Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi ya ce, "munzo shigowa naga fitarsa Ashe na shaida motocin nasa kuwa.
Baki bobo yata6e batareda yayi maganaba.
Saican yace halan yauma kazo kacikamin bakin office da yaranka?.
Hhhhhhh kaima Kasan dolene Dan babu yanda za'ayi subarni nafito ni kad'ai.
Bobo Yakuma ta6e baki, Sakai awahala kenan, haka kawai ace duk Inda mutum zayi ana binsa tamkar wata jela?.
Girman kenan my guy Ammar yafad'a yana dariya.
Ammar ya ce, "mutumina kafa rame wlhy mike damunka?.
Bobo yafitar da huci mai zafi, babu komai Ammar.
To shikenan tunda babu komai yafad'a yana mik'ewa.
Da sauri Bobo yaruk'oshi Dan yasan haushi yaji, yi hak'uri abokina zauna muyi magana.
Ammar yadawo yazauna, wlhy Abdulmaleek kana bani mamaki yanda kake iya 6oyrmin wasu al'amura naka awasu lokutan.
Bobo ya ce, " kayi hak'uri Ammar bawai ina 6oye maka wani Abu baneba, saidai ina ganin wannan sirrin gidanane, dukda nasan babu abunda zan iya 6oye maka arayuwata, kai kad'aine abokina Dana yarda dashi, nasan kaima hakane.
Hakane Bobo amma Dan ALLAH miyasa kake 6oyemin abinda ke damunka?, ina kula dakai tunda nadawo kana cikin damuwar datafi tada akan Rasuwar marigayiya Ni'ima.
Sabodafa damuwar dakake ciki su Appa suka yanke shawarar yimaka Aure, to amma maimakon asamu sauk'i sai kuma damuwarka ta k'aru.
Minene damuwarka Abdulmaleek?, kasanar dani mu nemo mafita.
Bobo yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yadafe tebir d'in gabansa da hannu bibbiyu.
Wato Ammar da ina cikin kewar matatane Dana rasa, dakuma tausayin Nawal na rashin uwa, wannan yasa nak'iyin aure dukda dama Kasan matan bawai suna agabana bane, su Appa sun takura nayi aure harda kai aciki, amma na ce, "muku har yanzu ban shiryaba, an auramin Rahmane saboda bijirewar yayarta akan aurena.
Tundaga randa aka kawo yarinyar gidana ban k'ara yarda ta ganniba saida na d'akko Nawal..
" amma kasan wani abin mamaki?."
Ammar ya girgiza kai.
Koda muka shigo gidan saitamana tarba ta mutunci, ko kad'an bata nuna fushinta akan rashin zuwana garetaba.
Wannan itace jarabawa ta farko data cinye, saikuma yanda take kula da Nawal, wlhy idan baka saniba bazakace ba ita ta haifetaba, abu na uku tsafta, iya girki, saidai akwai shegen muskilanci atareda yarinyar wlhy.

Ammar ya tuntsure da dariya, to aii indai miskilancine babu matsala tunda kaima halinkane.
Harara Bobo ya galla masa malam aii wannan ta fini.
Bobo acigaba da bandamuba kafin ayi auren, amma yanzu ganinta agidan saina shiga wani hali, Dan gsky ina buk'atar mace.
Ammar yagyara zama, to aii ni banga abin damuwa ananba, ba matarka bace?, kawai kanemeta mana.
Ammar baka fahimceni bane, haryanzufa yarinyar k'aramar yarinyace, bata wuce 17 ba, banafa ta kammala secondary, kosu khursiyya sun girmeta da shekara d'aya.
Murmushi Ammar yayi, karka damu abokina aii yaranma sunfi bada Nutsuwa ka gwada kagani kuma.
Amma Dan ALLAH karagema kanka damuwa.
To aiini bakasan wani abuba, tayayama zan tunkareta na nuna mata ga abinda nakeso?, kasanfa banason raini wlhy.
Dariya Ammar yayi ya ce, "Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak'i, wlhy AAA kana bani dariya, lokuta da dama nakan rasa kai wane irin mutumne?, wlhy da aikin Soja ka dace ba lauyaba, kaifa wani irin murd'ad'd'en mutumne, towai sanda kake gwadama Margayiya Ni'ima soyayaya kirana kayi na koya makane?.
Ajiyar zuciya Bobo ya sauke, bazaka ganebane kawai kadai.
To ganar dani cewar Ammar yana kallon Bobo.
Komawa yayi yalafe jikin kujerar yanad'a lilata ahankali, Ammar ya ce, " my guy kafito kawai anamijinka kaji, kakula da matarka na tabbata Rahma Alherice arayuwarka, kaga kuwa yanda ka canja kak'ara fari, so ka kwantar da hankalinka kayi k'ibama, Rahma k'yak'yk'yawar yarinyace nitsatstsiya ga ilimin addini, wlhy randa na kalli vedio d'in bikinku jinayi inama ina wajen, bak'aramin birgeni tayiba awajen walimarnan.
d'an iska awajen biki kanata tattalin yarinya amma yanzu kazo kana mata muzurai.
Murmushi bobo yayi ya ce, ''kankadai akeji.
Kaima za'aji nakane, amma saikaje hanun Rahma, mik'ewa yayi yana dariya kaga bara nawuce sumayya nacan na jirana harkaja na wuce lokaci.
Bobo daketa murmushi tun d'azun ya harareshi iskanci zakamin kenan?..
A'a babu wani iskanci gsky dai.
Bobo ma ya mik'ewa yayi, nima tafiyar zanyi zanje na d'auki Nawal a school, yau direbanta babu lafiya.
Ayya ALLAH yabashi lfy.
Amin.

Tare suka fito, kowa yashiga motarsa, Ammar da tawagan 'yan sandansa suka tafi, shima Bobo yanufi school d'in su Nawal ya d'auketa sai gida.


.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Sun shigo gidan falo babu kowa, sai k'amshi da k'arar AC ke tashi, saikuma TV dake kunne amma babu k'ara sosai.
Nawal ta ce, "papa momy na d'aki zomuje, tarik'e masa hannu.
Rahma tana tsaye jikin wardrobe tana d'aukar kaya suka shigo, batayi zaton taredashi sukeba, Cikin farin ciki tad'auki Nawal tana juyi da ita suna dariya, babyn papa da momy ya School.
Momyn lfy.
Masha ALLAH my lovely daughter, muje namiki wanka to kiji dad'i.
"K indai kina tareda Nawal baki ganin kowa sai ita?.
Da sauri ta kalli gurin da maganar take fita, Dan batayi tunanin suna tareba.
Kayi hak'uri basan tare kukeba aii sannu dazuwa, sai matse jikinta takeyi Dan daga ita sai tawul.
Baice komaiba yajuya yafita, amma ya rikice daganin surar Rahma, dukda k'aramar yarinyace amma tanada sura mai k'yawun gani, yanaso yak'ara ganin ainahin Rahma d'in.
Da wannan tunanin yak'arasa d'akinsa, kaya yacire yashiga wanka.


β˜…β˜…β˜…
Bayan wasu 'yan lokuta kowa ya kammala abinda yakeyi, suka had'u afalo sukaci abinci, itadai Rahma kanta ak'asa.
Yakula tunranda yay mata abinnan bata sakewa dashi, kuma bataso su had'a ido, tak'ara birgeshi da samun matsayi a zuciyarsa Dan yana k'aunar mace mai kunya

_(kunya tana d'aya daga cikin tarbiyya ga mace, amma 'yammatanmu na yanzu sun 6arar, aganinsu rashin kunya itace wayewa, gsky anama wayewa bahaguwar fahimta, yakamata mugyara, kunya tana d'aya daga cikin alamomin imanima wlhy, ALLAH yasa mugane.)_

Duk suna falo zaune, Rahma da Nawal suna game da aka had'a da TV, shikam boss yana karanta jarida.

Safna tayi hon maigadi yalek'a danyaga wanene, ganin bak'uwar motace yasa yaytsaye batarda ya bud'eba, cikin haushi Safna talek'o tana masa magana cikeda masifa, aii babu shiri yabud'e mata gate d'in tashiga, guri tasamu tai farking sannan tafito, sai harar mai gadin takeyi, sanye take cikin jan less Riga da siiket sun kamata sosai amma sunyi mata k'yau, ta d'ora siririn farin gyalenta a kafad'a, takalmi da handbag d'inta duk farare, tad'auki sak'on Rahma tanufi k'ofar datake zaton itace zata sadaka da gidan.
Sallama tayi tareda kwankwasa kofar.
Rahma tamik'e da sauri lah kamar muryar aunty Safna nakeji.
Da sauri Bobo yad'ago kai yana kallonta danjin ta ambaci Safna.
K'ofa Rahma tanufa, shikuma ya ta6e baki yaudai zaiga yarinyar datace bata sonsa...........



πŸ’ƒπŸ» _ayye mata kuk'ame k'am sabuwar rawa, nidai bansan maganarba, bansan zafin ata6anba, nidai nace Ku k'ame k'am kusami natsuwa_πŸ€£πŸ€”???????…


πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚πŸ€ΎπŸΏβ€β™€goooooooooπŸ˜‚πŸ˜œ






*_luv u oll my fan's_*
*_(((S))).........2017_*
[11/12, 2:55 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_β€’{BoBo}β€’_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


4⃣5⃣

Rahma tarungume Safna cikeda farinciki, itama rungumeta tayi Dan tayi kewar 'Yar k'anwarta abokiyar fad'anta, I miss you my lovely aunty.
Miss u too my lili na.
Safna tad'agota daga jikinta tana fad'in 'Yar lukutar ummi kinfa k'ara lukucewa, mi angon naki yake baki haka?.
Rahma tarufe fuskarta saboda jin kunya, kai aunty Dan ALLAH ki bari.
To na bari Safna tafad'a tana kama hannunta sukai cikin falon.
Rahma ta kalli mazaunin Bobo wayam, Nawal ta kalla data maida hankalin akan game, baby ina papa?.
Nawal tad'ago tana dariya, yashiga d'akinsa momy..... Tsayawa tayi tana kallon Safna, saikuma ta kalli Rahma, momy wacece wannan?.
Aunty ce babyna.
Nawal ta taso ta rungume Safna, oyoyo aunty na.
Itama safna rungumeta tayi tana fad'in oyoyo babyn mom.
Bayan sun zauna Safna sai bin Nawal da kallo takeyi, gani take kamar tasan yarinyar.
Rahma tadire tiren kayan motsa baki agaban safna, tana fad'in wlhy aunty banyi zaton ganinkibafa.
'Yar dariya safna tayi ta ce, ''saikuma gani kin ganni.
Zama tayi sukafara hira, kamar basu bane sukeshan fad'a ada.
Sun shagala sosai akan firar idon Safna ya sauka akan hoton Bobo, wani k'ululu cikinta yabada, batagama dawowa daidaiba Bobo yafito daga d'akinsa.
Ah bak'uwa mukayi agidan??.

Afirgice safna tad'ago tana kallonsa, fad'uwar gaba, bugun zuciya, murd'awar ciki, duk suka k'ara samunta alokaci guda, yanda take raba ido akan Bobo sai kawai ya d'aure fuska.
Itama Rahma kallonta takeyi ita atunaninta Safna taji kunyane akan abinda ta aikata abaya.
Safna taduk'e k'anta bisa cinyarta danjin falon yana juya mata, jikinta sai rawa yakeyi, lallai ta tabbata kuka rahamane tunda gashi ita yau takasayinsa.
Bobo yana zaune saman kujera yad'ora k'afa d'aya kan d'aya, dagashi har Rahma idanunsu nakan Safna, Nawal ma tana mak'ale abayan Rahma tana lek'en Safna, bobo yakalli Rahma, dama tanada wani ciwone?.
Kai Rahma ta girgiza masa ta CE, ''amma dai ban saniba ko bayan nabar gidan.
Lumshe idanunsa yayi ya ce, "bata ruwa tasha, Rahma ta tsiyayama Safna ruwa a Kofi tabata, jikin Safna na Rawa takar6a ta shanye duka tamik'ama Rahma kofin, k'ara mata bobo yasake fad'a.
K'ara mata takumayi, aii ko ta shanyeshi tas.
Rahma takalli Safna kamar zatayi kuka, aunty ki kwanta kihuta, kiringa fad'in _innalillahi wa'inna ilaihirraji'un_ zaki samu nutsuwa insha ALLAHU.
BABU musu Safna tabi shawarar Rahma ta kwanta, dukda ayanzu jitake babu Wanda tatsana aduniya sama da Rahma d'in, jitake tamkar tatashi ta shak'eta ta mutu, talumshe idanu tana ambatar innalillahi..... Danjin zuciyarta tana shirin fashewa.

Bobo dai tuni yad'auke kai daga kallon Safna, ya maida hankalinsa ga TV.
Bayan kamar minti15 Safna tad'anji Nutsuwa tazo mata, tabud'e ido tareda tashi.
Rahma tai saurin fad'in aunty Yaya jikin?.
Murmushi Safna tayi Wanda yafi kuka ciwo, da sauk'i kuyi hak'uri na rud'aku, juwace nakeji dama tun ina hanya.
Sannu Rahma tashiga jero mata, Dan ita tayarda da zancen na Safna 100%.
Bobo kam azuciyarsa ya ce, " juwar kuma bata tashiba saida kika ganni?, shifa Sam bai yarda da maganartaba, Dan haka yacigaba da kallonsa batareda yak'ara kallon ko inda sukeba.
Safna kam tafad'i hakane saboda tunowa da maganar malaminta, dayace kota had'uda bobo karta nuna masa komai harsaitaje wajensa yabata wani sirri, da wannan tunanin tad'anji sanyi aranta, shiyyasa ta tashi ta zabga wannan k'aryar.
Takai kallonta ga bobo daya maida hankali kan latsa wayarsa, muryarta na rawa ta ce, "ina yini.
Lfy, kawai ya ce, " yamaida Kansa ga waya.

Falon yay shiru nawasu 'yan mintuna, safna dai satar kallon Bobo takeyi, sai yanzu yak'ara tabbatarwa da k'yak'yk'yawane ajin farko, Ashe ranar kallon tsoro sukayi masa, lallai ALLAH yayi halitta awajennan masha ALLAH, sai sambatun k'yawun bobo takeyi ita kad'ai zuciyarta.
Rahma kam tayi shiru tana tunanin halin da safna tashiga yanzun nan, kome ke damun 'Yar uwar tata?.
Bobo yamik'e Dan ganin kallon k'urillar da safna take masa, yakalli Rahma bara nad'an kwanta kafin sallar la'asar, kitadani idan lokaci yayi.
To. Rahman tafad'a kanta ak'asa.
Shikuma yanufi d'akinsa, harya shige safna tanabinsa da kallo.

Nawal ma tamik'e momy zanje wajen papa.
A'a Nawal kibar papa ya huta kinga ya ce, "barci zaiyi, Nawal ta kwa6e fuska tana shirin yin kuka, momy nimafa barcin zanyi.
Tokije d'akinmu ki kwanta, kamar gsk tanufi d'akin Rahma, dataga basa kallonta saita gudu d'akira, papan ta.
Safna ta ce, " wannan yarinyarfa ina kuma samota?.
d'an murmushi Rahma tayi, aunty yarinyarsa ce wadda matarsa tarasu tabari.
Baki safna ta ta6e shine kekuma aka jajibo aka kawomiki?, kedai sakaraice wlhy, kina 'Yar yarinyarki har anfara kiranki da suna momy mtsoooow, nibansan randa kanji zai wayeba wlhy, danice agidannan wlhy saidai yasan Inda zaikai 'yarsa.
Itadai Rahma batace komaiba, saima wasa da zoben hannunta datakeyi, amma har zuciyarta bataji dad'in maganar 'Yar uwartaba, aganinta aii d'a na kowane, kuma shida gidansa tahanashi ajiye Wanda yakeso?, itafa har zuciyarta tana k'aunar Nawal, kuma yanda zata rik'e 'ya'yan cikinta haka zata rik'e Nawal.

Yana zaune abakin gado yana danna laptop Nawal tashigo.
Lah papa bakayi barciba?.
Bobo yad'ago yana kallon d'iyar tasa, banyi barciba babyna ya akayi?.
Na cema momy zanzo wajenka, shine ta ce, " a'a wai nabarka kagaji zakayi barci naje d'akinmmu na kwanta.
To miyasa bakije kin kwantaba?.
Ai bata ganniba nikuma na gudo nan, ammafa karka gaya mata.
Murmushi yayi Dan ganin yanda Nawal tazaro idanu saikace wata babba, to shikenan bazan fad'aba yanzu ya za'ayi?.
Ta ce, "papa barci zanyi.
To zoki kwanta, kan gadon tahawo ta kwanta, kwantar da kanta tayi kan k'afarsa daya tankwanshe, tana kallon rubutun dayakeyi a laptop suna labari, dahaka barci ya d'auketa, yagyara mata kwanciya dankar wuyanta yay sanyi.

Afalo kam safna da Rahma suna hira, dukda safna dauriya kawai takeyi, Dan zuciyarta na cikeda tsanar Rahma, dakuma haushin tashin bobo Afalon, Dan bata gaji da ganinsaba.
Tamik'a mata sak'on ummi gashi inji ummi.
Rahma takar6a ta na dubawa, miye kuma ummina tabani?, safna ta ta6e Baki ta ce, " zata kiraki tamiki bayani, kinga bari nawuce, safna tafad'a tana mik'ewa.
Kai auntuna tun yanzu?, Rahma tai maganar tamkar zatayi kuka.
Kenifa banason iyayi, dama kika samu Nazo shine zakimin Ta6ara.
Sanin halinta yasa Rahma tai saurin fad'in yi hak'uri aunty Safna wlhy nayi kewarkune sosai. Dan ALLAH yaushe zaki dawo?.
Kallonta kawai safna takeyi, zuciyarta na raya mata yarinya karkiyi farincikin sake zuwana, Dan waywayowata gidannan ba alkairi bane ba agarekj, bazan ta6a barmiki bobo ba, abayama kuskurene da rashin sani, amma ayanzu kam sai Inda k'arfina ya k'are, bobo nawane nikad'ai.....
...
Ta6ata Rahma tayi aunty mikike tunani haka?.
Ajiyar zuciya Safna ta sauke, ta k'ak'aro murmushi, karki damu zandawo kwannann.
Cikeda farinciki Rahma tarungume safna.
Kayan kwalliya ta had'a mata hadda wasu k'ananun kaya masu k'yau da aka saka mata alefe, safna takar6a ko godiya babu ta tafi.
Har bakin mota tarakata, saida taga fitarta sannan tadawo ciki.
Batanemi su Bobo ba tahau gyaran gidan, da shirin girkin dare.

Safna kam tana fita saitaji hawaye sunabin kumatunta, abinda takesonyi tun d'azu amma sukak'i zuwa, gangarawa tayi gefen titi tasamu guri tai farking, kifa kanta tayi a sitiyari tanata rabzar kuka tamkar ranta zai fita, sai surutai takeyi kamar Sabuwar kamu.
Wlhy Rahma bazan barmiki Shiba, wlhy saidai idan ki mutu na mallakesa, kota halin k'ak'a saina rabaki dashi, idan ban samesaba mutuwa zanyi, Rahma miyasa zakimin haka ki auri abinda nafiso fiyeda komai arayuwata?, wlhy saikin barmin bobona, saikin barmin.....tasaki wani wahalallen kuka.

(Ni bilynku na ce, "kaga wani salo, Safna kinyi sake Rahma ta dafe.)

Cikin matsanancin kuka Safna ta kira basira ta zayyane mata komai, ita kanta tarazana sosai danjin labarin, safna ta ce, "baseera miye mafita?, kibani shawara, wlhy kwakwalwata na gab da tarwatsewa nashiga uku baseera namutu.
Kinga safna ki kwantar da hankalinki, gobe idan ALLAH yakaimu zamu koma wajen malam.
Baseera muje yanzu please.
A'a kiyi hak'urin goben, wlhy yau Abbana yana gida, kuma yasan banida lectures d'in yamma, baza'a barni na fitoba, kiyi hak'irin giben saimuje da sassafe.
Shikenan safna tafad'a jiki a sanyaye.
Motar taja tanufi gidan, Dan kukan datayi yad'an rage mata wani abun.
......
Rahma tagama komai tak'ara saka turaren wuta, jin kwala kiran sallar la'asar yasata nufar d'akin bobo danta tadashi, kwankwasa k'ofar tayi dukda tasan yana barci, bata jira amsaba tashiga da sallama.
Hakan tayi dai dai dafitowar bobo daga wanka, yana d'aure da fad'in tawul ita k'ugu zuwa guywa, hannunsa rik'e da k'arami ya ratayo a wuyansa.
Da sauri Rahma tajuya zata fita tana fad'in ashema ka tashi.
Eh natashi, ina zaki? Kizo kid'auki yarinyarki gatanan tamin barci ad'aki.
Rahma tajuyo kanta ak'asa, Ashe nan tazo?, nazata tana d'akina?.
A'a tana nan dama ta ce, "karna gaya miki gudowa tayi.
Murmushi kawai Rahma tayi tad'auki Nawal tafice abinta.
d'an murmushi yayi danganin yanda take Sinne kai da had'e hanya, yasan danta gansa babu kayane.

Tana falo yafito sanye cikin blue d'in wando da jar Riga, yayi k'yau sosai, Dan dama bobo akwai gayu gakuma tsafta, uwa uba k'yawun haiba.
Yad'an kalli Rahma, bara naje masallaci, daga nan zan wuce gidansu Ammi.
To ALLAH yatsare. Saika dawo.
Amin yafad'a akan la66ansa, yafita yanamaijin dad'in addu'arta gareshi.
Rahma tayi shiru tana mamakin yanda bobo kan sakata cikin al'amuransa ayanzu, komiye dalilin hakan?.


.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Safna tadanna uban hon, babu shiri baba mai gadi yabud'e mata gate, aguje tashiga gidan, tai farking, handbag d'inta kawai tad'auka tayi cikin gida, anan tabar kayan da Rahma ta bata, ALLAH yasota ma ummi na d'aki babu kowa afalon.
Ta fad'a saman gadonta tana kuka, wlhy saina raba wannan auren, Dan bobo nawane nikad'ai, bazan ta6a zuba ido ina kallonsa amatsayin mijin k'anwataba, saina mallakesa kota halin k'ak'a, konawa zan kashe kuma koyaya iyayenmu zasu d'auki lamarin itadai saita mallaki bobo.
Haka taita kuka har aka kira magriba, dama batayi sallar la'asarba, kuma da alama magribar ma babu niyya.
Ummi takalli agogo waini ina safna tamak'alene har yanzu shiru?.
Talatu mai aiki ta ce, "Hajiya aita dawo tun d'azu.
Kai talatu da gsk?.
Wlhy kuwa Hajiya.
Hankalin ummi ya kwanta takoma d'aki dama ko lazimi bata kammalaba tafito.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Bobo kam koda yay sallar la'asar saiya nufi gidansu, bayan sun gaisa da maigadi yashige ciki.
Yakashe motar yafito, cikin kasaitarsa yanufi cikin gidan, afalo yatarar da khursiyya da khairiyya suna kokawa akan gyale.
Tsaki yayi yana daka musu tsawa, kai dallah miye haka?.
Da sauri suka nutsu.
Ya ce, " Ku wad'anne irin shashashune?, kun kirma amma kunacin k'asa.
Yaya gyalenefa na ajiye zansaka gobe idan zamuje gidanka, shine ta d'auka wai zata fitadashi yanzu......
Karya take Yaya...
Katsesu yayi suduka, kumun shiru dallah, hannu yamik'a yakar6i gyalen, batareda yak'ara tankasuba ya haye saman Appa.
Saida yaje k'arshen benen sannan yajuyo ya ce, "idan kun gadama kucigaba da fad'an harna sakko, yay shige warsa.

Khursiyya ta tura baki baba, hankalinki ya kwanta ya kwace duka, tobake kika jaba cewar khairiyya.
Kardai Ku fasa, kuyi tayi harya dawo kune zakuci dukan banza tunda kunsan halinsa sarai, Ammi ce mai maganar tana fitowa daga kicin, Ashe duk abinda sukeyi tana jinsu.
d'akinsu suka koma, kowa tana zum6ura baki gaba, Ammi ta girgiza kai tana nufar saman Appa itama............




*_tofa masu karatu yanzu aka fara, matsaloli sunyi yawa, Alh sunusi yana nan daburin koyama bobo hankali, koya zata kasance?._*
_Safna taci burin mallakar bobo, ko zatayi nasara?._
_Bobo da Rahma, koya zata kasancene?, shin zasu fara soyayyane?, koko Safna zata Shiga tsakaninsu?, kozaibi sha warar Ammar ne kafin safna tayi wani abu?._

To mucigaba dabin labarin *_Abdulmaleek bobo_* muji yazata kaya ga wannan cakwakiya, waye keda nasara acikin mutanennan 4?.
Bobo, Rahma, Safna, Alh sunusi.
~Karmu gajiya masu karatu yanzu aka fara game d'in saidai bamusan wazaiyi winning ba acikin mutanennen 4.~

*_acigaba da gashi!!!!!πŸ‘ŒπŸΌ_*









Luv u oll my fan's
*_(((S))).......2017_*
[11/12, 2:55 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_β€’{BoBo}β€’_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*


4⃣6⃣

Appa yatashi zaune yana murmushi, oyoyo babana nida Ammi.
Shima bobo dariyar yakeyi, yaje dafda Appa yazauna tamkar zai shige jikinsa.
Appa yamik'a masa hannu su gaisa, amma saiya nok'e ya ce, "ina yini Appa.
Dariya Appa yasakeyi, mukarram bakaso musamu ladan musabahane?, mirmushi yayi batareda yace komaiba, Appa yakamo hannun bobo yahad'e danasa yana fad'in ya iyalin?.
Suna nan lfy Appanmu, sunama gaisheku.
Muna amsawa. yau baka je aiki bane?.
Naje Appa, amma nataso dawurine saboda d'akko Nawal a school.
Ok, to ina direbanta?.
Wai bayajin dad'in jikinsa, shine nacemasa yahuta kawai.
ALLAH yabashi lafiya to.
Amin.
Assalamu alaikum.
Wa'alaikisslam. Appa da bobo suka amsawa ammi sallamarta, bobo yamik'e da sauri yakar6i kayan hannun ammi, kai Amminmu da kanki?, miye amfanin wad'ancan yaran?.
Dariya tayi tazauna, to mukarram inbanyiba wazaiyi?, hidimar mijinace fa.
Murmushi bobo yayi, shiyyasa kullum yakeson Amminsa haryau baiga macen datakai amminsu iya tattalin mijiba, gashidai sun tsufa amma har yanzu suna tattalin junansu tamkar yara.......
Ammi tak'atsema bobo tunani da fad'in mukarram ga abinci.
Firgigit yadawo da kallonsa Kansu, Ammi mikikace?.
Tunanin mi kakeyine?.
Bai 6oye musuba yafad'a musu abinda yake tunani, Dan akwai fahimtar juna da shak'uwa tsakaninsu da iyayensu.
Daga Ammi har Appa dariya sukayi danjin firicin bobo, ammi ta ce, "toga abinci azuba?.
A'a ammi nima matana tacikamin ciki da girkinta mai dad'i.
hhhhhh d'an bantan uba, ashedai gaskiyar Hamza dayace kanason matarka, babanafa akwai iya taku.
Dariya sosai bobo da Ammi sukeyi danjin zancen Appa, appa ya ce, " naji dad'i sosai wlhy, ALLAH yak'ara Baku zaman lfy da zuri'a tagari.
Kansa ak'asa ya ce, "amin."
Hira sukacigaba dayi, Appa yanacin abinci, bayan ya kammala ya ce, "mukarram!.”
Yanda Appa yakira sunan nasa yasan tabbas maganar muhimmiyace, shima cikeda girmamawa da nutsuwa ya ce, " na'am Appa.
Appa yagyara zamansa, yanamai tsurama bobo ido, mukarram mike tsakaninka da Alh sunusi Dala?.
Ajiyar zuciya bobo yasauke, cikin nutsuwa yayma Appa bayanin tun farkon tsintar muheebat dakuma abinda yake faruwa a yanzun.
Appa ya girgiza kai alamar gamsuwa, ya ce, "ina alfahari daku sosai 'ya'yana, ngd ma ALLAH dayayiku masu hankali dasanin darajar d'an Adam, lallai kaburgeni sosai babana, kuma Nagoya maka baya d'ari bisa d'ari ka kwatoma yarinyar hak'k'inta, β€œI'm proud of you my dear son”.
ALLAH yatsare minku aduk inda kuka tsinci kanku.
Amin Appa mungodema ALLAH dasamunku amatsayin iyaye nagari, bamuda abin biyanku saidai muyita binku da addu'a har k'arshen numfashinmu.
Ammi dai sai murmushin jin dad'i takeyi.
Appa yacigaba da fad'in dama abinda yasa kaji namaka maganar yaune Alhaji Sadiq

Please Login or Register in order to submit comment