Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fura da nono tabashi Mahmud yaji dadi sosai yadinga godiya,

Kudi yaciro yabasu amma suka ki karba seda yayi kamar zaiyi kuka sannan baffa yace dari biyar ta isa badan yaso ba yamaida sauran, har bakin kasuwa suka rakashi......

Muje zuwa 🎄
ASEEYAH BASHEER ALEEYU 💕

🎄 FULANIN DAJI 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄
🎄 🎄
🎄
N@ B aleeyu 💕 page 1⃣3⃣
Dan achaba suka tara yafitar dasu daga dajin dama kuwa Dan achaba biyu tak adajin semai kudi ke hawansa bayan Yan keken mai garinsu wato wanda yake babba adajin yanada keke biyar wadanda ake masa haya dasu
Wannan kenan "

Tafiya sukayi mai nisan gaske tun Karfe tara nasafe suke tafiya adajin basufita adajin ba sekusan 12 waima saboda suna gudu, dari biyu2 suka biya sannan suka sake taron wani Dan achaba yakai Su cikin gari nanma sunyi tafiya ta kusan 1hr sannan suka isa cikin gari, anan naga sun tsaya Mahmud yakira a turo musu mota takaisu airport,

ba afi 20mnt ba segasu mota kusan ukku tareda soldiers 6 kowane dakayansa Saye kowace mota soldiers biyu ce aciki tagaba ita aka saka bag dinsu, tabiyu Ahmed yashiga dayan soldier yashiga gaba se maijansu, ta ukkun itace wadda Mahmud yashiga basu tsaya ko inaba se Filin jirgin sokoto,

Nan ma cike yake da soldiers sunyi layi2 kamar masu assembly, suna isa kowacce mota da mai bude ta, soldiers biyu suka musu iso suka shiga jirgi, zamansu keda wuya, aka kawo musu fish kebabs & pasta, se green smoothies,

Mahmud yaci abunsa Ahmed kuwa cewa Yayi ajaye masa shi Dan zai sashi amai, baturen yace me za'a kawo sir cikin harshen turanci, seda yadau few minutes sannan yace fish stew, Mahmud yaja tsaki yace inba iskanci ba meya banbanta wancan da wannan, Ahmed yagalla masa harara ai dai sekaci abunda kake so koh kabarni inci wanda nakeso, Mahmud yace dayake nan gidanku be ay dole kayi yanda kaga dama mtsss yasake Jan wani tsaki

Karfe 2 daidai suka isa abuja , kafin agama tanbadodinsu inji Ahmed 😂 har 3 tayi dole aka hanasu wucewa gida, wani gidan aka je dasu akwai komai na bukata aciki wanka sukayi suka tada sallah azahar da la'asar, mai aiki takawo musu abunci ta lemuka ferfesun kaji ne dakuma jellop rice , kadan suka Ci, suka barshi news suka buda suna kallo, Nan Mahmud yaga wani minister yana jawabin cewa za'a tada fulanin dajin wajaki, domin bincike yanuna cewa akwai man fetur sosai akasan kogin dajin bayan nan, akwai computer tana nuna cewa akwai zinare da gold awani gida, Carab idonsa yafada kan gidan da ake nunawa akwai gold da zinare aciki bakowa ne gida bane illah gidansu joda

Tini hawaye suka wanke fuskarshi yanzu idan antada Su ina zasuje, Wadanda basu yarda da kowa ba, shiru Yayi jin minister nafadan za'a basu million guda kudin gidansu da kudin barin gari inda za'a bawa kowane mai gida dubu dari ukku da hamsin,

Mahmud yace Ahmed dajin damuke fito ne fah, Ahmed yace ehh nagani, Mahmud yace amma kasan ba'a yi adalci ba koh? Ahmed yace sosaima kuwa yaza'a tada Su ba'a tanadar musu gurin zama ba mutanen dake tsoron birni kosunzo cikin gari wlh tsoro da wauta irin ta fulani zata wahalar dasu

Mahmud yace bama shiba, dubi wannan wake ken gidan ace 1 million kuma wai har kudin barin gari ay wannan gidan koba komai aciki filinsa kadai zaiyi 4 millions balantana akwai dukiya akasansa then kuma ace har kudin barin gidan hava it's not fair , Ahmed yace kozaka bi musu hakkin Su ne, Mahmud yace I think so, Ahmed yakallesa kasan kuwa waye wannan minister din, Mahmud yace koma waye shi bai isa ay shege ke maganin shege,

Ahmed yace what is it to do with them? ar u Dsame cousin? Mahmud yayi murmushi yace se yanzu nagane baka San aykin kaba , kasata fa nake yiwa aiki base Dan uwana ba, Ahmed yace ni kake gayawa bansan aykina ba , Mahmud yace kwarai da gaske indai har bazaka iya ceton wanda baka saniba ko wanda kake kyama to lallai baka San aykinka ba

Ahmed yafusata ainun, yadauko wayarsa yace look.....sekuma yafasa , Mahmud yace mezan gani, manta kawai inji Ahmed, haka Suka cigaba da argument har 4 tayi Ahmed yace nifa nagaji dazama nan gidan, kawai mutun yadawo dan iskanci baza'a barshi yaje gida ba , Mahmud yace kana iya tafiya ai,

Ahmed yajanyo wayarshi yakira driver dinshi yayi masa kwatancen gidan yace yazo maza2 yadaukeshi nan da nan kuwa Segashi, amma me mai gadin gidan yaha nashi shigowa yakira Ahmed yagaya masa Ahmed yace what nonsense gidan ubansa ne koya, Mahmud yace lfy sarkin masifaffu, Ahmed yace wancan banzar mai gadi ne wai driver bazai shigo ba, sekace gidan ubansa ne

Mahmud yadafasa calm down man, order aka basa nasan commissioner ne, kasan yanaji damu soyake muhuta sosai sannan akaimu gida, duk Wanda yafito daga wancan dajin ai dole yana bukatar dogon hutu, Ahmed yace to cemasa akayi muna bukatar hutun nibana son haka wlh, Mahmud tashi yayi yadauko masa eviron drink, ya zuba a cup yabasa, Ahmed yakarba yafara sha seda ya shanye ta tass sannan yabasa cup huhhhhhh naji yahuro iska tareda ajiyar zuciya, are you Okey Mahmud ya tambaya, Ahmed dakansa yake kasa yace yeah.......

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B aleeyu 💕 page 1⃣4⃣
Bayan magrib commissioner yaturo musu da mota biyu kowacce akwai 2 soldiers aciki dayan tadauki Ahmed dayan kuma Mahmud kowannensu akayi dashi gidansu,


Wani katon gida naga an faka da Ahmed kamar wani gari, tsarinsa kadai yakoda ni , carpet ce ja mai matukar laushi ashinfide mai tsawon gaske har zuwa wata karuwar kofa kamar dai get , flowers ce shimfide ako ina, kamshi kadai ketashi narasa ta inda yake fitowa

Wata chocolate din yarinya naga tafito dagudu sanye cikin doguwar riga ta wani mayen less white & black tayi daurin dan kwali oll back simple make up tayi amma tahadu, hannunta rike da flower murmushi kawai take hakoranta tass dayan haurenta sanye da hauren makka

Flower tamika masa tareda rungumesa tana wlcm bros, dariya yake nikam nayi mamakin ganin wannan hero yana dariya , hw ar u 6ter? Yarinyar tace am ok bros yagajiya, Yace bagajiya, 6ter gajiya tabi jiki shin ma wai kintaba ganin soja yagaji, yarinyar tace Au haka nefa, rugumeta yayi suka shiga daga ciki ,

Katuwar kofar aka bude zokuga wani hadadden parlour tsayawa nuna irin haduwar gurin kauyancine, ku kissima aranku kawai, Wata kyakkyawar mata naga tafito tareda wata beauty se murmushi suke, matar takarso tace wlcm son, kansa kawai yadaga mata, yarinyar tasauko daga downstairs tana wani yauki tamkar miyar kubewa , ahankali ta furta big bros wlcm, tancuu shine abunda yafada

Yarinyar dake makale ajikinsa tace bros muje inrakaka dakinka nasan kana bukatar hutu, Ahmed yace 6ter jeki huta mana, tace no bros 2dy its ur dy, murmushi Yayi to naji muje , hannunsa tasaka ahamatanta tajashi suka bi wata hanya, wani hadadden daki naga sun shiga, aiko nace baza'a barni abaya ba atare muka shiga, daki ne kato yafi hall din Dan fodio set din kujeru biyu ne aciki sannan wani wakeken gado mai runfa gadon tamkar na cikin joder akbar, kamshi ketashi kota ina , shkar kamshin yayi tareda Jan hancinsa yace 6tor I lyk it, yarinyar tace to ay gashinan sekayita shaka

Hannunta yajanyo suka zauna kan gado yace Hafsa gayamun dame2 yafaru bayan tafiyata me akayi miki waya bata miki rai bayan tafiyata ???? Dariya ta aza kai yaya koma me akayi ai yawuce balantana ma ba abunda yafaru, Ahmed yace u ar lie, nasan dole Anyi wani bazaki gayamun bane, tace yaya believe me i swear, kafada yadaga any where zanduba camera ta, ido tagwale kai yaya allah bayasan tada fitina,

Ahmed Yace zan mareki wlh get out b4 I show you my anger , kafadarshi tadafa tace relax bros, tarike kafadunsa lok at me, lok into my eyes, jajayen idonsa yadago yakalleta sekuma yamaza yajanye murmushi tayi, ta tashi tabude fridge tadauko masa eviron drink tabasa, amsawa yayi yasha, tace ar u okay, yeah ya amsa mata, tace gud nyt ta fice daga dakin,

Tana fita tasame wannan yarinyar da matar adakin wato hajiya da amina, hjy takalli amina tace kalleta wai ita mai yaya, amina tace barta black gul kawai yarinya kamar yar tsintuwa babu inda tadauko abbanmu, hjy tace wayasani to ko yarsa tinda kowa yasan halin gyatumarsu, tuni hawaye suka wanke fuskar Hafsa, kofar dasukaji anbude dakarfi ce yasasu juyowa azatonsu Ahmed ne har hantar cikin Su takada, abdallah ne yashigo se tangadi yake alamar yabugu,

Hafsa tadubesa ta karkada kai cike da takaici, tawuce dakinta tabarsu atsaye, mamma zoki kaini dakina shine abunda yake fada, tace wato ba sallama kawai in kaika dakinka, amina tace hava mama baki ganin yanayinsa ne

Yace mamma yanaga anyiwa gidannan decoration ne baki mukayi, amina tace big bros ne yadawo, Yace wht nonsense big bros dady ne, ni lokacin da zandawo daga india ba shegen dayayi mun wannan decoration din se shi mai sati biyu kacal, in possible" yadauki cup shuri yatashi sama carab se hannun Ahmed yacabe cup din dukansu suka juyo suna kallansa

Gurinsa yadum faro kamar wani zaki tafiya yake tamkar ruhit acikin doom sumar kansa nata tashi sama dukansu sun tsorata daganin yanayinsa, wuyan abdallah yacabko ya wazga masa mari, ar u mad? Hjy tace kai mezaka masa ne haka, Ahmed yajuyo dakarfi yana cizon lebensa, Yace dukansa zanyi zaki rama masa ne ? Amina tace bros tomeyamaka ne?

Ahmed yasaki wuyan abdallah yacakumi wuyan amina yace mekika ce, ta marmasa ido, tuni yawan ke ta da mari yadago fuskarta yasake marinta ya hankadata kasa hannunsa yadago zai sake kaimata duka, abdallah yarikesa tabaya, yajuyo yana yinayiwa hannun sa kallan wulakanci yace ina tausayin wannan kucakin hannun naka alokacin dazan cire shi anawa , hhhhh😂 abdallah yace wai mekake takama dashi indan Dan wannan Dan iskan cos naka wlh bazai tsorata niba............

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B aleeyu 💕 page1⃣5⃣
Ahmed yayi murmushi tareda kimtse fuska yasa hannunsa yadinga janye hannun abdallah se kat2 kakeji tuni abdallah ya kwarma ihu, Ahmed yace no no tin yanxu ya ciyo kwalarshi har sunajin bugawar zuciyoyinsu, Yace wato baka dena shaye2 ba koh? Abdallah yace meye matsalarka aciki

Hjy tace shi nagani inaruwanka da rayuwar shi, Ahmed yatura abdallah dakarfi yakaraso gurin hjy kamar zai hau kanta yace bakida hurumin hanani hukunta Dan uwana, hjy da tsoro tayi shiru gudun yamata wani abu

Tin safe Hafsa ta tashi tahada masa special break nuggets da tea se aresh da kwai , takai masa dakinsa danshi baya cin abunci a dining se in dady yana gari , ita ke basa tea din da nuggets har yagama tasaka tissue tagoge masa baki sannan itama taci nata , tagyara masa daki dukda bakomai yayi ba, tawanke toilet, sannan ta kunna bona tarufe dakin,

Ahmed yashirya cikin kananan kaya riga da wando black n Wight yaja motarshi se gidan commissioner yasanarda shi dalilin zuwansa gidan, wato yanaso acanza zancen tada fulanin daji, commissioner yace sedai kayi hakuri son amma har nacika file din , Ahmed yace shiit yanzu miye abun yi sir gsky Anci hakkinsu akwai wani gida danagani ance wai 1 million za'a basu alhalin gidan yakai 4 sannan duk sauran mutanen dajin wai dubu dari ukku za'a basu da hamsin,

Commissioner yace karya ne masu gidan 10 million mukayi za'a basu sauran jama'ar dajin kuwa 1 million ne, Ahmed yace bahaka yafada ba a news jiya, commissioner yadauko wayarshi yakira minister, minister yace bincike yanuna babu komai agidan ansamu mistake ne afarko, girman gidan yasaka za'a basu 1 million

Commissioner ya ajiye wayar yace wannan shine fist work da zan baka kaje kabinciko mun, gaskiyar al amari, Ahmed yace ok sir gobe zakaji komai, commissioner yayi murmushi yace am proud of you son, I sure will do it, Ahmed yace yeah sir I shall do it with my heart, murmushi Yayi yace I know son, all d best.

Haka yabaro gidan commissioner yanata nazarin yadda zai bullowa lamarin , Mahmud kuwa yanacan yana nasa tsarin, duk arude yake damuwarshi daya baisan inda zai sake haduwa da joda ba idan sukabar dajin

A DAJI KUWA,,,""
Mutanen dajin labari yazomusu cewa za'a zo atada Su saboda haka Suka fara koke2 gabaki daya dajin yazama tsit kowa da bukin zuciyarshi, gwaggo tacewa baffa tun ba azo aka wulakantasuba Su tattara inasu2 subar dajin kunsan fulani da shegiyar zuciya ,

Haka Suka tattare duk wani abun amfaninsu, gwaggo tace sokoto zasuje sunemi Yan uwansu akwai kanwar babarta dake aure sokoto amma asaninta a masina suke, dajin kowa yafito yanata kukan rabuwa dasu hansai tarike joda sunata kuka kamar wadanda sakon mutuwa yariska har sunkai bakin kasuwa joda tace gwaggo ina zuwa, ta falfala da gudu , gwaggo na Kiran ina zaki amma ina har tabace musu dole suka tsaya jiranta

Joda kuwa ramenta datakesa kudin da Mahmud kebata taje tabude tagansu kuwa suna nan, tayi hamdala tadauko har zata duba nafarko tace kai nama San hansai zata iya budewa, Dunkule Su tayi a zaninta takoma gun Su baffa

gwaggo tace mekika tusa azanin nakine haka, tace gwaggo kudin da yaya Mahmud kebani ne dik yasha fura nikuma se in sakasu arame gwaggo tace mugani, Koda aka kirga dubu ukku cib duk Yan dari biyar ne, gwaggo tace hamdan khasiran, wadannan sun ishemu rayuwar mu ko jirgi mukeso zamu samu, lol kuji gwaggo fah😅

Dan achaba biyu suka tara daya da kayansu tareda baffa daya kuma gwaggo da joda, har Suka kai wajaki kauyen sokoto, Nan Suka dinga tanbayar gidan margayi alpha nuhu, dakyar suka sami wanda yasan shi yace musu ay yadade da rasuwa sedai yayan shi suma kuma ukku daga cikinsu suka rasu sora biyu mujittaba se muktar mujittaba yana cikin garin sokoto muktar na masina shida iyalanshi,

Mutimin yayi musu jagora suka shiga motar sokoto dari hudu da hamsin aka kaisu wato dari da hamsin2 abakin tasha aka ajiyesu, suka tan bayi gidan mujittaba aka nuna musu kusaga masallacin shehu inda makarantar almajiran fulani,

gwaggo cike da murna tashiga gidan kasancewar gidan da tasha titi ne kadai yaraba Su, rike take da hannun joda baffa na janye da kayansu.......
WAYE JODA?
MENENE ASALINTA?
kubiyoni Dan jin wadannan amsoshin

Muje zuwa 🎄
ASEEYAH BASHEER ALEEYU 💕

🎄 FULANIN DAJI 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄 🎄
🎄 🎄 🎄
🎄 🎄
🎄
N@ B aleeyu 💕 page 1⃣6⃣
Asalin joda =
Alpha nuhu shine kakan gwaggo wanda yahaifi mahaifinta wato muktar , mujittaba, ayuba, suwaiba se kasim ayuba da kasim da suwaiba duk sun rasu, dukansu yayan halimatu sadiya ne, wato matar alpha nuhu

Sadiya asalinta yar sudan ce, wato Arab agurin karatu alpha yahadu da ita anan ya aurota, yazo da ita kasar masina takusaga, kasar saudiyya, alpha fulani ne na usuli tin kaka da kakanni, kuma makoho ne sedai akwai dinbin ilimin addini agaresa hakama yayansa sunsami karatu sosai,

Alpha yarasu yabar yayansa biyar tareda matarshi, maimuna itace mahaifiyar gwaggo wadda takasance ya tafari ga malam muktar, se kanwarta saratu sukadai ne ga malam muktar gwaggo ta taso cikin gata da soyy sutura babu wadda bata daurawa muji

Ganin haka yasa A'i da yayanta ukku kishi wato luba, hadiza da abdul hadi, ganin uwayensu maza sundora ma gwaggo son duniya, hakan yasa A'i biyar bokaye tana karbar magani tanayiwa uwar gwaggo da itadin, tin ta nayi yana karyewa har allah yabata sa'a

Watarana gwaggo tafito daga makarantar allo, tana shigowa gidan A'i tace mata tashiga bayi tadauko mata buta tana tafiya A'i najanta da fira har tamanta da addua daganan aljannun da aka tura suka figeta se dajin wajaki, suka yada ita sannan suka mantar da ita gida

Agida kuwa Anyi ne manta har an gaji babu haukar da uwayenta ba suyi ba daga karshe suka sangana dalilin dayasa mahifinta komawa kasarsu kenan wato masina

Ai kuwa bokanta yatabbar mata cewa gwaggo bazata dawoba se har jikinta ko jikin danta yagamu dana dai daga cikin danginsu sannan zata dawo a hayyacinta, gwaggo kuwa abakin kogin kada aka yada ita, anan ne baffa yaganta , yadauko ta saman jakinsa yakaita gidan Su

Mahaifinsa barau shine yacigaba da kula da ita har taji sauki daga nan tazama yar gida, zuwa wani Dan lokaci barau yahadata aure da dansa wato baffa, shekararsu kusan biyar sannan gwaggo ta haifi danta wato sani baifi wata uku ba yarasu tasake haihuwar wani shima aka saka masa sani watansa bakwai yarasu seda tayi yaya kusan biyar suna rasuwa mata da maza dukansu bada shekara suke mutuwa

Joda ce tashida itace kuma auta dalilin dayasa ake sonta kenan
Wannan kenan "

gwaggo tayi sallama tashiga gidan, Wani dattijo tagani rike sa alkalami da allo yana rubutu ahankali abubuwa suka fara tariyo mata, dasauri tace malam!
Kansa yadago yana kallanta muryar wa nakeji kamar innata, tace nice malam, malam yace dama kina raye,

Zama tayi tadinga basa labarin rayuwar ta har zuwa yanzu malam yakalli baffa yace angode Dan uwa allah yasaka muku da alkhairi ameen, tace malam inna baba da innata, malam yace suna masina tun bayan rashinki da mukayi, yakasa zama kasar nan, tace saratu fa? Seda yayi Jim sannan yace allah Yayi mata cikawa, yanzu shekara goma kenan, hawaye suka dinga zuba afuskarta

Malam yace hakuri zakiyi yanxu ina zaki masina zakije ko nan zaki zauna domin nima kwanan nan nake shirin komawa can nagaji da nanan kudina kawai nakeso Su cika, gwaggo tace nawa ake zuwa ai munada kudi, malam yace dubu goma ne duk mutun daya

Baffa hai bahause bata iya San kudi ba, mezatayi da dubu goma hanake ko makka zasu kaini, malam yace hmm nan fa ba irin dajinku bane. ....

🎄 FULANIN DAJI 🎄
N@ B aleeyu 💕 page 1⃣7⃣
Ahmed yayi duk wani bincike da zaiyi an tabbatar masa dacewa, babu komai acikin gidan, amma kuma seda yasamu ganin governor da minister yayi korafi akan gidansu, haka yadinga shige da fice seda yaga anbiyasu yadda yakamata, sannan hankalinsa ya kwanta, yakira commissioner yashaida masa yayi murna kwarai yace Ahmed kwazonka da jajircewa na burgeni,

Mahmud labari yazomasa, amma baisan wanda ya gyara al amarin ba, yadaiji dadi sosai , Yace insha allah zanje next week in kai musu ziyara kamar yadda nayiwa kanwata al qawari wato joda"

Malam yakira gwaggo yagaya mata cewa tafiyarsu jibi ne dama bagabadai zasuba abdul hadi da matarshi nanan, gwaggo badan ranta yasoba tazauna suka wuce aka bata dakin, hasiya tazauna aciki, haka suke zaman gidan a wahalce domin kuwa hadi bashida imani ko kadan, seda tagwammace zaman daji da gida, amma koba komai taji dadin ganin danginta, joda tazama boya agidan , duk jumu'a setafita da tallana ruwa bakin masallaci, dayake nan bakowa keson fura ba akwai ta ko ina ,

Ahmed yatabbar da gaskiya ya kauda rashin",, ta ma'ana yatsaya tsayin daka aka gina ma kowanne mutun gida dai2 danasa tsarinsa dai2 talaka, gidan baffa ne kadai ba'a ginaba saboda ba asamu ganinsa ba andai killace gidan, Nan cikin kauyen sokoto wamakko kudin gidan dakomai suna hannun shamsudden wanda suke cewa deeni wato PA na minister,

Ahmed yagama komai yaje yasamu commissioner yayi masa bayanin yadda komai yakasance commissioner yayita sakawa Ahmed albarka, yana fita yace aransa allah nuna mun ranarda zan aurawa Ahmed yata sarina, murmushi Yayi allah yanuna mun wannan Ranar ameen zanyi alfahari dashi cikin zuriata idan har yakasance surikina

Ahmed yadawo daga barrack dinsu yashigo hannunsa rike da hularsa, yana takon girma karar rawar gidan yadanna mai nuna ana bukatar ganin kowa dakowa, cikin minti biyar kowa yahallara harda abdallah da masu aikin gidan hjy da yar gold din yarta amina,

Ahmed yace kunsan cewa taraku nan gurin agabadai yana nufin akwai important issue dazakuji, so ba wani abu bane, dad zai dawo gobe at 4 to 6 pm ana bukatar gyara agidan nan da cook, yakalli husaina wadda itace shugaban masu aykin abinci yace zanbaki list din abunda ake bukatar kidafa, hjy tace amma ai....Ahmed yada mata hannu ✋🏻 amma me bannemi kowa Yayi mgn ba kona bada order ne, Iye?

Yamaida kallansa ga mai gyaran gidan yace tsohuwa baki bukatar gyara ko bayani you know how to make diz house special nd cute veuryfull, ar u hear me? Tsohuwar tace Yes sir, Ahmed yace gud, se kai mai gadi kafi kowa rawar kan tsiya idan bakayi hankali ba kana kusaga rasa aikinka,

Ali driver katabbatar anwanke duk motors din dasuke gidannan, remain you Hafsa yanuna ta, kibiyoni ki karbi keys din dakin dad kitabbatar kin gyara shi nasan zaki iya, abdallah ka kiyaye kanka daga shaye2 nan kasan abunda yakai baba Egypt natsawon wata shidda duk matsalarku ce kaida uwarka da wannan fantimotin yanuna amina, ta haifar masa da hawan jini,

So all of you b care full idan akayi something bad or rubbish, har nagani white my ayes wlh, rankowa a gidannan zai baci, har yajuya zai wuce hjy tace inada magana, Tsayawa Yayi batareda yajuyo ba, Yace bayanzu ba banda enough tym dinda zan karbi korafin ku, dts oll yayi shigewarshi

To mekuke jira muna fukan banza kunwani tsayawa kuna kallona , tadaka musu tsawa tuni kowa yasani inda zashi , Hafsa ta kunshi dariya tabi yayanta da gudu.........

🎄 FULANIN DAJI 🎄 N@ B aleeyu 💕 1⃣8⃣
Dakinsa tabisa yabata keys din yakara jaddadamata cewa tana shiga tarufe kofa domin baya bukatar kowane Dan iska yashiga dakin , atake zasu sace wani abu tunda dukansu sunzama gwaska , Hafsa ta kyalkyale da dariya, hava yaya yadai sata, Yace oh to karya namusu ko sharri, Hafsa tace a'a bance ba, Yace dallah kije aykinki ko sekin gama min iyayin tsiya, har zata wuce yace look Tajuyo idan akayi sallar la'asar kizo nabaki list din girki dazamu bukata, toh kawai tace masa tafita

A parlour tasame Su hjy se zagin Ahmed suke, Hafsa tace dubi wai iskanci mutun da gidan ubansa a hanashi shiga dakinsa, hjy tace inbanda iskanci ma wai alhj zai dawo amma se abakin dansa zanji, sannan kuma shi zai tsara mana yadda komai yakasance banida ikon shiga dakin mijina se in yana ciki bani zan tsara girkin danakeso ba wai se shashan dansa

Hafsa tayi kamar batajiba tayi hanyar dakinta, amina tace ke zonan Hafsa tayi mata banza, abdallah yace ke Dan uwarki ba mgn ake miki ba seda tajuya sannan tace ai ba ke ne sunana ba, duk Wanda bazai kirani da sunan da ubana yarada mun ba ai seya bari

Abdallah ya taso da karfi ya zare belt zai zaneta hjy tace a'a Dan mama kada ka tabata yayanta nagida,
Da kibarshi yatabata wlh in nuna masa banbancin kashi da masa, gabadansu suka juya suna kallan Ahmed yace wato dama dukanta ake agidan nan idan bana nan, kekuma yanuna Hafsa shegiya wawiyar banza ni uwata ba haka takeba ba wanda zai takata bata rama ba bansan ko zuciyar wa kika gado ba, dad dina bahaka yakeba,

Zuciyata ce tadauko, daga kofa sukaji wannan sautin, Ahmed yace woww abba kaine, nine ahmadu muhammadul mahi "!
Hafsa ta aza dariya kai abba duk wannan sunansa ne, Yace sosai kuwa, kema in kina so injero miki naki dasauri

Please Login or Register in order to submit comment