Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata gwana guda daya a cikinsu,ta auna takuma sani cewa ita din ba kowan kowa bace akanta,dalili kenan daya sanya tasake qauracewa hada koda hanya da ita,babu abinda take bari ya gitta tsakaninsu saidai tsautsayi wanda baya wuce ranarshi,tsakaninta da afnan ko kallo bata bari ya hadasu saboda gudun bacin rana,tana gudun ranar da zata kaita bango ta tabbatar abun bazai musu dadi ba,wanda bata fatan hakan saboda gudun fadawa bigiren da ba nata ba,tunda tasani koma meye yafaru ita zafa zamo a qasa,bata da wanda ya tsaya mata,bata da wani gata bare galihu irin nasu.


ƙararrawar data buga ita ta alamtawa kowanne ɗalibi lokacin fita assembly yayi,hakan ya sanya kowanne ɗalibi tattara komatsansa zuwa filin assembly,ciki harda bilkisu.


Kamar kullum haka tabi layi da kowanne dalibi kebi saboda gudanar da abun a tsare,a ɗarare take kamar kowanne lokaci,gani take kamar kowa kallonta yake,kamar kowa ya lura da tsufan unifoarm dinta,kamar kowa yana iya ganin aibun dake tattare da ita.


Cikin sahun daliban daya dake baya ta tabo ta gabanta tana shuna mata bilkisu wadda rashin tazara dake tsakaninsu yasanya karaf idanuwan bilkisun ya nuna mata su,amma saita dauke kanta ta maida idanunta ga abinda ake gabatarwa a wajen,duk da haka kunnuwanta suna iya jiyo mata maganganunsu,duk da cewa dafarko bata jin me suke fada
"Gafa mutuniyarki" saita tabe baki
"Sai shegen kyau amma da alama babu abun" dariya suka saki ƙasa ƙasa sannan ta sake cewa
"Anya ko ba 'yar aikin wani gidan bane suka taimaketa suka sata a school din nan?,don ko kusa ko alama batayi kama da wadanda iyayenta zasu iya sata a nan ba" dariya dayar tasake ƙunshewa sannan tace
"Da alama dai kam..." Maganar da principal yasoma ita taja hankalinsu ya hanasu ci gaba da tattaunawa akan bilkisun,wadda tuni tashiga dogon nazari da tunani,abinda ta fuskanta shine,duk sanda talaka yayi gangancin shiga tsarar masu hannu da shuni ya banu?,ba gasu iyayen ba baga ƴaƴansu ba,ta lura kamar gado ko kuma halayyace a jininsu,mafi yawa yaran suma sukan taso da irin wannan ɗabi'a da halayya irin ta iyayensu,saboda za'a iya cewa sun taso sunga sunayi.
7/11/21, 4:28 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAD'IN RAYUWA* 👑




*_Wannan littafin na kudine kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data dace cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,babu cigiya,babu a dauko mana_*

09032345899
Ko
09033181070

*_KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.._*



4



Har aka kammala assembly ɗin ba zata iya tuna abu ƙwaya ɗaya data ɗauka ba,bata dawo hayyacinta ba sai data tsinto sunanta ana kiranta amatsayin wadda zata rufe taron da karatun ƙur'ani,kamar yadda tasaba yawancin lokuta ita ake kira.


Wata baiwa ta musamman Allah yayi mata na dadin murya da iya rero ƙur'ani,saidai zata iya cewa ta tsani wannan kiran,kiran yakan sanyata taji gaba daya ta muzanta,kana ta tsargi kanta,amma babu yadda ta iya haka ta taka zuwa gaban taron assembly din dake cike da dalibai da malamai,cikin daddaɗar muryarta dake cike da tsoro har tana ɗan rawa rawa tayi basmala sannan tasoma karanto ayoyi daga cikin suratul anbiya'i shafi na qarshe.


Kamar koyaushe dukka idanu sukayi mata caa,kowanne akwai abinda ke kawo cikin ranshi dangane da ita,wanda mai tunani na ƙarshe ke ayyana
"Kyakkyawar sura mai ɗauke daddaɗar murya,cikin tsaffin tufafin makaranta",abu mafi ban mamaki a idanuwansu,don kaf fadin makarantar babu wanda yake da suturar unifoarm maqasqanciya irin tata,banda Allah yayi mata baiwar tsafta da iya kula dasu da ba'asan yanayin da zasu kaya ba,ita kanta tasan da cewa zasu tashi tamkar na almajirin dake karatu a tsangayar da babu kulawa.


Gamawarta yayi dai dai da shigowar motar dake kawo afnan makaranta,wanda hakan ke nuna yau ta makara kenan,wanda ba kasafai hakan ke faruwa ba,bata daga cikin sahun daliban dake makara,gajeran jawabi aka dauraye dashi kana aka sallami kowanne ɗalibi kamar yadda aka saba.


Dai dai ƙofar aji sukayi kaciɓus da afnan wadda ke ƙoƙarin amsar jakarta daga hannun wata matashiya da suke kusan sa'annin juna,wadda kusan koda yaushe itake riƙo mata jaka da sauran abinda tazo dashi makarantar har zuwa ƙofar aji,wani lokaci kuma har mazauninta,duk da cewa itama ɗaliba ce amma da alama an sanyata makarantar ne musamman saboda afnan ɗin,don kusan itace take mata dukkan wata hidima data shafi makarantar,kamar ɗauko mata jaka yayin zuwa da komawa,da kuma kuma kawo mata abincin break,siyo mata wani abu idan tana da buƙata dadai sauransu.


Wani kallo ta jefawa bilkisu,wanda sarai ta ganta amma ta ɗauke kanta kamar bata ganta,don ita ko ɗaya bata a cikin lissafinta,hakanan bataga na meye zata damu kanta da rayuwar wani ba.


Kamar kullum kuma kamar ko yaushe,ta bada dukkanin hankalinta ga karatunta,don tanaji a zuciyarta shine abu guda ɗaya tak da zai iya kaita ga tudun muntsira nan gaba,duk da bata da yaƙinin yadda rayuwa zata kasance anan gaba,akwai yiwuwar ci gaba ko kuwa guguwar data afko tsakiyar rayuwarta zata sanya dukkan ƙarfinta ta sake aza mata nauyin da dole zai sanyata takai ƙasa saman gwiwoyinta?.


Daidai lokacin da aka saba fita don ɗalibai su huta na tsakiyar lokacin karatu aka kada ƙararrawa,babu ɓata lokaci kowanne yasoma tashi daga mazauninsa don yasamu ya sarara yakuma huta,ga bilkisu ma haka take,saidai yau ta ɗanyi nawa sakamakon note da bata gama kwafa ba saman allo,gwanar sauri ce ta fannin rubutu,amma saboda wanki data mai yawa jiya a gidan umma luba na kayan sawarta yatsunta ke mata zugu har zuwa yanzu,tayi wankinne tana fatan idan an lissafa zata hada mata da albashinta wani abu ya daɗu akai wanda zata riƙe a hannunta bayan ta gama biyan bashin umma katti saboda ƙannenta da bata ƙaunar ko misƙala zarratin tagansu cikin yunwar da bata da abun basu.


Mintina goma kyawawa ta daɗa kafin ta kammala,zuwa sannan ajin nasu yasoma ɗumamewa da ƙamshin abinciccika da kuma snacks kala kala,ta zuge jakarta a nutse ta maida littafinta,kana ta zari wani da zata duba zuwa lokacin da za'a koma ɗaukan darasi.


Dai dai lokacin afnan da ƙawayenta suna saman babbar darduma mai kyau da laushi da sukan shimfida suci abinci anan,wanda duka cikin kayan afnan ne da take zuwa dasu,gab da zata qaraso inda suke ta jiyo jan tsakin afnan din,cikin murya dake cike da izza tace
"Bansan nayi kuskuren zabar school din nan ba sai daga baya,nayi tunanin zata zama best makaranta cikin list na makarantun da magajiya tabani na zaba,sai kuma naga kaman ba haka ba"
"Me yafaru?" Halima ƙawarta dake buga game a tablet dina ta fada bayan ta dakata da game din da take,kaman ba zata amsa ba sai kuma tace
"Ina ganin mutanen da ba ajin rayuwarmu daya ba a cikinta,hakan ai zubewar girma ne,qasqanta ce a wajenmu" ƙarshen maganar tata yazo daidai da sanda bilkisu tazo dab dasu,dukka sai suka ɗaga kai suna kallonta kana suka sheƙe da dariya,saboda sun fuskanci inda maganar tata ta saka gaba
"Don't mind mana......kinsan da yadda aka shigone?,may be 'yan alfarma ne kamar yadda basira take tare dake anan,ki gane mana" farha ɗaya daga cikin aminan afnan ta fada.


Wani abu ta hadiye tanajin maganar na mata suya har cikin ranta,ɗaya daga cikin dalilan kenan daya sanya bata bari koda hanya ta hadata da afnan din,saita ƙara sauri tafice daga ajin gaba daya,tana ƙoƙarin sharewa da manta abinda kunnuwanta suka jiye mata.


ƙarfe biyu na rana aka tashi kamar yadda ƙa'idar makarantar take,kamar yadda ta sabawa kanta tana daga cikin sahun farko farko na ɗaliban da suke riga kowa fita daga makarantar,saidai yauma tayi nauyi kamar dazun,sakamakon kwantan note da malamin daya shigo musu a period din ƙarshe ya musu da bata kammala ba,da sauri sauri ta kammala ta hade kan litattafanta ta baro ajin,gaba daya hankalinta kuma yakoma kan ƙannenta da gidan aikinta,tana fatan yau idan taje ta dace umma luba ta sallameta da kudin aikinta.


Kamar kowanne lokaci dai harabar makarantar zuwa wajenta akwai ababen hawa sosai,waɗanda dukkaninsu sunzo ɗaukan ɗalibai,haka ta dinga ratsawa harta samu hanya tafice gaba daya tadauki hanya zuwa gida,cikin tafiyarta dake cike da nutsuwa da kamun kai,saidai tun batayi nisa ba taji ƙugin mota daga bayanta,wanda kafin a ankara tazo ta wuce da mugun gudun daya haddasa tashin ƙura har saman fuskarta,da hanzari ta daga kai tabi motar da kallo,ɗaya daga cikin motocin masarautar kaisa ne,gakuma tabbacin fuskar afnan ta glass,wanda suna haɗa idanu taja glass din xama ta zuge.


Kai kawai bilkisun ta kaɗa,wai na meye?,meta tsare mata?,da wannan tunanin da ɓacin ran tadinga takawa zuwa gida,zafin rana qura da yunwa irin ta kowanne dalibi dake kwasota daga makaranta tana sakadarta.


Dukkaninsu babu wanda bai haddace lokacin dawowarta daga makaranta ba,saboda haka batayi mamaki ba data samesu zaune dukkaninsu suna dakon dawowar tata,ƴar rige rigen taryarta suke,tana kallonsu fuskarta cike da murmushi,zuciyarta cike da farinciki idan ta tuna a ranar yau tana da abinda zata basu suci,babu abu mafi ɗaga hankali da sanyata cikin ƙunci irin ranar da zatazo,suyi mata irin wannan tarbar amma bata da abun basu.


Sai data dora hannunta saman kan kowa ta amsa oyoyo ɗinsa,hauwa ce ta ƙarshe,ta dubeta cikin kulawa
"Fillo(da yake wani lokaci da sunan da take kiranta kenan),kice yau da celebration jiki yayi kyau kenan ko?" Kaita daga tana murmushi
"Na warke yaaya,naji sauƙi ai,harma na ɗebowa umma katti ruwa" duban yarinyar take sosai,ba zata hanasu yi mata aiki ba saboda ko babu komai a matsayin babarsu take,saidai wani lokaci tana mamakin rashin imani da tausayin umma katti,a yanzu tana da yaƙinin idan ta ƙarasa cikin gidan akwai abinci cikin abincin da take saidawa,amma babu wanda zata iya sanma cikinsu,idan kaga ta bayar ta ranar ba ƙaramar sa'a suka taka ba,ko ranar babansu ya kawo cefane,ko wani cikin custumers dinta yaji tausayinsu ya siya musu
"Ya akai hannatu?" Bilkisu ta tatambayeta sanda take kada kansu zuwa cikin gidan ganin yadda tazuba mata idanu,saita saki murmushi tace
"Babu komai" daga haka ta hada kansu dukka suka shige ciki.


Ilai kuwa tana tsakiyar kulolin abincinta tana ciniki tana haɗa kan kuɗinta,tanayi tana 'yan waƙe waƙenta duniya tayi mata daɗi,donko kula da sannu da gida da bilkisu tayi mata batayi ba,itama bata damu ba ta jasu suka shige daki,domin idan da sabo ya zame mata jiki,ba baqon lamari bane a wajenta.


Tasan yunwa suke ji,saboda haka tasoma ɗauko garin ta wanke tabarshi ya jiƙa kafin ta sauya kayanta,wanda da zarar ta dawo take fiddasu daga jikinta,bata sake tabarsu,don idan tabarsun suka sake jin jiki bata da wata madafar.


Tana canza kayan tasake lura da hannatun dai tana kallonta kamar dazun,sai data gama sanya atamfar tata riga da fallen zani wadda tadan soma jin jiki tayi haske daga ainihin kalarta ta daura dankwali sannan ta isa gaban hannunta ta duƙa
"Anya kuwa lafiya kike hannatu?irin wannan kallo?,kamar yau yaaya maigadon ta zama baquwarki ne?" Sai ta saki murmushi wanda idan kalura dakyau akwai abinda ke damunta a zuciya,saita sake kallon nata sannan tace
"Ba abinda yake damuna yaaya,kawai ina sha'awar yadda kike zuwa makaranta abinki,sai nakeji a raina dama nice ke,inason naga na iya karatu da rubutu irin naki,inason na zama likita nadinga saka fararen kayan nan,ina yiwa mutane allura" daga yadda take maganar zai gaya maka har cikin zuciyarta da gaskene,hakan saiya kashe jikin bilkisu,ta ƙaƙaro murmushi tace
"Hannatu,wannan karatun saboda ku nake,saboda kuma ku samu kuyi karatun nake nawa karatun,karatuna nakune,na muku alƙawarin in sha Allahu nan gaba dukkaninku sai kunyi karatu yadda ranku yakeso,kowa zai zama abinda yakeso da izinin Allah,kudai kuyimin addu'a ko yaya nasamu aikinyi kunji" dukkaninsu babu wadda fuskarta bata faɗaɗa da fara'a ba,wanda hakan ya nuna mata yadda sukeson karatun sosai,saidan kawai babu yadda zasuyi ne,da wannan murnar tabarsu tajawo garin kwakin tasoma kwaɗa musu,kafin daga bisani ta rarrabawa kowa itama tazauna cikinsu sunaci tare tana sake jansu da hira,tare da basu labarin abubuwan da take da burin yi musu nan gaba idan Allah ya hore mata,hakan kuwa yasake faranta musu da basu qwarin gwiwa,kowa yadinga jefa mata tambayoyi tare da sake karanto mata abinda yakeso,bata gaza ba bata kuma qosa ba tadinga bin kowa tana bashi amsa daidai da yadda yakeson ji,tana kuma cike da fata a cikin zuciyarta ta cika musu mafarkansu.


Cikin raha da annashuwa suke ci kai kace sun samu naman kaza ne,haka kowa yacinye yasha ruwa,cikin ikon Allah dayake ba wani ci ne dasu ba duka sun ƙoshi alhmdlh,sannan tasake gyarawa ta ɗauki hijabinta tamusu sallama tawuce wajen aikinta,bayan ta jadda musu banda yawo,ana kuma idar da sallar magariba dukkaninsu suwuce makarantar magariba,itama sai an taso daga makarantar dare sannan zata dawo gida.


Tunda tafito daga gidan nasu ta fuskanci layin nasu cike yake da jama'a,a rayuwarta bata ƙaunar irin wannan ranar da samarin layin nasu kan zauna su kafa dandalin hira,wanda yawanci duka bai wuce zancen wane da wance,meyake faruwa a wannan gidan,wancan gidan me ake ciki?.


Hakance kuwa ta kasance,don tunda ta doso majalissar aka sauya topic ɗin yakoma kanta,matashi nafarko da ake kira auwali shiya soma tankawa
"Tubarkalla ma sha Allah,kaf unguwar nan....kai bama unguwar nan ba,nidai a rayuwata ban taɓa katarin ganin yarinya mai ƙuruciya da kyau irin yarinyar nan ba" wani daga can sashen ya cafe zancan
"Sai rashin dace da uba da tsantsar rashin gata da talauci ba....kaini wallahi ban taɓa ganin asararren mutum irin ubanta ba,Allah yabaka kadarar yara mata amma kayi watsi da ita?ita kadai wannan yarinyar kadarace,ba qaramin jari bace a wajensa amma bai sani ba"sai wani shima ya kama
"Ai yarinyar nan wallahi inda ace ni wani shege ne da tuni na saka kai nayi wuf da ita,kai wannan idan tasamu wani hutun dajin daɗin aiba ƙaramar mace za'ayi ba" sai sauran sauka sanya dariya,wani daga ciki yayi hanzarin katsesu
"Kai gatanan fa takusa isowa,kada kusata ta tsargu da Allah,waske kawai".


Dai dai lokacin da abubakar saddiƙ ke tsaye daura dasu,jikin wani shago daya siya kati ya tsaya yana lodawa,dukkanin maganganun cikin kunnuwansa sukayisu,baiko ɗago ya dubesu ba saboda hirar tasu sam batayi masa ba,hakanan yasamu kanshi da sha'awar ɗaga kai yaga wacce halitta suka sanyawa idanu haka,daidai sanda yagama sanya digits na katin ya dannan request kana ya ɗaga kai yana kallon sashen da yake tsammanin tanan ta taho.


Baisan ya akayi ba,baisan me yasa yasamu kanshi da binta da kallo ba kamar sauran,duk da cewa baya cikin ɗabi'arsa sam,saiya lumshe idanunsa kana yabude sanda ta tserewa ganinsa,kunnuwansa sukaci gaba da jiyo masa hirar samarin suna ci gaba da ɗorawa daga inda suka tsaya,hakanan yaji bazai iya jurar ci gaba dajin abinda suke faɗa a kanta ɗin ba,saboda haka ya taka zuwa inda ya aje motarsa ƙirar kia ƙarama mai ƙofa hudu yabude yashiga yazauna yana kiran wanda yasanya kuɗin saboda shi.


Sun ɗan ɗauki tsahon wasu mintuna suna magana dashi kafin su kammala,ya datse kiran yana sauke numfashi,hakanan saiya samu kanshi da gaza tafiya yana sake nazari kan wasu abubuwa,daga bisani uzurin dake gabanshi yasanya tilas yakunna motar yana barin layin,saidai yanaji ajikinsa tabbas lallai akwai yiwuwar dawowarshi unguwar nan gaba.


Kamar kullum aiki tasamu sosai gidan umma luba,tunda ba kasafai take iya tsaiwa ta kauda komai ba agidan,don wani lokaci sammakon fita take wajen aikin nata,musamman idan akwai wani abu da za'a gudanar ko wani aiki na musamman.


Bata damu ba don ya zame mata jinin jiki,ta zage tayi dukkan abinda ya kamata,kafin wani lokaci gidan yakoma hayyacinsa sannan ta ɗora mata girki kamar yadda tabar mata sallahun ta girka ɗin amma kuma kaɗan,don ba kasafai ma ake mata girkin ba,saboda yawancin lokaci zuwa lokaci takan taho da lafiyayyen abinci daga can gidan aikin nata,har itama wataran idan rabo ya rantse takan samu.


Tana tsakar gida bayan ta idar da sallar magariba tana addu'ar Allah yashigo da umma luba yau da wuri don tasamu zuwa makarantar dare,saboda yau zata bada haddar akhdari da sukeyi,addu'arta taci,don kuwa ana gab da soma kiran sallar isha'i sai ga sallamarta.


Cikin girmamawa bilkisu tamiƙe tana mata sannu dazuwa,ta amsa fuskarta a sake da fara'a tana cewa
"Sannu mai gado da aiki" murmushinta mai sanyi tayi ta amsa
"Yauwa sannunmu"
"Wayyo Allah makashin kakata" tafada tana sauke uban faggon kayan dake daure a kanta bayan tasamu gefan abun sallar bilkisu ta baje,da alamu a gajiye take sosai
"Bani ruwa in soma sha don Allah bilkisu,ki zubomin abinci yau a tsaye muka wuni,hidimar tafi ta kullum yawa" saita miqe a nutse takawo mata ruwan da abincin,sannan tasamu waje tazauna,tana jira ta sallameta tawuce.


Tana cin abincin tana sakowa bilkisun hira,duka kusan na gidan aikinta ne da irin ayyukan yau da sukayi,umma luba badai surutu ba,sai kuma akayi katari ita bilkisun bamai yawan son magana bace,amma duk da haka ita bai dameta ba,duk sanda taso hira takan zauna tayita zuba mata labarine koda da murmushi zata amsata bata damu ba,a haka harta gama cin abincin ta wanke hannu sannan bilkisu tamiqe tana jawo takalmanta
"Umma zan wuce gida"
"A gurguje haka,ki tsaya yau Allah yayi albashinmu ya iso kema na sallameki,nasan kina da buƙatu da yawa...kai wannan rayuwa Allah ya iya mana"ta qarashe fada tana tabe baki,bata amsa ba sai komawa da tayi tazauna tanajin ranta yana mata fari,don ba ƙaramin jin daɗin samuwar kuɗin tayi ba.


Jakarta ta rataye data shigo da ita ta janyo,ta zuge zif din tana fidda sabbin kudi ƙar daga ciki bakinta har kunne tana cewa
"Ai in gaya miki yau shar damu,albashi harda ƙari,wai amma ƙarin da muka samu mu samu mabuƙata dake cikin anguwrmu muyi musu sadaka....kinji fa,saikace mu ba mabuƙatan bane,ai babbar buƙata kawai najisu a lalitata,atoh"ɗan murmushi bilkisun kawai tayi,don ita zancan bai burgeta ba,don wannan tana ganin yashiga nau'in ha'inci,tunda tamkar an amince maka ne an baka wani aiki amma ka gaza cikashi,banda hakama ita kanta shaida ne su umma luban suna ƙaruwa sosai da gidan da suke aikin,saboda ana yawan musu kyautar abinci ɗanye akai akai,harshi kansa kudinma koda ba lokacin albashinsu bane,hakanan suturu babu laifi masu tsada tana dasu duka silar gidan aikin,amma dayake ɗan adam ɗan adam ne,batasan mesuke da buƙata ba kuma.


Kuɗin aikinta cas ta irgo ta bata
"Ungo riƙe nan,ga kuɗin watanki saura na wanki"hannu biyu tasa ta karɓa kamar kyauta ta bata tana godiya,sannan ta sake irgo wasu ta bata
"gashi wankin ki na dubu ne da ɗari biyu" sosai taji daɗin ƙarin,don bata tsammaci zata samu har haka ba
"Na gode"
"Nice da godiya ai mai gado,saboda yadda kikemin ɗin nan sai ƙalilan masu amana,tsahon lokaci ko cokali ban taba nema na rasa ba ai kuwa kinga ba duk mutum ba....ungo cikin kuɗin sadakar dai na bada wani abu,aidai nayi tunda na fitar komai qanqantarsu" dubu daya tasake miƙa mata,data hada kuɗaɗen hannayenta sai taga ta kusa tasamma dubu biyar,abinda ba zata iya tuna yaushe ne hakan tafaru ba,riqe kudi masu yawa har haka ba.


Harta miƙe ta sake dakatar da ita
"Sake zama ƴarnan ki dangwali alfanun riƙon amana"tayi magana tana janyo ƙullin uban kayan data shigo dasu tana sake cewa
"yau muma mun dangwala mun dangwala harmun godewa Allah,kayan ɗiya kuma jinin sarauta yauni luba a hannuna,muma zamu raɓawa jikinmu irin suturarsu,muji abinda suke ji,wannan karamci nasu ya isa". Tana maganar tana kokawar bude qullin kayan.


Tana kwance kayan wani daddaɗan ƙamshi na musamman ya bule wajen,kayane faggo guda kamar za'a sunce dila,namijin ɗaurin da aka masa yasa baka ganin yawansu sai an bude.
7/11/21, 4:28 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAD'IN RAYUWA* 👑



*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*


*_Wannan littafin na kudine kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data dace cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,babu cigiya,babu a dauko mana_*


09032345899
Ko
09033181070


*_KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.._*



5


"Zauna ki lissafa duka ƙannenki ki zabar musu kowa yasaka,yau fulani inajin juyen kayan drower ɗinsu sukayi....ki zaɓa na saida na saidawa,na bada na bayarwa,don ba shakka waɗan nan kaya yadda suke fes kamar ba'a sanyasu ba ƙaramin kuɗi zan samu dasu ba Allah mai gado" murmushi takuma saki wannan karon mai sauti,tana sake jinjina son kuɗi irin na umma luba,kayane masu asalin kyau daraja da tsada,wanda duk wanda ya kalla koda bakasan kuɗinsu ba amma kasani ba masu
ƙarami ko matsakaicin kuɗi bane,tanajin umma luba naci gaba da sambatu gami da bata labarai,ta tsugunna tana duba su hauwa'u tana zaɓarwa kowa,duk da sauran tasan sun musu yawa amma haka ta ɗauka musu,tana kintatar zata bayar a maida musu dai dai jikinsu.
"Ana abu a masarautar KAISA,wani abunma sai jibi idan Allah yakaimu" takai ƙarshe tana sakin guɗa,da alamu dai cikin nishadi take yadda ya kamata.


Sunan masarautar dataji ya fito daga bakin umma luba sai taji duka kayan sun fice mata arai,AFNAN itace abu na farko daya soma faɗo mata a rai,kenan kayan sjn fito ne daga gidansu?,wala'alla ba za'a rasa nata a ciki ba,sai taji kamar ta barwa umma luba kayan,amma hakan bazai yiwu ba,saboda niyyar alkhairi tayi a gareta,dole ya hade kansu ta bata leda babba ta saka ta mata godiya kana tafito.

Kamar yadda ta qudirta din bata koma gida ba sai data shiga makaranta ta bada haddar dake kanta,saboda bata son ta rasa rana daya cikin ranakun zuwanta makaranta,musamman da a yanzu suke gab da kammala haddace qananun litattafan addini su tafi zuwa manyan,ba qaramin dadin karatun takeji qwarai da gaske,koda yaushe takan godewa Allah wanda bayan ya hanata wasu abubuwa na rayuwa amma bai hanata hasken ilimi da qaunarsa ba,ba ita ba koda qannenta a yanzu ba zaka kirasu jahilai ba ta fannin addini,tunda alhmdlh dukkaninsu suna zuwa makarantar Allo da safe,suje ta magariba bayan sallar magariba.


A hanya take tunanin abinda zata siya musu suci,saboda tasan bata bar musu abincin dare ba,hakanan babu yaqinin za'a basu suci,taso siya musu wani abun amma duka abinda ta lissafa zaija kudine,sai taliyar hausa ta fado mata a rai,idan ta siya kuma akwai bata lokaci kafin dahuwarta,mai yiwuwa su qosa ko wasu daga cikinsu ma suyi bacci,saita wuce gida kawai tana fatan asamu sauran abincin sayarwa wajen umma katti,tunda ba'a rasata da saura.


Tun daga soron gidan mamaki yacikata fal jiyo muryar mahaifinsu yana hira cikin walwala da dariya
"Allah hakimu,yau kuma wanne manzan rahamar aka saukar mana?" Tayiwa kanta tambayar zuciyarta cike fal da taraddi,ba zata iya tuna lokaci na qarshe data jishi cikin irin wannan yanayin cikin tsakar gidansu ba,idanma zata tuna din zata iya cewa tun aurenshi na qarshe da yayi suka rabu,da wannan tunanin ta qarasa kutsa kai cikin gidan.


Bata sake daskarewa ba sai data ganshi tsakiyar yaran,ko ina farantai nashe nashe da shinkafa da miya kowa na kaiwa baka,data lura dakyau ma sai take ganin kamar tsokokin kaji saman abincin,a haka ta dinga takowa idanunta akai,tana jin tamkar mafarki take
"Ke meye hanka,kalli gabanki mana,idan kuma yunwa kikeji kije ki amshi naki abincin wajen kattime" muryar mahaifinta kenan dake magana yau cikin cikakkiyar isa sabida cikakken awo da cefanen da yake ganin yayi,maganar tashi taja hankalin 'yan uwanta kan shigowarta,dukka suka bar abincin sukayi wajenta,wasu suna mata sannu da zuwa,yayin da wasu keta faman nuna mata rasha da gwabar da yau suka samu a gidan nasu,wanda sun manta rabonsu da samun koda arziqin fara damai da gishiri bare miyar kaji,wasu daga cikinsu ma namam suketa tura mata taci,saita maida hannayensu cikin sanyin jiki,don ita sam abun bai mata ba,hakanan bai burgeta ba,suma don basu gama sanin ciwon kawunansu bane,ta tabbatar da walakin,hakanan akwai wata a qasa,cikin tattausar muryarta da take tsarin halittarta tace
"Na gode,maza kuzauna kuci"
"Kujimin ja'iran yara,yo itama da nata kason ai,banson kilbibi idan zaku zauna kuci ku zauna" baban nata yakuma fada,duk sai suka zauna sukaci gaba da cin abincinsu.


Sai a sannan tadubi sashen da baban nata yake a ladabce tace
"Barka da wuni baba,an wuni lafiya"
"Lafiya lau,sai yanzu kike dawowa?" Ya fada kamar yana ganin takai dare da yawa,kai ta jijjiga kawai
"Eh....na tsaya makarantar dare ne"
"To madalla" ya amsa yana afa

Please Login or Register in order to submit comment