Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lomar shinkafa bakinsa,miqewa tayi zata wuce dakinsu,sai kuma ta fasa taga gwara tasoma sauke nauyin bashin kudin umma katti a kanta,saboda haka tasauya akalarta zuwa dakin nata,dai dai lokacin da baban nata ya qwalawa umman kira yana cewa
"Kattime....kinga...gwara ki fito ki sake abinki,kici kazarki kisha jar miya ki godewa Allah da budin daya kawo yau"
Wani mugun tsaki ta saki sanda bilkisu ke saka kai dakin
"Ka hutar da yawun bakinka,aiba saika fada ba abinci zancishi,tunda haƙƙina ne Allah ya ƙwata yabani yau,amma duk wani iyayinka da ɗigiminka na riga dana daɗe da haddacesu,jiya bayau bafa,nasan dai ƙarshen alawa qasa,to mu zuba mugani,Allah ya bada sa'a" ta qarashe zancan tana dukan cinya gamida zunkuda zamanta,da alama masifa tana cinta.


Sallamar bilkisun ma sama sama ta amsa mata,bata bata dukka hankalinta ba sai dataji da biyan bashi tazo mata,saita maida kai sukayi lissafi ta cire mata kuÉ—inta,tasa hannu kuwa ta amshe abinta ta linke kana ta tura mata kwanon abinci har guda biyu,daya shinkafa daya miya
"Ga naki kason nan,yau Allah yayi babu kwanan yunwa" umma kattin ta fada tana sake gyara boyon kudinta,da kallo tabi kwanukan,ita sam ko daya abincin bai bata wani sha'awa ko armashin ci ba,saboda ba umma katti ba,ko ita tasoma shanshano abinda ke shirin faruwa cikin gidan,wata ƙila ma nan da wasu 'yan kwanaki masu zuwa
"Allah ya amfana" kawai ta fada tana É—iban kwanukan tafice zuwa dakinsu,yaran na ganin fitowarta kuwa dukka suka bita daki sukabar baban anan,don dama ba wani sabo ko shaquwa bane tsakaninsa dasu.


Kaya tacanxa ta ninke wadancan don sune nadan fitar sannan taxauna sosai tajawo kanukan tasoma budewa,dai dai lokacin da amina wadda itace qarama a cikinsu tace
"Yaaya yau abincin yayi dadi wallahi,hadda naman zakara irin na gidansu hasana" ta qarashe maganar alamun walwala da annashuwa na bayyana muraran saman fuskarta,sai murmushi ya subewa bilkisun,yayin da hauwa hannatu da umaima suka sanya dariya
"Wai kice aikin babba ne aminatu,zakara ne bama kaxa ba"sai a sannan maganar ta bawa yarinyar dariya itama
"Ku matso maza musake ci" hannatu ta zaro ido tana sha cikinta
"Ai yaaya duk cikinmu yau ba wanda baiyi mugun qoshi ba,ni har amai nake ji wallahi,saboda nayita cine ina hutawa,don bansan yaushe zamu sake qoshi haka ba" da qaramin murmushi mai dauke da tausayi take dubansu sannan tace
"Bakin da Allah ya tsaga ai baya hanashi abinci hannatu" daga haka taja abincin tana ci,jifa jifa suna hira tana tattambayarsu abubuwan da suka faru bayan bata nan,da yake haka dabi'arta take,idan tadawo cikin hikima a cikin hira take bugar cikinsu wasu abubuwan,wanda anan ne idan taji wani kuskure da wani yayi ko ba daidai ba saita gyara mishi kota tsawatar masa.


"Ya akayi ne hauwa kuluwa?" Bilkisu tafada sanda take gama cin abincin da tsakurarsa kawai tayi ta ture,saita sauke hannun daga tagumin datayi tana murmushi
"Yaaya,duk kin fimu kyau,sai nadinga ji dama nice ke" murmushi mai sauti ya subuce mata,har fararen jerarrun haqoranta suka bayyana
"Toh?,yau kuma hauwa'u"
"Nima yaaya,na dade ina gani,ko qawayena idan sukazo sai suyita kallonki,suce kamar ba gidanmu daya ba,waike kin fimu kyau,kalar 'yan gayu dake" hannatu tayi nata sharhin daya sanya bilkisu dariya dole,sai data tsagaita sannan tace
"Kuma duka masu kyaune hauwa'u,bakigama ke 'yar fillo bace,gashinki ma yafi nawa santsi dakyau,kema hannatu baki kallon mudubi?" Maganar saita dan jefa yarinyar cikin tunani
"Yaaya" takira sunan bilkisu a sanyaye wanda hakan yayi calling attention na bilkisun sosai
"Na'am" ta amsa mata da dukka hankalinta
"Da gaske ni 'yar fulani ce?,amma ban taba ganin mamana ko 'yan uwanmu ba,tunda mamana ta tafi ban sake ganinta ba,kodai bazan sake ganinta ba yaaya,ko itama mutuwa tayi kaman mamanki?" Shuru ya ratsa dakin,yarinyar na dubanta tana jiran amsa daga bakinta bilhaqqi,maganganun yarinyar sosai suka taba ranta,suka koma soso wani sashe maigirma na zuciyarta,tausayinta yasake ninkuwa a ranta.


Kama hannun yarinyar tayi a tausashe sannan tace
"Mamanki bata mutu ba tana nan da ranta,kullum tana tunaninki kuma tanason ta ganki,amma wataran saidai kawai ki ganta tazo ganin hauwanta" murmushi ya kubcewa yarinyar,cike da nuna zumudi da kuma fata mai tarin yawa tace
"Da gaske anty?"kai ta jinjina mata alamun tabbatarwa
"Da gaske jidda" sai farinciki ya mamaye fuskarta.


Da wannan hirar ranar suka kwanta,yayin da suka tadawa bilkisun tabo sosai cikin zuciyarta,don kowanne yanuna sha'awa dason ganin mahaifiyarsa,inama ace itama zata samu dama koda sau daya taga tata uwar,ta zanta da ita ko sau dayane kuwa?,tausayin yaran take wani lokaci fiye da kanta,don gwara ita tasan dukkan wanda yamutu haihata haihata shida dawowa doron duniya,amma sufa?,ta qyamaci halin mahaifinta dakan raba yaran da iyayensu yakuma kasa riqesu yadda yakamata,yayin da wasu daga cikinsu iyayen ne a karan kansu suke fushi saboda abinda mahaifinsu ya aikata su watsar da yaran.


A daren ranar sai datayi kuka sosai kafin bacci yayi awon gaba da ita.


☀ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸


*MASARAUTAR KAISA*


Kamar yadda muka fada a baya babbar masarauta ce mai cike da iko mulki da wata cikakkiyar izza,tun shekarun masu tsaho da suka shude a baya har kawo yau,wanda tana gogayya da dukkan masarautun da suke maqwabtanta dama na nesa da ita,masarauta ce data cika ta tumbatsa da wani irin salo na mulki mai cike da adalci da qasaita na daban uwa uba kwarjini da daukaka da Allah yayi mata.


Babbar masarauta ce wadda take da fadin qasa,tarin al'umma,kaisa garine da yayi iyaka da kano da jigawa,garine mai albarka noma da kiwo,hakanan al'ummar ciki na rayuwa ne qarqashin adalin sarkinsu maimartaba sarki Abdallah mu'az nuhu kaisa,wanda tun tale tale na kafuwar garin mulkin garin a hannunsu yake,shi kansa gadon gado yayi daga iyaye da kakanni.


Gidan sarautar kaisa babban gidane wanda zaka iya kiranshi kai tsaye da gari guda,mai dauke da sassa sassa bisa tsari da fasali tun daga farkon gidan, gidajen ƙananun bayi da manyansu,bayi,masu qananun muqami da matsaikaita,securities na gidan wasu daga cikin dogarawa da sauran hadimai na gidan,haka tsarin yake daki daki har zuwa ainihin unguwar da matan sarki suke da iyalanshi da sauran makusanta.


Sarki Abdallah adalin sarki ne wanda al'ummar garinsa kejin dadin mulkinsa qwarai da gaske,yana da tausayi ga talakawanshi,mutum ne mai sauqin kai duk da awasu al'amurran bashi da sauqi ko kadan,hakanan kaifi daya ne shi,magana daya yake babu canji,mutum ne mai qoqarin riqo da addini duk da cewa yayi karatun boko.mai zurfi,don kafin zamowarshi sarki ya riqe muqamai iri daban daban masu tarin yawa,tun daga qananu zuwa manya,don har ambassador ya tabayi,kafin daga bisani yadawo gida bayan Allah ya yiwa mahaifinsa rasuwa ya amshi sarautar garinsu.


Sarki Abdallah nada matan aure hudu,ta hudun da ya aura bayan zamowarshi sariki ta rasu bayan ta haifi yarinya daya dashi,matarshi ta farko hajiya saratu ya aureta ne tun kafin zamowarshi sarki,a lokacin yana ministern mai na qasa,wanda basu jima sosai da ita ba don haihuwarta biyu Allah yayi haduwarshi da mayarsa ta biyu haj adama,wanda sun dan zauna zaman kishi lokaci maidan tsaho kafin Allah yasake yin aurenshi da Aishatulhumaira,a lokacin yana ambassador a qasar mali,diyar sarautar qasar itama kamar yadda yake.


Tun haduwarshi da ita tashiga zuciyarsa qwarai da gaske takuma tafi dashi,saboda wani irin kyau da Allah yayiwa aishan,kowa yasan yadda kalar fatarsu da yanayin kyansu yake wanda yake dan zubi da na ethopian's,uwa uba jan aji da shan qamshinta wanda ya amsheta qwarai yakuma dace da matsayinta,wata irin mace ce da Allah ya zuba mata kwarjini da farinjinin manema,don shi kansa a sannan sai daya danci wuya kafin yasameta.


Sai neman auren aishan yazama wani abu na daban wajen haj saratu da adama,tun daga sanda sukayi binciken kan wacece aishan hankalinsu yatashi qwarai da gaske,suka kasa sukuni saboda sunga cewa tako ina tafisu,sannan shi kansa mai gayya mai aikin sun fahimci kamar yana zumudin abun,duk da yadda yake qoqarin boyewa da dannewa,duk ta yadda zasu shiga a fasa abu ya faskara yaci tura,tilas daga qarshe dai suka shirya plan na tararshi gaba da gaba,suka sameshi a falo yana hutawa suka tada mishi maganar,yayi qoqarin fahimtar dasu da lallashinsu amma suka toge,daga qarshe ma suka sanya masa kuka hajiya saratu tace
"Kawai dai duka take takenka mun gane ,mun fahimci inda kasa gaba kuma mun fahimci me kake nufi,saboda Allah yabamu haihuwar 'ya'ya mata bamu haifan maka maza saboda kana sakaran ka amshi sarauta kana neman magaji tun yanzu,to ai muma bamu muka baiwa kanmu ba,kuma cikin daya haifi 'ya mace shi zai haifi da namiji" shuru yayi na mamakin kalamanta,sabodashi sam ko sau daya ma bai taba darsa wannan tunanin cikin ranshi ba,saboda babu wanda yasan gawar fari sai Allah,shi kanshi mai martaba a sannan yana nan da ranshi bai mutu ba bare yayi wani tunanin mulki.


Idanu kawai ya zuba musu,suka dinga tashin hankali kala kala har akayi auren,yabar aisha a qasarsu saboda shima a sannan yana can yana aikinsa,sam ita aishan bata damu dasu ba,duk da tana da kishi tana kishin mijinta saboda yadda take sonshi amma ko zancansu bata masa,taja mutuncinta sosai,tun bata fahimci yadda suke kishi da ita ba harta gane,saboda haka tasan halin kowacce cikinsu duk daba qasa daya suke ba,kuma abdallah baya mata zancan kowacce cikinsu amma ta fahimci kowa,macace mai matuqar saurin gano abu,kaifin basira da hangen nesa,yanayin yadda abubuwa ke gudana idan yakoma can wajensu kawai ya isa ya bayyana mata komai.


Basu sassauta kishinsu a kanta ba sai datayi haihuwar fari itama tasamu diya mace,kai kaga walwala da sakin jiki,harma suka yanke haj saratu zataje har can mali barka da taron suna,shi kansa yayi mamakin yadda suka sake din,amma bai kawo komai a ranshi ba donshi bai saka zancan haihuwar mata ko maza a wani babin ba,hasalima ya manta taqaddamar da sukayi dasu lokacin auren aishan,sai yayi murna sosai saboda yana tunanin sun sassauto ne saboda zuri'a da aka soma hadawa.



Haka kuwa akayi,ta shirya tsaf tayi siyayya ta alfarma suka tafi da duka yaran su hudu,nata biyu nimra da zunaira,sai na adama biyu Aafiya da afra.


Gidansu aisha gida ne na karamci suma,saboda haka tasamu saukar girma data sake sanyata ta bambance aya da tsakuwa,bugu da qari duka yadda suke hasashe ashe abun yawuce hasashen nasu,don yadda taga anata hidimar bikin sunan jaririyar cikin gidan nasu,aishan 'yar gata ce gaba da baya.


Tunda tazo suka gaisa aka kai mata yarinyar bata kuma bari sun hadu ba,saidai duk wani abu daya kamata ayiwa baqo dama wanda bai zama dole ba duka an yiwa saratun,takuma aiko aka mata godiyar kayan barka,saidai a jikinta taji cewa ba zuwan Allah tayi ba,to koma mene batajin zata bari kota yarda a cutar mata da diya,don tun sanda ta haifeta take mata mugun so.


Yadda saratu tazo data tashi komawa saiya zaman gwiwa kusan a sanyaye,don ta ganewa kanta abubuwa masu yawa,ciki kuwa harda kyau da Allah ya yiwa yarinyar na daban,ga uwa uba gatan data gani ana nuna musu,koda ta dawo ta baiwa adama labari sai sukayi zugum,inda daga qarshe adaman ta katse tattaunawar tasu da cewa
"Koma meye dai mu godewa Allah data yiwo mu,don inda namijine kuma saita Allahu,sai abinda idanuwanmu suka gani kenan".


Tafi tafi haka rayuwa ta dinga tafiya har zuwa sanda maimartaba ya kwanta ciwo,wanda ciwon nashi kusan shine silar daya sanya abdallah ajiye aikinsa na ambassador,yadawo gida gaba daya saboda shine babban danshi,wanda kuma sukagi shaquwa dashi fiye da kowa,wannan karon harda aisha itama tabiyo mijinta nigeria donta zauna dashi,a sannan dukka matan nashi ciki garesu,saidai akwai bambancin watanni,na saratu shine mai watanni bakwai,adama wata shida,yayin da aisha nata keda wata biyar,saboda tsayinta da yanayin shigarta yasama ba kowane ke lura dashi ba.


A wannan zaman da sukayi tare da sake karantar kowa tsaf ciki da bai,haka suma sun sake fahimtar tazarar data musu a zuciyar mijin,katsam saiga al'ummar gidanma kusan suna neman komawa qarqashinta,kasancewarta mai budadden hannu,ba baya bace wajen kyauta,duk da tarin izza da qasaitarta,duk da bata cika sakin fuska ko faran faran da jama'a ba,amma duka wannan bai damu mutane ba,da yake yanzun kusan kowa yafi ga abun hannun dan uwanshi.


A wannan lokacin tsakanin adama da da saratu kowa fafutukar ganin ya haifi da namiji yake a cikinsu,kudi suka dinga bararwa suna baiwa malamai na Allah daba na Allah ba ana abubuwa iri iri saboda su haifi namiji,gamida alqawura iri iri ga hadimansu na duk wanda yazama silar samun namiji a cikinsu zasu 'yantashi,masu 'yanci kuma zasu wadatashi,saboda kowacce tana ji a jikinta lokacine yayi da mijinsu zai karbi sarauta,wanda hakan ke nuna cewa abu na gab zuwa kansu.


Amma a zahiri idan sun hadu kowacce fata takewa 'yar uwarta nako itace tasamu babu komai,saidai kowanne ta qarqashin qasa akwai hadimansa dake masa aiki a sashen kowaccensu ba tare da kowannensu yasani ba.


Ta fannin aysha kuwa hankalinta a kwance yake,sabgarta kawai take da kula da mijinta,da kuna tayashi kulawa kan lalurar mahifinsa,sun tuttura mata sabbin fuska don su shiga jikinta kamarsu amma basu samu wannan damar ba,saboda halinta na dabanne ita,tana da matuqar wayo da takatsantsan,don haka ita basu da wani labari daya danganceta ko sassanta sai dan abinda ba'a rasa ba.


Wata biyu da dawowarsu a safiyar wata asabar saratu ta haihu,tashiga tashin hankali da matuqar girgiza sanda unguwar zoman dake amsar haihuwarsu ta shaida mata diya mace tasamu,babu jimawa labari ya karade gidan,ranar sashin nata tamkar zaman makoki akeyi,saboda kowa yasan yadda ta qwallafa rai akan da miji kuma bata samu ba,dukkanin hadimanta ranar kaffa kaffa suka dinga yi,babu wani mai qwaqqwaran motsi ko dariyar kirki,a haka labari yasamu adama,tayi rawa tayi shewa tayi juyi gaban mutanen da take gani amintattun tane,wadanda sune suka kawo mata labarin,saidai batasan cewa sune makasan nata ba,kana ta umarci hadimanta maza su shirya abinci mai rai da motsi a kaiwa saratu,itama tana bisa hanya.


Isar abincin da isarta sassan saratun ba wani tazara mai yawa,donta qagauta taje ta ganema idanunta
"Haka Allah yashirya,qaddararsa kenan" adaman ta fada cikin fuskar jimami sanda take zaune kusa da saratu wanda ke kashingide saman wata kujerar hutawa dake wani daki na musamman da aka kebe saboda hutawar.


Nannauyar ajiyar zuciya saratun ta saki,kana a hankali ta dora idanunta kan adaman,tuni labarin abinda tayi ya rigata isowa,saboda haka tar take kallonta,saita miqe tazauna sosai sannan tace
"Qaddararmu ce gaba dayanmu halan" saita san dakata tana ci gaba da duban adama tana shaqar numfashi sannan ta dora
"kuma na rantse da sarkin da babu wani saishi,indai ni saratu uwar gida ga Abdallah bani nasoma haifa mishi É—a namiji ba,babu matar da zata haifa É—a namiji cikin gidan nan".


Gaban adama yafadi tsoro yadan shigeta,kada fa yazamanto namiji ne a cikinta saratu ta aikata abinda zaisa yakoma mace,amma a zahiri saita dubeta duba na mamaki
"Tofa....kamar yaya,me kike nufi?" Sai data koma ta kashingida sannan ta bata amsa a taqaice
"Lokaci zai nuna" daga haka bata kuma tanka mata ba,saita aje mata yarinyar saitin qafafunta tamiqe tana cewa
"Lamarin ubangiji dai rubutacce ne,Allah ya qara lafiya,nina wuce" binta tayi da kallo,sai ta saki shu'umin murmushi
"Kinsan ubangiji ne adama?,muzuba mugani" ta fada cikin ranta,kana ta waiwaya tadubi yarinyar daketa bacci abinta batasan ma me ake ba,sai taji dama ta bude idanu ta ganta a matsayin d'a namiji ba mace ba,takirayi daya daga cikin barorinta tadauki 'yar ta maidata cikin gadonta.
7/11/21, 4:28 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRADIN RAYUWATA* 👑


*_wannan littafin na kudine,kuma AMANA ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data dace cikin nutsuwa sa kwanciyar hankali,babu cigiya babu a dauko mana,SIYI DA KUDINKI KISAN KEMA KIN ISA_*

0903 234 5899
KO
09033181070


6



Sanda abdallah yazo ganin É—iyarsa ya amsheta hannu bibbiyu cikin farinciki kamar sauran haihuwar,ba tare da nuna wani abu har fili da zuciyarshi,abinda yadan sake kwantar mata da hankali kenan,duk da burin dake ruruwa cikin zuciyarta wutarshi bata ragu ba bare ta mutu,taji alwashin duk tsiya duk runtsi itace zata fara samawa abdallah magaji ta kowacce hanya,ba zata taba bari wata cikinsu ta karbi wannan kambun ba.


Aisha kam sai bayan kwanaki uku da haihuwar sannan ta taka taje cikin rakiyar hadimanta wanda kusan dukkaninsu amintattun tane,saboda an hadasu ne da ita tun daga masarautarsu,qalilan ne wadanda suke haifaffun masarautar kaisa.


Tajewa da jaririya kyautar saitin gwal sarqa dan kunne abun hannu harda zobe da awarwaro,tun daga ranar bata sake komawa ba.
Suna akayi kamar yadda aka saba gagarumi,yarinya taci sunan sa'adiyya mahaifiyar saratun suna kiranta da walida,hakanan taci gaba da rainon walida tana zuba idanu kan cikin adama da aisha.


Kwanaki arba'in darda doriyar takwas akai itama adama ta haife nata cikin bayan sallar la'asar,itadinma Allah ya nuna isarsa,buwayarsa da kuma ikonsa,tun la'asar akayi haihuwar amma dif babu labarin abinda ta haifa din,tana canbtana tantama da tunanin idanuwansu ne basuga dai dai ba amma namiji ne,sam bata ta wahalar da yarinyar tasha wanda ba'a samu ta fara kuka ba saida qyar,har sai bayan sallar magariba sannan komai ya tabbata.


Sosai tashiga rudu da tashin hankali itama,don dukka malamanta kowa ya tabbatar mata da cewa namiji ne zata haifa wannan karon,abu na farko data soma fada shine
"Tabbas ba shakka wannan surkullen saratu ne,kuma wallahi bataci banza ba,sai tasan dani take zancan".


Itama tuni labari ya dade da isar mata,tasa aka shirya lafiyayyen abinci aka aika sassan adaman kamar yadda itama tamata,sannan tashirya cikin tawagarta suka je barka
"marhaba lale,ashe abokiyar tagwaitakar walida ta iso..." Ta qarashe tana dariya dariyar da zata nuna maka hakan ba qaramin dadi yayi mata ba kenan.


Adaman na zaune a lokacin tanacin farfesun naman rago,saidai jinsa take kamar tana tauna plagyl tana hadiya ne,fuskarta kai kace dare biyu akeyi,maganar saratu yasa tazuba mata idanu,kana cikin kauri da kaushin murya tace
"Burinki yacika,amma kisani...komai nisan jifa qasa zai fado,hakanan na rantse da girman Allah kamar yadda kikaci alwashi nima naci....dukkanin wanda yayimin kan kara saina masa na itace" saman cinyarta ta isa tadora mata yarinyar tana sakin murmushi sannan tace
"Ga fili gamai doki nan....saura sukuwa" saita soma takawa tafice daga dakin tabaiwa barorinta dake can falon farko umarnin su aje saqon kayan barka suzo suwuce.


Wannan ma aishan kamar wancan karon,batazo na sai bayan kwana uku,itama ta bata kwatankwacin abinda ta baiwa walida tatafi.


Tun daga wannan ranat dangantaka tayi tsananin tsami tsakanin saratu da adama,aka shiga takun saqa naban mamaki,yiwa juna zagon qasa,da zamba iri iri.


Aisha na gefe batasanma sunayi ba,dama babu abinda zai hadata dasu,yanayin halayensu yasa ta sake takatsantsan da komai da kuma kowa,hatta da diyarta bata barinta ta qetare sashenta bare tayi nisan kiwo,saboda batajin zata iya dauka idan wani mummunan abu yasameta.


Sai dukka hankulansu ya karkata yakoma ga aishan sanda tashiga watan haihuwarta,kamar tunaninsu ne yazo daya,kowacce saita soma mata aike dake nuna tsantsar kulawa,bata taba cewa kada a karba ba,amma kome suka kawo din bata yarda ya rabi inda take.


Ziyara da suka shiga kawo.mata akai akai kuwa kai tsaye ta soketa ta dakatar dasu ba tare da shakka ko shayin gayawa kowaccensu ba kai tsaye,hakan yasake basu mamaki yakuma tabbatar musu aishan da halayenta na dabanne,kuma lallai jinin sarauta na yawo a jikinta koma bayansu da za'a iya cewa taka haye.


Yadda ta fahimci sunayin saiya sanya nata qaunar samun da namiji,sai taji tanason ta haifa da namijin taga yaya zasuyi?,tanason ita tazama mace tafarko da zata samarwa abdallanta magaji.


Kwana hamsin da biyar cikin dare naquda ta kamata ganga ganga,a lokacin kusan mafi yawan al'ummar gidan da suka damu da rashin lafiyar mai martaba har zuciyarsu kusan idanunsu biyu,cikinsu harda al'ummar sashenta,a daren abdallah yana can sassan maimartaba cikin dakinsa suna fama dashi saboda yadda ciwonsa yatashi ainun fiye da kowanne lokaci,saita kira mutum biyu cikin amintattunta suka kebe iyasu suna kula da ita.


Daidai lokacin data haifi ABDUL_AZEEZ bawan mabuwayi,a sannan mabuwayin ya nuna buwaya da ikonsa yadauki ran sarki mu'az nuhu.


Kaqqarfar ajiyar zuciya tasauke
Tana furta kalmar
"Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus salihat".


Ita da kanta ta hana afitar da jinsin abinda ta haifa din tun cikin daren,sai zuwa wani lokaci data shirya susani din.


Sanarwar haihuwar abdul_azeez ta karade gidan hade da sanarwar mutuwar mai martaba,wanda hakan ya taimaka wajen janye hankalin mutane wajen son sanin me aka haifa?,wanda wannan yabata damar shiryawa sosai da tsara yadda zata fuskanci gaba,ta riga data sani haihuwar abdul'azeez zai iya zame mata wani babban qalubale a rayuwarta tsakanin abokan zamanta.


Abdallah bai samu shigowa ganinta ba sai bayan sallar magariba,tana zaune tana kallon yadda yaketa faman murmushi yana kissing yaron kamar zai maidashi ciki,duk da cewa yana cikin alhini da jajjaɓi na rashin da yayi amma fuskarshi ta nuna farinciki mara misali,hakan shike nuna shaidar cewa yanason magaji kamar yadda kowanne mutum keso,amma shi kansa baisan yana da wannan feelings din ba,saiyau feeling din ya bayyana kanshi da kanshi
"Allah kenan,mai kyauta yakuma amsa a duk lokacin da yaga dama,Allah ya amshi mai martaba sai gashi ya bani wani copy din" cikin tayashi alhini aisha ta girgiza kai
"Allah yayi mishi rahama,yasa can tafi nan"
"Amin don annabin rahama....amma wannan fa" saiya dakata yana sake jujjuya abdul'azeez a hannunshi,sai murmushi yasake kubce masa
"Dan somalia ne,aisha kinmin wayo,ku yadauko zam,dan da alama har kalar fatar ma,na tsira da minahil kenan?" Duk da yadda zuciyarta itama take babu dadi saboda rashin da sukayi saida murmushi ya kubce mata,sai daya tattofeshi da addu'a sosai kana yamiqa matashi ya mata sallama.


Har ya fita yadawo ya dubeta
"Zan aiko da saqon da za'ayi masa amfani dashi,ki tabbata an masa amfanin dashi yadda yadace"
"In sha Allahu" ta fada


Washegari kuwa sai gashi,wani rubutune mai garin magani da za'a masa wanka dashi akan towel,sai a shanya towel din yabushe,da wani irin man shafawa da za'a dinga shafe masa duk jikinsa duk dare idan zai kwanta,kobai fada ba tasan na tsarine,kuma taji dadin hakan sosai.


Duk da wannan rasuwa da akayi hakan bai hanasu son sanin me aisha ta haifa ba,duk da basu samu zuwa ganinta ba amma sunata faman aiki gami da leqo 'yan bugar ciki ko ince leqen asiri,saidai hadiman nata 'yan gaske ne,don har sukayi suka gama basu san me aka haifa din ba,har sai ranar bakwai din mutuwar mai martaba
A ranar ne akayi radin suna ba tare da wani shagali ba saboda mutuwar
Kuma a ranar ne aka nada Abdallah kan karagar mahaifinsa,yazama shine sarkin garin kaisa.


Ba qaramin girgiza zukatan maqiya sukayi ba sanda saqon radin sunan jariri yakai musu da sunan MUHAMMAD ABDUL'AZEEZ,don haj saratu saboda tsabar rudewa cewa tayi
"Abdul'azeez ko aziza?,anya kuwa kunji dakyau?" Tafada cikin razani da rudani tana duban barorin nata.


Dukkaninsu kawunansu suka sadda kamar sun aikata mata wani laifi,sannan daya daga cikinsu tace
"Ki yafemu ranki ya dade,tuba muke....amma ba shakka abdul'azeez shine sunan yaron" sauran duka suka jijjiga kai alamun hakane
"Zaku iya tafiya" tu buqaci su bata wuri,saboda yanzu babu abinda take da buqata sai kadaicewa.


To bangaren adama ma kusan haka abun yake,amma ta dake itama takuma shirya kyautatuttuka ta aika sassan saratun hade da saqo,wanda tace tana tayata murnar samun magaji,Allah ya rayashi.


Tunda taga saqon tasan cewa da biyu adaman ta aiko dashi,hakan kuwa ya qular da ita yakuma fusatata,amma dole ta danne a idanun mutane ta amsa takuma aika mata da saqon godiya.


Bayan nan haka tasake shirya kyaututtuka kala daban daban na alfarma masu yawan gaske ta aika sassan aisha,tace kyauta ce zuwa ga yarima abdul'azeez daga uwarshi,itama aishan ta karba,takuma bada tukuici mai tsoka,irin tukuicin dake nuna zallar isa da qasaita.


Murmushi adaman tayi sanda taga tukucin,tadinga kada qafa tana ayyanawa wala'alla aisha ta yaba shi yasa ta bada irin wannan tukucin haka,take wani shiri yafado mata aranta,ta tafa hannuwanta cikin nishadi ta kashingida tana tsara yadda komai zai gudana.


Tun haihuwar abdul'azeez take nuna mishi soyayya da qauna mai yawa,wani irin so takewa yaron,yashiga zuciyarta da yawa,har takan gaza tantance shida minahil wa tafiso.


Wani kwarjini da farinjini Allah yabashi tun daga quruciya,hakan yasa ta sake takatsantsan dakuma kaffa kaffa a kanshi,ko ina zai shiga akwai sanyawar idanu akanshi saboda tsaro,wannan yayi tasiri qwarai wajen rage hanqoran mafarautan rayuwarsa,yakuma takurasu tare ta qara musu qaimi wajen ganin sun aiwatar da qudurinsu.


Ta bangaren adama kuwa ta bada himma sosai don ganin ta nunawa duniya tana qaunar abdul'azez,haka tadinga qoqarin ganin ta jashi jikinta ta yadda komai zai tafar mata a sauqi,saidai babu wannan damar daga wajen ayshan,ita da abdul'azeez din saidai ta ganshi daga nesa,idan ma kuwa zata ganshi a kusa ta gaban idanun masu tsaronshi ne.


Tsakanin fulani adama da fulani saratu tun haihuwarsu ta uku babu wadda tasake koda batan wata,hakan yasanya zargin juna a tsakaninsu,kowacce tana ganin 'yar uwartace tayi mata wani abu,hakan yasanya dukkaninsu suka sanya aka rufe mahaifar juna ba tare da sun sani ba.


Bayan haihuwar abdul'azeez da shekara hudu aisha tasake haifan diya mace wadda taci sunan mahaifiyar mai martaba suna kiranta da uswa,bayan ita sai arifa sannan sumaira da huda auta.


Kusan a iya cewa

Please Login or Register in order to submit comment