Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tareda yan tsarabarshi, se sun sha fira sannan yakoma, joda tafara Jin sauqi,

khalthum kuwa kullum tana hanyar asibity duba joda, ta tsinewa Ahmed yafi aqirga, joda tace kenifa na barshi da allah kifita harkanshi kawai, khalthum tace wlh joda da ace nice ke to wlh kuwa kodan uban waye bai isaba yatakani shi har ya isa ba soja ba bura'uba, joda ta rufe mata baki kae khalthum kiyi hakuri Dan allah kiyi shiru banasan irin wannnan zage2

Doctor ya ajiye biro dinsa yabi khalthum da ido to itakuma wannan wacece? Tambayar dayayiwa kansa kenan wadda ba'a amsa, yana saurarensu duk firar dasuke, sedai bai tanka ba amma yafahimci wannan khalthum din akwai zafi dukda joda ma nada nata zafin, shakuwa mai tsanani tashiga tsakaninsu da doctor dinta, sedai tana cike da kewar abdallah , ana haka Sega shi murna gun joda ba'a magana,

Seda tagama yimasa shagwaba sannan suka sha yabata hakuri kan dadewar da yayi, yana fita gwaggo tace joda wai ni miye tsakanin ki da wannan yaron ne? Joda tace bkomai gwaggo cewa yake ni kanwarshi ce gwaggo tace to wlh kiyi hankali dashi nidae wlh dama kin yanke wannan alakar atsakaninku, joda ta juye baki a ranta tace kuji gwaggo fah Dan baki san miye so bane shi isa kike cewa na rabu dashi

Gwaggo tace mekika ce? Joda tafara a'a in in dama cewa nayi, gwaggo tace dallah yimun shiru shasha yarinya ana nuna miki gsky kina kaucewa, joda tasadda kanta kasa tace Dan allah kiyi hakuri gwaggo, gwaggo tace bkomai ina kara jadda da miki bana San tarayyarki dashi karshen mgn kenan, joda tace gwaggo Dan allah kibani lokaci yadda zan koyawa zuciyata rabuwa dashi bazan iya farat daya ba, wlh tausayin shi nakeji har kuka yake mun , gwaggo tace oh yaro man kaxa

Ahmed zaune kan gadonsa yana latse2 awayanshi, Mahmud yashigo yazauna, Ahmed yace daga ina haka, Mahmud yace daga gurin joda nake har tafara Jin sauki, doct din yasan aykin shi wlh, ni naso na ganshi na masa godiya, Ahmed yatabe baki yacigaba da aykinsa, Mahmud yace kozaka je ka dubata, Ahmed yagalla masa harara yace inje inyi uwarme acan? Mahmud yace uwarka xakayi acan da iskanci Dan kawai kaje dubata shine wani abun bayan koba komai akwai lada aciki

Ahmed yace ni kake zagin uwata akan wata banza , Mahmud yace yihakuri banji dadin zancen kabane shi isa, Ahmed yasadda kae yacije lebe yacigaba da aykinsa, wayarshi ce tadau ruri uban tsaki yabuga ganin wake masa waya , daga ganin yanayin shi Mahmud yagane ko waye kemasa waya, Mahmud yace da kayi hakuri dae kadaga wayar ka Mai sonka yafi makiyinka, Ahmed yace agareka hakan yake ni agurina gwara makiyi akan masoyi .......

Muje zuwa 🎄
ASEEYAH BASHEER ALEEYU 💕

🎄 FULANIN DAJI 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄
🎄 🎄
🎄
N@ B aleeyu 💕 page 4⃣8⃣
Mansura nagani anci ado tamkar wata amarya se kwarkwasa take tana juya duwawuna, dakin Ahmed tanufa ba fargaba ko darr azuciyarta, knocking tayi nayi kusan minti biyar shiru ba'a bata izinin shigaba, hakan yabata damar murda key din dakin tareda sallama, Ahmed na zaune kan kujera yana kallo a system dinshi baida go ba , ya amsa sallamar tsaye tayi tana jiran dagowarshi, can da taga tsayin bamai karewa bane tace barka da hutuwa ranka yadade, banza yamata yacigaba da harkokinsa

Ahankali tasake cewa Ahmed ya hutuwa, nanma shirun ne yabiyo baya , mansura kam tadan tsargu , tasake cewa Ahmed mgn fah nake maka amma kamyimun shiru , Ahmed yadago afusace yace waeke mayyar ina ce, mekikazo yi a dakina na nemiki ne kokuma ya? Mansura tajuya masa baya gudu kar yaga hawayenta, tace hava Ahmed kaso mai sonka koda kashi ne, bare mutun,

Ahmed yace ay kashin ma yafiki daraja agurina, da zanga kashin da kuwa zakiga yadda zan daukaka darajar shi sama da taki wawiyar banza jahila kawai get out yanuna mata kofa, bamu su mansura tafita amma me? Tana kae kofa tatsaya batareda tajuyo ba tace wlh Ahmed ina mai shaida maka cewa sena aure ka kota halin kaka, ka soni koka kini bashine damu wataba burina naganni a gidanka amatsayin mallakinka

Ahmed yace shege kafasa idan kika cigaba da cusa kanki a rayuwa ta to wlh zakiyi Dana sani na har a bada , mansura tace ok toh shikenan Muje zuwa nida kae, kasani bazan kara kawo kaina agareka ba, dakanka zakaje neman aurena, kasaka wannan a ranka!!! Ahmed yayi murmushin mugunta yace duka bokayen duniya da malamanku basu isa suja daniba, ki koma kigayawa bokanku yayi kuskure da yayi tunanin zai iya galaba akaina, malaminki yaudaran ki yake ba abunda zai iya yimun, mansura tayi shiru Jin kalaman sa kana tafice daga dakin

Dakin hjy taje tafada kan gado, hjy na sallah ta Idar tace lfy mansura kika fada kan gado dakarfi haka ? Mansura tace inafa lfy anty kinji yadda Ahmed yace, nan ta zayyane mata yadda sukayi dashi, hjy tace indan wann karma ranki yasosu ina baki tabbacin Ahmed naki ne har kin samesa, mansura tace allah ko antyna, hjy tace sosea ma dubi nan, wani Dan karamun kwalba ne da turare aciki, hjy tace yana Jin kamshin wann shikenan angama dashi

Mansura tadaka tsalle wayyo dadi kasheni , hjy tace ungo kiyi hankali dashi dashi bakaramun kudi nazuba aka bani shiba har Niger aka karbo mun shi, mansura tace to ya ake amfani dashi? Hjy tace ajikinki zaki sakashi kisamesa, seki gayamasa cewa yaushe zae turo ayi mgn, mansura tace kae anty wlh ina Jin tsoro kinga yadda ya wulakanta ni yau

Hjy tace hakuri zakiyi tinda kekike nema ba'a gaggawa, idan kika bi komai ahankali zamuyi nasara, mansura tace to yanxu yaushe zan saka hjy tace bayanzuba se bayan kwana biyu, ni bani turaren kar kije garin rawar kan tsiya kifashe shi , mansura tace wae anty ina amina tin danazo bangantaba yanxu har 10:30 ace bata dawo ba, hjy tace ay wlh bataji ne nayi2 ta dena yin dare se ayita zagina agari bataji ne yanxun idan Ahmed zai fara yiwa mutane iskanci....shiru tayi Jin ihun amina gabadansu suka fito aguje

Ahmed suka tarar yana dukanta yana ball da ita hjy tasaka salati na shiga uku Ahmed kashe ta zakayi, Seda yamata lis sannan yace Al qur'an idan nakara ganin ki kinfita da irin wann shigar ta yayan arna wlh sena kakkaryaki bare kuma har kiyi dare haka tukun na ma gidan ubanwa kika fito?

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B aleeyu 💕 page 5⃣0⃣
Cikin muryar kuka tace gurin bithday din saurayina Ahmed yakara hankata saurayi koh, to wlh kishiga taitayinki idan nakara ganinki kinfita koda get ne batareda izinina ba wlh se jikin ki yagaya miki
Kuma kisani kitattara kayan ki ki koma islamiyya on Sunday, hjy tace kae ya isa haka sekace wani ubanta zaka wani gindaya mata sharudda haka, Ahmed yace inada ikon yin hakan ne kuma babu ubanda ya isa yajanye wann tsarin, hjy tace koda uwarta ne, Ahmed yajuyo afusace yace koda ubanta ne!

Dae2 nan abba yashigo yace tabbas ko ubanta bai isa yajanye wann dokar ba bare kuma uwarta, hjy tabuga tsaki taja amina sukayi sama Ahmed yamaida kallansa ga abba yace abba barka dazuwa, abba ya amsa da lfy lau Ahmed yagajiya, Ahmed yace ba gajiya, abba yace Ahmed kayimun dae2 kacigaba da hukunta kannenka wann shi zai tabbatar mana dacewa koda mun mutu mun bar baya muna da wanda zai tarbiyan tarda yayanmu, Ahmed baice ,komai va yashiga maida belt dinshi daya Zare

Joda kam jiki Alhamdulillah tafara warwarewa, har wata kiba naga tayi yan kasusuwan jikinta duk sun bace, tayi cif cif da ita, yau satinsu biyu kenan, idan anyi lesson a skull khalthum tana tashi seta biya gurin joda tamata bayani sannan ta wuce gida, abdallah kuwa kullum yana kan hanya shida Mahmud narasa wayafi bata kulawa acikin mutun uku doctor ko abdallah kokuma Mahmud dukda khalthum ma ba'a barta abaya ba

Abdallah yakalli joda yace bae yaushe zaki koma gida? Joda tace nima bansaniba ask doct, abdallah yace okey ana haka Sega doct ya shigo, abdallah yabasa hannu suka gaisa, Yace doct yaushe za'a bata sallama ne, doct yace itace tace maka tana bukatar sallama? Abdallah yace no, doct yace gud taji sauqi ne har tana iya komai sa hannun koh? Abdallah yace no hava gashi kana gani , doct yace to me kake bukata da abata sallama tinda ba kula zakuyi da ita agidaba kamar yadda yakamata

Abdallah yace shikenan allah yabaki lfy kanwata ameen , joda tace doct mura kakeyi ne, doct yadaga mata kae yacigaba da rubuce2 joda ta tabe baki bansan meyasa yake bata ranshi ba idan yaga abdallah agurina , sedai kayi ni bamai rabani dashi shine hasken idaniyata abdallah yace bae zanwuce sekuma night, joda tace tom amma Dan allah karkayi dare sosea kamar yanda kakeyi, abdallah yace kinsan fah inada abubuwa agaba nane matse wa nake ina lekowa gurinki,

joda tace nadae gayama idan nayi bacci karka kuskura katadani, abdallah yayi murmushi to ranki yadade , yana fita doct yarufo kofar dakarfi har Seda joda ta tsorata, tace lfy doct? Ba lfy ba shine amsar daya bat! Joda 😳 meyafaru? Kace mura kake kuma gashi muryanka ayanxu qlw, doc yace yess , ba lfy ba, banason ganinki da wann yaron zai bata miki tarbiya yaron dake shaye2 , joda tace ya isa haka bakada wann hurumin na shiga tsakanina dashi koma dae meyake sha ina sonsa ahaka kuma babu wanda ya isa ya rabani dashi , doct yadaka mata tsawa dacewa how dare you ni zaki gayawa mgn tuni joda tashiga taitayinta

Doct yace b carefull you do not know me , joda ta kankame jiki tafara kuka abunda yatsana kenan kukunta glass dinshi yasaka yabar mata dakin , yana fita tafara tunanin anya kuwa ta kyauta hakan datayi, yinin ranar baidawo ba baixo bata lunch ba bare na dare haka tawuni da yunwa , damuwa fal aranta duk wanda yaxo dubata haka zai hakura yakoma anrasa kanta ,Mahmud da abdallah atare suka zo tana Jin shigowarsu ta lafe kamar mai Jin bacci...........

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B aleeyu 💕 page 5⃣1⃣
Ahmed yafito daga room dinshi zai shiga kitchen yahada coffee , mansura kuwa dama tana labe kawai segata aguje dae2 nan Ahmed yafito suka hadu da juna dasauri Ahmed yaja dabaya yana kokarin rufe hancinsa 🙊 Jin wani kamshi tareda wani yanayi yana shiganshi, ganin haka yasa mansura yin sauri takarasa kusansa ta ware hannayensa Ahmed yashiga juye2 da kanshi yarasa inda yake masa, dadi kasa yadinga yi har yakai kan carpet yazauna

Mansura tace yade Ahmed, ahankali yadago idonsa dasuka kada sukayi jajir yace bakomai ina son na kwanta, mansura tajanyo hannunsa sukayi room dinshi, kan gado ta ajiye shi , ido kawai yake binta dashi, mansura tace mekake bukata ne, Ahmed yace bacci nakeson yi , mansura tace bismillah , kwantawa yayi tareda wasu tinanin wadanda yakasa gane kansu, mansura tadaka tsalle tayi dakin hjy da gudu tafada kanta I love you my cwet anty wlh yakamu, anty kinga kuwa yanda yake kallona, hjy tace dakyau seki fara aykinki bawasa

Karfe 2 dae2 Ahmed yafarka tareda rike kanshi dayakejin yana juyawa , yana son tuna abunda yafaru amma yakasa , wanka yayi yashirya cikin kananan kaya , yana kokarin fita wayarshi tadau ruri, new number ce saboda haka baidaga ba Seda tayi kusan 3 miss call sannan yadaga tareda fadan yess, Jin muryar mansura yasa shi Jan tsaki tareda fadan ya ake ciki? Mansura tace inaso karakani shopping ne, Ahmed yace kinga na miki kama da mai rakiyar mace

Mansura tace shikenan tinda baka sona, Ahmed no kigane banda gud tym ne amma zan baki driver, mansura tace ni idan baxaka kai niba kabarshi kawai kafi driver agurina, Ahmed calm down mana zaki iya barin firar har zuwa night yanxun inada abun yi ne, mansura tace allah yakaimu, my man I love you.....Ahmed yace uhm.....Thanks mansura tace au baxaka cemun you love me ba, Ahmed yace ay base nafada ba fadanshi bashi yake tabbatar dashiba, mansura tace dukda haka nidae nidae inason Jin wann kalma daga bakinka , Ahmed yace sena dawo I'm busy ya tsinke wayar yafita

Mansura tace ay day tinda baxaka iya cewa baka sona ba komai yayi nakusa kammalawa da matsalar ka, Ahmed kuwa yana Jan mota yana mamakin kanshi shi kam yarasa meke damunsa akan mansura yana Jin wani feeling akanta yarasa ko miye , yafe yake yana shan wakar ice prince. Waya yake da hafsa cike da kulawa yanata tambayar yakaratu ba abunda kike bukata hafsa tace bakomai bruhh , sedai ina neman wata alfarma guda daya Ahmed yace yes go on " hafsa tace bruhh plss ina son mgn da joda, Ahmed yace hafsa zaki fara koh? hafsa tace sowie bruhh, Ahmed yace dont lemme warn u again , hafsa tace bruhh.....shhhh yafada bana San Jin komai dole tayi shiru tareda Jin wayar ma ta tsaneta duka

Joda kwance abun duniya duk ya isheta tin ranar bata kara saka doct a idonta ba sedai yaturo wata likita tadubata idan joda ta tadubata ya doct baya xua se tace mata yana busy ne, gashi ankusa bata sallama tinda hannun yayi kyau yanxu tafara motsa shi da kanta yau sunada text skull saboda haka tin wuri tashirya driver yaxo yakaita a skull se xua dubata ake ana mata sannu karfe 12 dae2 suka fito exam principal yatava izinin komawa gida ganin yanda take

Dama kuwa driver na jiranta tana fitowa suka sa kae se asibity dae2 kofar shiga asibity tahadu da Ahmed Yana fitowa dumm taji gabanta yafadi dasauri take ja dabaya baya, Ahmed kuwa yatsuramata ido yana kallan shigarta acikin uniform, ido yazare 😳 naga ya yada key din motar shi ya na fadan jodaaaaaa❕ wani rin tsalle naga yayi yacab kota suka fada gefen titi , mai motar yafito da niyyar basu hakuri sekuma yayi turus ganin irin kallon da Ahmed kebin joda dashi ita kuma idonta arufe..........

Muje zuwa 🎄
ASEEYAH BASHEER ALEEYU 💕

🎄 FULANIN DAJI 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄
🎄 🎄
🎄
N@ B aleeyu 💕 page 5⃣2⃣
Joda ta turasa da karfi da koma gefe tana maida nunfashi , Ahmed yamaida kallansa ga mai motar yace kae mahaukacin inane kana ganin ta tana yowa baya da baya baka iya yi mata horn ne? Mutumin yace to ay laifin ta ita batasan kan hanya take ba , Ahmed yace bazaka gane laifin ta bane Seda ace ka maketa wlh daka san katakarowa kanka bala'i,

mai motar yace yi hakuri ranka yadade, amma dae kanason matar nan taka dayawa, Ahmed yace what? 😡 ubanwa yagaya maka cewa matata ce, Mutumin yace am sorry irin yadda ka tsorata ne da kuma yanda naga kana kallanta yayi kama da yanayin so mai babban Al amari aciki , Ahmed yace bansan raini kagan namaka kama da banza ye ne, wann kanwata ce yanuna ta batareda yakalletaba Mutumin yace ayya gsky kana son kanwar nan taka dayawa, shi isa kuke matukar kama big eyes dinnan naku iri daya da sexy lips dinn , Ahmed yadaka masa tsawa, tuni yashiga motar shi yabar wajen ganin yanayin Ahmed

Tin randa Ahmed yafurta cewa kanwarshi ce takasa daena kallanshi se mamaki take yau itace Ahmed ya kecewa kanwarshi ce, murmushi naga tayi wann shine nabiyu ko menene oho" Ahmed yadauko jakarshi ko kallan inda take baiyiba yanufi motar shi Kamar ance yajuyo, yagan tabishi da ido wata harara yaballa mata tuni tajuya da sauri, ashe akwae ruwa agurin jinta kakeyi tisss tafada aciki kuka tafashe dashi wayyo gwaggo hannuna wayyo hannuna Ahmed yayi Jim kadan sann yafito yaganta se hawaye take, tsaki yabuga yace zakumin shiru kosaena kara karye miki hannun

Joda ta dukadda kanta se sheshsheka take wayarshi yaciro yakira wata nurse cikin kankanin lokaci Sega su su uku yace ku kaita sama a dubata yana kai nan yafice yayi gurin motar shi " joda kam se kuka take har suka isa da ita sama, cikin muryar kuka tace Dan allah kukiramun likita nah, dayan nurse tace karki damu yanxun zaizo zanmasa waya, joda tacigaba da kuka sunata bata hakuri, kwance daurin sukayi sann suka duba, dayar tace anisa dubamun ay kamar taji sauki,

Wani doct ya izo mata yace bashida lokacin zua, shi yaduba daurin yace base ansake wani ba taji sauki sedai kawai Dan wann faduwar datayi ne amma zua 5dyz za'a bata sallama, joda taji dadin Jin hakan Dan kuwa ta qagu da zaman asibityn, baccinta tayi na kusan awoyi biyu se kusan la'asar tafarka sann taje tayi kowace sallah takoma kwance tana tunanin irin yadda doct yadau abu dazafi haka, abunci aka zuba mata amma bawani cin kirki tayi masa ba sama2 taci takoma kan gado

Abdallah yashigo rike da Yar ledarshi, yanata fa man yiwa joda murmushi joda kuwa ta kawadda kanta gefe, Yace kanwata nayi laifi ne? Joda tace a'a kawai banajin dadi ne, abdallah yace meyake damunki, joda tace bakomai kawai dae bana Jin dae2 ne, abdallah yace ayya bae konakira doct ne adubaki, joda tace a'a bana bukatar hakan bacci zanyi, dayaga dae dole bata san firar ya ajiyemata ice cream dinta yayi mata saeda safe

Mansura tareda amina suna saukowa downstairs, dae2 nan dad yafito room dinshi aikuwa yayi kamar baigansuba, amina tace dad barka da fitowa yaamsa da yauwa, mansura ma tagaidashi yakarba bayabo ba fallasa, mansura tace jeki kiramin Ahmed amina tace what? Ahmed fah sokike ya bibbigeni a banza wlh baxan jeba yaushe ma kikayi wann matsayin keda ko Kin samesa a dakinsa wulakanta ki yake bare kuma ya amsa kiranki ay seki saka ya sanbadeni wlh yanxun zaifito ya shuka miki rashin kunya

Mansura tace dakata kiga, wayar ta taciro tasaka kira Seda tayi ring yakai biyar sann yadaga, amina tace ahto, dama dae kin hakura da wann miskilin dayafi, mansura tace hava babyna yabaka daukan waya, Ahmed yabuga Dan tsaki sann yace ina toilet ne, mansura tace ok kasameni a dining akwai maganar da zamuyi, Ahmed yace bacci nakeji sedai kayi bari har natashi gobe kenan understand? Mansura tace hava kae wae goma mutun yake da bukatar ganawa dakae seka kawo masa naka uzurin na daban idan baxaka zo yanxuba abar zancen kawai............

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B aleeyu 💕 page 5⃣3⃣
Ahmed yadaga kafada yace alright , amina tabushe da dariya tace mena ga yamiki anty wlh ko dad baya masa wann ikon kince dole se yanxu, ay wann dolen dakika ce shizai ha nashi xuwa koda kuwa yayi niyyar xuwan, mansura tace ke wlh zanci ubanki kikama mun bakinki Yar iskar yarinya....shiru tayi Jin kamshin turaren sa nadosota , dukansu suka juya Dan ganin ko waye amina ta Zare ido 😳 can a maqogaro tace bruhh, binta yayi da harara tuni takama hanyar dakinsu

Mansura ta washe baki tace ashe zakazo durling amma Seda kabatamun rae, murmushi yamata wanda yafi komai ruda ta, kujera tajamasa yazauna sann tadauko lemu tazuba musu tareda cup, bismillah tace masa Ahmed yace thanks. menene maganar? gabanta yashiga faduwa tadaure dae tace Ahmed nasan kasan cewa babu wani namiji danakeso a duniya sama dakae akanka zan iya komai zan iya bada rayuwa ta akanka banajin......

ya isa yadaga mata hannu, let go 2d strength point, mansura tanisa sann tace Ahmed inaso katura gidanmu neman aurena! What aure kuma? dama nace miki zan aure ki ne ? Mansura tace fyn yanxun katabbatar mun dacewa baka sona, Ahmed yace bahaka bane amma naga dae bawani dating muke dake ba kuma ni bantaba yimiki zancen aure ba hasali ma banida ra'ayin aure ayanxu, mansura tace lamme ask you menene ribar Soyy? Ahmed yace aure, mansura tace gud sbd haka aure zamuyi bafashi shine zaibada tabbacin muna san Juna,

Ahmed yabita da kallan mamaki kana yace umurni kike bani ko kuma shawara ? Mansura tace shawara dae Ahmed yace gud to zanyi shawara da zuciyata, mansura tace hava Ahmed nida kae munasan juna tome nawani shawara, Ahmed yace ni bance ina sonki ba shawara kuma dole ce adukkan lamari, mansura tace kenan baka sona Ahmed yace waeke meyasa kincika mita ne hava yaja tsaki yayi dakinshi

Amina dake labe tace tirkashi kenan angama da bruhh amma wlh baga badae ba se yayi kamar zai warware komai sekuma yakasa, amma anty zakici ubanki wann ba namijin so bane, mansura tace mekike sakawa ne haka, firgigit tafarka daga dogon tunanin da take, , tace bakomai anty ina mamakin yadda bruhh ke yarda da bakon Al marin dake zuwar masa , mansura tace nan gaba sekinga yana driving dina, amina tace hehehe aykuwa da nabada gold dina sadaka

Ahmed yafada kan ga danshi se juyi yake meke damuna wann bakon Al amarin fah meyasa bana iya gaya mata bana santa , meyasa zanbiyewa umarninta allah kamun gata fadawa yayi kan gadonsa yana Jin haushin kansa meyasa ma ya amsa kiranta sekace wata u warshi, wayarshi yajanyo yakira Mahmud ring biyu yadaga hello mah kazo yanxun ina gida akwai matsala, Mahmud yace subhanallah ganinan zuwa momy zankai unguwa idan nasauketa zan biyu , okay sann ya tsinke wayar

Har bacci yasoma dibanshi Sega Mahmud yashigo zaune yatashi, Mahmud yace gani mod ince dae ko lfy daga ninka nasan ba lfy ba meyake damunka, Ahmed yace wato Mahmud narasa abunda kedamuna wlh nakasa yimata gardama ina biyema umarninta Al hali basanta nakeba nakasa furta mata cewa bana santa bansan meyasa ba, Mahmud yace waye ita haka ? Ahmed yaja dogon nunfashi sann yace mansura kanwar hjyr gidann, Mahmud yayi murmushi yace why not ka aureta tinda tana sonka koba komai zaka moru domin mace idan tana sanka zata iya yimaka komai arayuwa sabanin hakan kuwa se hakuri

Ahmed yace kana ganin aurenta zai zamemun alkairi senake ganin kamar batada kyakkawar tarbiya Mahmud yace shedanne ke kawo maka wann aranka koya take auren irinsu jahadi ne babba yafi auren wadda kake da yakinin cewa tana da gud behaviours, Ahmed yace amma dae nasha gayama maka nafi ra'ayin mace karama wann kam ay kona girmeta kadanne, Mahmud yace karka duba wann ba'a kanka aka soma ba.............

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B aleeyu 💕 page 5⃣4⃣
Ahmed dae abubuwa sun kwance masa , yana Jin tsoron yadda zai tinkari dad da wann zancen kae bama dad ne matsalar ba a'a abba ne keda tsaurin ra'ayi , bakinshi yatabe yace anyhow dae ni ita nakeson aure, dama kuwa aure suke son inyi saboda haka ba fashi aurenta kadaine kwanciyar hankali na, ayadda nakeji dinnan kamar ana mintsilana dole na aureta da wann tinanin bacci yayi a won gaba da shi, uhm....tirkashi masu karatu yakuke hango wann Al_amarin ?

Yau dae kam ansallami joda, amma bawani nishadi a fuskarta, dayan nurse tace hava joda ko bakya farin ciki da wann rana ne allah yanuna miki kin bar asibity nan lfy tareda sa'a, joda tace ina muryana sedai kawai damuwana daya ne ina son likitana domin in mishi godiya, dayar ta kalli daya sann tace keday kiyiwa allah godiya kawai , amma wann likitan dakike ganin bahagon namiji ne ba'a iya yimasa dae2

Gwaggo tashigo tace wae mekike jira ne tindazu driver yake jiranmu awaje haka dae tafito asibity bada san ranta ba, jikin ta bakwari , driver yagida ta asma dae wani iri, suna isa gida tabude ganbu tafita bata jira gwaggo ba, amma me takasa gane kofar dakinsu

Please Login or Register in order to submit comment