Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka ce wallahi basu Sani ba amma an tashe su,gabad'aya hankalinta ya tashi gashi har ana nema a kira isha'i da yake yayansu yana gari nan da nan aka shiga nema,mai iccen unguwar tasu ne ya bayyana musu abin da ke faruwa anan cikin wanan maganar saiga su Ashfa a adaidaita sahu ita da wanan bawon Allah ya dawo da ita gida...


Har tsakar gidan su Ashna ya shigo ya tsugunna yana tabawa inna hak'uri tace wallah babu komai ai tsautsayine Allah ya tsare gaba.

Murmushi yayi sanan ya ajje musu dubu biyar yace ta d'an sai maganin da ya dace bayan fa anbata magani a asibitin inna tace bazasu karb'a ba haka ya DAGE sai sun karb'a aikuwa inna tace angode madallah Allah ya saka da Alkhairi, har ya wuce suna kallan kallo da Ashna yana kawo ido zasu had'a sai tayi saurin kufcewa saboda wani maganad'insu dake shiga tsakanin..


Yana fita yayi Murmushi mai kyu sanan yaje inda ya ajje lifan d'in nasa ya d'auka ya k'ara gaba.....



Khalid ne yace"wow kaga wani balaraben mutum ni wallahi NADAUKA ma Anty baya jin hausa,dukkaninsu sukayi dariya inda suka bar Ashna cikin tunani....




Vote,share, and comments fisabillilah.✍🏻
[11/16, 18:27] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*



*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/


*Page 25_26*

Kwana Ashfa d'aya a gidan su inda tace bama sai yazo ba zata dawo sa kanta dan kar yazo gidan su,aikuwa haka akayi ta tari keke napep ya kaita har k'ofar gidan ta,ta sauka ta zuge jaka ta bashi jud'insa ita kuma ta bud'e get d'in ta shiga gidan.

Daman ya fad'a mata tunda ya ajje ta shima bai koma ba dan yace shima bai kwana anan ba.

Dayake da daddare ta dawo hakan bai bata damar ganin wasu bak'in al'amura ba a gidan nata,haka shima ya dawo musu da takeaway suka ci abincin restaurant dan kuwa ita tace bata iya girki dan ta gaji. Haka suka shema hankalin sa kwance yake ta barci har asuba sanan suka tashi suka yi sallah suka k'ara komawa,basu suka tashi ba sai k'arfe 11:00pm tashi MALIYA yayi da mik'a sanan ya juya ganin Ashfa yayi shame² da alama ma bata tashi tayi masa abinda zai ciba...


D'aka mata duka yayi a cinya da sauri ta ware idon ta tare da Jan tsaki"haba dan Allah Malam mene haka ina barcina fisabillilah zaka tashe ni mtwsss nifa banason irin haka."
"Ke dalla dakata min,kinzo kin kwanta sai uban barci kike to uban wane zai girka abin da zanci har in tafi wajen aikina."
Zabura tayi cikin hanzari ta bud'e ido had'e da fad'in" kan uba ni kake zagi akan nace maka bazan iya girka maka breakfast ba ahhh lallai MALIYA. "


Basar wa yayi yace "mantas kawai yanzu dai abani ruwan wanka sanan ko tea ne ki had'a min matata."
"Hmmm mtwsss aikin kawai." Ta fad'a taba sakkowa daga saman gadon had'e da Jan tsaki.


Bayan tayi komai ta zauna ne sai ta lura cewa bata ga akwatunan taba,kai abu kamar wasa nema yake ya zama gaske ta duba ko ina sama ko k'asa ta nemi akwatuna da kayan dake cikin akwatunan amma sunce d'auke mu inda kika ajje mu. Wani uban ihu ta kurma tana fad'in"shikkenan sun talauta ni shikkenan sun kassara ni b'arayi sun shigo sun sace min kayan lefe.

Tayi dab'as a k'asa tana ta kuka kamar an aiko mata da mutuwa da sauri kamar ta tuna da wani abu zumbur ta mik'e ta d'aukko wayar ta ta dannawa MALIYA kira.


"Sun cuceni sun kassara ni wayyo ni." Haka take ta fad'a yana sane yasan kan zance amma yayi kamar bai Sani ba yana fad'in" na shiga uku lafiya lafiyar ki kalau Asfa,lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya b'arayi sun kassara ni sun hauro jiya sun sace min kaife."
"Whatttttt?"
Ya fad'a irin a mutuk'ar razane d'inan..

"Ok,ok,gani nan zuwa."


Baifi minti goma ba sai gashi da Ado da Musa sun zo haka suka k'araci jajanta musu sanan suka tafi,haka aka zarce kwana uku kullum Ashfa sai tayi kukan bak'in ciki hardai ta dawo ta sama wa kanta sauk'i...




Zaune yake saman tabarma itama ta zauna saman tabarma suna ta magana mai amfani dan kuwa Ashna da Muhammad tuni sun had'a kansu duk da dai bata tab'a furta masa kalmar soba duk da irin son da yake fad'a mata yana yi mata ba ita ba harta da y'an gidan su sun sheda wanan yau kimanin wata shida kenan da had'uwar su da Muhammad tasan cewa tabbas tana sonshi kuma ta SHAK'U da shi,amma saidai abu d'aya ita tana da kunya sosai har yanzu gani take yayi wuri ta fad'a masa kalmar so..

"am Ashna ina so kimin wata alfarma guda."
Muhammad yace yana sake gyara zama.
"Ina jinka yaa."
"Uhm ina sonki,kinsa ni ina mutuk'ar k'aunar ki ban tab'a ganin macen datayi min sama dake ba Dan Allah kibani dama na turo magabata na ayi maganar auran mu."


Gabantane ya yanke ya fad'i dakyar ta aro y'ar nutsuwar data iya ce masa"shikkenan yaa zanyi tunani."
"Ok zuwa yaushe?"
"Uhmm zan dai fad'a maka." Tafad'a tana sunkuyar dakai.
Dariya yar kad'an yayi sanan yace"shikkenan fulani ina jiran amsarki,ki Sani baccina takaitaccen har sai naji kyakkyawar amsar da zata fito daga bakin ki.
"Shikkenan yaa kar ka damu."




Bayan ta shiga gida ne ta samu su Inna suna zaune suna fira. Zuwa tayi ta kwanta saman cinyar inna sanan ta bud'e kanta tana mai fad'in"inna dan Allah cigaba da tsefe min kai,kinga sumayya ta fara amma bata k'arasa min ba." Dariya inna tayi tana karb'ar kibiyar tana magana"ikon Allah kenan ke bazaki iya tsifar ba har sai an miki."
"Aa inna ba haka bane kawai dai nagaji ne."
"Hhhhhh mai kika yi kika gaji."
" inna kenan."
Dukkaninsu dariya suka sa,sanan Ashna tace"inna kinsa maike faruwa."
"A'a Ashna ina zan Sani ai sai kin fad'a."
"Wai shine have yanaso zai turo."
Inna tayi dariya tace"shi wa kuma."
"Kaiii inna yaaa fa."
HHHHH bashi da suna ne"
"Uhm Muhammad junior."

"To Ashna ke kuma mai kikace dashi."
"Nace sai nayi shawara.


" duk macen data samu kamar junior a matsayin mijin ta to ina da tabbacin tayi sa'a kuma ba kowace mace bace junior zai zo a matsayin hana sonta da aure ta guje masa mutum mai nagarta kirki mutunci gashi yana da sana'ar sa daidai gwargwado idan Muhammad ya arure ki to zan kasance cikin farin ciki da MURNAR cewa yarinya ta tayi dace da samun miji nagari wanda ake kira da mijin marainiya...



Shiru Ashna tayi batare datace komai ba amma taga mutuk'ar farin ciki a fuskar inna tabbas koba komai ahalin ta zasuyi farin ciki,Muhammad zan aure ka saboda farin cikin ahalina shine nawa ni har yanzu bansan mene soba amna inajin nayi mutuk'ar shakuwa dakai tamkar mun dad'e a tare zan aure ka dan farin cikin ahalina....




Kwance take taukam takasa barci kawai tunanin sa take" duk macen da ta samu miji tamkar Muhammad to tabbas zatayi rayuwa mai inganci a gidan Auren ta,rayuwar mace tana lalacewa ne sanadiyar rashin samun miji nagari idan mace ta AURI miji nagari ko wace ita to tabbas rayuwar ta zatayi kyu zata zama abar sha'awa a wajen yan uwa,amma tabbas idan kika had'u da aka sin haka zaki rayu cikin bak'in ciki ne mara misaltuwa Allah ya had'a da miji nagari."



"Inna yaya ake gane miji nagari?"

"Miji nagari ya banbanta da sauran mazaje,shine wanda zaisoki a duk yanda kike zai kaunace ki har iya k'arshe rayuwar sa,zai fifita buk'atunki akan nasa,koda baya tare dake bazai tab'a bari ki wulak'anta ba,zai kare mutuncin ki da iya k'arfina dukiyar sa da komai nasa,shine wanda idan kika nuna kina son abu muddin bana cutarwa bane zai fiki jin son abin a cikin ransa daidai sauran su.....





Juyowa yayi ya watsa mata wani kallo sanan yace" Ashfa zaki iya tuna watan mu anan gidan ina nufin wata nawa kenan da AURAN ki?"

"Ban gane ba wanan wace irin tambaya ce,ai kafi d'an dako sanin hanyar Tasha."

"Ok dakyu to gidan nan bana ubana bane kuma kema ba na tsohon ki bane dan haka ki tabbata kin tattara kayan ki zamu sake gida daman wata shida mai gidan ya bani haya daga haka ba k'ari dan haka ko kice Abban ki ya samamana wani wajen zama ko kuma duk inda ya samu wallahi na watsaki tunda naga kamar shid'in kawai dai kud'in Allah yayi masa amma ba zuciyar yi........
[11/16, 18:27] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*



*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/


*Page 27_28*

"Kam bala'in nan van gane abin da kake nufi ba,MALIYA fito min a mutum dan ban gane inda ka dosa ba?"

"Ok baki gane inda na dosa to lallai tabbas zaki gane,abin da nakeso dake shine kafin nan kafin gari ya waye ki tattara komai,ji yanda kika maida musu gida dan Allah da k'azantar ki yanda kika San munyi shekaru a cikin gidan nan,ke kawai kiyi wanka kisa kaya kika Sani babu abin da kika iya sai shashan ci to wallahi bazai yiyu ba da sake."

"Ahayyye dad'ina da gobe saurin zuwa yanzu ni kake fad'awa irin wanan magan ganun MALIYA, ahhh lallai sai yanzu nake yarda da maganar nan da ake cewa duk wacce ta d'auki miji uba tabbas wallahi sai ta mutu marainiya,na shiga uku MALIYA yaushe akai daren harda gari zai waye?"

"Ohhhh wanan like tambaya ta ai tuntuni Roman yabar kan kazar ina fatan kin gane mai nake nufi."


"Kamar yaya ban gane ba."

"Zaki gane zaiki bayani mtwsss. Ya fad'a had'e da bangajeta ya shige ya fita..

Sororo tayi tana binshi da ido tace lallai kam yau sai anyi ta ta k'are kutttt har ni yake da bakin da zai cimin mutunci wai gidan haya ni zai kama wa gidan haya nashiga uku mai hakan yake nufi. Ita duk a tunanin tama sai yau ta tunano y'an uwan MALIYA basu tab'a zuwaba tunda ta aure shi banda abokinsa Ado da Musa babu wanda ta Sani nasa gashi ta d'auka tazo gidan Arzuk'i amma ina sai taga k'andas gidan ne kawai yanzu kuma dan rainin hankali yace nata ba gidan sa bane to wallahi bari ya dawo saidai ya kaita gidan babansa dan idan tavar gidan nan yasin bazata koma wani ba saidai ayi yadda za'ayi....



Shiru² har k'arfe sha biyu MALIYA babu shi babu dalililnsa hakan yasa hankalin ta ya d'an fara tashi...



Shi kuma MALIYA yana fita ya fara tafiya kawai bai ankare ba mota tayi sama dashi ta dawo dashi k'asa hakan yayi sanadiyyar sumewar sa idan akaishi asibiti cikin gaggawa...



Abun yayi mutuk'ar bata mamaki ina yaje haka da bai dawo ba har wanan lokacin itafa bai tab'a mata haka ba,haka dai kusan a zaune ta kwana washegari da safe taji wayar ta tayi k'ara..


Juyowa tayi ta d'auka ta kara a kunnen ta"innahlillahi take ta maimaitawa mijin ta yayi hatsari yanzu haka yana emergency tabbas bata ga ta zama ba.


Da sauri ta d'auki hija d'inta ta maka ta fito a har gitse ta nufi asibitin daka fad'a mata yana nan can asibiti murlata ne b'angaren y'an emergency ta nufa aikuwa ta hango Ado da sauri ta k'arasa inda yake tana tambayar sa mijin ta...


"Kiyi hakuri ya samu hatsarin mota ta bige sa ne amma dai insha Allah muna sa ran farfad'owar sa likita yace zuwa nan da kwana biyu sanan ya samu Kara guda biyu a hannu da k'afa...


D'aura hannu akai tayi tana kiran nashiga uku na lalalce karaya...


Sosai Ado ya ringa bata hak'uri yana kwantar nata da zuciya har tayi shiru..


Bayan kwana biyu bai farfad'o ba ita take ta zarya amma ta sanar da inna yau shine sukace zasu zo su duba sa dan yau saura wata uku bikin Ashna da yake ba zuwa take ba shiyasa suma basa wani zuwa...



" wai ni Ado in tambaye ka dan Allah kafad'amin gaskiya."

"Ina jinki Ashfa."
"Dan Allah ina iyayen MALIYA da danginsa suke yau kwana mu biyar fa anan har yanzu baya hayyacin sa kuma haryau banga koda yaro karami yazo azuwan familyn sa bane."

Dam k'irjinta Ado ya buga a hankali ya tattaro nutsuwar sa inda yace"ina mai baki hak'uri Ashfa zan fad'a miki gaskiya amma ba yanzu ba...


Zatayi magana doctor ya kirasu yana cewa "ALHAMDULILAHI yaudai TUKUR ya farga masha Allah kuma da alamun nasara."
Ashfa cw ta gyara tsayuwa sana tace"TUKUR likita wanene kuma TUKUR?"

Kafin Dr. Yayi magana tuni Ado yace yanzu ba wanan lokacin bane zao muje kawai..


A tare da su inna yau da suka jera kusan kwana uku kenan suna zuwa ita da Ashna suka nufi d'akin da dr. Yace yanzu yana can,suna zuwa suka tarar allurar bacci ce take saikin sa amma abin mamaki sai cewa yake"Gwaggo,gwaggo,kaka, kaka,Baba,Baba, kuuuu..yaa..feee..min..,mutuwa...zan..yi."


Too Ashfa ce ta rik'e baki a zuciyar ta tana cewa su wane kuma haka...


A hankali a hankali ya fara bud'a ido dakyar ya d'aga ido ya dubi inda Ado yake yace"Ado inaso ka kaini k'auyen ina buk'atar na nemi yafiyar gwaggo da kaka da baba, wallahi ji nake kamar ana tsomani a ruwan zafi saboda radad'i da azaba na bijire musu na tawo birni nak'i jin maganar su...



Ashfa data rasa gane ma inda zancen mijin nata ya dosa ce ta kurma ihu take ta zube a wajan wanwanr tamkar wata gawa......



Da sauri su inna da Ashna sukayi kanta Ashna tana kuka inna tana salati haka suka shafa mata ruwa aikuwa dakyar ta farfad'o tana sauke ajiyar zuciya...


MALIYA ne ya juyo ya dube ta yace"kiyi hakuri Ashfa na yaudareki na yaudari Abban ki,kuyi min aikin gafara wallahi Ashfa bani da komai niba kowa bane kawai dai rud'u ne irin na duniya sanan kuma da biyewa San zuciya shine ya kawoni nan...



"Ahhhh MALIYA karkace min haka dan Allah ban gane abin da kake nufi ba Dan Allah karkace min baka da komai k'arya kake min tayaya hakan zata kasance dan Allah kar kace min haka." Tafad'a tana k'ara rushewa da wani rikitattan kuka... Ashna ce ta kamo hannun ta tana lallashin sa tana bata hak'uri maganar innace ta katse nata kukan ta.



"Ashfa da TUKUR kenan ai daman duk abinda za'ace an ginasa bisa tafarki nasan zuciya to tabbas abin nan bazaiyi k'arko ba hak'ik'a ba kai kad'ai ne ka yaudare taba itama ta yaudare ka Ashfa gaki gashi ba karyace k'aryace ki fad'a masa gaskiya ki fad'a masa ke wacece mahaifinki wanene.....??
[11/16, 18:27] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*



*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/

*saidai kuyi min afuwa masoyana banso na tak'aice muku wanan labari ba,amma yanayi ne yazo da haka ina fatan ZAKUYI min afuwa tunda har na isar da darasin da nake son isarwa Allah yasa mu amfana da abin da muka karanta.*😍



*Page 29_30*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚

"Tabbas ranar wanka ba'a b'oyen cibi." Ashfa ta fad'a hawaye yana ta ambaliya a kuncin ta.
"Ka yimin afuwa nima MALIYA mun d'aukko tafarkin da bazai d'aure ba shine na k'arya ka karya min zuciya nima na karya maka na maka karyar iyaye ko dan vantaka hak'ik'a banda dangantaka da su Rukky illa k'awance dake tsakanin mu nid'in y'ar gidan talakawa ce amma Sam ban tsaya a inda Allah ya ajje niba na kasance mai hangen nesa duk da cewa a gidan mu munfi karfin ci dasha sanan iyayen mu suna mana suttura daidai gwargwado,iyayena sun bani tarbiyya indai nayi watsi da ita na biyewa San abin duniya yanzu gashi yanda rayuwa tazo mana hak'ik'a naji haushi nayi danasanin bijirewa maganar MAHAIFIYATA da kuma ta ahalina nayi,amma ina rok'on Allah ya yafe min abubuwan da na aikata Allah kuma yasa iya kacin jarabawar mu kenan,duk da haka rayuwa tazo min zanyi hak'uri bazan sauya kaba MALIYA Allah shine mai azurta bayinsa Allah ya azurta mu..



Jin abin take tamkar a labari dan kuwa tunda ta shigo tayi sallama basujiba gabad'aya hankalinsu ya tattaru waje guda hakan yasa itama hankalinta ya dawo kansu tabbas labarin yayi mutukar bata mamaki kamar a tatsuniya sun Gina auren su ta hanyar k'arya da San abin duniya. ALLAH sarki rayuwa sai ta tuna da uncle da matar sa,wai Allah da har ina neman inyiwa kaina,duk na dauka MALIYA yana da amana amma ina hmmn Allah ya kyuta... Byana ta dawo daga tunanin tane tayi gyaran murya nan suka kula da ita,gaisawa tayi dasu sanan tayi musu ya mai jiki bayan wasu mintuna ta ajje musu kud'in ta juya abin ta...




" Hello Afnan,muna nan clinic ciwon uncle ya tashi ki fad'awa Hajiya." Hajju tace batare da tajira abin da Afnan d'an zatace ba ta katse wayar dan yanzu haushin Afnan take ji tana ganin zai mutu amma baza ta tai maka masa ba a dalilinta na banza. Cewar hajju a zuciyar ta..


Murmushi Afnan tayi sanan tace "tabbas zanyi wanan dan ahali Allah zai bawa uncle lafita kuma na amince zan aureshi. Karaf a kunnen hajiya.

" Afnan kin amince zaki AURI uncle. "
"eh Hajiya hajju ta matsa gashi har ciwon sa ya tashi na amince zanyi wanan dan Ahali."
"Shikkenan ba komai Allah yayi miki Albarka ya had'a KANKU duka ya baku zaman lfy."




Bayan watanni uku da yayi a asibiti sai suka bashi sallama inda agida zai karasa jinyar..


Tuni mai gidan haya yasa an musu parking d'in katansu a gidan su Ashna ya dank'arawa gidan sa mukulli ya kulle haka MALIYA yace yanaso suje garin su,sai ya k'arasa jinyar acen yanaso ya rok'i iyayen sa su YAFE masa,aikuwa bayan kwana bakwai da dawowar su daga asibiti sukayi shirin tafiya harda ado,inda suka nufi hanyar garin su MALIYA, tafiya ce sosai dan kuwa da nisa aka shigo wani gari mai suna dama gari sanan suka hau babur ya kaisu k'auyen su MALIYA Ashfa taga tashin hankali yanzu daman a wanan k'auyen dajin yaje rayuwa tabbas taga rayuwa haka suka sauka a gidan su MALIYA y'an k'auyen sai zuwa kallon su suke anga dai canji sosai a tattare da MALIYA gashi da wata balarabiyar mata acewar yan k'auyen amma fa k'afarsa har yau nan nad'e take da fulasta har a hannun sa.



ALLAH sarki rayuwa duk iya rashin jin da yayi da mamansa ta gansa saida tayi kukan farin cikin ganin sa dan su atunanin suma ga mutu,haka ya ringa kuka yana neman yafiyar ga kaka nan tak'ara tsufa bama ga gani sosai amma tana jin muryarka sa ta gane ya nemi tafiya sosai yace yana so yaga Baban sa ya nemi yafiyar sayar masa da gona da yayi ai kuwa nan sabon kuka ya b'arke dan Allah yayiwa Baban sa rasuwa shekara guda kenan,Allah yaji kansa ameen.





Ashfa taga rayu dan kuwa saida suka shekara a k'auyen sanan yace zasu dawo kano yaci gaba da buga bugar sa haka sukayi sallama da su gwaggo tana masa fatan nasara da Allah ya bayar da abin da akaje nema suma hawo mkta zuwa kano.




Duk wanda yaga Ashfa a lokacin nan sai yace ba ita bace dan tayi bak'in wahala ta rame gashi Allah ya azurtata da haihuwar y'a mace watan ta uku,tayi wata kala tamkar dai y'ar k'auyen...



Gidan su suka nufa sai abin ya bata mamaki ganin wata mata zaune tana ta kuka kayan miya,tambaya tayi dan Allah ina matan gidan matar tace ai itace matar gidan,saida tace tsohuwar matar gidan sanan aka ce mata ai sun tashi amma babu nisa inda suka koma layi biyu ne a bakin titin gidan yake bata gane ba dai saida y'ar matar tarakasu wani katafaren gjda wanda daga gani kasan an shimfid'a naira naira ta kwanta.


Murmushi Ashfa tayi sanan tace"a'a yarinya gaskiya inaga biki gane kwatancen ba."

Yarinyar ce tace"wallahi nan ne ba gidan su Khalid ba da sumayya da Ashna amma tayi aure."

"Eh nan."
"To wallahi nan ne."

Haka suka kwankwasa mai gadi ya bud'e musu shi ya d'auka ma bara suka zo,har zai koresu daidai kuma lokacin inna ta fito tana wa mai gadin magana, kana ganin ta zakaga yanda hutu ya tsarata amma har yanzu hankalin ba akwance yake ba sakamakon har yau bata da labarin Ashfa.


Da sauri Ashfa tayi wulli da jagarta ta ruga da gudu wajan inna tana rungumeta da kuka.
Itama innar kuka take nan dai suka shiga ciki da MALIYA da yake zare ido ta kuma yarsa da ta kwanto ta ta bashi dan kuka take...


Wani kata faren palor aka sauki MALIYA inda kuma ita suka shiga d'aki da inna tana ta kuka...


Bayan komai ya lafa ne inna ta bata labarin Muhammad Muhammad junior mijin y'ar uwar ta Ashna shine ya Gina musu wanan gida,ashe basu san Baban sa shine rik'e da kamfanin diamond ba,yana da kud'i sosai su kuma yazo musu a talaka ranar daza'ai kaita yace musu kada siyi komai tunda bai samu gidan bayan da zaisa taba da daddare yace ga motocinan zasu d'aukkota aikuwa nan masu jai Amarya sunga ikon Allah dan tsayawa ma fasalta gidan Ashna b'ata bakin yanzu haka dashi da ita da mamanshi suna Dubai dan acen take awo kuma acen zata haihu bayan ta haihu lafita zasu dawo....


ALLAH sarki rayuwa tayi kukan farin ciki ta taya yar uwata murna,inda sukuma aka basu wani b'angaren daga cikin gidan inna daman ya mata girma amma dai matar yayansu ma anan take duk da haka ya ishesu anan suka zauna shi kuma MALIYA yacigaba da fita kanikancinsa yana samu yana rufamusu asiri aikuwa kafin shekara Ashfa ta murmure ta dawo Ashfan ta komai nasu abin Sha'awa gashi y'ar uwar ta Ashna tarik'e ta sosai da amana dan wasu mak'udan kud'i tavawa Ashfa inda take juyawa inda take sarin less a Dubai da sauran su ta kama ma har zuwa suke Allah ya samu su Albarka, haka suka cigaba da rayuwa cikin farin ciki babu k'arya babu yaudara.....




*TAMMAT BILLAH LAIFIN DAD'I K'AREWA ANAN NAKAWI K'ARSHEN WANAN LABARI NAWA MAI SUNA A SAMA,YA UBANGIJI KASA MU AMFANA DA ABIN DA MUKA KARANTA KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH KA YAFE MIN NGD TAKU A KODA YAUSHE REAL HAAJARA ABLA 08130561988.*😍😘✍🏻



*20/11/2021*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment