Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sha ba tare da ta sani ba.
A nitse ta gabatar da sallarta kafin ta shirya a gaggauce ta fito, cikin shigarsu ta laiyoyi da tai masifar yi mata kyau, yarintarta ta kuma fitowa fili, da ace ba a Dalhi bane anan gida nigeria ne to tabbas wani cewa zai kayan kawai ta saka ba lauya bace, duk da anan d'inma akwai wa'yanda suke mamakinta,tana cikin sakawa phart d'inta key Kate tai saurin k'arasowa tana gaisheta had'e da mik'o mata doguwar farar takarda.
‘’Mom ce tace na baki, ta huce Germany kuma ba yau za ta dawo ba, kuma sannan Driver yana zaune cikin sabuwar motar da aka kawo miki jiya yana jiranki.‘’
Kate ta gaya mata duk cikin yaren nasara.
‘’Ok‘’ Fanan tace bayan ta amshi takardar, ta bata key d'in phart d'in nata, ba sai tai mata bayani ba ita ta san me za tayi, daga haka
ta nufi gurin sabuwar motar dake d'aukar mata ido, fara k'al da ita sai shek'i take....













KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai.
Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal.
09037093702

CIKIN DUNIYARMU complet 500
KATANGA complet 500
CIN AMANA complet 300
#N.W.A
#Comment
#Share
[7/5, 8:09 AM] Rabi: BEBEARTH




CIN AMANA



Wattpad@Rashuna


4

Tun kan ta k'arasa jikin motar taji k'irjinta na bugawa da wani irin sauri sauri, wanda ba ta san dalilin jin hakan ba, kafin ta k'arasa aka bud'e mata k'ofar gidan baya, wanda alamu suka nuna kenan an hango tahowarta maimakon ta shiga gidan bayan sai ta bud'e gaba ta zauna, saboda ita hakan sam ba ya tsarinta, dalilin kenan da yasa ta zab'i irin drivern da take so, saboda duk yawancin drivern da Dad yake kawo mata k'azamai ne, idan ta zauna gidan gaba warin yai ta damunta, gasu kuma ba musulmai ba warin daud'a da warin kafirci sai ya had'u ya bada wani irin wari mai wahalar shak'a.
Kamar yadda ba ta kalli gefen da yake ba, haka zalika shima ko gefenta bai kalla ba ya fara k'ok'arin tayar da motar dama oh reddy Abraham ya bud'e musu k'atoton gate in gidan, tana k'ok'arin tace masa ya tsaya za taiwa Abraham magana taga ya ja ya tsaya a dai dai gurin da Abraham d'in ke tsaye sai a lokacin ta juya ta kalleshi, cike da mamakin ta ya akai yasan abinda ke ranta, akan tsagun fuskarsa idonta ya sauka, tsaki ta ja a ranta tana fad'in
‘’Sam wannan tsagun bai kamaci kamilalliyar fuska irin wannan ba, mtsss yana d'an k'auye ko me ya kawo shi Dalhi oho?‘’

(Chai masu karatu da alamu dai Dad baiyi tunani irin na Fanan ba, ko da yake da fa lauya muke tafe, tunaninta da ban yake, ku muje zuwa dai. )
Jin tsakinta a karo na biyu yasa shi waigowa ya kalleta, saukar idanuwansa cikin nata ya haifar mata da wata muguwar fad'uwar gaba, had'e da jin sauyin yanayi a jikinta, juyar da fuskarta tayi gefe had'e da danne k'irjinta da take jin bugawarsa sosai sai a lokacin taji Abraham yana gaisheta cikin yaren Indiyanci, numfashi ta d'an ja had'e da amsa mishi kafin ta koro masa tambayar da ke damunta, itama cikin yaren da yai amfani da shi.
‘’Abraham nikwa nace jiya waye ya dawo da ni cikin dare?‘’
‘’A gaskiya madam ba nace ba, don a jiyan ina toilet, fitowa nayi kawai naga motarki a parke, ni kaina abin ya mugun d'aure mun kai, ta yadda akai kika shigo cikin gidan bayan a rufe yake .‘’
Da hannu kawai tayi masa alamun yaje, ta riga ta saddak'ar aljanu ne kawai suka d'aukota daga ita har motarta suka kawota gida, kamar yarda suke mata a 'yan kwanakin nan su kawota k'ofar gida, sai gashi wannan har cikin gidan suka shiga da ita, cikin phart inta shima cikin bedroom inta aka kwantar da ita akan gado, inba aljanun ba waye ya isa ya shigo cikin gidansu wanda yake da mugun tsaro na kata'i.
Muryarsa ce mai taushi ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi.
‘’Ina mukai?‘’
‘’Nayi tunanin shima ka sani‘’
Wani kily smile ya saki me d'an sauti, ko kad'an ba tayi gigin juyawa ta kalleshi ba sai dai ta ji sautin murmushin nasa.
‘’Shima idan kika bani damar hakan zan kaiki, sai dai kawai ba na buk'atar zargi ya shiga tsakaninmu daga fara aikina a yau.‘’
‘’Mtssss ba na son doguwar magana, tana bani ciwon kai‘’
‘’Ni kuma ba na son tsaki‘’
‘’Ya kwa zamar maka dole ka koyi yadda ake sabo da shi, tunda har aiki za kai a k'ark'ashina domin shi d'abi'ata ne.‘’
Ta fad'i hakan a zafafe kafin kuma tace.
‘’Muje court in Shiva Raju, baice komai ba sai hanya da ya d'auka yana sakin b'oyayyen murmushi, kafin yace.
‘’Allah huci zuciyar shugabata, tun daga yau ma na fara koyon sabo da fitarsa daga bakinsa, ina kuma fatan hakan ya zamo mini hanyar da zan cireshi daga bakinki gaba d'aya, don ba d'abi'a ce me kyahu ba.‘’
Wani tsakin ta kuma ja wanda yafi dukkan wanda take sauti, kafin ta fara warware takaddar da Kate ta bata, don taga alamun in ta biyewa d'an k'auyen nan ciwon kai zai bata, kawai idan Dad ya dawo za ta sanar masa a canja mata shi.Ba komai takaddar ta k'unsa ba sai sanar mata da yake yayi tafiya zuwa American kuma zai d'auki tsawon kwanaki kafin ya dawo, zai iya kaiwa gab da bikinsu, ya nuna mata tsananin kewarta da zaiyi kafin ya dawo, don idan yayi tafiya ko waya ba sa yi har sai ya dawo, kuma ta kasa sanin dalilinsa har ila yau, har gara Mom suna waya amman sai dai Mom d'in ta kirata ita in ta kira ba za taje ba, kuma har yau ta kasa sanin dalilinsu na b'oyeta ainihin k'asar da zasu je, k'asa d'aya suke zuwa amman zasu gaya mata k'asa biyu mabambamta, wanda cikin biyu babu wacce suke zuwa, duk wata hanya da za ta bi ta san meyasa suke b'oye mata ta kasa sani, a hakan ma ba su san ta san ba ainihin inda suke zuwa suke gaya mata ba.
Jin tsayuwarsa yasata numfasawa kafin ta fara yunk'urin fita daga motar cikin sanyin jiki, wata matashiyar yarinya ce da ke tsaye a bakin court in ba ta wuce shrkaru goma sha uku ba ta rugo da gudu ta rungumeta tana kuka har da ajiyar zuciya.
‘’Yi hak'uri yi hak'uri‘’
Shine abinda Fanan d'in ke jajjera mata tana shafa bayanta alamun rarrashi kafin muryar yarinyar ya ratsa kunnenta.
‘’Naji tsoro sosai Aunty, har ina da kacen shigowarki cikin lamarin rayuwata, wallahi nayi tunanin wani abine ya same ki, wanda zaisa nak'i yafewa kaina har abada.‘’
‘’Babu abinda ya same ni Esha, gaya mini me ya faru?‘’
Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata kafin tace.
‘’Aunty an kori k'arar,kuma sun sanar mini wannan ce damata ta k'arshe tun da bani da lauya da shaidu an rufe case d'in gaba d'aya, yanzu haka ma shi mahaifinsa ya saka ya bar k'asar.‘’
Dafe kanta tayi had'e da ambaton. ‘’Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.‘’
Mahaifiyarta ce ke aiki anan court in, nan ne ya zame mata gida saboda rashin asali har ta haifi Esha wanda tun cikinta na k'arami mahaifinta ya rasu, anan court in Esha ta bud'i ido nan takewa kallon gidansu takewa kallon tushensu, tana da shekaru goma cif ciwo ya sark'e mahaifiyarta ta rasu, anan taci gaba da rayuwa ita kad'ai tana aikin da mahaifiyarta take, kasancewarta kyakkyawa ta ajin k'arshe, tun tana shekara sha uku komai na budurci ya gama bayyana a jikinta, hakanne yasa wani d'an me kud'i yai amfani da RASHIN GALIHUnta yayi mata fyad'e, kuma ya tsallaketa ya barta a bakin court in, ita ta d'auketa ta kaita asibiti, har sai da taji sauk'i ta bata labarin abinda ya faru, ita kuma tai mata alk'awarin k'watar mata 'Hak'k'inta, hakan yasa ta shigar da k'ararsa ga kotu, mahaifinsa kuma yai amfani da dukiyar da yake da ita, ya samu lauya tantiri da ya dinga d'ebo shaidun k'arya, yau itace damarsu ta k'arshe idan ba su kawo shaidu ba, hakan yasata jajircewa sai da ta had'o dukkan wata shaida, sai gashi ta b'ata damar da hannunta, ta karya alk'awarin da ta d'aukar mata, wannan shine karo na ba adadi da giya ke sanyawa ta fadi a case amman ba ta tab'a jin rad'ad'i da b'acin rai irin na yau ba, har ta ji giyar ma ta fita daga kanta sam, saboda case d'in a jiyan ta k'wauracewa shan giyar amman sai da Sameer yayi sanadiyar da ta sha, meyasa meyasa yai mata haka?
Wani zugi da tiriri take ji a zuciyarta, ga kuma tausayin Easha da ya dabaibayeta, muryar Br Aditya ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi.
‘’Dama na gaya miki bazan tab'a saken da za ki samu nasara a kaina ba, haka zalika wannan da zamu zauna yanzu ma mafi aala kawai ki juya gida.‘’
Yakai k'arshen maganar yana wata shegiyar dariya, wani shegen murmushi Fanan ta saki tana me kallon Easha tace.
‘’Ki kuma bani dama na inganta rayuwarki, wanda nake fatan hakan ya rage zugin abinda ke ranki za ki bini?‘’
‘’Zan biki Aunty‘’
‘’Yauwa shiga mota ki jirani.‘’
Kafin ta waiwaya tai masa kallon sama da k'asa taja tsaki ta nufi cikin kotun yabi bayanta yana sakin murmushin mugunta.

Sun fafata sosai kafin Allah ya bata nasarar k'watowa bayin Allah marayu hak'k'insu da k'anin majaifinsu ke shirin danne musu, tare da mahaifiyarsu suka rungumeta suna godiya saboda ko sisinsu ba ta karb'a ba domin Allah ta tsaya musu har suka samu nasara, cike da takaici da muguwar tsana Br Aditya ke kallonta yana k'issima a ransa sai yaga bayanta...










KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai.
Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira500kacal.
09037093702

CIKIN DUNIYARMU 500
KATANGA 500
CIN AMANA 300

#N.W.A
#Comment
#Share
[7/6, 9:39 PM] Rabi: BEBEARTH

https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v
[11:51PM, 11/24/2021]
Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata.


CIN AMANA



Wattpad@Rashuna



5

A gajiye ya k'arasa masaukinsa, kasancewar yau yasha yawo da Fanan gurare da dama akan wata shari'a da zasu gabatar nan da sati biyu, kayan jikinsa ya soma cirewa kafin ya fad'a toilet, jikin mirro naga ya tsaya yana d'ayo wani abu daga fuskarsa, abin mamaki sai naga tsagun fuskarsa yake d'ayewa, kenan babu tsagu a fuskarsa?(To dai babu me bamu wannan amsar masu karatu muci gaba dai da bin littafin.)
Yana d'ayewa yana sakin murmushin diramarsu da Fanan, ya rasa me yasa idan yana tare da yarinyar yake matuk'ar jin nishad'i a zuciyarsa.
‘’Astagfirillah‘’ Ya furta kamar wanda ya aikata sab'o yana me saurin kawar da tunaninta daga zuciyarsa, ruwan wanka ya had'a ya shige ciki yana me lumshe idonsa, ya d'an jima sosai a ciki kafin yayo wankan ya fito ya shirya cikin kayan bacci farare k'al da su ya kwanta kan lallausan gadonsa yana mai jin nutsuwa a zuciyarsa, rubf da ciki yayi ya janyo laptop insa ya soma aiki a ciki, kafin wayar dake gefensa ta fara ruri tana neman agaji, sai da ya fara gyara zamansa sosai kana ya d'aga wayar yana bada dukkan hankalinsa a kai, bana jin me suke fad'e kawai dai naji yana ambaton ‘'Yes SIR’' Da dukkan alamu da ogansa yake magana, suna kammala wayar wani kiran ya shigo amman naga vidio call ne shi, murmushi ya saki kafin ya gyara kwanciyarsa zuwa rigingine ya d'aga wayar, a tare suka ajiye wata wawiyar ajiyar zuciya ·
Dak'una fuska tayi tana marairaice idanuwanta cikin nasa kafin tace ·
‘’Tsakaninka da Allah yau sau nawa ka tunani?‘’
‘’Woo ho Fadilaa, meyasa kike son k'ureni ne, kinsan ban iya k'arya ba, kuma in na gaya miki kizo kina jin ba dad'i kuma kinsan duk duniya ina kokawa da wanda zai sanyaki bak'in ciki, burina ko da yaushe farin ciki ya dauwama a rayuwarki·‘’

‘’ Ni kaine kawai farin cikina, burina kaso ni ni kad'ai ka kula dani, ka riritani, komai kakeyi ya zamto tunanina yana mak'ale da kai, amman kayi hak'uri in na b'ata maka rai·‘’
‘’ A'a baki b'atan rai ba, kawai dai kinsan bana son kidinga min irin tambayoyin nan, sanin kanki ne ban iya k'arya ba na gaya miki abinda ke raina na sosa ranki ni kuma bana son hakan, kinsan ina matuk'ar k'ok'ari gurin baki dukkan soyayyata‘’

‘’ Na sani sosai, nima soyayyarka ce take sanya ni yin komai, fatana da burina bai wuce na kasance ni kad'ai a cikin zuciyarka ba da duniyarka gaba d'aya, bazan tab'a iya tarayya da wata ba akanka, ka rik'e mini wannan alk'awarin·‘’
‘’Bazan gaji da gaya miki ban miki alk'awari ba, saboda ba nine da ikon juya zuciyata ba, amman zan iya danne dukkan abinda nake ji matuk'ar hakan zai sanyaki farin ciki, saboda ban damu da rayuwata ba, rayuwarki kawai na sanya a gaba, sunyi bacci ne?‘’

‘’Uhmmm, ina jin Aseep ne kawai bai yi ba, suna d'akin Abba·‘’
‘’Ok, da safe ma gaisa ki shafan kawunansu‘
’’
‘’Insha Allah‘’
‘’To meye labari?‘’
‘’Labarina yaushe zaka dawo?‘’
‘’bazan ce ga rana ba, saboda bansan tsawon kwanakin da aikin zai d'aukemu ba, amman in na samu lokaci zanzo,na ganku ko a ranar ne na juyo·‘’
‘’Tom shikenan, amman nayi kewarka sosai·‘’
‘’Dan Allah da gaske kike? kalli cikin idona ki gaya mini‘’
Dariya tayi tana saka hannuwanta ta rufe fuskarta alamun taji kunya·
‘’Ashe to ba kewar tawa kikayi ba kenan’’
‘’Allah nayi kewarka sosai da sosai, nai maka tanadi sosai‘’
‘’Wayyo dad'i, nesa ba ta maganin kusa, amman za ki ganni soon insha Allah·‘’
‘’To Allah yasa‘’
‘'Amin‘’


Bayan kammala wayar tasu sosai Fadila ta zurfafa cikin tunani, tana mugun tsoron shigowar wata rayuwarsu hakan yasa take kaffa kaffa da masoyinta, Allah ya yita mace me mugun kishi, kuma bata da lafiyar zuciya, amman hakan bazai hana idan yaga wata yana so ba Abba ya shige masa gaba, duk da ta san da wuya Faruoq ya yadda ya aikata hakan a gareta kasancewarta me k'arancin lafiya, da kuma girma da kimar mahaifanta da yake gani, wanda har kwanan gobe tasan ba ta cikin zuciyar Faruoq illa soyayyar da yakewa mahaifanta da kuma soyayyar da yake mata ta yaya da k'anwarsa duk kwa k'ok'arinsa da yake na ganin ya cusa soyayyarta har ya bata k'arfin guiwar yarda da hakan·
Hashim Abdussalam shi kad'ai mahaifiyarsa ta haifa tun bai fi shekara goma ba mahaifinsa ya rasu, bayan fitar mahaifiyarsa daga takaba ta tattara abinda ya bari ta nufi saudiya ta bar Hashim a hannun k'anin mahaifinsa wanda itama wane a gurinta sabili da auren zumunci sukayi·
Ya rayu cikin gidan kanin mahaifinsa rayuwa me inganci ya taso da sana'a irin tasa wato sana'ar Kanikanci (Bakanike) har gyaran manyan motoci yake yi kuma suna kawo masa kud'i sosai har yaso yafi k'anin mahaifin nasa kud'i me amsa sunan mahaifin nasa a yanzu kuma surukinsa, don da 'yar wajensa Ruqayya suke soyayya har an saka musu rana jira ake,ya k'arasa gininsa asha biki, har zuwa wa
nnan lokacin mahaifiyarshi ba ta zo ba sai dai waya da sukeyi in ya kirata·
Alhmdlilllah ansha biki lafiya bayan kammala ginin nasa, amarya ta tare cikin kwanciyar hankali, zamansu suke lafiya lau babu tashin hankali, tafiya takai tafiya kusan shekaru bakwai babu haihuwa ba labarinta, gashi dukkaninsu Allah yayi su da mugun son yara kamar me, amman haka suka hak'ura suka mik'awa Allah lamuransa suna kai kukansu, duk da Rukayya taso ya k'ara aure yaki sam sabida baya cikin k'addararsa·
Ana cikin haka kira ya samesu daga asibiti, mahaifinsu ne tsautsayi ya samesa ,shigar bulet ne a cinyarsa da kafad'arsa kuma sun raunata shi sosai, gefensa wani beautyn yarone yana ta tsanyara ihu, yaron ya d'auka ya bawa Ruqayya yace·
‘’Gashinan amanata ne, idan kuka cuce shi ban yafe muku ba duniya da lahira , ku kirashi da sunana Umar Faruoq·‘’
Iya abinda ya iya fad'a musu kenan ya amsa kiran mahaliccinsa ba tare da sun amayar da tambayoyin da ke cunkushe fal a zuciyoyinsu ba·

Mutuwarsa ta rikirkitasu tazo musu da sabon yanayi wanda basu tab'a zatonsa ba, sunyi kuka kuka na sabo da soyayya da kuma kewa gashi kuma ya tafi ya barsu da amana, amanar da ta kusa jefa rayuwarsu gaba d'aya a halaka har sai da ta kai suka bi dare sukaiwa garinsu mahaifarsu 'yan uwansu danginsu, b'atan dabo, babu wanda yasan inda suke bare yaji labarinsu, mahaifiyarta basu fi shekara biyu da aure ba ta rasu, dama su biyu ta haifa ita da qanwarta da take bi mata kuma rana daya akai bikinsu ita Abuja aka kaita, sai waya sukayi ta sanar mata sun bar kano····











KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai.
Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan littafi mai suna KATANGA zai zamo bakandamiya da zarar ya ratsa duniyar marubuta, akwai abin amfani a ciki, yi k'ok'ari ka mallaki naka kar ka tsaya jiran na aro, domin kwa akwai hanyar da zamu bi mu gyara zaman auranmu a gidajenmu cikin tarbiya da koyarwar islama, ba nan kad'ai ya tsaya ba akwai hanyar da mace za ta tsaftace jikinta cikin koyarwar islama ba tare da ta sanya abinda zai cuceta ba, akwai d'umbin abin amfani a ciki mudai had'e a cikin KATANGA an jima ba'ayi kamarsa ba maza neme shi akan farashi mai sauk'i naira 500 kacal.
09037093702


#N.W.A
#Comment
#Share
[7/7, 3:50 PM] Rabi: BEBEARTH

https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v
[11:51PM, 11/24/2021]
Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata.


CIN AMANA



Wattpad@Rashuna


6

Kaduna,anan suka dasa sabuwar rayuwa, bayan ya nema musu hayar d'aki d'aya a wani kwarab'ab'b'an gida.
Cikin Hashim da Ruqayya bazan iya tantance muku wanda yafi son Faruoq ba dukkaninsu sunai masa soyayya irin ta d'a da mahaifi, dukkan wani buri nasu suka d'auka suka azashi a kanshi,bazai wuce shekara d'aya da rabi ba, amman akwai shi da matuk'ar wayo ga farin jini, yana takawa da k'afafunsa magana ce dai sai gwaranci ba a jin me yake fada, sunsha matukar wuya kafin su samu ya saki jiki da su, don rigima sosai ya dingai musu.
Abinci Ruqayya take siyarwa, saboda a lokacin Hashim bai samu garejin da zai dinga aiki ba, da wannan sana'ar tata suke samu su rufawa juna asiri, har Allah yasa ya samu wani gareji yake zuwa aiki can, cikin ikon Ubangiji sai ya fara samun alkhairi sosai har ya kama musu gida su kad'ai don Faruoq yafi sakewa sosai, duk da su yanzu ya sake da su sosai har bakinsa ya d'an fara bud'ewa Ruqayya yana kiranta da Oummi, wanda itace take koya masa idan yace Umma sai ta gyara masa tace ‘’Oummi‘’A haka har ya saba, Hashim kuma Abba daman da hakan ya bud'i baki.
Soyayya da k'aunar da sukewa Farouq ta saka sam sun manta da ba sune suka haifeshi ba, don tuni sun dad'e da barin hakan sirri a tsakaninsu, sunyi alqawarin baza su tab'a bari yasan ba sune ainihin mahaifansa ba yanda suke jinsa a ransa suke ganin ko da mahaifansa na,ainihi sun bayyana baza su iya basu shi ba mutuwa kad'ai suka aminta za ta iya yi musu KATANGA a tsakani.
Faruoq ya tashi da soyayyar Oummi da Abbansa, shima komai Oummi Abba kamar yadda suma komai Faruoq, duk wani samunsu a hidimta masa suke tafiya a haka har ya isa sakawa a makaranta, suka samu makaranta me kyau suka sanya shi Alhmdlillh kuma ya tashi da kwanya sosai.
A haka rayuwa tayi ta gangarawa tana tafiya a hankula har Faruoq ya zama saurayi ya kammala makarantarsa ta secondary, ya kuma zab'i aikin police, Abba ne ya tsaya mishi da wannan aikin nasa na kanikanci har ya shiga makarantar 'yan sanda a lokacin ne kuma Oummi take ta fama da tsohon cikinta sunyi murna sosai lokacin da suka san da zaman cikin, Faruoq ma sai murna yake zaiyi qanwa, yaso sai da Oummi ta haihu kafin ya tafi makaranta amman har ya tafi Allah bai kawo hahuwar ba sai tafiyarsa da kwana biyu ta tashi da nak'uda, abinka da jikin girma kuma tayi doguwar nak'uda sosai sai da ta kwan biyu a asibiti ana shirin mata cs Allah ya kawo haihuwar ta haifi 'yarta mace, sunyi murna sosai har da 'yar uwarta Habiba, da tun fara nak'udarta tace a kira mata ita don tana ji a jikinta kamar baza ta tashi ba duk da itama Habiban ciki gareta na wata bakwai da yake haihuwa take tayi basa zuwa da rai, kusan shekararta biyar ba ta kuma samun ciki ba sai yanzu kuma sun qwallafa rai a kansa daga ita har mijin nata.
Ana mayar da ita d'akin hutu ta fara wani azababban ciwon ciki tuni ta sanya aka kira mata Abba ta fara neman yafiyarsa, shi kuma yana bata baki akan ta daina fad'in haka insha Allah zai dainai mata ba mutuwa zatai ba, girgiza masa kai ta shiga yi cikin raunin murya tace.
‘’Ina ji a jikina bazan tashi ba, ka kira mini Habiba.‘’
‘’Kar ki d'aga mata hankali kinsan ciki gareta itama.‘’
‘’Na sani ka kira mini ita dan Allah.‘’
Tana rufe bakinta sai ga Habiban ta shigo kamar ta sani, murmushi ta saki tana mayar da kallonta kan Habiban kafin tace.
‘’Kiyi hak'uri zan barki da marayu don ina jin da k'yar zan tashi, ga amanar Faruoq nan da k'anwarsa, ina son bayan kin haihu kici gaba da shayar da ita na baki ita halak malak, ina

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment