyarta kadai ma ya riga yasa tayi fail,bayan fitarshi Jameelah ta koma Jameelarta fuska ayamutse tace"Ke! bari kiji idan kina cin kʼasa tou tabbas ki kiyayi ta shuri don naga kamar da rawar kai kika shigo gidan,ni idan kika takani bazan wani damu ba ammh karki bari kice zaki dauki wannan banzar dabiʼar ta cin mutuncin mijina agaban idona ko agaban wani don asannan ne zaki san ainihin kalata sbd ni hawainiya ce mai canzawa aduk sanda taso,, _*DCP  SULEIMAN ALASSANA GIDADO*_ ba abun rainawarki bane harki tsaya kina tanka masa magana muryarki asaman nashi,,don haka hattara amarya in ba haka ba uwargida zata gyara miki zama....!ʼʼ

   Cike da tsantsar mamaki Hafsah ta mikʼe tsaye tana fadin"Lallai na yadda kishiya da ababen mamaki take,,wato kukan da kike ta sharbʼawa da kuma tsantsar tsoron da kika bayyana mana duk ta munafurci ce ashe,zuwa dakkoni da kikai ma nasan tabbas akwai wani abunda kika kulla ammh sai Allah besa kinci nasara ba,,kai kishiya akwai munafurci wallahi ammh ki......ʼʼ

Jameelah tayi sauri taran numfashinta"Malama abunda kika gani ba munafurci bane illah kishin ilmi irinta wayayyun mata ba irin naki na en kʼauye masu nuna kishin jahilci ba,,ada kin so ne na dunga biye miki don mu hana masa kwanciyar hankali agida?sannan ya koma ya tsaneni?tou wallahi kinyi kʼarya kuma kinyi kadan,,ki sani ke baki isa kija da mace kamata ba matar dʼan sanda....ʼʼ

Wani miyau mai dʼaci Hafsah ta hadʼiya kan tace"Dake ni dʼin kuma ba matar dʼan sandar bʼace sai matar direban gidanku ko?idan kuna ma da direban kenan,waya sani ko daga cikin tsiya aka tsamoki zuwa cikin daula...ʼʼ

Akʼaikaice Jameelah ke kallonta don sosai kalamanta na kʼarshe suka soya ranta,murmushi ta sakar mai ciwo kan tace"wannan kuma ina ganin ba damuwarki bace ammh abunda kawai nakeso ki sani shine ke dʼin ba dʼaya kike dani ba,auran matar dʼan sanda is very annoying sbd sheʼs already trained,sumbar da kika kamamu ma muna yi na tabbata you were very shocked and suprised sabida baki tabʼa ganin irinsa ba,kadan kenan kiga gani kuma idan kikai sakaci zan dauke hankalin mijin ya dawo kaina ke kuma ki rasa gane kanshi gabaki dʼaya,don haka kibi asannu....!ʼʼ

   
     ★★_____________

  Acan waje kuma Gidado ya amshi ledojin kazar da Sagir ya kawo masa hadda kwalayen lemummuka ahadʼe,yayi masa godiya sosai,Sagir sai tsokanarsa yake yace"Malam kai dai kabi yarinyar mutane asannu banda rawar kafa kasan dai watakila sabuwar shiga ce..ʼʼ tsoki Gidado yaja kan yace"Dadʼina dakai kai dʼin dʼan iska ne,rawar kafar meh zanyi bayan dakai dani duk munsan cewa ba yau ne zan soma ziyartar wannan duniyar ba...ʼʼ

   "Amma dai ba iri dʼaya bane ai...ʼʼ ya furta yana kʼyakʼyatar dariya,Gidado ya bʼatsar da zancen yace"Gara dani ma ina da har guda biyu kai kuwa dʼayan ma ta gagareka ajjewa,,gwauro kawai...ʼʼ murmushi mai ciwo Sagir ya saki kan yace"Ai ni tunda kuka hanamun auran Surayya toni da aure kuma sai wani ikon Allah...ʼʼ yana gama fadʼar hakan yaja mota yayi gaba ayayin da Gidado yabi bayan motar da kallo cike da tausayinshi,hakʼikʼa Sagir sunso juna da Surayya ammh Allah beyi cewa ita matarsa bace sbd Tsoho ne ya hana,tunda dʼan aminin mahaifinsu wato Awwal ya nuna yanason Surayya kuma dake mahaifinshi nada kʼyakkʼyawar alakʼa da Tsoho shiyasa kai tsaye Tsohon ya rufe ido ya bawa Awwal dʼin ita ya hana Sagir....

  Jan jiki yayi ya koma ciki tare da umartan security daya rufe gidan goma..



   "Inaso ki sani kafin na rufe tarihin daren farkona ya zama dole nabar miki abun mamaki wanda bazai tabʼa gogewa ba acikin zuciyarki....ʼʼ Hafsah ta fadʼa tana watsa mata kallon tsana

"Allah ko?hmmm then Iʼll anxiously be waiting! zanta jiranki daga ciki don bazan so mijina yazo ya ganni anan ransa ya bʼace yace nayi disrecpecting nashi banbi umarninsa ba,kinsan ni matar aljannah ce..ʼʼ ta ida maganarta tare da kashe mata ido dʼaya,Hafsah na shirin magana suka ji Gidado na kʼokarin budʼe kʼofa,taku dʼaya biyu Jameelah tayi ta sadata kanta da part dʼinta dake tana kusa da kʼofar sabʼanin na Hafsa dake can nesa da inda take,saida Jameelah ta aika mata da gwalo kan ta rufe kʼofar wanda adaidai lokacin ne shi kuma ya sako kai ya shigo,

Kallonsa ya sauka akan Hafsah rai amatukʼar bʼace yace"Hafsah da gani zamu samu matsala ni dake,wato ke bazan baki umarni kibi bako sai abunda ranki yaso shine zakiyi right?ga yarʼuwarki nan ita tabi maganata ta wuce bʼangarenta ammh dake ke dʼin fitinanniya ce mara kunya mai neman rigima shiyasa kika nunan cewa ke kin isa...ʼʼ

Azuciye tace"Ita da kake yabonta ai yanzu itama ta shige aguje data jiyo motsinka....ʼʼ

    "Tunda har ban sameta anan dʼin badai ai shikenan,kuma ni tsoron data ji ta gudun ya burgeni sbd ta gujewa bʼacin raina ne ammh dake ke baki damu ba shiyasa kikayi tsayuwarki bbu alamun tsoron,,kinga ni karbi kazar da kike tawa mutane hauka da balli akanta...ʼʼ ya fadʼi yana mikʼa mata,fusgewa tayi sannan ta juya zuwa part dʼinta tana rusar kuka,yabita da kallon ina da aiki sosai agabana,ya latso Jameelah yace ta fito ta kʼarbi tata kazar,koda ta fito bata bari sun hadʼa idanu dashi ba ta kʼarba tare da godia sannan ta koma ciki,

  Kai tsaye part dʼin Hafsan ya nufa ya tarar da ita kwance saman gado tana rusar kuka,ledar kazar kuma tayi jifa dashi har yakai can kʼarshen gadon,sai yaji duk ta bashi tausayi ammah be nuna mata hakan ba yayi tubʼewarsa ya shige bandakʼi don watso ruwa,bayan ya gama ya dauro alwalarsa ya fito,,abun mamaki sai ganinta yayi tana yagar kazar tana korawa da lemur,da gani ta canza shawara daga baya kenan,kala bece mata ba har ta gama tayi gyatsa,anan ta mikʼe akʼasa ta bingire da bacci,yaso ya tada ita ta dauro alwala su gabatar da sallah ammh kuma sai ya kʼyale kawai,,can ya dakkota ya kwantar asaman gado tare da lullubʼa mata bargo sannan ya koma saman doguwar kujera ya kwanta bayan ya kashe musu wuta,wayarsa ya jawo ya shiga neman Jameelah awaya ammh be sameta ba,haka ya haqura ya rungume hannayensa saman kʼirji,,bbu jimawa wani nannauyar bacci yayi awon gaba dashi shima,itama Jameelar anata bʼangaren sai data ci kukanta kafin bacci ya kwasheta,,tata kazar kuwa ah fridge dʼin dakinta ta jefashi don bata cikin mood dʼin cinsa...

    Asuba nayi shine ya soma tashiwa ita kuwa gimbiyar tana nan kwance tana sharar baccinta hankali kwance,ga wani irin munsharin da take jaa wanda ko kadan bayaso,matsawa kusa da gadon yayi yasa hannu ya tabʼota,yaci saʼa ta budʼe ido yace"ki tashi kiyi sallah asuba tayi...ʼʼ tsaki taja ta juya masa baya ta cigaba da baccinta,kwafa yayi yace"Karki sake in dawo in tarar baki daga ba...ʼʼ yana gama jawabinsa ya kadʼa kai ya fice daga dakin zuwa part dʼin Jameelah don itama ya tayar da ita duk da cewa ya tabbata ta daga don bata wasa da ibadah,

  Ah bathroom ya tarar da ita tana daura alwala sai shima ya shige don suyi tare,ko kallonsa batayi ba har ta gama sabʼanin shi da yake ta jifanta da murmushi,shine ya jasu sallar kuma yaso ne su hadʼu duka ah babban falo har Hafsan sannan ya jasu sallar ammh yasan in har Hafsan daya sani ne tou kuwa bata daga ba kuma bayason ta bʼata musu lokaci shiyasa kawai ya jasu sallar,bayan sun idar ya jawota jikinsa ganin bata da niyyar gaidashi yace"Haba hearthrobe yau ko dʼan annurin fuskarki bazan samu bane balle akai ga batun gaisuwa?ʼʼ bata kai ga bashi amsa ba sai ji sukai wayarta ta dauki kidʼa,shine ya tashi da kansa ya dakko mata,cike da mamaki yake fadʼin"Meya faru kuma da maman su Kasim ke kʼiranki da wannan asubancin?ʼʼ  [yana nufin matar Baba Munniru]

   Wuf! ta mikʼe itama dauke da mamaki da tsoro akan fuskarta tace cikin rawar murya"Anya lafiyaa kuwa?ʼʼ

    "Dauka dai muji...ʼʼ ya furta yana mikʼa mata wayar,tasa hannu ta kʼarba jiki na rawa tare da danna receive tace"Assalamu alaykum Momy barka da asubanci.........!ʼʼ



 


  _*Kash!kuyi haquri na yanke muku jindadi ammh duk salon ne yazo da hakan,tofa meyasa momy take kʼiran Jameelah ah irin wannan lokacin?*_

_*Ga Gidado nan dai da matayensa,da mai 'KISHIN JAHILCI' da kuma mai KISHIN ILMI' ...koya zata kʼaya? muje dai zuwa*_


_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488


_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_


  *🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
     _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

_*💍NANARH AYEESHAʼS PAGE..!😘*_

  _*💫BABI NA SHA SHIDDA..💥*_

!.......Acikin wannan daran aka tasa kʼeyar Gidado gaba zuwa gidansu Hafsa tamkʼar karamin yaro,dashi da Baba Munniru,Baba Haruna sai kuma Aliyu da abokinsa Sagir wanda aka nemoshi awaya babu shiri,abunda abokin nashi ya aikata sam be mishi dadi ba,suka hada kai shida Aliyu sunata zaginsa acikin mota,Aliyu yace''wallahi malam ka bʼata wayonka,gaka nan dai ana ganinka anga mai wayau ashe abun ba haka yake ba da sauranka..ʼʼ

Baya cikin mood dʼin cece kuce shiyasa kawai yayi ignoring dʼinsa,Baba Haruna ne ya masa jan ido ganin yafi kowa zakewa yace''wai kai Aliyu bazaka rufewa mutane baki bane..?ai gara dashi har mata biyu gareshi kaifa dayan ma ta gagareka ajjewa ka tsaya kana ruwan ido,karka bari in sake jin muryarka acikin motan nan idan ba haka ba zan mugun sassabʼa maka,kaima Sagir ka kama kanka banison shirmen banza da wofi...!ʼʼ

Ba shiri kowannensu ya kama kansa,Gidado kuwa tunda suka kamo hanya uffan bece ba har kawo lokacin nan,lumshe idanu yayi yana tunanin sabbin halayen Yumminsa da take gwada mishi wanda ada can ba haka take ba,akwai soyayya da mugun shakʼuwa atsakaninsu don kusan zai iya cewa tafi kʼaunarshi akan sauran yaʼyanta ammh tunda ya auri Jamila komi ya sauya zani,abu kadan saita rufeshi da fada tamkʼar dama jiransa take ya aikata ba daidai ba,tunda ya auri Jamila zai iya kirga iya adadin daya zauna gashi ga mahaifiyarsa suna fira cikin so da kuma kʼaunar juna wanda ada can kafin yayi auran bazai iya misalta iya adadin zama na aminci da sukayi ba da kuma kʼaunar juna dake tsakaninsu ba,ammh ayanzu why diz sudden changes..?kodai haushinsa takeji akan rashin haihuwa..?ammh idan hakan ne toh meyasa bata dauki zafi da sauran ba sai shi..?


Wani zafafan hawayen dayake ta kafewa ne suka samu damar zubowa,adaidai lokacin suka iso kʼofar gidansu Hafsa,agogo ya nuna 10:15pm,bayan hannu yasa yana share hawayen gudun kar wani ya ankara dashi yana kuka,kowa ya fito sai ya rage shi kadai aciki yana tunanin ya fito ne ko kuwa aʼah,be gama yanke shawara da zuciyarsa ba yaji Baba munniru na fadin''zaka fito ne ko kuwa mu koma..?don bazamu shiga ciki babu kai ba...ʼʼ

Dasauri ya fito yana gyara zaman rigarsa wanda kananan kaya ne ajikinsa ko bari ya canzasu baʼa bari yayi ba aka taho gidan surukai dashi ahakan,bubbuga gate dʼin gidan suka soma yi,baʼa wani jima ba mai gadi ya budʼe musu,suka mishi bayanin kansu yace bari ya nemo musu iso awajen masu gidan,su Daddy na falo duk an zuba uban tagumi ana jimamin wannan alʼamarin har ita Hafsan,sai kuka take rerawa ahankali,Daddy ya dubeta afusace yace''Zaki rufewa mutane baki ko kuwa saina tashi na tattakaki anan..!?tunda zaman gidan kikeso ai gashi nan saiki zauna da tushi banza mara albarka wacce tayo gadon uwarta...ʼʼ


Dasauri mami ta tari numfashinta''A'ah ban gane tayo gadon uwarta ba..?ka tabʼa ganin nayi yaji ne balle naje gida da sunan ka sakeni..?ʼʼ  wani irin wawan kallo ya kwasheta dashi yace''Ai don ina hakʼuri dake ne da kuma shanye abubuwan da kikemun inba haka ba daʼace wani ne bani ba inajin da tuni kun rabu Amina,ki sani darajan yaʼyanki kike ci har kika kai tsawon lokacin nan agidan nan,ga yʼarki nan ta kwashi halayenki kaf ta dorawa kanta kuma.....ʼʼ

''Daddy don girman Allah ku bari wai meyasa kuke haka ne..?ʼʼ Mukhtar ya katsesu cikin tsananin bʼacin rai,mami tayi shewa ta mikʼe tana kokarin magana sai ga Ayuba mai gadi yayi sallama hakan yasa tadan natsu ta koma ta zauna,aka bashi izinin shigowa,dukʼawa yayi yake sanar dasu bakin da akayi,daddy ya washe hakʼora cikin tsananin farin ciki yace''Toh toh masha Allah kai Mukhtar tashi kaje ka musu iso ciki..ʼʼ

Mukhtar shima ya mikʼe yana jin wani irin farin ciki na ratsashi don ko ba komi yanason ayi sulhu kʼanwarsa ta koma dakinta,suka fice shida Ayuba,mami kuwa wani tsalle tayi ta dire take fadi cike da masifa''Wallahi Alhaji tun wuri idan sulhu sukazo nema agaskiya bazamu kʼarbi kokon bararsu ba don lokaci ya riga da ya kure babu zancen maida hannun agogo baya,insha Allahu Hafsa ta gama aurenshi ya bata takaddarta kawai....ʼʼ


Jin abunda ta fada yasa Hafsa fashewa da uban kuka tace''mami don girman Allah kiyi hakʼuri ni inason mijina kaddarace tazo mana ahakan,wallahi nina hankalta zan koma nayi maneji da igiya dayan daya sauran mana...ʼʼ kwasheta da wawan mari tayi tace''In sake jin wannan maganar ta fito daga bakinki saina sa almakashi na yankeshi,kinsan da cewa kina sonsa toh meyasa kika bari hakan ta faru..?toh ki sani ko zaki koma wannan gidan ba yanzu ba sai shima dʼin ya gane kuransa,oya maza ku tashi ku shige ciki kafin su shigo..ʼʼ


Da gudu ta shige ciki adaidai lokacin ne kuma su Aliyu sukayi sallama suka shigo,mukhtar ne agaba sai sauran suka mara mishi baya,Gidado ne akarshe kan nan nasa akasa,Ganin manya ahadʼe yasa Daddy saurin mikʼewa yana musu maraba da zuwa cikin mutunci da kuma karramawa,mami kuwa ko kallo ma basu isheta ba,suka samu wuri suka zauna aka gaisa dakyau,daddy ya umarci Nabeelah data kawo musu ruwan sha,sukace aʼah abarshi kawai sun gode,


Nabeelah ta shige ciki don tseguntawa  Hafsa cewa ai tare akazo dashi Gidadon,Baba Haruna ne yayi gyaran murya ya soma magana bayan an natsu kasancewar shine babba,yace''Alhaji muna zaune sai ga kiranka donmu harga Allah bamu da masaniyar afkuwar wannan alʼamarin,kuma fa ana tare har shi dʼin ammh be gaya mana komi ba saida ka kira kake sanar da mahaifinshi,agaskia wannan abu beyi dadi ba ammh ya zaʼayi tunda kaddararsu ce tazo da hakan,sai muyi imani da cewa hakan bazai faru ba saida hukuncin ubangiji,ayi hakuri don girman Allah yaro yayi babban laifi shiyasa muka tasoshi agaba don ya nemi yafiyarku sannan kuma ya maida ita atake tun kafin mutane su ankara da halin da ake ciki...ʼʼ


Kallon Gidado yayi wanda kansa ke adukʼe yace''kai maza ka bada hakʼuri sannan kace ka maidata...!ʼʼ

Caraf mami ta cafe tace''Ai wallahi koya bada hakʼuri ba komawa zatayi ba sai lokacin da muka so...ʼʼ azuciye Daddy ya kalleta yace''wai ke Amina meyake damunki ne..?ya zakice bazata koma ba shin kece keda iko da ita koni..?maza shiga ciki kibar maza suyi magana...ʼʼ

Tsoki tajah sannan ta shige tana gunguni,daddy ya dafe kansa cike da takaicin yadda ta dizgashi gaban surukansa,Mukhtar shi kansa ji yayi tamkʼar ya rusa kuka ko zaiji sanyi aransa,su baba haruna kuwa sai jinjina rashin mutuncinta suke,suka sake tabbatar da cewa lallai kam biri yayi kama da mutum,halayenta ne kaf yʼar ta kwasa,Shi kanshi Gidado aransa yace''Ashe halayenki ta kwaso tsaf...ʼʼ


Daddy yace''Don girman Allah kuyi hakʼuri kunsan shaʼanin mata sai ahankali,badamuwa yarinya zata koma dakinta ayau dinnan basai gobe ba..ʼʼ har ya mikʼe zaibi bayanta sai Gidado yayi hanzarin dakatar dashi yace''Daddy karka matsa mata don Allah abi komi asannu kuma ahankali,ni abunda yasa na saki Hafsa ba don komi bane illah fusatani da tayi,ta nunamun cewa ban isa da ita ba tare da yiwa matata da sauran yanʼuwana gorin haihuwa........ʼʼ


''Yo! Kujimun zancen banza fa toh kʼarya tayi..?nace kʼarya tayi..?su dʼin ba juyayyu bane..?ka gayamun yaʼyan da suka fito daga tsatson mahaifiyarka acikinku akwai wanda ya haihu ne...?baka ma gode Allah cewa Hafsa ta aureka ba tare da nuna damuwa akan rashin haihuwar taka ba..?ita wancan wahalalliyar ita taga zata jure zama dakai ammh Hafsa dai bazata koma gidanka ba,dama kaddarace ta hadaku kuma kaddarar ta rabaku,alhamdulillah naji dadin hakan sosai,akarshe ina mai shawartarku daku hanzarta binciken mahaifiyarku don ina tuhumarta akan cewa dasa hannunta acikin rashin haihuwarku dukah....ʼʼ



Gabaki dʼaya kallonta ake cike da mamaki da alʼajabi,ashe da Daddy ya korata ciki labʼe ta musu,afusace Gidado ya mikʼa jikinsa na mugun shaking with running tears yasa hannu ya ciro wata farar takadda ya isa ga daddy ya mikʼe mishi yace''Daddy kuyi hakʼuri ga takaddar Hafsan ammh kamar yadda na fada afarko ayanzu hakan ma ina kan bakana ne donni nagartaccen mutum ne wanda baya tabʼa canza maganarsa,i always stand by my words,idan Hafsa ta hankalta kuma taga zata iya cigaba da zama dani da lalurar da mahaifiyarta ta zayyano toh ina maraba da ita...ʼʼ da rawar jiki shima daddy yasa hannu ya karba,kafin yayi magana tuni Gidado yasa kai zai bar falon ana kiranshi ko waigowa beyi ba,dasauri Aliyu da sagir suka bi bayanshi,Baba Haruna da Baba munniru suma suka mikʼe afusace suka sallami daddy suka fito,dasauri daddy da mukhtar suka bi bayansu ammh ina ko sauraransu basuyi ba,


Afusace daddy ya koma ciki yana nuna mami da yʼar yatsa''Amina saʼarki daya ni ba irin mazajen nan bane masu daga hannu su daki matayensu ba,daʼace ni irinsu ne da ayau kin yabawa aya zakinta,ammh kije ni _*BILYAMINU AHMAD NA SAKEKI SAKI DAYA*_ sakamakon cin mutuncin da kikawa surikaina kuma surukanki,idan kinje gidanku kya musu bayanin hakan....ʼʼ yasa kai ya shige,

Mukhtar dasu Hafsa da suka fito suka shiga nanata kalmar innalillahi suna kuka gami da fadin'' haba Daddy haba Daddy meyasa kaima ka biyewa zugin shaidanʼʼ mami kuwa zubʼewa akasa tayi tana birgima har daddy ya dawo falon ya cillar mata fara takadda yana fadi cike da dacin rai''Amina na gaji da zama dake,ayau hakʼurina ya kʼare ga takaddar sakin nan arubʼuce sannan kuma gana yʼarki wanda mijinta ya bayar abata....ʼʼ ya fada yana sake cilla mata wata farar takaddar,su Hafsa sai kuka suke rusawa har Mukhtar,

Daddy ya shige ciki ya kulle kansa yana kuka,sam Allah be hadashi da mace ta gari ba,haka ma yaʼyansa ukun duk babu na kirkin gara gara Mukhtar yana da hankali sosai kuma baya biye biyen mata,shidai barshi da shaye shaye,

Can mukhtar ya nufi Hafsa ya shigeta da bugu yana fadin''shegiya yʼar iska ai duk kece kika jawo aka saki mahaifiyarmu kuma wallahi tun wuri ki dau damarar bautuwa acikin gidan nan,billahi azimu Hafsa babu tausayi ko rangwame atsakanina dake...ʼʼ kuka yaci kʼarfinsa ya cigaba da bugunta harsai da tayi laushi........



   *********
Bayan fitar Aliyu ya samu Gidado yana dukan mota iya karfinsa hadda shuri yana kuka gami da fadin''Yumma why..?ni dama na dade ina zargin dasa hannunki acikin rashin haihuwar yaʼyanki sabida tsanar da kike nuna mana musamman ni tayi yawa ammh shiru kawai nayi don aganina bazaki tabʼa iya aikata abunda nake zarginki akai ba,Yumma meyasa kika hana mana haihuwa...?wani laifin ne mukayi miki da muka cancanki girman hukunci makamancin wannan...?you need to ans my question Asap....

Ya fada yana kokarin bude driverʼs side,Aliyu wanda ya gama jin zancensa shine yayi saurin dakatar dashi yace azuciye''kai Gidado meye haka..?shin kayi hauka ne..?meyasa kake kokarin barin maganganun matar nan suyi tasiri ne acikin zuciyarka..?

Azuciye shima yace''Aliyu ka rabu dani ai gaskia ta fada,itace mutum na uku data fadamun wannan maganar,sauran da suka gayamun ban tabʼa daukar zancen serious ba ammh ayau na dauki na mamin Hafsa don ina ji ajikina mahaifiyata tana da hannu agame da rashin haihuwata da sauran yanʼuwana....ʼʼ


Girgiza kai Aliyu yayi shima din zuciyarsa ta shiga zarginta ammh sai ya daure yace ahankali''plsss Gidado ka binne maganar nan kar kowa ma yaji don ba gaskia bane ni ban yadda ba....ʼʼ kafin yace wani abu sai gasu Baba haruna sun fito rai bace tare da sagir wanda ya koma dakko agogonsa daya manta dashi,babu wanda yace da wani kala har aka isa gida,Jamila sai kiransa take tayi awaya ammh ya kasa dagawa,can ta kira Sagir shine yake fada mata cewar ta

Please Login or Register in order to submit comment