Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hafsah bayan bai ta6a kaita wajenta ba balle kwatance,lallai mata kenan yasan tabbas bincike tayi akan Hafsah,shidai addu'arsa dai aynzu shine Allah yasa karta bashi kunya,bayan yakare wayar da Sagir har zai koma can cikin gida sai yaji kamar ana magana kasa kasa ata wani lungu,ahankali yaja jiki ya lafe ajikin bango tare da kasa kunne yana sauraro,muryar Kasim d'an Baba Munniru ne ya daki dodon kunnuwansa,

    '' Don Allah ki yarda da kalaman da suke fitowa daga bakina,soyayyarki ce ke 6oye acikin zuciyata wadda ta zamo sirri tsakanin zuciyata da kirjina,hakika nayi tattalin wannan sirrin da cewa bbu wanda zan fadawa shi sai ke kadai da kika fi cancanta ah zuciyar yan mata,tabbas na zaga zuri'ar nan,ga yan mata nan da yawa acikinta ammh ko kadan banga wacce tamun ba kamarki *MUBEENAH* ,kuma na zabi fallasa sirrin zuciyata ne aduk randa Allah ya kawoki garin Abuja sai gashi ya fad'a ah bikin Hamma Gidado,plsss enmata kice wani abu man don Allah ki amince mu zamo mutane na farko da zasuyi auren dangi acikin zuri'ar nan kinji plsssss na hadaki da Allah Mubeenata ina sonki kuma ina qaunarki....''

Jikinta ne ya dauki rawa sosai,zufa ya shiga tsastsafo mata kota ina don sosai kalamansa suke neman rud'ata,da rawar murya tace''Ham..ma  ka...sim don girman Allah karka ce dani haka,,yabba (haka suke kiran babanninsu) zai mun fad'a sosai don ya hanani tsayawa da samari saina gama aji shidda wai,kuma zanso ka cire soyayyata aranka tun kafin wani yaji ma don kasan ba'a ta6a auren dangi ba ah zuri'armu tou baka ganin watakila asamu matsala idan zancen nan yyi kuskuren fita har akaji? Hamma Ka.....!''

  ''Mubeenah ki gane man! wlh Kasim ya kamu da mugun sonki kuma gaskiya wlh bazan iya hakura dake ba,insha Allahu akanmu za'a fara auran dangi acikin zuri'ar nan,kawai yanzu so nake ki tabbatar mun da amincewrki kar kiji tsoro nida kaina zanje na samu tsoho da maganar kinji?

Ajiyar zuciya ta sauke don idan tace itama din be kwanta mata arai ba tofa tawa Allahnta karya,tace''Tou shikenan naji ammh nidai muyi abunmu asirrance tukunnah zuwa nan gaba idan na kare makarantar saika fito da maganar ammh aynzu gaskia ban bada goyon baya ba....!''

Murmushi ya saki yana kura mata ido cike da zallar shaawarta,yace''Tou gimbiya yadda kikace hakan zaayi nidai amincewarki din dama kawai nake da bukata,tunda kuma kin amince ai komi mai sauki ne,yanzu dai bani lambobin wayarki wanda zamu dunga communicating ta hanyarshi idan kin koma....!''

Wani kasaitaccen dariya Baddo ta saki mai kayatarwa kan tace''Ai yabba ya hanamun rike waya wai saina gama school tukunnah,kaji fa shekaruna goma sha bakwai ammh sai cewa yake wai har yanzu ban mallaki hankalin kaina ba saina kai sha takwas tukun…'' ta ida maganar tare da cuno baki gaba,shi ko sake bin zubin halittarta yyi,komi yaji sai kace ba er sha bakwan ba,girgiza kai yay kan yace''Gaskia kam yabbanmu bai kyauta mana ba,ya zaayi ace zankaded'iyar budurwa kamarki ace bata da waya?yanzu miye abun yi?''

''Abunyi shine ka fita daga harkarta kafin watan soma cin ubanka ya matso kusa kana jina ko?'' ah firgice duk suka juyo kallonsu ya sauka akan Gidado dake tunkaro lungun fuskarsa ahad'e tamk'ar be ta6a sanin dariya ba,gaban Kasim ya shiga dukan chalugud'e,ba shiri ya jingina da bango yana fadin''Hamma Gi.......''

''Hammar kutumar ubanka?yarinya kankanuwa kamar Baddo ce ka jawo zuwa lungu kke kokarin 6atata?eyyy tambayarka nake…!'' ya fad'a cikin tsananin fusata,Kasim yace cikin tsorata''Hamma wlh ba 6atata nakesonyi ba kawai ce mata nayi inasonta da aure…!

Takaici duk yabi ya cika Gidado yace''Sonta?meh yarinya karama kamarta ta sani agame da so?in da gsk kake ma tou meyasa baka gaya mata ah filin duniya ba sai janta lungu kayi wato salon ka yaudareta da soyayyar karyarka ka 6ata mata rayuwa ko?ai duk ina la6e ina jinku kuma na rantse da Allah idan ka sake bari na ganka da ita ah ke6antaccen wuri kaji nace Allah sai kayi kwanan cell bayan na gama farfasa maka jiki da rodi...!""

Gidado yashiga karkad'a yatsun hannunsa biyu yana fadi cike da zafi''Oya tun daga wajen tsugunna ka soma tsallen kwad'o don idan ka bari na matso kusa abun bazai maka k'yau,,maza nace...'' ya ida maganarsa tare da zaro belt din wandonsa yana huci tamk'ar namijin zaki,da sauri Kasim ya tsugunna tare da kama kunnuwa biyu ya shiga tsallen kwadon kuma ta gabanshi zai bi hakan yasa duk ya kara tsorata,ita kuwa Baddo da baya baya ta soma ja tana zubar da ruwan hawaye tare da shessheka,zuciyarta fal tsoro,kallonta Gidado yay yace''Idan kika sake na sake jin shesshekarki Allah saina matso na miki duka black and blue,oya maza kama bakinki....!'' da sauri tasa hannu ta kama le6unanta ammh hawaye be bar zubowa ba,Gidado ba sauki ai saida ya shaud'a masa belt din sau biyu yana fadin''Dan iska mai 6ata yara kawai...'' shi kuwa Kasim aguje yyi cikin gida,kuka ya kufcewa Baddo ganin yana kusanto inda take,ta manne da bango ssai tana fadin''Hamma Gidado wlh shine ya jawoni zuwa nan baa son raina bane don Allah kayi haquri karka dakeni wlh banda ma lfy...!'' yanka mata wawan mari yay yana huci yace cike da haushinta''Shegiya yar iska ashe abunda kikeyi kenan acan kano bamu sani ba?ana yabonki ashe ke din tantiriyace,musa ah fuska fir'auna ah zuci,kaca ne yasa miki ah kafafu ya jawoki nan da kike cewa baason ranki bane?meyasa baki hadashi dasu Yumma,Hajju ko Umminki ba daya matsa kizo,dake kema irinsa ce shiyasa kika biyoshi lungu ku shek'e ayarku da sunan soyayyarka karya ko?''

Wani sabon kukan ne ya kufce mata jin irin mummunar zaton da yakeyi akanta,girgiza kai tashiga yi ayayin da sabbin hawaye ke ziraro mata tace cikin karyewar murya'' _*SULEIMAN…!*_ ka yarda dani wlh _*'MARYAM'*_ da _*'SHAGARI'*_ basu haifi 'yar iska ba,tsautsayi ce kurum ta kawoni lungun nan ammh bawai da nufin iskanci ba kamar yadda kke zato...!'' tana gama fadar hakan tabi ta gabanshi ta wuce zuciyarta na tukuki,shi kuwa jikinsa ne yyi sanyi da kalamanta ammh sai ya fuske tare da doka matsa tsawa yace''K…! ni sa'an wasanki ne da har zaki ambaceni da ainihin sunana kai tsaye bbu girmamawa?kai uban waye yace ma ki kira wannan sunan bayan ba kowane yake da hurumin ya ambaceni da ita ba har sai idan wannan din ya taka wani matsayi ne awajena?…''

Murmushi kawai tayi tana share hawaye ta juyo tace''Kowa ma yana da wannan hurumin ambatarka da ita sai in har bata kama ba,tou ba gashi yanzun data kaman na ambata ba tare da sanin nayi ba?'' tana gama fadar hakan ta wuce abunta ta barshi tsaye nan da tsananin mmkinta,wai shine ayau yarinya karama kamar Baddo ta tsaya tana tanka mishi magana bayan kowa shakkarsa yake acikin zuri'ar nan,ko Kasim dinma ba sa'ansa bane,ya girmeshi nesa ba kusa ba,Kasim befi 25 ko 26years ba balle ita mai 17,kwafa yayi yace''Gaskia yakamata na gyarawa yarinyar nan zama don naga tana neman rainani kafin tazo nan gaba ta bani kunya acikin jama'a…!

    
____________★

Wani abun mamki sai gashi manyan dangin amarya hadda iyayenta sun amshi Jameelah da hannu bibbiyu,aka hadasu ita da amaryar aka musu nasiha mai ratsa bargon jiki,daga karshe aka fito tafiya bayan amarya tasha kukan rabuwa da iyayenta da kuma yan'uwanta,Jameelah rike da hannunta tana ta lallashinta,,Su Nabeelah suka ce sufa basu yadda Hafsah ta shiga motar jameelah ba don basu yadda da ita ba,wasu ma sukace gaskia ne suma basu yadda ba,kalilan ne sukace sufa sun aminta da Jameelar,murmushi Jameelah tayi tace''Tou ai sai wasu su biyomu acikinku idan har baku yadda dani ba,Allah na tuba idan har naso yi mata wani abun ne ai da tuni nayi basai takai ga aure mun miji ba ammh da yake my heart is pure kuma inason wannan auren da mijina ya qaro shiyasa nazo karbar amaryata da kaina wanda hakan na cikin tayashi murna ne....!'' 

''Karya kike munafuka akwai wata kullalliyar da kika shirya mata ne aranki kuma baki isa ba Allah bazai ta6a sa kici wannan nasarar ba,kice da bokanki in jini Hindatuwa goggon amarya wai yayi karya…!

Murmushi kawai Jameelah ta saki zuciyarta na azalzala ammh dake ita din macece er bariki sai bata nuna cewa maganar ta zafeta ba,majority sunki yadda ta shiga motarta,hakan ya jawo cece kuce ga kuma dare na lulawa,,Hafsah amarya dai taga ana 6ata mata lkc ta dubi Jameelah dake kusa da ita tace''Yayata ina motar taki ne?muje in shiga...  ''

wasu sukace cike da mmki''Hafsah meh kikace?kin amince zaki shiga motar kishiyarki?''

Wata ta kara da''Ke wacce irin mutumce baki tsoron ta miki wani muguntar ko kuma ma ta kasheki?''

''Babu ruwan kowa dani imma ta kashe ai abakin aurenta... '' cike da mmki ake kallonta ita kam Jameelah sai da gabanta ya fadi dajin wannan furucin ammh sai ta dake ta kamo hannunta sukayi wajen motar,bbu wanda yyi yunkurin hanawa ammh akace Nabeelah da wata kanwar mahaifiyarta subi bayanta..........


   **
Cikin ikon Allah kuwa abinda ba'a zata ba kuma baayi tsammani ba sai gashi an isowa da Gidado da amaryarsa lafiya lau,yana dakin Hajju yasoma jin bud'a ya karade gidan,an kaita wajen tsoho ya sanya mata albarka tare da nasihu duk an musu daga Jameelar har ita Hafsan,iyaye maza ma sun tofa albarkacin bakinsu sannan daga karshe aka nufi part din Hajju da ita don tasa mata tata albarkar da kuma bata  _*'RUWAN KWARYA…!*_ tasha kamar yadda sukeyi ah al'adance,hannunta makale acikin na kishiyarta jameelah...........



 

  _*Salon na daban ne my fiful muje zuwa*_
_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

   _*7 free pages to go don haka ku hanzarta yin register*_




_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_
*🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   
*#An_Intense_Jealousy_Story*

          _*💫BABI NA HUDU...🤟☝*_

………! Ah barandar sashin Hajju suka iske ita Hajjun zaune tana jiran isowarsu,hannunta dukah biyun rik'e da wani babban k'warya wanda ruwan magani yayi rabinsa,zaune agefenta kuma Yumma ce,adayan gefen kuma Haj.Karama wato matar Baba Alseny,sai kuma sauran kishiyoyin farfadanta dake tsaye acan gefe,da gud'a aka karaso da Hafsah wajen hannunta sakale acikin na jameelah,Ramlah ta taimakawa Jameelah suka durk'usar da Hafsan agaban Hajju wacce sai faman shesshek'ar kuka take tayi irin dai ta amare,Hajju ta mik'awa Yumma k'warya tana fadin''Ummerherny rika mun nan…!'' Yumma tasa hannu ta karba idonta k'yam akan Hafsa surukar tata,Hajju ta mik'e tsaye dauke da murmushi akan fuskarta ta aza hannunta akan Hafsa tace''yata muna miki barka da shigowa cikin zuri'armu mai albarka,wato zuri'ar *'TSOHO SULEIMANU*' ,,Hafsatu Allah yasa kin shigo asa'a da kuma kafar dama,Allah kuma ya baki ikon bin mijinki sau da kafa da kuma kyautatawa danginsa sannan kuma ya wanzar da zaman lfy atsakaninki da abokiyar zamanki,Allah kuma ya azurtaku da zuri'a zayyaba.....!'' sai jero mata ameen ake tayi,ita kanta amaryar tana ta amsawa ne ahankali,

  Hajju ta cigaba''Akarshe kuma ina rokanki wata alfarma da kika bani dama na gudanar da wasu al'adunmu da muke yiwa duk wata wacce ta shigo cikinmu shi da kuma wacce muka bayar waje wato namu 'ya'ya matan kenan, _*'WANKAN RUWAN KWARYA DA KUMA SHANTA'*_ domin kariya agareki acikin rayuwar aurenki wannan shine al'adar,,shin Hafsatu da mutanenta kun bamu wannan damar?don hakan shine zaisa muyi maraba da ita acikin zuri'armu…!''

  Kai tsaye mutanenta suka ce sun amince,Hajju ta dubi amarya da kanta ke duk'e akasa tace''Amarya inason naji ta bakinki,shin ki amince amiki wannan al'adar tamu…!?'' murya na rawa tace''Naaaa....amin...ce.....!''

Habawa ai sai ko'ina ya dauki gud'a....

   ____________★★

Sauri sosai Baddo take ta raftawa don tazo agudanar da wannan al'ada ta zuri'ar tasu agabanta ta gani sbd ba'a ta6ayi tana nan ba,duk bukukuwan da akai tayi da wayonta dinnan bata samun damar zuwa don alokacin sai kaga tana cikin jarabawa ne,wannan shine karon farko da za'ayi shi agabanta wanda ta dad'e tana ta dokin zuwan wannan ranar,kaya kala uku ne suka wankewa Hajju ita da su Hanifa kannan Kasim tou shine aka kwashe kayan ah igiya aka bata takai dakin Hajjun,wannan dalilin nefa yasa take ta sauri takai kayan dakin sannan ta komo waje tasha kallo,sai ji tayi ta buge mutum ah kofar shiga dakin Hajjun,ninkakkun kayan kanta suka fad'o tare da watsewa akasa,ta daga kai tana duban wanda ta bugen,idonta ne ya sauka akan Gidado wanda ke watsa mata wawan kallo,gabanta yayi wani irin bugawa da sauri ta juya zata koma,ganin hakan yasa yyi hanzarin sa hannu yayo grabing kafadarta cike da mugunta tare da forcing dinta ta waiwayo gareshi,lafiyayyen kwankwashi mai kyau ya zuba mata yace cike da tsanarta''Hegiya kin buge mutum kin juyo zaki koma ba tare da kin bashi hakuri ba dake ni kin rainani ammh na tabbata da'ace wancan abokin iskancin naki kika buge da har rungumarsa zakiyi kina bashi hakuri,come on will u get down on ur knees and say sorry ko kuwa saina fasa bakin tukunnah…!?'' kuka ta sanya masa meh daga hankali tace''kayi hakuri ni wlh bansan da mutum abakin kofar bane....''

''Yar iska kawai ina zaki sani kuwa bayan idanun sun rufe da iskanci?dallah mallama give me way na fita kafin na zaune miki aruwan ciki,dubi abu kamar buhun siminti....'' ya ida maganarsa ah kufule,azuciye tace''Nidai wlh Hamma na gaya maka kabar kirana da er iska ni ba ita bace plssss....''

Kallonta yay akaikaice yace''wato nine ma dan iskan ko?'' ya furta yana kokarin kwanto belt,da sauri ta jaah da baya tace''A'ah wlh ba kai bane niche...!'' ta fada hawaye na ziraro mata,,murmushin mugunta yyi sannan yace''Good gal....kuma daga yau sunanki yar iska,koki bari na dunga kiranki da hakan ko kuma a'ah bakiso gwara inje in fasa kwan ince musu na ganku kuna shek'e aya ah lungu ta bayan sashin Baba Haruna,,tou wanne aciki kika za6a?…!'' runtse ido tayi tana jin zuciyarta na azalzala da muguwar tsanarsa,shiru ta masa taki bashi amsa,hakan yasa murmushin mugunta sub'uce mishi yace''okay fine i will assume u choose option one and daz very good of you,,tou yar iska bani hanya in wuce…!''

     ******
Kwaryar Hajju ta karba tare da bismillah sannan ta kwararawa Hafsa tun daga kai har kasanta,ko'ina ya dauki gud'a ita kuwa fashewa da kuka tayi don dole kaji wani irin imani da tausayin kanka ya ratsa zuciyarka ah sa'ilin da ake maka wannan wanka,Hajju ta rage kadan aciki ta mika mata tace''karbi ki shanye wannan…!'' hannu na rawa ta karba ta kafa abaki ta shanye tass! sannan ta mayar mata da kwaryar,Hajju ta karba ta daga empty kwaryar sama sannan ta kifar dashi,,ji kke taratasss!ya fashe sai aka shiga rangad'a gud'a akan nada,fashewar wannan kwaryar ba karamin firgitar da Baddo tayi ba don ah tsorace ta shige jikin Gidado tare da fasa ihu jikinta na rawa,adaidai lokacin kuma Hanifa ta tunkaro dakin take fadin''Baddo kina ina ke meh son ganin al'adar wankan ruwan kwarya gashi dai an sake sha dake ku....!'' maganarta ta yanke ah sa'ilin da kallonta ya sauka akansu Baddo rungume dashi,sannan kuma ga belt din dayaso kwancewa ada ya daketa dashi ammh sai be karashe kwancewar ba ya barshi,hakan ne yataimaka wajen raya mummunar zato acikin zuciyar Hanifa,cikin rawar murya tace''Ham...maaaa ashe da...damaa kai din dan...dan iska ne ban sani ba?habba Bad..doo hadda kema kin biye masa ya 6ata miki rayuwa abanza?''

Dasauri ta juya zata koma,hakan yasa yayi hanzarin tura Baddo ta fadi kasa sannan ya finciko Hanifa,tana juyowa ya sauke mata mari yana huci yace''Ke don ubanki nine zaki kalla ki kira da dan iska don bakki da kunya?abunda kika gani is unintentionally don haka idan kika sake naji wannan zancen awaje tou wlhy saina saki kinyi zama ah prison harna tsawon shekaru biyar......'' atsorace ta dafe kirji tace''Na shiga uku ni Hanifa ah prison dai??''

Dariya ne yaso kufce masa ganin tsoron dake shimfid'e akan fuskarta,yace''Yes! you heard me right prison nace sannan kuma bayan kin fito i will cut ur head off,so be warned idan kinason ganin kanki araye,,now get the hell out of my sight....'' da sauri tace''Insha Allahu bbu wanda ma zaiji zan kiyaye Hamma...'' ta juya tabar wajen da sauri sauri har tana harde kafafu,ya dubi Baddo dake durkushe tana kuka yaji wani irin muguwar tsanarta ta sake samun matsugunni acikin zuciyarsa,yace cike da tsanarta''An saba da iskanci shiyasa aka rungumeni don jan raayina,tou bari kiji ni din ba irinsu bane sannan kuma ke baki da abunda zai iya jan hankalina zuwa gareki,,bbu abunda zaki nunawa matayena sai ma su su nuna miki daga Jameelata har hafsata,so i beg u karki sake hada jikinki da nawa koda wasa ne if not sai kin yabawa aya zakinta,,foolish gal kawai yar iska.....!'' ya ida maganarsa tare da jan wni irin dogon tsaki,komawa gaban dressing mirror din Hajju yayi ya dauki turarenta mai kamshi ya feffeshe jikinsa dashi sannan ya fita ya barta zaune tana cizgar kuka kamar ranta zai fita,dakyar ta iya dagawa ta ninke kayan sannan ta zuba mata ah wadrope ta fita waje tama tarar an gama komi sai ma shirin kai Hafsa mota ake don ayau dinnan zaa sadata da dakinta,,kuma Tsoho ya bukaci da kar kowa ya bita,yace Gidado ya kwashi matayen nasa su wuce abunsu,don haka yan'uwanta sukayi sallama suka wuce gida bayan sunga tafiyarsu Gidadon,ammh kafin su wuce saida kawayen amarya suka kasa suka kuma tsare wai fa alallai sai an sallamesu,Gidado beda lokacinsu don haka sai yabar su sagir wai suji dasu,,

Hafsa ce abaya ayayin da Jameelah ke zaune ah gidan gaba,straight Asokoro road ya nufa inda anan ne gidan nasu yake,Gida ne wanda ya amsa sunansa da gda,no long story kunsan dai mutum kamarshi mai matsayi babba awajen aiki ya dace ya mallaki gida na kece raini,Jameelah ce dai ta sake ruko hannun Hafsa suka shiga ciki,sashi daya ne ammh mai girman gaske wanda kowacce tana da part dinta ammh kofofin kowani part nata cikin makeken falon gidan ne,duk inda ka taka sai kafarka ta nutse,ko'ina clean ga wani daddadar kamshin daya gauraye guri,wannan duk aikin Jameelah ce iyayen tsafta,tanan kuwa Gidado yake tsananin alfahari da ita da kuma biyayyarta agareshi,kai tsaye part dinta Jameelah ta kaita sannan ta komo nata don watsa ruwa,

  Ah gefen gado yasamu Hafsa zaune harta kwabe mayafi ta ajje,azuciyarsa yace''Allah sarki Jameelata aranar da aka kawomun ita dakyar na iya yaye mayafinta ammh wannan ko jira na roka bata bari nayi ba she allow me to see the face free of charge,agaskia Jami tayi ne....!''

Tsokanarta ya shiga yi yace''Amarsuu ke ko dan jan'aji irin dai taku ta amare bbu?''

''Meh ka gani?''

Takaici ne duk yabi cikashi ganin ita bata masan abunda tayin ba,kamar bazai sake magana ba can kuma yace''Gani nayi baki jira na roki ah bud'emun fuskar ba kamar yadda dai naga akeyi,sai ganinshi nayi free of charge,yanzu fisabilillah idan daace da abokaina na shigo fa ai da kin kunyatani ba kadan ba don zuwa zasuyi sutayi dani wai matata ba kunya ba class.....!''

Ah zuciye tace''Suce din mana ina ruwana badai an kawoni gidan masoyina ba?sannan kuma kai din yau ne na soma ganinka da har zanji kunyarka?'' mmki ne ya kusan kasheshi tsaye anan da yadda ta karba masa magana,lallai kam zaiyi fama da ita don ya lura sosai zatayi rashin kunya abunda Jameelah bata masa kenan,tana mugun gudun 6acin ransa.....

Kala bece mata ba,har zai fice daga dakin sai ga kiran sagir na shigowa,yana dagawa Sagir yace''Kai dan iska da fatar dai ka tsaya ka siyawa amarya kaza akan hanya don nasanka akwai shegen mantuwa.....!''

Dafe goshi yayi yace''Goddd!! wlh Sagir na manta kuma gashi yanzu to eleven,,ammh bari inje Allah yasa suna nan....'' 

''Suna nan mana har 12 suna kaiwa,and please idan zaka siya ka siyawa uwargida don azauna lfy haka ake yi...''

Murmushi yay yace''Ai Jameelah bata da matsala....''

Sagir yace''Kai dai ka siya mata banson gaddama,infact jirani gani nan zuwa dashi....'' kan ya sake magana ya kashe wayar,murmushi yayi yace Allah sarki Sagiru abokin kwarai....

''Gidado wato niche ma mai matsalar ko?'' haka yaji Hafsa ta furta ah kufule,,da mmki ya waigo yana kallonta yace''Kinji na fadi hakan ne?''

Saida ta saki dan siririn tsoki kan tace''Ai cewa kayi wancan matar taka batta da matsala which means badin ina kusa ba kaso kace masa niche mai matsalar ko?''

Hmm lallai ina da aiki sosai agabana abunda ya iya ayyanawa aransa kenan,be bata amsa ba yace''Nidai kije ki watsa ruwa kafin kazar amaranku ta iso don nasan shima din gab kike da tsareni da tambayoyi akansa tunda na lura ke din kunya be isheki ba…!''

Dirowa tayi daga kan gadon tace''Lallai ma Suleiman niche din bani da kunya?...'' wani irin shewa tayi gami da tafa hannaye tace''Lallai ko ni Hafsa zan gwada maka rashin kunya irin tawa acikin gidan nan,,kai dai zuba idanu kasha kallo,,kuma wni wanka ne zanyi bayan wacce aka mun da sunan wani al'adar banza?duk anbi an jika mutum da ruwa mtswwww...''

Har ya daga hannu zai kifa mata mari,ko mai ya tuna kuma sai gani nayi ya dakata tare da dunkule hannun,zuciyarsa na azalzala,,tsantsar mmki ne ya cikata ta kama kugu tana fadin''Eyyy meh nake gani haka Suleiman?marina kke shirin yi?lallai da baka kuma ba don kana marina tou wlh matarka zata jishi ah jikinta itama...!''

Idanunsa sunyi jajur dasu tamk'ar jan gauta,yama kasa furta komi dkyar yace''Fine Hafsah nagode...!'' ya juya yabar dakin ransa ah jagule,ah makeken falon ya hango Jameelah zaune cikin night gown dinta tana rusar kuka don tana ta juyo hanyaniyar Hafsah,muryarta asaman na mijinta,,jikinsa ne yay sanyi qalau ya nufi inda take....................!!



 

_*yanzu wasar zaya soma armashi😎sai ku biyoni*_

_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488



_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_

       *🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   
*#An_Intense_Jealousy_Story*

          _*💫BABI NA BIYAR...✋*_

…! Zama yayi akusa da ita tare da jawota ta fad'o jikinsa,kuka take sosai mai tsuma zuciya wanda ya had'e da kukan kishi,hura mata iska yayi acikin kunne don yasan abinda tafi so kenan idan har zai lallasheta kana yayi mata rad'a ah kunne''Hearthrob wannan kukan na menene haka ko duk na kishin ne?I beg you karki daga hankalin Gidadonki plsss,,trust me nadai auri Hafsah ne akan tursasawar iyaye ammh zuciyata tana tare dake ne....!ʼʼ

  ''..Naji na kuma amince ammh ai gashi shi gangar jikin kuma ka raba mana ai,,Suleiman hakikʼa ina tsananin kishinka ammh kokari nake na danne zuciyata don banison na kasance acikin matayen dake tafiyar da rayuwarsu akan kishin jahilci,,bani son ganinka cikin tashin hankali mijina balle ace niche sanadin shigarka cikinta,,tun baʼa kwan ba Hafsah ta riga da ta nunan da kalar data shigo ammh karka damu sahibul kalbi zanci maganin hakurin zama da ita saidai kuma ta kiyaye kar hakurin nawa ya kare wataran,,Sahibuna plsss na rokeka karka dunga biyewa fitinarta gaji.....ʼʼ

      Wani kallon shaukʼin so yake binta dashi yana jin wani irin zazzafar soyayyarta na shigarsa dakyau,,ahankali ya zame hular kanta ya cusa kansa aciki yana shakʼar kamshinsa,da sauri takai hannu ta rikʼe kan nasa tace"No no no plsss stop it sahibul kalbina its wrong,pls karmu shiga hakkʼin amarya ka tashi

Please Login or Register in order to submit comment