Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

morewa bacci,Koda ta tashi yau ba zazzabi sai dai Dan rashin kwarin jiki da batada,tana shirin Fara gyara gidan taji sallamar Zainab,sosai taji dadin shigowarta,Dan haka ta yakar hakora, tambayarta tayi jikinta sannan tace,

"Dama zuwa nayi inga yadda Kika kwana da jikin,Dan nasan tunda waccan me kirar samudawan ta dawo yau ana can ana kashe arna"โ€ฆ

Sai a lokacin Dije ma ta tuna da dawowar sajida Dan Sam tama Manta, murmushi tayi tare da tunawa da lallai Kam Bata ganin Habeeb,tunda gimbiya ta dawo.

Kallon Zainab tayi tare da fadin, "ke yarinya ba dole yayi rawar kafa ba,first love dinshi ce fa! Ni wallahi nama Manta da ta dawo,nasan Yana can ana ta kashe shi da luv shiya sa,Dan haka Ni Bari in tashi in samama kaina abinda zan afawa zumbili na".Tare suka shiga kitchen din sukayi girki Mai sauki,sunayi suna hira, har suka Gama,bayan sun Kare ne sun ci sun koshi sannan Zainab ta gyara Mata gidan,Dan Dije kasa tashi tayi sai bacci,Sam batayi wani tunanin Habeeb ba.

*****

Kwana biyu cif ya kwashe batare da yasata a idonshi ba,duk yadda yaso zuwa dubata sai tasan salon da tayi Masa ta shagaltar dashi,yau ta Kama girkinta ne,Dan haka yaketa zumudi ya tashi aiki,sosai ya fahimci Sajida shiyasa yau ya kudiri niyyar sai magrib ma zai koma gidan,yasan duk bala'i dai lokacinta ya fita.

Saida yayi sallah sannan ya dawo,Yana shiga ya isketa zaune saman sallaya ta idar da sallah tana addu'a,wanka ya shiga Dan haka tana idarwa ta Mike ta zauna saman gadon tana jiran fitowarshi,ya Dan jima sannan ya fito,da kallo ya bita,sai yaga kwana biyun dabai ganta ba harta Kara mishi girma da Kuma kyau, murmushi ta sakar Masa,shima ya mayar Mata da martani,Sam baiyi tunanin bazatayi fushi dashi ba sabanin hakan Daya gani,itako Dije anata bangaren Bata ga abin fushi ba Dan ta dauka haka akeyi in kanada kishiya har sai kwananka zakaga miji,sosai suka Nuna sunyi kewar juna,inda Nan da Nan suka suka shiga aikawa juna sakonnin soyayya.Bayan sun Sami nutsuwa ne suka Kara yin wanka,kwance take jikinshi tanata Mai korafin jikinta ciwo,cikin salon shagaba.Babu ko knocking sukaji ana Murda kofar alamun ana so a shigo.

Janyeta yayi daga jikinshi yaje ya bude kofar batare ma Daya tambayi waye ba,Sajida ce tsaye sanye cikin Riga da wando theree quarter,Bata Bari yasamu damar tambayarta meya kawota ba,illah rabawa datayi ta gefenshi ta shige,sakin kofar yayi ya juyo tare da fadin,

"Ke malama lafiya Zaki shigowa mutane daki Kai tsaye haka!"

Farrrr tayi da ido itako Dije kallon ikon Allah ta tsaya yi,Dan wata dariya ce tazo Mata,wadda takasa danneta,ganin hakan yasa Sajida nufar inda Habeeb yake Dan ta kunsawa Dije bakin ciki,sakalo hannunta tayi a wuyansa tare da kashe murya,Wanda shi Habeeb tsabar bakin ciki ma ya hanashi ko motsi,cikin wani salo tafara furta, "Haba my man! Shine ka barni cikin kewar ka,kasan na Saba da Jin dumin jikinka, musamman kwana biyun Nan,ka nunamin Inada muhimmanci a rayuwarka,kasa na yadda nafi kowacce mace kamar yadda ka fada,Dan haka.......Bata karasa ba sukaga hasken flash,dukansu waigawa sukayi,sukaga Dije tsaye rike da wayar Habeeb tana musu hoto,Yana shirin yimata magana yaji tace,

"Dan Allah tsaya Yaya sauran Daya,gani nayi kunyi min Kama da wata tunkiya da ragon Inna da nake wasa dasu lokacin Ina karama,sai Naga Anty Sajida sakkkk tunkiyar wallahi.....๐Ÿ™Š

Comments with

*Alkalamin khady* โœ
[7/9, 9:00 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*AWESOME WRITER'S ASSO..* ๐Ÿฎ
( _palace of excitation n'd pleasant writer's_)

*TAME GARI*

NA
Khadeeja Usman

6โƒฃ1โƒฃ

Sakin baki Habeeb yayi Yana kallon Dije,dan yama rasa abinyi,itako Sajida iyakar Shaka ta shaka,.Basu ankare ba suka ga ta nufo su tana fadin,"yaya kudan gyara muyi ๐Ÿคณ selfie Yaya saika Dora a secren server din wayarka kowa yaga matanka.Cikin zafin nama Habeeb ya mika hannu da niyyar wafce wayar, aikuwa sai gani yayi ta kwasa a guje zuwa falo,Sajida da tun dazu ta rabu da jikin Habeeb tsabar takaici kamewa tayi a gurin,shi kuwa rufa Mata baya yayi,zagaye falon suka kamayi,inda daga karshe ya cafke ta,ya shiga kokarin kwace wayar,boyeta tayi a jikinta, hakan yasa ya matseta tare da kokarin lalubar wayar,har suka fada saman kujera,mutsu-mutsu ta shiga yi,ya rasa yadda zaiyi da ita,Dan haka yafara Mata cakulkuli,dariya take yi sosai tana gaggantsarewa,shi kuwa hakan datakeyi ya Fara jefa shi cikin wani yanayi,sosai take shigewa jikinshi,Wanda hakan ya Kara canza akalar lamarin,Wanda yasa suka Manta da batun waya suka shiga romancing din juna.


Cikin wannan yanayin Sajida ta iske su, Wanda tsabar bakin ciki Bata San lokacin da taji hawaye na zubo Mata ba,Dan haka ta nufi kofar fita,cike da Dana sanin zuwanta part din,gaskiya wannan plan din na mummy Sam ba basira a ciki,gara Nima nasake taku,wallahi saina ci uban yarinyar nan,haka ta karasa bangarenta tana ta sakawa da kwancewa,tare da kudirewa ranta saita ci uban Dije.

Su kuwa tsuntsaye sosai suka shagala,inda suka kasa jurewa har Saida suka Isa babbar head quarter,sosai suka samu nutsuwa,sannan suka yi wanka,magani Dije Tasha yayi Mata allura Nan ta zube a jikinshi tanata mishi shagwaba,shi ko duk yabi ya sukurkuce Mata Dan a rayuwa Yana son mace Mai shagwaba,Dan haka ya kyaleta suka ta shan shagalinsu har bacci ya dauke Dije.

*******

Yau Akayi sunan Yusrah,inda yaro yaci sunan Daddy wato,(Khamees) suna kiransa da sudais,sosai akayi shagali,kowa yayi rawar gani,domin kuwa yaro yaga gata,su mamy da Daddy sun yi rawar gani hakama Habeeb,bare Kuma angon karni.Sosai su Dije suka dau wanka,ansha pic kala-kala,sai muce Allah ya Raya sudais.

*****

Yau kwana biyu da yin suna, Alhamdulillih! Jikin Dije ta Dan ji dadin shi ko Dan treatment din data Samu kwana biyu,zata iya cewa tun ranar da Sajida ta shigo part dinta basu Kara haduwa ba,sai ranar suna, tasan abinda tayi matan Nan ne yasa ta yin shuru kwana biyu,Kuma dama tana sane tayi hakan,gobe ma ta Kuma.

Tana zaune ita kadai,taji duk zaman ya dameta,gashi mama mariya Bata Nan,Dan taje gida wani biki da akeyi,Wanda su kansu su Dijen su so zuwa Amma kememe mazajen suka hanasu,ganin ta gaji da zaman ita kadai gashi Sha biyu ne yanzu na rana,Dan haka ta yanke shawarar tafiya gurin Zainab Dan ta Dan rage lokaci,fitowarta kenan tana shirin rufe kofa ta tsinkayo tahowar Sajida ta nufota,dakatawa tayi da rufe kofar inda dai-dai Nan ta karaso,tana isowa Dije tace,

"Ah Aunty,kece mu shiga Mana",duk da tasan da akwai abinda ya kawota,Amma ganin Bata Nuna ba yasa itama ta bita hakan,ba yabo ba fallasa suka shiga,inda Sajida tana shiga gadan- gadan ta nufi gaban T.V din dake manne a bango,ga mamakin Dije gani tayi Sajida ta fito da muciya daga jikinta tahau farfasa kayan wajen,duk abinda takeyi Dije na kallonta Bata Kuma yi yunkurin hanata ba,Saida ta tabbatar ta fasa duk wani abu datasan zai fashe,sannan ta tako zuwa gaban Dije,wani shu'umin murmushi ta sakarma Dije kafin ta juya tace,kinyi kuskure khadeeja,Habeeb na Sajida ne ita kadai,naso kin bar gidan Nan salin alin tun kan na Nuna Miki kalata,Amma Naga bakyajin magana,kin samu guri kin mike kafafu,to ki sani kishi da mace kamar Ni ba abune Mai sauki ba,Dan haka ki jira abinda zai biyo baya,tana Gama fadar hakan ta juya ta fice,yayin databar Dije tsaye da tsabar takaicin barnar da tayi mata.

Zama tayi saman kujera,tare da dafe kanta,yayin da takejin wani tukukin bakin ciki na taso Mata,bawai na komai ba,sai na barnar da Sajida tayi Mata,amma babu komai wallahi zata San tayi.

Ji tayi an turo kofar da sauri,yayin data tashi a firgice tana kallon kofar,Habeeb ne sai Sajida a bayanshi,gani tayi Yana Binta da kallo,inda ita Kuma ta maida kallonta ga Sajida,gani tayi ta sakar Mata murmushi,a ranta tace,hmmmm! Na fuskanci baki sanni banne har yanzu kalata Daya Kika sani Bari na Nuna Miki na biyun,Habeeb na shirin yin magana,yaji Dije tace,

"Haba Dan Allah Aunty! Yanzu Saida Kika fada Masa duk abinda ya faru? Kin San halinsa yanzu hankalinshi zai tashi,shiyasa nace kada ki fada Masa Dan nasan halin sa yanzu zai damu,Ni Kuma bana son ganinshi cikin damuwa,kin San masu irin lalurar mu in ta taso barna mukeyi,Ni yanzu babbar damuwata ma Bai wuce tunanin wace barna zasu sani nayi Nan gaba ba,gashi bani kadai ba,Kar su sa mafarki da burin mijina ya zube,amma Dan Allah Yaya kodaa sun taso kaga nafara barna,kada ayi kokarin hanani Dan nasan bazasu cutar Dani ba,ke Kuma Aunty pls Dan Allah kidaina sanar da Yaya irin wannan lamarin,Kinga mijin mu ne ya fita nema,Bai kamata mu dinga daga Masa hankali ba, yakamata mu dinga Masa addu'ane a duk lokacin da ya fita,Dan haka Yaya ka kwantar da hankalinka ba abinda ya faru banji ciwo ba garin fashe-fashen Ina lafiya baby'nka ma lafiya yake,takร rasa makaganar tana Kama hannun Habeeb tare da dorawa saman cikinta ta shiga yawo dashi.......

Dan Allah ku Kara hakuri,Ni kaina na Matsu na Gama muku book din Nan wallahi.

*Alkalamin khady* โœ
[7/9, 9:02 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
AWESOME WRITER'S ASSO..
( place of excitation n'd pleasant writer's)

TAME GARI

NA
Khadeeja Usman

6โƒฃ2โƒฃ

Sosai ta shiga tashin hankali da Jin kalaman Dije na karshe,Wanda tsananin firgita da jinsu yasa mamaki da Kuma takaicin maganganun yarinyar na farko suka bace a kwakwalwarta,kalaman Habeeb ne suka dawo da ita daga duniyar tashin hankalin data fada,ji tayi Yana fadin,

"Haba baby! Meyasa haka? Nidai zan iya jurar komai a wannan larurar taki,Amma bazan juri salwantar unborn dina ba,Dan haka ya Zama wajibi muje gurin masu magani Dan a rabaki dasu,Dan Kar wataran su cutarmin dake".

Shigewa tayi jikinsa,inda cikin sigar shagawa tace,
"Ah ah my Yaya! Kada ka Kara furta cewa zaka rabani da su,Dan idan sukaji ka wallahi sai wani bakai ba,Dan kasan dai fada da aljani ba Dadi,kawai dai sukan sauke fushinsu ne akan abinda ya Bata musu,Amma ka taba gani sun cutar Dani"?

Yana shirin yin magana,ta Dora yatsanta saman bakinsa shhhhhh....alamun yayi shuru,kada kace komai Yaya,Dan maganar daka fada dazu na batun rabani dasu ma,sun ruga da sunji komai,Dan haka sai nayi yaki wajen Basu hakuri.Tunda yaji ta furta haka ya wani canja kalar fuskarshi ya koma kalar tausayi,tare da fadin Dan Allah baby ki Basu hakuri wallahi nasan karonmu dasu ba Dadi,bisa kuskure na furta kalaman rabaku,ban San tare aka haifeku ba,wallahi ban son tuna ba......"

Katseshi tayi ta hanyar fadin, "kada ka damu yaya,ai Kai na jikina ne yanzu bakada matsala dasu,Dan sun Riga da sun sanka,sun San matsayinka a gurina,Nidai tunanina kawai wannan barnan ya za'ayi a gyarata? Tayi maganar cikin sigar tambaaya.

"Baby wannan duk ba wata matsala bace kada ki damu,yau za'a canza wasu insha Allah, bari ma na Kira wasu collogue na wani company da suka shirya Mana office dinmu su zo suga yadda za'a Kara tsara wurin kinji,fatana Allah yabaki lafiya.

"Ameen yayana!Dije ta fada tana me kashewa Sajida ido Daya,wadda ya zuwa yanzu Sam Bata fahimtar wani abu da sukayi, maganar cikin Dije ita ta tsaya Mata arai,dawowar tunaninta, shine yayi dai-dai da kashe Mata ido Daya da Dije tayi,gani sukayi ta juya ta fice tare da fashewa da kuka.Dukan su basusan dalilin kukan ba,ita dai Dije abinda ta bari, tana kukan ne Dan ganin batayi nasara ba,duk da batasan me ta fadawa Habeeb ba,illah dai tayi farin cikin kashe gobarar datayi duk da batasan mafarin tashin ta ba.

Ajiyar zuciya ta sauke,tare da fadin,

"Yayana pls kaje kaji matsalar Aunty,kaga ta fita tana kuka,ta karasa maganar tana shafar gefen fuskarshi,Kama hannun nata yayi ya sumbata kafin yace,

"Ki kula da kanki kada ki taka kwalba,zan Kira yanzu zansa a gyara.

********

Yana shiga ya isketa tana kuka,ya jima tsaye sannan ya karasa saman kujerar,tallafo ta yayi zuwa jikinshi,amma me? Saita shiga zamewa,tare da buge hannunshi,cike da mamakin abinda tayi mishi ya tsaya Yana kallonta.A nata bangaren kuwa,tsananin takaici da wata irin tsanar shi taji ya ratsa zuciyarta,gani takeyi yaci amanarta,tunda har yayiwa Dije ciki,gani takeyi ya daina sonta kwata-kwata,Dan haka ta Kara tsananta kukanta,shiko yama rasa me zai ce Mata,Dan haka ya zuba Mata ido kawai Yana kallonta.

Itako saka kawai takeyi da warwara Dan batasan ma abinda zata yi ba tukun,duk wani abu data kulla akan yarinyar Saiya warware,ta dauka Kiran Habeeb da tayi ta fada Masa cewar yazo ga Dije Nan aljanunta sun tashi harta farfasa kayan dakinta,ta dauka zatayi nasara Habeeb ya Kora Dije gida,tunda yasan wahalar da suka Sha a gidan da ita,Amma Kuma sai labari yasha bambam ta tonowa kanta abinda zai iya zamar Mata ciwon zuciya.

Ganin taki daina kukan ne,Kuma taki bashi damar jin matsalarta, yasashi tashi ya fita Dan
Yin abinda ke gabansa.

Yana fita ta Kara fashewa da kuka,tare da daukar waya ta Kira mahaifiyar ta,tana dayawa cikin kuka tafara fadin,

"Na shiga uku mummy! Na mutu, wallahi mummy I will die, she's pregnant mummy"!

Cikin sanyin murya tace,
"Kinga ki nutsu kiyimin bayanin abinda ke faruwa,Dan ban fahimci inda maganar taki ta dosa ba?

Cikin Kuka ta labartawa mahaifiyar ta abinda yake faruwa.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace,

"Sajida abinda zance dake yanzu shine,kawai kiyi hakuri,kiyi naki 'yan dabarun,Dan wallahi Ni kaina Ina cikin matsala,Dan mahaifinku Ashe ya Dade da yin aure a boye ban sani ba,duk tafiye tafiyen dayake cewa yanayi Ashe suna tare,jiya da daddare sai gashi ya dawo tare da matar harda yara hudu Kuma duk maza,Ni gashi duk taronku Mata Allah ya bani,Kuma ke kadai nasamu Kika auru,Dan haka kiji da kashe taki wutar nima inyi kokarin neman ruwan kashe tawa,tana kaiwa Nan ta kashe wayar.

Wani kukan takara dasawa zuwa can ta mike,tare da share hawayen ta,tabbas zata dau mataki,babu macen data Isa ta haihu da Habeeb,tunda ta tabbatar yanzu ba ita ba haihuwa,yanzu wazai Bata shawarar? Wa take dashi yanzu,Dan ita Sam Bata wani damu da Jin auren mahaifinsu ba,Dan dama ai yasaba,Banda abin mummy ma meye na wani kishi!( Niko nace hmmmm sajida ai shi kishi ba ruwanshi da tsufa... Fata dai ayi Mai hankali da tsafta.)

Haka ta gaji ta mike ta shiga nemarwa kanta mafita.

*******

Tunda safe take leke ta window tana Allah-Allah Habeeb ya fita,Dan yau dakin sajida yake,sai wajen karfe goma sannan taga ya fito,cikin shigarshi ta manyan kaya dinkin zamani,yayi Mata matukar kyau,sai dai fa yau bataga Yar kadaferiรฑ anzo yin rakiya ba,ko lfy oho musu! Ita dai burinta ya fitan,sai da taga megadi ya bude Masa kofa ya fita itama ta koma ta Kara kimtsawa.

๐Ÿ˜ณ Karamar jaka trolly Naga Dije ta jawo,kome zatayi da ita oho?

Direct part din Sajida ta nufa,tana zuwa ta tura kofar,zaune ta ganta kan kujera ta Dora kafa Daya kan Daya tana yin breakfast,Jin an bude Kofa yasata maida hankalinta ga kofar Dan a tunaninta ma Laila ce da sukayi zata zo yanzu.

Kallon Dije tayi data Sha dogon hijabi har kasa,sannan ta tsaya Mata a ka ta rike kugu da duka hannunta biyu sai wani zare Mata ido takeyi,cikin ko in kula tace "malama ke Kuma lfy? Kika zo kikayi ma mutane tsaye a ka".

Hmmm "lafiyar kenan! Dama zuwa nayi na Dan taba kuruciya,Dan na kwana biyu ban tuna baya ba".

"Kamar Yaya kenan?

"Kada ki damu, zuba ido kiyi kallo,gani tayi Dije ta cire hijabin jikinta,ai da sauri Sajida ta mike,ganin Dije saye da biri da wando Kuma tied,Bata Kara sarewa ba Saida taga Dije ta zuge jakar data shigo da ita,muciya ce da tabaryar karfe,ludayin Miya pock,da duk wani abu mai kalar makami,Dan haka ta mike da sauri tayi bayan kujera tana fadin,na shiga uku,yau Yan daba ne suka hauro,tana tsaka da haka taji karar bude Kofa,Laila ce ta shigo ta mayar da kofa ta rufe harda sa key,Wai Dan Kar wani ya shigo asami akasi yaji sirrin da zasu Tattauna akai,da takun kasaita ta karaso falon wadda sai yanzu idonta ya sauka akan Dije dake tsugunne tana fidda kayan aiki.

Waigawa tayi ta hango Sajida make bayan kujera,alama Sajida take Mata da Dije,hakan yasa ta dau haske,inda take cikinta yabada kuuuuuuuu ...Dan Bata Manta karon wancan lokacin ba,kamar barauniya a hankali ta zame takalmin kafarta ta lallaba Sadaf Sadaf ta nufi mabuyar sajida.

Duk abinda sukeyi Dije na kallonsu Amma ta share,tabaryar da muciya ta dauka,inda ta shiga aiki kamar yadda sajida tayi Mata,sosai tayi barna itama har Saida ta gaji,su kuwa su Sajida da zarar sunji karar fashewar abu sai su Kara curewa waje Daya.

Zama tayi tana maida numfashi,sannan ta Fara magana tana fadin,yanzu aiki ya kammala saura yiwa bil'adama bille,

Jin abinda tace yasa su Sajida rudewa da neman mabuyar datafi ta inda suke,kansu ne ya hadu ji kake kummmmmm, kowacce hannunta tasa ta toshe bakinta tare da matso kwallar azaba,a cikin wannan halin Sajida tayiwa Laila alamar ta Bata wayarta,da kyar ta lalubo ta cikin hand bag ta Mika Mata, number Habeeb tasaka ta shiga kiranshi cikin rudewa,Kira wajen biyar tayi Masa amma Bai dauka ba Nan ta Kara tsinkayo muryar Dije tana fadin yauwa Bari mu tashi mu Fara aiki Dan mu kammala da wuri,saboda yau zamuyiwa Mai martaba gyaran fuska.........

*Alkalamin khady* โœ
[7/9, 9:03 AM] El~hajj: ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
*AWESOME WRITER'S ASSO....*
( _Palace of excitation n'd pleasant writer's_)

*TAME GARI*
NA
Khadeeja Usman

6โƒฃ3โƒฃ

Banda zufa ba abinda ke karyo musu gaba dayansu,wayar ta sake Kira tare da fadin "Dan Allah ka dauka Mana",tana Fadi tana yarfa hannu,harta Kiran ya Kara yankewa Bai dauka ba,Nan suka Kara jiyo muryar Dije tana fadin,
"Wai Kuna inane,Akuyatu"?kuyi sauri ku Kira su aunty arwanatu,da Yaya lugudanatu,ke nama Manta in ki biya ku taho da tumakatu 'yar sarkin wanzamai,da kawu kwaya-kwaya Dan Naga yafi iya irin na zamani,ku iso da wuri Dan Allah Kar Mai martaba ya gaji da jira ya Fara tsinke gashinshi da hannunshi.
Sosai cikin sajida ya bada wani sauti,ji kake kuuuuuuuu.....kallonta takai ga Laila taga yadda ta hada zufa ga wani marayan kuka da takeyi,tasa hannunta ta toshe bakinta,da sauri Sajida ta Kara Danna lambar Habeeb Allah Allah takeyi ya dauka.
Shikuwa Habeeb silent yasa wayarsa ya shiga wata tearter ne,kuma koda ya fito ya Manta Bai maidata normal ba,sai zuwa can ya tuna ya daukota,Yana daukowa Kiran sajida na katsewa, kasancewar bayada number,yasa shi niyyar sharewa,Amma Kuma Saiya ga missed calls Kuma da number,hakan yasa shi tunanin Kiran number yaji ko waye,Yana Kira kuwa yaji muryar sajida cikin tashin hankali tana fadin,
"Please Habeeb come and help us,wlh zata kashemu,Wai bille zatayi mana,Dan Allah ka taimaka kazo Yan......Bai ko karasa Jin abinda take fadiba yaji wayar ta yanke.Cikin kidima ya fito a office,kacibis sukayi da Naseer ya shiga tambayarshi lfy?,Sam yakasa bashi amsa illah fada mishi da yakeyi sun zo...sun kawo ziyara,cike da rashin fahimtar idan maganar sa ta dosa ya kalleshi Dan neman Karin bayani,Amma Ina! Har yakai parking space ya shiga mota,cike da mamaki yabi bayanshi shima a tashi motar, kasancewar ba Wanda yasan abinda ke faruwa a gidan hakan yasa kowa dayaji irin horn din da ake bugawa hankalinsu ya tashi,duk suka firfito suka tsaya Jin Mai zai faru.
Direct part din Sajida suka ga Habeeb ya nufa a guje,kowa Saiya rufa Masa baya,gani sukayi ya tsaya cakkkk....kome ya tuna oho?
Baya yayi sannan ya jawo Naseer ya tura shi gaba tare da fadin,
"Please bros ka taimaka ka shiga wallahi mutanen khadeeja ne suka tashi sun rutsa Sajida a ciki,ban San meke faruwa ba,Dan tunanina kada Susa tayi abinda zai Kai ga salwantar abinda ke cikinta,kaga ba ita kadai ba......katseshi yayi ta hanyar fadin,
"Ai wallahi Inka ganni a lahira kaini akayi,ka Manta irin azabar da muka Sha,sannan kakemin maganar Wai in shiga to Kai me zai Hana ka shiga tunda matarka ce a sunfi saninka a kaina"....
"Ba Wai batun haka bane,kaga Kai ka fini abin Nan shine nace,me zai hana Kai din ka shiga Inya so in kaga abinda ke wakana saika kiramu" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka.
"Anki shiga din' nace Anki shiga din,wato Kai kaki Ni ka turani,toh Baga su mamy ba,su shiga Mana Dan ban San a yanayin daka iya riskarsu ba,Dan haka su da suke mata,Kuma manyanmu,su Fara shiga kawai mugani.
"Dan uwarka bazan shiga ba,Ni nace yaje ya auro irin aljanu,aiga 'yar uwarta Nan ita ta shigan Mana,sai Ni ko,salon a je a hada Dani tunda kun gaji da ganina to alkur'an ba inda zani,Jin muryar su mamy na tashi yasa su Sajida bare baki tare da sakin ihu.Sosai Habeeb ya Kara kidimewa,inda ya nufi kofar kamar gaske,Yana tabawa yajita Gam,Dan haka ya shiga murzawa,
Muryar Dije ya jiyo tana fadin,an Gama ranka ya Dade za'a hada harda na wajenma,ai da gudu Habeeb ya kwasa ya nufi bakin gate su mamy ma duka suka rufa Masa baya,suna kaiwa Nan suka tsaya maida numfashi,mamy ce cikin mayar da numfashi ta shiga tambayarshi meya sa shi gudu,?
Shima cikin haki yace, cewa sukayi Wai a hada damu".
Dafe kirji mamy tayi tare da fadin,

"Me za'a hada damu din?

"Nima ban sani ba,Amma Inaga salon azabar su ne na aljanu".

"Oh ni karima na shiga uku Wai ma waya tabosu ne?"

"Wallahi mama Inaga sajida ce Dan ga motar kawarta nana da alama tare suka jangwalo su".
To basai abin ya Kare akansu ba mu miye namu a ciki,cewar yusra dake kokarin sauke Sudais tana mikawa Naseer, Zainab ce tace ai kun San lamarin iska,su kan me uwa da wabi sukeyi.Haka dai suka tsaya curko curko,ganin hakan yasa baba Mai gadi ya karaso tare da tambayar su meke faruwa,sosai suka Masa bayani,inda ya tayasu jimami tare da fadin akwai shawara in kun amince,me zai Hana maza fade ta muji.
" Dama nace Mai zai Hana a kirawo irin malaman Nan masu rukiya! Kwarai kuwa ka kawo shawara cewar mamy Bari na Kira malam buba,ai ko tsayawa batayi taji me zasu ce ba ta matsawa malam buba Kira,Yana dayawa ta sanar dashi ya zo gidanta ba lafiya zai cire aljanu,Nan yace Mata Yana zuwa.

Sadaf Sadaf suka dinga tafiya kamar barayi,har suka karasa bakin kofar,suna zuwa da kyar Habeeb ya Dan matsa ta gefen window Wai ko zai gano wani abu,Amma ba halin ganin Dan ko Ina a rufe yake ruf,

su kuwa su Sajida,suna can Banda kuka ba abinda ba sukeyi, musamman da sukaji Dije na cewa a hada Dana wajen ai duk sai suka Kara karaya.

Itako Dije Saida ta tabbatar ta huta sannan ta yunkura tare da fadin,Yaya gurguwa tashi muje mu Fara kaddamar da aikinmu,tana mikewa ta shagide kafa da mere baki ta dauko lafciciyar wukar Nan ta cikin set din wukake,wato ta Sara Kashi,ta nufi bayan kujerar,Sajida data Dan zuro Kai Wai taga ya ake ciki taga Dije a haka ai saita mike tayi tsalle saman kujera,hakama laila,Nan suka shiga zagaya falon,itako Dije dada karkacewa ma takeyi tana fadin,haba bil-adam ku tsaya Mana ayi muku komai cikin sauki,na yantse a hankayi janyi muku,Kuma bajan bayi jininku ya juba a kasha ba duk Jan lashe.....wata uwar sufa Sajida tayi Saida hannunta ya bugu,Amma Bata ko tsaya Jin zafin da taji ba ta nufi kofa Allah ya Bata sa'a ta murza key ta bude,tana fitowa su Kuma saiga su mamy da malam buba............

๐Ÿค”

To fa me zai faru kuma gaba! Ga malam ga aljanun Dije

๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ

*NIDAI BA RUWANA YASEEN*

*ALKALAMIN KHADY* โœ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€
AWESOME WRITER'S ASSO..
( Palace of excitation n'd pleasant writer's)

TAME GARI
NA
khadeeja Usman

hakika duk inda masoyi yake yanada Dadi,masoyana kune abin alfaharina, khadeeja novel fans daga 1 har zuwa 10 na yaba da kokarin comments dinku,da sauran group din da nake ciki,Ina alfahari da dukan masoya tame gari nagode sosai masoyana ๐Ÿ˜˜



6โƒฃ4โƒฃ


Yana gaba su mamy na binsa a baya kamar barayi,itako Dije sunata faman zagaye ita da Laila a falon,Dan cewa tayi an Kara musu karfin hukunci yanzu Kam harda aski za'a musu,umarni ne daga Mai martaba.


Ganin shigowar su mamy,yasa Laila wage baki iya karfinta tana ihu,tana Kiran azo a taimaka Mata,Wanda sai a wannan lokacin Dije ta ankare da jama'ar da suka hallara a falon.Ji tayi ance malam gata Nan cewar mamy tana Nuna Dije,itako Dije ganin haka yasata sulalewa kasa tare da rufe ido Wai ita ta Suma.

Shi kuwa malam tunda ya kyalla ido yaga Dije Fara tas da ita,gashi tayi 'yar kubul- kubul,fatar ta sai sheki takeyi,saboda jaririn cikin dake jikinta,hakan yasashi lasar baki kamar tsohon maye, musamman Daya Kai duba zuwa kirjinta ganin yadda yake cike.


Juyowa yayi ya fuskanci su mamy tare da fadin,"gaskiya Hajiya lamarin

Please Login or Register in order to submit comment