Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so ta amsa sunan 'yarki bana son Faruoq yasan d'iyar da na haifa ce saboda hakanne zai bani damar cika burina na had'asu aure, ku sanar mishi 'yar da na haifa itama ta rasu, don Allah kumin alqawarin rufe wannan sirrin tsakaninmu mu uku.‘’
‘’Insha Allahu Yaya ba mutuwa zaki ba da kanki zaki shayar da 'yarki .‘’
‘’Ina ji a jikina bazan tashi ba Habiba ku dai kumin wannan alqawarin, bansan ya rayuwar Faruoq zatai ba idan yasan ba mune mahaifansa na gaskiya ba kuma ina son yarinyata ta kasance a k'ark'ashin inuwarsa wannan ce kawai hanyar da zata saka burina ya cika.‘’
Takai k'arshen maganar tana sauke idonta akan Abba da ke bitar kalamanta cikin k'wak'walwarsa, shima zaiso yarinyarsu ta kasance inuwa d'aya da Faruoq to amman ta ya ya?muddun suna son Faruoq yaci gaba da amsa sunan d'ansu na ainihi sai dai dole ta hanyar da Oummi ta kawo d'in, to amman kuma ba cewa akai Oummi mutuwar zatai ba, zafin ciwone kawai yasata yin wayannan maganganu, don su kwantar mata da hankali dukkaninsu sukai mata alqawarin da take so har ta saka Abba ya kira mata Faruoq da kanta ta sanar masa ta haihu yarinyar ba tazo da rai ba, kuka wiwi Faruoq ya nemi guri ya zauna yana yi ya qwallafa rai sosai akan k'anwar tasa, yaso zuwa a washe gari Abba yace yai zsmansa ba sai yazo ba....










KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai.
Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal.
09037093702


#N.W.A
#Comment
#Share
[7/12, 7:03 PM] Rabi: BEBEARTH

https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v
[11:51PM, 11/24/2021]
Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata.


CIN AMANA



Wattpad@Rashuna


7

Tsakiyar dare ciwo ya dawowa Oummi sabo a wannan dare kuma ta amsa kiran mahaliccinta, Habiba ce kawai ta sani kuma ba ta sanarwa da Abba ba sai zuwa safiya, jarumta sosai Allah ya saka mishi da kansa yayi mata wanka zuwa k'arfe takwas na safe har an kaita makwancinta, ana tafiya Faruoq yana zuwa kwata kwata ba ya cikin hayyacinshi·

Habiba kuwa dauriya kawai take yi amman ga tanan ne sam ba ta jin dadin jikinta mutuwar 'yar uwar tata ta kad'ata yadda ba kwa zato, tana cikin wannan halin kiran waya ya sameta Allah yayiwa mijinta rasuwa sakamakon had'arin mota, fad'uwa tayi a gurin a sume don k'wak'walwarta ta gaza d'aukan wayannan al'amuran, anyi ko wani dabaru a gida amman ba ta farfad'o ba hakan yasa aka nufi asibiti da ita, bincike na farko likitoci suka sanar da in dai ana son cikin jikinta da rai sai an mata cs an ciro shi ba b'ata lokaci Abba ya saka hannu aka shiga da ita·
An ciro mata d'a namiji amman k'ank'antarsa ta sanya sai da aka sanya shi cikin kwalba·
Jaririyar Oummi kuwa tana cikin asibitin an kwantar da ita saboda lura da akai itama ba ta da cikakkiyar lafiya kuma tana yawan suma·
A b'angaren Farouq kuwa rufe kansa yayi a d'aki duniyar gaba d'aya tayi masa zafi, kalamanta yake tunowa sanda zai tafi makaranta ashe ganawar k'arshe sukai yaji muryarta ta k'arshe jiya a waya, yayi kuka sosai kuka na sabo kukan da ya tabbata Oummi ta tafi kenan baza ta dawo garesu daga k'arshe yayo auwala ya kalli gabas yana nemawa Oumminsa rahama gurin Ubangiji·


A haka rayuwa ta nutsa taci gaba da tafiya zuk'ata babu dad'i sai dai godiya ga Uabangiji, Habiba ta fauwalawa Allah lamuranta yayin da ta fara shayar da tagwayan yaranta, ba ta b'oyewa dangin mijinta ba ta sanar musu macen yarinyar yayarta ce da ta rasu saboda rabon gado don har sun fara zancen kamar jira suke ya rasu·
Macen sunanta Ruqayya suke mata lak'abi da Fadila namijin kuma Abubakar suna kiranshi da Fahad, sun taso kansu d'aya komai nasu iri d'aya Habiba ko kad'an ba ta bam bamta su, in ba su da suka sani ba babu me cewa ba 'yan biyun gaske bane·
Bayan shekaru biyar Abba da Habiba (Oummu)suka dai daita kansu sukai aure suka tare a gidan da Abba ya gina anan Kaduna unguwar kawo, Fadila da Fahad suna cikin shekarunsu shida a duniya ajinsu d'aya a makaranta suna primary 3·
Faruoq kuwa ya zama d'an sanda yana cikin shekarunsa 21 da d'an albashinsa suke samu su rufawa juna asiri sai kuma d'an abinda Abba ya samo, sosai yake bawa k'annensa kulawa komai ya samu Fadila da Fahad, suma sun shak'u da shi sosai musamman Fadila indai yana gida tana gurinsa a lokacin ne kuma Fadila take yawan suma aka kaita asibiti inda bincike ya nuna tana d'auke da ciwon Hyphatetic (HC)a cikin zuciya yake a hankali yake dakatar da bugawar zuciya idan ba'a ankara ba sai zuciya ta tsaya gaba d'aya kuma aikinsa da tsada bama ayi anan k'asar tamu sai k'asashen waje·
Kowa ya jijjiga da jin ciwon da Fadila ke d'auke da shi gashi basu da ko kwatan kudin aikin ko da kwa sun sayar da dukkan abinda suka mallaka haka akai mata 'yan dabaru suka dawo gida zuciyoyi babu dad'i amman dukkaninsu sun d'ebo sabuwar kulawa sun d'ora akan Fadila, Abba ya saka ana yi mata rubutu tana sha cikin ikon Ubangiji kuma sai ta jima ba ta suma ba a haka rayuwa taci gaba da gangarawa da dadi babu dad'i·











KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai.
Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal.
09037093702


#N.W.A
#Comment
#Share
[7/15, 3:34 PM] Rabi: BEBEARTH

https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v
[11:51PM, 11/24/2021]
Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata.


CIN AMANA



Wattpad@Rashuna


8

Fadeelah ta tashi da soyayyar Faruoq a zuciyarta musamman yadda yake bata kulawa duk abinda take so shine yake mata, tun ba ta san wata iriyar soyayya take masa ba har ta farga da yadda ta zurfafa cikin soyayyarsa yayin da ta mallaki hankalinta, ta riga da ta san ba ciki d'aya suke da Faruoq ba saboda yadda Oummu ke nuna mata saboda samun cikar burinsu kar ta rayu da soyayyarsa ta 'yan uwantaka tazo ta bijire musu daga baya.
Fadeela fara ce k'al irin farin nan me shiga ido, akwai ta da kyau dai-dai misali, suna da shekaru goma sha shida suka kammala secondary Fahad har ya fara zuwa university ita kuma Abba yace sai dai tayi a d'akinta, to da yake dama karatun ba damunta yayi ba sai ba ta wani matsa ba, sam ta kasa saurarar wani saurayi da sunan soyayya, kuma abinda ta lura ma su Abba ba su bata damar hakan ba, ga soyayyar Faruoq tana ta cin zuciyarta wani zubin har ta hanata rintsawa, musamman yanzu da yayi mata nisa yau yana wancen k'asar gobe yana wancen saboda yanayin aikinsa, gashi bai san tana yi ba abinda ta lura ma shi har yanzu yanai mata kallon k'anwarsa da suka fito ciki d'aya.

Faruoq H. Abdul Salam copy colour ne, doguwar fuskarsa na d'auke da tsayayyan hanci me kyahun gaske, idanuwansa ba wasu manya bane cen, amman kyawawa ne, don idonsa kad'ai abin kallo ne, suna d'auke da zara zaran eye lashers, ga cwt lab'b'ansa masu gwanin burgewa, babu saje ko gemu akan fuskarsa haka zalika ba ya barin suma kullum kansa a saisaye yake, dogon mutum ne tsayayye Allah yayi mishi suffar k'arfi gashi da k'wak'walwa da jajircewar aiki, saboda naicinsa da iya bincikensa ya samu nasarar shiga hukumar 'yan sanda ta duniya (police interpol)
a yanzu yana da shekaru talatin da biyu a duniya, yanayin aikinshi yasha mishi kai ko zancen aure ba ya yi gani yake idan ya tsaya soyayya za ta cinye masa lokaci, yanzu ko zaman gida ba ya yi da wuyq yayi sati a gida, yanzu ma yana Oyo tare da yaransa amintattu Yousuf da Khalil da Sadiq.
Abba da Oummu kuwa sunyi d'amarar tunkararsa da maganar auransa da Fadila tun da ta riga tayi candy jiransa kawai suke yi ya dawo asha biki.
A daren kwa da ya dawo Abba ya tunkareshi da maganar had'asu auren da suke so suyi da Fadeela inda ya nuna shi sam bashi da burin yin auren zumunci soyayyar da yakewa Fadeela soyayya ce ta k'anwa da yayarsa da suka fito ciki d'aya shi a yanzu ma bai shirya aure ba ya rok'i Abba da kar ya bari Oummu ta ji saboda zaiji kunyarta ya karb'i abinda babu shi a zuciyarsa, hankalin Abba yayi k'ololuwa gurin tashi ko kad'an bai tab'a tunanin Faruoq ba son Fadila yake ba duba da yadda shak'uwa ke tsakaninsu tun da ya jima da karantar Fadilan na sonshi sai yayi tunanin soyayya suke yi, a ranar Abba raba dare yayi bai bacci ba tunani yayiwa zuciyarsa yawa yabi ya cunkushe, mene ne amfanin b'oyewa 'yarsa d'aya tilo da yayi shine mahaifinta na gaskiya idan har Faruoq bai karb'i buk'atarsa ba?
Kenan burinsu shi da Oummi zai ruguje, ya rayuwar 'yarsa d'aya tilo za ta kasance idan ta san Faruoq ba sonta yake ba, gashi ba lafiyar zuciya ce da ita ba, don kwanaki Faruoq ya had'a kud'in da zaai mata aikin, amman sai likitocin suka ce zuciyarta ta tab'u, bai zama lallai in akai mata aikin ta rayu ba jin hakan yasa Abba yace a fasa aikin shine suka basu shawarar a kiyaye b'acin ranta, a dunga sanyata farin ciki ko da yaushe to za ta zauna cikin lafiya...










KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai.
Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal.
09037093702


#N.W.A
#Comment
#Share
[7/16, 5:02 PM] Rabi: BEBEARTH

https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v
[11:51PM, 11/24/2021]
Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata.


CIN AMANA



Wattpad@Rashuna


9

A b'angaren Faruoq ma yayi da kacen k'in amsar tayin Abba, saboda tunawar da yayi ya dad'e da karantar soyayyarsa cikin idanuwan Fadeela duk da k'ok'arinta na b'oye masa kuwa amman idanuwanta suna fallasata, baya da burin wani abu ya samu Fadila ta sanadiyarshi don haka zai aminta da aurenta saboda,gudun fad'awarsu matsala gaba d'aya.
Washe gari da safe yaje ya samu Abba akan ya amince da auren Fadilan, amman don Allah kada Oummi da Fadilan su san da ya bijirewa aurenta, zaiyi k'ok'ari gurin sauya soyayyar da yake mata zuwa bigiren soyayyar aure saboda ba ya son abinda zai tab'a zuciyar Fadilan, amman kaish rashin sa'ar da akai Fadilan ta kawo kai d'akin Abban sanda suke maganar ta riga taji komai don haka tayi saurin juyawa ba ta bari sun ganta ba.
Faruoq yana k'ok'ari gurin nunawa Fadeela soyayya duk da ba ya jinta a zuciyarsa har yanzu, soyayyar nan da yake mata ta k'anwarsa ba ta canja zani ba, Fadilan ma ba ta nuna masa ta san ya amince da aurenta ne saboda lalurarta ba, duk da in ta tuna hakan ta kan ji ba dad'i a ranta, a haka dai har aka sanya musu rana.


Kwatsam a wata ranar Asabar Abba yana gida bai fita ba, haka ma Faruoq yana d'akinsa shima, hutawa yake ranar sai suka ji muryar wata dattijuwa tana sallama, Abba da suke hira da Oummu yace.
‘’Kamar muryar Umma nake ji.‘’
Kafin su amsa mata a tare suna lek'owa, Umman tasa ce kuwa a tsaye ta bisu da kallo gaba d'ayansu, Abbane ya fara cewa.
‘’Sannu da zuwa Umma, yaushe kika dawo daga saudiyar, dama kinsan gidan nan ne.‘’
Wani kallo ta jefeshi da shi kafin tace.
‘'Sannu tatacce mara kunya, yanzu Hashim rashin hankalin naku har yakai ku k'auracewa ahalinku kui musu b'atan dabo saboda tsintaccen muzuru, in Ruk'ayya ba ta da hankali ai kai ka fita hankali.‘’

Gaban Abbane ya yanke ya fad'i, kamo hannun Umman yayi yana k'asa da murya yace.
‘’Umma don Allah ki shiru, kizo mu shiga ciki ki huta.‘’
‘’Nak'i nayi shirun.‘’Ta fad'a tana fisge hannunta daga nashi kafin ta kalli Oummu tace.‘’Kema Habiba kina tare da su kenan, dama kema ance sam ba'a jin labarinki tun da suka gudu, to ina Ruk'ayyan?‘’

Tana kai k'arshen maganarta Fahad da Fadila suka shigo d'auke da sallama a bakinsu, ganin iyayan nasu a tsakar gida da wata dattijuwa yasa su yin turus suka tsaya kafin idanunta su sauka a kansu ta kuma jefo musu tambayar.
‘’Su waye wa'yannan yaran?‘’
‘’Umma kizo mu shiga ciki ki huta duk zakiji komai‘’ Cewar Abba yana dad'a kamo hannunta to a yanzu dai ba tayi mishi musu ba ta biyo bayanshi zuwa ciki.

Faruoq tun da yaji kalmar TSINTACCEN MUZURU kalmar ta tsaya mishi a zuciya ya rasa me yasa, bacci yake son ya d'auke shi, kusan watansa guda ba ya k'asar sam bai samu hutu ba yau yake son ya samu amman tun da yaji wannan kalmar gabansa ke fad'uwa sam ya kasa samun sukuni innalillahi yake ta ambata a zuciyarsa.


Bayan Umma taci abinci tayi sallar la'asar da aka fara kiraye kirayenta, Abba ma ya tafi masallaci shi da Faruoq, Umma ta kalli Oummu tace.
‘’Kusan watana biyu ko uku da dawowa, duk wani dangi in na zaga sai ace ba'a san inda kuke ba, hankalina in yayi dubu ya tashi, gashi kusan shekaru ashirin rabon da muyi waya da Hashim tun da layina ya samu matsala, gashi bai tab'a bani labarin kun yiwa danginku b'atan dabo ba,idan kikaji wahalar da na sha kafin a lalibon inda kuke sai kin rik'e baki.‘'

‘’Allah sarki, shima yana nan kullum sai yayi k'orafin ba ya samun ki a waya, kuma abinda yasa bai gaya miki ba ma kano ba saboda kince masa ba zaki dawo ba har sai ta Allah ta kasance da ke a can, duk magiyar da yake miki akan kizo ko da sau d'aya ne ki koma amman kikace ba za kizo ba, ya damu k'warai da gaske, bare da yaga an d'ebi wayannan shekaru masu tsayi ba tare da kunji muryoyin juna ba, sai ya dinga cewa to ko Umma ta rasu ne, har sai da Faruoq yayi mishi alk'awarin Hajji bana ko zaku had'u a can.‘’

‘’Yo nima kawai ji nayi hankalina ya yo gida, ina son nazo naga d'ana d'aya tilo ko ya ajiye mini dozin d'in jikokin da yake yawan fad'i?‘’ Murmushi kawai Oummu tayi a dai dai lokacin Abba ya shigo, bayan da ya k'ik'k'iro aike ya aiki Faruoq saboda sam ba ya son sui wannan maganar da Umma yana cikin gidan don haka bai shigo ba sai da yaga tashin motar Faruoq d'in, Fahad da Fadila ma sai da Oummu ta aike su.
Komai da ya faru daki-daki Abba ya zayyanewa Umma, mahaifiya ce ita babu damar ya b'oye mata, kuma ta riga ta san Faruoq d'in ba d'ansu ba ne.
Umma kuwa salati take da sallallami tana ganin rashin hankalin Ruk'ayya da Hashim, musamman ma Hashim d'in tunda ita Ruqayya mace ce hankalinta ragagge ne.
‘’ Lallai kun cika mahaukata musamman kai Hashim, in banda rashin hankali yaushe zaku b'oye 'yar cikinku saboda ba kwa son tsintattcen muzuru ya san ba ku kuka haife shi don kawai kuna son ku hadasu a inuwar aure, tunda nake ban tab'a jin wannan d'anyan labarin ba a film ko gidan redio ko littafin hausa, amman sai gashi yau a cikin tsatsona, ba sahakka soyayyar da kukewa wannan tsintaccen tafi wacce kukewa 'yar cikinku, to bari kaji a yau d'in nan sai wannan tsintaccen yasan ba kune mahaifansa ba kuma babu ta yadda za'ai na had'a jini da wanda baisan daga inda ya fito ba ‘’
Gurfana Abba yayi a gabanta yana ta bata hak'uri akan tayi shiru don Allah, amman ina ko saurarasa ba tayi sai fad'a take kamar za ta ari baki.

Da baya da baya Farouq bayan ya gama jin bayanin Abba ji yake yi anan jujjuya shi ko ta ina wani irin jiri yake yi, kalmomin Abbane suke yin k'ara bita a kwanyarsa da bin bango ya samu ya koma d'akinsa.
Tun da yaga Abba ya aikeshi yasan akwai abinda yake son b'oye mishi, akwai wani abu da wannan matar tazo da shi da ya danganceshi Abba ba ya son ya sani shine abinda zuciyarsa ke gaya mishi don haka yayo rivers ya dawo, da ya san abinda kunnuwansa zasu jiye mishi kenan da bai dawo ba ya tafi aikensa sahunsa a likafa, amnan ina k'addara ta gifta dole ne ya san k'addarar dake zagaye da shi cikin rayuwarsa.
Kansa ya rik'e da hannuwa biyu yana jin kamar zai rabe gida biyu, abinda yake ji cikin zuciyarsa so yake ya gaza yafi k'arfin kwanyarsa rintse idanuwansa yayi da suka kad'a sukai jajir yana ambato sunan Allah daga haka yaji hawaye ya fara zuba daga idanuwansa sai ya fara jin sauk'in abin daga zuciyarshi.
Kuka yayi sosai kukan da ya jima baiyi kamarsa ba don tun mutuwar Oummi rabon da yayi irin wannan kukan, daga bisani ya karb'i k'addarar da Allah ya rubuta masa da hannu biyu don ba shi da jaa da hakan bazai zamo mutum me kokawa da k'addararsa ba haka zanen k'addararsa ya rubuta zai rayu tare da mahaifan da basu suka kawo shi duniya ba, amman sun masa abinda bai zama lallai wa'yanda suka kawo shi duniya sui masa ba, yama godewa Allah da ba garari yayi a duniya rayuwarshi ta gurb'ace gaba d'aya ba, baiyo shi da mahaifa ba amma ya bashi mahaifan da suke sonsa fiye da son da sukewa 'yarsu da suka kawo duniya, anya kuwa za'a samu tamkar Oummi da Abba kuwa? kai ina bazai yuhu ba, su d'in na daban ne mutane ne masu girma da kima a idanuwansa bashi da wasu wanda suka fiye mishi su a cikin duniyar nan, in da ya godewa Ubangiji da sai da ya karb'i auren Fadila hakan ya faru da bai karb'a ba da wani idon zai d'aga ya kalli Abba?Bashi da shi bashi da wani karsashi bare idon da zai d'aga ya kalli Abba, mafi aala kawai sai dai su nemeshi su rasa gaba d'aya...















KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai.
Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal.
09037093702


#N.W.A
#Comment
#Share
[7/17, 8:48 AM] Rabi: BEBEARTH




CIN AMANA



Wattpad@Rashuna



10

Har Fadila da Fahad suka dawo Umma na fad'a da sababi, ta rungume Fadila tsam-tsam a jikinta tana jin k'aunarta mai girma a zuciya, (Dama ance abin cikin k'wan yafi k'wan dad'i)

Bayan Umma ta gama zayyanawa Fadila komai, fadila ta d'ago idanuwanta da suka jik'e jagab da hawaye tana kallon Abba, wata iriyar soyayya da k'auna iyayanta sukewa Faruoq ko wata iriyar soyayya ce tabbas ta girmama girma mafi k'ololuwa, ta rayu tsawon shekarunta da mikin bata da mahaifi, ashe mahaifiya ce ba ta da ita, suna tare da mahaifinta cikin gida d'aya suna shak'ar iska d'aya, amman ya b'oye mata shi d'in mahaifinta ne ba shakka soyayyar da sukewa Faruoq ta ninka soyayyar da suke mata.
Rarrafawa tayi ta isa gabansa kafin tace.
‘’Anya kuwa Abba kana sona?‘’

‘’Waye zai haifi 'ya yace ba ya so Fadila?‘’
Ya fad'i haka kafin ya janyota ya rungumeta yaci gaba.
‘’Tsawon shekaru mukai muna buk'atar haihuwa ba mu samu ba sai a kanki, munyi farin ciki mun nuna godiya ga Ubangiji, tun kina ciki muke miki soyayyya har kika zo duniya soyayyar ta rikid'e ta koma zallar k'auna,munyi hakane ba don ba ma sonki ba sai don nuna soyayyarmu gareki, Faruoq rainanmu ne munsan bazai tab'a barinki ki wulak'anta ba ko da bayan ranmu, kuma idan ya san ba mune mahaifansa ba zai shiga damuwa damuwar kuma har ke za ta tab'a, babu wanda zai so ace ya tashi bai san asalinsa ba, abin da ciwo, wannan ciwon muke jiyewa Faruoq, kuma muna son muganku a cikin inuwq d'aya domin ko

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment