Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sukeso bazai hanasuba, Dan Andad'e ba ayi wani shagaliba agidan.
Har k'arfe tara suna gidan, saida Appa yace yakamata sutafi gida hakanan wajen iyalinsu sanan suka mik'e kowa yanufi gidansa.
Bobo bayan yarakasu harabar gidan yanufi d'akinsa jikin a sanyaye, yama rasa wane irin tunani zaiyi shikam.............



_Tofa masu karatu, Yaya kenan?, shin ina Safna?, gafa gwaninta zai angwance, kowacece amaryar Bobo?, ya wannan zama zai kasance?, kudai biyoni kawai, basirar aunty bilyn Abdul ce, nikam copy nakemuku masoya._


*_hummm wasa farin girki, masoya yanzufa aka fara, kumuje zuwa wai mahaukaci yasai kura, yanzu muka dasa alk'alamin labarin Bobo!._*





*_masoya muna godiya ALLAH yanar zuminci._*
[11/12, 2:15 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_


_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*

_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*



1⃣3⃣&1⃣4⃣

*_Gidansu Safna_*
Safna na kwance akan gado tana chart, sai faman murmushi takeyi, da alama tana jin dad'in charting d'in.
Rahma dake zaune akan sallaya tana karatun alkur'ani ta waigo ta kalli safna dataketa 6a66aga dariya harda rik'e ciki, kai Rahma ta girgiza tareda fad'in ALLAH ya shirya azuciyarta.
Kanta tamaida tacigaba da karatunta.
Safna kam bamatasan tanayiba, dariyarta taketayi cikin farinciki, hira takeyi da Baseera akan nemomata Bobo, Baseera tana gayamata akwai wani guy a unguwarsu sunansa *boy shiyakama subama aikin, Dan tasan cikin sauk'i zai samomusu bobo da labarinsa.
Tak'ara wani d'an ihun farinciki, tareda fad'in saini mata agidan Bobo.
Rahma takuma kallonta cike da mamaki, ganin bazata barta tayi karatunta cikin Nutsuwaba yasa tarufe alkur'anin tayi addu'oin ta tamik'e ta ajiye alkur'ani ama'ajiyarsa.
Hijjabinta tacire tana fad'in aunty Safna kofa sallar magriba bakiyiba har anyi isha'i amma kina kwance kina charting akan abinda k'ilama bazai amfaneki da komaiba.
ALLAHU Akbar maikaratu nagaba, Safna tafa idonta akan waya, tacigaba da fad'in malama Rahma jawo wata ayar na haddace wannan.
Ajiyar zuciya Rahma ta sauke, ta ce, "Niba malamarki bace, kuma ba wa'azi nake mikiba, ina tunatar dakene dannaga kin shagala.
Wani wawan dundu safna tasaukema Rahma abaya, Dan ubanki idan aljanna takice ki hanani, shegiya 'Yar iska uwar tsari, kenikam daba agabana ummi ta haifekiba wlhy danace anmata canji a asibiti, anya kuwa acikin 'yan barka wata bata sace ainahin d'iyar da ummi ta haifaba ta ajiye mata ke?.
Rahma tashare hawayenta ta ce, " kije kitanbayeta k'iladai kece aka canja mata, Dan halinki daban dana mutanen gidanna.
Afusace Safna taduro daga gado tana d'urama Rahma zagi.
Tuni Rahma tafice tabar mata d'akin.
Afalo taci karo da abbansu yadawo masallaci, sannu da dawowa Abba. Yauwa d'iyar albarka ina zuwa haka?.
Ba inda zani Abba, nadai fito falone nasha iska.
Masha ALLAHU, ina 'Yar uwar taki to?.
Tana d'aki Abba.
Yauwa jeki kiramin ita zamuyi magana, ina umminku?.
Ganinan Abba Shaheed ummi dake fitowa daga d'aki tafad'a.
Tamai sannu dazuwa sannan tafara shirya musu abinci.

Rahma tatsaya abakin k'ofa ta ce, "aunty Safna kizo Abba yana kiranki.
Shegiya munafuka gulmata kina kaimasane?.
Niba munafuka bace, yace dai kizo..., tana gama fad'a tafice.
Safna tasakko daga gadon tana mita, zan koya miki hankaline 'Yar banza maikan dankali.
(Araina nace kekuma maikan doya ko?.)

Kusada Abba taje tazauna, Abba gani.
Kanta yashafa yana murmushi haba safnan Abba miya faru kika k'unshe kanki a d'aki?.
Zamanta ta gyara tana ballama Rahma harara, babu komai Abba nayi sallane INA zaune ina Azkar.
Da k'yau 'Yar albarka.
Rahma kam ido tazaro waje danjin k'aryar da safna ta gilla, saikuma ta k'unshe baki tana dariya.
Safna na kallonta, Dan haka haushi yak'ara kamata.

_(Hattara iyaye kuringa kula da addinin 'ya'yanku, akwai yara dayawa masu wasa da salla irinsu Safna, wata zakiga tana zaune tana chart za'a kira salla, amma ko'a kwalar rigarta, har Matan aurema akwai masu halinnan, musamman yanzu da karatun Novels sukayi tasiri arayuwarmu, yakamata duk lokacin da aka Shiga sallah kiringa lek'a d'akin yaranki kitabbatar suma suyi, ALLAH yasa Mugane)._

Ummi ta ce, "kutaso ga abinci, atare suka tashi har zuwa dani, anacin abinci Safna na chart saida ummi Tamata magana sannan ta ajiyewayar tana zum6ura baki.
Bayan sun kammala Rahma takwashe kayan, takaima masu aiki su wanke.
Falon tadawo Inda iyayenta suke zaune harda safna.
K'asa ta zauna kusada Abbansu.
Zamansu babu dad'ewa ya Shaheed da ya Muneer sukayi sallam.
Cikin girmamawa suka gaida iyayensu, suma suka tambayesu ya iyalinsu?.
Kowa ya amsa da lfy k'alau.
Suma su Safna suka gaishesu.
Bayan gama gaishe2 Abba ya ce, "dama bawani abune yasa na tarakuba zancen auren safna ne yatashi.
Wata irin d'agowa Safna tayi arazane, aurena kuma Abba tafad'a da k'arfi!!!.
Suduka kallonta sukeyi, Abba ya ce, " eh aurenki safna ta, kiyi hak'uri abin yazo miki wani iri kuma 1time, wlhy nima haka lamarin yazomin babu shiri.
Kuka safna tafasa tana fad'in itafa wlhy akwai Wanda takeso Dan haka bazata yardaba.
Ya Shaheed ya daka mata tsawa, wlhy idan bakimana shiruba jikinki zaiyi tsami, iskancim banza kawai, Abban kike fad'ama haka?.
Toni Dan ALLAH baza'a bari aji uzurinaba haka kawai amin auren dole, narantse bana sonsa karma afara wlhy.
Idan bahakaba kuma wlhy zanbar gidannan.
Duka ya Muneer yakai mata tatashi dagudu tashige d'aku tana kuka da fad'in wlhy itafa bata sonshi.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce, "akwai matsala kenan?......
Babu wata matsala Abba Shaheed ashema ita ta haifemu bamu muka haifetaba, wlhy acigaba da hidima kawai, idan ankaita ta mutu aranar, ni wlhy dama halin Safna ya isheni agidannan.
Shikenan ummin Muneer yanzu dai munyi dasu ranar juma'a zasu kawo komai, nasanar da Alhaji Rabi'u, (yayan ummi), sannan kuma suma su yaya na sanar dasu shida Abubakar.
Tom ubangiji ALLAH ya tabbatar da alkairi yasa ayi damu.
Amin Abba yafad'a, ya kalli su Muneer ya ce, " to manyan yayye yakukace?.
Dariya sukayi, yayi daidai Abba ALLAH ya Sanya alkairi, insha ALLAHU zamu fara shirya biki.
Tattauna maganar bikin suka cigaba dayi har zuwa wani lokaci, daganan su ya Shaheed suka tafi gidajensu.

+.+.+.+.+.+.+.+.+.+.+.
A 6angaren bobo kam abubuwa biyune suka cinkushe masa tunani, ga tunanin yarinyar da akaima fad'e, gakuma tunanin zancen Appa na yau, yasan appa sarai mutumne mai sauk'i da sanyi, komai zaiyi zaiyishine cikin hikima da lallashi, to amma mutumne kaifi d'aya idan ya ve e babu maisakashi fad'in A'a, Dan duk abinda zaiyi baya yinsa da ka saiyayi bincike.
Yasan ko giyar wake yasha bai isa ya gujema Auren nan ba, to amma shikam harga ALLAH baiji zaiso wata mace bayan Ni'ima ba, duk macen datayi kuskuren shigowa rayuwarsa bazata samu wani farincikin saba, ya rintse idonsa, ahankali yak'asa gaban wani k'aton hotonsa shida Ni'ima, sunyi k'yau sosai ahoto, suna tsayene gaban wasu filawoyi sun fukanci juna, yad'an rissina yadafa cikinta sannan tanada cikin Nawal, itakuma tana kallonsa shida cikin tana murmushi.
Hoton sunyi bala'in k'yau, wasu hawaye suka zuraro akumatunsa, baidamu daya gogeba sai shafa hoton daya cigaba dayi, yad'au tsawon lokaci yana kallon hoton daga baya yafad'a kan gado yana hawaye kamar wani mace.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Babu 6ata lokaci aka su Appa suka kai k'ud'i da komai ranar juma'a, antarbesu tarba ta mutunci da girmamawa, cikin girmama juna komai ya gudana aka tsaida biki sati uku kacal, saidai daga amarya har ango suna cikin tashin hankali, garama angon yadaure sosai yamaida komai ba komaiba, harma yanad'an saka baki idan 'yan uwansa suna maganar shagalin bikin.
Haka yasa ammi taji dad'i sosai itada Appa, sai albarka suke saka masa.
Nawal ma sai murana take ankusa kawo mata momynta.
Shirye shiryen biki ya kankama sosai Dan hidima akeyi babu kama hannun yaro, abubuwa sosai su ya Hamza suke shiryawa.

+.+
Yarinyar da akaima fad'e tana samum sauk'i saidai har yanzu bata iya magana, kullum sai Bobo yaje asibitin safe da yamma, har yanzudai ba'a samu iyayentaba ana kan nema, gashi bata magana bare asamu wasu bayanai daga gareta.
'Yan sandama suna aikinsu na binciko Wanda ya aikata laifin ta hanyar Number motarsa da matashin nan ya d'auka.
To ALLAH yasa adace amin.

A6angaren Safna kam abubuwa sun cakud'e danta tsaya kaida fata batason auren, anbuga anbuga tak'i, anyi lallashin abanza, hardai takai yau ya Shaheed ya zaneta amma abanza, Dan tace wlhy aka matsa mata zatabar gidan.
Hankalin Abba yatashi sosai, yarasa mafita, gashi har anfara shirye shiryen biki, Dan gobe za'a kawo lefe............







*_Luv u oll fan's d'in aunty bilyn Abdul._*
[11/12, 2:15 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_


_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*

_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*


1⃣5⃣&1⃣6⃣

Tana kwance agadonsu tana sharar kuka Rahma tashigo, da sauri tak'arasa gaban gadon tana fad'in haba aunty Safna yakamata kibar kukannan haka, ko sokike kizo kanki yana ciwone?.
Safna ta tashi zaune dolene nayi kuka Rahma kinajindai yanda ya Shaheed yace aure babu fashi, wlhy nikuma bana sonsa....
Rahma ta katsemata zancen da fad'in toni aunty Safna ganinake tunda bawani kike soyayya dashiba kawai kiyima su Abba biyayya mana. Tunda kinsan bazasu cutar dakeba.
Safna takamo hannun Rahma tarik'e gam kamar tana gudun kar'a kwace mata ita, ta ce, "Rahma bazan 6oye mikiba, zan gaya miki dalilin bijirema su Abba.
Wlhy sati hud'u dasuka wuce zuciyata tayi tuntu6en kamuwa dason wani bawan ALLAH, a makarantarmu muka had'u kuma wlhy ina bala'in sonsa, kullum sainayi mafarkinsa.
Lokaci k'an k'ani guy d'in ya sace zuciyata, nikam nad'auki aniyar nemoshi duk inda yake, inaji ajikina shine uban 'ya'yana, yanzu haka nabada kwangilar nemosa, shiyyasa duk abindasu Abba zasuyi saidai suyi bazan yarda amin Auren doleba.
To amma aunty kina ganin kinyi dai dai kenan?.
Da Sauri tad'aga mata hannu kinga baneman shawara nakeba, nabaki labarin sirrin zuciyatane kawai, Dan haka sauraramin, ragamar rayuwata ahannuna take Dan haka bazan yarda azalunceniba inaji INA gani.
Ainaga kema kin isa auren, miyasa Abba bazai aura masa keba saini?, idan kinajin banyi daidaiba toke kice su aura masa ke, nikuma abarni da Wanda nakeso, danhaka tashimin anan banason shishshigi da k'wala kai afaranti.
Haka Rahma ta hak'ura dukda k'ok'arin datakeyi na fahimtar da yayar tata muhimmancin biyayya ga iyaye, da illar bijire musu, amma firr Safana taki'i saurarenta, daga k'arshema abin fad'a yaso yazamar musu.
Rahma tabata hak'uri ta tashi tafita.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Bikifa ya kankama, bak'i harsun fara sauka, ayau kuma za'a kai lefe Dan haka matansu ya Is'haq duk suna gidan.
Akwatuna har goma sha biyu nagani baje afalo, dangi anata d'agawa ana jinjina kai dayaba k'yan kayana, Appa da babban yayane sukayi lefe, ya sulaiman yad'auki nauyin duk wani abincin daza'aci, ya Hamza kam suna 6angaren cashiya, shine yahad'a faty za'ayi dina da daddare bayan an d'aura aure ankawo amarya.
Ammi ta had'a mother night ana gobe d'aurin aure.
Suma su khairiyya da matan su ya hamza ba'a barsu abayaba sun had'a Sisters day washe garin d'aurin aure da safe kafin ayi walima.
(Nace hummm kaga bikin d'an gata).

Ango kam babu abinda zaiyi saidai gyaran gidansa, Dan za'a canja MASA fenti da abundan ba'a rasaba tunda andad'e babu kowa agidan, "tun bayan rasuwar Ni'ima daya Shiga rud'ani kamar yayai hauka yasa Appa ya tattaroshi yamaido gida kusadasu.
Kayan lefe kam sunyi masha ALLAHU saidai mak'iyi aunty Rashida matar ya is'haq tafad'a tana fesama kanta turare.
Dariya suka shek'e da ita suduka, aunty Sameera matar ya Hamza ta ce, "k'yaface haka aunty Rasheeda tunda kina ragema amarya turare.......
To aii gara kafesa, k'ila idan amaryar tazo wannan mijin nata maikama da soja ya hanaka fesawa.
Dariya suka kuma shek'ewa da ita harda tafawa kamar wasu k'awaye.
Adai dai wannan lokacin kuma Bobo yashigo falon shida ya Hamza.
Ahankali suka fara tsagaita dariyar tasu, ya Hamza ya ce, " kukuma lfy?, miya sakaku dariya haka?.
Aunty Sameera ta maimaita musu abinda yafaru, dariya ya hamza yayi, bobo kam saiyayi murmushi yana kallon aunty rasheda dake dariya, ta ce, "ka kafeni da ido konayi k'aryane?.
Kauda Kansa yayi yana murmushi, ya ce, " aunty Rasheeda kenan, kisanifa saikin biyama matana turarenta babu d'aga k'afa.
Nanmadai dariya akayi, Aunty ummy ta ce, "lah bobo dama kanason auren nan amma idan anyi magana kaita wani basarwa?.
Okey da kin d'auka banasone aunty ummy?, tsaya kiga ikon ALLAH bayan d'aurin aure zakisha mamaki Romeo zan zama.
Dariya sosai sukeyi harda ya hamza da Ammi dake sakkowa daga saman Appa.
Shikam bobo d'akinsa yashige yana murmushi.
Bayan sunyi dariya mai isarsu suka koma tsokanar bobo ya Hamza yana kare masa, danshi tunda yashige d'aki yak'i fitowa.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Alhmdllh yau lefe ya iso gidansu Safna, anyima 'yan kawo lefe tarba ta girmamawa, kowa ya kalli lefen saiya jinjina kai, Dan kayane masu k'yau da birgewa.
Sund'an dad'e agidan sannan suka tafi cikeda tukuyci na girma.

Cikeda zumud'i Rahma tashiga d'akinsu, Safna tana zaune tana chart da baseera daketa k'ara zugata wai karta yarda da wannan auren, *boy ya ce, " yana gab da samo mata bobonta.
Murmushin jin dad'i taketa zabgawa, k'arar rufe k'ofa da Rahma tayi yasa Safna d'agowa, Rahma tak'araso gurinta tana washe baki, aunty Safna kinga kayan lefenki kuwa jar ubancan kai, wlhy kamar basusan ciwon kud'iba.
Baki safna ta ta6e sannan tagallama Rahma harara yarinyarnan na kula kemafa kanki da motsi, banace kidaina jingina aurennan danibane Dan uwarki, kakin yakamata kitaya farinciki Dan lefennan nakine baniba kam, saikuma tayi wata 'Yar dariya Rahma lefena yana nan zuwa daga Bobona, k'ilama sannan kinada ciki hhhhhjhhhh ta shek'e da dariya harda rik'e ciki.

"Na ce, " hummmmm".

Rahma kam girgiza kai kawai tayi, tana mamakin halin kafiya da dagiya irinna Safna, tanayin Abu kamar batada ilimin addini, ALLAH ya k'yauta tafad'a afili tana ficewa ad'akin.
Amin safna tafad'a ita tana Raka Rahma da harara.

Ran Abba a 6ace yake, sai safa da marwa yake afalonsa, gobe d'aurin aure amma Safna ta tsaya kaida fata bata son aurennan, yau Uncle Abubakar sau biyu yana dukanta shida ya Shaheed amma tace Sam batasan zancenba, daga k'arshema kayanta tahad'a waizata bar musu gidan.

Ya Shaheed ne yashigo falon Abba da sallamasa, Abba ya amsa yana mai tsurama Shaheed d'in ido kamar yau yafara ganinsa, ya Shaheed ya rissina ya gaida Abba sannan ya zauna ak'asa kan kafet.
Shima Abba saiya nemi waje ya zauna.
Ya Shaheed ya sauke numfashi Kansa ak'asa ya ce, "Abba dama wata shawarace nazo da ita.
Ina jinka Shaheed Abba yafad'a da hanzari.
" Hummm Abba inaga tunda Safna tak'i har yanzu, dataje tamana abin kunya inaganin kawai mubarta, inhar zasu yarda kawai abashi Rahma.
Abba yazaro ido waje, Shaheed baka ganin Rahma batayi k'ank'antaba!?.
Abba batayi k'ank'antaba, tafa gama secondary, kuma yanda nasan Rahma da hakuri da biyayya bazata bijirema umarninkaba kamar yanda safna tayi, nasan zata yarda ta auri Abdulmalik indai Rahma ce......
Dai dainan Rahma tashigo falon, tiren dake hannunta ya su6ce, abinda ke ciki yazube jikinta sai rawa yake saboda jin furucin ya Shaheed na k'arshe.
Ya Shaheed ne yamik'e da sauri yakamota ya zaunar, cikin taushin murya ya ce, kiyi hak'uri Rahma kibi umarnin Abba kifiddashi daga kunyar mutanen daya tara, kikalli gidannan cike yake da danginmu, wasuma daga wani gari suka taso, kituna d'unbin mutanene da Abba ya gayyata wad'anda zasu halarci taron d'aurin aure gobe idan ALLAH ya kaimu.
Rahma kema kinason Abbanmu yaji kunya?, kamar yanda Safna tayi, jibi kiga yanda hankalin Abba yake atashe akan abinda baifi k'arfiba daga garemu.
Rahma tad'ago kai takalli mahaifinsu dashima su yake kallo, gabad'aya fuskarsa ta canja, Abbansu muntum mai sauk'in kai da hak'uri amma yau 6acin rai ya maidashi wani iri, ita saitagama kamar yarame.....
Ya Shaheed yad'an ta6ata, da sauri takalleshi, ya ce, "baki aminceba kema ko?.
Yanda ya Shaheed yay maganar saiya bata tausayi shima, ahankali ta jinjina kai, cikin kuka ta ce, " nayarda yaya wlhy na amince zan fidda Abba kunya... Shashshekar kuka tahanata k'arasawa."
Cikin farin cikin ya Shaheed ya rungumeta, Abba kuma yarungumesu gaba d'aya.
Sai albarka suke saka mata da addu'ar fatan alkairi, itakam tana kuka tana sharar hawaye.
Abba yakira Appa ya sanar masa komai bai 6oye masaba.
Appa ya ce, "babu wani damuwa da Safna da Rahma duk d'ayane tunda daga tsatso d'aya suka fito, shima yayta sakama Rahma albarka.
Abba yaji dad'i sosai, sukayi sallama.
Ummi ma Abba yakirata tazo d'akin, jin abinda yafaru yasa ta rungume 'yartata cikeda farinciki dakuma saka mata albarka, saidai gefen zuciyarta tana tausayin Rahma, aganinta nawa Rahmar take, amma babu yanda zasuyi, sun tara d'unbin mutane wannan ne kawai mafita agaresu Baki d'aya.
Fatanta ALLAH yasa mijin nata yakasance mai kula da tausaya mata, Dan Rahma tanada rauni sosai, dukcikin 'yayansu babu Wanda yakai Rahma hak'uri, daga ita sai ya Muneer, sune suka d'ebo halin mahaifinsu Sak, na Rahma ma yafi nasa, Dan Rahma akwai hak'uri, kuma yaran gidan duk sunfita k'yau sosai.
Rahma ba fara bace amma tanada d'an haskenta daidai gwargwado, zamu iya kiran rahma tsaka tsaki batada tsawo bakuma gajera bace, tanada d'an jiki Dan 'Yar lukutar ummi ma da akece mata, idan akafad'a tayita kuka bataso, tanada k'yanta daidai gwargwado (saidai Safna tafita k'yau nesa ba kusaba), Abu mafi d'aukar hankali ajikin Rahma shine idanunta, wasu irin idanu Rahma take dasu masu hasken tsiya da girma kamar suffar kwai, duk yanda ran Rahma ya6aci basa canja kala saidai su k'ank'ance.
ALLAH yabama Rahma baiwar juya idanu, gasu masha ALLAHU da girma, sau dayawa idanun Rahma kan fisgi hankalin mutane kanta Dan danan tashiga ransu Dan ita mutumce mai saurin Shiga rai, indai zaka zauna da ita saita shiga ranka.
Wannan kenan.πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ‘ŒπŸΌ

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Labaridai ya isa kunnene Bobo "wai Amarya bata sonsa", amma abin bai bashi haushiba sosai, tunda dama shima ba auren yakesoba, Dan haka da yarinyar tasoshi da karta soshi duk uwar ubansu d'aya ko akwalar rigarsa, shi dama wadda za'a bashi yanzu d'in ta ce, " itama bataso, da wlhy har k'yauta zai mata.
Na ce, "hummmm.........






❀❀❀❀❀❀❀ *_masoya kumuje zuwa yanzufa aka fara gashi suya sai ran sallah_*πŸ˜‚πŸ‘ŒπŸΌ
[11/12, 2:16 PM] mrs bilkisu: πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_{Bobo}_


_Story & editin_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

✍🏿 _Written_
*_Marak'isiyya_*

_hak'in mallaka_
*_Aunty Bilyn Abdul_*

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Bily giro_*



1⃣7⃣&1⃣8⃣

Kafin la'asar zazza6i yarufe Rahma, tana d'akin Abba kwance ak'udundune, ya Muneer yashogo da Dr kaleed har cikin falon Abba.
Abba da kansa yashiga d'akinsa yatasoda Rahma daketa rawar sanyi, saman kujera ya zaunar da'ita Doctor yashiga aikinsa, babu wata matsala Alhaji 'Yar damuwace kawai Dr Kaleed yafad'a.
Abba ya ce, "to Dr babu wani taimako da za'ad'an bata kenan?.
A'a zan mata allura da magani tad'an samu barci, insha ALLAHU daga nan zuwa yamma zata koma Normal, yanzudai idan namata allurar tad'an samu koda tee ne tasha saitasha magani tayi wanka da ruwa maid'an sanyi ta kwanta, insha ALLAHU normal zata tashi nanda anjima.
To madallah Dr mungode sosai.
Babu damuwa Alhaji aii aikinane.
Babu 6ata lokaci Dr yayma Rahma duk abinda yadace, ummi tabata shayi tad'ansha kad'an tabata magani Wanda tashashi da k'yar Dan Rahma akwai tsoron allura da magani, bataso ko kad'an allurarma saida lallashi akayi.
Bayan tasha maganin ummi ta taimaka mata tayi wanna a bayin Abba, kaya aka d'akko mata tasaka takuma kwanciyarta a gadon Abba sai barci.

Hummmm wai ina Safna?.
Tana nan acikingidan kuma labari yakai mata, ancanjeta da Rahma, Dan haka tadage tarink'a tsallen murna ita taci nasara, shikenan zata mallaki bobonta nanda lokaci kad'an, har ruwa tazuba k'asa tasha Dan dad'i.
Cikeda farinciki takira Baseera ta guntsa mata, murna sosai ta tayata harda jinjina da yaba k'ok'arinta na dagiya.
Bayan sungama da baseera takira zeenat itama, zeenat ta ce, " wlhy Safana kin tafka babban kuskure a rayuwarki, na tabata nangaba saikinyi Dana sani Mara iyaka, son zuciya yasa kin bijirema iyayenki akan Wanda baima San da zamankiba, ke kanki bakisan Inda yakeba yanzu, bakida tabbacin zai kar6eki kobazai kar6i soyayyarkiba, wlhy kidaina biyema hud'ubar baseera zatayita kaiki tana baroki a tashar wahala ne......
Safna ta k'atseta atsawace, kee!!! Dallah malama yimin shiru, nakiraki nafad'a mikine danki tayani murna ba surutun banzaba, aiikin banza kawai mtsowww taja tsaki tana yanke wayar.

"Daga can Zeenat ta girgiza kai tana fad'in ALLAH ya shiryeki Safna, amma zakiyi nadama wlhy na tabbatar."

Babu Wanda yakumabi takan Safna shagalin biki akacigaba da gudanarwa, itama tafita harkar kowa agidan lamuran gabanta kawai takeyi harda yima Rahma dariyar mugunta.
Na ce, "hummmm.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*
Bobo ya lalubo wayarsa dake wringing daga aljihun jins d'insa, ido yad'an zaro tareda kallon Ya Sulaiman dake duba yarinyar da akaima fad'e.
Lfy kuwa bobo?.
Tab ya Is'haq ne kasanfa sunacan suna jiranmu..... K'ara kiran da akayine yasa Yakuma kallon wayar, ya is'haq d'innedai, d'agawa yayi tareda yin sallama.
Abdulmalik wai kuna inane kaida sulaiman?, ya Is'haq yafad'a daga can.
Wlhy muna asibiti wajen yarinyarnan amma gamunan zuwa Ku k'ara hak'uri.
Tom yakamatafa kuyi sauri Dan akwai abubuwa agabanmu masu yawa.
Gamunan yanzunan insha ALLAHU.
yanke wayar yayi tareda dawo da kallonsa kan ya sulaiman, ya Sulaiman yakamatafa muje kasandai masifar babban yaya, muk'arasa kafin ya k'ulu.
Gsky ne muje kawai aii nagama harma takoma bacci.
Bobo yad'an lek'a fuskarta, ya ce, " baiwar ALLAH, wlhy rashin maganar yarinyarnan yana damuna, yakamatafa ace iyayenta sunsan halin datake ciki.
Hakane gsky to amma yazamuyi? tunda bamusan idan takeba, saidai mucigaba da addu'a. Idan kuma tak'ara samun lfy mubi shawarar Ammi mumaidata wajenta kawai.
To shikenan bobo yafad'a yana fitowa.
Waje yanufa shikuma ya sulaiman yashiga office Dan ajiye kayan hannunsa.
Babu dad'ewa yafito, mota yashiga Inda bobo ke zaune a mazaunin direba, bobo yatada motar suka fice daga asibitin.

.+.
Gidansu Safna kuwa anyi shirin kamu Wanda aka had'a a babban harabar gidan nasu, saidai matsalar amarya babu lfya tana d'akin Abba kwance tana barci.
Hafsat matar ya Shaheed ta kalli ummi, ummi to yanzu yaza'ayine harfa dangin angon sun iso ga babu amarya, dama Safna zata mana alfarmar yanzu kawai saita zauna amadadin Rahma d'in.
A'a barta kawai hafsat, nibanamaso muna saka Safna acinkin sha'anin bikinnan, takalli agogon dake hannunta, hafsat inaga bari kawai atada Rahma d'in dukda dai bata dad'e da kwanciyaba.
A'a ummi abarta

Please Login or Register in order to submit comment