Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba yayi da kallonta,yanajin qaunarta da wani farinciki na takar sa'ar samun karbuwa wajen mahaifinta karon farko tana ratsashi,shi kansa ya yabawa kansa kan namijin qoqarin da yayi wajen tsallake matakai guda biyu masu matuqar tsauri a wajensa kafin isa kan bigiren da yake kai yanzu,mataki na farko shine fitowa ya bayyanawa bilkisu soyayyarshi a gareta,duk da wani kwarjini da kamewa ta musamman da Allah yayi mata,duk kuwa da qarancin shekarunta,mataki nabiyu yadda ayau harya tsaya gaban mahaifinta magana ta gudana a tsakaninsu.


A hankali tamiqe daga tsugunnon tasoma takawa zuwa shiyyar qofar shigewa gidansu,hakan shiya farkar da hamza daga duniyar tunanin daya tafi,cikin zafin nama yayi dan tattaki ya cimmata
"Bilkisu,ya zaki tafi ko gaisawa bamu...." A nutse ta daga idanunta ta kalleshi ba tare data furta komai ba,sai yaji kwarjininta ya cikashi harya danja baya kadan yana dubanta,ta kalleshine kamar yadda tasaba kallon kowa amma sai yaji wani iri harya kasa sake ce mata komai har zuwa sanda ta tura qauren gidansu dake dab da qarasa karyewa gaba daya su jingineshi tashige.


Ajiyar zuciya yasaki mai nauyi,yana qaunar bilkisu irin qaunar da baisan adadinta ba,duk da cewa shi a karan kanshi yana ganin kamar tafi qarfinsa a zubi da baiwar kyau da Allah yayi mata,kamar yadda abokanshi sukan sha gaya masa
"Hamza,kabar ganin yarinyar nan tafito daga gidan masu qaramin qarfi,ba tsarar aurenka bace,irinsu kyawunsu shune jarinsu,duk talaucinsu baka rasa wani hamshaqin mai kudin da zai qyallosu yayu wuf dasu,sannan uwa uba akwai qishin qishin din dangin babarta masu wadatane,ba'asan dai dalilin wanzuwarta a haka cikin wahala ba". Wadan nan kalaman dama ire irensu yasha jinsu bakin abokansa da yawa,amma yakan basu amsa da cewa
"A rashin tayi akan bar araha,a rashin kira kuma karen bebe ya b'ata,hakanan matsoraci baya zama gwani,kudai kubarni na gwada sa'ata kawai" da wannan tunanin yasaki ajiyar zuciya kana yasoma takawa yana barin layin,cikin zuciyarsa yanajin ko iya haka yasoma taka matakin nasara kan bilkisu,kuma yana fatan nan gaba nasarar tashi tafi haka.


Baqiqqirin tsakar gidan nasu yake,babu hasken fitila ko kadan banda wadda ke fitowa ta tsakankanin labulen dakin umma katti kamar yadda sukan kirata,banda tallafi da rahamar ubangiji na hasken farin wata babu abinda zai hana mutum mai qarancin gani yazuba tuntube a tsakar gidan nasu dake warwatse da kwanukan da sauran tarkace nan dacan,wanda basu wuce na sana'ar abincin daren umma katti ba,kusan haka al'adarta yake,duk sanda tagama sana'arta ta dare tashi take tawuce daka abinta tashiga sabgoginta na irgen kudi dakuma wassafa abinda zata siya gobe bayan tatake cikinta dana yaranta,dana mai rabo cikin yaran mijin nata,tacusa kudinta qasan filo tamaida kanta takwanta tahau jan minshari,aikin kusan na bilkisu ne,wanda duk safiyar duniya bayan ta idar da sallar asuba bata maida kanta ta kwanta,saita kintsa gidan,kana tayiwa qannenta wanka itama tayi tashirya cikin tsummokaran unifoarm dinta tawuce makaranta.

Ajiyar zuciya tasaki tadinga ratsa kwanukan tana wucewa zuwa dakinsu da take hango haske kadan kadan,wanda hasken take da yaqinin na acibal bal din data hada musu da kanta,amma tayi mamakin ina suka samu kudin kalanzir din suka zuba,idanunta nakan dakin cike da tausayin yaran harta isa bakin qofar dakin.


Da sallama ta daga labulen tashiga,dukkaninsu suna zaune kusan su goma gaban tabarma qwaya daya da sukayi tarayya wajen kwana akai,tun daga jikkunansu basai ankai ga fuskokinsu ba ya isa ka gane tsantsar rashin gata da kulawa dake tattare dasu,gamida buqatuwar tallafi cikin rayuwarsu.


A hankali take nazartarsu,fuskokinsu babu walwala sam,idanunta yasauka kan wacce ke kwance kan tabarmar,hauwa'u ce,da sauri ta cire takalmanta ta qara hanzari zuwa cikin dakin a dan rude tana fadin
"Subhanallahi,hauwa'u jikinne?"
"Tunda kika tafi yaaya yau bata fito ba,zazzabi take tayi" cewar daya daga cikin yaran,wadda tadan daresu duka a shekaru.
Saita waiwayo tana dubanta
"Baba yaga yadda take?" Ta tambayesu,sai kusan dukkansu suka kada kai
"Kunci abincin dare?" Tasake tambayarsu
"A'ah" suka bata amsa kusan a tare,don babu wanda cikinsu cikinsa baya kiran ciroma,ciwon 'yar uwar tasu ya sanya suka daina damuwa da yunwar sosai,don dama kwana da yunwa ba wani sabon abu bane a wajensu.


Zallar mamaki yasake cikata,wacce iriyar rayuwa suke haka wadda bata da wani maraba da rayuwar marayu,marayunma marasa galihu,wadanda basusan uwa uba ko wani dangi nasu ba,hauwa'u na daya daga cikin yaran da take matuqar tausayi cikin qannen nata,kasancewar taqamaimai a yanzu babu wani tartibin waje da za'a ce ga inda dangin mamanta suke,sakamakon fulani ne na tashi baban nasu ya aura,sadda xaman ya gagara sukazo suka mashi diyarsu suka bar masa tashi gamida karba mata takardar sakinta
"Ina hannatu?"ta tambayesu bayan ta lura da cewa bata dakin
"Tafita roqo mata magani a chemist" sakin hauwa'u tayi tamiqe da hanzari,sam bata qaunar idan dare yasoma yi taga daya daga cikinsu a waje,hannatu kusan itace babba a cikin yaran,saboda ta tasamma shekara sha hudu,shekara biyu bilkisu ta bata
"Ina zuwa" ta fada da hanzari tana ficewa,dukka yunwa gajiya,damuwa dama abinda ke damunta damuwar yaran saita murqushesu,tunaninta na farko inda zata sama musu abinda zasuci,na biyu maganin da hauwa'u zata sha kome qanqantarsa,tana tsaka da wannan tunanin sukayi karo da hannatu wadda itama ke tafe cikin damuwa,kasancewar hauwa'u ce aminiyarta cikin yaran duka gidan,duk da ta bata shekara biyu itama,amma tasu tafi zuwa kusa.


Sosai bilkisu ta hada rai tana dubanta
"Daga ina kike?" Maimakon ta amsata sai hawaye yabiyo kuncinta,cikin muryar kuka tace
"Naje samowa hauwa magani a chemist din bala amma ya hana" kukan yarinyar ya kashe mata jiki da zuciya sosai,maimakon fada dataso mata saita kasa,ta kama hannun hundatun
"Amma bana hanaku fita ba daga sanda akayi sallar magariba ba hindatu?ban isa na gaya muku kujiba?" Kai tashiga girgizawa sosai,har yanzu tana hawayen tace
"A'ah wallahi yaaya kin isa,jikinta ne har huci yakeyi,tanata rawar sanyi,shi yasa na kasa zama,amma kiyi haquri" shuru tasakeyi tana hadiye wani abu mai daci da tauri,yaran tamkar sun fahimci babban qalubalen rayuwa,gibi gamida nakasa da rayuwarsu ke ciki,sai suke qaunar junansu sosai tamkar uwa daya uba daya suke,tsahon wasu mintuna sannan ta iya bude bakinta
"Ki daina kuka,zata samu lafiya,amma kada ki sake fita,banason fitar dare kwata kwata"
"To yaaya"
"Muje ciki" tafada,hannatun tayi gaba tana biye da ita a baya har zuwa tsakar gidan.


Dakinsu ta shige yayin da ita kuma ta durfafi dakin umma katti,bakinta dauke da addu'a Allah ya dorata a kanta,yasa tasamu abinda zata baiwa yaran suci sukwanta.


A hankali ta yaye labulen bakinta dauke da sallama,tana kwance kamar yawancin daga ita sai daurin qirji da dankwali mai santsi wanda bai dauru sosai ba,saijsn gwarti take abinta,duka rumfar tata cike da tarkace,yaranta duka sunyi bacci sai lariya dake zaune saman kan uwar tana cin abinci.


"Yaaya,kin dawo?" Tafada,kasancewar akwai fahimtar juna tsakaninsu,duk da yadda uwar kan kyaresu idan taga suna nunawa juna qauna
"Nadawo lariya,umma tayi bacci?"
"Eh amma bata dade ba" kan bilkisu tace komai lariya tasoma bubbuga saman kan umma kattin tana cewa
"Umma kitashi ga yaaya bilki tadawo" kafin takai ga hanata har umma kattin tatashi,a fusace tazauna dungurgur tana gyara zaman dankwalinta dake shirin zamewa tana duban lariyan
"Me za'a siya da saikin tasheni" sai datakai lomar shinkafar bakinta sannan tace
"Ba abinda za'a siya,yaaya bilki ce tazo nemanki" maficin da take firfita dashi wanda garin bacci yazame yafadi ta jawo takai mata bugu
"Shine don tsohonki zaki tasheni haka sai kace wata diyar gwamna,du randa kika sakemin irin haka saina sassabar miki" itadai lariya cigaba tayi dacin abincinta,sai data gyara zamanta sosai fuska a dinke ta maida kanta ga bilkisu wadda ke rakube kamar wadda ruwa yaciyo
"Bashina kikazo biyana da kika saka aka tasheni sa tsohon daren nan?" Gabanta ne ya yanke yafadi,babu alamun zata samu abinda tazo nema kenan da alama,kaita kada a sanyaye
"A'ah,amma in sha Allahu zuwa jibi za'a biyani zan kawo miki"shuru tayi ranta a bace na wasu sakanni sannan tace
"To meye?"da qyar ta iya buda baki tace
"zuwa nayi don Allah idan za'a samu sauran abinci wajenki,yarancan duka ba wanda yaci abinci,ga hauwa na kwance ba lafiya" sake dinke ranta tayi
"Ai kinsan rabon tsohonki da cefane a gidan nan ko kawo qwayar hatsi yau sati guda cur ko?,kuma duk randa yakawo din idan na dafa ba wanda nake hanawa ai" tasan magana ta yada mata amma saita shanye
"Nufina abincin siyarwa,saimu saka a lissafi...."
"Babu" ta fada da hanzari tana katsar numfashinta gamida juyawa da niyyar komawa ta kwanta
"Akwai wanda kika rufe da abun tatar taliya fa" raliya tafada,saita daga kai ta watsa mata harara sannan tace
"Tunda kece uwata aisaiki dauko ki bata ko?,zakici qaniyarki kema idan idan kika qureni,xan barki da iya abincin da tsohon naku ke kawowa kiga idan zaki rayu" daga haka ta maida kanta tayi kwanciyarta tana qananun mitoci
"Yara sai shegen ci,na rana ma dana dubi Allah nabasu ashe basu gani ba zuba idanun na dare sukeyi,sai kowa ya lashi walqiya ya kora da ruwa ai ya kwanta".


A sanyaye ta juya tafuta daga dakin tana tunanin meye dabara ta gaba,a haka har takai soron gidan batama sani ba,tana yunqurin fita wani tunani yazo mata,saita koma wajen tukwanen shinkafar umma katti dake jiqe.


Tsintsirar da ruwan dake ciki tayi a hankali har zuwa sanda ya qare,ya zamana saura qanzon shinkafa dake can qasan,cikin kwanukan dake wajen ta dauki guda daya ta wankeshi tas,sannan ta saka hannu ta dinga tsame qanzon tana zubawa a farantin,haka ta dinga yi harta tsame qanzon tas,ta sake wankeshi,ta tsaneshi dakyau,ta tsaya tana dubanshi sanda yake digar sauran ruwan da bai gama digewa ba tana wassafa yawanshi,duk da bashi da yawa,duk da bazai ishesu su qoshi ba,amma tasan a qalla zasu rage wata kafar,ba zasu kwanta da yunwa mai hana bacci ba,to amma inda gixon ke saqar inda zata sama musu mahadi,tasan cewa ba za'a rasa mai da yaji wajen umma kattin ba,amma tayi imanin koda ta roqa ma a yadda yau take kan tsininta ba zata bayar ba,tunda abun yau ba iyasu kadai ya shafa ba,harda mai dugungurun gum dinma gaba daya wato babansu.


Ta dauki tsahon mintuna kana ta taka da kwanon a hankali zuwa dakin,tana shiga kowannensu yazubawa farantin idanu,da alama a zaqe suke,hakanan cikinsu cike yake da yunwa,jira kawai suke su samu abun sawa a bakin salati,tausayinsu yasake cikata,inama ace wani abincine mai kyau da dadi a hannunta da zata ciyar dasu,wanda zasu kwanta suna murna cikinsu a qoshe taf kamar kowanne yaro mai gata da 'yanci?.


Saita isa tsakiyarsu ta aje farantin tana cewa
"Bari na samo maku mai da maggi ko gishiri kunji?" Fuskarsu fadade da fara'a da farinciki na qanzon da aka samu suka amsa da to,hannatu tace
"Umma tabarki kin debo?,dazu dazan kankare mana muci hanani tayi ta sheqa masa ruwa" tausayi yasake cikata har idanunta wannan karon ya hada qwalla,ba shakka duk yaron da aka haifeshi cikin gidan nasu ya fado cikin wata jarrabawa ne ta rayuwa,hakanan dukkaninsu ababen tausayi ne,duk da cewa gwara wasu da wasu a cikinsu,tunda akan samu wadanda iyayensu kan leqo da abun arziqi suga yaran nasu,saidai kusan da zuwan nasu da babu duka sammakal,don da zarar uban ya qyallara idanu yaga abinda aka kawo din zai rage mishi wani nauyi zai dauke,ko yace ayi amfani dashi a gida,wanda kwana daya ko biyu ya qare,maimakon abarwa yaron da aka kawowa yamora.


Kasa bata amsa tayi saboda batason suga qwalla a idanunta ko rauninta,tana tunanin idan sukaga rauni a nata idanun yaya nasu zuciyoyin zasu kasance?,saboda haka ta juya kawai tafice a dakin,saidai tana isa tsakar gida ta kasa riqesu suka soma bin kuncinta,tasanya tafin hannunta a hankali tana sharewa gamida dosar qofar fita gida qafafunta kamar ba zasu dauketa ba,duk da bata da yaqinin samun abinda zataje nema,amma tana fatan a dace kodon yaran.


Karo suka kusayi da wanda ke ke shigowa,dukkaninsu sukaja baya yana fadi cikin fada fada
"Kai,waye wannan?!"
"Nice" ta fada a tausashe tana daga kai don ganin waye,sulaiman ne,yaya a wajenta wanda suka hada uba daya,kusan rabi da rabi yake rayuwarshi a gidan,saboda kaf nauyinsa baikai mahaifinsa,d'a ne ga matar malam bilya ta farko wadda suka jima da rabuwa,tafiye tafiye yake qwadagonshi da neman kudinsa,kuma ba laifi yana samun na rufawa kanshi asiri,duk da bai tsinanawa uban komai sai abinda yaga dama,saboda haushi da takaicin yadda ya watsar da rayuwarsu dake cike a zuciyarsa.
7/11/21, 4:28 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAD'IN RAYUWATA* 👑




*_Wannan littafin na kudine,amana ne a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data dace cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,babu cigiya,babu a dauko mana_*

3


"Maigado?,ina zaki haka?" Ya fada bayan ya sassauta muryarsa daga fada zuwa sanyi,maimakon tabashi amsa saita sadda kai tana wasa da yatsunta,hawayen da take qoqarin riqewa tun dazun suka balle mata,daidai lokacin da nepa suka kawo wuta,hakan ya taimakawa sulaiman wajen ganin hawayen nata
"Lafiya?,cewa nayi ina zaki,idan babu amsa kuma matsamin nawuce"
"Zanje na samowa yara mai da yajin da zasuci abinci ne" shuru ya ratsa tsakani sulaiman najin takaici na sake ratsashi,mai hali dai bai fasa halinsa?,saiya sanya hannunsa a aljihun wandonshi yaciro dari biyar da yayi niyyar baiwa baban nashi a yau yamiqa mata
"Ungo wannan,ki saya muku wani abun" hannunta har rawa yake saboda murna da dadin dataji,wani abu da yaketa qulle mata numfashi tun dazun taji ya saketa,farinciki yacikata har murmushi ya subuce mata
"An gode yaya sule,Allah ya qara budi"
"Amin" ya fada yana binta da kallo sanda take ficewa cikin hanzari,sosai yarinyar take bashi tausayi,yana lura da kuma ankara da yadda take dawainiya da rayuwar yaran bakin qarfinta,tamkar ita ake haifawa su,ko kuma daga cikinta suka fito,ita kanta abar tausayice,saboda baya manta sanda mahaifiyarta take raye gatan data samu,baya kuma manta sanda anty zuhra take nan,duk da baisan meye dalilin bacewar anty zuhran da daina ganin gilmawarta cikin rayuwarta ba,da wannan tunanin yacusa kanshi cikin gidan.


Abu kala kala ta dinga ayyanawa a ranta,tayi tunanin siya musu suci su more a daren da kudin,har tayi hanyar sai kuma taja ta tsaya turus tana juya kudin a hannunta,idan har tace zata siya musu abu me dadi suci to kuma gobe fa waye zai basu?,hakan ya sanya ta sauya tunani,ta nufi kanti ta siya musu garin kwaki da suger,sannan tashiga gidan gwaggo rabi maqociyarsu ta siyi mai da yaji maidan dama,takuma siya gasarar koko da yake suna saida ita,ta ayyana a ranta gobe bazasuyi tashin yunwa wunin yunwa ba,mai da yajin yanzu zata zuba musu a qanzon suci,ta rage wani gobe ta kwada musu da garin,da safe kuma ta dama musu kunu susha,tuna hakan kawai ya jefa murmushi kan fuskarta,harya bata qwarin gwiwa da karsashin nufar gida bayan ta siyawa hauwa'u paracetamol satches daya,tana fata ko zazzabin ne kawai ya saukar mata,duk da tasani ba shine ainihin maganin daya kamata tasha ba,amma ragi ragi ne.


A hanzarce tashiga soron gidan nasu wanda jan qwai na wuta ya haske,saita hangeshi rakube daga bayan qofa riqe da takardar tsire yana kaiwa baka da sauri da sauri,da alamu baison wani ya ganshi,gabansa kuma robar fanta ce qaramar 35cl.


Motsin da yaji ya sanyashi saurin cilla ledar tsiran da gara robar saqon qofar yana boye hannunsa dake cike da maiqo da quli qulin tsire,saita sadda kai kamar bata ganshi ba zata wuce,yayin da jikinsa yabashi cewa tariga data ganshi,saboda haka yahau nade tabarmar kunya da hauka
"Ke maigado daga ina kike a daren nan?" Kafin ta bashi amsa yadora da bambami
"Banason iskanci da diban albarka fa,wato yawon dare kikeson koya ko?,ina cewa baki jima da dawowa daga wajen aiki ba shine yanzu zaki sake zargawa qafarki igiya ki fice?"
"Kayi haquri baba,maqot...."
"Rufen baki ki wuce ki bani waje,sakarya kawai" bata sake yunqurin cewa komai ka kare kanta ba tawuce ciki,don dama ta qagu ya sallameta din,tunda tasan fadan gwaggo a kofa yakeyi,idan da sabo ta saba da ganin dabi'unsa kala kala,ita abinda yafi damunta yabarta takaiwa 'yan uwanta abinci,idan yaso idan tadawo ko gutsi gutsi da namanta zaiyi yayi.


A zagaye ta samesu da farantin qanzon kai kace tururuwa ta samu hasken candle guda daya,tasauke ajiyar zuciya tana godewa Allah daya sanya tasamu mahadin da zata kawo musun,da batasan ya zataji ba a yadda ta samesu.


Cikin hanzari ta hada kwadon tsaf,tasa kowanne ya wanke hannu suka soma ci a tare,bayan sun gama ta baiwa hauwa'u paracetamol din tasha sannan sukayi shimfida da zannuwan da sukan lullube sumuntin dakin su kwanta.


Sai data tabbatar da kowanne ya sanya haqarqarinsa ya kwanta sannan ta zare yalolon hijabinta ta fita zuwa tsakar gidansu dontayi alwalar da zatayi shafa'i da wuturi,abu na qarshe da takan gabatar duk dare kafin ta kwanta,saboda bakoda yaushe take samun damar tashi sallar tsakar dare ba.


Tana bakin famfo a duqe tana daura alwalar amma tana iya jiyo cecekucen baban nasu da baba katti,cin mutuncine dai data saba masa duk sadda ta hadosu,tana iya jiyoshi yana cewa
"Abincine dai ki jiqa kayanki ki sha,da baki bani ba ai Allah yabani wanda yafi naki,bakin da Allah tsaga baya hanashi abinci,kuma wallahi nasan maganinki,na gane take takenki,saboda kwana biyu kina ganinki ke kadaice cikin gida kike tunanin kinfi qarfina kinsha kaina,to zanyi maganinki ne,mu zuba dani dake,shege ka fasa" qaramar guda umma kattin tasaki kana ta dora da cewa
"Ahayye,yoni Allah na tuba wane darene jemage bai gani ba?,aisai na ranar mutuwarsa,kare kuma da kudinsa sai yasha lahaula,kai kaga zaka iya,ga fili nan ga mai doki saura sukuwa...." Itadai daga haka tasamu ta gama alwalarta tashige daki tana mai qyamatar rayuwa irin ta gidansu,ta tuna mahaifiyarta,duk da cewa sanda tarasu bata da wayo amma tana iya tuna wasu abubuwa dangane da ita,hawaye ya sake cika mata idanu sanda taga nan da nan bacci ya kwashe yaran,ta kabbara salla tana maida dukka damuwarta baya don ganawa da ubangijinta.


Ta jima saman abun sallar tana addu'a kamar yadda tasaba sannan ta shafa,ta nufi can bangon dakin inda akwatinta take,wadda asanda take sabuwa ta zuba kyau da d'aukan hankali,anty zuhra ce ta taba siyo mata ita dab da sanda zasu tafi,budeta tayi ta ciro unifoarm dinta tana dagawa,tun daga tsarin dinkin da kalarsu zakasan cewa na private school ce mai tsada,duk da yadda suka tsufa amma tsarinsu bai bace ba,a wanke suke fes kamar yadda bata taba barinsu babu wanki duk da yadda suke neman agajin hutu saboda tsufa,saita zauna anutse tasoma musu ninkin guga,ta shinfidasu qasan wajen kwanciyarta,tana fatan su miqe kafin safiyar gobe,saboda batasamu gogesu ba yau,duk da cewa a kwance suke saboda laushi da sukayi dakuma sabo da guga,sai data gama jerasu sannan ta shinfida zaninta a sama ta kwanta kamar sauran 'yan uwanta.


Ta kafin bacci ya ziyarci idanunta saboda tarin tunane tunane na rayuwa da abubuwan da suke cikinta na qalubale iri daban daban,daga qarshe dai sarkin barayin yayi nasarar saceta,baccin da yake cike da mafarkai na burikanta na rayuwa da takeso ta cimma,ciki kuwa harda inganta rayuwar qannenta.


***** ****** ****** *****


Sanye da daurin qirji da kuma lullubin hijabinta tashigo dakin nasu wanda yake share fes kamar ko yaushe,kai bakace ana kwana a dakin ba saboda tsananin tsafta,duk da cewa babu komai qasan dakin sai sumunti da kuma tabarmar da kusan rabi da rabinta a cinye yake da suke kwana akai amma saika zuba abinci akai kaci.


Fitowarta kenan daga wanka bayan tagama tsaftace gidan,takumayi wanke wanke kamar yadda tasaba kullum kwanan duniya,sai data tsugunna ta rarrabawa duka qannen nata kunu a cikin kofin sannan ta miqe tasoma shiryawa,idanunta akan ratattaken agogon da iya awanni kawai yake iya nuna mata,ta maqalashi saboda tashinsu sallar asuba dakuma lokacin tafiyarta makaranta,tana qiyasta mintinan da zasu kaita makaranta daga nan gida,tana saka ran ta isa kafin lokacin da za'a soma assembly yacika.

Mai kawai ta shafa,sannan ta goga alimun a hammatarta,kafin ta dangwali turarenta dan duri da take siya duk qarshen wata,unifoarm dinta dake saman akwati ta dauko tahau sanyawa,cikin mintina qalilan tagama shiryawa tsaf.


Wani irin sassanyan kyau unifoarm din sukayi mata,kai kace wasu kaya ta saka na azo a gani,ya fidda sigarta sosai fiye da kayanta na gida,abu dayane tak ya musu cikas tsufan da sukayi,saidai tsaftarsu tadan boye wani daga cikin aibunsu.


"Takwas tanayi hannatu karki bar kowa kuwuce kamarantar allo,kar nadawo acemin yau wani baije ba,hauwa'u kawai na yarda abari tasake jin qwarin jikinta tukunna"
"To yaaya" hannatu ta fada sannan suka fara mata rige rige na adawo lafiya tana amsa musu harta fice daga dakin,ta ratsa tsakar gidan nasu tana wuce custumers din baba katti dake siyen qosai harta fice daga gidan gaba daya ta dauki hanya cikin nutsuwa kamar yadda tasaba.


Ajiyar zuciya tasauke sanda tashiga harabar makarantar taga ba'a fara fita assembly ba,hakan ya alamta mata ba qaramin sauri tayi ba.


Kamar ko yaushe ajin yasoma cika,saboda makarantace dake da tsari da doka,ba kasafai dalibanta ke makara ba,duk da cewa makaranta ce ta 'ya'yan masu hannu da shuni.


Babu wanda zaiji sallamarta ma idan tayi saboda kowa sabgar gabanshi yake,hayaniya ce ke tashi,saboda haka saita wuce direct sit dinta,wanda kowa dama yasan wajen zamanshi kuma anan yake zama koda yaushe,kujerarka da table dinka kai kadai harda 'yar locker daga qasa.


Ganin kamar akwai sauran lokaci yasa tazauna tazuge jakarta tana sake gyara zaman litattafanta,gamida sake dubasu daya bayan daya taga kota dauko kowanne,lokaci lokaci masu shigowa takan daga kai ta amsa sallamarsu,wasu idan sun kirayi sunanta ta amsa tare da qoqarin dora murmushi kan fuskarta.


Kusan ita daya take rayuwa cikin ajin tsahon shekaru,bata yarda ta rabi kowa ba,kamar yadda babu wanda ta bawa fuskar ya rabeta,ta sani ko ba'a gaya mata ba dukkaninsu kaf ajin matakin rayuwarsu da nata ba iri daya bane,kallo daya zakayi ka tantance hakan,akwai mutane da dama da sukaso qulla qawance da ita amma ta toshe wannan kafar,wanda hakan yasa wasunsu suka qullaceta suke ganin tsabar girman kaine,ko don taga tana da kyau?,ko kuwa ubanta qila wani shegen ne wanda wala'alla yafi dukka nasu iyayen hawa tudun muntsira.


A hankali daga bisani kuma sai abubuwa da yawa da suke gani tattare da ita suka sauya tunaninsu suka sakasu acikin duhu,na farko dai ita ba'a mota mai kyau da tsada ake kawota kamar su ba,koda motar haya bata hawa bare akai ga ta gida,a qafa kulli yaumin take zuwa,abu na biyu,bata zuwa da abinci mai tsada irin nasu hakanan idan lokacin break yayi bata kashe ko ficika da sunan siyan wani abu da zata saka a bakinta,hasalima saidai ta dauki litattafanta a sannan ta sake sabon xaman karatu,ko kuma tafice daga ajin tatafi can baya inda babu mai ganinta bare ya dameta ta zauna,harsai an gama sannan tadawo cikin aji,na uku tunda suka soma karatu basuga wani sauyi daga sutturar unifoarm jaka ko takalmi ba daga gareta,kamar yadda yawancinsu ba unifoarm guda daya garesu ba,duk da haka kuma lokaci zuwa lokaci sukan sauya da sabo koda ace bai tsufa ba,wannan sune abubuwan da suka sauya tunanin wasu da dama a kanta amma banda mutum guda AFNAN ABDALLAH KAISA.


Yarinyar da jinin sarauta ke zagayawa a jikinta,hafaffiyar diya ga sarki Abdallah mu'az kaisa,babbar masarauta wadda keda qarfi iko da kuma izza,masarauta ce mai matuqar girma da fadi da iko cikin dukka masarautu dake nahiyar,masarautar da a tarihinta dama can gwarzuwar masarauta ce wadda tayi shuhura takuma yi suna.


Baya ga jinin sarauta dake yawo a jikin afnan 'yar gata ce wajen mahaifiyarta,sannan uwa uba Allah ya hore mata baiwar kyau hakanan tana da qwaqwalwa da basira da saurin gane karatu,saidai dukka wadan nan abubuwan sai taga tamkar bilkisu bilyamin nason zartata kyau dakuma kaifin basira,sannan yanayin da take kallon bilkisun tana mata kallon mai zallar girman kai,bayan bataga wani abu da zata nuna mata ba game da gata ko sarauta,kusan kowa na ajin neman fada yake a wajenta dason samun shiga,amma sai taga hakan sam bai damu bilkisu ba bare ya dadata da qasa,hasalima rayuwarta take ita daya abunta ba tare data damu da shiga sha'ani ko shirgin kowa ba,sai Allah ya jarrabi afnan da dora dukka idanunta da damuwarta kan bilkisu,tana fata dai dai da rana daya bilkisun ta rabi kota shigo gonarta,amma hakan bata taba gittawa ba,dalili kenan daya sanya haushin bilkisu yasake cikata,tasake amannawa ranta cewa zallar girman kaine kawai ke damun bilkisun ba komai ba.


Hakan saiya haifar da takura ga bilkisu,afnan ta sanya mata idanu duk wani motsinta,koda hanyace ta hadasu sai tayi wani abu na nuna wulaqanci takura ko muxanci a gareta,babu abinda bilkisu ta tsana a rayuwa irin wulaqanci muzanci ko toxarci,tana da haquri dauke kai da kawaici,to ammafa bata jurar wulaqanci,duk inda tasan zata wulaqanta idan tashiga takanyi namijin qoqarin janye jikinta daga wajen,ta san afnan din ko wacece,don tanajin yadda sautari 'yan ajin ke hirarta gamida yadda kowa keson ace itace babbar qawa a gareta,duk da kuwa har yau bata da

Please Login or Register in order to submit comment