Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai daga can yace, my wife, na'am, tace, zaki 'yamun dimple d'in ki? Inaso dama yadawo fuska ta, dariya tafara duk da atsorace take da shi

SAMEER dai bai tab'a jin shi jikin wata mace ba, saboda haka, sai ya zama na, wani iri yakeji hankalinsa duk baya jikinsa, yamutsata yafarayi, hannunsa take rik'ewa amma ina, Yakai k'ololuwa, dan ya rantse saiya shiga duniyar Macury

Haka, dai abu yacigaba, har yakai bakinsa kan......


*Benaxir* dai taga kanta, yau gashi ita datake rubuta labarin wasu, yau gashi nata first night d'in yazo

Nidai ganin Bena tanata kuka, kuma ga 'yan NAGARTA kusa dani, bashiri na fita, dan bansan ajiyo kukan Bena

Haka na tarkata kayana nayi waje, saboda da alama SAMEER, dai abinda yake tarawa shekara da shekaru, ita yake zubarwa a jikin Bena

Wayyo bara nayi shiru, yanxu Aunty Lubie tace nayi......


Safiya nayi, na koma, Benaxir nagani a nad'e akan bed, shikuma gogan Sallah yake, jin motsin tashinta, yasaka shi juyawa, da sauri ta kauda kanta

My wife, kin tashi, babu amsa, haka ya ajiye Qur'an d'in, ya hayo gadon, kanta ya d'ora kan cinyarsa yace ya jikin?, ni kacikani, anqi a cika ki, mai kuka kawai daga d'an k'aramin abu kincukamun kunne da, Jabo, Lubie Beebalo haka ake

Yanda yayi maganar ne yabata dariya, sosai tad'an dara

A hankali yake sakko da ita daga kan bed d'in, already dama ya had'amata ruwan wanka, da kyar ta zauna a ruwan, saboda wai zafi, to kafita zan iya da kaina, a'a fitowa xakiyi kuma hakan shi zaisa kiji dad'in jikin ki, nidai Allah nace baxan fito ba, ka fita kawai, haka ya fita yanamata dariya, sosai yakejin wani farinciki, dama haka aure yake? godiya yaibga Allah dakuma iyayen sa, da sukayi masa zab'i na alkhairi, dan kuwa matansa alkhairi ne

Irin wad'an nan mata haka, aisai President, amma gashi Allah yaba shi su, da naso nayiwa kaina

Godiya ga Dr Ak dayabani shawarar hak'uri, da nunan ZAB'IN iyaye alkhairi ne

haka dai ta daure, ita abin mamaki yake bata, saboda yanda taga yake mata, kamar wadda tabashi wani Abu
Nikam nace ai wannan yafi komai, duk tak'amar namiji daji da kansa indai kika bashi, wannan to kin gama da ji da kansa

Duk kuma tsananin so, da tattali randa ya jiki ba wannan to bakida wata k'ima
Mata ayi hattara

Saidaga baya kuma ita da kanta, ta k'ara had'a wa ta shiga, alwala tayo, tayi sallar ta, dama asubah ce

Komawa baccin tayi, shikuma, lokacin ya dawo, bawa gadon yayi, janyota jikinsa yayi ahaka suka koma baccin tare


Basu tashi ba, sai wajan 11, wanka sukayi, lokacin Mom ta aiko musu da abinci, part en Jabo aka kai, ita ta d'ibi nata, sannan takai ragowar bakin k'ofar Uwar gida

Lokacin d'aya fito ganinsa yayi, komawa sukai

Karyawa sukai, shikuma yace bara ya shiga yaga ya Hauwa ta tashi, kiss ya mannamata a kumatu ya fita

Hauwa tana karyawa, wayarta ta janyo, last seen d'in *Bena* ta duba, amma taga rabonta da online tun jiya

Kiranta tayi, bugu d'aya ta d'auka, ke tun d'azu nake kiranki shiru?, kodai anyi aiki jiya?, bansaniba *Bena* tace, basufi minti 5 ba, sukayi sallama

Lokacin shi kuma, ya shigo, ganinta yai da makeup d'inta powder kawai da lipstick amma tayi kyau, ga k'amshi ta ko ina

Rungumeta yayi, yace good morning, ya bak'unta, kin tashi lafiya?

Amsa masa tayi, anan ya zauna, saboda gaba d'aya yarinyar ta burgeshi, alkaki ta kamasa, yanaci suna hira

Baisan haka take da diri ba, saidata mik'e da ido ya b'ata, harda had'iyar miyau, shi dai bazai gaji dayiwa iyayen sa addu'a ba

Daga jiya zuwa yau, baisan adadin farin ciki da yaji ba, kuma daga gani basuda hayaniya

Lallai zaikwashi gara jikin wannan yarinyar haka yace

Saidai ya jima, sannan yafita, haka xaman yaci gaba, kuma kullum sunawa juna waya, da bawa juna, labarin yadda maxajensu suke masu

Har yanxu Allah baibashi ikon, had'asu danyimusu fad'a ba, kuma ayau yake shirin fita daga gidan *Benaxir* zuwa wajan Hauwa, bayan sati d'ayan da ya d'iba awajan *Bena*


Sosai sukayi wata shak'uwa, kuma taji son sa, sosai a zuciyarta, hartakejin dama ita d'aya ce batada abokiyar zama

Bugawa Jabo tayi, tace yaufa zaifita daga gidana, wallahi kamar kada ya tafi, dariya tayimata, uhum su *Benaxir* anji dad'in harka, har ba'a son miji yatafi

Hak'uri ta bata, tace ai adalcin kenan, kuma, kince yana sonki?, to ki daure kitaya mijin ki bawa waccan hakkinta

Nima kinga, ai saiyau zaishigo wajena, kuma babu abinda ya nunan, kuma daidai gwargwado yana kula dani

Haka dai sukayiwa junansu nasiha, sallama sukai

Hauwa angyara gida, tareda taimakon house girl d'in da Mom ta kamusu, tsohuwa da yarinya

Magreb nayi, tayi girkin ta, tuwo tayi da kunun aya, saboda Mom tacemata yanason kunun gyad'a da tuwo, itakuma bata iya kunun gyad'a ba, shiyasa tayimasa na aya

Sabanin *Benaxir* dabata iya, tuwo ba.

Editor
Aunty Lubie

@ut@r h@jiy@
[11/24, 2:10 PM] Autar Hajiya: [25/09 10:08 am] @ut@r h@jiy@💅🏻💦✍🏻🌹🍇💦💖: *NIGERIAN🇳🇬 Girl*

*ZAB'IN WA ZANBI?*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussain*

*Short novel*

*Dedicated to Add Benaxir, & My dear Hauwa M Jabo*

*Page 19-20*

Ana sallan Isha'i ya *SMS* ya shigo banganshi da leda ba, ko kuma yashigo lokacin natafi samo labarin *FUTUHATUL KHAIR* ne, Allah a'alam

Shiga yayi wani yadi ne jikinsa, d'an Kuwait jikinsa yanada santsi kamar Imrati, azuciyata nace hala wannan mutumin yana son, yadi dan kusan kullum dashi nake ganin sa

Zama yayi kan d'aya daga cikin kujerun da sukayiwa parlour'n k'awanya, k'afarsa mai kyau wadda gashi yayiwa luf luf ajikinta, mik'eta yayi akan Center table d'in dake kusa

Wayarsa yake matsawa, daidai lokacin ita kuma Jabo ta fito, tana sanye da riga da zani, na Atamfa zanin single ne, amma kasancewarta mai hips mai kyau sai zanin ya zauna kamar skirt, sosai Atamfar ta amsheta

Ga wani sirrin k'amshi daya lura tanayi, dan ranar daya fara ganinta sosai turaren yayimasa dad'i, bayan bikin su ma, yaji k'amshi yanason k'amshi sosai

Tunda ta tawo, yake kallonta, dan tatafi da d'an ragowar Imaninsa, 'yar lukuta ce, abinda bakinsa ya furta

K'arasowa tayi, kujerar dake facing nasa ta zauna, d'an durk'usawa tayi, sannu da zuwa?

Yauwa, ya gida, da kwalliya? Lah, nibana kwalliya fah kalla kaga nuna masa fuskarta take, huum nidai banyardaba kalli lips naki inda sukayi pink, kinsa janbaki, nidai ban saba

To bara nagani, ko wasa kike, da wayo da wayo, yaje har inda take, hannunsa yakai kan lips nata, wow taushi saikace *NAGARTA bread* , sosai ya shagala da abinda yake, saidayaji tace kagani, bansa komai ba

Nidai nasan, kinsa wani abin kikasaka wanda baxan iya ganin saba, amma abu mafi sauqi tsaya kiga inda zansan k'arya kike, kinsa Jan baki

Bakinsa ya kai kan nata, juyawa nayi naga Aunty YBK na nan, sainaga bata nan, aikuwa saina qara gyara tsayuwata, dan ganewa idona

Sosai yake tsotson lips nata, kamar wanda yasamu *GALAXY chocolate* yana shan nan a yangance, daga lip kuma sainaga yana k'ok'arain kai hannu inda zuciyarsa ke muradi, cak ta rik'e hannun, plx kaci abinci kaji, abinda tace kenan tayi saurin mik'ewa, ashe kan cinyarsa take
Ya ilah! Yausha nahau masa cinya? Batada amsa illa gaba da tayi

Jiki ba kwari yabita, zama yayi ita tayi saving nasa, kanta sunkuye lallai indai haka aure yake, to yanada girma, wato duk abinda mukeji kuma muke rubuta wa, ba komai bane saiyafaru kanka

Tunanin me kike?, ba komai, anya juway kodai kina tuna...... dariya tayi tace Allah ni ba haka ba


Tare sukaci tuwan datayi, santi sosai yake Leman ayarma haka yasha, kai Allah nagode maka, daka bani mata wad'anda suke perfect awajan girki


Roman da tayi, atunanin ta kamar bazai ciba, shima haka yaci, saidaga baya yace,'yar gidan Mom kada kicikamun ciki, nakasa komai

Kallonsa tayi, tace mezaka kasa, ido ya kashemata yace bazaki gane ba

Sosai taji mutumin ya kwanta mata, saboda yanada sauk'in kai, kalli yanda yake mata kamar sin shekara tare, ko ba Auren had'i akayi ba

Brush suka tashi sukai, daga nan, ya d'an kalli kwallo, sannan ya shiga internet, anan yaji *Labarin, rataye farouq, da kuma kama Safwan Safana, akan manyan ta'addacin da suke wa k'asa, anan aka nuno bikin Candy da Mohd Adeel ma*, haka yayi d'an dube dubensa sannan ya mik'e lokacin Hauwa hartafara bacci, dama gata gwanar son bacci

D'aukanta yayi cak, wayyo ihu tafara, ganin shine saita rufe idonta, dariya yai yace, ainine zanyi ihu, wannan nauyi haka? Lallai ya F na aiki, dayake d'aukan ki

Ni banda nauyi, amma kaga k'awata lukutace, Adda kike nufi?, Adda batada k'iba saidai tanada hips, Jameela M Ali, mana, lokacin ne ya direta yace nazata Addan itama lukutace irinki?

Pillow ta jefamasa tana wallahi Adda kyakywace dan baka gan taba, dama ina zanganta, miqewa tayi wanka tashiga

Shikuma lokacin ne, yayiwa *Benaxir* waya yamata sallama

Wanka, yashiga shima bayan fitowarta, d'an shafe shafenta tayi, sannan ta d'auko rigarta da hijab tasaka

Yana fitowa shima d'akinsa yayi acan ya canja kayansa zuwa na bacci, sannan naga ya d'auko Leda d'akinta ya koma

Ganinta yayi yana sallah, tsayawa yayi ta idar, sannan yashiga gaba, nafeela sukai, dan nunawa Allah godiya

Kaxace ya fito da ita, (kitchen noodles) romanta kad'an ne, sai ice cream da Haleeb ta qasar UAE

Bismillah yace mata, dan naga masu k'iba saida abinci kusa, murmushi tayi, tace saikuma gashi banda cin, ya xa'ayi kenan?

Bawani ko d'azu kinfini loma wajan cin tuwo, haka kika ringa turawa, sosai tayi dariya jin yanda ya juya zancen, shine fa yake loma, daga k'arshe ma, plate d'in ya d'auke

Batada ta cewa, haka dai tad'anci sai *Haleeb sa'ud* d'in data d'anci, bakinsa suka wanke sai gado

Jabo dai yai za'aci kwakwa, dama kunsan 'yan sokoto da gyara, tunsuna yara, to Jabo dai saidai muce ayi kuka da birgima lafiya, dan saikin yabawa aya zak'inta

*Asubah ta gari, jabosameer*


Koda safe bantadda komai ba, saima first aid box dana gani, akan gado, k'arar ruwa naji, haka na d'an lek'a, Jabo nagani cikin jacuzzi kamar matacciya, tayi wani iri, abin tausayi abin dariya, ga idon nan tabarkallah yayi ja, azuciyata nace lallai SMS baiyiwa Jabo ta dad'i ba, *(garama Moh yayiwa Sumy a hankali)*


Da kansa yayimata wanka, yabarta aciki dan tayi na tsarki, kulawa sosai yabata

Mom anci sa'a tayimata waya a safiyar, saijin muryarta tayi, bashiri tabazamo mayafi ta tawo

Ganin yadda take, yasaka Mom cewa bazai kashe mata 'ya ba, bara ta tafi da ita

Ba yadda ya iya, haka yanaji yana gani aka tafi da ita, sosai yajishi wasai, lallai mata rahama ne

Kuma ko wacce da kalan nata baiwar, shiyakasa tantance wace tafi wata cikin su, *Bena* har albarka haka yace


Kwananta uku da tafiya, gurin *Benaxir* ya koma , baiyimata k'araya ba,, haka ya fad'a mata komai

Bataji komai ba, tunda itama tasan ta kawo nata, saima riritashi datake dayimasa favourite nasa kunun gyad'a


Acan kulawa sosai Mom take bata, tare suke kwana, wayarta bata tawo da itaba, shiyasa bataji motsin Benaxir ba, itama haka wajan Benaxir shiru ba Jabo

Yaune Abbun SMS zaidawo, dayake ana bikin da kwana d'aya yayi tafiya, yau kuma zaidawo

Matar Albarka, sunan dayake kiran *Benaxir* dashi, na'am mijina har ajannah, dariya sukai, Abbu yau zaidawo kuma Mom tace muje duka, ita Hauwa tana gidan, kinga kwasan juna, tunda ni ban had'a kuba

Saiki shirya da wuri, tom tace

Tashi tayi, da sauri tayi hangar kitchen, kaza ta d'auko, wani had'i tayi mata, sannan tayimasa kunun gyad'a

Tana gamawa, wanka ta shiga, Swiss boyel ta d'akko red ne, rigar har gwiwa take,anyi stone work ajikinta

Tayi kyau, takalminta da jaka, ta d'kko, lokacin harshi yagama ya fito

Wow masha Allah, kayi kyau, anya ba nik'ab zaka na sawa ba? Kin jiki ke zance irin wannan kyau haka? Kodoi mufasa fitar nan? Nabiya tukwicin kwalliyar?

Sanin halinsa datayi, a d'an zaman datayi dashi, yasaka batace komai ba, tak'ara gaba, au nikikayiwa haka? zan rama, saidai ka rame haka tace

Kayan ya d'auka, kullo k'ofar sukai, shiya bud'e mata gaban motar suka tafi

Can kuma, *Hauwa*, itama itada Mom haka suka wuni yimasa girki, duk abinda sukasan yanaso sun masa

Suna gamawa, wanka suka shiga, 'yan aiki kuma sukafara gyara gidan

Lokacin da *Benaxir* da Sameer sukazo Mom tagama shiryawa, *Hauwa* kuma tana cikin d'aki

Abokin Abbu ne, ya d'auko shi daga airport

Shi yasa Sameer bai jeba, bud'e gate d'in da akayi shiyabasu tabbacin Abbune , shid'in ne kuwa, yana shigo wa, sannu da zuwa akayi masa

Amsawa yayi, sannan ya shiga d'akinsa, Mom ce tace *Benaxir* hau sama, *Hauwan* tana ciki


Miqewa tayi, sama ta hau, murd'a handle d'in k'ofar tayi, *Jabo* tana gaban mirror, ta juya baya, sai sallama taji, juyawa da zatayi sai ganin *Benaxir* tayi, da gudu tace *Benaxir* itama tace *Jabo*

Editing by
Aunty Lubie

@ut@r h@jiy@
[11/24, 2:11 PM] Autar Hajiya: [25/09 2:18 pm] @ut@r h@jiy@💅🏻💦✍🏻🌹🍇💦💖: *NIGERIAN🇳🇬 GIRL*

*ZAB'IN WA ZANBI*

*®NWA*

*Short novel*

*©Zainab Y Hussain*

*Dedicated to Adda Benaxir, nd Hauwa M Jabo*

*page 21-22*

Jabo ina kika shiga wajan kwana biyar ina neman layinki, ke kuma ko ki kirani

Manyan kinga yanda kika koma, lallai auren ya amsheki, inji Bena, dariya suka saka, xaunawa sukai a bakin gado

Bena ta manta haka akace tazo sugaisa da kishiyarta, ita ma Jabo ta manta, Mom tamata waya tace ga abokinyar zamanta zata shigo

Hira suke sosai, harda sako labarin NWA da yanda sukeso komai ya tafi daidai, Jabo ce tace Ina Aunty YBK?, kwana biyu naga bata online ko haryanzu basu gama exams d'in ba?

Sun gama, jiya ma ta hau, kecedai kowa yafaraiwa tsiya, dad'i miji kin mantamu

Dariya tayi tace nida miji zai kashe, wallahi kuma Bena da akecewa 'yan sokoto suna shan magani, nifa bansha komai ba, banqi ba, naci (jelar ayii), da kaza mai had'a da nonon rak'umi amma bayan haka wallahi banci ko nasha komai ba


Amma idan kini yanda naji, saikace ana..... kedai bari, na gurzu, d'an mutumin baimin a slow ba

Dariya Bena takemata ganin ahaka ma idonta yacika da qwalla, huum nifa abin ba sauqi, naxata bazan k'ara moruwaba, amma gashi yanzu harna saba, tunda Kishiyata bata da lafiya, wajena yakoma, ai Jabo naga ta kaina, kinsan washe gari saiga Mamu, tamun waya wai ya labari? Kiji wallahi idan bakeba banga wadda zan fad'awa sirri na ba, kema d'in ba komai ba

(Ina ganin rashin hankali da wawancin 'yammata da suke zama suna bawa k'awaye labarin abinda ya faru tsakanin su da maxajen su, haukane wannan kuma manzon Allah yayi hani akan haka, plx koda hira ta kama kayi, to kasan da irin wad'anda xakayi, Allah yasa mu dace)

Ai Jabo saidai hak'uri amma idan Allah ya baka miji mai kwakwa ba yadda xakayi jarumine mijina gaskiya kuma yanada hankali SMS

Da sauri Jabo ta d'ago ido tace waye mijin ki? Sameer ai nan gidan surukaina ne, Abbun sa zai dawo yau shine mukazo, Maman sa tace wai abokiyar zamana tana sama nazo mu gaisa, ni kuma naganki na shan take tana ina?

Ai jijiyoyin jikin Jabo ne, suka dena aiki na 'yan sakanni, jitayi kamar a mafarki, indai haka ne kuwa *Benaxir* ta tabbata itace *Kishiyar ta*

Bena ce tace, Jabo nan gidan 'yan uwan kune? A'a gidan Mom ne, *SURUKATA*, banganeba kina nufin kice *SAMEER shine mijin ki?* tabbas shine, indai hakane kenan kece Hauwa?, kada nashiga rud'u

*Itadai Jabo gaba d'aya ita tatafi wata duniya daban, kenan duk hirar da suke, dama mijin su d'aya?, dama suna zaune gida d'aya suke hira?, kenan Bena itace uwar gidan ta, ZAB'IN mahaifinsa?, yanzu duk shawarar da suke bawa juna dama miji gida zasu aura? meye abinyi yanxu*

Duk maganar datake batasan tafito fili ba, sai jin maganar Bena taji tace *abin yi shine mu d'auka dama haka Allah yaso, kuma k'addararmu tazo a haka, tunda had'uwar online mukai dake, ba garin mu d'aya ba, ba tare mukai school ba, balantana nasan saurayinki ko kisan nawa, kinga kenan rubutaccene wannan auren daga rabbi samawati*

Fatana tunda munsan juna munsan halin juna, kuma munsan cewa abokan zama muke, muyi hak'uri mu rungumi mijin mu, muyi masa biyayya mu taimaka masa, wajan sauke hakkin kowacce

Koba haka ba, tafi su kaji yo a bayan su, juyawa sukai Mom, Abbu, Sameer, sune abakin k'ofa

Qarasa shigo wa sukayi, zama sukai, Mom ce tace ubangiji Allah ya had'a kanku, Allah kuma yasa abinda mu kaji kuna fad'a har zuciyarku, kurik'e juna da aminci

Kaikuma Sameer kagansu k'awaye ne, nikaina shaidace saboda yanda naji sunayin waya da hira a chat, saboda haka kaxama mai adalci tsakanin su KA rik'e sirrin kowacce

Mom nima fa nasan tsakaninsu, dan babu wadda bataban labarin junansu, Allah yayimuku albarka

Rungume juna sukai suna masu farinciki


A haka aka sakko akaci abinci, daga nan sai hira, ranar dai gidan Mom aka kwana

Washe gari suka tarkata suka koma gidansu

Zama ne ake naso da juna, da mutunta juna, da amana, shi kansa maigidan sosai yakejin dad'in halin matansa, komai tare

Idan wannan keda girki, to saikaga wadda ba itace da shiba hartafi mai girkin yin aiki


Hauwa datake 'yar sokoto, sosai ita ke had'a musu abinda jikinsu zaiyi kyau, babu cuta

Kowa yazo gidan, sai sun baka sha'awa, duk da ance tsakanin harshe da hakori ana sab'awa, to kosunsami sabanin baya zuwa ko ina

Dakansa yakai kowacce gidan su, tare sukaje kuma tare suke kwana, k'awaye nasu duk suma sunsan kishiyo yine, amma babu mai maganar wata agurun wata, saboda babu fuska

*Bayan wata bakwai*

Daga Bena har Jabo nagani da qaton ciki, kowacce tayi nauyi, shikuma yana zaune tsakiyarsu Mango da Cherie (Agwaluma) yake yan kamu su, gaba d'aya yanxu shine abin tausayi, saboda wahala suke bashi, daga wannan tace wannan sai wannan tace wancen

Yanxuma *Jabo* ce tace Cherie take so, saidaga siyo, yace baby mango yake so, haka yaqara komawa ya siyo

Yana shigo wa *Benaxir* tace itakuma manyan mango take so irin mai smenting nan, harara ya watsa nata, dariya suka sheqe da ita

Tsakani da Alalh, yanxu bakwa tausayamun, daga wannan sai wannan, *Benaxir* ce tace, nidai idan baka siyo mun kace, naga banice ko soba, d'anka ne yake so, tana gama fad'a ta juya masa baya

Ganin yadda ta juya, yasaka bashiri ya juyo da ita, peck yamata sannan ya fita

Dariya suka saka, masa ganin yanda yafita

Yana dawowa sukace ya zauna, ya yanka, haka yake musu idan yabawa wannan saiya bawa waccen

Dama *Jabo* uwar ci, haka take cin nata, taci na *Benaxir*, Bena sarkin hak'uri saida tayimata murmushi kawai

Mom kullum ana hanya, za'ayi jikoki har biyu lokaci d'aya


Yau tunsafe Benaxir keta naquda, sosai *Jabo* hankalinta ya tashi, ganin yadda Bena ke yada kai, gashi sunzo asibiti nan ma, shiru

Mom hankalinta itama ya tashi, sosai addu'a take mata kan Allah ya sauke ta lafiya

Jimawa kad'an itama *Jabo* tafara labour, hangomun SAMEER gashi kwarraren likita amma yakasa komai, akai, sai da taimakon Dr Sa'adatu da Dr Ummul fadeela, Allah ya kawowa Bana haihuwa

"Twinc duka mata, wayyo murna, haka aka gyara mai jego

Can kuma, itama Allah ya sauki, Hauwa lafiya Lou, tasami d'anta namiji amma Allah tayimasa rasuwa

Kuma gashi kamar su d'aya da Sameer babu Inda ya barshi, haka akayi masa, wanka pic ya d'aukeshi, daga nan aka kaishi gidan sa na gaskiya

Kuka sosai yayi, saboda yadda yakeson yaga d'an Hauwa, kuma yaron yashiga ransa

Zuciyarsa tanason Hauwa sosai, *Benaxir* kuma yana girma mata saboda macece mai hankali da hak'uri, saboda haka yaji d'acin mutuwar *Mohd* sunan daya sawa Babyn

'Yan uwan Hauwa da Mom tasa sosai suke farinciki Hauwa nada ciki

Ashe duk abinda Hauwa take Babyn baxaizo da raina, haka Allah yaso

*Benaxir* itama saidatayi kuka na rashin Babyn k'awarta, sosai mutuwar ta bigeta

Lokacin da aka sallamesu, gida suka koma, part d'in mai gidan duka aka koma

Jabo itama tayi shar da ita, anyi mata wanka, 'yan uwanta sunzo wad'anda suke kusa

Lokacin data shiga wajan Benaxir duka kowa yana zaune, karb'an Babyn tayi, sosai ta musu addu'a

D'ayan ta karb'a shima tamasa, hawaye ta share, Benaxir ce tadafa kafad'arta, tace kiyi hak'uri haka Allah yaso

Wadda take hannunta Babyn ta karb'a, maidamata ta k'arayi tace, ga Babyn ki duniya da lahira, 'yarkice halak malak nabaki ita

Juyawa tayi, tace Ya Sameer nayi abu bada shawararkaba, ina fatan banyi laifi ba

Bakiyiba, yace haka kowa yasamata albarka, sosai Hauwa taji dad'i, godiya kawai take zubawa

A ranar kowacce tafara bawa nata Babyn Mamma

'Yan gidansu *Benaxir* tun ana gobe suna, sukazo, tareda matan yayunta *Anee da Fido* wad'anda suma haihuwa ko yau ko gobe

Kayan barka masha Allah, kunsandai basaina tsaya b'ata bakina wajan fad'a ba, komai dai gashi nan

Dangi koina sai xuwa suke, daga na Hauwa harna Bena

Yara sunci sunana, *Fatima da Xahra* Allah yarayasu

*kusaurareni a Episode d'in k'arshe*

*Ubangiji Allah kayiwa Kakanmu, malamin mu, Rahma albarkar shugaba SAW, Mahiru Shareef Bala*

Editing by
Aunty Lubie


@ut@r h@jiy@
[11/24, 2:11 PM] Autar Hajiya: [25/09 6:05 pm] @ut@r h@jiy@💅🏻💦✍🏻🌹🍇💦💖: *NIGERIAN🇳🇬 GIRL*
*ZAB'IN WA ZANBI*

*®NAW*
*©Zainab Y Hussain*

*Short novel*

*Dedicated to Adda Benaxir & Hauwa M Jabo*

*END*

Da safe kaya irue d'aya suka saka, babyn ma kaya iri d'aya, idan kagan su dole subaka sha'awa yadda suke tafi da komai nasu cikin hankali

Masu vedio coverage sunzo, daga NAGARTA photos aka d'auko su, camera man, ma haka

Gida ya cika ya tumbatsa, da jama'a, na Jabo daban, na Bena daban, amma kuma bazaka tantance kace wannan na wani bane, saboda komai iri d'aya ne

Du kayan dasuka saka, iri d'aya ne, wani Abbansu Benaxir ne ya d'in komusu, wani kuma daga gidan su Jabo aka kawo musu

Da safe tareda uban gayyara aka ci sunan, saidayaga rana tafara kuma mutane suncika, ba shiri ya fice, tunda yaga Aunty YBK tazo, yasan yanxu zaisha tsiya

Haka akaci suna, kowa dana sa Babyn a hannu, gara Benaxir tana bawa mutane, amma Hauwa tana jikinta, har dariya ake mata

Wajan k'arfe 5 ne, kuma akatafi walima a Taj mahal, 'yan India ne suka bud'e wajan, komai su sukayi

Mutane ba yawa akayi, saboda komai anraba agida, wannan Mom ce ta had'a, Shadda suka saka, d'in kin Mali, wayyo hangomun Hauwa, ta amsheta sosai, saboda shaddar red CE,kuma kunsan abinka damai k'iba ko yaya ne kaya suna zauna masa sunyi d'as a jikinsa

Bena ma tayi kyau, sosai saboda, yanxu idan kaganta baka cewa itace, jikinta ya murje tayi wani irin fari, saitazama irin balck american nan, ko nace rani mukhraj ta India, hips d'inta dai dai, ga kuma kyauna haihuwa

Mama Hassy ce, ta tsunkuleni tace @ut@ irin wanga kallo haka, kamar baki Santa ba?

Mama ai Adda Benaxir ta canja, Allah da fari ban ganeta ba, saidatayi magana, lallai Aure rahma, jibi itama Jabo kamar ba itaba, ninarasa ta zab'e bansan wace tafi kyau ba

Huum, kyaji dashi, kidaiyi a hankali da mutane a wajan, tana fad'an na tuna, bashiri na matsa naciga ba da d'auko rahotona

Waleema tayi kyau, ta qayatu, ansha kid'a an danse, su Maman Bobo ana kan gaba, wajan rawa

Anee ma, da tsohon cikinta saidata rausaya, nima kuma gwanar rawa, ajiye biron nayi, natafi filin rawa, ana lik'i ina fakar idanun mutane ina cusawa a........

Juyawar dazanyi na d'auki birona dan cigaba da rubuto muku labari, sainaga wayam babu komai, lallai wace ta sacen kodai yarone, ina dubawa kuwa naga Adnan(Ummin Adnan) ya d'auki Biro, Adeel kuma (Ummi luff) ya d'auki littafin bayanda zanyi haka nayi saurin fita dan nasamu wasu kayan aikin, Dan naga Ummi Aysha da Pharty, da Meemi suna watsa jinyar kaza a cikin jaka, Mrs Omar ba jaka, sokewa naga ta nayi

Shiyasa nake sauri inga dakuma wa, ake satar chicken choudry
Kafin na dawo, sai motoci nagani, suna ficewa

Har an tashi, kuka ne kawai Banyi ba, da zanga yaran nan kuwa da na dake su, sunana naji ankira, ina waigawa yaran nagani cikin motor suna mun gwalo

Haka dai nayi takaicina nabi, motar dan naga idan na tsaya banda abin hawa, zanyi biyu babu

Alhamdulillah, haka suka ci gaba, da rainon yaransu cikin kulawa, mijin su kuma arziqi alhamdulillah, saboda yanxu asibitinsa reshensa har Abuja, sokoto, Bauchi

Dubu d'ari biyar biyar yabasu suja jari, Benaxir Gidan kifi ta bud'e, wanda alhamdulillah akullum ana fita dashi kuma ana samun riba ta wajan dubu d'ari

Hauwa ma, Gidan kaji itakuma ta bud'e kowanne sai sambarka, mijin su na musu komai, bai ragesu da komai ba, yabasu jari bawai Dan, suyiwa kansu wani abuba, a'a dandai suji dad'i ya basu

Umrah duk azumi da Mauludi, bata wucesu tun kafin ma su haihu

Iyayen su na alfahari dasu, saboda babu wadda ta tab'a kai k'arar

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment