Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai likitafa ya ce, tana buk'atar Hutu, gashi dangin ango since k'arfe tara akwai mother Night, yakamata tasamu ishashshen barci kafin sannan, yanzu bari nayima Basman aunty Yahanasu magana saita shirya tazauna amadadin amarya tunda kusan kansu d'aya.
Yauwa hakama yafi, dama gasu suna kama ba laifi.

Haka suka saka Basma aunty yahanasu k'anwar ummi tashirya tsaf tamkar amaryar, idanma baka saniba saika d'auka Rahma d'ince Dan suna matuk'ar kama, idanuwa kawai Rahma zatafi Basma.
Dahaka aka gudanar da kamu Wanda yak'ayatar da dangin ango, su khairiyya da khursiyya dasu aunty Rasheeda sai zuba lik'i suke wa amarya, Dan basusan ba amaryarsu bace.
Dahakadai taro yatashi gab da magriba Alhmdllh.

Duk shagalinnan da akeyi Safna tana d'aki kwance abinta, da barcima takeyi kid'an da'aka sakane yasa tatashi tana mita da tsaki anhanata barci wai, wayarta ta d'auka takira *boy danneman k'arin bayani akan aikin data bashi.
Ya ce, "mata yana nan yana k'ok'ari.
Tana yanke wayar takira Baseera sukaita labarinsu Rabi duk akan bobone.
Na CE hummmm.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Su bobo suna isa gidan suka Tatar da ya Is'haq da ya Hamza zaune aharabar gidan, harda wasu samari wajensu bakwai, cikin samarin danginsune, ya Hamza yana cikinsu sunashan shafta.
Ya Is'haq kam yana gefe zaune saman mota Dan bakomai yake Shiga cikinsuba kasancewarsa babba.

Bayan bobo yayi fakin suka fito, wajensu ya Hamza suka k'arasa, hannu sukaita bama matasan samarin ana musabaha🀝.
Bayan sun gama gaisawa Bobo yanufi Inda Ya Is'haq yake.
Hannu yabashi shima suka gaisa.
Ya ce, "kunje kun wani mak'ale a asibiti tamkar kun manta da abinda me gabanku.
Sorry babban yaya, bobo yafad'a yana had'e hannayensa waje d'aya alamar tubaπŸ™πŸ».
Dirowa ya Is'haq yayi, to yazanyi idan ban hak'uraba ma.
Motocine suka fara shigowa gidan, bobo yabisu da kallon yana fad'in wannan gayarfa daga ina?....
Daidainan ya Hamza da ya sulaiman suka k'araso garesu.
Ya Hamza ya ce, " daga gidan amaryarka suke, sun halarci kamune.
Baki bobo yad'an ta6e ya Hamza miye kuma kamu?.
Kafin ya Hamza yabashi amsa aunty Rasheeda da aunty ummy suka k'araso, aunty sameera dasu khursiyya suna biye dasu.
Bud'a aunty Sameera tarangad'a akunnen bobo, yay saurin toshe kunnansa, saida tagama sannan ya kalleta fuska a shagwa6e, kai aunty Sameera dodon kunne zaki kashemin?.
Dariya suka shek'e dashi suduka, yayinda aunty Rasheeda tafara fesama bobo turare mai shegen k'amshi, kaima ankamaka kamar yanda mukaje kama amaryarka.
Dariya su ya Sulaiman suka saka danganin yanda bobo ya kwa6e fuska tamkar zaiyi kuka, ALLAH matannan nakula kun rainani yafad'a yana hararsu.
Dariya sukayi gaba d'aya harda wasu daga cikin dangi dasuka zagaye wajen.
Aunty ummy ta ce, "tab wlhy Bobo matarka ta had'u jar ubancan kai, kaiga wasu idanu masha ALLAHU, (" nace hum danma bakiga na asalin amaryarba kenan), tacigaba da fad'in aifa inaga aka kawo amaryarnan bazaka ringa fitaba, aikinma hak'ura zakayi dashi.
Dariya sosai ake shek'awa, dukda haushi da yacikama bobo ciki wannan bai hanashi murmusawaba, ya ce, ''yan sa ido, kunje kunata k'arema yarinya kallo, halan har muninta kun gano?.
Wata Zainab acikin danginsu ta ce, "wlhy ya Abdulmalik babu mai iya gano munin Rahma amarya, masha ALLAHU kam komai yaji zam zam..... Tak'are maganar da rufe baki.
Nanma dariya akayi, shikam ya ce, kwadaiji dashi sa'idinniya kawai masu barci da ido d'aya, yana gama fad'a yafito daga wajen.
Wasu daga cikin 'yammatan jisuke inama sune da wannan guy d'in, lallai yaci sunansa Bobo.
Wasukam kishine yacika zuciyarsu, Dan sundad'e suna nuna masa so yana basarwa saboda jin kai, wasukam har iyayensu saida sukai masa talla amma ya ce, "kai kasuwa.
Cikin gidan yashiga Dan soyake ya d'auro alwala, babban falon k'asa cike yake dam da mutane, yanashiga suka hau tsokanarsa wai angon k'amshi angon k'amshi."
" aransa ya ce, "za'a gogudai".
Haka yagaida wad'anda zasu iya jinsa ya haye sama d'akinsa bayi yashiga yad'auro alwala yafito, su aunty Sameera ma duk sunshigo ciki.
Yazo zai fita Ammi ta ce, " mukarram!.
"na'am Ammi ya amasa yana juyowa, k'arasowa tayi Inda yake takama hannunsa suka fito.
Wani d'an lungu tajashi ya ce, " Ammi lfy dai ko?.
Lfy lau mukarram dama tambayarka zanyi d'azu kuwa kaje gidansu amaryar taka?.
Gefen wuyansa ya sosa, afuwa ammi, wlhy abubuwane sun mana yawa.
Kanta ta girgiza haba mukarram ya inamaka kallon mai hankali amma kanason 6ata wayonka?, babu dad'ifa, iyayen yarinyarnan bazasuji dad'iba ace bakaje gidanba tunda aka fara maganar aurennan, shin kai zakaso ayima su khursiyya hakane?.
A'a wlhy ammi bana fata, amma Dan ALLAH kiyi hak'uri nayi kuskure, insha ALLAHU zan bata hak'uri anjima idan munje mother night.
To shikenan ammadai Baka k'yautaminba, Bahaka nasoba.
Tom kiyi hak'uri Dan ALLAH.
"Ya wuce."
Yauwa ammi an kar6o d'inkin Nawal kuwa?, wlhy namanta shaf, kuma harda wanda zata saka anjima.
Eh khairiyya ta amso d'azu kafin sutafi wajen kamu.
Yauwa harnaji dad'i, bari naje sallah ammi har an tayar inagama su yaya sun wuce.
To saikun dawo.

Masallaci yanufa ammi kuma takoma ciki.


.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Anayin Sallar magriba Safna ta sid'ad'e tabar gidan, sai gidansu kamal, acewarta bazataje wajen wani mother Night ba, saikuma tana zuwa gidan ta tarar dasu Ameera suna shirin zuwa harda momynsu.
Dayake momynsu kamal tasan komai Dan baba abubakar yasanar da ita, (k'anin Abba ne, kuma mahaifi gasu Br kamal abokin aikin bobo) batace mata komaiba itama, safna tashige d'akin Ameera tayi kwanciyarta, sukuma suka nufo gidansu Safna d'in, akabarta itakad'ai agidan sai 'yan aiki.

Rahma ta farka bayan sallar magriba, kasancewar tana fashin Sallah saikawai aunty Madeena matar ya muneer tasata tayi wanka.
Mai kwalliya tafara aikinta na fente fuskar Rahma.
Itadai Rahma bin kowa kawai takeyi da ido, kad'an kad'an saita share hawaye, saida mai kwalliya tamata magana sannan ta tsagaita da kukan aka tsantsara mata kwalliya ta d'aukar hankali.
Wani doguwar riga bubu aka bata tasaka, tawani material Orange da d'igo d'igon lemon green ajiki, aka nad'a mata lemon green d'in d'ankwali, sai fashion na 'yankunne da sark'a maid'an tsawo, tasaka bak'ar coka wadda ta manne awuyanta.
Yasalam nafad'a yayinda naga amaryar k'amshi tafito ras kamar ba Rahman ummiba, tayi k'yau masha ALLAHU.
Fos aunty hafsat tabata, wadda itama takasance lemon green, sannan tasaka takalmi lemon green shima mara tudu.
Hummm komaifa yaji ajikin amarya.

Ihsan k'anwar Br kamal tamatso kusada ita, kai Rahmana kinyi k'yau wlhy, na tabbata angonnan yaganki saiyace gwamma da akayi, wlhy saikin susutashi.
Basma ta ce, "ni tsorima nake karya rikice yace daganan sai gidansa.
Duka Rahma takai musu, cikin dasashshiyar muryarta datasha kuka ta ce, " yan iska kawai, aii dama halinku d'aya.
Dariya suka shek'e da ita harda tafawa.



*_Bobo_*..........






*_godiya muke masoya, ALLAH yabar zuminci._*
[11/12, 2:16 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_


_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*

_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*


*_"wannan page d'in nakine Maman useey alkairin ALLAH yakaimki har gidan baban useey, ni marak'issiya naji sak'onki wajen aunty bilyna."_*
Luv uπŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ‘ŒπŸΌ

1⃣9⃣&2⃣0⃣

A 6angaren bobo kam bayan sun dawo daga masallaci aharabar gidan suka sake zama, hira aketayi da barkwanci, saida aka k'ara kiran sallar isha'i sannan suka mik'e, masu sake alwala suka sake, wadda tasu bata karyeba sukayi gaba.
Ana idar da sallah suka shigo gidan, shiri suka fara, kowa yana k'ok'ari kada time ya k'ure.
Bobo kam wanka shima yashiga, yafito d'aure da tawul fari a k'ugunsa, k'arami kuma yana goge kansa zuwa fuska da wuya har k'irjinsa zuwa k'asa.
Wurga tawul d'in yayi saman kujera, yaja kujerar madubi ya zauna, mai yafara shafawa, hardasu farar fauda afuska, yashafe kansa da mai mai k'amshi har zuwa sajensa dad'an gemunsa na gayu, yasa kum yak'ara taje kansa da gemunsa, sannan yay amfani da burosh wajen kwantar da sajensa, yako kwanta luf sai walk'iya yake da tashin k'amshi.
Turarurruka yad'auka kala kala yafeshe jikinsa, sannan yanemi guri abikin gado ya zauna batareda niyyar saka kayaba.

Atsakar gida kam mutane harsun fara fita, Dan kowa bayaso atafi abarsa, dandanan motoci suka fara d'aukar mutane, kowa ya cakire da kalar kayan dayakeso, manyan iyayene kawai suka saka wani Dan datsetsen less fari tas, suka nad'a Orange d'in gwagwgwaro, masha ALLAHU abin sai Wanda yagani.
Su khairiyyama ba'a barsu abayaba, sunci ado da dogayen riguna na lemon green d'in material sunyi k'yau masha ALLAHU, suda matansu ya sulaiman duk iri d'aya suka saka.
Nawal ma anshiryata cikin farin less irinnasu Ammi, doguwar riga aka mata, aka nad'amata Orange d'an kwali, yarinyar tafito d'as kamanninta da bobo ya k'ara fitowa.
Tare suka shiga Mota da Ammi.

Ya Hamza yafara waige waige, cikin Jan tsaki ya ce, "wai mi Bobo yakeyine tun d'azu yafasan saiyaje sun taho da amarya, gasu ammi harsun wuce.
Ya is'haq shima yay tsaki ALLAH yaron nan d'an wulak'ancine, Hamza kaje d'akinsa kaga miyakeyi?.
Ya Hamza yanufi d'akin Bobo, ya Sulaiman dai baice k'alaba.
La'ilah Abdulmalik minene haka?.
Bobo dake zaune yana latsa waya yad'ago yana kallon ya Hamza daya had'e cikin Farin Suit sai k'amshi yake.
Minayine yaya?.
Bansaniba, dallah malam kana 6atamana lokaci katashi kasaka kaya, su Ammi harsun wuce.
Baki yaturo kamar wani k'aramin yaro, nikam wlhy ya Hamza barcima nakeji.
A'a kakan barci kakeji ya Hamza yafad'a ahasale, wlhy zankira ya Is'haq.
Da Sauri bobo yamik'e, yafara saka gajeren wando da bes, ya warware had'ad'd'un Suit lemon green sai d'aukar ido sukeyi.
Wandon yafara sakawa da Orange d'in Riga mai dogon hannu, ya tsuke k'ugunsa da belt, ya Hamza yad'auki nektayit d'in green yafara saka masa, shi abumma dariya yabasa, amma baiyi dariyarba gudun kar ya Hamza yasake k'uluwa.
Da taimakon ya Hamza yasaka rigar Suit d'in, yafara saka botiran ya hamza na gyara ma kwala d'in. Takalmima saida ya taimaka MASA yasaka, sannan yak'ara feshe jikinsa da turare, yad'auki wayarsa d'aya yazura a aljihun Suit d'in, suna tafiya yana d'aura agogo.
Na ce o'o me bobon Ammi sai a slowly.

Saida ya Hamza yaga yashiga mota a baya, sannan shima yashiga mazaunin direba Nasiba d'iyar k'anwar Ammi na gefensa.
Suma su ya is'haq suka tada mota, suna gaba su bobo na bayansu har anguwar su Rahma.

Ak'ofar gida suka faka, ya Hamza yafita shida Nasiba har cikin gidan suka Shiga sukace afito da amrya ango yazo.
Gaban Rahmane yafad'i Ra's, jitake tamkar tafasa ihu, kowacce irin tarba angon zai mata ta tanbayi zuciyarta?.
Batada mai bata amsa, tana cikin zancem zuci aunty Ruk'ayya ta ce, taso Rahma angonki yazo.
Jitake tamkar ta ce, bazataba amma yazatayi.
Haka aunty Rukayya takamo hannunta sukayo waje, dama dayawan mutanen sun tafi sai k'alilan suka rage.
Kowa yashiga mota amarya kawai akejira.
Ya Hamza yabud'e d'ayan gefen da Bobo yake zaune Dan ganin amarya tafito. Azuciyarsa ya ce, ''masha ALLAHU, gsky amaryar auta ta had'u.......
Isowarsu ta k'atse masa tunani, yayinda gaban Rahma keta fad'uwa azatonta Ya Hamzane angon, kanta na k'asa aunty Ruk'ayya tasakata amotar.
Wani k'amshine da sanyi suka bigi hancinta, tashak'a talumshe ido azuciyarta ta ce, ''oh ALLAH, wannan wane irin k'amshine?.
K'ok'arin gyara zama tayi saitaji ta dunguri mutum, dasauri tajuyo ta kallesa, yana zaune ak'ame kamar wani jinin sarauta, saidaifa k'amshin amaryar tasa ta narkar da zuciyarsa, saiwani lumshe idanu yakeyi, ahankali yajingina bayansa da kujerar ya lumshe ido.
K'irjin Rahma sai dukan uku uku yake, jitayi wani sabon zazza6i yana neman rufeta, dukda kallon fisha tayima angon nata ta tabatar ya had'u masha ALLAHU.
YA Hamza dake tada mota ya ce, amaryarmu ykk?.
Muryar Rahma na rawa ta ce, "ina yini.
" lfy lau, ya fara hidima?."
Alhmdllh tayi maganar ahankali.
Tad'an kalli gefen Bobo ta ce, ina yini.
Dukda yagane dashi take amma yay shiru.
Takuma cewa ina yini, sai asannan ya amsa da lfy, ykk?.
Kasa amsashi tayi, sai kawai tayi k'asa da kanta tana wasa da zoben hannunta.
Sunkusa isa wajen faty d'in Bobo yatashi zaune sosai, wata leda yad'akko agefensa yazaro rafar 'yan 200 guda hud'u yad'ora saman cinyarsa.
Rahma data k'urama zonen hannunta ido saikawai taga mutum ya d'oro hannunsa saman cinyarta, gabanta ya ce, "wani Rasss!, fos d'inta yazare data d'ora saman cinyarta ta d'ora hannunta akai.
Tabud'e idonta ahankali daga rintsewar datayi, Fos d'in yabud'e yaga 'yan 50 rafa biyu sai wayarta, wayar yaciro yasaka kud'in daya ciro aleda yasa a fos d'in maida wayar yayi zai rufe fos d'in amma tak'i shiga dan tacika dayawa.
Ciro wayar yakumayi yarufe fos d'in yad'ora mata saman cinyarta, wayarta kuma yasaka cikin aljihun suit nasa, nufinsa idan sunje angama taron talik'a kud'in saiya bata.
Itadai Rahma batace masa k'alaba Dan batasan miyayi da fos d'inba.
Har gaf da d'akin taron ya Hamza ya faka, yafito yabud'e musu k'ofa, asanyaye Rahma tafito, duk kunya ta isheta tasaba duk inda zataje saida k'aton hijjab, amma yau gata kod'an gyale babu, sauk'intama Rigar bubuce kuma tabud'e bata matsetaba.
Su yaya Ishaq suma fitowa sukayi daga motarsu, suma kayansu iri d'aya dana ya Hamza.
Suma sun yaba da amaryar k'anin Nasu sai masha ALLAHU suke jerowa.
Ya Hamza yashiga d'akin taron yasanar da MC amarya da ango sun iso.
Aiko nanfa yafara kayayato, falon taron yay tsit anzuba ido aga amaryar Bobo d'an gayunnan maiji da kansa.

Ahankali Bobo yatako har zuwa gaban Rahma data duk'ar dakai k'asa kamar ace ar ta gudu.
Ahankali ya ce, "bismillah muje.
Jerawa sukai suna tafiya ahankali har cikin wajen, bayansu kuma su ya Sulaiman ne suka take musu baya.
Tunda suka shiga wajen taron jikin Rahma yay sanyi, Dan ita irin mutanan ne masu tsoron shiga mutane, dandanan tafiyarta ta sauya, sai wani sassarfa takeyi.
Raf raf raf raf!! d'akin taron yad'auki tafi lokacinda Rahma ta hard'e taigaba kamar zata fad'i, da sauri Bobo yaruk'o hannunta yana fad'in ezeee madam.
Ajiyar zuciya tasauke danjin bata fad'iba, a u okey?, yafad'a yana kallonta. Kai tad'aga da sauri.
Tom kiyi ahankali plzz karki ji ciwo.
Ngd tafad'a tana kallon k'asa, to muk'arasa ya nuna mata hanya.
Ahankali suka taka zuwa inda aka tanar musu, sunbirge mutane gsky saidai mak'iyi, kowa fad'i yake sun dace da juna, Ammi saijin dad'i takeyi Dan harga ALLAH Rahma tashiga ranta.
Suna zama DJ yasaki wak'ar because, i luv u. Wannan wak'ar Bobo ce dayake bala'in so sosai, ya Hamza yabada wak'ar asaka Dan Bobo.
Aikuwa sai sakin lallausan murmushi yakeyi danjin dad'in wak'ar.
Masu hotuna kam sai aikinsu suke, itadai Rahma kanta yana k'asa tana shak'ar daddad'an k'amshin turaren Bobo.
Bayan wak'ar tak'are aka fara gudanar da abinda ya tara mutane.
Ammi tayi bayani da godiya ga d'unbin mutane dasuka halarci mother's Night d'in, sannan taima amarya da ango fatan alkairi.
Rahma taji dad'in bayanin ammi itada danginta, wannan kad'ai ya isa yanuna mata dangin mijin nata suna sonta.
Ankira amarya da ango filin rawa, shuru sukayi kamar bazasu tashiba, kowa da abinda yake kitsawa a zuciyarsa, saida mc yasakeyin magana sannan suka mik'e ahankali.
Afilin rawar suka tsaya k'ik'am babu mai motsi balle rawa, itakam Rahma dama bata rawa da dadai safan ce kam wannan gwanace.
Bobo yafiddo rafar kud'i yafara lik'ama Rahma idonsa k'yam akanta, itakam kanta na k'asa, Dan danan guri yad'au ihu da tafi, jiki a sanyaye Rahma itama tabud'e fos d'inta danufin d'akko 'yan wazo d'inta saitaga kud'i dayawa.
d'agowa tayi ta kalli bobo, shikuma yad'aga mata gira kuwa, da sauri tamaida kanta k'asa, yamatso da bakinsa wajen kunnenta cikin muryarsa mai taushi da laushinnan ya ce, "ko bakisone?.
Ajiyar zuciya ta sauke itama ahankali ta ce, " ngd sosai".
Hak'k'ine akaina aii yafad'a idomsa agefe kamar bashi yayi maganarba.
Batace komaiba itama tazaro kud'in tafara lik'a masa gashi yamata tsawo, amma ahaka taringa masa lik'i ihun mutane da tafi yak'aru, masu hotuna da video sai haskasu sukeyi.
Ammi ta taso itama ta rungume Rahma tana saka mata albarka, tafara lik'ama Rahma 'yan dubu dubu, (abin na manyane masu karatu), Bobo ma yakoma lik'ama Ammi sai murmushi yake saki itama Ammi haka, Rahma kam kanta ak'asa itama tana lik'ama ammi.
Su yaya sulaiman ma suka taso, dandanan gurin ya kaure da lik'i kamar ba'asan ciwon kud'iba, k'awayen ammi da danginta duk suntaka rawar gani, hakama dangin Rahma ba'a barsu abayaba, kai wannan taro ya k'yatar masha ALLAHU.
*_(can na hango Aunty bilyn Abdul tana lik'a 'yan naira 5🀣😜🀐, ba ruwana kartajini)._*
_karfa kuce nina fad'aπŸ€ΈπŸ»β€β™€_

Sai k'arfe 11:30pm taro yatashi lfy, kowa yafara k'ok'arin tafiya, Rahma duk barci yacika mata ido, cikin mota take zaune tana jiransu bobo sugama sallamar bak'i shida yayunsa, saida kuwa suka gama sannan suka shigo, yanzu kam wani d'an uwansu bobone zai maidasu ba ya Hamza ba, su ya Hamza matansu suka d'auka da yaransu sukayi gida.
Rahma ta kifa kanta kan cinya harta fara barci, kallonta kawai yayi baice komaiba, shifa koma sunanta bai saniba, bai tada itaba har sukaje gidan.
Yay shiru yana tunanin yanda zai tasheta.
Lukman ya kallesa Bobo kona baku gurine?, a'a malam wane kabamu guri gida zata shiga, ita barcima takeyi.
To ka tada ita dare na k'arayi shabiyu saura fa.
Daurewa yayi yad'an ta6a bayanta, ko motsi batayiba, yakuma d'an bubbugawa, firgigit ta tashi da addu'a abakinta, tad'an kallesa, shima idonsa na kanta, munzo yafad'a akasalane.
d'auke kanta tayi tabud'e motar, saida safe tafad'a cikin muryar barci, harta rufe motar Lukman ya ce, "haba malam aii ka rakatadai kasani kotanada magagin barci.
d'an tsaki bobo yayi shima yafito, harta fara tafiya yad'an hanzarta ya cimmata, dama ita kad'ai mai gadi yake jira Dan haka k'ofar abud'e take.
Dariya Lukman yashek'e da ita, sai Bobon Ammi yafad'a harda dukan sitiyari.
Har k'ofar falonsu yarakata, saida takama k'ofar zata bud'e sannan ta ce, " saida safe.
ALLAH yakaimu yafad'a yana juyawa.
Amota yasamu Lukman yashiga gaba suka wuce gida suma..........






_masoya I luv u._
[11/12, 2:17 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_


_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*

_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*


*_"dolene na gaisheku Nice Hausa novels, mungode sosai da k'auna, ALLAH yabar zuminci, Alkairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke."_*
Luv u ollβ›ΉπŸ»β€β™€.


2⃣1⃣&2⃣2⃣

Jiki a sanyaye Rahma tak'arasa cikin falon, tamaida k'ofar ahankali tarufe.
Ajiyar zuciya ummi dake zaune a fallo tana jiran dawowar Rahma ta sauke.
Dama ita take jira dantaga kowa yashigo amma banda Rahma.
"Lah ummi bakiyi barciba?, Rahma tafad'a a sanyaye. Mik'ewa ummi tayi tana murmushi, inani ina barci auta bata dawoba.
Murmushi Rahma tayi kanta ak'asa.
Ummi ta taso takama hannunta suka nufi d'aki, mutane duk sunyi barci, wasukuma suna gidansu ya Kamal.

Rahma tarage kayan jikinta sannan tazauna bakin gadon inda ummi take zaune itama da wasu tarkacen robobi agabanta.
Ummi miye wad'annan?, Rahma tafad'a tana d'aukar wata robar Zuma tana kallo.
Maganin basirne, kinga k'ar6i wannan takardar kiduba, d'azu malam saddiqu na islamiyyarku yakawo bayan fitarku.
Cikin mamaki Rahma takar6a tana bud'ewa, murmushi tayi tareda d'agowa tana kallon ummi da itama kallonta takeyi, ummi wai kinsan miye?.
A'a saikin fad'a.
Sak'one daga islamiyyarmu, wai gobe idan ALLAH yakaimu sun shiryamin walima k'arfe 9:00am to 12:00pm, dukda abin yazo babu shiri.
ALLAH sarki bayin ALLAH, ummi tafad'a cikeda jin dad'i, aiko mun gode musu da wannan karramawa.
Aiko dai, Rahma tafad'a.

Abubuwa ummi ta rink'a dannama Rahma a darennan, harsaida Rahma ta ce, " ALLAH ummi nak'oshi cikina zai fashe.
Dariya ummi tayi ta ce, "to barshi haka saida safe.
Daga nan wasu kayan gyaran jiki ummi ta murjema Rahma jiki dasu sannan suka kwanta.

*_BOBO._*
suna Isa gida yanufi d'akinsa, kayan jikinsa yafara ragewa, yana k'ok'arin zaro wayarsa a aljihu saiyaga ta Rahma, Kansa ya dafe O ALLAH, namanta ban bata wayartaba, zubesu yayi a durowar gefen gadon harda tasa, daganan yacire kayan jikinsa, bayi yashiga, bayan wasu 'yan mintuna yafito, badai wanka yayiba.
Shirin barci yayi ya kwanta, saidai barcin yak'i d'aukarsa, fuskar Rahmace take MASA gizo, k'yawawan idanunnan NATA yake hangowa, yasaki wani lallausan murmushi Wanda bansan na miyeba, saikuma yaja siririn tsaki yana gyara kwanciya.
Nima waje nayo nabarsa.

*_Washe gari_*
Tunda sassafe Rahma ta tashi tai wanka kasancewar tana fashin sallah, Basama tafara yarfa mata k'unshi, masha ALLAHU nafad'a Dan k'unshin yana bada ma'ana.
Jikin Rahma duk yayi sanyi, ta tabbata yau babu fashi saita bar gidansu, cikin dabara take share hawayenta dankar Basma tagani dansukad'aine a d'akin.
Zuwa 8:00am angama k'unshin, yayi k'yau sosai, 8:30am akasa Rahma yayi wanka agurguje dantafiya walimar makarantarsu.
Shiri tayi cikin zani da riga na atanfa pink, ta d'ora bak'ar alk'yabba mai shara shara wadda amaren zamani ke yayi, tayi k'yau sosai dukda yau babu kwalliya afuskarta, dak'yarma tayarda Basma tasaka mata pink d'in janbaki Wanda shiga da kwalliyar alk'yabbar.

Wajen walimar yayi k'yau sosai, acikin harabar islamiyyar za'ayi, malaman sunyi k'ok'ari gsky dukda abin yazo babu shiri.
Wajen da'aka tanada na musamman dan d'alibai su Rahma suka zauna, iyayen yara dayawa sun halarci wajen, su Abba ma duk sunje, su ya kamal ya muneer ya shaheed, da sauran matasan anguwar da iyayensu, dan Rahma mutuniyar kirkice, tsakaninta da kowa a anguwar sai girmamawa, batada hayaniya wannan yasa takasance mai jama'a kowa yana sonta.
Gurin yayi tsit ana addu'a, shigowar wasu motoci hud'u yaja hankalin mutane kowa soyake yaga suwaye?.
Appa yafara fitowa shida wasu dattijai uku, da alama abokansane, mota ta biyu kuwa matasan family nasune, ta ukuma haka harda ya ishaq da wasu zasukai sa'anninsa, motar k'arshe kuwa, ya Hamza da sulaiman, Lukman da tauheed ne, sai Bobo Wanda yakashe kala cikin manyan kaya, purple d'in shaddace mai haske ajikinsa, rigar iya guywa d'inkin zamani, yayi k'yau sosai harda d'ora bak'ar hula.
Wow! Wasu 'yammata dake gefen Rahma suka fad'a, d'aya tace kai Ruma guy d'incan ya had'u wlhy, dama ya ce, "yana sona?.
Rahma tad'ago dantaga wanene wai suketa kurantawa haka?, gabantane ya fad'i tayi saurin kauda kanta.
Abbane yataso shida abokansa da shuwagabannin makarantar suka tarbi su Appa.
Masauki maik'yau aka basu kamar ansan da zuwansu.
Bayan gaishe2 akaima bak'i barka da zuwa.
Itadai Rahma tunda tamusu kallo d'aya bata sakeba.

Dukda da daddare yaganta hakan bai hanashi ganetaba, babu laifi yarinyar tanada k'yau da nutsuwa, bobo yafad'a azuciyarsa.
Mayun idanunsa yadasa mata batareda ya saniba.
Rahma datakejinta atakure, jikinta yana bata kallonta akeyi, tana d'agowa sukaima juna kallon ido cikin ido, Dan suna fuskantar junane.
Da sauri

Please Login or Register in order to submit comment